Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so ni? Cikin waye yayi idan ba Kai ba Malam zaka dinga pretending,Sitiyari ya daka yace ke dama Haka kike da sharri? Ni a Ina muka taba haduwa har nayi Miki ciki? Tsoro ya bani yanda Naga har ya canja Yana huci,ba shiri nace Wasa nake maka,Harara ya balla min yace wlh da a Nan zanyi parking na zaneki a gefen titi,ko na maidawa su Fadila ke su daure ki,shuru nayi ban sake magana ba naga masifa yake ji,Office dinsa Muka je na Sha kallon haduwa Kai fada ma Bata Baki ne,Har wani Palo ne da bangaren wasu kujeru na Alfarma,Sanyi da kamshi ke tashi,maaikatan dage Building din suna Aiki karkashinsa sai kwasar gaisuwa sukeyi,a kujera na zauna Yana ta aikinsa ,Yar wayata na dakko Ina ta Game,1pm yunwa ta kamani dama ban karya ba sai ga Abinci Umma ta Aiko Driver ya kawo a Basket,Ni na fara eba naci na koshi sannan nayi Alwala a toilet dinsa me kyawun gaske,Sallah nayi tare da adduoi na,Yace an tsaida Sallah ne? Tun yaushe naji wuyar duniya ban San Sanda na tsaida ta ba,ya fiye Miki ai,yaushe Jauron naki zai zo zance ne Wai? Yana magana Yana buga Stamp a takardu.
Ai kar yazo ace Ina kwashe kwashe,a'a mene ne ba ruwanki da wani Kawai idan yayi Niyya yazo mana,mamaki ya kamani ya akayi yake so yazo? a jiki na naji Kamar da matsala nace bazai zo ba sai idan naje ganin gida Kauye zamu hadu, Fu'ad da wayo yace to ba Kya sonsa Kawai Amma ai saurayi yazo zance shine magana,nace Watarana zance yazo,Bai sake cewa komai ba Nima haka.

Bayan komai ya lafa ban sake Jin komai ba bana ko fitowa daga part din Umma sai wajen Nene Ina zuwa, Har ciki na ya wuce wata biyar Amma ciki Sam Bai ko dago ba abin mamaki,Ga awo Ina zuwa ance yaro lfy yake, Umma da kanta ta sani a makarantar Boko me tsada ganin Ina da kokari Kuma na iya karatu da Rubutu turancin ne Bai zauna sosai ba sai a hankali,na Kara wani wayewa na goge,gashi Umma sai Kaya take Dinka min,ga Ready made etc,Naila ta shirya ta tafi Kano wurin kanwar Nene zata Dan Huta,Mama Kuma Ana saura kwana Uku Abbi yace ta taho Saudiyya suyi Azumi tare,Su Momy Suka ce Allah kaimu Bayan Sallah kafin su dawo sai dai suga Rumaila a prison,kafin ta tafi Momy,Mama da Fadila sun Kira Abbi sun fada masa komai akan cewar Rumaila Yarinyar Yan fashi ce,sannan Fu'ad shine ya Mata ciki, Abbi dai Bai yarda ba Amma yace bincike Yana da dadi ya fasa zaman Saudiyyan gida zaizo yayi settling komai sabo da Haka Umma ma Bata tafi ba.

Kwana daya tsakani sai ga Abbi ya dawo lokacin Kuma su Momy again sunje sun sanarwa wasu Yan Sandan daban tare da jika su da kudi,a ranar Abbi ya Tara kowa na gidan muka hallara kaf,Abbi ya kalli kowa duk Muna kasa shi kadai ne a kujera a zaune,yace ba sai nayi bayani ba kowa yasan dalilin zuwa na,Fadila ance kece kika San komai,to mene komai din akan Rumaila? Fadila har da mikewa tsaye kamar a makaranta tayi bayanin barazanar da Rumaila tayi,sai Bayan ta Gama kaf Momy itama aka Bata dama ta Mike tayi Karin bayani Tace yau Zan daina boye boye kowa yasan gaskiya,Ni dai na Sha Kama Rumaila a part din Fu'ad,sannan Bayan barinta gidan Nan da wasu lokaci ta fara laulayin ciki,Bayan an Mata test aka tabbatar tana da ciki na wata Uku,idan aka tantance lokaci ya nuna tabbas ba a Kauye tayi ciki ba a Nan gidan ne,Abbi yace waye Hujjar ki? Momy Tace a Kira Baba Jummai,Nan take aka Nemo Baba Jummai,Abbi yace Baba Jummai me kika sani tsakanin Fu'ad da Rumaila,Baba Jummai ta kwashe komai daya faru lokacin da Yan fashi suka zo fashi gidan sannan Tace ta fanshe Ni Kuma nasan fansa ta da tayi dama sun Saba masha'arsu da Fu'ad badan Allah ta fanshe Ni ba,na kalli Baba Jummai nace kiji Tsoron Allah Baba Jummai ki tuna Allah Yana kallonki,Da Ubanki ne yake kallo na,Ni zaki yiwa rashin kunya,Abbi yace Jeki Baba Jummai,Bayan ta tafi ya kalli Momy yace sauran shedunki Zaki kawo min,Nan take Momy ta Kira Wayar Rabi,Bugu daya Rabi ta dauka,Momy ta sa waya a handsFree kowa na ji,Abbi ya karbi Wayar yace Rabi Abbi ne, Nan take ta gaida shi,yace tambaya Zan Miki me kika sani game da cikin Rumaila? Dama can Momy sum Gama hada Baki da su Rabi,ai Rabi Tace Ciki Kam tayi shi Kuma Fu'ad ne yayi Mata ciki,tunda Muka zo gidan Nan kullum sai taje part dinsa tana fakewa da gyara Masa part dinsa,daga baya Kuma har cikin dare sai muga ta sace jiki ta fita cikin talatainin dare,Har binta mukeyi a baya sai muga Fu'ad da Kansa ya Bude Mata kofa ta shige,Watarana har rungumeta ya Sha Yi a Gaban mu,munyi munyi ta daina Mun Mata fada tace ba ruwan mu, Kuma ranar bikin Fadila kowa ya gani a kunna maka video din bikin zaka ganta a saman cinyarsa wannan ita ce sheda babba,.

Abbi ransa ya baci yaji kamshin gaskiya Amma duk da Haka yace a kunna Masa video dama mama ta tana da abinta a waya sai ko ta kunnawa Abbi ya kalli zahiri,kan Abbi ya kulle ya rasa ta ya zai warware abin Nan a sirri ba tare da kowa yaji ba ko ba komai Dan ya rufawa dansa asiri duk da Bai yarda ba Amma ba a shedar mutum,Amma Sam Bai yarda Dansa zai yiwa wata ciki ba musamman Fu'ad,Itama Rumaila Sam baya Jin ma ko a jikinsa zata zama Yarinyar Yan fashi Sam bazai yuwu ba Amma dai duniya ko danka ne ba a shedar sa sai anyi bincike.

Umma Kuka takeyi tun tuni,Abbi yace to duk naji Haka ya Isa,Ke Rumaila tsakaninki da Allah ya abin yake Fu'ad shine ya Miki ciki? Ina Hawaye na tausayawa Umma da shi kanshi Fu'ad a dalili na ake ta Masa sharri Ana Bata Masa suna,da suna zaman su lafiya a dalili na Abu ya lalace,Kawai Nace Abbi ba shi bane,to idan ba shi bane ya zakiyi da Maganar Jummai? Nace wallahi Jummai da kanta ita ta nemi Alfarma akan kar su Bari muyi a gabansu Suka amince Muka Shiga bargo,kayan mu Kawai Muka cire suka karba Dan su tabbatar munyi wani Abu har komai da Mukayi kamar Shirin Film Haka Mukayi, yace naji to Maganar su Rabi fa? Nace Allah shine shaida Bai fi sau Uku ba na taba shiga part dinsa Kuma Ni gyara Masa dakinsa nayi shine har Momy taga na fito daga ciki, Amma wlh in Banda a biki Fu'ad Bai taba rike ko da yatsa na ba,to waye ya Miki cikin kenan? a Nan na rasa me zance Kawai Dan na Kare Fu'ad Nace wani saurayi nane Jauro,Ina Gama fada Abbi yace zauna,Kai Fu'ad fa duk abinda Rumaila ta fada gaskiya ne? Fu'ad Yace a'a Abbi, yasan karya shima zai yiwa Abbinsa Bai San ya sadu da wata mace ba a duniya Kawai yace nine nayi yiwa Rumaila ciki kareni tayi,Abbi ransa ya baci yace Kai Ni Wai ya zanyi ne da wannan kullun masifa haka,Kai Fu'ad idan Rumaila ta Haihu dole sai ka aureta na Gama magana daga yanzu ka sani wallahi sai na Daura maka aure da ita tunda ka amsa laifinka,ka bani kunya banza shashasha kaci sa'a daya ta Umma wallahi da sai na daureka Nasa an maka hukunci me tsanani,Rumaila Ina godiya da karar da kika nuna min da Umma kin San Dan mu ne Amma kika boye gaskiya sabo da kunyar mu na jinjina Miki Allah Kuma ya Miki Albarka ya Kara shiryar mu baki daya.

Momy ba haka suka so ba burinsu a Kori Rumaila ko a kamata sai Tace to Maganar Yan fashin fa?Abbi yace wannan zancen banza ne daga bakin mutanen banza....kafin Abbi ya rufe Baki Yan Sanda masu yawa bataliya Guda sun cika palon tare da Nuna Rumaila,Ogansu yace You are Under Arrest,Rumaila ta Mike tsaye,Abbi zaiyi magana sukace baka da damar magana idan Kuna so ku bi mu station,sai ayi magana Amma ku idan kun yafe Mata mu hukuma dole sai munyi bincike a kanta sosai,idan Bata da laifi zamu sake ta Amma baza mu bada Belin ta ba sai Mun Gama bincike a kanta, Fu'ad ya Mike yace ai ba Haka doka tace ba,Abbi ya kalle ni yace kiyi Hakuri Rumaila za a dinga Kai Miki abinci Ana kula da ke Allah zai isar Miki Kuma Inshaallah zanyi wani Abu,Kawai bin Yan Sanda nayi muka tafi.
Cikin Sel suka sakani tare da kulle Ni Bayan sun karbe wayata da dankunne etc.

Ni kadai a ciki na zauna kamar marainiya tunanin rayuwata ya dawo min na daga kaina sama Hawaye ya shiga sintiri a kumatuna, Fu'ad kuwa Abbi yabi Yana cewa Dan Allah kar a kulle ta ka bada kudi masu yawa a saketa idan kayi magana abin zai fi,Abbi Dan Allah a samo hanya,Abbi yace Fu'ad ka Dame Ni Wai ko dama son Yarinyar kakeyi ko kuwa sha'awarta kake? so kake a fito maka da ita kaci gaba da Yi Mata wayo? Shuru Fu'ad yayi yace Abbi gwara ma ka fito da ita wlh Dani za a kulle a Sel din,Abbi ya zaci Wasa Fu'ad yakeyi yace to ai dole sai anbi a hankali ta karkashin kasa kasan case din babba ne,a Bari suyi bincike Mana ai dole gaskiya zata Yi halinta, Fu'ad Yace Abbi su Momy ne fa za suyi ta Basu kudi Ana azabtar da ita,so kake kafin a Gama bincike Yar mutane ta mutu,Kuma tana da ciki? Abbi Yana sani yace to Ina ruwanka Wai? Fushi Fu'ad yayi Ya koma wajen Umminsa yayi Mata rada a kunne ta Dan murmusa ya tafi,wanka ya dauka cikin wata arniyar Shadda sea blue Yana kamshi yasa Driver ya kaishi police station inda aka kaini,Ina ciki kamar marainiya,Wurin Dpo ya Shiga ya zauna,ya buga ya buga yaki bada Belin Rumaila,Takaici ya kama Fu'ad ya zaro kudi masu yawa ya ajiye masa a saman table ya cire agoginsa me tsada ya Mika musu yace Bude min inda take na Shiga ka hada ka kulle Dani,Dpo kuwa yace Fine ya Kira yaronsa Suka tafi da Fu'ad har cikin Sel,Ina ganinsa farin ciki ya lullube Ni tunani na fitar Dani za ayi sai Kawai naga an bude Masa ya shigo shima an maida kofa an Rufe dani da shi a ciki Dan Sandan Yana cewa Soyayya dadi,Amma fa ka birgeni a kulle budurwarka ka shugo a hada da Kai harda biyan kudi akan kulle ka kaima,to wannan a kanta zaka iya kashe kanka ma.

Duk da Haka naji dadi ko banza Ina ganinsa mantawa nakeyi da damuwa ta,Bai min magana ba nace kaima kamaka sukayi? Ae Kawai yace min,Murmushi nayi nace yunwa nake ji Allah yasa Umma ta kawo Mana Abinci sai kuwa ga Umma da kanta tazo aka fito Dani Kawai Fu'ad Yana ciki,muka gaisa Umma Tace ki Kara Hakuri kinji very soon Zaki fito Abbi zaiyi maganin komai nace Inshaallah na gode Umma,Abinci kala kala aka bani a kwando Umma ta tafi Ni Kuma na shiga da shi ciki sabo da Fu'ad ya biya kudi ba a takura Mana,Sel dinma daga Ni sai shi aka barmu ya biya kudi,Abinci na Bude na ebi yanda zai min,nace Kai fa? Yace sai dare kici naki Kawai,Zama nayi Ina ta ci Yana kallo na,tunani na tafi Hawaye ya zubo min nayi saurin gogewa,Mene na kuka Kuma? Iyata nace Ina Hawaye Ni gwara na tafi kauyenmu,Abincin ya karba tare da daukan spoon din ya ebo abincin yace Ahhh Bude bakin,Murna ta kamani har ban San ma na daina kukan ba nace Da gaske kake Yi? Yace ae kina Bata min lokaci,Nace Dan Mazon Allah fa? Yace Uhmmm Zan fasa,da Sauri na Bude Baki na fararen hakorana Suka bayyana ya zuba min jullof rice din da Naman rago,nace dake hannunka ne sai ya karawaa girkin dadi,yace kaji karyarki ko Ni baza ki yaudareni ba yarinya,Yana ta bani a Baki sai da na cinyes tas Nasha ruwan roba me sanyi,Magriba na Yi,Suka Bude mu Muka Yi Alwala tare da sallah,Har Isha Mukayi Basu ce mu koma ciki ba sai Bayan Isha sannan Muka koma Suka kulle mu,Abincin ya zuba shima zai ci nace kawo Nima na baka a Baki? bana so ya furta yaci gaba da cin abincinsa ya koshi,Kasa kwanciya yayi ba shimfida bare pillow,Kwanciya nayi ya gaji ya kwanta shima tare da Dora kansa a cinya ta Ina daga kwance shuru muka Yi a Haka bacci ya kwashe mu.

Jin Fu'ad ya kwana a police station Abbi da sassafe yabi ta sama manyansu ya kashe case din gaba daya,aka Kira su momy aka ja musu kunne Nan ma gwiwarsu tayi sanyi,Bamu San anyi ba muna kulle sai gani Mukayi Yan Sanda an bude mu Ana ta Bamu Hakuri,na fito nace da karku bude mu Mana wallahi ku gani,wani katon ciki cikin Yan Sanda yace Iyyeee kaji Yar fici har da ke Wato kin Isa ko? Nace ae har nayi yawa,Wayoyinmu da komai namu suka Bamu muka fita Uban Izzar Ana ta takama Yana wani kumbura,Taxi Muka Shiga sai gida.

Bayan komai ya lafa Abbi duk tafiya aikin Hajjin ma fasawa yayi a gida kowa zaiyi Azumi,wannan Azumin shine Azumin da zanyi talatin cif a duniya,tunda aka fara Azumi a garden dukkan Yan gidan suke taruwa kowa da kowa Kuma kowa da carpet dinsu daban,Nan sunyi rukuni can ma Haka,wacce ke da girki itace ke Zama a shimfidar Abbi, Fu'ad kuwa shi kadai ne a carpet dinsa Kato,Yanzu Yan gidan ganin Basu da sauran abin da zasu Yi min sai dai tsangwama da hantara,ko da na fito wajen na nufi carpet din Yan matan tun kafin na karasa Safna da Naila Suka min alama da hannu na koma,Umma tana tare da Abbi,matansa su Momy nasan ma bazan rabe su ba Kawai sai na juya na koma wajen Fu'ad shima Ina tsoro kar ya Kore Ni sai kuwa gashi Bai ce komai ba na zauna kasan kafafunsa.

Zamu fara cin abinci kenan Khaleesat Tace je ki karbo min yaji,to nace na Mike Zan tafi Fu'ad ya daka min tsawa zauna idan ta Matsu taje da kanta,ai kuwa na koma na zauna,Na fara cin abinda nake so a cikin kayan Shan ruwansa kowanne abinda ke so yake ci,idan Ina son wani abin ma wajen Su Islam nake ebowa ba ruwansu Dani har Hira mukeyi da su,a nutse kowa ke ci Amma Ni sabo da bana jure yunwa kamar yaki Haka nake ci,in cinye wannan in shanye wancen,duk abinda Fu'ad yaci ya Kara ragewa Haka Zan dauke na Kara dannawa ciki na,Su Hakeem suyi ta min dariya,Islam yace shi yasa kullum buleliya kike Zama kina ta cika gaki har kin Zama Yan Mata sai Aure Wanda ya aureki ya Dace,kalarki bakwa tsufa, Fu'ad ya Harari Islam,Islam yace sorry Babban Yaya na manta na Yaba maka Mata,Ai sai Fu'ad ya dinga bala'i shi ba matarsa bace,Ni dai Ina cin Dankali na nace Kai kudi sunyi a rayuwa dole Iya taso kudi Ashe Iya ta Gama gano kan kudi,Yanzu Fadila ma tana can tana soye soyenta,Iyata Allah ya Baki halin yin soye soye kema,aka dinga dariya har su Khaleesat naji girki harda tuno da Fadila,na Bude farfesun kaji nace to jama'a su Fadila ko Ana can Ana soye soye ko Kuma Ana ta fada da Miji Bata iya girki ba,nasan ma tana can tana ta shirga Masa kwaba a gidansa,wlh ayi Sauri a Kai Mata me Aiki kar ya sako ta da wuri akan girki kadai ya Isa a koro Fadila bare sauran munanan Halayenta,wa ya sani ma ko yanzu Mari ta Sha Guda Uku oho,Momy ta jefe Ni da takalmi karya kike Munafuka,Abbi Basu San me akeyi ba, Fu'ad Yace dazu da Rana a kasan tiles kika kwanta kina ta birgima Akan kina Azumi ko magana bakya Yi,Makarantar safe data Yamma duk Baki je ba Akan Azumi Amma yanzu an Sha ruwa kinfi kowa surutun masifa.

Nace Ina ma da Iyata yanzu Muna mutunci da sai na Kira ta naji wacce wainar take toyawa ita da Ali Shagali me shayi,au bakwa ma mutunci kika ce?Muna magana su Momy suna gulma mama Tace kinga suna Hira shegu,Momy Tace Ina kallonsa Yana ta wani kashe Mata Ido daya da alama yau tare zasu kwana Dan Kira yake mata.
Ni kuwa ban sani ba naci gaba da surutu na nace da gidan talakawa ne da yanzu Mata Ana ta kishi Ana masifa da bala'i har makwafta Ashe kishi ma an fi Yi a gidan talaka,Kai tsiya tana gidan talaka,Amma Nan kowa da kudinsa Ina ruwan wani da wani,Habaici na fara yiwa su Momy Ina Waka nace Alhmdllhi naci na Sha yanzu ko me za ai ayi,gida Ana Zaune lfy akan Yar yarinya an hargitse Ana ta yaki Ana kashe Kudade Ana tashin hankali,Allah ya Zabeni, Waliyiya Rumaila,na zama Waliyiya,Mikewa Fu'ad yayi yace ke kin dameni wlh bana son surutu dazu bakya iya cewa komai an Sha ruwa kin Dame mu,Nima binsa nayi nace ai har Kai a Sel fa ka kwana sabo Dani,ka Mari su Fadila ka murdewa Khaleesat hannu sabo dani,ka bini Sel lailahaillallahu Kamar Fu'ad a Sel sabo da Rumaila,kuma ka bada kudi, wayyo Ni... Na kyalkyale da Dariya nace ka bani abinci a Baki Ashe kana da tausayi Kai mashaallah,Ahhh Baki Ahh bakin Subhannallahi,Allah so na kake Yi Kawai gwara ma ka fada min ka huta,ko sai Watarana idan ba kowa sai ka rada min kace Kawai Ina sonki , Fu'ad Yana tafiya Ina ta Shan gabansa Ina surutu.

Yanzu Ya Fu'ad cinya ta da laushi Sanda ka kwanta? Dariya ce ta kamashi na takura Masa gaba daya,Yana Dariya yace kamar dutse Ni Azumi nakeyi Ramadan ban San wani laushin cinyarki ba,Zan sake magana ya fisgo hannu na zai min mugunta na kwace da kyar na gudu na barshi Nan Yana ta Dariya.
Yace Allah ya kawo wani abu ya sameta bazan sake ceton ta ba tunda yanzu na zama abin tsokanarta har tana ji da kanta Wai Ina sonta,har ya koma bangarensa idan ya tuno sai ya kama dariya shi kadai.

Haka tare muke Shan ruwa,Tarawi ma duk Muna zuwa,tahajjud tazo idan Muka tafi sau da dama ba a gamawa Dani bacci zai sa na gudu gida,sai yaga Ana fitowa Dani baya ganin Ana komawa Dani yasan guduwa nakeyi,kullum Ina karatun Boko Dana Addini na goge sosai na waye haduwa da kawaye duk na canja Nima na rage wani Haukar Kauye.

Ranar da za ayi azumin karshe zobo na hada lafiyayye me kauri yasha pineapple da Banana a ciki yayi dadi matuka,Muna Shan ruwa yau ma Ina shimfidar Fu'ad na zuba Masa a glass cup ya dauka banyi zaton zai Sha ba ya kurba ya dago da fuskarsa Muka hada Ido ya Bata Rai ya balla min Harara yace da tun farko kin San kin iya wannan Dan mugunta sai da kika Bari an Kai last Ramadan an Gama Zaki fara hada wannan,Dariya nayi da farko nayi zaton Bai Masa dadi bane,Abbi na kaiwa a juck ya dinga Santi,Su Islam ma na Basu Amma su Momy da yaransu suna kallo Ana ta Sha Ana dadi nace ku kuyi Hakuri bakwa kaunata Nima bana kaunarku baza kuji dadi na ba Sam,Safna Tace zobon banza wa zai Sha kazantarki,nace Nima bazan baku ba,baza ma Ku Gane kurenku ba sai na zama Antynku Nan gaba zaku sani,Kuna kallo dangina zasu zo suyi ta wadaka da kayan Dan uwanku ku kuwa sai dai ku zauna a palon Baki ko kitchen Dina baza ku samu matsayin shiga ba,sai dai ku hango su Rukayyatu Yaya ta da kannena su Basira da Basiru a kitchen suna ta dafa Indomie da kwai ku kuwa sai dai mu gaisa na koma daki na barku a Palo ku bushe anan ko ruwa baza ku samu daga wajena ba,Kuma Yan uwana su dinga saka super super ku kuwa sai dankwali irin na tsofaffi me Asabari,
Dariya aka dinga Yi Banda su Momy da su Safna,Abbi yace Rumaila kema tsokanar fada ne da ke kullum sai kin kulasu ki kyalesu Haka nace magana ta wuce Amma kinfi so kullum ki tsokane su,Dariya Umma tayi tace ai Wasa takeyi itama ba aikatawa zata Yi ba...Inji uban waye wannan muguwar aikatawa zatayi Mama ta bada Amsa Kai tsaye.

Duk an Mana dinkunan Sallah sai abinda ka gani Kawai kala biyar na samu, Fu'ad ya min kala biyu,Abbi ya Mana da Yan gida kala biyu na samu Umma ta Kara min wata Arabian gown ta zuwa Idi,kala biyar takalma na kala Uku da jaka kala Uku da mayafai kalar kayan Guda biyar,Inner wears sababbi kala kala,harda kana Nan Kaya wata na yo Order daga Dubai masu shegen kyau Umma tasa na zabi kala hudu ta siya min,na makalewa Fu'ad sai da ya bani kudin kayan kwalliya dubu goma da kaina naje na siyo har da wasu rigunan Yan kanti na Karo abina.

Washe gari Idi masu Aiki tuni gida ya dau kamshi yasha gyara na musamman, kowa yaci wanka Muka tafi masallacin Idi Allah yasa Bamu da nisa, Fu'ad da abokansa Suka shigo wajen su bakwai palon Umma a Nan zasu ci abincin Sallah,fitowa nayi na shiga kitchen na fito da nama a plate Ina Kiran Yar Aiki Tasalluwa Ni tuwo zanci ki kawo min Ina fada na zauna a palon Mazan sai kallo na suke yi,na gaishe su suka amsa, Tasalluwa ta kawo min tuwon shinkafa miyar Egusi na karbi tuwon nace ke Tasalluwa me Zan gani Haka Sallah guda wannan dan tuwon kamar tsaiwar wata shi Zaki kawo min,kin San fa bani kadai bace mu biyu ne ya kike Haka ne sai kace wata bakar kadara Baba Jummai,ai a Yan aikin gidan Nan ba kamarki ko Sarkin Izzar gidan Nan Dole sai ya iya cin girkin ki,Haba Tasalluwa Uwar tuwo,tuwo da Miya sai Tasalluwa.,Tasalluwa tana washe baki ta Karo min tuwo Leda Uku na karba na tafi dakina Ina cewa ki sa Abula ta kawo min ruwa da lemo da Red Apple Guda biyar.
Fu'ad a ransa yace Bari Baki su tafi tunda Habaici kike min Zaki sani,su kuwa abokan sai Dariya sukeyi Wai Dan tuwo Kamar tsaiwar wata.










Masu Sharhi Kuna birgeni Ina Jin dadi Kuma Ina godiya.







AsmaBaffa
🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈






FREE PAGE








DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM






NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.


ACCOUNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39










31-35








Official









By
AsmaBaffa









PAGE NAKU NE

Ummy Manga
Momyn Sultan
Rukayyatu
Maryam














Bayan Na shiga Bedroom Dina cikin abokan Sayyeed yace gaskiya ta hadu tunda na taba ganinta a gidan Nan nake sonta Dan Allah Friend kayi min hanyarta ko na samu na fita a gwaurantaka, Tsaki Fu'ad Yaja yana Danna wayarsa,na fito na fito na Manta Umma tace karbo Mata wasu flasks a kitchen,na fito a kitchen Na tsinci Muryar Fu'ad yace Ke Ina Ummata? Nace banji me kace ba na karaso kusa da shi na duka Ina tambaya me kace,Tsaki Yaja yace Umma ta nace,Oh tana can taje karbo dinkunanta da Suka rage,a hankali nace kayi kyau,Bai kula Ni ba.

Masu aiki ne Suka cika musu gabansu da kayan

Please Login or Register in order to submit comment