Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a karshe
to za'a kai lemu ne babu biskit
dayyabu! ka dauko kwali daya a
bude shi a gabanta shima duk
karin gada guri ne
Dayyabu yace ba matsala bari in
dauko
Ya sake shiga cikin shagon ya
dauko kwalin biskit mai 'ya'ya
wanda ba'a budeshi ba daya fito
ne yace
Bari in kulle shago na muje kada
mu barta ita kadai
.
Ya dauki kwalin biskit din kamar
wanda zaije wajen baikon aure"
baban yara ya dauki samirar
dake cike da indomi da kwai an
shimfida a sama" yana ta
kwarara kamshi" shi kuma
Auwalu ya dauki biredi da shayin
suka dugunzuma su ukun suka
tafi dakin"
Baban yara suka sa gaba tunda
shi yasan yarinyar" shi ya
jagorancesu suka shiga" talatu
tana a zaune kamar wacce aka
dasa
Baban yara yace yana fara'a
to gamu mun shigo
Ya ajiye kwanon samirar a kusa
da kires din lemun Auwalu ya
ajiye mata nasa kofin shayin da
biredin" Dayyabu ya ajiye mata
kwalin biskit" talatu ta kalli lodin
kayan sun cika tsakar dakin
kamar wadanda suka fito da
kayan lefe a gani"
"ta tambaye su"
"duk wadannan kuma na
menene?
Baban yara yace da ita
Duk abinci ne" kin san ance yana
da kyau ka karrama bakon ka"
Ya juya kan abokansa biyu da
suka rakoshi" suna zare idanu
suna kallon talatu yace da ita
wadannan abokai nane sunzo ne
su gaisheki suma"
talatu tayi murmsuhi"
"sannunku malamai" ina wuni?"
Dayyabu da Auwalu suka kware
baki suka amsa a lokaci guda
"lafiya lau"
.
Suka ci gaba da murmushi ba
tare da sun san abinda zasu ce
da ita ba" baban yara ya dubi
lemun yaga bata dauki ko daya
ba" ya tuna baizo da abin bude
kwalba ba" yayi saurin daukar
kwalba daya yace
"Bari a bude maki lemun ki fara
dashi" yara sun dauke mani
ofiner" bana rabuwa da ofina a
dakin nan
Yasa hakori ya fara kici-kicin
bude lemun da karfi har yana
rintse idanu"
Dayyabu yace
"mancewa nayi" ni kuma dana
taho da tawa ofina ta shago"
Da kyar baban yara ya bude
kyalbar lemun ya taso da karfi ya
fito ya jika mashi fuska" yayi
saurin ajiye kwalbar yana borin
kunya"
"Gas yayi yawa a wannan
kwalbar shi yasa take da
wahalar budewa"
ya turawa talatu kwalbar a
lokacin ne tace dasu"
"to ku dan bani wuri mana inci
abincin naku..." tayaya zan iya cin
wani abu ku uku kun tsareni da
kallo ?
.
Kamar wadanda suke jiran
umarninta tana fadar haka su
duka ukun sukayi waje" suka fito
suka tsugunna a bakin kofar
suka fara yin kus-kus cikin rada
suna magana
Dayyabu ya fara yiwa baban yara
korafi
"kana ganin zata bada hadin kai
kuwa baban yara ?
"Ba matsala dayyabu"
Baban yara ya karfafa masa
gwiwa
Kasan yanzu tana jin yunwa ne"
bata ci abinci ba" mu jira taci ta
koshi sannan sai mu shiga mu
fada mata abinda muke so zata
amince"
Auwalu mai shayi wanda ya kasa
kunne yana sauraron radar da
suke yi yace a karshe Nima ina
ganin kamar haka-
haka take" kada fa kaja muyi
wahalar banza baban yara!
ya juyo bangaren Auwalu dake a
gefensa daga hagu yayi kasa-
kasa da muryarsa yace dashi
"kada muzo da kosawarmu a fili
Auwalu" kasan irin wadannan
wayayyun yaran na gari sai
anbisu a hankali" ba gaggawa
ake musu ba"
Suka yi shiru suna jiran talatu ta
gama cin abincin"
Baban yara ya leka dakin ta
hanyar wasu huje-huje dake a
jikin tsohuwar kofar tasa"
ya sameta a kishingide akan
gadon har taci abinda taci ta fara
shirin yin barci" yayi saurin
juyawa inda sauran abokan nasa
suke a zaune sunyi jigum suna
jiran tsammani" yace dasu ta
hanyar sirri
.
"ta gama cin abincin" ya za'ayi
kenan?"
Dayyabu ya mike yace
"to kunga dai na fiku bayar da
kayayyaki a harkar nan" gaskiya
nizan fara shiga"
Auwalu ya kwabeshi da sauri
kaji kauyancin banza haka kawai
zaka shiga sangwam-gwam ba
ayi mata bayani ba fa
ai sai an dan yi hira tukunna an
nuna mata inda aka fuskanta
sannan zata yarda" ku kuna
abune da jahilci har yanxu
Baban yara yace
Gaskiya ne Auwalu to kuzo mu
shiga muyi mata bayani kada tayi
barci naga ta fara gyan-gyadi
.
Bayan samarin uku sun gama
gudanar da shawarwarin su a
waje sai suka sake shiga cikin
dakin su duka suka sami
bakuwar a kishingide a kan
gadon tadan tsakuri abincin
kadan...
.
INA UBAN BALIGAI YAKE NE GA
GILLI NAN BATA TAFI BA FA
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 08
.
.
Bayan samarinn uku sun gama
gudanar da shawarwarinsu a
waje sai suka sake shiga cikin
dakin su duka suka sami
bakuwar a kishingide akan
gadon ta dan tsakuri abincin
kadan ta kurbi lemun baifi sau
biyu ba bata taba shayin da
suka ajiye mata ba ballantana
kuma dirkeken kwalin biskit din
dake jiranta
Da taji motsin shigowarsy saita
bude idanu ta tashi zaune tayi
hamma sannan ta dan bata ranta
Barci take ji fa gaskiya
Baban yara wanda yake son ya
kwantarwa da abokansa biyu
hankali don kada su damu yace
da bakuwar
Haba tun yanxu zakiyi barci ko
hira bamu yi ba?
Sai a lokacin Auwalu yayi kokarin
yin magana
Ai bata ci abincin ba ma naga
koma yana nan bata taba ba
Da yake baya iya yi mata
magana baban yara yake yiwa
korafin to amma duk da haka
sai ta bashi amsa tace dashi kai
tsaye
.
Don kada ma kuce nayi muku
wulakanci ne banci ba shiyasa na
dan tsakura nagode
samarin uku zazzaune a kasa
babu ko tabarma suka tasa
bakuwar tasu suna kallonta
wacce take a hakimce akan
gado ita ta fara yi masu
magana akwai alamar sun fara
isarta tace dasu
to naji kunce zakuyi hira wacce
iriyar hira kuke so ayi na fada
maku barci nake ji
A lokacin dayyabu ya dunguri
baban yara da kafa yana nuna
masa ya fito fili yaya magana ba
boye-boye
Baban yara ya fara inda-inda
yace
Eh to kinsan ai idan aka ce miki
ga samari da 'yan mata dole ayi
hira ayi soyayya koba haka bane?
talatu tace
Gaskiya kuwa haka ne baban
yara yaci gaba da cewa
yauwa, to dama haka nake nufi"
amma dai ina jin ga Auwalu yana
da magana" bari kiji komai a
bakinsa" Auwalu yi mata bayani"
Auwalu mai shayi ya gyara zama
yadan sosa kai yace
"Eh..ai duk abinda ka fada baban
yara ba kuskure daman dai shi
komai na rayuwa ance taimakeni
in taimakeka.. Ko ba gaskiya ba?"
to amma ga dayyabu bari yayi
maki bayanin abinda ya
kamata Dayyabu kayi magana
.
Auwalu da baban yara suka dubi
dayyabu wanda baiyi tsammanin
shi zasu dorawa wannan nauyin
ba" ya fara dabircewa ya ce
"to...ai kun gama magana" mudai
soyayya ce ta hadamu dake"
kuma yadda muka fara da
mutunci" to bazamu kare da
rashin mutunci ba" Rayuwa juyi-
juyi ce... Duk wannan abu da
kikaji muna fadi maki to soyayya
ce" mun san ke wayayyiya ce" kin
gane abinda muke nufi"
talatu ta yatsine fuskarta kamar
zata yi kuka
"Nifa malamai gaskiya ban
fahimci abinda kuke nufi ba"
kunki fitowa ku fada min
magana sai kewaye-kewaye kuke
tayi mani" ina ga da zaku fito ku
fada mani abinda kuke nufi
gaskiya zaifi"
samarin kauyen uku suka kalli
juna
Auwalu tace
Baban yara kayi magana mana"
ya zatayi mana haka?
Baban yara ya juya ya kalli
dayyabu yace"
Dayyabu ka sake yi mata bayani
yadda zata gane
Dayyabu ya kalli talatu ya
tambayeta yanzu ke malama duk
wannan
maganar da muke yi baki gane
inda muka dosa ba" baki
fahimcemu ba"
talatu ta girgixa kai tace Gaskiya
ni ban gane ba
.
Auwalu yayi karfin hali yace da
ita"
Amma dai ai kin san Hausawa
sunce ita rayuwa ka taimakeni ne
in taimake ka!
talatu tace cikin fushi-fushi
"Eh, tun dazu ai kuke ta fadar
haka" to me kuke nufi da
taimakeni in taimakeka? gani
nayi baku sanni ba" nima ban
sanku ba" sai yau muka hadu" to
kun bani wajen kwana" gashi
har na kwanta" kun kawo mani
abinci naci" to me kuke so kuma
inyi maku" sai ku fito ku fadi
gaskiya" na gaji da wannan
dogon turancin" barci nakeji" in
zakuyi magana kuyi magana" in
bazaku yi magana ba" don Allah
ku tashi ku fita barci zanyi" zan
kulle kofa
Samarin uku suka sake kallon
juna kowa yana tsammanin dan
uwansa zaiyi magana da
bakuwar tasa suna ta bata mata
lokaci sai zare idanu suke yi saita
tashi daga kan gadon ta tsaya
kansu tace ku dan fita in rufe
kofar....
Sai da safenku"
su duka ukun suka tashi jiki
babu kwari suka fice daga dakin"
suna fita ta turo kofar ta kulle
tasa sakata" suna ji suna gani
.
Rufe kofar keda wuya suka fara
yiwa juna banbami kamar zasu
bugi in buga"
Dayyabu wanda a fusace yace
"Duk abinda ya faru laifinku ne"
ku fito kuyi mata bayani kuce ga
abinda muke so" amma kowa
yayi shiru" kun barni sai ni kadai
nake ta magana
Kuma sai wani
abu ya taso kuce ku wayayyu ne"
haka ake wayewar? ance kuyi
mata bayani yadda zata gane
kunki
Auwalu ya karba da cewa duk
wa yayi mata maganar bani
bane?
Nine fa nace mata mun taimaketa
ya kamata muma ta
taimakemu kuna ji kukayi shiru
baku yi karin bayani ba Gaskiya
kun cucemu kawai asan abinda
za'ayi ni bazan yarda ba
.
Baban yara yace
Ni ai na gama nawa tunda nina
ganta na daukota nazo da ita
kuya kamata kuyi mata magana
dalla-dalla harta fahimci ga halin
da ake ciki amma kuna abu
kamar kuna jin tsoro Har yanxu
wallahi baku waye ba Dayyabu ya
sake duban sauran
abokanansa
Wai kuna jin da gaske bata gane
abinda muke nufi ba
Ni ina ganin fa kamar so takeyi ta
raina mana hankali
.
GASKIYA TA RAINA KU
KARKU YARDA HAHAHAHAHA
MAGANIN SHEGE AI SAI SHEGE DAN
UWAN SA
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 09
.

.
Auwalu ya katseshi da cewa
bata gane komae ba Ya za'ayi
ta gane bayan kowa ya kasa
cewa da ita komai Ni banga laifinta ba..Ko menene mu kuka
jawo
.
Samarin kauyen uku sun dade
suna ja'-inja a tsakaninsu kafin
Amadu baligi da yaransa uku su zo wajen a fusace
Da zuwansu ko sallama basu yi
ba Amadu baligi yaci kwalar
rigar baban yara ya fara yi masa
kwaratsi
Ina wannan bakuwar yarinyar da
aka ce ka dauko tana ina?
Baban yara da sauran
abokanansa biyu sun san matsayin Amadu baligi a
kauyensu don haka ba wanda
yake son rigima ya hadashi da
uban baligai indai mutum bazai
yi kokari yayi abota dashi ba ko
ya zama yaronsa to babu wani
mutun da zai zama makiyin
Amadu baligi
Baban yara ya nunawa Amadu
baligi dakinsa yace
tana ciki tana barci
kafin Amadu baligi yace wani
abu yaransa uku DAMINA DA GARUJE DA KWATSAMI suka
hada karfinsu suka bangaje
kofar dakin baban yara wacce
tayi tsawa ta fada cikin dakin
hade da wani tsohon bulo da
yake rike da ita shekara da
shekaru da kuma baragunsan
kasa wannan ya faru a lokaci
guda da farkawar talatu daga
barcin da ta fara"
Dayyabu da Auwalu suka koma
gefe a tsorace suka zama 'yan
kallo" Amadu baligi ya saki
kwalar rigar baban yara ya nufi
dakin da yake fayau babu kowa"
da shigarsa ya sami talatu a
tsorace tana kokarin fitowa"
Ganin yadda fuskar Amadu baligi
take cike da fushi da kuma
rashin tausayi sai talatu ta hutar
da kanta wajen tsayawa bashi
hankuri don kuwa ba yau maza
suka fara dukanta ba a wajen
yawace-yawacenta na dandi ba"
akwai yanayin da ake samu idan
namiji yayi fushi baya jin magiya
da kuma neman afuwa dole sai
ya buga sannan zuciyarsa zata
lafa ya hakura daga baya
Don haka sai talatu bakuwa ta
dora hannuwanta biyu akai
koda Amadu baligi ya shara mata
mari bai sami fuskarta ba sai dai
ya bugi hannunta talatu ta fara
kuka acikin dakin ragowar
samarin dake a waje suna
saurare basu yi yunkurin shiga
su ceceta ba
.
"Ba kece nace kibar garin nan ba
ki koma gida ba? kin dauka ina
wasa dake ne?
Amadu baligi ya ware karfi ya
rika gabza mata hannu kamar ya
samu kato dan uwansa hakan
yasa dole talatu ta bada kai" don
kuwa bazata iya jure kare kanta
ba ta fadi war-was tana ihu
hancinta yana zubar da jini a
tsakar dakin faduwar da tayi ne
tana haure-haure yasa tayi baza-
baza da tarkacen abincin da su
baban yara suka kawo mata
Amadu baligi ya jawo kwalbar
lemu daya a cikin kires zai
rusawa talatu a goshi kenan sai
yaji an rike hannunsa ta baya ya
juya a fusace a lokacin ne yaga
ADO GARUJE" yana yi masa murmushi
"Afuwa uban baligai"
ya amshi kwalbar daga hannun
Amadu baligi" sannan ya shiga
tsakaninsa da yarinyar wacce
ganin mai cetonta ya shigo sai
tayi saurin ja baya tana kokarin
gyara zaninta da ya kwance
bata daina kuka ba
"me yasa ka shigo garuje baka
barni na karyata ba don ubanta?
har kudin mota fa na kawo na
bata nace ta koma gida bana son
ganinta a wannan kasar tawa
amma da yake 'yar iska ce ta zauna bata tafi ba
.
Garuje wanda ya tabbatar ba
dole bane Amadu baligi ya
hakura indai yana ganin talatu a
dakin don haka sai yayi kokarin
fitar da yarinyar zuwa waje idan
aka rabashi da ita na wani dan
lokaci ya daina ganinta bayan
komai huce sai a barta ta fito
kafin aji umarnin da zai bayar a
lokaci na gaba
Ado garuje ya janyeta suka fita
waje inda su DAMMA suke tsaye
suna dariya wasu daga cikin
mutanen dake a layin 'yan ba
ruwanmu suka tsattsaya a waje
suna kallon abinda ke faruwa
don kuwa indai za'a ga wata
mace a tare dasu Amadu baligi
to an san ba 'yar mutunci ba ce
komai akaga suna yi mata ba
wanda zaice musu uffan
Da Amadu baligi ya fito daga
cikin dakin ne ya kalli baban yara
dake a gefe guda tare da
dayyabu ya nuna musu yatsa
yace dasu cikin kakkausar murya
ku kuma daga yau idan gilli ta
sake zuwa garin nan kuka
dauketa saina aikata ku zan
nuna muku ku kananan marasa
kunya ne anan gida kuke iskancinku ana kyaleku baku je
ko ina ba
.
Ba wanda ya mayarwa Amadu
baligi martanin maganarsa
saboda sun san ba tsaransu
bane ko ba komai maganarsa
da ya fada sun san gaskiya ne
su ukun marasa kunya ne a
kauyensu kawai shi kuma ya zauna a layin jan bulo yayi karen
babbar motar kaya na wata
takwas daga arewa zuwa
fatakwal" yaje abuja yayi wata
tara yana amsar hannun kwaryar
babur yana acaba a kowanne
dare idan masu babur sun gama
aikinsu na rana"
Wadannan kadan ne daga cikin
shaidar karatun yawon duniyar
da Amadu baligi ya mallaka
kuma akan biyun da za'ayi masa
jarrabawa a cikinsu zai fito da
sakamako mai gamsarwa"
shiyasa idan ya dubi mutum yace
dashi karamin mara kunya
baza'ayi wani musu ko jayayya ba
.
