Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kalleni shekeke a ransa yace karuwar gida,a fili yace yaushe Zan turo? Nace ko yaushe,hararata yayi a boye yace kin Amince? Nace ae ka turo,wata zuciyar tasa tana gargadinsa kar ya kuntata min Yana so na ba karya,Yana ta tunani har ya manta yace zai aureni ya rikeni tsakani da Allah,Allah sarki Islam mantawa yayi da komai yaci gaba da Nuna min soyayya Yana Yi min dinkuna ba karamin kashe min kudi yake Yi ba,Ni Kuma Sam bana sonsa da aure, Fu'ad shine kullum a Raina shine burina,Amma Ina kallo Abbi da Kansa tare da Yan Uwansa suka min wakilci tare da zuwa har kauyenmu wajen Affa,Affa yace kwandala bazai kashe ba suje ya bar musu Ni gaba daya,Abbi Haka Suka dawo aka saka ranar Aure na da Islam Nan da wata biyu,Islam sai murna yake yi,Ni kuwa kullum a bakin ciki nake,da dare nayi kuka na koshi,sai Shirye shirye akeyi tsakanin Umma da su Nene da Abbi,sai Islam dake doki Yana Murna,Momy Kam Tace wallahi tana Nan akan bakanta Babu Wanda ya Isa yasa Danta ya auri karuwar yayansa.

Fu'ad kuwa an daina ganinsa ma a gidan sai jefi jefi gaba daya baya hayyacinsa,Umma ta tambayeshi yace ba komai,Su Rabi suna Jin Labari Rabi ta kwala Ihu ta Dira tsalle tare da cewa karya ne Ina Raye Rumaila ta auri Dan gayu dangina karya ne,Ni ba a aureni ba a auri Rumaila karya ne,Kawai sai ganin Rabi nayi da Saude sunzo gidan da Ledar kayansu da yawa,Ga biki ya taho,Umma ta sa kullum sai naje gidan gyaran jiki,Ni ba son abin nakeyi ba.

Kullum Momy da su Khaleesat a Zagina suke ga su Rabi sun Karu,ga Son Fu'ad ya min yawa,ga matsalar dake tsakanina da Iyaye na,Naje makaranta na dawo karfe biyu,Momy a Compound ta tare Ni tare da cin kwala ta tana girgizani tana masifa da bala'i,Can Garden Kuma Abbi ya kawo masu karatun Qur'ani suna tayi zasu Yi sauka Wai Allah yasa ayi biki lafiya a Gama lafiya,Karatun da nake juyowa shi yasa naji kaina ya Sara Nan take na Kurma Ihu Aljanun da bani da su suka tashi,Ina girgiza na yage Hijab Dina na jefar na suri Momy Kamar tsinke nayi jifa da ita kanta ya daki jikin mota ta zube kasa sumammiya,idona yayi jajir Ina Ihu jikina Yana rawa,matan gida da Yan aiki Suka dauki ihu,Mazan gidan Suka yo kaina,Umma ta fito da Sauri, Fu'ad kuwa cikin Malam masu karatu ya taho da babban malamin,Islam ya fito da gudu,Ina ganin Malamin na Fadi kasa Ina birgima Ina wani irin Nishi,yatsan kafata ya rike babba ya shiga rero karatun Qur'ani,Wani Ihun nakeyi Ina birgima,Daga can malamin yace Kai waye?
Aljanin dake jikina ya fara magana Yana cewa sunana Salahu,Laifi tayi Mana me girma,Dan me zata kwara Mana ruwan zafi muna kwance muna Hutawa a makwararar gidansu,nazo Bara gidansu ta kwala min kwano tare da korata shi yasa Ni Kuma na shigeta na rigada na aureta Kuma wallahi sai Naga karshenta bazan taba fita ba.

Malamin yace yaushe ta zuba muku ruwan zafin? Aljanin yace tana shekara goma sun dafa taliya sun Tace Bata Bari ruwan ya huce ba ta zubo Mana Muna kwance dama Yan Adam Mata da yawa suna Mana Haka Basu San wajen hutawarmu bane sai Kawai su dinga sheko ruwan zafi Basu Bari ya huce,Nazo Ina Bara a gidansu na fito a siffar mutum yaro ta karbi kwanon ta kwala min a kaina shi yasa nace sai Naga karshenta Kuma wallahi bazan barta ba,duk Wanda ya aure ta ya auri masifa har danginsa ta Zama tawa,Nine na Sadu da ita,Islam najin Haka ransa ya baci kishi ya taso Masa yace Malam yanzu ko an daki Rumaila wa aka duka? Malam yace Aljani ka daka,Zumbur na Mike da Muryar Aljani nace au fada zakayi da Ifritu to Bismillah,Islam kishin Aljani ya sadu da matar da zai aura Fu'ad Yana rike shi Yana Karfa ka dake ta Islam,Malam Yana Kai Islam saurara Amma Islam Iya karfinsa ya samu ya zage ya Kai min Uban naushi sai da na tashi sama Zan fado kasa Fu'ad yayi sauri Allah yasa kusa da shi na taho Zan Fadi ya cafeni a jikinsa,Lokacin da Islam ya Kai min duk tunaninsa Aljani ya daka lokacin Kuma Aljani tuni yayi tafiyarsa ya barni aci ubana,Ina faduwa Aljanin ya dawo jikina ya shige abinsa yayi luf yasan Wanda ya aureni ya aurarwa Kansa masifa,Ni kuwa Suma nayi jini ta Hanci ta Baki,Dan rashin Imani su Khaleesat murna sukeyi,Suka kwashi mamansu sukayi asibiti,Islam ko ta kaina baibi ba yayi tafiyarsa wajen Momy dinsa Yana Bata Hakuri Yana cewa na fasa aurenta Momy bazan auri Aljana ba,Momy data Suma Nan take ta wartsake tana Jin dadi.

Abbi Yana dawowa Islam yaje yace ya fasa aurena,Abbi ya kada ya Raya Amma yace Sam baya so na yanzu,Ni kuwa Ina can Tuni Fu'ad yayi Hospital Dani Yana ta shara gudu,agajin gaggawa aka bani,Abbi ya bimu Asibiti daga baya shi da Umma,ba abinda likitoci Basu Yi ba akan na farfado Amma babu alama,Umma tana kuka Tace Kaine duk ka jawo wannan abin Fu'ad da ka amince da tashin hankali Bai samu Rumaila har aljanunta sun tashi ba, Fu'ad Hawaye ya zubo Masa karon farko yace Umma wallahi Ina sonta,Abbi ya kalle shi yace shashan banza,na fasa aurawa kowa Rumaila ko ta warke ta samo wani Mijin da kanta ta kawo, Fu'ad yace Please Abbi Zan haukace,Abbi yace ka Dade baka hauka ce ba ka dage ka nemi soyayayyarta,tana sona Abbi,Inji uban wa? Sai ka Bari na gani da Ido na, Fu'ad yace to zaka gani Abbi, Umma Tace Dan Allah karku damemu da wata Soyayya Rumaila tana wani Hali kana ji Doctor yace sai tayi kwana biyu ko Uku Bata farfado ba Kuma zata iya wucewa Kiyama, Fu'ad yace Wlh idan ta mutu sai na daure Islam har abada ya dakar min Mata
Abbi Yana takaici yace rufe min Baki.







Karshen Free page.
aasassaaaaaa

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment