Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma'ana bazan iya wani Abu dakeba Wanda yashafi auratayya....dam..dam...Damm kirjinta yabuga!am bbu komai ALLAH yabaka lfy "Amma meyasa bakasanar daniba?"eh to naga Baki bukatane shiyasa...bejira amsartaba yashige ciki...
Har ciki ta bisa ta duba wayarsa sbd baya d'akin Yana toilet"ta duba text message bataga komaiba "haka Kuma vedio dakuma receive call nasa ... ajiyar zuciya tasaki had'e da ficewa...
Cikin sauri Abba yafito dg toilet d'in sbd Yana hangenta ta kofar toilet d'in.
Girgiza Kai yyi had'e da cewa akwai k'amshin gsky ga Wanda yaturomun sakon nan"sannan Wai da gske itace takashemun yaro?"
Wani jiri yaji had'e da sarawa yaji kansa na Masa,jinsa yake tamkar bashiba "
Number in da Suraj yabasa yarubuta sako kamar haka...

Inason ganin vedio d'in"
Sannan inason sanin sirrinta...yyi saurin turawa .

Kwanciya yyi kan bed Yana juyi...wani mugun faduwa gaban sa yyi sakamakon tuno hjy Kaka mahaifiyar sa da yyi"rabonsa da ita 2 years kenan...wani iri yakejinsa jiyake kamar ma mafarki yake,ko Kuma wani Abu na damunsa...

*********
Duk yadda riyan ta so barin jikinsa abun yaci tura,hakan yasa ta hakura ta lafe ajikinsa bacci yyi awan gaba dasu..

Washe gari ita ta rigasa tashi ,tawi wuf tabar jikinsa"
Byan sun kimtsa umma da Abdallah na fira dukda Bata cika mgn sosaiba sbd kunya , yyinda riyan ke cikin d'aki sbd zamanta atsakar gd sai Abdallah ke jifanta da kallo Mai wuyar fassara..
Abdallah ya dubi umma fuska bbu walwala yace wlh umma gabana ke faduwa gashi nayi mafarkin Abba na,Ina gudun kada muguwar matar nan tayi Masa wani Abu"inaji ajikina Abba baya qlau....cikin damuwa umma tace insha ALLAH Yana klau kuma ALLAH ya fita ni inada wata shawara Abdallah...
Sallamar Hafiz da ammi ya katse musu zance.
Cikin farin ciki aka tarbesu had'e da murna,kafin ammi tagabatar da kanta gun umma, yyinda umma tamata godiya akan jajir cewarta ga lamarin Abdallah"suka Taya juna farin ciki...shikuwa Abdallah Jan Hafiz yyi gefe suna gulmal riyan..

Ammi ta ji Dadi sosai da kakar Abdallah keda Rai ,hakan yasa ta dubi umma tace inda wata shawara Mai zai Hana ,yau mu koma kano tare dake !gobe saimu nemi jirgi muje Mai duguri,muje mu warware wa hjy Kaka koami... ajiyar zuciya umma tayi had'e da cewa wlh kamar kinsan abinda ke Raina,inason sanar da Abdallah haka kuka shigo d'azun...
Saidai matsalar guda bamusan gdn ba... murmushi ammi tayi had'e da cewa ga Abdallah nan zai bamu address na gdn..
Umma tace to"
Nan ammi ta waiga gundasu Hafiz suke taga suna 'kus k'us tayi murmushi had'e da cewa inkungama gulmar sai kuzo ai...dariya sukayi bak'i daya had'e da tasowa.... Yyinda riyan byn sun gaisa tun d'azun tabar tsakar gdn...

Kaf ammi tamasu bayanin yadda sukayi da umma"cikin jin Dadi Abdallah yace eh ammi hakan yyi"kafin yabawa Hafiz ful address na gdn hjy Kaka...

Ana gama azahar ,su ammi da umma suka yiwa riyan da Abdallah bankwana dukda riyan taso binsu"umma ta Mata tas tace baza taba ,intabisu tabarwa wa mijinta"shikuwa Abdallah ganin tana kuka sai yaji bbu dad'i "yyi zaton k'ilama kukan k'insa take..


########
Haka Abba yakwana cikin damuwa da fargaba had'e da tarin tambayoyi wad'anda bashida Mai fassara Masa su...gefe guda Kuma yanajiran yaga suwa mom zata had'a shi dasu su aikasa lahira ,sbd shi garama yamutun ko yahuta da wannan halin dayake ciki...


Da misalin karfe 12:30 pm suka iso gdn hjy Kaka"umma ce agaba sbd tasan hjy Kaka afuska "kasancewar ammi batasantaba"
Sallama sukayi acikin babban parlourn gdn"dattijuwar mace ce ,Yar kimanin shekara 70- 72 aduniya"zaune da farin glass a fuskar ta, kallo d'aya zaka Mata kasan tana cikin damuwa"kasancewar fuskar ta ta bbu walwala..
D'agowa tayi da nufin amsa sallamar masu shigowa,sukayi 4 eyes da umma... akidime ta tashi tsaye,tana nuna umma had'e da cewa Wana ke gani kamar BINTU? k'anwar HAJARA... murmushi umma tayi had'e da cewa eh hjy nice...kuka hjy ta fashe dashi had'e da cewa bintu Ina HAJARA da Abdallah jikana ,rabona dashi shekara 8 kenan ,ubansa kuwa ya manta cewa nice mahaifiyar sa shekarata 2 rabon da nagansa...ta fad'a had'e da sakin kukan bak'in ciki...da sauri umma ta k'arasa ta rungume hjy Kaka tana kukan tausayinta...


Bbu abinda kakeji sai shashshekar kukan hjy Kaka sbd bayan sun gaisa sun huta sunnmata bayanin komai da mutuwar wucin gadi da Abdallah yyi da aurensa da kurciyar da mom tayiwa HAJARA,"duka Saida suka sanar da hjy Kaka...cikin damuwa hjy Kaka ta hau yiwa su ammi da Hafiz godiya da kyakykyawar fata sbd gudunmuwar dasuka bada ga rayuwar jikanta..kafin ta dubi umma tace gsky bintu Zama a garin nan be kamaniba Dole nabiku muje kaduna Naga Yaya rayuwar d'ana take"tunda ta gama mallakarsa har yamanta Dani amatsayina na uwar dana haifesa"tsakanina da wannan Mata ALLAH ya isa har abada bazan yafe mataba"wannan wane irin rashin imanine wannan ? lallai ikon ALLAH baida karshe saikace almara,amma bbu komai haka ALLAH ya rubuta yakuma so ,tunda gashi Yana warware komai..ammi tace haka ne hjy ki kwantar da hankalinki to Amma ke miyasa Baki nemi HAJARA ba?"
Wlh y'an nan ,tun bayan rasuwar mijina banida lfy ,hakan yasa k'anina dake aiki akasar Madina yamaidani can ,yana kuladani nakusa shekara 4 acan.. alokacin da nadawo ,nasmi HAJARA Bata nan ,natambayi Kabiru sai ya nunama besantaba ,da matsa Masa sai yace yarabu da ita,sai ayanxun nasan kurciya akamata"sannan na fahimci sarkin miskilancin nan(Abdallah) yadauka itace uwarsa ,Kuma beson laifinta,naso ankarar da shi,abin yaci tura,zuwan dayyi Wanda bansake ganinsaba har yanxun ,nace Masa yazo Zan sanar da shi wata mgn Mai mahimmanci,tundaga ranar bekoma zuwaba,saidai ubansa yace mun yatafi ingila karatu..bayan tafiyarsa da shekara 2 naje har gd ,nayiwa hassu tas na zageta and na fahimci ita taraba Kabiru da danginsa,nakuma bukaci yasaketa ,sai yanuna Sam bazai iyaba,yahau mun magiya ,nayi hkri.nikuma nace bbushi bbuni,na Hana kowa zuwa gdn,har tsawon shekara 2"bezoba babu Wanda yaje adanginsa,dama shine babban agurin a sai ,halliru kaninsa,da autata safara...

Shiru sukayi kowanne zuciyar sa cike da tausayin wànnan ahali nasu Abdallah , lallai mom irinsu aduniya annobace babba..

Bayan wasu mintina
Hjy Kaka tace ,insha ALLAH zamuyi nassara akanta ,gobe insha ALLAH saina biku acan,har gdn sa ,muga zai ganeki ,Kuma zai nemi yafiyata sbd bayin kansa bane ,ta fad'a tana nuna umma..

Umma tace to shikenan ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi..

Suka amsa da Amin...

Washe gari da da guri suka kimtsa,kafin hjy Kaka takira su halliru da safara'u tasanar da su tafiyarta kaduna,juma suma zata bukaci ,suje nan gaba...

Gurin bayan sallar la'asar ta su hjy Kaka suka iso gdn Alh Kabir girma su 4 Hafiz,ammi,umma,hjy Kaka...

Kaitsaye babban parlourn gdn suka nufa, Hafiz yyi saurin cewa,kubari nashige gaba,ke Kuma matar sai kibiyoni abaya , yafad'a Yana nuna hjy Kaka Yana murmushi"dungure Masa Kai tayi tana cewa haba ai kamun tsufa ,nabarwa Matarka Kai, tafad'a tana dariya sbd har cikin ranta tana kaunar Hafiz jinsa take tamkar jikanta ne shima...

Sallama Hafiz yyi"mom na kwance cikin kushin ta aza k'afa d'aya kan d'aya,da alama duniyar ta Mata dad'i...

Amsawa tayi a yatsine, had'e da dubar Mai yin sallama,idonta yahango Hafiz...

Gabanta yyi mugun faduwa,rabaon ta dashi tun ran bakwai na marigayi Abdallah"had'e rai tayi had'e da cewa mlm lfy?"in maula ta kawoka,to ai Wanda kake zuwa gurinsa ya shek'a barzahu..azatonki kenan , matsiyaciya annamimiya Mai bak'ar aniya to jikana nabusa doron k'asa bai mutuba,tunda ransa ba a hannunki yakeba...hjy Kaka tafad'a had'e da fitowa dg bayan Hafiz, yyinda umma da ammi suka bayyana...

Wani mummunan faduwa gaban mom yyi,tuni gabanta yahau dukan 100 100 lolx...ammi tayi murmushi had'e da cewa naja'at Musa ce tsaye agabnki ,nasan a hospital Baki ganeniba,to yanzun nasanar da ke ,Kinga kin fita dg duhu ko...umma ta karbe zancen da cewa nikuwa nasan Baki sanniba nice BINTU k'anwar HAJARA da kikayiwa kurciya,Kuma nice mahaifiyar Riyan matar Abdallah...wani irin zabura mom tayi, tuni kunnan ta ke jiyo Mata gargadin klboka,inhar yaga jinin matarsa to zai tunata...saidai kafin tayi wani Abu , sallamar da Abba ya kwad'a tadaki dodon kunnanta..cikin tsantsar tashin hankali tace alh kada...kad... BINTU UUUUU!Abba yafad'a da k'arfi had'e da nunata da yatsaya,saikuma yadafe kansa had'e da runtse idonsa ,yanajin hajijiya, had'e da juwa ,asukwane Hafiz dake rungume da hannayensa na kallon tashin hankali acikin idanun mom,yyi saurin tarbe Abba... yafad'i sumamme...
Mom kuwa da gudu ta nufi kofar fita,Amma Ina...umma tayi saurin fincikota ta wanketa da wani gigitaccan Marka lafiyayyu guda 3 ,saiada jinta na wucin gadi yadauke, kafin,ta hankada ta,ta fadi kanta yabigi k'asa...ammi ta kamawa umma suka aza keyar mom ,suka kaita wani d'aki suka rufe...

Kafin sukoma su Sami Hafiz na yarfawa Abba ruwa .

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Abba yasaki ,Yana furta INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU'UN....

Faruq da Alhasan na shiga cikin gdn ,suka Sami hussy na kuka ummi na rarrashinta,Zama sukayi akan 2 seater, Alhasan yace kingani ko ummi ?abinda nake hangowa kenan gashi yafaru...

Ya isa haka Dan.... maganar ta mak'alewa ummi, sbd jin kanta yyi mugun sarawa...

Rufe ido tayi had'e kwantar da kanta jikin kujerar da ga nan Bata sake sanin inda kanta yakeba...

Da adduar tashi dg bacci ta falka abakinta, had'e da bud'e idanunta,taga su hussy , Alhasan da Faruq zagaye da ita suna Mata sannu...
Kallon su take tamkar Mai nazari tasan tabbas yayantane,to Ina Abdallah yake ?"
Cikin wani yanayi tace Kai Ina Abdallah yake???"" Da Kuma abbanku?....


Bayan tafiyarsu umma,akabar riyan nata hawaye..

Kekensa yaja ,ya iso gabda ita.

Ahankali yace....


Share

BY MMN FAREESA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾




Story & written by
mmn fareesa



Dedicate to all my fans🥰🥰

p 45


"""Ahankali yace Riyan !yakamata ace kindena kukan nan haka pls"inkuma nine bakya San gani insha ALLAH Inna sun dawo koban warkeba Zan sallameki "yafad'a had'e da kafeta da golden eyes nasa akan fuskarta..
Afirgice ta d'ago kanta suka had'a ido da shi,sai yyi murmushi Mai kashe zuciyar masoya..tsab yagane kobata sonsa to akwai tausayinsa azuciyarta da k'wayar idonta ,dama yyi hakan ne bisa plan d'in su dasuka shirya da Hafiz Dan yagane tana sonsa..mlm Dan ALLAH katafi kawani zo katsare da ido...ta fad'a had'e da murgud'a baki tana k'unk'uni" bedena kallonta bekuma Yi mgn ba,saima burgesa datayi ,sbd intana Masa hakan jinsa yake acikin nishadi... hannunsa Yayi saurin azawa kan nata ya rik'e Gam,kallonsa tayi tawani d'aure fuska ALLAH kacikamun hannu "kosokake kaci zalin d'ina ne?" Dariya yyi har fararan hakoransa suka bayyana...kafin yyi mgn jankwata k'ware(k'adangare) yafad'o k'asa jikake timmmmm!ahhhhh wayyo ALLAH Yaya Dan ALLAH kakoresa"riyan ta fad'a cikin tsoro had'e da buya bayan Abdallah ta rirrik'esa,kanta na a kafad'ar sa, hannunta nakan kirjinsa zuwa cikinsa, yyinda gogan naku yawani riketa Gam "Yana cewa yishiru bazai Miki komaiba"yafad'a had'e da Kiran Inna mairo dake cikin d'akinta...da sauri ta fito ...saikuma tayi baya ganinsu ahaka.shikuwa Abdallah ko ajikinsa saima cewa yyi Dan ALLAH Inna afitar da k'adangaren nan yatsoramun ita..sai asannan Inna ta lura dashi tasaka tsintsiya ta korasa...ajiyar zuciya riyan ta saki sai a sannan talura da yadda suke da Abdallah ,tayi wuf ta cikasa... amma sai yyi saurin riketa yace matsoraciya bbu inda Zaki tafi oya zauna inda kika tashi fira zamuyi yau"zance nazo...
Batasan lokacin da tasaki y'ar dariya ba sbd yabata dariya"Wai zance yazo.shikuwa shagala yyi da kallonta,sai yaji kamar karta bar jikinsa...kinyi kyau my baby Riyan"turo baki tayi had'e da cewa Yaya niba baby bace"murmushi yyi had'e da cewa ke baby ce Mana amma aguna..
Riyan muje kirakani daki zanyi waya,yyi Mata k'arya...bbu musu ta bisa d'akin"
Har gefen katifa ta kaisa ta taimaka Masa ya hau "wayar ta je ta kamasa sai ya karb'a yahade da hannunta,ya fisgota ta fad'o jikinsa"
Lumshe ido yyi ya rungume ta akirjinsa Yana ajiyar zuciya,kafin yyi k'asa da murya yace aidai namiki wayo ,yanxun bacci zamuyi kafin ayi magrib..
Ba'ason baccin maraice nidai kacikani Dan ALLAH"Kai da bakada lfy,Amma saikayita.... had'e bakinsu yyi guri guda,hakan yasa takasa Ida zancenta....


**********

Kallon kowa yake da idanunsa"ahankali Yadubi hjy Kaka yace hjy Ina hajjona?"(sunan dayake Kiran ummi)wlh nayi wani mummunan mafarki Wai anrabani da ita Kuma Abdallah ya mutu... murmush me ciwo hjy Kaka tayi had'e da cewa ba mafarki kayiba da gske ne, labarin Mai tsayine Kabiru ,kaje kayi Sallah inkun dawo Zan maka bayanin komai ,nida wad'an nan bayin ALLAH n,ta fad'a had'e da nuna su ammi...tashi Abba yyi da taimakon Hafiz suka fice atare zuwa masjid.,,,,,

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU UN!kalmar da dad'i ke fad'a kenan Yana , hawaye, tabbas hassu kin cuceni kin zalinceni ,kin rabani da matata har da juna 2 ajikinta,shin Ina zanga HAJARA ne?"inbacin dare yyi da yau bbu abinda zaisa naki zuwa Naga Abdallah.. yafad'a had'e da rungume Hafiz,yace nagode! nagode!! ALLAH yasa muku da alkhairi kaida mahaifiyar ka"tabbas Hafiz Kai Mai kaunar Abdallah ne,insha ALLAH kaida Abdallah bakuda banbanci agurina,Zan Kuma maye maka gurbin mahaifinka,tuni hassu ta so zugani akan nayimaka kaca kaca kafita arayuwar Abdallah"Ashe Kai garkuwane agaresa...shima Hafiz d'in kukan yake Yana cewa insha ALLAH Abba Dama can a uba na daukeka"
Kallon umma Abba yyi yace wlh BINTU tun danaga RIYAN gabakusa Dani kinji...bbu musu ta matso... Alhasan yyi saurin cewa nifane auta Abba dubeta k'atuwa da ita take auta... murmushi sukayi hjy Kaka tace yakanan Mai gdna zika zauna kusada ni, dariya yyi yace to matar...ummi ta dubi umma tace yanzun ita riyan d'in suna tare da Abdallan ?
Ummi tace eh ,muje gun bak'ar dagar can sai nakirasu namusu albishir"
Tashi tsaye sukayi ,ammi nacewa ummi ai Hafiz ya tafi yadakko taslim dg skul anyi hutu,Amma bazukai dareba zasu dawo"
Murmushi ummi tayi had'e da cewa ALLAH ya maidosu lfy"suka ce Amin...kafin hjy Kaka dake rik'e da hannun Alhasan tadubi Faruq tace to wannan Kuma waye?
Murmushi Alhasan yyi had'e da cewa surikin Abba ne"ma'ana Wanda hussy zata aura ne...su Faruq sai aka washe Baki, yyinda uwar gayyar tayi banza dasu,dukda Alhasan yabata haushi ,dayyi k'arya,bacin ita basonsa takeba...
Abba yace Kai Masha ALLAH gsky naji dad'i,umma tace to ALLAH yasa alkhairi yakaimu lokacin...turo baki hussy tayi tana cewa wlh k'ar.... hararan da ummi ta Mata yasaka ta yin shiru....

Kofar umma ta bud'e ... adedenan Kiran riyan yashigo ,cikin d'oki umma ta d'aga"ko gaisawa basuyiba riyan tasanar da ita Abdallah yasamu k'afafunsa da gske kike y'an nan?"gaba d'aya sukace meya farune?"Abdallah ya tashi da k'afafunsa"wani farin ciki sukaji ,hussy da Alhasan suka rungume juna, yyinda umma tasanar da riyan su ummi sun dawo gd cikin koshin lfy.... shigewa Baki dayansu...sukayi adakin..
Mom na kwance tamkar gawa,sai wari da zauri d'akin keyi"gefenta tulin kashine datayi tun jiya sbd larurar ajiya tasameta"idanunta akafe tana kallonsu"murmushi Mai ciwo ummi tayi had'e da kamo Alhasan da hussy ta dubi mom tace ,ikon ALLAH sai kallo ayau kin ganni gani ga yarana da Kuma ubansu zamu shiga sabuwar rayuwa, yyinda kekuma Taki rayuwar ta wulakanta ta mutu da ranta ,Kinga yadda ALLAH yyi dake , to kisani wanda kikayiwa hakan ya warke,ciwo yadawo kanki ,keda samun lfy har abada insha ALLAH , sannan kisani hakkinmu dakika d'auka da zalintarmu dakikayi munbarki da ubangiji,sai ranar gobe,bazan tab'a yafe mikiba har abada ALLAH ya isa tsakaninnu dake...Abba yarik'e hannun ummi bbu kunya ,Yana murmushn k'arfin hali yace kibarta ahaka,ko warin kashinta da fitsarinta ya isheta"inhar my son yadawo zuwa jibi to zansaka afitar da ita dg gdn nan akaita titi ta ida rayuwa acan... tabbas hakan yyi sbd. Haka yadace da ita,cewar hjy Kaka tana kukan tausayin zuri arta....

Gaba d'aya suka koma cikin gdn,sukaci abinci,mazan suka wuce masjids sbd magarib ta gabato,basu Jima da fitaba,hafis da taslim, hade da feedo dake fama da tulelen cikinta,suka shigo gdn,,,idanun taslim da feedo jajir sbd kukan tausayin su Abdallah da mahaifiyar sa, kasancewar yau Hafiz ya sanar da su komai ,sbd yason yau dai insunga wani Abu Dole su tambaya,hakan yasa yasanar dasu kawai..,,,,,

Bayan anyi isha'i 'auka zauna ababban parlourn gdn ,aka Kira Abdallah da riyan a video call"kowa yagansu ,sukayi mgn da kowa,ummi jinta take tamkar ansakata a aljanna Dan farin ciki,shikuwa Faruq yayarda da cewa duk Dan hakkin daka Raina shike tsone maka ido"mutane na daukar su hussy basuda asali ,Ashe sukeda babban asali ga arziki da ilimi"fatansa ALLAH yasa hussy ta amince dashi amatsayin abokin rayuwarta,yagodewa ALLAH dayaka shimai saukin kaine
da yanzun inyyi musu wani Abu yaji kunya,shi harga ALLAH tsakani da ALLAH ya keson hussy...

Abba ne yanunawa kowa part d'in sa, hussy nada d'akinta daban ,taslim ma,sai Alhasan, sannan part din hjy Kaka daban na ummi daban na umma daban ,na Hafiz ma daban da ammi , sannan sai part d'in Baki...
Yyinda part d'in Abdallah gobe za'ayi Masa gyara xuwa jibi agama insundawo su sauka....

Gaba d'aya Hafiz kusan raba dare sukayi suna video call da Abdallah har riyan tayi bacci,Saida feedo ta karbe wayar ta kashe tukum suka Bari...


Abba da ummi kuwa suna kuryar d'aka"ana firan soyayya da yaushe gamo..lolx....

Alhasan da Faruq na d'aki d'aya.
Suna kwance"Faruq yace insha ALLAH jibi gsky zantafi gd sbd office ,Kuma kaga naga,familynku ko?"
Murmushi Alhasan yyi had'e da cewa wannan gsky ne,Amma nafiso sai su Yaya da matarsa sundawo sbd yaganka, sannan maganar hussy kabarta nasan yadda zanmata Inna da gske Bata sonka Zan gane...
Murmushi Faruq yyi had'e da cewa ah ah kabarta ,pls kada kamata Dole,nifa atsarina banason auren wacce Bata Sona gsky...hmmm kaidai kabarni kawai....

Taslim da hussy suma suna d'aki guda"dukda dai hussy ta girmi taslim sosai Dan taslim bazata wuce 22 years ba...
Ammafa sai fira suke acikin kankanin lokaci suka Saba... wannan kenan.

#######
Washe gari byn duk kowa yyi break fast,masu aiki nata kaida kawowa,yyinda umma da ammi suka fita ,ammi zataje hospital, yyinda umma zataje,gdnta ta kwaso kaya da gdn zuwaira mai abinci tasanar da ita komai sbd aganinta Dole duniya zatasan Abdallah be mutuba,tunda zaidawo gd"sannan zuwaira ta taimakesu alokacin da suke buk'atar taimakon....
Hjy Kaka ma na part nata,itama ummi haka...

Taslimce zaune kan kujera a waiting parlourn gdn ,tana kallo atashar mvc 2... k'amshin turaren nmj taji"had'e da motsi....kafin ta duba taji wata murya akausashe ance ke canza tashar nan"
Cike da mamaki ta d'ago Kai, sukayi ido 4 da Alhasan...

Kicin kicin da fuska yyi had'e da cewa ko bakyaji...

D'aure fuska tayi,ta janye idanunta,tace yoni nasan wacce Zan canzane"


Ke nalura dake tun jiya,kinfi k'arfin ki gaida mutane ke y'ar rashin kunya ko?"kina wani Shan k'amshi, to ko hussy dake kanwatae,tana gaidani balle ke.... murgud'a baki tayi had'e da cewa to waini me ruwanka danine ,gaisuwa Kuma bazan gaidakaiba....cikin tsawa yace ke wlh Zan tattaki anan wlh...gama belt nan sai naba ka sata Alhasan cewar Hafiz dake rik'e da hannun feedo"kasancewar zuwansu kenan parlourn...
Cike da jin kanya Alhasan yace Yaya barka da fitowa"amsawa yyi cikin sakin fuska kafin Yadubi taslim yace bakida hankali ba yayanki bane kike Masa rashin kunya,wlh kada kibari ammi tasani,Zaki basa hakuri ko kuwa...

Cike da mamaki taslim kedubar Hafiz ,ganin wannan rashin adalcin k'ara ra,saikace bashine yafara takalartaba,dama da shiyasa Bata Masa mgn ba jiya,Dan talura Yana izza da girman Kai....bazaki basa hakurin ba ko?"

Maganar Hafiz ta dawo da ita tunanin ta...

Ahankali tace kayi hakuri"tafad'a fuska daure"

Shima fuskar adaure yace yawuce,yabar parlourn...

Dariya Kuma feedo tayi ta dubi taslim tace ikon ALLAH ku Kuma da wannan salon zaku Fara taku soyayyar...

ALLAH ya kiyaye nasosa ,Yana wannan jida kan da izzar... tafad'a had'e da fice was,cikeda jin haushi...

Hafiz yyi murmushi had'e da cewa hmmm tunda abokina ya sallama ma ai kowama yasallama,muje mmn baby, yafad'a Yana Jan hancinta, murmushi tayi had'e da cewa inama Inna fara nak'udar Kai zaka karbe cikin ka haihu"hararan Wasa yyi Mata had'e da kin manta ai,nidai kinsan Gurin jin dad'i nafi auki, shiyasa na k'agara ki haihu sbd cikin nan Yana takurani wlh...


Bangaren riyan da Abdallah....


Share


BY

MMN FAREESA🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾



Story & written by
mmn fareesa


Not edited❌


p 47

.... Zaro ido tayi had'e da tashi tsaye tana kallonsa"bakinta na motsi... murmushi yyi had'e da cewa da gske ne abinda idanunki suka nuna Miki"kada kiyi mamaki da ikon ALLAH!ubangiji ya yadda yau Nike takawa da k'afafuna"
Cikin farin ciki riyan tace Alhmdllh !yah ALLAH ka bayyanar da baiwarka cikin aminci... tafad'a tana d'aga hannayenta sama"murmushi yyi had'e da cewa ameen , adedenan ya iso beyi wata wataba yad'aga ta sama Yana juyi da ita Yana murmushi "gaba d'aya yabata kunya , addua take ALLAH yasa kada wani yafad'o gdn yagansu "Yaya kasaukeni " bafa mukad'ai bane pls , nak'i saikin had'a ido Dani tukum saina saukeki...ninama ga kamar Baki murna da tafiyata ba ko?"kafin tayi mgn sunji muryar mlm Yana musu gyaran murya had'e da cewa Masha ALLAH Alhmdllh !
Sauketa yyi ,Yana murmushi ko ajikinsa "yyinda riyan tashige d'aki da gudu"sbd jin wata iriyar kunyar mlm yagansu ahaka"
Sosai mlm yyi farinciki da samun tashin Abdallah , yyinda Inna ta fito ta tayasu murnar wannan abin dad'i... d'akin yakoma"
Tana jin motsin shigowarsa ta rufe idonta"murmushi yyi had'e da rage kayan jikinsa "yarage sg shi sai boxer ....jinsa yake tamkar yau yafara rayuwa"lallai in har ALLAH ya baka Rai da lfy kagode Masa kobai baka komai ba aduniya,ya yarda da ake cewa lfy jarice...
Kansa ya kallah yanjin farin ciki Wai shine yau yake tafiya da k'afafunsa.
Kan kafitar yanufa Yana cewa garama ki bud'e idonki yarinya "wanka Zaki tashi muyi! yafad'a Yana haurawa kan kafitar yahad'e jikinsu gu d'aya"yasakar Mata nauyinsa ....wani yarrrrrrrr!sukaji dg shi har ita,Yana murmushi"murya can k'asa k'asa yace muje toilet muyi wanka ,Kinga nima saina Rama kallenin dakikeyi inzakimun wanka ,kafin nayi Mai gaba d'ayan.... atsorace ta bud'e idonunta...tsab acikin nasa...turesa ta hauyi dg jikinta,tana janye idanunta , had'e da turo baki ashagwabe tace Wai miye haka?"bbu kyaufa mugunta da cin zali nika.... had'e bakinsu yyi guri guda yafara aikamata da hot kisses...ta yi iya yinta Akan tak'waci kanta ta kasa"
Shikuwa gogan ,yafama Fara fita hayyacinsa,sabida romancing d'in ta kawai yake, yyinda riyan ta rufe ido,jikinta amace" da alama tana karb'an sak'onsa.... Saida taga Yana kokarin cire Mata riga yasakata cije Masa labb'ansa ,yyi saurin sakar Mata Baki "yana cewa lah lah zankuwa rama"yafad'a Yana d'age gira"kafin ta yi hanzarin Masa cakulkuli ,yyi saurin janyewa dg jikinta Yana k'yalkyala dariya"tayi wuf ta tashi dg kan kafitar,kallonta yyi had'e da cewa zamu had'e anjima yarinya"Zaki gayamun hakkin nawane bbu kyau ko kuwa?"matsoraciya dake kawai...


Bata sauraresa sbd abinda yamata yanxun ta tsorata ,takuma Yi mamakinsa!dama haka yake?

D'akin Inna mairo ta nufa , yyinda Abdallah yafito yawuce bayi Dan yin wanka ,inyafito yagyara fuskarsa datacika da kasumba,kafin yasanar da Yan gd yasami k'afa,dukda yasan Abba jiya yace yau zasuxo adubasa ....

************
Cikin wani irin farin ciki sukace da gske Dan ALLAH?"
Ammi tace wlhy ,bara nakira...hands free tasaka wayar byn tayi calling!salamu alaikum cewar ummi...wa'alaikumussalam hajjonah!cewar Abba cikin wani yanayi"tuni hawaye suka zubowa ummi Dan bazata tab'a mantawa da muryar Abba ba"kiyi mgn Dan ALLAH kice wani Abu...hussy ta kalli Alhasan tayi murmushi had'e da nuna Masa ummi da ido Wai da alama suna soyayya da abbansu alokacin dasuke tare"kasancewar itama ummi a hands free tasaka wayar...Abba ummi kuka take ,sunana Alhasan d'anka jininka... wayyo ALLAH Abba ga hussy nan nima y'arka ce"suka had'a ido da Faruq ta galla Masa harara...
Cikin farin ciki yace ya'yana dama HAJARA kin haifwmun cikin dake jikinki?"kashe wayar ummi tayi sbd kada Abba yyi katob'ara ga yarah..

Alhasan ne yakarbe wayar yasake Kira ,cikin farin ciki yasanar da Abba gasu a kano agdnsa...
Abba yace suje air port gashinan tafe a heli copter zaizo yatafo dasu kaduna... sannan yasanar da da Alhasan yacewa ummi suna tare da BINTU k'anwar ta...

Bayan awa 3...
Bakajin komai sai shashshekar kukan ummi, Alhasan,hussy, Faruq, shikanshi abban kukan farin cikin dawowar iyalansa taye" yyinda umma ke rungume da y'ar uwarta...
Bayan sun tsagaita kukan ,ummi tayi ajiyar zuciya had'e da cewa Alhmdllh ALLAH nagode maka da kakamun k'arshen wannan K'ADDARA daka jarabemu da ita"sannan ta dubi ammi tace baiwar ALLAH nagode ! nagode!! nagode!!! ALLAH yasa ka d alkhairi,yabar zumunci Dan ALLAH akiramun Hafiz d'ana yazo namasa godiya"ubangiji yabawa Abdallah lfy gobe insha ALLAH kukaini naje nadubosa"Abba yace to shikenan dama yau zamuje sai ALLAH yasa kuka dawo yafad'a had'e da kamo hannun hussy yace autana zoki zauna kusa Dani kinji...bbu musu ta matso kusada Abba tana dariya had'e da yiwa Alhasan gwalo.. Alhasan

Please Login or Register in order to submit comment