Su damma suka daukowa talatu
kayanta suka tasata a gaba suka
tafi da ita suka bar su baban yara da abokansa suna tunanin gyaran barna da asarar da ta
dado musu a cikin wannan dare
.
AI KADAN MA KENAN
KUKA GANI
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 10
.

.
Anyi haka da minti talatin Amadu baligi ya huce kamar
yadda ya saba ya dauko babur
dinsa a gida yazo gidan karuwai
inda su Damma suke tare da
talatu a waje suna yi mata nasiha
ko don gaba kada ta rika yin
taurin kai duk garin da ta sauka
ta rinka ladabi idan baligi ya
kafa doka a kasarsa kada tace zata karya
Amadu baligi wanda ya sake
ranshi yace da ita
zoki hau muje in mayar dake
gida
talatu ta taso daga cikin karatan
uku dake tsare da ita ta hau
babur din Amadu baligi tana rike
da ledar kunshin kayanta kamar
yadda tazo da su kafin Amadu
baligi yaja babur din ne su tafi ya
dubi yaran nasa yace dasu
Zan kaita tsaunin yalwa sai can
cikin dare zan dawo kada kubar
wadannan makadan borin su
kafa wasa saboda naga abin
nasu akwai rainin wayau
kwanaki sunyi wasa dan alherin
da zasu yiwa mutane ma suna
ganin asara haka suka tafi dama
nace zasu dawo garin su same ni
kada kubar kowa yahau bori yau
.
Amadu baligi yaja babur din suka
sheka a guje shida talatu a zaune
ta danne masa baya baiji lokacin
da kwatsami yace
Duk shegen da yace zai hau bori
yau kafin ya kira aljanun suzo
kanshi mu zamu fara mu hau kan nasa mu turmumusa mutum
yaji irin tamu dafin
Ragowar karatan biyu suka fashe
da dariyar shekiyanci a lokaci guda
.
BABI NA HUDU
GARIN DUBARUDU
Ban gunduma ce dake da hakimai da
kuma kansila idan aka koma
sashin mulki" akwai karamin
ofishin 'yan sanda wadanda
suke sasanta kananan rigingimu"
idan kuma abin yayi karfi sai su
dauka sukai babban ofishin
karamar hukuma"
Garin dubarudu" yayi suna wajen
gidajen mata masu zaman banza
kamar yadda ake sakaya masu
muguwar sana'ar tasu yadda
za'aji dadin fada wasan dambe
a garin dubarudu wani muhimmin abu ne mai zaman
kansa idan lokacin wasa yazo
baki sukan zo daga kowanne
lungu na cikin kasa da kuma
wadanda baza'a rasa ba daga
jamhuriyar niger
.
Babban gidan dambe yana daukar mutane fiye da dubu
shida" idan aka hada da 'yan
kallo da suke mikewa a saman
katangar da ta zagaye gidan" Da
yamma tayi za'a fara
rugunguntar zuwa a sami wuri
a lokacin ne makadan dambe
suke fara kida suna kirawo
mutane don kowa yazo bakin aiki"
Raba garin dubarudu da karuwai
abune da zaiyi wahala badon
komai ba sai don nan ne matattarar tsayawar motocin
safara idan mutum yazo
wucewa ta garin motocin da
suka yada zango a bakin titi zai
fara gani wanda irin wadannan
direbobin ne suka ajiye
karuwan" saboda su rika tsayawa wajensu duk sanda
suka kai kaya kudu suka dawo
Idan dare yayi ba abinda mutum
zaiji sai tashin kade-kaden
mawaka da 'yan amshi a gidaje
daban-daban bayan karuwai
akwai 'yan daudu dake sana'ar
abinci sannan kuma jefi-jefi
masu wasa da maciji sukan
kawo ziyara don garin
dubarudu ya tattara duk wani
nau'in holewa da sharholiya irin
na mutanen karkara
Wani direban tangul ya taba
dawowa daga aiki tare da
yaronsa suka sauka a garin
direban ya tambayi yaron motar
ko nawa suke dashi a hannu
yanzu yaron motar ya kirga
kudin yaga suna da tsabar kudi
dubu dari da arba'in direban ya
amshi dubu arba'in din ya bawa
yaron motar izin daukar dubu
ashirin yace yace ya zabi yarinyar
da zasu kashe kudin tare shi
dama yana da tasa da ya ajiye a
garin
.
Direban ya tafi dakin karuwarsa
sai yaron yayi kwanciyarsa a
cikin mota ya adana kudinsa
Bayan kwana biyu direban ya
sake dawowa wajen yaron
motar ya kara amsar dubu talatin
yace da yaron ya sake dauka
dubu ashirin shima yaje ya huta
Da yaron motar yaga ya sami tsabar kudi a hannu dubu
arba'in kuma da yaga kudin zasu
kare a banza a wajen karuwai
sai ya hau mota yaje gida yakai
nasa kudin aka sai masa maraki
na dubu talatin da biyar aka
daure masa
Yaje gidan ubangidan nasa ya sami matansa biyu ya tambayesu
menene matsalarsu ? matan wadanda suke zaune cikin
yunwa kwana da kwanaki ba abinci suka lissafawa yaron
motar maigidansu abubuwan da
suke bukata tun daga kan abinci
da sutura duk takalmansu sun
tsinke ko silifa basu dashi ga
katangarsu ta rushe mutane
suna ganinsu idan sunzo wucewa
yaron motar ya kashe masu
ragowar kudin duka yasa aka
gyara musu gidan yayi musu
komai da zai barsu ya koma wajen aiki har kuka suka rinka yi
suna cewa ya gaida musu mijinsu
Sun Gode ! Sun Gode!
.
Dole ne matan suyi godiya dan
kuwa a shekaru goma sha uku
da mijin nasu yayi yana jan
tangul bai taba tsinana musu
komai ba sai yanzu da yaron
motar nasa yazo musu da
wannan abin arzikin
.
Da yaron motar ya koma direban ya tambayeshi ragowar
kudi yace sun kare duka bai damu ba saboda yayi zaton
karuwarsa ya kashema wa sai
da suka koma gidane yaga abinda yaron motar yazo yayiwa
iyalansa sannan yaji labarin har
yaron ya sayi maraki da fara zuwa dashi aiki zai zama mai
arziki gashi shiko kaza bai mallaka ba a duniya daga shi sai
rigarshi
.
Aranar ya kira yaron ya zazzageshi fata-fata..
.
.
Loading page 11
KAZAR KARFI--> 11
.

.
A ranar ya kira yaron ya
zazzageshi fata-fata yace ya
koreshi ya nemi wani dan shaye-
shaye don kuwa a
cewarsa yaron sakarai ne bai san
aiki ba.
.
Irin wadannan garuruwa
wadanda suka tara karuwai
suna jawowa mutane da dama
rashin tattali da kuma fadawa
tashin hankali da fatara
Dubarudu gari ne wanda matan
aure suke fushi dashi don kuwa
akwai mazajen da suke wata da
watanni a dakin karuwansu ba
tare da sun tuna gida ba
Wadansu matan kuma dake a
kusa sukan hada kansu su zo
har gidajen karuwan su nemi
karuwar da ta rabasu da mijinsu
su casata su kwashe kayan
dakinta duka su ba 'yan dako su
kai musu gida
Shiyasa don kaje garin kaga
mutane suna sana'a da kuma
harkokin arziki amma kullum
suna a tsiyace to bata lokaci ne
mutum ya tsaya tambayar yadda
akayi kada mutum yaje garin
yaga matasa suna noma buhu
dari a shekara amma riga tana
neman kauce musu har ma a
tsaya mamakin ko meyasa?
.
Dirka-dirkan karuwai ne da suka
cika garin dubarudu dama
sauran garuruwan dake a
jahohin kasar nigeriya suna
taimakawa wajen koma bayan
tattalin arziki kuma suna
habbaka talauci da rashin aikin yi
.
Da karfe daya na rana Amadu
baligi yazo garin dubarudu ya
sami abokinsa Bala yana jiransa a
bakin titi da fitowarsa daga
mota suka tafa suna dariya kura
gareku masu awaki bala
yace da Amadu wanda ya bashi
amsa da kurari
sa'a dai ko dare ko rana wuya
koda magani ba dadi yaro. Suka
sake jinjinawa sannan
suka kama hanya zuwa inda
gidajen holewar suke acan
yamma da garin suna cikin
tafiya ne bala ya fara yiwa Amadu
tambaya akan talatu
ban hada komai da ita ba bala
kawai na mayar da ita gida
wajen babanta shine jiya yake
fada mani ta sake guduwa Bala
yace
Na ganta da idona tana wajen
wani dan dambe cikin bakin 'yan
wasan da suka xo
sunansa TAMARKE
ko dazu na gansu tare sun fito
sun sayi nama sun koma ina jin
daki ya kama mata
.
Amadu ba tare da wani zullumi
ba yace
muje in sameshi in fada masa
kanwata ce Balan dubarudu bai
kai Amadu
baligi wauta da jarumta ba
kuma bashi da wani tarihi mai
kayatarwa a yawon duniya dan
tarihin laifinsa bai taka kara ya
karya ba kawai dai an taba
kasashi a wajen neman wata
yarinyar da yake so a ranar da
aka daura auren yaje da yaransa
suka sami angon suka kamashi
da tsiya suka samu filayar
kwance noti suka cire masa
faratan kafafuwa dana yatsun
hannu saida yayi wata biyu yana
jinya kafin wasu faratan suka
sake fitowa
sannan kuma ya taba ajiye wani
mugun kare wanda ya addabi
mutane ba damar a wuce ta
kofar gidansu karen bai tasowa
mutum da cizo ba idan kuma
mutane suka bugi karen da
adda Bala yake fitowa ya bisu a
guje dole sai ya ramawa karen
sannan zai hakura" sai da 'yan
sandan tuhumar manyan laifuka
na jiha suka kamashi yayi wata
daya a hannunsu sannan suka
cusa masa ladabi na wucin gadi
aka sami saukinsa yadan saurara
Idan aka dauke wadannan
abubuwan bashi da wani tarihi
da 'yan sanda suka adana a fayil
dinsa
.
Amadu baligi da balan dubarudu
suka isa inda sansanin 'yan
damben suke suna a zazzaune a
gindin wata katuwar bishiya
inda wani mai balangu yayi
sabon gashi wani mai gurmi
yana zaune a benci a gefe guda
yana kada gurminsa yana waka
da katuwar muryarsa dake kama
da banbaro ba tare da kowa ya
mayar da hankali ya saurari
abinda yake cewa a wakar tasa
ba batare da shi kuma hakan
yasa ya gaji yayi shiru ba
Karuwai shida ke tare da 'yan
damben tara wanda hakan ya
nuna uku daga cikinsu ne kawai
basu tare da nasu karuwan
yawancin 'yan damben suna
sanyene da matsattsun singileti
wadanda suka fito da
kwanjinansu da kuma jijiyoyin
hannun kamar igiyar daure dami
Ba wanda zaiso ya kalli
fuskokinsu don kuwa dukan
yau da kullum ya canjawa kowa
halitta a cikinsu wani hancinsa ya
murgude wani kuma habarsa
ta karkace wani kuma bashi da
hakoran gaba wani idonsa daya
ya mutu da wahala a sami wani
dan dambe daya a cikinsu wanda
komai nasa yake lafiya garau
kamar yadda babarsa ta haifeshi
.
Amma matan da suke tare dasu
basu damu da muninsu ba
saboda kowacce tana sane da
dubban kudin da ake ajiyewa a
matsayin
( KAZAR KARFI )
A Filin wasa kuma duk wanda
yayi
nasarar yin kisa kacokan ake
daukarsa a bude huluna ana
zagayawa dashi cikin fili 'yan
kallo suna zuba masa kudi suna
yi masa jinjina saboda in dai kato
zaiyi kisa ya sami kudi mezai
hana su zauna dashi suyi
nema?
.
Kafin Amadu baligi yayiwa kowa
magana a cikinsu ne Bala ya kira
daya daga cikinsu wanda yafi
sabawa dashi Akwai tamarke a
wajen yana zaune yana gyara
wata katuwar layarsa wacce ta
fara barewa a hanci babu talatu
a wajen me yiwuwa tana dakin
da tamarke ya kama mata
Amadu da bala da daya daga
cikin 'yan damben suka kebe
gefe guda mai kada gurmin
wanda ya karkace hularsa
kwaurin ladi ya fara yiwa bala
waka saurayin ya juya ya
harareshi sannan da ya dawo da
hankalinshi kan dan damben
yace dashi....
.
ANA WATA GA WATA KENAN
TALATU TA ZAMARWA UBAN
BALIGAI CIWON KAI
12 LOADING..
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 12
.

.
Ka gane ko WARURE
wannan aminina ne ba anan
garin yake ba to wata kanwarsa
ce ta gudu daga gida tazo nan
garin jiya ita ce yarinyar nan da
tamarke yayi kwanan gida da ita
jiya dazu ma na gansu tare to
shine muke so a taimaka mana
ka fadawa tamarken ya sallami
yarinyar ta fito mu tafi da ita
Warure ya girgiza kai yace dasu
kun san halin wancan dan iskan
ba mutunci ne dashi ba ba lallai
bane ya bada hadin kai ya fito da
ita ba ina jin yarinyar
ma bata nan yanzu tabi wasu
yara sun tafi wajen wani ajo da
akeyi
sai a lokacin Amadu yasa baki
yace
kayi masa magana mana
kanwata ce ya fada mana inda
akeyin ajon sai muje mu sameta
acan
warure ya juya ya dubi inda
abokan sana'ar tasa suke zaune
suna hayaniya da zage-zagen
wasa a gindin bishiyar ya
daga murya yace tamarke ji
mana
.
Katon wanda Zai iya kayar da
bajimin sa idan suka hadu ya
dago kai a fusace
me ye fa?
ya bukata da kakkausar muryasa
yana zaro idanu da warure ya
tabbatar tamarke bazai zo ya
samesu ba saiya tambayeshi
ka gane wai gillin nan daka
tsinta jiya suke nema ina take
ne?
tamarke ya hada rai ya mayar
masa da martani
su waye suke nemanta? me
zasu bata?
Da Amadu baligi yaga kamar kan
yaron ya cika da zapi sai yace
dashi a fusace shima aki kada ka
daukemu kananan
yara mana! Muna tambayarka
inda talatu take ne Ina ruwanka
da abinda zamu bata kasan
yadda muke da ita ne?
tamarke ya tashi tsaye kamar
wanda aka watsawa wuta yace
da Amadu
kai dan Iyayenka kasan ni ko
wanene kake fada mani haka?
to na boyeta bazan fito da ita
ba Ka ware in daina ganinka
anan in ba haka ba zan aikata ka
billahillazi
Bala ya dafa Amadu baligi don
kada fada ta shiga tsakaninsa da
yaron sauran 'yan damben suka
fara ba yaron baki
yawane tamarke wannan ba
tsaranka bane kawai ka barsu su
ware
wata karuwa tace dashi tana
dariya
kisan kai kake so kayi tamarke!
saboda waccan abin kake
mikewa? to kace kayi fada dawa
idan ka bugeshi ya fadi? idan
karfi kakeji ka bari anjima zan sa
maka
KAZAR KARFIN
Sarkata in hada ka da mai gidana
.
Ta bugi kirjin wani faskeken kato
wanda yayi dariya ya tona asirin
wawulonshi babu hakuran gaba
Haba barshi dai yayi da
tsararrakinsa kada ki zuga yaro
ki jawo a binneshi anjima da
daddare
Amadu baligi yayi murmushi ya
tambayi tamarke
kai ni kake zagarwa iyaye?
tamarke ya sake tasowa ya
matso gaba
"Dan uwarka an zageka! Me zaka
yi?
Kafin bala ya rike Amadu tuni har
ya nufi inda tamarke yake a guje
warure ya bishi don ya shiga
tsakaninsu da tamarke sauran
'yan damben suka yi zaune suna
kallon yadda fadan zai kasance
suna dariyar mugunta don
kuwa a yadda suka san zafin
hannun tamarke ba karamin
wauta wannan bako yayi ba da
zai fada masa"
TO AMMA ZAFIN HANNUN
TAMARKE SUKA SANI
BASU SAN ZAFIN HANNUN AMADU
BALGI BA
.
Kartin biyu suka hadu da juna
tamarke ya fara kawowa Amadu
duka wanda ya rika
bahaguwarsa ya dakatar dashi ta
hanyar tokareshi baya" kafin
tamarke ya samfa daya hannun
nasa tuni har Amadu baligi ya
aika badamiyarsa wacce tafi illa a
fuskar mai tsautsayi
.
Da fadawar hannun Amadu akan
fuskar tamarke ya fada ihu ya
fadi a rikice saurin dukan da
Amadu yayi masa kamar yanayin
da zai faru da mutum ne idan
hannun fanka ya mareshi idan
ya mike akan kujera bai sani ba
fuskar tamarke tayi dameji
kamar fuskar gilashi a duka daya
tayi ratsi-ratsi kamar
tamarke yayi hadarin mota 'yan
damben suka tashi a fusace tare
da karuwansu suka ja baya suna
kallon Amadu baligi
saboda basu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment