Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba harda ke dan haka ki zauna tare zamuci."
"A'a kar muyi haka dakai nikam tuni naci nawa tun kafin ma kazo wanan naka ne,dan haka sai na dawo.... Kafin ya samu zarafin magana tuni ta tashi tafara tafiya mai mutuk'ar Jan hankali...


Dakyar ya sauke idon sa daga kallon inda ta bari sanan ya maida hankalin sa kan abubuwan da akayi masa. Haka ya zauna ya ringa ci ba kama hannu yaro,da yake sunyi shi dad'an Auki hakan yabada damar yaci iya cinsa yabar ragowar,text ya tura mata da yagama haka ta dawo palorn suka zauna suka cigaba da fira...


Zuwa ma wanan lokacin tuni jikin Ahsfa yayi sanyi dan kuwa kana kallon sa kasan bawani wayayyye bane,wanan tunanin ta kautar sanan wata zuciyar tace mata,ai daman su irin masu kud'in nan wasu haka suke bazaka tab'a cewa sun mallaki wani abu na'azo a gani ba.


Muje zuwa....


Bayan sun gama firar sune sukayi sallama ya koma gida cike da farin ciki da d'aukin cewa burin sa ya kusa cika...


Kamar ko yaushe haka suka cigaba da waya,take suka fara soyayya duk sanda tayi wanka tazo fesa turaren da yabata sai ta tuna dashi,tace a zuciyar ta turare mai mutukar dad'i da sanyi k'amshin daga alama daman kalar sa masu kud'i suke sh shafawa....



Kamar kullum yauma yana wajan aiki,aiki yake sosai ya du'kufa,kamar a mafarki ya jiyo muryar ta tayi masa sallama amsawa yayi sanan yace" ah madam ce barkan ki da wanan lokacin sannu da zuwa gyara mota za'a miki?"

"Yawwa MALIYA, aa ba gyara nakawo ba wanki nakawo,kasan ina zuwa wajan saloon d'inan dake kusa daku duk bayan wata biyu shiyasa nake kawo ta da kaina."

"Ok ok nagane to bari nazo sai nayi miki."


"Ok shikkenan babu damuwa."


Haka yayi sauri ya karb'i mukullin motar tata ya shiga ya fara aikin sa,yana cikin wanke motar ne yaga wasu mak'udan kud'i da alama dai mantasu tayi dan haka sai ya d'auka ya ajje a wajan sa kafin ya gama wankin idan ta dawo ya bata...



Haka ya kammala wankin motar,saidai k'ash ya manta Sam ya ajje wanan kud'in itama kuma daman ta manta dasu,bayan tazo haka ta biyasa kud'in sa sanan ta shiga mota ta tafi.. Saida yaje gida sanan ya tuna da ajiyar kud'in da yayi a jakar aikin sa,yana dubawa kuwa yaga kud'in suna nan,yanzu ya zaiyi nan take imani ya ziyarci zuciyar sa tabbas bazai tab'a mata kud'i ba zai matar mata da kud'in ta,amma ina zai ganta ita da bata zuwa sai idan Allah ne ya kawota...



Washe gari yaje wajan aiki bayan ogansu yazo ne yake ya sameshi yace" am oga dan Allah tambaya zanyi maka."

"Ina jinka mai ya faru." Oga yace.
"Am daman ina so kamin kwatance gidan su Hajiya Afnan."

"Gidan su Hajiya Afnan kuma,mai zakayi da kwatance?"

"Am oga akwai abin da zai kaini,na mata wanki mota ne sai na manta da wasu kayana a bot sai yanzu na tuna kuma inaso zanyi amfani dasu."

"Taf aikuwa saidai kayi hak'uri Danni ban tab'a tambayar ta unguwar data ke ba,kuma ni bani da number ta balle na kirata,saidai kabari RANDA Allah ya dawo da ita sai ka karb'a...


Haka akayi da MALIYA yayi ta zama da kud'in Hajiya Afnan amma abin mamaki biyar bai tab'a ba cikin kud'in,bayan wata d'aya da faruwar al'amarin a hanyar sa ta zuwa wajan aiki yazo zai tsallaka titi yaga motatar tayi parking tana magana da wani...

Da sauri ya k'araso wajan motar,saida ya bari tagama magana da wanda take magana sanan ya k'araso a ladabacce yace"ina yini madam."
"Lafiya kalau MALIYA ashe ana ganin ku." Tafad'a tana murmushi.

Dariya yayi sanan yace" ina nan madam kune dai kukayi wahalar ganai."
Murmushi tayi sanan tace'gaskiya ne to yakuke."
"Lafiya kalau,am madam tun ranar da kika kawo wankin mota,tun ranar nake tunanin yanda zanyi na had'u dake,sai yau Allah ya had'a."
"Saike kallon sa tayi sanan tace,to Allah dai yasa lafiya."

"Lafiya kalau madam sai Alkhairi daman ranar da nayi miki wanki mota naga wash kud'i da kika fito dasu akan kujerar kika ajje kuma kudad'e da yawa shine na d'auka naajje ajakar aiki na da zummar idan nagama na maida miki,to sai Allah baiyi ba na manta,kuma saida na koma gida na tuna,nayi ta neman inda zan sameki ko gidan ku amma bansamu ba sai yau Allah ya had'ani dake."

Murmushi tayi sanan tace"ayya nayi ajiya sanan na rasa a inda na ajje,to na d'auka madai a d'akina ne shiyasa ma kawai ban damu ba,Allah sarki amma gaskiya kana da amana sosai sai naji ka burgeni."

Cike da jin dad'i yace" nagode madam idan bazaki damu ba,bari naje na d'aukko miki."

"Ahhhh MALIYA kawai ka shigo sai na kaika wajen aikin ,kuma abin da kaimin naji dad'insa dan haka wanan kud'in ka rik'e na bar maka daman Allah yayi rabonkane."

Gigicewq MALIYA yayi ya ringa zuba mata godiya har baisan iya kacin godiyar da yayi mata ba,har saida ta b'ata rai akan batason tayi kyuta a ringa mata godiya haka..


Adaidai danger ne,danger ta tsayar daau suka tsaya,adaidai lokacin kuma Rukky ta d'aukko Ashfa sunje wani supermarket sun dawo suma sun tsaya a wanan danger,daga idon da Ashfa zatayi ta hangi MALIYA da wata kyakyawar budurwa gashi daga gani taci fa tada kai..


"Rukky kinga maliya na da wata budurwa tana tuk'asa ko ina zasu haka,gashi ma dai daga gani ba unguwa zasu ba Dan naga kamar baiyi wanka ba..


Da yake su motar su Rukky akwai tin sukum su MALIYA babu tin shiyasa ma MALIYA baiga Ashfa ba,har saidai aka basu hannu suka wuce.....



Bayan ta sauke shine yayi mata godiya sanan yace dan Allah idan bazata damu ba tabashi number ta kodan wasu gyararraki idan sun tashi,babu musu ta bashi yayi saving da madam sanan ya tafi inda zashi,ita kuma ta wuce gida....




Zaune take saman k'aramar katifar ta bayan sun dawo gida,tayi dairling number maliya yana ganin itace yayi saurin d'agawa bayan sun gaisa tace yau nagan ka a danger dakai da wata budurwa a Mota...



Da sauri MALIYA ayya amma ni ban gankiba kice kin fita kema,wallahi wata k'anwatace muka fita da ita zata wuce office nikuma zani wani waje. Ai da kinsani kin kirani a lokacin."
"A'a abinda yasa bankiraba kar na katse muku hanzari na d'auka budurwar kace."

"Budurwa kuma hhhhhh to ki kwantar da hankalin ki k'anwatace......
[11/16, 18:26] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/


*Page 15_16*

Bayan kwana biyu da haka ne rayuwa ta k'arya ta cigaba tsakanin Ashfa da MALIYA,duk sanda Ashafa zatayi zance da MALIYA tofa a gidan su Rukky za ayi wanan zancen ana haka har sukayi wata biyar da had'uwa...


Zaune take kan y'ar k'aramar katifar ta. A gefen katifar ta d'auki wayar ta bayan dogon nazari da kuma shawarar da zuciyar ta ta zartar mata...

Sak'o ta fara shirin turawa MALIYA kamar haka..

_ASSALAMU ALAIKUM BAYAN GAISUWA TARE DA FATAN KA TASHI LAFIYA,MY DAMAN ABIN DA YASA NA TURO MAKA WANAN SAK'O BA KOMAI BANE SAI ILLA NA SHEDA MAKA CEWA DADYNA YA BUK'ACI DA NA FITO DA MIJIN AURE,NIKUMA NAJI KAI NAKESO DAN HAKA KAI NA ZAB'A INASO KAYIWA MANYAN KA MAGANA. NGD DAGA MAI SHIRIN ZAMA MATAR KA ASHFA MUDDASIR._


Bayan ta tura masa da sak'onne ta tashi dan tayi wanka. Tana fitowa tsakar gidan ta tarar an gyara ko ina na cikin gidan komai tsaf² da yake kuma yau alhamis duk su Ashna suna nan babu islamiyya dan su sukayi wanan aikin ma ita tana cen tana baccin data saba..

Murmushi tayi sanan tace"Allah sarki Ashna ta,ked'in ta daban ce wallahi ina k'aunar ki k'anwata ta kaina,Allah ya baki miji nagari."

Murmushi jin dad'i Ashna tayi sanan tace"tare dake tayata kema Allah ya baki miji nagari kyakyawa kamar ke wanda zaisoki ya kula min da rayuwar ki,ya k'ara ahagwab'amin ke kamar yadda kike a shagwab'e."
Dariya tayi sanan tace" that's my k'anwa kinyi addu'a mai kyu,insha Allah ni kam Allah ma ya bani mijin da zai ringa min komai da bazai sani aiki ba,kanwata ina zaune ina kwance saidai y'an aiki suyi min komai hhhhhh ke ya kika gani Ashna,zan k'ara kyu na k'ara komai hutu da jin dad'i zai karb'eni."

Dariya Ashna tayi sanan tace"Allah ya cika miki burunki yayata,ke kad'ai gareni y'ar uwa mace dole idan ba inna kece zaki zama a matsayin uwata kuma y'ar uwata abokiyar sirrina to ya zama dole na kula dake."


Duk da iskanci da san jiki irin na Ashfa da rashin son talaka da san abin duniya haka Ashna take ji da ita kuma take sonta duk duniyar nan bataso taga b'acin ranta saboda koba komai y'ar uwar tace kuma Allah ya sani suna junan su sosai Ashfa tanawa Ashna k'aunar da bazata iya misaltuwa ba haka ba Ashna take mata duk da kuwa cewa ra'ayin su ta ban banta inda Ashfa take da muradin auren mai kud'i ita kuma Ashna muradin ta ta AURI miji mai ilimi da rufin Asiri...



Bayan ya tashi yayi wanka yana shirin tafiya aiki kenan yaci karo da sak'on Ashfa. Da hanzari ya karanta sanan ya buga wata k'ara yana dafa Ado.

Ado kuwa razana yayi kamar zai ruga da gudu har ya tashi da niyyar guduwa MALIYA ya cakumosa yana k'ara wata k'ara da dariyar kamar wanda ya samu ciwan tab'in hankali..


"Wai dallah Malam mene haka,ashe da mahaukaci nake zaune bansani ba,wai MALIYA giyar wake kasha ne sai faman ihu kake kamar yau aka kwanto ka daga dawanau."

"Mtwsssss bazaka ganne ba dalla malami ni yau d'inan da kake ganina ina cikin farin ciki matuk'a.." Kafin ma ya k'arasa bayanin ya k'ara rusa wata k'ara yanaik'awa Ado wayar wai ya amsa ya karanta...


Ado ne ya amsa ya karanta tsaf sanan ya juyo ya kalli MALIYA yace"amma MALIYA ka samu tab'in kwakwalwa ko?"

"Bangane ba kamar yaya,ban fahimce kaba,mai kake nufi?"

"Ina nufin cewa Ashfa tace ka turo manyan ka ayi maganar aure,to yanzu in tambaye ka mai kake dashi mai ka tara da zaka iya tun karar auren yar mai kud'i kalar Ashfa,yanzu kai abin kunya ne ma ai ka kai kud'i sanan kace kasa ranar aure shekara d'aya, kai ka manta cewa y'ayan manyan nan idan anyi muguwar dad'ewa asa wata biyu ko uku,sanan mai kake dashi mai ka taka?"


Cike da gamsuwa da kuma mantuwa ya juyo ya kalli Ado yace "gaskiya abin da ka fad'a haka ne Ado,amma kasan me idan sun san wata ai basu san wata ba,nine fa MALIYA tunda nace maka sai nayi auren nan sai nayi amma kuwa maganar kai kud'i tabbas ba yanzu ba sai nan da wata biyu ko uku na gama wasu plan d'ina."

Yafad'a yana murmushi sanan yak'ara da fad'in"ai bari ma kagani. " daukko wayar yayi yafara tura mata da sak'o kamar haka.

_WSLM LFY KALAU NAKE ALHAMDULILAHI HAK'KA BAN TAB'A FARIN CIKI IRIN NA WANAN RANA DA NAJI KIN ZAB'ENI A MATSAYIN MIJIN DA ZAKI AURA,HAKAN YANA NUFI KIN BANI BABBAN MATSAYI A CIKIN ZUCIYAR KI,DAN HAKA INSHA ALLAH BAZAN BAKI KUNYA BA KUMA NAGODE SOSAI DA K'AUNAR KI A GARENI,SAIDA KUMA AYI MIN AFUWA DAN KUWA JIYA JIYAN NAN DADY YA TACI DUBAI AMMA NASAN BAZAI WUCE ONE MONTH BA DAN HAJA INSHA ALLAH YANA DAWOWA ZA'AZO AYI KOMAI A GAMA NGD._

Bayan ta gama wanka tana zaune tana shafa wani lotion mai d'an karan kyu da tsada ta gama tana tattare gashin kanta da yasha gyara ta maidasa baya tana shirin saka kaya taji shigowar sak'o tasan shine dan haka ta jinkirta da saka kayan ta d'auki waya dan ganin sak'o,shiga tayi ta karanta sana tayi murmushi a zuciyarta tace kaji manya. Fara matar masa da amsa tayi kamar haka
_Allah ubangiji ya dawo mana dad d'in mu lafiya babu komai nima zan fad'awa nawa dad d'in Allah ya dawo dashi lafiya._

ALLAH yayiwa wa Baban Ashfa rasuwa tun shekara d'aya da suka wuce,lokaci d'aya ciwon ciki ya kamasa a ranar Allah ubangiji ya karb'i kayan sa,sai ya kasance babban yayansu shi yake kula da cinsu da shan su to dan ma ba mazauni bane tafiye² yake haka zasuyi ta fad'a da Ashfa idan ya dawo akan abubuwan da take dan yagaji da ganin ta so yake tayi aure ko zai huta ,Hankalinsa ya kwanta.


Bayan kwana biyu da yin maganar ya cigaba da zuwa gidan su Rukky suna had'uwa da Ashfa soyewa yanzu idan kaga TUKUR bazaka tab'a cewa d'an kauye bane dan yazo tsakiyar birni ya waye ya goge..


Zaune Rukky take saman tabarmar dake tsakar gidan suna ta fira da inna da Ashna,Ashfa kuwa tana band'aki tana wanka daman abin da tafi kwarewa akai kenan.


"Yanzu rukyya ya kamata ki ringa yiwa k'awar ki fad'a ya kamata ta nutsu I yanzu yakamata ace tasan inda yake mata ciwo ta daina kule kulen SAMARIN nan haka ta fito da d'aya tayi aure hankali na zaifi kwanciya." Rausayar dakai Rukky tayi sanan tace"insha Allah inna komai ya kusa zuwa k'arshe dan kuwa dady yana dawowa na fad'a masa iyayen saurayin ta zasu zo wajensa dan su gama kinsan yana abuja kuma wanan satin zai dawo."

"To shikkenan babu komai Allah ya tabbatar da Alkhairin sa Allah yasaka muku da Alkhairi kuma yanda kuka zame mana tamkar y'an uwa Allah ya biya muku buk'atunku...


Ashfa tana da y'an uwan mahifin ta Dana mahaifiyar ta amma saboda basuda hali shiyasa bama tabi koda ta kansu balle ma ta d'auki su a matsayin iyaye..


Wani abokin sane a wajan aikin su da suke avota tunda yazo sanan duk sun San juna har da ado su uku suna zaune gidin wata bishiya kan tabarma suna shan iska MALIYA yace" Ado,Musa yanzu haka nagama shirina amma Musa yanzu aikin zai dawo kanka,wato so nake ka samo min opay na iyaye kasamomun k'osassaun mutane a hayo shadda mai kyu da malun malun da huluna komai a tsara shi zasuje su kaimin kud'in Auren Ashfa,kuma dan Allah a samo wanda baza mu samu matsala dasu ba........





Share fisabillilah indai kuna jin dad'in sa.🙏🏻
[11/16, 18:27] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/

*BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHIM.*


*Page 17_18*

Dukansu suka shek'e da dariya had'i da tafa hannu sanan Ado yace"shegen gari,lallai MALIYA ka waye sosai kama fini wayewa,wai Allah opay na iyaye fa kace." MALIYA ne yayi tsaki sanan yace"aikin banza har yau kana zuwa birni amma bazaka waye ba. Yanzu idan ba opay d'inba tayaya zan aureta wa nake dashi a wanan garin mtwsssss ai na fad'a maka bama opay na iyaye ba komai da zaka ga anyi a bikin nan to wallahi opay ne."

Zaro ido Ado yayi sanan ya kalli MALIYA yace"wai mai kake nufi bangane ba."
"Mtwsss ai daman bazaka tab'a ganewa ba amma idan lokacin ka gane yazo zaka gane." Musa ne ya katse su da cewa"yanzu kai banda abin Ado idan bata wanan hanyar ba taya kake ganin MALIYA zai AURI y'ar attajiri kamar Ashfa ai dole saida opay d'in."


"Yanzu abinda baku gane ba,bakwa ganin babanta zai iya bin cike akan mu idan ya gano gaskiya fa,tunda ai ba hauka yake mai kud'i kamar wanan da zai ka sa sanin wanda zai bawa yar saba dole fa sai yayi bincike." Cewar Ado.

Duk sai yanzu wanan abin ya fad'o musu amma duk da haka MALIYA bai karaya ba yana fatan Allah zai basa nasara,shifa yana ji a jikinsa cewa sai ya auri Ashfa....



Kamar yadda suka tsara haka komai ga tafi,inda Musa ya shiga ya fita daman ya saba da wanan sarkar ya samu iyayen da zasu zo a matsayin iyayen MALIYA an samo musu kayan sawa na alfarma wanda shima opay d'insa suka yi...



Cike da murna da jin dad'i yau ta tashi sai kujiba² take ta rasa inda zata saka ranta saboda jin dad'i naganin cewa burin ta yakusa cika ta kusa ta zama matar wani,wowwww abin yayi mata sosai ta kasa zaune ta kasa tsaya. ALLAH sarki inna itama tana farin ciki dan kuwa bazata k'iyin farin ciki ba tunda burinta bai wuce tasamu Ahsfa ta samu miji nagari wanda zatayi aure ba hankalinta sai yafi kwanciya...


Ansa lokaci yau iyayen MALIYA zasuzo shi kuma yayan Ashfa ma baya nan amma inna ta fad'a masa a waya yace idan ya dawo zaiyi bincike. Agida Ashfa ta fad'a musu MALIYA fa ya shahara babu wanda bai San mutumin arzi'ki bane,amma dole inna tace tabbas idan yayan ta ya dawo tofa za'ayi bincike...


Da yake ba gidan su za'a zoba,gidan su Rukky za'a zo,tuni kuma Maman Rukky tasanarwa da Abbanta yau zai karb'i kud'in Ashfa da yake ya santa, amma duk da haka saida yace y'an uwan babanta ko biyu ne suzo ayi agabana su. Haka kuwa akayi aka fad'a musu,duk da dai ba'a San ransu ba haka suka hak'ura sukaje dan kuwa da haka sukace bazasuba,saboda bata d'auki su da muhimmanci a rayuwar ba...



Ashfa da Ashna,dasu Khalid da meenal mai kimanin shekara sha uku,sai murna suke Ashfa zatati aure,sunyi abubuwan snacks kala² inda suka d'auka suka kai gidan su Rukky haka aka had'a da abubuwan da Maman su Rukky tayi itama...



B'angaren MALIYA kuwa a cikin wad'anna kud'in da madam Afnan ta bashi yabasu dubu d'ari yace ita zasukai za'asa date wata uku sanan ya basu rabin kud'in su,idan an kammala za'a cika musu haka su idi sukasha malin malin su uku MALIYA yazo da motar madam Afnan data kawo wanki ya kaisu gidan su Rukky...



Haka sukazo tamkar wasu manyan mutanen saidai idi da yamak'alawa kansa Alhaji idi yace sud'in ba y'an garin nan bane a katsina suke aiki ne ya kawo su nan shiyasa ma bazai sansu ba,haka dai batare da dogon bincike ba aka karb'i kud'i sanan akayi saving date..
Murna kam a wajan MALIYA ba'a magana,Ashfa ma murna take sosai saboda burin ta zai cika gashi an kawo 100k wowww abin dai sai hasidin iza hasadin,haka ta ringa d'ayrawa a status wai ALHAMDULILAHI SAVE THE DATE KAZA GA WATAN KAZA...


Bayan ansa ranar Ashfa kuma aka cigaba da soyewa yana kashe mata kud'i dan duk kud'in da ya samu akanta suke k'arewa....



"Madan barka da zuwa." MALIYA ya fad'a cikin girmamawa.. Murmushi tayi sanan tace"MALIYA ikon Allah. "
"Ina fatan kinzo lafiya ya gida ya kuke?"
"Lafiya kalau Alhmdlh what of u.?"
"Nima kalau."
Murmushi tayi sanan tace"haka ake so."
"Madam wankin ne ko kuma...
" a'a MALIYA ba komai bane,kawai dai nazo ne na nemi alfarma."
"Alfarma kuma madam."
D'aga masa gira tayi ba tare da ta maimaita ba.
Kafin yayi magana tace"idan babu abin da kake kuma bazaka damu ba inaso ka rakani unguwa."
Cike da washe baki zai raka kyakkyawa mai kud'i kuma kamar madan Afanan yace"ahhhh babu wata damuwa amma dan Allah ki bani minti 5 nayi wanka yanzu a gidan wankan nan sanan mutafi."
Komawa mota tayi ta shiga sanan tace"ok don't worry sai ka dawo."
Juyawa yayi cike da jin dad'i ta nufi gidan wanka...


Tun sanda MALIYA yayiwa Afnan wanan abin ya zama ta rik'eshi a zuciyar sa ta kasa mantawa da amanarsa yana da amana gaskiya ne irin wanda idan aka bashi amana bazai tab'a cinta ba shiyasa taji ta wani yarda dashi...


Aikuwa baifi minti5 ya gama ya shirya kamar bashiba,ba laifi da yake chocolate color ne yayi kyu amma iya nashi,haka yazo suka shiga motar suka d'auki hanya..

Tafiya suke babu wanda yacewa kowa komai kowa yayi shiru kuma kowa da abin da yake sak'awa a zuciyar sa.
"Hmmm su MALIYA ba magana kayi shiru kamar ruwa ya cinye ka."
"Uhm babu komai banso na cikaki da surutu saboda nason manya basu son surutu."
"Uhm MALIYA kenan kana burgeni saboda kana da nutsuwa."
Wani dammm yaji k'irjinsa ya buga ina burgeta toooo ace dai tace tana sona wayyo Allah wallahi da tsaf zan yarda dan daga gani sunfi su Ashfa kud'i... Katse masa tunanin sa tayi da cewa" a wace unguwa kake da zama?"
"Am ina fagge."
"Ok tare da mahaifanka?"
"A'a mahaifana sun mutu."
Kawai ya tsinci kansa da fad'ar haka."
"Ayya Allah yaji k'ansu yasa sun huta.
" dangin kafa a wane gari kuke."
Tsintar kansa yayi da shek'ewa da kukan muna finci yana mai cewa"sunan Abubakar kamar yadda kika sani anfi kirana da MALIYA, muna zone a k'auyen GODE da yake anan k'auyen kano,mun d'in fulanin tashi ne daga nan mu koma can haka muka koma dajin falgore anan ne k'addara ta ritsa damu inda y'an fashi da masu kidnapping d'inan sukazo suka kashe nakashewa haka suka tattara gaba d'aya shanun mu sukayi gaba dasu sanan suka tarwatsa mu kowanne ya gudu yana neman wajan tsira.....





Keep share comments and vote fisabillilah. HAAJARA ABLA takuce.✍🏻
[11/16, 18:27] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/

*wanan page d'in kacokam d'insa sadaukar wane gareku y'an group d'in saina AURI MATAR NOVEL. Gaisuwa ta mussaman gareku Maman Najwa da Aisha shaleleta haajara abla takuce.*❤️💋



*BIMILLAHIR RAHAMANUR RAHIM.*


*Page 19_20*

Cike da jin tausayin sa na labarin sa ta kalle sa sanan tace"Allah sarki,kayi hak'uri ka daina kuka Allah yana tare dakaina dan Allah ka daina kuka Allah yaji k'ansu yayi musu rahma yasa sun huta sanan Allah ya bayyana maka wad'an da suke raye."

Cike da kukan munafinci ya k'ara karkata kai yana cewa"bani da gata,kibarni inyi kuka madam bani sa gata."
"Kabar fad'ar wanan kalmar dan Allah,kana da gata babban gata bana tunda kana da Allah,Allah shine fatan kowa da kagani a duniya kayi hakuri."

Haka yayi shiru yana jimanin munafinci har suka k'arsa wani babban super market dake kan titin tal'udu..

Bayan tayi parking suka fito suka shiga,tayi siyaya yana biye da ita abaya kamar jela yana tura mata k'aramin basket d'in datake saka duk wani kayan data zab'a,. Bayan tagama tata siyayyar ne ta fara soyayyar maza haka tasiyo kaya masu kyu da tsada ta kashe kud'i sosai dan harda su shadda gizna guda biyu ta siya,gani yayi leda d'aya an zuba mata iya kayan data siyaa na mata d'ayar ledar kuwa harda su takalmim maza hula shaddodin nan guda biyu duk a ciki aka zuba haka dai aka had'a sha tara ta arzik'i a wanan ledar....


Har k'ofar shagonsa takawo sa a motar sanan ta fito da niyyar sallamar sa,abin mamakin bai wuce gani yayi wad'anan kayan data siya masu tsada ta bud'e bot ta d'aukko ta basa,kasa rik'ewa yayi hannunsa yana rawa bakin sa yana rawa yama kasa magana. "Karb'i mana MALIYA naka ne." Tafad'a tana murmushi. Cike da mutuk'ar nuna farin ciki da jin dad'i yace"kina nufin kice duk wad'anan kayan nawa ne ni kika saiwa."batare da tayi magana ba ta d'aga masa kai tana murmushi.

Amsa yayi cike da rawar jiki yana ta godiya da yi mata addu'oin kala daban daban. Haka ta koma mota ta tayar har ta wuce yana binta da kallo yana addu'a....



Yana shiga shagon ya tarar da ado ya dawo shima,zama yayi sanan ya ajje ledojiin hannunsa Ado ne ya kalle sa sanan ya k'alk'ale da dariya yana mai furta" ahhh mutumina har an fara siyayyar auren." Zaro ido MALIYA yayi sanan yace"AURAN waaaa?"
"Bansani ba,idan lissafina ya tafi daidai ai inaga baifi one month ba."
"HHHHH sai kuma na fad'a maka siyo kayan zanyi,mtwsss wanan da kake gani tsuntsu na samu daga sama gasheshshe HHHHH . yafad'a yana dariya.
"Bangane tsuntsu daga sama gasheshshe ba dan Allah kayi min bayani...


Anan MALIYA ya labartawa ado abubuwan da yake faruwa Ado cike da mamaki da al'ajabi yace" tooo ikon Allah sai kallo,ai kai wallahi kace ka shigo birni a sa'a,yanzu ba gaba gaba idan akayi wasa sai kaji tace tana sonka."
MALIYA ne yayi wata irin zabura ya mik'e daga kishingid'en da yayi yace" mai kace so kuma,lallai baka da hankali Ado babbar yarinyar kamar wanan kana ganin ta kasan naira ta kwanta,hmmm daga gani ba babatan yafi Baban su Ashfa kud'i."
Ado ne ya shek'e da dariya sanan yace" to kaga kuma kuna soyayya da ita Ashfan da ya dace ace saidai kazo a maigadin gidan ta,ai abin na Allah ne."
"Wuuuuu da kuwa na warke wallahi duka zan aure su,tunda daman ita tasan ni ba mai kud'i bane kaga babu wani zancen k'aryace k'aryace,amma gaskiya nifa tunanina bazai bani Afnan zata iya furta min kalmar soba,saboda yarinyar tana da aji Allah nefa ya had'a jinin mu yazo d'aya."

"Hhhhhhh kamar yadda Allah ya had'a jinin ku to haka Allah ZAISA taji tana sonka."

"Kai Abokina kana k'ara fasa min kai wallahi,ai da kuwa na warke."


Haka suka cigaba da firar su nidai abla na fito na barsu hhhhh.


A kwana a tashi babu wahala a wajan Allah kuma duk ranar da aka saka dole zatazo yau ya kasance saura sati biyu bikin MALIYA da Ashfa inda aka had'a lefe na bakinta dan saida

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment