Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yara ya nufi shagon wani
abokinsa mai katon kai kamar
dan ruwa" wanda baya son fitar
kudi a hannunsa" kuma ba
karamin kunyar mutum zaiji ya
bashi bashin kaya ba" Amma da
yake shima ba mutumin arziki
bane" Idan aka zo masa da zancen bakuwa bata da gurin kwana yakan yi rawar jikin zuba
nasa hannun jarin akai mata Baban yara ya sanarwa dayyabu
yana son lemo kwalba biyar
manya" amma fa zai lamunce shi
cikon kudin sai gobe"
Dayyabu dake cikin shagon yana
sauraron baban yara" ya mirgina
katon kansa cikin rashin
amincewa"
"Gaskiya kayi hakuri baban yara" saboda ina son zanje
sayayya ne gobe" kudin nake ta
faman hadawa basu gama
haduwa ba ma" lemun nan bazai
samu ba gaskiya"
Baban yara ya rokeshi a karo na biyu"
"duka nawa zaka biyoni ? ina da dari biyu a hannuna gata" baifi ka bini dari da hamsin ba dayyabu"
saurayin ya sake mirgina katon
kansa" Tab! Dari da hamsin?" ya fada
cikin jimamin yawan kudin"
.
"Gaskiya baxan iya ba baban yara" duka nawa muke cin riba a
sana'ar ? kasan tireda fa ba wani
riba gareta ba" yanzu kaga biskit
sai ka sayar da kwali daya baifi
ka sami naira ashirin ba sai in wuni anan banci dari da hamsin
din ba" sai ai ta ganin mutum wasu kudi yake samu kuma duk
abin hakuri ake yi
Dayyabu yayi tsaki don kuwa
har ya tuno da lissafin da yayi
dazu da safe na wasu kudi
yana zaton zaiga dubu uku yaga
dubu biyu da dari shida baisan
abinda yaci dari hudun ba yau
wuni yayi yana fada da
kwastomominsa akan fushin
wadannan kudi da ya rasa inda
suka makale Ga kuma wannan baban yara ya wani zo wai a
bashi bashin lemu bazai yiwu
ba gaskiya!
Da baban yara ya tabbatar bazai
samu bashin lemu a wajen dayyabu mai shago ba sai ya
koma gefe yayi kamar zai tafi ya
fara sake-sake a xuciyarsa yana
magana yana cewa a baiyane
kamata yayi kawai in sayi kwalba uku in hankura ai sun
isheta dama dai zai danfi dacewa ne taga anzo da
kwalaben lemun da yawa babu
harkar karanta
.
Da Dayyabu mai shago yaji baban
yara yana maganar ashe wata
bakuwa zai kaiwa lemun sai ya
daga murya daga cikin shagon
ya tambayeshi
kunyi bakuwa ne baban yara?
ya bashi amsa sau daya a takaice
Eh sanna ya koma kan lissafin
da yake yi da hannu Dayyabu ya
sake tambayarsa cikin kosawa
yar uwarku ce tazo ko kuwa dai
tsintuwa ce Baban yara?
wata tsintuwa ce nayi dayyabu
yace da mai shagon
Dayyabu yayi saurin fitowa daga
dan tsukin shagon nasa da yafi
kama da dakin tantabaru ya saki
ranshi ya fara fara'a har zuwa
lokacin da yazo ya tsaya a inda
baban yara yake yace dashi
to ai kai baban yara ai gayamun
abinda ake ciki zakayi tunda
wuri ban san bakuwa kayi ba ai da babu abinda zai gagara
bari in debo lemun kwalba
nawa kake ganin ya kamata akai mata a wadace?
.
Baban yara wanda yayi mamakin
yadda dayyabu mayen kudi ya
canza ra'ayi lokaci kankani yace dashi
Dama kwalba biyar nake so a kai
mata" ko dai bazata shanye su
duka ba ai kaga anyi mata burga
Dayyabu yayi farat yace dashi"
"kwalba biyar din me kuma?" ai
irin wannan kiras daya ake kaiwa a ajiye baban yara" tasha-tasha har ta gaji" idan ta tafi sai a
dawo da ragowar ko nawa ta
rage" bari in shiga in hado kiras daya akai mata" kaga sai muje
tare koya ka gani?"
shakiyan samarin kauyen biyu
suka tafa hannuwansu suna
dariya"
Baban yara yace
"Ba komai dayyabu ai duk daya ne nima idan kayi tsintuwa ai
kana tunawa dani
Dayyabu ya koma cikin shagon
da sauri" ya bude katuwar
randar da yake zuba lemuna a
ciki" ya jawo kiras din da babu
komai a ciki ya fara tsamo
kwalaben lemun daga cikin
sabuwar randar dake cike makil
da ruwa har wuya" ya rinka
shirya kwalaben a cikin kiras din
kala-kala bakake da jajeye da
shudaye" saida ya cika kowanne
gurbi sannan ya kinkimi kires din
yayi waje dashi" inda baban yara
yake a tsaye yana jiranshi"
.
"Ai kaga haka yafi baban yara"
ince dai kwana zatayi ko bada sauri zata tafi ba?
Baban yara ya tarbeshi ya amshi
kires din lemun cikin farin ciki"
sannan yace dashi
"kwana zatayi mana" ta isa tace
zata tafi ne" a ina zata kwanta""
na fada maka tsintuwa ce ta
fado hannuna a banza" sai
yadda nayi da ita"
Dayyabu ya fashe da dariyar jin
dadi" baban yara yace bari in
kai mata lemun sai in dawo
akwai Auwalu shima yana can zaizo" shi kuma a bangarensa
indomi za'a samu da kwai da shayi
Dayyabu yace
"yauwa, to ai kaga haka yafi baban yara" shi dama harka irin
wannan idan zamuyi ita" to mu rika nuna muma fa mun waye" ai abin duk barazana ce! Ko acan
gari suma ba wata tsiya suke
kashewa matan ba" duk karya
ce" gara mu nuna mata muma
wayayyau ne" don kada ta rainamu"
.
Baban yara yayi dariya" ya juya
zai nufi dakinsa ya kaiwa talatu
bakuwa kires din lemun wanda
ya rikeshi hannu bibbiyu" kafin
ya tafi ne dayyabu ya kalli
kwalaben dake cike da kires din
da kuma makudan kudin da suka
lashe" sai ya matsa yace da
baban yara cikin sanyin jiki"
"to baban yara" dan Allah ka rike
amana" ita kadai zata sha" mu hakura zamuyi" idan muka
samu tasha ko kwalabe biyu ne"
sai mu dawo da sauran idan ta
tafi" ba tararwa lemun zamuyi
muyi ta sha ba kaga bashi nake
amsoshi a gari kuma gobe zanje
inyi musu balas in amso wani
Baban yara yace dashi
"Ai na sani dayyabu" kada ka
damu bazan sha maka lemu ba"
ita kadai za'a ajiyewa"
Dayyabu mai shago ya saki ranshi
yauwa to yi sauri ka dawo mu
shirya yadda za'ayi
Baban yara ya kinkimi kires din
lemun ya kai dakinsa ya samu bakuwar a zaune a bakin gado
kamar yadda ya barta dazun" da
shigarsa yayi murmushi
kiyi hakuri" na barki a zaune
ke kadai tun daxu ko?
tace dashi a sanyaye kamar
wacce take mura! ba komai
.
Baban yara ya ajiye mata kires
din a gabanta cikin barazana
yace da ita
To ga abin sanyaya makoshi fa
na kawo maki bana so ki rage
mani koda kwalba daya bari in
dawo kada dai ki kosa
talatu tayi murmushi bata ce
dashi komai ba har baban yara
ya sake bazama ya fita jikinshi na
rawa yazo daidai shagon dayyabu kenan yaci karo da
Auwalu mai shayi ya gama hado
tasa gudumawar yana dauke da
katuwar samira a hannu daya a
daya hannun kuma kofin shayi
ne da katon biredi guda daya akaiKAZAR KARFI--> 04
.
Baban yara da dayyabu suka
tarbeshi kowanne ya amshi hannu daya Auwalu yace cikin
damuwa
ya ake ciki ne tun dazun inata
jiranka ka dawo ka dauki
indomin mu tafi najika shiru
Baban yara yace dashi Na tsaya nan wajen dayyabu ne
na amshi lemun nakai mata
Auwalu ya kalli dayyabu cikin
rashin amincewa da ganinshi
tare da baban yara suna
maganar bakuwa tare bai so
dayyabu ya shigo cikin al'amarin
ba Da dayyabu ya fahimci haka a
fuskar Auwalu sai yayi saurin cewa
Na bada kires din lemu akai
mata saboda kada mu nuna
mata karanta ta daukemu
kauyawa
.
Jin hakan yasa Auwalu ya saki
ranshi don kuwa dama baya so
ace shi kadai zaiyi asara su kuma
su kwashi gara basu bayar da
komai ba duk da haka don dai
ya kara ba dayyabu wani aikin
sai yace a karshe
to za'a kai lemu ne babu biskit
dayyabu! ka dauko kwali daya a
bude shi a gabanta shima duk
karin gada guri ne
Dayyabu yace ba matsala bari in
dauko
Ya sake shiga cikin shagon ya
dauko kwalin biskit mai 'ya'ya
wanda ba'a budeshi ba daya fito ne yace
Bari in kulle shago na muje kada mu barta ita kadai
.
Ya dauki kwalin biskit din kamar
wanda zaije wajen baikon aure"
baban yara ya dauki samirar
dake cike da indomi da kwai an
shimfida a sama" yana ta
kwarara kamshi" shi kuma
Auwalu ya dauki biredi da shayin
suka dugunzuma su ukun suka tafi dakin"
Baban yara suka sa gaba tunda
shi yasan yarinyar" shi ya
jagorancesu suka shiga" talatu
tana a zaune kamar wacce aka dasa
Baban yara yace yana fara'a
to gamu mun shigo
Ya ajiye kwanon samirar a kusa
da kires din lemun Auwalu ya
ajiye mata nasa kofin shayin da biredin" Dayyabu ya ajiye mata kwalin biskit" talatu ta kalli lodin
kayan sun cika tsakar dakin
kamar wadanda suka fito da
kayan lefe a gani"
"ta tambaye su"
"duk wadannan kuma na menene?
Baban yara yace da ita
Duk abinci ne" kin san ance yana
da kyau ka karrama bakon ka"
Ya juya kan abokansa biyu da
suka rakoshi" suna zare idanu
suna kallon talatu yace da ita
wadannan abokai nane sunzo ne
su gaisheki suma"
talatu tayi murmsuhi"
"sannunku malamai" ina wuni?"
Dayyabu da Auwalu suka kware
baki suka amsa a lokaci guda
"lafiya lau"
.
Suka ci gaba da murmushi ba
tare da sun san abinda zasu ce
da ita ba" baban yara ya dubi
lemun yaga bata dauki ko daya
ba" ya tuna baizo da abin bude
kwalba ba" yayi saurin daukar
kwalba daya yace
"Bari a bude maki lemun ki fara
dashi" yara sun dauke mani
ofiner" bana rabuwa da ofina a
dakin nan
Yasa hakori ya fara kici-kicin
bude lemun da karfi har yana
rintse idanu"
Dayyabu yace
"mancewa nayi" ni kuma dana
taho da tawa ofina ta shago"
Da kyar baban yara ya bude
kyalbar lemun ya taso da karfi ya
fito ya jika mashi fuska" yayi
saurin ajiye kwalbar yana borin kunya"
"Gas yayi yawa a wannan kwalbar shi yasa take da
wahalar budewa"
ya turawa talatu kwalbar a
lokacin ne tace dasu"
"to ku dan bani wuri mana inci
abincin naku..." tayaya zan iya cin
wani abu ku uku kun tsareni da kallo ?
.
Kamar wadanda suke jiran umarninta tana fadar haka su
duka ukun sukayi waje" suka fito
suka tsugunna a bakin kofar
suka fara yin kus-kus cikin rada
suna magana
Dayyabu ya fara yiwa baban yara korafi
"kana ganin zata bada hadin kai
kuwa baban yara ?
"Ba matsala dayyabu"
Baban yara ya karfafa masa gwiwa
Kasan yanzu tana jin yunwa ne"
bata ci abinci ba" mu jira taci ta
koshi sannan sai mu shiga mu
fada mata abinda muke so zata
amince"
Auwalu mai shayi wanda ya kasa
kunne yana sauraron radar da suke yi yace a karshe Nima ina ganin kamar haka-
haka take" kada fa kaja muyi wahalar banza baban yara!
ya juyo bangaren Auwalu dake a
gefensa daga hagu yayi kasa-
kasa da muryarsa yace dashi
"kada muzo da kosawarmu a fili
Auwalu" kasan irin wadannan
wayayyun yaran na gari sai
anbisu a hankali" ba gaggawa
ake musu ba"
Suka yi shiru suna jiran talatu ta
gama cin abincin"
Baban yara ya leka dakin ta
hanyar wasu huje-huje dake a
jikin tsohuwar kofar tasa"
ya sameta a kishingide akan
gadon har taci abinda taci ta fara
shirin yin barci" yayi saurin
juyawa inda sauran abokan nasa
suke a zaune sunyi jigum suna
jiran tsammani" yace dasu ta hanyar sirri
.
"ta gama cin abincin" ya za'ayi kenan?"
Dayyabu ya mike yace
"to kunga dai na fiku bayar da
kayayyaki a harkar nan" gaskiya
nizan fara shiga"
Auwalu ya kwabeshi da sauri
kaji kauyancin banza haka kawai zaka shiga sangwam-gwam ba ayi mata bayani ba fa
ai sai an dan yi hira tukunna an
nuna mata inda aka fuskanta
sannan zata yarda" ku kuna
abune da jahilci har yanxu
Baban yara yace
Gaskiya ne Auwalu to kuzo mu
shiga muyi mata bayani kada tayi
barci naga ta fara gyan-gyadi
.
Bayan samarinn uku sun gama
gudanar da shawarwarinsu a
waje sai suka sake shiga cikin
dakin su duka suka sami
bakuwar a kishingide akan
gadon ta dan tsakuri abincin
kadan ta kurbi lemun baifi sau
biyu ba bata taba shayin da
suka ajiye mata ba ballantana
kuma dirkeken kwalin biskit din
dake jiranta
Da taji motsin shigowarsy saita
bude idanu ta tashi zaune tayi
hamma sannan ta dan bata ranta
Barci take ji fa gaskiya
Baban yara wanda yake son ya
kwantarwa da abokansa biyu
hankali don kada su damu yace
da bakuwar
Haba tun yanxu zakiyi barci ko
hira bamu yi ba?
Sai a lokacin Auwalu yayi kokarin
yin magana
Ai bata ci abincin ba ma naga
koma yana nan bata taba ba
Da yake baya iya yi mata
magana baban yara yake yiwa
korafin to amma duk da haka
sai ta bashi amsa tace dashi kai
tsaye
.
Don kada ma kuce nayi muku
wulakanci ne banci ba shiyasa na
dan tsakura nagode
samarin uku zazzaune a kasa
babu ko tabarma suka tasa
bakuwar tasu suna kallonta
wacce take a hakimce akan
gado ita ta fara yi masu
magana akwai alamar sun fara
isarta tace dasu
to naji kunce zakuyi hira wacce
iriyar hira kuke so ayi na fada
maku barci nake ji
A lokacin dayyabu ya dunguri
baban yara da kafa yana nuna
masa ya fito fili yaya magana ba
boye-boye
Baban yara ya fara inda-inda yace
Eh to kinsan ai idan aka ce miki
ga samari da 'yan mata dole ayi
hira ayi soyayya koba haka bane?
talatu tace
Gaskiya kuwa haka ne baban yara yaci gaba da cewa
yauwa, to dama haka nake nufi"
amma dai ina jin ga Auwalu yana
da magana" bari kiji komai a
bakinsa" Auwalu yi mata bayani"
Auwalu mai shayi ya gyara zama
yadan sosa kai yace
"Eh..ai duk abinda ka fada baban
yara ba kuskure daman dai shi
komai na rayuwa ance taimakeni
in taimakeka.. Ko ba gaskiya ba?" to amma ga dayyabu bari yayi maki bayanin abinda ya
kamata Dayyabu kayi magana
.
Auwalu da baban yara suka dubi
dayyabu wanda baiyi tsammanin
shi zasu dorawa wannan nauyin
ba" ya fara dabircewa ya ce
"to...ai kun gama magana" mudai
soyayya ce ta hadamu dake"
kuma yadda muka fara da
mutunci" to bazamu kare da
rashin mutunci ba" Rayuwa juyi-
juyi ce... Duk wannan abu da
kikaji muna fadi maki to soyayya
ce" mun san ke wayayyiya ce" kin
gane abinda muke nufi"
talatu ta yatsine fuskarta kamar
zata yi kuka
"Nifa malamai gaskiya ban
fahimci abinda kuke nufi ba"
kunki fitowa ku fada min
magana sai kewaye-kewaye kuke
tayi mani" ina ga da zaku fito ku
fada mani abinda kuke nufi
gaskiya zaifi"
samarin kauyen uku suka kalli juna
Auwalu tace
Baban yara kayi magana mana"
ya zatayi mana haka?
Baban yara ya juya ya kalli dayyabu yace"
Dayyabu ka sake yi mata bayani
yadda zata gane
Dayyabu ya kalli talatu ya tambayeta yanzu ke malama duk wannan
maganar da muke yi baki gane
inda muka dosa ba" baki
fahimcemu ba"
talatu ta girgixa kai tace Gaskiya ni ban gane ba
.
Auwalu yayi karfin hali yace da ita"
Amma dai ai kin san Hausawa
sunce ita rayuwa ka taimakeni ne
in taimake ka!
talatu tace cikin fushi-fushi
"Eh, tun dazu ai kuke ta fadar
haka" to me kuke nufi da
taimakeni in taimakeka? gani
nayi baku sanni ba" nima ban
sanku ba" sai yau muka hadu" to
kun bani wajen kwana" gashi
har na kwanta" kun kawo mani
abinci naci" to me kuke so kuma
inyi maku" sai ku fito ku fadi gaskiya" na gaji da wannan
dogon turancin" barci nakeji" in
zakuyi magana kuyi magana" in
bazaku yi magana ba" don Allah
ku tashi ku fita barci zanyi" zan kulle kofa
Samarin uku suka sake kallon juna kowa yana tsammanin dan
uwansa zaiyi magana da bakuwar tasa suna ta bata mata lokaci sai zare idanu suke yi saita tashi daga kan gadon ta tsaya kansu tace ku dan fita in rufe kofar....
Sai da safenku"
su duka ukun suka tashi jiki babu kwari suka fice daga dakin"
suna fita ta turo kofar ta kulle tasa sakata" suna ji suna gani
.
Rufe kofar keda wuya suka fara yiwa juna banbami kamar zasu bugi in buga"
Dayyabu wanda a fusace yace
"Duk abinda ya faru laifinku ne"
ku fito kuyi mata bayani kuce ga
abinda muke so" amma kowa
yayi shiru" kun barni sai ni kadai
nake ta magana
Kuma sai wani
abu ya taso kuce ku wayayyu ne"
haka ake wayewar? ance kuyi
mata bayani yadda zata gane
kunki
Auwalu ya karba da cewa duk
wa yayi mata maganar bani
bane?
Nine fa nace mata mun taimaketa ya kamata muma ta
taimakemu kuna ji kukayi shiru
baku yi karin bayani ba Gaskiya
kun cucemu kawai asan abinda
za'ayi ni bazan yarda ba
.
Baban yara yace
Ni ai na gama nawa tunda nina
ganta na daukota nazo da ita
kuya kamata kuyi mata magana
dalla-dalla harta fahimci ga halin
da ake ciki amma kuna abu
kamar kuna jin tsoro Har yanxu
wallahi baku waye ba Dayyabu ya sake duban sauran
abokanansa
Wai kuna jin da gaske bata gane
abinda muke nufi ba
Ni ina ganin fa kamar so takeyi ta raina mana hankali . . .KAZAR KARFI--> 05

.
Matar tace dashi
"ka ga dari biyu nan akan kabet"
to wallahi ita kenan dani" ita din
ma kudin adashi ne ban riga na
aika ba Baban yara sai dai kayi
hankuri da ita"
ta miko masa" ya amsa cikin
sanyin jiki" saurayin dan kimanin
shekaru ashirin da uku" gwani
ne wajen kure kai indai akan
mace ne
Yace da ita
Bani samira inje in hado masa
abinci Hada min kofikan zuba
lemo ta dauko masa samira a
cikin
dakinta a sama ta hado da
cokali da kofikan zuba lemo
biyu" har zai fita sai ya sake tuno
wani abin
"Dan taimaka mini da mafici da
rikoda
Da yake ta saba da irin wannan
are-aren kayan sai ta dauko
masa rikoda da maficin"
Ban daiyi zubi ba batiran sunyi
sanyi sai ka sayi sababbi
Baban yara ya fice ba tare da ya
tsaya sauraron shawararta ba
ya koma dakinsa dake kofar
gida ya kaiwa talatu maficin ya
ajiye rikodar a kusa da ita ya ce
"wani shashashan kani gareni
zuwa yake yi yana daukar mini
kaya yana shiga dasu cikin gida"
baya dawo min dasu sai naje na
dauko da kaina na rasa inda ya
kai mani bidiyona da janareton
da nake tayarwa yana ba dakina
wuta har fankata ma ban san
inda ya kaita ba
.
Baban yara yayi tsaki" talatu tayi
murmushi a karo na farko tace
"Ai ba komae ko haka ma ya isa
ta daga kanta ta duba ko ina a
cikin dakin bata ga inda turken
kwan lantarki yake ba babu
kuma wani soket a jikin bango"
babu wuta a garin" bata san
yadda wannan saurayi yake ba
dakin nasa wuta da janareta ba
tare da waya ba
Bata yi masa bayani ba ko
tambaya a game da haka ta
barshi ya tafi dauke da katon
kwanon da zaije sayo mata
abinci"
Ya isa dandalin garin inda masu
abinci da masu sayar da
shayi da kwai suke da rumfuna"
ga jama'a nan a zazzaune a ko
ina akan benci" samari da kuma
matasan dattawa"
Baban yara ya sami daya daga
cikin masu sayar da shayin da
kuma indomi" ya kebeshi don
kada mutane suji bayanin da
yazo
yayi kafin ya sayi abinda yake so"
su koma bayan rumfar" Da
zuwansu baban yara ya mika
masa dari biyun yace dashi
"ka gane Auwalu wata bakuwa
nayi yanzu-yanzun nan to ina son
ka hadani sosai dari biyun nan
kawai gareni" ka hada mani
indomi guda biyu ka soya kwai
biyar ka hada mani shayi dabam
a kofi ka zuba madara
gwangwani daya muji nawa ka
biyoni gobe zan baka kudinka...
Ba wasa Auwalu"
.
"Dan siririn mai shayin mai kama
da karas" ya washe baki da
zumudi yace da baban yara
"to kai irin wannan idan ta samu
ai muma ya kamata ku rika
tunawa damu baban yara a ina
ka samota ? Baban yara yace a
banza na
ganta dazu a bakin gari ina jin
bakuwar gilli ce tazo bata sami
daki ba"
Auwalu mai shayi yace
"A to gaskiya nima ina ciki
baban yara" bari in hada mata
komai da komai muje sai in bar
yaro ya tsare min shagon kafin
mu dawo
Baban yara yaba Auwalu mai
shayi hannu suka tafa faa!!"
sukayi dariya"
"kai mutumin nan" ashe kaima
baka barin banza ta wuce ka?
"Ina fa zan bari baban yara ?
Auwalu mai shayi ya koma cikin
rumfar ya fasa kwayaye yana
kadawa" yasa yaronshi ya dora
taliya a wuta baban yara ya
zauna a benci yana jiranshi ya
gama su tafi"
Akwai alamar yaji dadin wannan
hadin gwiwa da Auwalu mai
shayi ya nemi su yi Dama bashi
da kudi dari biyu ne da yazo da
ita ta huta itama to amma akwai
bukatar ace sun sayi lemun
kwalba ya mance ashe da
sauran cefane gashi kuma
Auwalu baya sayar da lemo" to
amma tunda dayyabu mai shago
yana dashi" bari yaje su
shawota
Yace da Auwalu"
"kafin ka gama hada indomin da
kwan" bari inje wajen dayyabu in
sayo lemu in dawo"
Auwalu yace dashi
"to, kayi sauri fa" ba dadewa zan
gama"
.
Baban yara ya nufi shagon wani
abokinsa mai katon kai kamar
dan ruwa" wanda baya son fitar
kudi a hannunsa" kuma ba
karamin kunyar mutum zaiji ya
bashi bashin kaya ba" Amma da
yake shima ba mutumin arziki
bane" Idan aka zo masa da
zancen bakuwa bata da gurin
kwana yakan yi rawar jikin zuba
nasa hannun jarin akai mata
Baban yara ya sanarwa dayyabu
yana son lemo kwalba biyar
manya" amma fa zai lamunce shi
cikon kudin sai gobe"
Dayyabu dake cikin shagon yana
sauraron baban yara" ya mirgina
katon kansa cikin rashin
amincewa"
"Gaskiya kayi hakuri baban yara"
saboda ina son zanje
sayayya ne gobe" kudin nake ta
faman hadawa basu gama
haduwa ba ma" lemun nan bazai
samu ba gaskiya"
Baban yara ya rokeshi a karo na
biyu"
"duka nawa zaka biyoni ? ina da
dari biyu a hannuna gata" baifi
ka bini dari da hamsin ba
dayyabu"
saurayin ya sake mirgina katon
kansa" Tab! Dari da hamsin?" ya
fada
cikin jimamin yawan kudin"
.
"Gaskiya baxan iya ba baban
yara" duka nawa muke cin riba a
sana'ar ? kasan tireda fa ba wani
riba gareta ba" yanzu kaga biskit
sai ka sayar da kwali daya baifi
ka sami naira ashirin ba sai in
wuni anan banci dari da hamsin
din ba" sai ai ta ganin mutum
wasu kudi yake samu kuma duk
abin hakuri ake yi
Dayyabu yayi tsaki
.
06 LOADING.......
KAZAR KARFI--> 06
.
.
Dayyabu yayi tsaki don kuwa
har ya tuno da lissafin da yayi
dazu da safe na wasu kudi
yana zaton zaiga dubu uku yaga
dubu biyu da dari shida baisan
abinda yaci dari hudun ba yau
wuni yayi yana fada da
kwastomominsa akan fushin
wadannan kudi da ya rasa inda
suka makale Ga kuma wannan baban yara ya wani zo wai a
bashi bashin lemu bazai yiwu
ba gaskiya!
Da baban yara ya tabbatar bazai
samu bashin lemu a wajen dayyabu mai shago ba sai ya
koma gefe yayi kamar zai tafi ya
fara sake-sake a xuciyarsa yana
magana yana cewa a baiyane
kamata yayi kawai in sayi kwalba uku in hankura ai sun
isheta dama dai zai danfi dacewa ne taga anzo da
kwalaben lemun da yawa babu
harkar karanta
.
Da Dayyabu mai shago yaji baban
yara yana maganar ashe wata
bakuwa zai kaiwa lemun sai ya
daga murya daga cikin shagon
ya tambayeshi
kunyi bakuwa ne baban yara?
ya bashi amsa sau daya a takaice
Eh sanna ya koma kan lissafin
da yake yi da hannu Dayyabu ya
sake tambayarsa cikin kosawa
yar uwarku ce tazo ko kuwa dai
tsintuwa ce Baban yara?
wata tsintuwa ce nayi dayyabu
yace da mai shagon
Dayyabu yayi saurin fitowa daga
dan tsukin shagon nasa da yafi
kama da dakin tantabaru ya saki
ranshi ya fara fara'a har zuwa
lokacin da yazo ya tsaya a inda
baban yara yake yace dashi
to ai kai baban yara ai gayamun
abinda ake ciki zakayi tunda
wuri ban san bakuwa kayi ba ai da babu abinda zai gagara
bari in debo lemun kwalba
nawa kake ganin ya kamata akai mata a wadace?
.
Baban yara wanda yayi mamakin
yadda dayyabu mayen kudi ya
canza ra'ayi lokaci kankani yace dashi
Dama kwalba biyar nake so a kai
mata" ko dai bazata shanye su
duka ba ai kaga anyi mata burga
Dayyabu yayi farat yace dashi"
"kwalba biyar din me kuma?" ai
irin wannan kiras daya ake kaiwa a ajiye baban yara" tasha-tasha har ta gaji" idan ta tafi sai a
dawo da ragowar ko nawa ta
rage" bari in shiga in hado kiras daya akai mata" kaga sai muje
tare koya ka gani?"
shakiyan samarin kauyen biyu
suka tafa hannuwansu suna
dariya"
Baban yara yace
"Ba komai dayyabu ai duk daya ne nima idan kayi tsintuwa ai
kana tunawa dani
Dayyabu ya koma cikin shagon
da sauri" ya bude katuwar
randar da yake zuba lemuna a
ciki" ya jawo kiras din da babu
komai a ciki ya fara tsamo
kwalaben lemun daga cikin
sabuwar randar dake cike makil
da ruwa har wuya" ya rinka
shirya kwalaben a cikin kiras din
kala-kala bakake da jajeye da
shudaye" saida ya cika kowanne
gurbi sannan ya kinkimi kires din
yayi waje dashi" inda baban yara
yake a tsaye yana jiranshi"
.
"Ai kaga haka yafi baban yara"
ince dai kwana zatayi ko bada sauri zata tafi ba?
Baban yara ya tarbeshi ya amshi
kires din lemun cikin farin ciki"
sannan yace dashi
"kwana zatayi mana" ta isa tace
zata tafi ne" a ina zata kwanta""
na fada maka tsintuwa ce ta
fado hannuna a banza" sai
yadda nayi da ita"
Dayyabu ya fashe da dariyar jin
dadi" baban yara yace bari in
kai mata lemun sai in dawo
akwai Auwalu shima yana can zaizo" shi kuma a bangarensa
indomi za'a samu da kwai da shayi
Dayyabu yace
"yauwa, to ai kaga haka yafi baban yara" shi dama harka irin
wannan idan zamuyi ita" to mu rika nuna muma fa mun waye" ai abin duk barazana ce! Ko acan
gari suma ba wata tsiya suke
kashewa matan ba" duk karya
ce" gara mu nuna mata muma
wayayyau ne" don kada ta rainamu"
.
Baban yara yayi dariya" ya juya
zai nufi dakinsa ya kaiwa talatu
bakuwa kires din lemun wanda
ya rikeshi hannu bibbiyu" kafin
ya tafi ne dayyabu ya kalli
kwalaben dake cike da kires din
da kuma makudan kudin da suka
lashe" sai ya matsa yace da
baban yara cikin sanyin jiki"
"to baban yara" dan Allah ka rike
amana" ita kadai zata sha" mu hakura zamuyi" idan muka
samu tasha ko kwalabe biyu ne"
sai mu dawo da sauran idan ta
tafi" ba tararwa lemun zamuyi
muyi ta sha ba kaga bashi nake
amsoshi a gari kuma gobe zanje
inyi musu balas in amso wani
Baban yara yace dashi
"Ai na sani dayyabu" kada ka
damu bazan sha maka lemu ba"
ita kadai za'a ajiyewa"
Dayyabu mai shago ya saki ranshi
yauwa to yi sauri ka dawo mu
shirya yadda za'ayi
Baban yara ya kinkimi kires din
lemun ya kai dakinsa ya samu bakuwar a zaune a bakin gado
kamar yadda ya barta dazun" da
shigarsa yayi murmushi
kiyi hakuri" na barki a zaune
ke kadai tun daxu ko?
tace dashi a sanyaye kamar
wacce take mura! ba komai
.
Baban yara ya ajiye mata kires
din a gabanta cikin barazana
yace da ita
To ga abin sanyaya makoshi fa
na kawo maki bana so ki rage
mani koda kwalba daya bari in
dawo kada dai ki kosa
talatu tayi murmushi bata ce
dashi komai ba har baban yara
ya sake bazama ya fita jikinshi na
rawa yazo daidai shagon dayyabu kenan yaci karo da
Auwalu mai shayi ya gama hado
tasa gudumawar yana dauke da
katuwar samira a hannu daya a
daya hannun kuma kofin shayi
ne da katon biredi guda daya akai
.
KOWA DA IRIN GUDUNMWARSA KENAN A HARKAR BARIKI ?
.
(c) SHAFIU DAUDA GIWAKAZAR KARFI--> 07
.

.
Baban yara da dayyabu suka
tarbeshi kowanne ya amshi
hannu daya Auwalu yace cikin
damuwa
ya ake ciki ne tun dazun inata
jiranka ka dawo ka dauki
indomin mu tafi najika shiru
Baban yara yace dashi Na tsaya
nan wajen dayyabu ne
na amshi lemun nakai mata
Auwalu ya kalli dayyabu cikin
rashin amincewa da ganinshi
tare da baban yara suna
maganar bakuwa tare bai so
dayyabu ya shigo cikin al'amarin
ba Da dayyabu ya fahimci haka a
fuskar Auwalu sai yayi saurin
cewa
Na bada kires din lemu akai
mata saboda kada mu nuna
mata karanta ta daukemu
kauyawa
.
Jin hakan yasa Auwalu ya saki
ranshi don kuwa dama baya so
ace shi kadai zaiyi asara su kuma
su kwashi gara basu bayar da
komai ba duk da haka don dai
ya kara ba dayyabu wani aikin
sai yace

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment