Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

?"
Har zai ce eh ,sai kawai yatsintsi kansa da cewa ah ah itadai Dr naja'at haruna ta ke"

Ajiyar zuciya mom tayi ,wadda basan cewa hafis yajiba,tace ok inaga kamace.


Shikuwa Sarai Hafiz yasan ada da naja'at Musa take bearing ,byn abbansa yarasu ta maida da sunan mahaifinta ,wato naja'at haruna.
Sannan ya boyewa mom ne sbd besan miyasa take son sanin ammice koba amminceba gashi tasaki ajiyar zuciya to meke faruwa ne?Amma in hankali ya kwanta zai tambayi a mmi d'in.

Sallama yyimata akn xeje yyi Sallah.

Bayan awa3,hakan yyi Dede karfe 3:25pm, doctors d'in sufa fito sunata sharce gumi.

Da hanzari su Abba suka taresu,Dr naja'at ta cire eye glass d'in ta tace kusameni a office"Bata jira amsarsuba ta nufi hanyar office d'in ta da wani likita ,da alama ita dashi ne zasuyiwa su Abba bayanin ciwon dake damun Abdallah.

Babu Bata lokaci su Abba suka rufa masu baya zuwa office d'in.

Share

BY
MMM FAREESA
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒบ AUREN WATA SHIDDA๐ŸŒบ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written by mmn fareesa


Wannan shafin nakine halak malak Queen minart๐Ÿฅฐ๐Ÿ˜˜ kiyi yadda kikeso dashi...


Not edited

P 25

""Bayan duk sun zauna koya ya nutsu"kafin Dr naja'at ta Fara mgn kamar haka...da farko dai Alh inaso kuyi hakuri ku maida lamarinku ga ALLAH ta hanyar karb'ar k'addararku daya k'addareku da ita! sannan kucigaba da Masa addua sbd shi ciwo lokaci guda yake shiga jikin mutum ,Amma sauk'i ahankali yake zuwa ind....ya isa haka pls kusanar damu Mike damun yaron mune?"cewar mom dake kallon Dr naja'at dake musu bayani"Dr naja'at Bata kalletaba da dubi Abba dake kallon ta tace maganar gsky Alh bazan boye maka ,munyi iya bakin kok'arin mu zurfafa bincike naganin munsan meye ke damun d'anka "Amma amsar guda ce"cikin k'osawa mom tace meye amsar?"
Dr naja'at ta cigaba da cewa binkicenmu yanuna Mana cewa Yana cikin koshin lfy!abad'ini kenan"azahiri kuwa idanunsa kawai ke aiki ajikinsa, sannan abinda muka gane yanxun na damun shine jininsa Yana kok'arin yahau, Kuma zuciyarsa na bugawa.
Hakan Yana nuna alamar cewa yasaka damuwa aransa ne,Kuma munyi kok'arin shawo kan wannan matsalar...salati kawai Abba ke maimaita sbd tashin hankalinsa yakaru akan nada, yyinda mom keta kuka da surutai..
Dr kamar yadora da cewa duk asibitin da zaku kaisa indai tsakani da ALLAH zasu gaya muku to amsar d'aya ce da nan "sannan ayanzun abincinsa yakasance me ruwane sbd be iya motsa bakinsa balle har yatauna abinci"zamu rik'e sa sai zuwa gobe musallamesa"Amma dai yanada iyali ko?"eh yanada Mata ,cewar Abba kafin mom ta yi mgn yarugata.
Dr Kamal yace ok to yakamata tazo kusa dashi sbd Yana bukatar kulawarta amatsayinta na iyalinsa,tunda yanxun komai sai anmasa.,,,,,

Insha ALLAH yanxun inmunyi la'asar zamuje adakkota tana gd"cewar Abba Yana duk'ar da Kai sbd ganin yadda mom ke jifansa da kallon tuhuma"


Gyaran murya Dr naja'at ta yi hade da cewa inada shawara Alh!

Abba yadubeta ya ce miye shawarar likita?

Gsky ciwon danku bana asibiti bane,ayadda na fahimta,ciwonsa na....ah ah dakata bamasan Jaye Jaye tunda kun kasa gane abinda ke damunsa inkun sallamesa zamu can za hospital ko mufitar dashi waje..cewar mom tana tashi tsaye.

Murmushi Dr naja'at ta yi domin yanxun ta lura mom ta daina Mata kallon sani,Kuma itama bazata nuna ta Santana,sai kawai tace to shikenan hjy ALLAH yasa adace" cikin Shan k'amshi mom ta ce Amin"sbd azatonta k'ila Dr naja'at ta ji shakkuntane...

Atare mom da Abba suka fice dg office d'in Dr naja'at.

Hafiz dke cikin toilet d'in office d'in yyi ajiyar zuciya sbd yaji komai ,ya fito zuciyar sa cike da tausayin abokin nasa.

Saurin dubarsa ammi tayi had'e da hararan sa tace har kabani tsoro,miye anfanin hakan kamana labe?

Murmushi Hafiz yyi had'e da cewa yi hkri ammi inason jin abinda ke damun AK ne"

Ok to kaje gd hakan nan tunda kaji,tun safe kake nan ,itama fiddausi yakama ta kaduba kaga halin datake ciki"

Zan tafi ammi Amma Dan ALLAH Zan tambayeki?"

Ina jinka "miye tsakanunku d hjy hafsat (mom) mahaifiyar Abdallah?"

Murmushi ammi tayi had'e da cewa meyasa kamun wannan tambayar?

Nan yashiga sanar Mata yadda mom ta tambayesa akan ta.....ajiyar zuciya ammi tayi had'e da cewa Zan sanar dakai wacece HASSU TSIYA TSABA! amma ba yanxunba ,abinda nikeso dakai kada ka nuna Mata cewa nice naja'at Musa,kanajiko?"eh ammi
Ok zaka iya tafiya...

*******

Abba d mom na fita takama balbalesa da masifa akan wane dalili zai ce Abdallah nada iyaline?"
Girgiza Kai yyi Kai tsaye yace basa abinci ,wanka , alwalla,kulada abinda yashafi tsiraicinsa ke Zaki kula Masa da sune?"
Tabe baki mom tayi had'e da cewa eh hakane muje to sai akawota nan d'in"ta fad'a. Cike da mamakin Wai yau Abba ke gaya Mata mgn a tsaye lallai da sake....
Saida suka sake zuwa d'akin da akaje Abdallah ,suka samu Yana bacci ga drip an d'aura masa
Kafin su fice dg room d'in sukabar ya'u direba agunsa....
Byn Abba yyi Sallah suka nufi gd shida mom...

Byn mom tayi wanka tasaka zulfa ayi Mata Kiran riyan.
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒบ AUREN WATA SHIDDA๐ŸŒบ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written
by mmn fareesa


Not edited

p 26

Riyan na zaune kan abin Sallah yana azkar,byn ta idar da sallar la'asar wacce ta dad'e tanama Abdallah addua ,kafin ta soma azkar yyinda k'asan zuciyarta ke tunanin Yaya jikin Abdallah da sauk'i ko bbu?"
Knocking d'in da taji ne yasaka cewa ashigo...byn zulfa ta shigo tasanar da ita Aiken mom kafin ta fice...
Tab'e baki Riyan tayi had'e da tashi ta ajiye cazbaza d'in,kafin ta fice ta nufi part d'in mom.",,,,,

Fuska bbu yabo bbu fallasa tayi sallama had'e da Zama kan carpet tace ganiiii!
Cike da mamaki mom ke dubarta sbd ta lura dg yau da safe zuwa yanzun wani hayak'in rashin kunya ko me Riyan keji,Amma sai Bata nuna mamakin ta,tadaiyi kwafa azuciyarta sbd gab riyan din take da barin gdn...
Ayatsine tace abinda Zan gaya Miki shine kishirya yanzun ki dauki abinda zaku iya bukata keda my son" acikin driver's din my son wani zai kaiki hospital gurnsa ki kula dashi kafin muzo anjima nida abbansa!
To insha ALLAH"riyan ta fad'a had'e da tashi ta fice"mom ta rakata da harara...
Bbu bata lokaci riyan ta shirya cikin doguwar riga ta amfa red tasaka hijab red,kafin ta fito taje bed room d'in Abdallah ta fito Masa da kayansa irinsu vest boxers jallabiya sbd tasan be wuce su mom take nufi ta fito Masa dashiba.... sannan ta Kira Hafiz tasanar Masa su had'u a asibiti "yace to...

Basu iso abitinba sai kusan 5:12pm "har room d'in da Abdallah ya ke driver d'in yanunama riyan , sannan ya tafi"cikin faduwar gaba ta murd'a kofar tashiga,bakin ta d'auke da sallama.... Hafiz ya amsa Yana kallon ta "byn sun gaisa ta ce yamai jikin?Yadubi Abdallah dake jingine da pillow bisa gado yace da sauk'i...
Matsowa tayi jikin gadon tana kallonsa tace yajikin?" ALLAH ya baka lfy" k'uri da ido yyi Mata Yana hongo tsantsar tausayinsa acikin k'wayar idonta,Wanda be tsammaci hakanba,azatonsa k'ila ma tace dole sai yasaketa Amma gashi ita rashin lafiyarsa tadameta....Yaya Hafiz ya ci abinci kuwa da wanka da Sallah???
Tambayar da riyan tayi ta sakashi dawowa tunaninsa,yanadaita aikin kallonsu..

"Ahankali Hafiz yace ah ah be jima da falkawaba ai"dama fresh milk ce da tea akace mu basa to komai dai akwai shi"to bara na had'a Masa tea din sai yyi Sallah da wanka.

Ok toshiken, Hafiz ya fad'a had'e da matsawa kusada Abdallah sbd byn farfadowarsa Yana Masa nasiha akan ya rungumi k'addararsa,dadai nasiha anan yafahimci yanajin mgn ,bede iyayinta"
Ahankali yace my man inason in sanar da Kai wata shawara Dan ALLAH inbacin nida riyan kada ka nunawa kowa kanajin mgn,inafatan kagane?"
Da ido Abdallah yace sbd me?
Hafiz yace Zan fad'a maka Amma da sauran lokaci... adedenan riyan ta iso da cup d'in tea mai kauri a hannunta ta dubi Hafiz tace gashito"
Gira ad'age yace nayime dashi?"
Kabashi yasha Mana"
Ke Kuma kiyi me Inna basa?"haba riyan! aike yakamata kibasa kinji"
Batace komaiba,taja kujerar roba Fara dake cikin d'akin ta matsa sosai kusada Abdallah dukda tanajin faduwar gaba ,haka ta daure, Hafiz ya d'ago kansa"had'e da bud'e Masa Baki har ya shanye duka Yana kallonsu da ido,kafin ta sake fito da fresh milk itama ta dura nasa , sannan ta basa ruwa yasha ...

Byn kamar minti12 , Hafiz ya fice dg room d'in"

Bbu jumawa yadawo shida wani doctor da keke me kujera suka Kama Abdallah suka aza akai"Hafiz ya shige dashi toilet sbd yyi arwala ya Rama sallolin dake akansa tunda Yana a haiyacinsa.

Bayan shigarsu riyan ta gyare gadon had'e da share room d'in sbd tasan Abdallah bayason k'azanta.


Bata jima da gamawaba suka fito, Hafiz ya saitashi ga alk'ibla yaga batarda Sallah dg zaune sbd lalurarsa...

Bayn ya idar ne Hafiz ya turasa acikin toilet , yafito Yadubi riyan yace kije kiyi Masa wanka"Amma kibi ahankali kada yashaki sabili inkin gama Masa ki fito ,sai nazo na fito da shi"
Zaro ido riyan tayi had'e da cewa wankafa?"girgiza Kai Hafiz yyi had'e da cewa eh riyan ai mijinkine ko?"Kuma akwai boxer ajikinsa....batasan sadda tasaki ajiyar zuciya ba.
Duk anacikin wani hali Saida hafis ya murmusa.


Kafin ta shige toilet d'in atsorace.

Zaune yake kan keken idonsa arufe,sbd jin k'arar bud'e kofar yasan itace saiyai maza ya rufe idonsa,dukda yasan akwai boxer ajikinsa sai yaji nauyin tagansa ahaka musammun sai yadda tayi dashi....wani imani yaji yasake shigarsa lallai rayuwa abun tsoroce "Wai ita wace irin mutumce yanxun duk rashin kwautatawar da yyimata ,bazaisa ta cusguna masaba kota goranta Masa sbd yanzun Yana k'asa..
Wata zuciyar tace sbd ita daban take"Kuma zuciyarta tsarkakakkace tasan ko ita Bata wuce ALLAH ya jarabetaba.....tunaninsa ya tsaya cak sbd jin hannunta da soso ajinsa tana murzawa....


Kofar toilet d'in aka Fara budewa ,kafin ta turosa akan keken,da Abba suka hade ido yyi tagumi cike da tausayi yake dubarsu...
Hafis ne yatashi yataimaka Mata suka saukeshi dg kan keken suka aza kan bed.

Kafin Abba yadubeta fuska asake yace sannu !kinji ALLAH yyimiki albarka yabaki ladar"
Fuska aduke tace Amin.

Abba ya matsa kusada da Abdallah ya rungumesa Yana Masa adduar samun lfy had'e da nasiha akan ya yadda da k'addara "
Kallon sa Abdallah keyi yanason yace Masa Ina mom?"ai azatonsa bazata iya yin nesa dashi Kona na 1minit ba Yana cikin wannan halin"ALLAH sarki riyan ! yarinyar dayake wulakantawa gashi ita tafimasa mahaifiyarsa,sai yanzun ya tunada da nasihar Hafiz agaresa daya ke Masa fadan yadaina wulakanta riyan sbd D'an Adam darajace dashi bakasan Wanda zai maka Rana ba!gashi yagani ya wulakanta ita Kuma ta taimakaesa.... lallai bazai tab'a mantawa da Hafiz da riyan arayuwarsaba , wadanda yatabbatar bbu wad'anda mahaifiyar sa ta tsana sama dasu arayuwarta... wasu hawayene masu zafi na tausayin kansa suka Fara ziraromasa agefen ido....

Cikin dubara Hafiz ya goge Masa sbd kada Abba yagani.

Da taimakon Abba da Hafiz aka shirya Abdallah cikin t shirt da wanso 3 quarter...

Gab da magrib ,Abba da Hafiz suka fice zuwa masjid,sukabar Riyan agunsa ita kadai.

Itama alwarlal tayi bayn ta saita Abdallah dake kan keke a alk'ibla.

Bayan sun idar ,riyan na kan abin Sallah tana lazimi kafin lokacin isha'i yyi.

Afusace aka banko kofar ,bbu ko sallama.

Da sauri riyan ta d'ago kanta Dan ganin su wayene.

Zeenat ce da hjy ikilima,suna jifar riyan da mugun kallo.

Wani faduwar gaba riyan ta ji Amma saita dake.

Abdallah na.....


Share

BY
MMN FAREESA.
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒบAUREN WATA SHIDDA๐ŸŒบ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written by
Mmn fareesa

Wannan shafin nakune y'an team d'in HASSU TSIYA TSABA....lolx..๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ

Not editedโŒ

P 27

Abdallah na kallonsu "Yana jiran jin meyakawo ne"yyinda riyan ta maida Kai tacigaba da abinta take batace uffanba....hmmm dole ki sunkuyar dakai Mana marar kunya"ko kinmanta ranar da kikamun gwalo sbd wannan nakashashshan mjin naki"?ok na mantafa Ashe auren contract nefa...cewar zeenat tana nuna Abdallah dake sauronsu yyi jigum tamkar gunki.
Hjy ikilima ta karbe zancen da cewa ai gara dabaki auresaba wlh "dayanzun anbarki da jinya ,yazamana Baki amfana da komaiba a auren nasa dakikayi.... ALLAH ya tsareni mom da Zama da nakashashshe,ai wlh ko ya aureni yazama haka dole yarabu Dani,dama inasonsane sbd kyau, aji.dakuma nassaba,to Kuma yanzun bbushi...hmmm yo insuke ai inhar basu yi sannuba abinda suka mallaka sai yakare gun neman magani...cewar hjy ikilima tana murmushin mugunta, had'e da cewa dubesa shida gawa duk days suke banbancinsu guda 2 shine numfashi d gani mutane kawai,Amma bayaji baya mgn "dayanaji saina gaya Masa abinda zaisa zuciyar sa bugawa,domin ni hjy ikilima nafi k'arfin aja Dani ko a wulakanta mun y'a daya Dana mallaka aduniya gashi kaga aya dg yau inkaji wani zai wulakanta wata ka mishi mgn yabari....
Riyan ta d'ago cikin tsantsar bacin rai had'e da tausayin Abdallah sbd ana ci Masa fuska Dan ALLAH yajarabesa,sbd azatonta bejin mgn da gske"

Salamu alaikum!bara namuku sallama sbd naga da alama dg y'ar har uwar bbu Wanda yasan darajan yin sallama ko amsata...keeeeeee k'aramar mar kunya....cewar zeenat tana nufar riyan tamkar zata daketa..
Murmushn takaici riyan tayi dukda tad'an tsorata tace hmmm ALLAH ya Baki saa kikawo hannunki jikina wlh ,Dana nunamiki ke danbace!Kuma JAHILA"nikike cewa jahila?"

Eh"ance jahila mezaki iyane?"

Inbacin jahilci Taya zakixo gun bawan ALLAN da ubangiji yajarabta da lalura kima Masa ba'a kosan goranta Masa...iyeeeee! tafad'a cikin tsawar dabatan ta iyataba....saurin janye zeenat hjy ikilima ta yi sbd taganin kamar riyan zata iya bige zeenat d'in sbd taji ance abin ba ajiki bane "zuciyace .
Mom rabu Dani naci uwarta wlh....hhhhhhh...kinadai zagin takusa dake batawaba"sannan kisani dama Abdallah yasha fad'a mun bayasonki ko kad'an hasalima cusa masake akayi...kutumar ubancan,cewar zeenat azafafe...ita kuwa riyan abad'ini Abdallah bece Mata hakaba tafad'a ne sbd zeenat taji haushi ,gashi Kuma ta ji haushin..

Yyinda Abdallah tun farkon Fara yab'a Masa mgn yakejin zuciyarsa na zafi had'e da k'una...Amma jin kalaman riyan sai yaji tamkar anyaye Masa abinda yakeji sbd shima ya fahimci riyan batasan yanajin mgn ba...

Hjy ikilima ta ja hannun zeenat had'e da cewa muje kibarta kawai zata ga abinda zai faru d ita... sannan Wanda takeyi danshi batada daraja agunsa sbd ai itama dama aka Bata ta auresa bashi yace yanasoba....hmmm hjy kenan ai Ni bandamu yasoni ko kar yasoniba !mijina ne ko auren me mukayi Zan Kuma kula dashi tsakani da ALLAH sabanin y'ar ki sake sonsa sbd wasu abubuwa, wad'anda mutum ke kuskure yace zai so Dan uwansa sbd su,ke kuwa Abu gudane yasaka Abdallah rashin kaunarki,shine rashin tarbiyya,dukda inazaton gadon hakan kikayi....Dan ALLAH momi kisakeni na lallasa yarinyar nan...

Hmmm kisaketa Mana!

Sannan inaso kusani keda ita sbd da alama bakuje islamiya duk abinda zai Sami bawa mai kyau ko marar kyau to yanada ga k'addararsa ne,sbd haka baku isa kumin komaiba suk abinda yasameni nayi imanin dg ubangijina ne.

Hmmmm haka kikace?"

Eh "basaina maimaita Miki ba,cewar riyan adake.

Kwafa hjy ikilima tayi had'e da cewa zakisan wacece Ni wlh,dg yau zuwa gobe Zaki fita dg rayuwar Abdallah Dan zansaka mahaifiyar sa tace yasakeki kota tsine Masa...

Kisaka niya Dan ALLAH tunda Bata lfy Yar sa kukeba ,to kisaka hartace zata tsine Masa ,kisani barazanar ki batayi amfaniba, sannan dg karshe kisani duk mai gsky yanatare da ALLAH,kija akuyar yarki kufice ko nata taramuku jamaa....kafin suyi mgn su Abba sun murd'a kofar sun shigo , kasancewar dawowarsu kenan dg masjid angama isha'i.

Koda Abba yaga hjy ikilima Saida yaji wani iri"sbd dama beson abotarsu da mom,Dan bbu yadda zaiyine kawai.

Fuska bbu yabo bbu fallasa ya amsa gaisuwar ta da jajen datake Masa akan Abdallah.

Wacce ta ke mgn tana karya wuya ita tausayi...

Riyan kuwa batayi mamakin ganin hakan ba,har suka fice itada zeenat.

Mamakine fal da al'ajabi acikin zuciyar Abdallah ,game da hjy ikilima da mom...

Sannan Kuma wani gefen na zuciyar sa cike yake dajin dad'in maganganun da riyan ta fad'a musu,sbd ko shi iya abinda zai fad'a d'in kenan, inda zai iya mgn.

Ya k'udurta aransa ko mom ta ce yarabu da riyan wlh bazai Mata biyayya ba" sai yanxun yagane dalilin dayasa Hafiz ya ce kada yanuna yanajin mgn.

Mgnar da Abba yyice tadawo dashi tunaninsa,Gurin tambayar riyan sunyi isha'i?tace ah ah"nan da toimakonsa Abdallah yyi isha'i yasha abinsha..


Gurin karfe 10:30 Hafiz ya shigo,byn sun gaisa da Abba yace Abba yaka Mata ka koma gd" nida riyan zamu kwana gunsa,anbani wani daki dake kusa Da nan ,ita riyan sai su kwana anan ita dashi..

Abba yace ah ah Hafiz kaga kanada iyali,kaje kawai tunda ga guards nasa awaje....kayi hakuri Abba kada muyi jayayya ,ai tana Gurin ammi(matarsa) can zata kwana,Tama koma can ,sai Naga yadda jikinsa yakasance kafin ta dawo ...

Abba cike da jin dad'i,yace to shikenan Hafiz ALLAH yyi maka albarka. Yabarku tare,naji dadin yadda ka dauki Abdallah Dan uwa agareka.
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒบAUREN WATA SHIDDA๐ŸŒบ
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

Story & written by
mmn fareesa


Not editedโŒ

P 28

..... Hafiz yyi murmushi had'e da cewa Amin,nan abban ya matsa kusada Abdallah ya rungumesa,yyi a ddua yasha famasa ajiki,kafin yyimusu sallama ya fice dg room d'in sbd body guards nasa Dana Abdallah na waje...
Byn fitar Abba riyan daketa gyangyadi ta dubi Hafiz tace Amma Wai Dan ALLAH me ke damunsane?Dan ALLAH! ajiyar zuciya Hafiz yyi had'e da zaiyane Mata abinda doctors sukace,yadora da cewa Amma yanajin abinda ake cewa....be k'arasa ba riyan tayi saurin kallon Abdallah sbd ta tambatar da abinda Hafiz yace,kaddai ace duk abinda yafaru d'azun akunnansa,gashi ta Masa k'arya... tafad'a azuciyarta.... yyinda Abdallah keta aikin kallonta sbd yafahimci abinda take tunani,sai yyi kok'arin kanne Mata ido d'aya...saurin janye idonta tayi ta dubi Hafiz dake cewa bara na je d'akin dake kusa da nan na kwanta har 11:tayi, yafad'a Yana hamma,kafin Yadubi riyan yace inyanason shiga toilet ,ki bud'e kofar body guards nasa na nan kice su kirani...bejira asartaba yanufi kofa...

Amma Kuma Dan ALLAH nifa....saikuma tayi shiru sbd ganin Abdallah yatsareta da ido.
Hafiz ya juyo yakalli Abdallah wanke Masa alamar yacewa riyan ta kwanta.
Murmushi yyi had'e da cewa to ke kinji both yace ki matsa kusada shi ku kwanta... yafad'a cike da tsokana Yana satar kallon Abdallah dake hararan sa...

Itama riyan murmushn tayi,sbd ta lura Hafiz tsokana ajininsa take.
Tabarma da bargo taja ta shimfid'a ta kwanta,shikuma Hafiz ya gyarawa Abdallah kwanciya kan bed d'in ya fice...

Can cikin dare riyan takasa bacci ,sbd tunanin ciwon Abdallah d a Hafiz ya fad'a Mata Wai doctors since basuga abinda ke damunsa ba"inhasashenta gsky ne to ciwonsa bana asibiti bane na gd ne.

Tashi tayi cikin sand'a ta matsa kusada Abdallah ,Wanda ke kallonta tun farkon tashinta Amma Bata saniba"

Gabansa ta tsaya tayi addioin tsari ta tofa Masa ga jikinsa ,kafin ta koma ta kwanta.

Lumshe ido Abdallah yyi cikin wani bakon yanayi...dg haka bacci yyi gaba da shi.

******
Washe gari tunda wuri riyan da Hafiz suka shirya Abdallah bacin yaci ya koshi,kafin mom da Abba su shigo tare da doctors.
Tsintar kansa Abdallah yyi da k'inson ganin mom dajin mugun haushinta,sbd haka ko kallonta be yiba ,yanaji tana cewa jiya da masassara ta kwana shiyasa batazoba, yyinda itama riyan ko kallo Bata ishetaba balle ta gaisheta...

Byn doctors sun gama dubasa ,aka sallamesa.

Mom tace dole acanza hospital.

Kai tsaye wata private hospital suka sake zuwa....hmmm saidai abin mamaki da ita d awaccen duk Abu guda suka fad'a gameda Abdallah..

Hakan yasa Abba yace sukoma gd gobe zai saka asama Abdallah biza konan da sati 2 su tafi Cairo ko Egypt adubasa sosai...

Da wanna suka koma gd.

Byn isarsu mom tace awuce da Abdallah part nasa,tasaka angyara d'azun.

Abdallah yyi mamaki kwarai ,azatonsa acan part d'in mom za'a yi jinyarsa.
..

######
Bayan 6 "yau yakama Abdallah kwanan sa 8 kenan acikin wannan lalura tasa,Wanda yakasance dg riyan sai Hafiz da Abba kawai ke kula dashi,Dan mom arana sau2 ta ke lekowa ta gansa ko sau d'aya.hakan yasa zuciyar Abdallah rauni da karaya had'e da wani zato.gefe guda be wuce saura kwana 9-10 afita dashi waje Dan duba lfy yarsa.... sannan kullum riyan namasa adduoi azamzam data saka Hafiz ya kawo Mata tana bashi Yana sha.. sannan anrufe campany d'in Abdallah sai byn yaji sauk'i wannan umarni ne na mom,hakan yatada hankalin mutanen dake aiki campany d'in...


Zaune yake kan keken sa, orange din t shirt ce ajikinsa da wando 3 quarter" riyan na tsaye a gefensa tana basa frash milk "sai aikin kallonta yake"a Dede ban mom ta shigo tana wani yatsina fuska had'e da toshe hanci....cikin al'ajabi Abdallah ke kallonta be ankaraba ya k'ware awahalce yabiyo Masa ta hanci da Baki,gashi baya yin tarin sai rawa bakinsa keyi cike da azaba...hawaye riyan ta ji sbd tausayinsa ...da sauri ta saka tissue bbu nuna ko k'yama tafara goge Masa na hancin kafin ta goge na bakin...

Mom ta tab'e baki had'e da cewa ke ki kula adunga gyara Gurin sosai sai wani d'oyi nakeji,bara naje in anjima na dawo ai sai zuciyata ta tashi nayi amai wannan kayan k'azanta haka...ta ida fad'a tana ficewa.

Riyan ko ci kanki batace mataba,ta dubi Abdallah da idanunsa sukayi jajir"yyinda jijiyoyin kansa duk sun tashi Rad'o rad'o"almar ransa yab'aci matuk'a...

Cikin sanyin murya riyan tace kayi hakuri Dan ALLAH,duk tsanani Yana tare da sauk'i...

Rufe ido Abdallah yyi yanajin wani Abu game da riyan,dake kula dashi tsakani da ALLAH Bata hantararsa ko nuna k'yamarsa gashi mahaifiyar sa na gudunsa , wannan wace irin rayuwace haka... lallai sai yanxun yafahimci cewa ciwonsa bana asibiti bane,gsky Yana sakaci gun adduoin neman tsari dukda wani time d'in yanayi,Amma yadauki hakan amatsayin k'addararsa...sai yatuna da hadisin monxon ALLAH (S AW) daya ke cewa TAHARIF I'LALLAHI!YA'A RIFIKA FI SHIDDATI...ma'ana(kasan ALLAH sadda kake cikin yalwa, zai Sanka sadda kake cikin tsanani.) Lallai RIYAN ba abin yadawa bace arayuwarsa gashi tana Masa addua kullum dare d safe Bata gajiya hakan yasakashi shima yanayin adduar azuciyarsa.... Gashi Kuma Yana ganin amfaninta tunda yanxun Yana iya d'a ga kansa ki ya girgiza sa....tabbas in har ALLAH ya bashi lfy bazai tab'a iya rabuwa da itaba dukda yasan batasonsa" Amma shi Yana Mata zazzafan SO"saidai inhar yaga ya jima be warkeba to dole ya hakura kada ya tauye Mata hakki,Amma shi tuni yyi ball yasoke auren contract ,saima fatan ALLAH ya yafemasa sbd yasan bbu kyau irin wannan auren".... sallamar Hafiz ta katse Masa tunani....


Da misalin karfe 4:47 Hafiz ne ke Jaye da Abdallah dake kan keken sa,suka nufi part d'in mom sbd tunda aka sallamesa dg asibiti yadawo gd kullum sai Abba yasaka guards nasa da Hafiz sun fita dashi Gurin shak'atawa da Gurin hutawa...

Har zasu wuce sai Hafiz yace baradai suje suyi Mata sallama dukda Abdallah beso sun biyanba.

Awaiting parlour suka shiga Bata nan...zulfa ce tace tana parlourn ta...hakan yasaka Hafiz karya kwana da Abdallah suka nufi parlourn mom.

Bayan sun shige corridor d'in da kofar take , Hafiz na kokarin bud'e wa....yyi saurin dakatawa sbd jin muryar mom na mgn arude....kamar haka..

Wlh kawata bbu lfy sbd banjima da dawowa ba dg Gurin boka,wlh kashe yaron nan zanyi sbd gudun abinda zai faru..sbd boka yacemun yaga ana mishi addua zata iya yiwuwa yaji sauk'i "sannan muddin ya warke to ciwon zaidawo ajikina, alokacin zantona ma kaina asirin duk abinda nayi aciki kuwa harda yiwa alhj asirin bin umarnina da rabasa da danginsa,dayiwa mahaifiyar Abdallah kurciya shekara ashirin da ,niyar dasuka wuce,Kuma muddin ya warke karyata ta Kare kenan" meye shawara hjy ikilima?"
Yauwa !hakan za'ai mugama da mitsiyacin mukashesa har lahira ,bana kaunar Abdallah ko kad'an!burina shine nagaje abinda ya mallaka.
Shiyasa nace Miki sakashi yasaki riyan bashine fa'idaba ,gara abarta ,Kinga bayan munga bayansa sai mu korata ta k'ara gaba...shi alhj koni na k'arasashi Nanda wata 6ko7 Kinga sai ace zafin mutuwar D'ansa ce da bak'in ciki yakasheshi...

Yo ai na amso magani gun boka ,yau da dare Zan zuba Masa a frash milk nabawa shegiyar matarsa tabasa zuwa safe ya mace Kinga...da safe sai akaisa kabarin.....ah ah kwfa kamar motsi nakeji bara na duba.....

Da sauri....

Share

BY
MMN FAREESA
๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒบAUREN WATA SHIDDA๐ŸŒบ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ


Story & written by
Mmn fareesa


Dedicate to all my fans๐Ÿฅฐ๐Ÿ‘
Masumin mgn a pc banmusu reply ba dawasu grps kuyi hakuri mutane sunmin yawa nakaranta comments naku ,naji dad'i sosai tunda akafara wannan novel ba'a tab'a yin comments masu yawa zafafaba. kamar na last page nagode๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜˜๐ŸŒน


Not edited

P 29

....Dasauri Hafiz yyi baya had'e da k'ok'arin juyawa da Abdallah"da hanzari Abdallah ya girgiza Masa Kai alamar su shiga kawai...daidaita nutsuwarsa Hafiz yyi had'e da bud'e kofar da sauri... adedenan mom ta iso tana dubarsu....boyayyar ajiyar zuciya tasaki sbd ganin bbu wani tashin hankali akan fuskokinsu "hakan ya tabbatar mata da cewa basujiba kenan....mom basai mun zaunaba gun shak'atawa dama zamuje dashi"shine nace bara muzo miyimiki sallama...gsky ka kyauta Hafiz kaji"nagode sosai d yadda kake kulamun da yaro, ALLAH ya baka ladar....tak'are da cewa ai

Please Login or Register in order to submit comment