Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi da tsangalalliyar Riga ta Da gudun tsiya na fito Kamar guguwa, Yan mazan gidan na gani suna ta motsa jiki suna tsalle da Dan gudu a cikin katon gidan,Girman gida ya Isa ba sai an fita ba,Wani na hango cikin fafaren Kaya Riga da wando Kaya na motsa jiki yana Dan gudu kadan,Ni kuwa na shararo da uban gudu na wuce shi Kamar Iska,Mamaki ya Kama mazan Dan sun San kaf Matan gidan su ba wacce take motsa jiki,Ni kuwa ban kulasu ba idan na kwashe da gudu sai na Kai karshen gidan Zan dawo na Kai na dawo,Daga Nan na dawo cikin Mazan Nan na Fara tsalle tsalle.

tsabar Jin kansu Babu ma Wanda ya ko kalle Ni kowa harkar gabansa yakeyi,su irgawa suke Yi suna one, two, three,four etc Ni kuwa Dan suce ta Gari ce sai bana irgawa sai dai na Fara cewa Subhannallah Daya Subhannah biyu Subhannallah uku da sauran su,Wani cikin Mazan ya galla min Harara yace Wai wannan daga Ina Haka? Ko a Dangin dangarere ban santa ba,sauran suka ce nima Haka Yar kauye ce ko aiki tazo Yi, Fu'ad ne yaja tsaki tare da komawa Part dinsa irin na dame shi din Nan,sai da na gaji sannan na koma cikin part din Nene.

Dakinmu na shiga nace Saude Rana tayi kuzo muje mu gaida masu gidan mu Taya su aiki Kar aga bamu da Tarbiyya,Rabi tace akwai masu Aiki ba abinda za a ce muyi,nace ba Tarbiyya bace kazo gidan mutane ka kwanta ko basa so ya kamata mu danyi wani Abu,Saude tace wlh tsinke bazan dauka duk wulakanta mu da suke Yi,Rabi ma Tace ba aiki ne ya kawo Ni ba,Ni kuwa nace zanyi Ni dai,ai Baki da zuciya ke Saude ta furta nace ae Ni ba abinda ya Dame Ni,Fitowa Muka Yi Nene Muka Fara gaisarwa ta amsa da Fara'a Tace Rabi kin San ko Ina Abbi ma Yana Gari kuje ku gaida su,to Muka ce Muka fito,Rabi Tace wannan gidan ko an gaishe su ba ruwansu Basu da mutunci Ni bazan Bata lokaci na ba,Itama Saude tace Nima Haka wlh,Nikam nace ki raka Ni Rabi sai ki dinga tsayawa a waje Ina gamawa sai mu tafi.

Haka kuwa aka Yi muka tafi,Part din Abbi Muka Fara zuwa Rabi ta buya daga waje Ni Kuma na shiga ciki a hankali,Sa'a naci Yana zaune a Palo shi da wani Abokinsa Babban mutum suna magana akan siyasa,a hankali nayi sallama cike da nutsuwa,Dake maza ne a mutunce Suka amsa min Abbi fari tas me Kama da Fu'ad yace karaso Mana,a gabansu na durkusa tare da gaishe su,Suka Amsa Abbi yace Nene Tace munyi Baki su Rabi ko? Ae na furta,Ina su Rabin? Ya tambaya na ce tana cikin gida Bacci sukeyi zasu Zo su ma,Godiya ya min na mike na fita,Ina Fitowa muka shiga part din wata matar da suke Kira da Umma,Umma Fara ce tas Kamar Balarabiya suna mugun Kama da Fu'ad,Ina shiga da fara'a sai na ganta a Dining tana Hada tea,Fu'ad na gani kwance a wata arniyar kujera 3seater Yana kwance ya mike.

Tsoron sa ya kamani akwai Kwarjini wani uban kamshi yake zubawa sanye cikin 3qutr da t-shirt Maroon yayi kyau Yana uban sheki,Umma ce ta kalle Ni da fara'a Tace shigo Mana Bakuwa,a nutse na Karasa gabanta tare da Durkusawa har kasa nace Ina kwana? Lafiya Alhmdllh,ya gajiya? Ina Su Rabi fa? Karya nayi Mata nace Basu tashi a bacci ba idan sun tashi zasu Zo su ma su gaida ki,To na Gode Dattijuwar ta furta,a tsorace na koma Gaban Uban Yanga da takama Fu'ad Yana latsa waya,Shima Dukawa nayi nace Ina kwana? Shuru ba amsa,na sake cewa ka tashi lafiya? Nan ma Shuru? Nace Allah yasa ka yini cikin koshin lafiya,Allah ya rabaka da duniya lafiya,Allah yasa ka mutu kana musulmi,Allah yasa Idan ka mutu ka kwanta lafiya cikin kabarinka yasa a kabarinka ba Kunama ko miciji Wanda zasu dinga galla maka cizo,Allah ya rabaka da kiyashin lahira da tururuwa tare da Sauron lahira me malaria ta lahira,kasan Sauron lahira shi ba Malaria yake zubawa ba Cancer ce take Kama mutum a kabari sabo da Gubar jikinsa,Fu'ad Yana jinta dariya ta Kama shi Amma ya danne abarsa da kyar,ita kuwa Umma cewa tayi tashi ki kyale wannan ba kulaki zaiyi ba an gode.
Mikewa nayi na fita Rabi tace kin gani na fada Miki wlh gidan Nan Basu damu da gaisuwa ba kina batawa kanki lokaci a banza,Umma kuwa Fu'ad ta lullube da fada Haba Abban Momy yanzu ka kyauta kenan? Ni wlh bana son wannan halin naka Sam,ayiwa mutum shedar kirki ai arziki ne,ko mutuwa kayi zaka samu yabo wajen mutane Amma kowa yazo gidan Nan sai ya tafi da sunanka a Baki bana son Iskanci wlh,Mikewa yayi zaune yace Umma I'm sorry idan Ranki ya baci Ni bana son magana ne Haka Allah yayi Ni,ka dorawa kanka dai gaskiya ka gyara, Alright Zan gyara kiyi hakuri ya furta tare da Mikewa ya Isa Dining.

Part din wacce ake Kira da Mama na Shiga itama part dinta sai Wanda ya gani ya tsaru,Yan Mata su Hudu na Iske a bangaren sun Sha gayu Suna ta faman Danna waya maka maka,Suna ganina suka Fara tuntsura dariya irin Yar kauye,Suna kus kus,ko a jikina Ni ba komai ke bani haushi ba,Mama ce ta fito Tasha Shadda tana wani taku dai dai,tunda ta ganni take wani Bata Rai tana min kallon wulakanci da kaskanci,Har kasa na duka tare da gaisar da ita Amma sai ta daka min tsawa tashi ke bana son gaishe gashen ku na mutanen kauye,ba abinda kuka sani Sai gaisuwa Jahilan banza,idan na sake ganin ki a part dina sai na sa an Zane ki shegun yara,in Banda rashin mafadi mu fa bamu San ku ba Amma kun biyo wata kawa kunzo wajen Dangin Rabi,to kawar taku ma bamu da wata dangantar kirki da ita,daga anga masu kudi sai a Fara kakalen dangi,Yan Matan Suka sheke da dariya Suna Tafawa,Rabi tana daga waje Bakin kofa tana Jin komai to tana Allah ya Kara,Mikewa nayi na fito Rabi ta dinga min dariya Amma ban kulata ba Kuma ko a jiki na.

Part din Babbar su Muka shiga Uwar gida Momy itama wasu Yan Matan da maza biyu a sashenta suna karyawa a Dining,sallama nayi Suka amsa ko kallo na Basu Yi ba na durkusa na gaishe su Amma da kyar Momy ta amsa tana wani Bata Rai sum sum na mike na fito Muka koma Part din Nenen kauye,Abinda muke so shi Muka karya da shi Muka goge bakinmu da tsokar nama,Bayan munyi wanka munci kwalliyar mu ta mutanen kauye na Samu Nene nace Dan Allah Dan Ara min Wayarki Zan Kira Iya ta na fada Mata mun Isa lafiya,Nene Tace wuu rufa min asiri Baki ji sunana ba Nenen kauye ai Ni tsoron waya nakeyi ban taba siye ba,an siya min ma naki karba Haka kawai Ni tsironta nake ji,Dariya mukayi Nene Tace je ki bangaren Umma itace kadai me mutunci a gidan Nan ita zata Kira Miki babarki,To na Furta Muka tafi tare da Rabi da Saude.









AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈







FREE PAGE





DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM







NA KUDI NE

SHIGA GROUP DARI BIYU 200


ACCOUNT NUMBER
0175487861 ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK.


MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39






3












Official







By
AsmaBaffa












PAGE NAKU NE

FLOWER
ZAINAB GARBA BUTALAWA
ZAINAB SABO











Shigar mu part din ke da wuya muka Iske Umma Tasha Wata Arabian Gown ta manyan Mata masu ji da kansu sai sheki takeyi,Fu'ad ne ya shigo cikin wani Danyen Yadi Brown ba karamin kyau yayi ba,agogonsa Apple,Takalminsa Kam irin Half cover ne me Arnen kyau da Alama Unguwa zasu fita,idanuwansa masu mugun kyau ya zuba su cikin Nawa Nan take wani tsoronsa ya sake kamani da sauri na janye Ido na tare da Furta Sannu Oga,duk na rude sai na kasa tambayar abinda ya kawoni kawai nace Sai anjiman ku muka Yi waje a tsorace,Fu'ad ne ya kalli Ummansa yace Umma wannan ba Yan uwan Abbi bane? Rabi ce Yar Uwa kawayenta ne su biyun cewar Umma,Amma Ana kallonsu suna yawo a gida da kazaman Kaya?ni wlh idan na gansu amai ke taso min,ko a sallamesu su koma Kauye seriously zuciyata tashi take yi idan na gansu, to mutan kauye ya zakayi da su idan zasu tafi yaran Nan Mata zasu Basu kwancen Kaya,Umma Ni bana so Ina gilmawa a gidan Nan ina ganin kazamai suna Mana yawo a gida ga kudi a dinka musu sababbin Kaya,Murmushi Umma tayi tace Sannu Alhaji me kudi,Murmushi yayi ta karba kudin ta zuba a hand bag Suka fita.

Cikin Yan Matan ta Kira Khaleesat sabo da taga ta Dan fisu hankali kudin ta Mika Mata masu yawa tace gashi Inji yayanku Driver ya kaiki Shopping Mall ki siyowa yaran Nan da Suka Zo Kaya ko Kala Shida shida ne a Kai su dinki ki karbi wannan nasu da Suka Zo da shi a zuba a Dust bin,Khaleesat tace Okay Umma a dawo lafiya,Fu'ad Wanda tuni ma ya Shiga rantsiyar motarsa driver ya tuka shi suka Fita, Itama Umma motarta ta shiga ta fita da kanta ma take Driving.
Ni kuwa Nene na kalla nace Nene wanne aiki zamu Yi Miki?Nene Tace duk Yan aiki ne keyi ba abinda zakiyi sai dai kuci ku huta,sabo na saba da yin aiki duk jiki na ciwo yakeyi sabo da banyi aiki ba,Part din Umma na koma na shiga cikin Yan aikin gidan muka gyara part din tare suna koya min yanda ake amfani da kayan aikin Yan gayu,Har girki Ina kitchen din na Taya su Suka yi,Cikinsu naji suna cewa Fu'ad part dinsa yayi Dirty Amma yace Bai so mu shigar masa part mu dinga fadawa kannensa su zasu gyara Masa gashi Yan Matan Nan Basu da mutunci,Cikin su wata Dattijuwa Tace cab ai wlh indai ba da kansa ya fada musu ba baza mu fada ba,sai su zageka duk Girman ka,Ina jinsu nace Ni zanje na gyara Masa kafin ya dawo na gyara na gudu ku Kuma sai kuce kanwarsa ce ta gyara,Yan aiki Suka ce ke wannan fa Bai San mutunci ba wlh ya kamaki a part dinsa sai yaci mutuncinki,Nace Ina ruwana Ni wani cin mutunci Yana bani haushi ne shi yaga duhu,Jikina ciwo yakeyi aiki nake neman Yi,to kiyi Sauri 4pm to 5pm yake dawowa daga Office,Cikin Yan aikin Ta'asubi ta rakani part dinsa,Subhannallahi ban taba ganin Haduwa irin part din Fu'ad ba Aljnnar duniya sai dai ya danyi Kura sabo da ba kullum ake gyara Masa ba,komai nasa ba irin na sauran bane na daban ne,Ta'asubi a gurguje ta nuna min komai da yanda ake amfani da shi ta fice,Bedroom dinsa na hau gyara.

Dake bed din me tayana ne cikin kankanin lokaci na canja Masa wajen Zama yanda zaiyi kyau,ba karamin kyau yayi ba Ni kaina ban San na iya gyara ba sai yau,Kayansa ma da aka karbo daga wanki sai Dana shirya komai na gyara su yanda ya Dace,Sai da na gyara komai har kudaden Dana gani masu Uban yawa a kasan pillow na maida su yanda na gansu,kayan kamshi da aka nuna min na saka kala kala tare da kunne AC,Na shiga toilet nan ma naci Ubanta da gyara abin nawa har ya wuce gona da iri kamar me Aljanu Haka na dinga darje ko Ina sai da ya dinga sheki Yana daukan Ido sannan na shirya kayan wankansa na saka abin kamshi na fito,Palon sa na gyara Suma Kujerun na canja musu tsari Kamar wata wacce ta taso a birni,Kitchen da ko Ina lungu da sako yasha gyara Nan ma kalar kamshin daban na kulle ko Ina tare da kunna AC kasa na fito da sauri,Ina fitowa na hango shi Driver ya dawo dashi ya fito da Ledoji a hannunsa Yana tafiya cike da Isa,Da sauri na Fara gudun buya Kar ya ganni na fito daga part dinsa,Ganin zai tarfa Ni sai na fada Bayan Flower s Dake jikin part dinsa,Zuwa yayi ta kusa Dani zai wuce sai ji nayi yace duk abinda na Rasa a part Dina kece,Baki na Bude cike da tsoro na mike nan take da gudu na koma part din Nene.

Labarin part din Fu'ad na shiga bawa su Rabi,Rabi tana zuwa Amma Bata taba sanin ya part din Fu'ad yake ba,nace irin wannan gadon nasa idan zaka na bacci a ciki Alqur'an baza ka taba yin mummunan mafarki ba,Kinga Ni kuwa ta Bature yace Pradise (paradise) ban so na fito ba Yasin kullum sai naje na gyara Masa idan baya Nan ko banza na Sha kallo,Wasu kudi dum a kasan pillow dinsa kamar na sato Fara (1000) Daya amma ba dama ban iya sata ba,Saude tace ke banza ce ai ko kin dakko Mana bazai Gane ba Tunda suna da yawa,Nace ba ruwana Wallahi tallahi ban iya sata baza ku jefa Ni a masifa ba,Baki Rabi ta tabe tace Kinga dai ko Ni da nake Yan uwansu bana shishigi a wajensu ya kamata ki kiyayewa kanki bacin Rai Yan gidan Nan ba mutunci gare su ba,shi Wanda Kika gyarawa part dinsa Bai da mutunci inda mutunci ma yake bai dosa ba Amma kina ta wani shigege Ranki zai baci a banza Rumaila,Baki na tabe nace Ni fa kafin kiga abinda ya Bata min Rai Ana dadewa ba abinda ya Dame Ni tunda Muka Zo Ni wlh Banga Wanda nake Jin Haushi ba ko a gefen takalmi na,wulakanci Kuma mun cancanta suyi Mana shi tunda kalle mu fa shigar da mukeyi su Kuma ki kalle su ga ilmi ga kudi ga wayewa mu kuwa fa?Dan an wulakantamu ai Bai kamata muji haushi ba mun dauki hakkinsu tunda mu Muka kawo kanmu,kema kina ji fa Rabi dangantakar taku ba Mai karfi bace Amma suke barinku Kuna zuwa har suyi muku Alheri gashi muna kawayenki munzo cin arziki,iya kazar da Muka ci ta Isa mu gode musu yaushe rabon da naci kaza? Ga girki me Dadi,muyi wanka muyi bacci a cikin nishadi da waje me kyau Wanda ko a mafarki bamu Yi zaton hakan ba,Muna ta surutun mu a palon Nene Ashe Khaleesat ta shigo bamu sani ba Jin su Rabi suna kushe su ta kunna wayarta tana recording duk maganganun mu bamu Gane ba,sai da Muka shiga wata hirar sannan tayi saving.

Fuska ta Bata tana wani Shan kamshi tace Kai ku taso Tailor zai auna ku,Junanmu muka kalla tace to munafukan kauye a fito karku Bata min time mu a wajenmu time Yana da muhimmanci bana kiwon Shanu bane,Saude da Rabi Suka sake Jin Haushin Khaleesat Ni kuwa ko a jiki na,Palon Wacce suke Kira da Momy ta kaimu,Bata da mutunci ko kadan,mun Sansu,Yan gidan maza da Mata muka Iske sun cika Palon har uban Yan yanga Fu'ad Yana kwance shi kadai an bashi kujera babbar ciki su Kuma sauran sai wani tsoransa sukeyi basa ko Maganar kirki bare Hira idan Yana Nan,Wani matashi Muka gani da Tape a hannunsa Alama ce ta shine tela shine zai gwada mu,tsoro ya Kama mu ganinmu Iskanci ne ace Namiji ne zai gwada mu,Momy ce ta wani tabe Baki tace Abba tela Dalla sauri ka gwada wannan kwailayen ban son su zauna min a part kalar kamshin sa ya canja ya koma wari,Karaf nace Alqur'anin Allah Muna wanka kullum Ni sau uku sau biyu nake wanka Agwagwa ma Haka ta ganni ta kyale,Saude ma tace Yasin kuwa.

Tsaki Momy taja tare da buga Mana tsawa ke dalla rufe min baki
Ni sam ba a bani haushi sai kallon Momy ma Nayi na saki Murmushi na me kyau,su kuwa su Rabi Kamar zasu Yi kuka,Saude Ce ta Fara tsayawa a gaban tela ga kunya sai ta Fara soshe soshe tana kankame jikinta,tsawa Momy ta daka Mata ba shiri ta nutsu aka gwada ta waje waje,ta fice tare da barin part din da gudu sabo da kunya,su kuwa sai dariya suke mana irin Yan kauye din Nan,Rabi ce ta tsaya a gabansa seke seke tare da murtuke fuska itama Ana gamawa tayi waje,ganin anzo kaina sai na shagwabe Fuska na tsaya a tsakiyar Palon Ina yarfe Hannu Kamar wacce take Jin zafin cizon kunama,Idona ya ciko da kwalla maza da Matan suna ta kallo na suna dariya,Kaina na dage sama tare da rumtse idanuwana Ina sanda Kamar barauniya,Bakina na tamke waje daya,tela yasa abin Aunawa a gadon bayana jiki na ya dauki rawa karrr....nace Kar yatsanka ya taba min fata,tela yayi banza dani,Damatsana yazo Aunawa muryata na rawa nace Ni dai Dan Allah indai Haka ne a kyale dinkin Nan,dariya Suka saki min,tsayina ya auna sannan yace juya bayanki zai auna Kuguna naji tsoro da karfi nace wayyo zai min cikin shege na shiga Uku Iyata,Har Fu'ad sai da ya kalle Ni Yana Murmushi.

By mistake Yana gwada Ni Hannunsa ya taba Hannu na sai ko na fashe da Uban kuka Ina cewa Wayyo Iyata anyi min ciki na shiga uku,abinda kike fada min na kiyaye gashi ya faru,kowa ya Bude Baki Yana mamakin irin uban kukan da nake rasga,Tela yace ke Baki da Hankali ne? Allah ya Isa shege mugu Azzalumi kayi min ciki,da Rarrafe na koma Gaban Fu'ad nace Dan Allah me fada ajin gidan Nan ka kaini asibiti a zubar da cikin Nan,idan ya Kai Wata takwas bazai zubu ba anyi kisan Kai,ka kaini da wuri Dan Allah wallahi Iyata korata zata Yi idan na koma,dama Iyata Aure Aure take Yi Babana baya ko kulani ya tsaneni Iyata ce tasa ya tsaneni tana ta tafiya Dani gidan Aurenta kala kala Dan Allah azubar min da shi, Khaleesat Suka sake kecewa da dariya,Tsawa Momy ta buga min bar min part Dina shashasha bakauyiya Haka ake yin cikin Dan Ubanki? Mikewa nayi idona jage jage da hawaye na kalli tela nace ka cuceni wlh sai dai ka aureni Kuma Ina Haihuwa gidanku Zan kawo Dan shegen Kuma Inshaallah sai yayi Kama da Kai sak yanda kowa ya gani yasan naka ne ? Daga zuwa gwajin dinki sai ka min ciki wlh bazan yafe ba har kabarinka na ci da wuta.

Fu'ad ne ya mike a nutse Kamar shima fita zaiyi Haka yabi bayana ya fita Mari naji ruwansa har Biyu masu mugun zafi Nan take sai da Dana ga duhu Yana Huci yace Baki da Tarbiyya babban mutun kike zagi kina Masa Allah ya Isa?maimakon naji Haushinsa sai ma wani birgeni da yakeyi da mugun kyawunsa Ina kallonsa yanda magana ke Masa kyau,Ban iya cewa komai ba sai ma Murmushi da nayi tare da furta Na gode wannan ma na karbe shi hannu bibiyu,tsaki ya ja yayi gaba abinsa Yana takun sa na isasun maza masu ji da kansu,Ni kuwa a fili na Shiga Irga tafiyarsa Nima Wai da turanci Ina furta Lef-rayit lef-Rayit (Left-Right) kumatuna na shafa na furta ba komai Tunda me kyau ne ya mareni ba wani banza can ba.
Su Rabi suna rabe sun ga duk abinda ya faru Dani Dariya Suka dinga min Kamar ba gobe,Shi kuwa mamaki yake Yi a ransa wacce iri ce wannan Bata fushi wannan anyi Yar iskar yarinya Haka yake furtawa a ransa har ya koma tsararen part dinsa.

Part dinsa ya koma yanda ya gaji da Tsafta a ransa yasan Lallai ko wace ta gyara Masa part din Nan ta San makamar tsafta ya kamata yasan wace ta gyara,Tasalluwa ya Nemo sabo da itace shugaban ma'aikatan gidan,Bata fuska yayi Yana muzurai yace Uban wace ta shigar min part har ta samu damar gyara min part Dina?bana ce Kar a bar kowa ya shigar min part ba,Tsoro ya Kama Tasalluwa tace kayi hakuri Alhaji Wlh nacewa tayi ita jikinta ciwo yake yi ta Saba da aiki a gidansu a barta tayi aikin ko ta Dan Wasa jininta, what? Nufinki wace ta shigo min sashe? Sunanta dai Rumaila cikin bakin Yan kauyen Nan da Suka Zo Amma kayi hakuri baza a sake ba,Fu'ad ya dinga mamaki a ransa yanzu wannan gajar ce ta iya gyara Haka? Ko dai karya ne?tunawa Yayi ya ganta a kusa da sashensa tana buya Amma ba komai zai gano gaskiya sannan ma Bai yarda itace ba,Tasalluwa ya nunawa kofa da Hannu yace Out Kar na fusata na koreki daga aiki Baki daya,Tasalluwa Kamar walkiya ta bar sashensa,kudinsa Daya ajiye yaje ya duba harda sake irgawa yagansu cif cif ba a taba ko sisi ba,a fili yace Zan kureki yarinya.

Ni kuwa harkata na Shiga a bangaren Nene na Shiga kitchen,Nene Tace yawwa ko kun iya fura? Na kalli Nene tare da kyalkyalewa da dariya nace harfa tallan fura nayi ai nayi mugun iyawa kawo kayan aiki kiga aiki Nene,Nene Tace Alhmdllh dama wannan uban Yan iyayin ne yace nayi Masa shi Bai Shan ta siyarwa Kuma Ummansa da dukka Yan gidan ba Wanda ya iya, Gero na karba na maida turmin can ta Bayan kitchen anan nayi surfe tare da daka Gero cikin Tsafta sabo da nasan Halin Ogan nasu,tsaf nayi furar lafiya na Gama na Gama Dakawa Zan Fara lailayawa Nene tazo Tace rufa min asiri ai matukar Kika lailaya to fa Abban Momy bazai Sha ba zaice anyi kazanta,Banga laifinsa ba nace yayi dai dai Haka na zubata a wani Glass Bowl aka ajiye a fridge dama Already lafiyayyen Nono Yana ciki.

Wanka mukayi Bayan munyi kowa yayi Sallah Amma Banda Dani domin sai Naga dama Kuma yau banyi Niyya ba,doguwar Riga ce a jikina wata dark Green kalar Yan fulani duk da ta tsufa Amma tayi min kyau,Su Rabi sun rigani cin Abinci suna daki suna kallon cartoon sai dariya suke Yi Ni kuwa bana son Cartoon shi yasa na fito Palon Nene ko Dankwali Babu a kaina kitsone guda biyu a kaina jelar murtukekiya Tana yawo a gadon bayana me tsayin gaske.
Kitchen na shiga tare da ebo Abinci Jullof taliya ta Sha nama zuku zuku,a kasa na zauna na mike kafafu tare da saka plate din a tsakiyar kafafu na ga ruwana na roba a gefe da lemo Fanta,Muna kallo Muna Hira da Nene,Kamshi ne ya daki hancinmu,Nene Tace ga uban Iyayi an shigo,Murmushi yayi kadan Yana uban gadara yayi Sallama Muka amsa nace Ina Yini? Ciki ciki ya Furta lfy ya Shiga harkarsa,Nene ce ta Shiga kitchen ta fito da Fura da Nono a gabansa ta dama Masa sannan ta Mika Masa,Ni kuwa Tv na kafe da Ido na saki Baki ganin an nuna Salman Khan a tallan Indian film,Baki na washe Ina faman tsotse yatsuna da nake cin Abinci da su,Nene ta kalleni tace oh Rumaila wannan kallo Haka rufe bakin Mana Haka Nan,Nace Nene Salman Khan ne fa,To a kansa wani banza Bai ma sanki ba kike wannan kallo kamar idanuwanki zasu Fado ga Baki kin Bude,Nene na kalla nace Yasin Nene da ki zagi Salman Khan gwara ki zagi Malam Haruna yayan Iyata Kawu na,Dariya Nene tayi tace akan wannan din? Nace yo ai Ni gwara ki Mari Malam Haruna ko a jikina,Nene Tace Allah ya shiryeki wlh.

Sharukhan aka sake nunawa,nace wohoho Ina gwanin wani ga nawa kaga Kauna da kanta, Soyayya ce da kanta a Nan wajen,shugaban masoya na duniya kenan Nene,Dariya Nene ta sake Yi tace shi Kuma wannan soyayya ya iya?nace ae Nene ai da ace Zaki

Please Login or Register in order to submit comment