Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba ganin wani
hannu yayi irin wannan barnar
ba koda kuwa a wajen dambe
ne!
Idan an fito fage shi kansa balan
dubarudu abin ya
kidimashi
yaja baya yana kallon Amadu
baligi wanda ya yiwa
shahararren
dan dambe duka daya ya watse
Shiru kowa ya kasa magana
kamar ruwa ya cisu Amadu
baligi bai sake waiwayar tamarke
ba wanda ya baje kasa yasan ai
irin dukan da yayi masa zai dauki
kwana masu yawa yana jinya
kafin ya warke ya sake yiwa wani
rashin kunyar
.
Ya fuskanci sauran 'yan damben
yace dasu
"Bana son rashin mutunci ya
shiga tsakanina daku saboda
nasan mutuncin sana'arku kuje
duk inda kanwata take ku fito
min da ita na baku nan da awa
daya idan ba haka ba komai ya
faru tsakanina daku ku kuka
jawo!
Amadu baligi ya juya ya tafi a
fusace" bala ya biyohi a baya
suka koma 'yan damben sun
dade a tsaye babu wanda ya
motsa a cikinsu saboda sun
tabbata ko daga ina wannan
jarumi ya fito hannunsa a cike
yake da zarce! Bazai taba
yiwuwa ace hannu yayi irin
wannan ta'asar a bugu daya ba
batare da an dade ana girka
hannun ya nuna da dafi ba
.
BA'A JIMA BA labari ya wasu ako
ina a cikin garin dubarudu
mutane suka fara yayata dukan
da Amadu baligi yayiwa tamarke
.
Abinda tafi daurewa mutane kai
shine babu wanda yasan ko
Amadu baligi wanene shi kuma
ba'a san ko daga ina ya fito Ba
.
UBA MA ASHE DA UBANSA KENAN
Ku Biyoni Domin Jin Cigaban
Labarin
KAZAR KARFI
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 13
.

.
Mutane suka fara hasashen idan
har a wajen dambe Amadu baligi
yayi irin wannan dukan zaifi
birge 'yan kallo ya sami alheri
bai kamata ace a wajen fada yayi
irin wannan dukan ba ya barar da dafi a banza
Amadu baligi yaje gidan bala
suka zauna a waje suna zantawa
kan fadan da ya shiga tsakaninsa
da dan damben mutane suka
fara tururwar zuwa ganinsa
don kuwa a yadda aka dauko
tamarke a babur fuskarsa tayi
dameji tana zubar da jini aka
wuce dashi asibiti kowa ya kadu
da akace duka daya kawai wani
bako yayi masa kuma bai nade
hannu ba ba wani shiri yayi
dukan tsabar dafi ne kawai da sinadarai
Akwai dalili kwakkwara da yasa
mutanen garin suka rika zuwa
suna jinjinawa Amadu baligi tun
zuwan wadannan bakin 'yan
damben suka disashe
tauraruwar duk wani dan dambe
na cikin gida duk wasan da za'ayi sune suke yin kisa har
yanzun ba'a kashe kowa nasu ba
.
Mutanen garin suna son wani
bako yazo ya daukar musu fansa ya kashe koda mutum daya ne a wajen wasa don su rage yiwa
mutane kuri suna cika baki Akidar mutanen garin su suna goyon bayan 'yan damben kudu
ne ba'a goyon bayan arewa amma tun zuwan wadannan
baki kudu batayi kisa ba duk
kisan da akayi daga bangaren
arewa ne dole ne hankalin 'yan
kallo ya tashi
Garban kauye shine fitaccen
jagoran shirya wasan dambe a
garin dubarudu yana da yaransa
wadanda suke wasa a gida wadanda tun zuwansu tamarke
ba'a jin motsin yaran Garban Kauye ya damu matuka yana son
ya sami wani sabon dan wasa
daga kudu wanda zai kashe
masa koda mutum daya ne a
cikin 'yan arewan nan
Yana a gida labari ya sameshi cewar wani bako abokin bala
yazo sunyi fada shi da tamarke
yayi masa wani duka wanda ba'a
taba ganin irinsa ba a tarihin dambe
Garban kauye ko gida bai shiga
ba ya garzaya a babur dinsa yaje
gidansu bala don yaga bakon da
yayi wannan abin alheri
.
Da zuwanshi ya samesu su biyu a
zaune suna shan fura Garban
kauye ya kashe babur dinsa ya
sauko yana dariya tun kafin bala
yayi masa sannu da zuwa yace
"ina bakonka shi nazo nema
Bala ya nuna Amadu baligi
Garban kauye ya kama hannun
Amadu baligi ya jijjiga yayi
masa jinjina
Amadu baligi yayi murmushi kadan
Mun gode! Mun gode.
Don Allah ya sunanka
ya fada masa
sunana Amadu
Garban kauye ya tambayeshi
Amadu kai mutumin ina ne?
Ina acan tashar Dan amarya ne
gundumar muje- dawa Garban kauye yace da Amadu
ina gida yanzun nan na sami labarin abinda ya faru tsakaninka
da tamarke wadannan yara sun
gallabemu tun zuwansu garin
nan suke yi mana garari kullum
su kadai suke yin kisa mun rasa
yadda zamuyi dasu
Amadu baligi yayi dariya Shi dama wasa haka ya gada
bashi da gwani sai mai sa'a
Sun sami sa'ar shigowa garin ne
amma da sa'arsu ta fadi zakaga Hannunsu ya kwanta
Garban kauye ya bata rashi da
daya tuno illar da wadannan 'yan
dambe suka yi masa a sati uku da zuwansu Duk
KAZAR KARFIN
Da ake kasawa yaransa basa ci saboda su ake kashe wa
.
Bayan ya gama sauraren bayanin
Amadu baligi sai yace dashi
"Ina so ka taimaka mana Amadu
ka daure kayi mana wasa ko sau
daya ne kafin ka tafi na tabbatar
kai kadai kawai zaka yi mana
kisa muma mu sani nasara
Amadu baligi ya girgiza kai yace
Gaskiya ba wasa nazo yi ba malam....
Dan gajeren mutumin mai kamar
a kifashi da kwarya ya fada masa
sunansa daya fahimci bai san abinda zai kirashi ba
"Garban kauye nake Amadu yauwa.... To sai dai kayi hakuri
malam Garban kauye ni zumunci
ya kawoni garin nan nazo neman wata kanwata ce wacce
ta gudu ta baro gida jiya ba dambe nazo yi ba kuyi min afuwa
Garban kauye ya nuna
damuwarsa a fili
"ka taimaka mana Amadu" ko sau daya ka tsaya kayi mana
wasa na tabbata kai kanka zaka sami alheri mai yawa a wajen mutanen mu dake garin nan
saboda kowa ya gaji da wadannan yara kayi hakuri
kayi mana wasa Amadu"
Sai a lokacin balan dubarudu
yasa baki
Amadu ka taimaka in kaga da sarari" tunda kwana daya kawai
zakayi" dama gobe ne ranar
babban wasa ka tsaya zuwa goben idan kayi wasa saika
koma da yamma
.
Garban kauye ya kara da cewa
"mu da kanmu zamu daukeka
mu mayar da kai har gida kada
kaji komai Amadu akwai yaron
da muke so kayi wasa dashi a
cikinsu" shi kadai ya gallabi
yaranmu da kisa sunansa
SHAGON SADI
idan har ka kashe
mana yaron nan" to mu ka gama
mana komai
Amadu baligi ya sake yin dariya
To idan kuma yaron ya kashe ni fa? bani da tabbacin zan iya
kashe muku shi saboda kaga
ban ga wasanshi ba kuma banzo da wani shiri ba" ba wasa
nazo nayi ba" bana fadawa dambe irin haka ba shiri ko a
zamanin da ina wasa bana daukar
KAZAR KARFI
sai na san
ko dawa zanyi wasa na dade banyi dambe ba yanzu ko
karamin yaro zai iya bugeni
.
Yaci gaba da dariya
Garban kauye yace dashi
Kada ka karaya Amadu zaka iya
buge kowa a cikin 'yan arewan nan.....
In dai irin wannan dukan da kayiwa tamarke....
.
ASHE DAI UBAN BALIGAI SHIMA GWARZO NE FANNIN DAMBE.
.
KU BIYONI
A
WHATSAPP
08082035050
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 14
.

.
To duk fadin kasar nan ba
wanda bazaka iya bugewa ba
ka daure kayi mana dambe kazo
muje in kaika gidana ka sauka
acan ni zan dauki komai naka
yanzu kai bakona ne ba bakon
balan dubarudu ba ne
Kafin Amadu baligi ya sake yin
jayayya ne Balan yace dashi
kada ka damu Amadu na amince
Garban kauye namu
ne wannan abu idan kayi mana
gida kayiwa ni dasu duk
daya ne
Amadu yace
to yaya maganar talatu kuma?
banason hankalina ya rabu biyu
nafi so in fara ganinta in tsareta
kada ta sake guduwa wani garin
ta bamu wahala
Balan ya karfafa masa gwiwa
wannan ka barmu da ita zamu
tare maka nan bangaren dama
don tana wajen tamarke shiyasa
bamuyi wani yunkuri akan dawo
da ita wajenmu ba zamu lura da
ita idan ta dawo ba zamu barta
ta matsa ko ina ba idan kayi
wasa gobe sai mu fito maka da
ita ku tafi gida
.
Amadu yadan rage fara'a kafin
yace zamu gwada mu gani Allah
ya
bamu sa'a
Garban kauye ya sake kama
hannunsa suka sake gaisawa
Mun gode Amadu. Bari inje in
fadawa mutanenmu aje ayi shela
cewar gobe muna da bako
wanda zai yiwa kudu wasa
Garban kauye ya hau babur ya
koma cikin zumudi ya fara
sanarwa mutane cewar sunyi
bakon dan wasa kuma gobe zai
fito yayi dambe da arewa
.
Kafin dare yayi labari ya watsu
ako ina a kauyukan mutane
suka fara fatan ganin goben don
suzo suga wasan
AMADU BALIGI
.
BABI NA BIYAR
.
SADI KARE GARKE
Ba boyayye
bane a wajen wadanda suka
shiga duniyar takadarai kuma
sukayi rayuwa tare da manyan
masu laifi
Yafi shahara a wajen sata don
kuwa anan ne ma har ya samo
sunan KARE GARKE Bayan sata
sadi ya iya sana'o'i da yawa
maganin fashewar taya Idan
satar ta kulle sai ya juya wani
bangaren yaci gaba da
rayuwarsa
sadi ba irin kananan barayin da
aka saba gani bane wadanda
suke tsallaka katanga a biyosu da
gudu su sha da kyar kuma ba
irin barayin da suke farke aljihu
bane a kasuwa al'amarin sadi
duk ya dame nan ya shanye
.
Inda nasa sharrin yake shine
idan zaiyi sata da yaje riga inda
garken shanu suke" zasu biyoshi
a cikin dare ba tare da wata
tirjiya ba kuma idan ya balle
garke guda ya shigo gaba shanu
suka bishi a baya kada mutum
yayi zaton zaibi sahun sadi da
shannun ya cimmasu don sadi
yayi lalatarsa ya kore garken a
cikin dare! Da ya nufi yamma sai
sawunsa dana shanun ya rika yin
gabas Idan kuma kudu ya nufa
to a arewa za'a ga sawunsa Don
ba karamin jarumi ne zai kama
kare garke ba idan yayi masa
sata
Sadi yana sha'awar wasan
dambe duk da yake dai ba
kasafai yake yarda ya dauki
KAZAR KARFI
Ba shi kansa yasan
bashi da isasshen dafi a wajen
dambe da dai a wajen sata ne
anan ba wanda yake jin tsoro
shiyasa yaja baya ya kama
girmansa yabar yaransa suna
fitowa wasa shi kuma yana
kulawa da nasarorinsu yana
basu shawarwari idan kuma
rikici ya balle a wajen wasa har
jami'an tsaro suka shigo sukayi
kamu anan sadi yake yin ranarsa
wajen amso yaran da
ake je dasu aka kulle
.
A duk cikin tawagar da sadi yazo
da ita na 'yan dambe goma sha
daya zuwa kauyen dubarudu
yafi ji da yaransa biyu wato
SHAGON SADI
da kuma
TAMARKE
yana son yaran ne saboda suna
da lokaci da wahala su fita wasa
wani ya kashe su indai basuyi
kisa ba to sai dai a raba wasa a
tashi babu kisa
Akwai labarin
SADI KARE GARKE
Acikin Littattafai kamar su
*JAMILA
*GANI KASHE NI
*BOYAYYEN MAKIRCI
*GOßE JAR KASA
.
Tun zuwansu garin dubarudu
dambe suna samun alheri idan
sunzo gidan wasan sadi yake
basu umarni duk wanda zai
dauki
KAZAR KARFI
shi yake turashi kamar yadda
duk
kudaden da aka samu shi yake
amsa yaba wanda yayi kisa
abinda ya kamata ya dauki nasa
ya kuma yagawa abokan
tafiyarsu wani abu
Sadi yana kwance a dakin
karuwarsa da yayi a garin
dubarudu daya daga cikin
yaransa yaje ya sameshi cikin
damuwa ya fada masa wani ya
bugi tamarke an kaishi asibiti
sadi ya tambaye yaron tare da
tashi ya zauna
Da wannen makami ya bugeshi
har yaji masa ciwo?
.
Da hannu ya bigeshi oga.... Wani
bako ne da yazo neman wata
yarinya kanwarsa akwai dafi
mai karfi a hannunsa fiye da
namu duka daya yayiwa
tamarke ya karya masa haba
Sadi ya tashi zaune akan katuwar
katifar karuwar wacce take
wanke kwanukan cin abinci a
waje
DUKA DAYA DA HANNU YAKAI
TAMARKE KASA ?
KUMA HAR AN KAISHI ASIBITI ?
Sadi ya rika nanata maganar
cikin zullumi don kuwa in har
wani zai iya zubar da tamarke a
duka daya to zai iya bige shagon
sadi kuma zai iya buge
kowa a cikin yaran da yazo dasu
garin
yaron sadi da yazo masa da
bakon labarin ya kara da cewa
Yanxu maganar da ake tayi a gari
shine wai mutane sun roki
gayen ya tsaye yayi dambe gobe
kuma ya amince xai tsaya
Sadi kare garke yayi shiru yana
tunani zuwa can yace da yaron
nasa
Ina shagon sadi yake a halin
yanzu ?
Yaron yace dashi
Ban san inda ya shiga ba. Baya
wajen abin ya Faru Amma
nasan yanzu..
.
WASH NA GAJI DA RUBUTU WA ZAI
TAYANI ?KAZAR KARFI--> 15
.

.
Sadi yace ba komai zan kirashi a waya
kaje zanxo in sameku mu hadu
musan yadda zamuyi a goben
yaron ya juya ya fice daga dakin
karuwar
A lokacin ne ita kuma ta shigo
taga ran abokin neman nata a
bace da yake ba matar aure ba
bace maimakon ta tambayeshi
ko me yake damunsa ta tayashi
jimami sai ta tsaya a kansa
kerere tace dashi
tun dazu nake tambayarka
kudin nan.. Ina sone zan cika ayimin sayayya ka bani kada kokaci ya kure
Sadi kare garke dake zaune ya
daga kai ya kalleta suka hada
ido ba wani alamar tausayi a
fuskarta a karo na farko a
rayuwarsa ya tsinewa bariki a
zuciyarsa da kuma karuwai baki dayansu karuwa.?
ya sake tabbatarwa da kansa bata yi ba
.
DAKIN DA AKA sauki Amadu baligi a
gidan garban kauye jere yake da
kofar shiga gidan wanda yake
fuskantar yamma tun sanda aka
yayata labarin zuwan Amadu
baligi da kuma wasan da zaiyi
washe gari wuni mutane sukayi
suna zuwa gidan garban kauye
suna gaisawa dashi wadansu
suna sayo masa nama suna
kawo masa wadansu kuma
lemu mutane sai karramashi
suke yi don kuwa suna saran
washe gari zaiyi wasa zai kashe
masu daya daga cikin bakin
damben da suka sauka a
dubarudu
Da dare yayi ne GARBAN KAUYE ya
bashi dakin saukar baki dake a
kofar gidansa suka yi
bankwana dashi sai da safe ya
shiga cikin gida shi kuma
Amadu baligi ya rufe kofa
Sai da karfe biyu na dare yayi
kokacin da kafa ta dauke sai
Amadu baligi yaji ana
kwankwasa kofar dakin daga
waje da ya tabbatar ba garban
kauye bane sai ya tashi daga
tsohuwar katifar da yake kwance
a kanta wacce ke kasa da harshe
aka sake kwankwasa kofar
Amadu baligi ya lalubo wukarsa a
kwankwaso wacce ko bacci zaiyi baya rabuwa da ita da ya
ciro wukar ne sai ya fara kokarin
kai hannu zai bude kofar dakin
bai damu da ko wanene yake
bubbuga kofar ba ko mugu ne
ya kawo masa ziyarar dare
yasan indai yana tare da wukarsa
zai iya tunkararsa koda wanne
nufi yazo
.
Saida Amadu baligi ya bude
kofar ne sannan ya gane kuskuren da yayi da yayi zaton
karamin mugu ne mutane ukun
da sukayi masa lale marhabun
sun banbanta da irin miyagun da
ya saba gani sadi kare garke ne
a tsakiya rika da karamar bindiga
a hannunsa tana kallon fuskar
Amadu" a kowanne gefensa
yaransa ne" daga habu wurure ne" a dama kuma Iro bahago
Sadi kare garke yayi murmushi
da yaga Amadu baligi yayi
saranda don kuwa wuka komai
kaifinta bata kai bindiga hadari ba
mayar da wukarka Amadu" nima
zan mayar da bindigata Munzo
ne sada zumunci ne ba fada muka zo muyi dakai ba"
Sadi yace dashi a sanyaye don
kada wani yaji muryarsa a kusa
Amadu baligi ya saki wukar ta
fadi kasa don ya nuna musu ya
basu hadin kai sadi ya sauke
bindigar ya sakata a cikin aljihun
wandonsa" A lokacin ne ya sako
kai ya shigo cikin dakin bayan
Amadu ya wuce ya basu hanya
.
Karamar fitilar zamani mai batir
uku wacce kusa take sakale da
ita a jikin bangon dakin bata
haske sosai amma hakan bai
hana ya baiyana mutanen uku a
fili ba da kuma kayan da suke
sanye da su
Dukansu bakaken kaya suka
sanya kanana wadanda zasu
taimakesu wajen sajewa da
duhu sadi ne kawai yasa hula
kaboyi ya bambanta da yaransa
biyu
Babu wurin zama a dakin in aka
dauke samfotin katifar ba
sauran wani abin arziki a cikin
dakin sai wani karamin buhun
dawa na ajiya dake a jikin bango
a kwance
Sadi ya zauna akan buhun a
yayin da Amadu baligi ya koma
kan katifar ya xauna warure da
Bahago suna a bakin kofar sun
toshe iskar da ke shigowa su
basu fita ba su kuma basu shigo ba
me yake tafe daku ?
Amadu baligi ya tambayesu cike
da masaniyar sune bakin 'yan
damben da garban kauye yake
bashi labari Da ganin kafadunsu
da kunnuwansu ya fahimci
hakan saboda aikinsa ne
Sadi yace dashi
Nasan bazaka rasa jin labarina ba ni da yarana? Nine sadi
kuma nina zo da wadannan yara
nan garin muna wasa sati uku
kenan muna samun alheri.
Dazu da rana kayi rigima da daya
daga cikin yarana wato tamarke kuma harka batashi a
fuska..... Yanxu haka yana asibiti
an kwantar dashi
.
Amadu baligi yace
"Ban so hakan ya faru ba ni kaina.... To amma yaron tsagera
ne Nazo neman kanwata ne
talatu aka ce dani shiya ajiyeta
na tambayeshi yarinyar shine ya
zagi iyayena kaji dalilin dukanshi da nayi
sadi yayi murmushi kamar abin
bai dameshi ba
wannan namijin dukan da
kayiwa tamarke shiya jawo maka
farin jini a garin nan har garban
kauye ya rokeka daka kwana kayi
wasa gobe suna so ka karya
mana lago ka farke mana laya ne
saboda tun zuwanmu babu
wanda yayi nasara akan daya
daga cikin yarana
"Nasan haka.... Amma ni ba ruwana da gabar dake
tsakaninka da garban kauye ni zanyi wasane kawai don nishadi
da kuma soyayyar da mutanen garin nan suka nuna min
.
Bana dambe da gaba kuma sanda nayi tashena bana yarda
inyi fada a wajen wasa...
.
WAI JAMA'A WA KUKE GOYON BAYA ?
AMADU BALIGI KOKUMA SU YARAN SADI KARE GARKE ???
KAZAR KARFI--> 16
.

.
Bana Fada da gaba agurin wasa Idan mutum ya kasheni nasan Allah ne ya bashi sa'a a kaina ba
wani gaba idan kuma nina
kashe mutum nasan ba karfina
bane ko iyawata wasa haka
yake ni ba fada nazo yi ba
Sadi ya girgiza kai cikin
gamsuwa da bayanin Amadu
baligi Naji dadin wannan kalamai
naka kuma na fahimceka
Amadu muma ba fada muke so
ba mun zone mu rokeka wata
alfarma kuma muyi yarjejeniya
dakai akan wannan wasa da za'ayi gobe ina so kayi mana
alkawari kuma ka fada mani
gaskiya inka amince in ma kuma
baka amince ba to ka fada min
gaskiya don in sani
Amadu baligi yace da sadi
Ina jinka ci gaba da magana
Sadi ya gyara zama akan buhun
dawar yace
mun san cewar idan dambe za'ayi kafi karfinmu ba wanda
zai iya kasheka a cikinmu
Amadu Wannan wata magana
ce a tsakaninmu da kai ka sani
muma kuma mun sani idan kayi
wasa gobe koda wa muka hadaka zaka iya bigeshi kuma
idan kayi mana haka ka karya
mana kwari a garin nan
.
Wanda hakan zaisa kwarjininmu
ya fadi muna samun abinci dai-dai gwargwado a garin nan don
haka nake so ka taimakemu
idan kayi wasa damu gobe ka
bari yarona ya bigeka yayi nasara
akanka ni kuma nayi maka
alkawari zamu bar maka duk
KAZAR KARFIN
da aka sa ko nawa
ne bamu so mun bar maka Ni
dai ina so ne kawai ka kare mani
mutuncina a garin nan tunda
kaga zuwa kayi kuma gobe zaka
koma mu kuma anan muke zaune nan ne wajen cin
abincinmu. Kayi mana
wannan halaccin kaji Amadu ko
nawa aka sa
KAZAR KARFI
zamu bar maka
A karo na farko tun zuwansu
dakin Amadu baligi yayi
murmushi sau daya yayi tunani
a gajarce sannan yace
to wannan ba wani damuwa
bane a gareni indai kana ga yin
hakan shizai baku damar ci gaba
da yin sana'arku. Ba wata matsala dawa anyi wasa goben
a cikin yaranka ?
Sadi kare garke wanda shima
yayi murmushin jin dadi yace Da shagona zakayi dambe
karamin yaro ne ka bishi a
hankali Amadu bazai iya daukar
dafin ka ba
.
Amadu yace dashi
"In dai don wannan ne ka
kwantar da hankalinka na
daukar maka Alkawarin zan
barshi ya bugeni ni dama ba
wasa nazo yi ba nazo neman
kanwata talatu ne wacce yaronka
ya boyeta
sadi yace cikin sauri
Ba boyeta yayi ba na bincika
naji" wata karuwa ce ta jata suka
tafi ajo wani gari sai gobe zasu dawo da zarar ta dawo saika
tasata ku koma gida
Amadu yace
shikenan ba damuwa sai goben
Sadi ya mike tsaye yasa
hannayensa biyu cikin aljihun
wandonsa (jeans)
"Na gode Amadu ina fatan zaka cika min alkawarin da ka
daukar min nima zan cika maka alkawarina bazamu taba
ko kwabo a
KAZAR KARFIN
da za'a sa ba kai zamu baiwa
duka
Amadu ya tashi don ya rufe
kofar dakin idan sun fita sun
fara isarsa haka nan
Shikenan sai goben
Sadi ya kama hanyar ficewa daga
dakin yaransa biyu suka fita
suka bashi hanya tun zuwansu
basuyi ko tanba sun hade fuskokinsu kamar dodanni"
Lokacin da sadi ya fita ne kafin
Amadu ya turo kofar ya rufe
dakin sai sadi yace dashi daga
can waje
.
Wata kila ka canza ra'ayinka
kafin goben" ko kuma in lokacin
yayi ka karya mana alkawari
idan kayi mana haka muna da
hanyar da muma zamu dauki fansa na tabbatar bazaka so ka
koma gida da gawar talatu gida ba" in har baka cika mana
alkawarin mu ba saina kashe
talatu kisan wulakanci
Sadi ya tafi cikin sauri tare da
yaransa biye dake take masa
baya a cikin duhun daren" Har
sukayi nisa Amadu bai daina jiyo
sautin tafiyarsu ba kamar
wadanda suke kwaba kasa
.
LOKACIN WASA YAYI
.
AN DADE BA'A TARA jama'a a
gidan damben dubarudu ba irin
wannan rana da yake dama anyi
yekuwa an sanarwa mutane
bakon wasa tunda wuri 'yan
kallo suka rinka tudadowa daga
kowanne lungu kafin karfe biyar tayi gidan ya cika ba masaka
tsinke"
An kafa itatuwan zama a gidan
damben" daga gaba kuma
bencine aka ajiyewa inda
yawancin 'yan wasan suke zama
da kuma wadanda suke da ruwa
da tsaki a wajen shiya wannan
wasannin dambe a gidan" filin
da 'yan wasan suke tsayawa a
zagaye yake da turakun itace da
igiya" ta yadda koda filin ya rikice
dai babu dan kallon da zai tsinka
ko ya shigo cikin da'irar
.
Ba'a bata lokaci ba kowa ya
hallara a gidan wasan"
makadane suketa aikin buga
kalanguna suna yiwa 'yan wasa
kirari" da yake kowannen dan
wasa akwai wakarsa wadda
akeyi masa kirari da ita" lokaci-
lokaci 'yan damben sukan je inda
masu kidan suke suyi musu
ruwan kudi su dawo baya suna
rawa da kirari mutane suna tafi
da ihu
Garban kauye yafi kowa kazar-kazar a wannan ranar" ya kasa zaune ya kasa tsaye yana ta
kaiwa da komowa fuskarsa cike
da farin ciki
A bangare guda Amadu baligi ne
zaune ana daura masa zare a
hannu A daya bangaren kuma
sadi kare garke ne tare da
yaransa goma sun taru a gungu
daya kowa ya daura zare sunyi
shirin wasa
.
Shagon sadi wani garjeje ne
tattirna wanda ga alama idan
har zai kwatanta yin fara'a sai
yafi yadda yake muni
.
KAI YAU ZA'A SHA KALLON TUMURMUSA MAZAJE
.
KU BIYONI DON JIN YANDA WANNAN DANKEN ZAI QARE
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 17
.

.
To amma baya yin fara'ar
ballantana har a gane hakan
yana kusa da sadi kare garke
yana wasa jini yana kaiwa iska
duka da hannunsa dake a nade
wani lokacin kuma yakan yi kirari
ba tare da kowa yaji abinda yake
cewa ba saboda hayaniyar
dubban mutanen dake cike da
gidan 'yan kallon da suke zaune
a saman katanga suna ta miko
gaisuwa suna gaishe da jaruman
wadanda sukazo gidan Bayan kowa ya gama shiryawa
sai Garban kauye ya dauki
makirfon din magana ya fito fage
ya fara da cewa
Jama'a 'yan kallo yau fa babban
bako wanda yazo mu gabatar
dashi a wannan fage yanzu
wanda kuma ni Garban kauye a
ckin aljihuna nasa masa
KAZAR KARFIN
Naira dubu hamsin
wannan jarumi ba wani bane
face Amadu daga tashan dan Amarya
Gidan ya kaure da ihu da tafi a
lokacin da Amadu baligi ya mike
tsaye ya fito a sanyaye ba wani
barazana ko kirari ya shiga
da'irar wasa inda kowa zai ganshi
yana sanye da wando iya kwauri
wanda ya tona asirin wata bakar
laya dake kaure a kafarshi ba
riga a jikinshi ya fito da bakar
tsoka waje wacce ko ita mutum
ya gani ya isa ya karaya don
kuwa Amadu yaci sunansa Baligi
tsattsagagge wanda ya kama
kasa akwai kambu a kowanne
hannunsa sannan kuma akwai
guru wanda shacinsa ya fito ta
cikin matsattsun wandonsa
.
Garban kauye ya dauko fatar
buhu ya shimfidata a kasa a
gaban Amadu ya ciro kudi daga
aljihunsa dubu arba'in ya zuba
su akan buhun mutane suka ci
gaba da ihu da tafi a lokacin ne
mutane suka fara ciro kudi daga
aljihunsa suna
mikowa wasu 'yan kore suka
cire hulunansu suka fara mikawa
mutane suna zuba kudi a ciki
Idan hulunan suka cika sai su
shiga cikin fagge su juye akan
buhun su sake komawa
Haka 'yan kallo suka rika miko
tasu gudunmawar
KAZAR KARFIN
ana zubawa a gaban Amadu
baligi kafin wani lokaci an tara
makudan kudi timm! Akan buhun wanda in za'a kirgasu
zasu kai dubu dari hudu Da gayyar mutane suka bayar da KAZAR KARFI mai yawa sun san
daben da za'ayi damben gaba
ne kuma kowa yana saran Amadu ne zaiyi nasara
.
Sadi dake a zaune akan benci
daya da karuwarsa ba abinda
yake yi sai dariya" yasan cewar
Amadu yaji gargadin da yaje yayi
masa a daren da ya gabata" ba
kudin bane suka dameshi" indai
shagon yayi nasarar ya bugeshi
Amadu bukatarsa ta biya kada dai mutuncinsu ya fadi a
garin......
A bangare guda gaba daya wasu bencina hudu duk karuwai
ne sunci kwalliya wadanda sukazo da mutanensu suna
zaune tare suna hira da dararraku wasu kuma suna
jayayyar wanda zaiyi nasara a tsakaninsu
Bayan an gama tara
KAZAR KARFI
sai garban kauye ya sake tsayawa yace da 'yan damben Ga
KAZAR KARFI
an tare" muna
jiran wanda zaixo ya dauka.....
Ina 'yan damben suke ? Makadan damben suka fara kida
suna kirari a lokacin ne sadi
kare garke yace da shago yace ya
dauka suyi wasa shagon sadi ya
shigo yana rawa mutane suna
ihu da tafi
Da zuwansa gaban Amadu baligi
ya duka ya dafa kudin don haka
damben ta hadu Garban kauye
ya tattara kudin ya kunshesu a
cikin buhun ya ajiyesu gefe guda
a kusurwar da'irar wasan kusa
da tirken da aka daura igiyar a
jikinsa
.
Shagon sadi da Amadu baligi
suka ja daga kowanne yana caja
hannunsa suna zagaya filin
zuwa can suka hadu suka gaisa
mawakan suka sassauta kida ya
koma kasa 'yan damben suka sake gaisawa sannan
kowa ya shirya ya gyara damtse
Shagon sadi ya fara kawowa
Amadu duka a fuska wanda yayi
saurin dukawa hannun ya wuce
a tsuyace kamar farfelar jirgin
sama Amadu yaja baya yayi
murmushi tunda yake bai taba
yin damben karya ba sai a wannan karon sun riga sunyi
yarjejeniya shida sadi bazai kashe masa yaro ba baya son
yin rigima da wadannan 'yan
damben yafi son yayi wasansa ya
gama lafiya ya koma gida dama
ba dambe ya kawoshi ba talatu yazo nema har ya kwana ya
wuni bata dawo ba amma ance
ya kwantar da hankalinsa yau
zata dawo kuma idan ta dawo
da wuri ma zata zo gidan
damben kallon wasa tunda duk
karuwan garin suna zuwa su
halarci gidan kamar yadda sukayi
sansani a gaba a halin yanzu ana
ihu da tafi tare da su
.
Shago ya sake kaiwa Amadu
wawan duka a fuska Amadu ya zuge ba tare da yakai masa duka ba suka canja waje suka sake
raba rana Amadu yasan da ace
damben zaiyi da tuni ya gama da
shagon sadi yana dai jan wasa
ne yadda zaiyi tsawo kafin yaba
yaron damar da zaiyi masa duka
daya ba inda zaiyi masa illa ba
sai ya fadi
"yan kallo suna ta kiran sunan
Amadu don ya jajirce kada yayi
wa yaron lagwa-lagwa har yayi
nasara akanshi sun bayar da
KAZAR KARFI
ne don suji dadin
ganin an kashe shagon sadi
wanda tun zuwansu garin ba'a
sami wanda ya kashe daya daga cikinsu ba
"Amadu! Amadu!! Amadu!!!
Masoya suka rika kiran sunansa
saboda kowa shiyazo gani a gidan
Wasanshi ne ba'a taba gani ba.
.
TATABURZA KENAN
IRIN WANNAN LAMARIN AKWAI TAYAR DA HANKALI
.
NIDAI INA BAYAN UBAN BALIGAI
.
KAI FA ?
KE FA ??KAZAR KARFI--> 18
.

.
Amma idan akayi la'akari da
mahaukacin dukan da ya yiwa
tamarke jiya dole ne kowa yazo
ya biya kudi ya ganshi
Sadi kare garke yana zaune yana
kallon yadda damben ke gudana
yana murmushin mugunta
yasan duk ihun banza mutane
suke yi su zasuci wannan
damben kamar yadda ya shirya
shida Amadu baligi a daren jiya
A cikin dubban mutanen da suke
kiran Amadu baligi ne yaji
muryarta daga baya Amadu zai
iya gane muryar talatu bai dade
da saninta ba amma ko ina yaji
maganarta ko dariyarta dole ne
ya ganeta
Amadu ya waiga baya cikin sauri
a lokacin ne yaga talatu a kusa
dashi a bencin gaba tare da
wasu karuwai uku yara da suka
shigo gidan tare ga alama yanzu
daga wajen ajon ta shigo gidan
Amadu yayi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment