Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa babana yakoreni"yakuma gargade Ni inhar yaji labarin naje gdn y'an uwansa zai tsinemun...
Hakan yasa naso ingudu awannan yanayin mota ta kadeni sai cikin yazube ,wanda yakadeni yakaini asibiti nayi kwana3 sannan nakoma gd nasanar dasu"tun kan in ida shiga gdn babana yyimun dukan tsiya yakoreni, mahaifiyata na kuka nabasa hakuri be saurareniba"tace natafi gdn danginta"sai yace innaje bakin aurenta!hakan yasa na kwana amakotanmu yau da asuba na hau motar Yola amma bansan Ina zanijeba..
Saida ummi ta Mata kuka sbd tausayi "sannan tace ki kwantar da hankalinki ,insha ALLAH zamu zauna tare kidai rik'e Amana Dan ALLAH.
Kukan farin ciki yusra tayi had'e da Mata godiya,kafin su tambayi gdn Mai anguwa aka nuna musu...

Byn sun gaisa had'e da samun tarba ta mutunci gun matan Mai anguwa.

Ummi ta Masa bayani,kamar haka"

Sunana HAJARA! wannan Kuma yusra kanwatace,mu Yan gudun hijirane,ankashemun miji da iyayena dg Ni sai muka tsira da cikin dake jikina.. ajiyar zuciya mlm dauda ( Mai anguwa)yyi Yana dubarsu had'e da nazartarsu.

Can yace to yanxun miye dalilin xuwanku anan gurina!

Ummi tace munaso Dan ALLAH kabamu masauki zuwa gobe insha ALLAH sai asama Mana gd karami musiya mukoma.

Masha ALLAH bbu damuwa !cewar mlm dauda"

******
Haka kuwa akayi washe gari mlm dauda yaje dasu ummi kasuwa ta siyar da sarkan gwal d'in ta anaira million d'aya da dubu dari bakwai...
Aka Samar musu gd karami na million d'aya da dubu dari"daki biyune sai kitchen da toilet sai soro guda.
Bbu laifi gdn Mai kyaune Kuma sabo yasha tayis da fanti ga famfo akwai..

Acikin kwana2 suka koma bacin sunyi Yan siyayyar abun amfani aciki harda katuwar freezer da yusra tabada shawarar ummi ta siya taruka Sanaa sbd Gurin akwai jamaa ga Kuma islamiya dake gaban gdn.

Hakan yasa ta siya bbu bata lokaci suka farayin zobo da kunun Aya ,cikin ikon ALLAH abin yasami karbuwa da albarka..kullum sai sunyi sob'o na tiya 2 kunun Aya na tiya3 ga pure water anashigowa asiya"Kuma duk cikin gd suke siyarwa harya Kare.
Da wannan Sanaa sukeci suke sha...

Cikin ikon ALLAH cikin jikin ummi nata girma byn wata6 ta haihu agd Kuma twins..mace da namiji"murna Gurin yusra baa mgn...

Acikin haka Yara suka tashi da kiriniya had'e da b'anna..

Kyawawa dasu macen wankan tarwada ce namijin bak'i ne.

Saidai matsalar dasuka Fara fuskarta itace!da farko anxata mijin ummi yarasu,byn ta yaye twins sai jawarawa sukayimata caaaaaa!abinka da farar mace bafulatana Kuma kyakykyawa...ita kuwa tasan Sarai tanada aure hakan yasa Bata kulasu..ko sakan musu fuska.

Hakan sai yasa ake zundensu Wai ai yaranta shegune basuda uba basuda asali"

Duk intaji hakan ranta na zafi da k'una"ita kanta yusra batajin dad'in hakan.

Sau tari insun fito waje saikaji yaran anguwa na tsokanarsu da cewa Ina babansu basuda uba.

Dasunzo gd sai suyita tambayar ta,ummi Ina abbanmu?"

Wani lokacin har hawaye take sbd rashin amsar dazata basu.saidai tace abbanku ya mutu.

Da wannan yanayin suka Fara tasawa har suka Kai she kara5 tasaka su skul harda islamiya.

Suntaso darashin ji had'e da k'iri niyar tsiya ga fad'a"akwaisu da Jan fad'a ,sai suyi Taran dangi ga Wanda suka ja.

Suna mugun son junansu da tsokanan juna musammun ALHASAN"yyinda yake Kiran HUSAINA da anty hussy!kasancewar itace babba"

Duk ranar da aka goranta musu Alan basuda uba sai sunyi kuka dukda atime d'in yarana sosai.

Hakan yasa ummi hanasu yawan fita sai intare da yusrane ko Kuma zuwa skul..

Ana cikin hakan"sunje kasuwa siyayya itada yusra...kwatsam yusra taga k'anin baban ta"yakuwa tsaidata had'e da tambayar ta Ina ta tafine anata nemanta tsawon she kara5 da wasu watanni?"

Ummi tamasa bayanin suna tare "byn yabinciko gsky yyimata godiya sosai washe gari yazo yatafi da yusra gd gun iyayenta... wannan shine dalilin rabuwarsu da yusra ,suka dawo rayuwa su kad'ai...

Bayan shekara 20....

Kuyi manage da wannan"
Happy week end🥰


Share

BY
MMN FAREESA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


Story & written by
mmn fareesa


Not edited❌

p 38

Bayan shekara 20
""Abubuwa da yawa sunfaru "aciki harda girman twins da tashinsu dg gdn dasuke da ALHASAN Yacanza musu sbd ayanzun shi cikakken d'an jaridane(Yana aiki agdn TV) kasancewar sa Mai k'wazo yasa acikin wad'anda gwamnati tabawa schooler ship hardashi"yatafi malesia yyi 5years acan"bayan yadawo yasami aiki yacanza musu gd..
Yyinda hussy tazama nursing"harda yanzun cikin su bbu maimarmarin aure arayuwarsa sbd basusan kosu suwayeba!hakan yasa basa soyayya dukda hussy tanada tarin masoya Bata kulasu wasukuma insunji basuda asali saisu shareta"
ALHASAN miskili ne shima akwai izza Amma baikai Abdallah ba"betaba son wata ya maceba,Amma yanada wata friend salimat dasukayi karatu a malesia tare "da farko suna mutunci Amma dg baya data nuna sonsa take sai ya nuna be ganeba yyi baya da ita,gefe guda Kuma y'an matan Yola na masifar sonsa kasancewarsa Dan jarida Mai farin jini....
Basa Jim dad'i suk sadda suka tuna basu son asalinsuba"sannan Kuma insunso tambayar ummi saitakama kuka hakan yasa suka Dena Mata mgnar"
Hussy ta tashi kyakykyawa wankan tarwada gajera yyinda Alhasan yatashi saurayi Mai jini ajika dogo Baki kyakykyawa Mai aji,miskili...
Inna kagansu zaka d'auka ba twins bane sbd hussy karamin jiki gareta saikace Alhasan ne yayanta.
Har yanzun shakuwarsu
Na nan saima karuwa datayi...ayanxun shekararsu 26.,,,,,

********
Zaune take acikin parlour madaidaici" Mai d'auke da kujerune matsakaita sai tv stand dake d'auke da plasma Media size da dvd sai receiver"sai carpet atsakar
parlourn..
Bubu laifi yyi kyau iya gwargwado ga Mai rufin asiri...wayar Alhasan ce hannunta tana duba sakunansa na PC chat"sai dariya take ta na girgiza Kai...wani fitinan nan kamshin turare yadaki hancinta"
Lumshe ido tayi had'e da d'ago kanta tabusa, sbd tasan Alhasan ne.
Wow gsky broth kayi kyau! wannan babban wanka haka sai Ina Kuma?"
Fuska bbu walwala ya zauna kusada ita had'e da aza kansa akan kafad'ar ta yace BABU atakaice!
Kobata tambayesa damuwarsa ba" tasan miye damuwar" sbd haka sai ta k'akaro murmush had'e da cewa gsky dagani "yakamata ace acikin Yan matan dake sonka kafitar da guda musha biki Dan ALLAH !konima nazama yayar miji arika girmamani... tafad'a tana dariya"tsaki yaja had'e da cewa matsalata dake kenan wlh..ah ah miye abin damuwa kaga ma kausar kawata tace tana ciki...hussy tafad'a had'e da ture Masa Kai dg kafad'ar ta.
ALLAH ya kiyaye wlh na auriaizo har get take rakosa,takuma musu gargadin duk time d'in dayazo su barashi yashiga...
Hakan yasa suka tsaya had'e da cewa kobashine bane,ana hakan yyi wuf yafice dg gdn" ita Kuma alokacin ta iso Gurin..
Sbd tashin hankali tuni ta fad'i Gurin su mamma...


********

Abdallah da mlm na zaune atsakar gd suna fira...sukaji sallama...da gudu riyan ta fito Dan darban ummanta sbd tasan da zuwanta sunyi waya ajiya ta sanar da ita sunan k'auyen datazo ta tambayi gdn mlm HABIBU za'a kaita..
Wani mummunan faduwa gaban umma yyi alokacin da suka had'a ido da Abdallah dake murmushi Yana Mata sannu da zuwa!Bata tab'a ganinsaba sai yau ,dama sau d'ayane yaje yagaida ita shima Kuma Bata kallesaba"
Fuskarsa ta Mata Kama da KB(sunansa na kuruciya) mijin HAJARA yayarta data Bata...

Dakewa tayi had'e da boye mamakinta"ta gaida mlm da Inna mairo kafin Abdallah da riyan suka bita d'aki suka gaida ita...

Kok'arin fita Abdallah ya keyi "sauri riyan ta ce lahh Kinga umma Yaya Abdallah fita zaiyi Wai kunyarki yakeji... murmushi umma tayi gabanta na faduwa sbd ta tuna sunan Dan Yaya HAJARA Abdallah"

Hararar riyan umma tayi hade da cewa to yyi dakene ?

Juyowa Abdallah yyi da keken Yana murmushi yace rabu da ita umma bacin yanzun kindena Yi da ita saini... yafad'a Yana kashewa riyan ido...

Turo baki tayi had'e da cewa umma Wai da gske?"

Eh Mana "

Dariya yyi ta Mata,itakuwa tana hararan sa"

Sosai umma ta jajanta Masa had'e cewa Dan ALLAH ko kanada photo na mahaifinka nagani sbd inason sanin gano wani Abu?"

Da mamaki abdallah yace ah ah wlh sbd manyan wayoyina matar Abba ta k'wacesu... k'aramar ce kawai hannun riyan"Amma Zan iya zanamaki tunda hannuna na aiki...

Umma tace ah ah abarshi kawai...ah ah umm tunda zai iya bbu komai fa cewar riyan..


Haka kuwa akayi cikin kankanin lokaci mlm yasaka aka samo pencil da colours Abdallah cikin kwarewa yasoma zana alhj Kabir girma....

*********

Zazzaune suke har da ummi suna cin abincin Rana"cikin son tsokana Alhasan Yadubi hussy yace kije ki gyaramun d'akina kihadamun ruwan wanka... murmushi tayi had'e da kallonsa ashek'e yace to Yaya angama!
Itadai ummi najinsu batace komaiba!
Ummi Wai kece kikayi girkin nan kuwa?"
Itace Mana!cewar hussy dason jin mezaice!
Haba no wonder shiyasa yyi mugun dad'i.....hhhhhhhhh😂🤣 dallah mlm bi ahankali kada ka k'ware Gurin yin Santi" to ninayisa ba wata ummi...

Yamutsa fuska yyi had'e da cewa hmmm to ai nima Wasa nake Dan naji Mai zakice ai!

Hmmm kajidashi ai ,sarkin gulma"kadai Fadi gsky kaji.

Naji ta Mohd bada kanki asare... had'e rai tayi had'e da cewa wlh ya isheka"

Haba my sweet hussy!Kinga kawai ayi Yar gida da friend d'ina farouq kawai"ummi kingani ko?
Tsaki ummi tayi had'e da cewa kunfi kusa ai...

Aje spoon d'in hannunsa yyi had'e da cewa muje mugyara d'akin kinji antyna yafad'a cikn marairai cewa...

Murmushi hussy tayi sbd tasan badan ALLAH yaceba"tashi tayi tabisa tana cewa hmmm su oh oh d agdn masu kud'i ka fito dakayi mulki da son jiki son ranka wlh, komai sai namaka, to inda babbuni ummi kasan bazayi makaba ko?


Yatsina fuska yyi hade da cewa Kinga inbazaki gyaramunba kirabu Dani ,kintasani agaba kinamun surutai...

Eh naje nayi ,kayi maganin abun manah"ance kayi aure amma kaki Yi,in kanada Mata saika juyata yadda kakeso...
Finciko hannunta yyi had'e da cewa me kike fade?"

Haba my sweet broth!Yaya Alhasan !muje nagyara maka d'akin.

Murmushi yyi mai sauti....


Abba ne zaune a office nasa.

Wayarsa tayi k'ara alamar shigowar sako!

Dubawa yyi saiyaga ansaka kamar haka.....

Kun rage comments ba kamar daba, kodan kunga kullum kuna samun 2 pages to dg yanzun 1 zaku samu"
Banason tanx ko steakers comments kawai....


Share


BY
MMN FAREESA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


Story & written by
mmn fareesa


Dedicate to all my fans🥰🥰👍

Not edited

P 41

Ak'agare yace miye shawarar?"

Ajiyar zuciya ammi tayi had'e da mik'e wa tsaye tana safa da marwa... cike da tausayawa tace na farko dole Abdallah yyi mutuwar wucin gadi sbd shi yak'i Dan yaudarane,inbaka iya Kama b'arawoba saishi yakama ka"
Ma'ana zanyiwa Abdallah allurar da zatayi 24 hours ajikinsa tana aiki "tun dg yau zuwa gobe kamar yanxun , sannan ta sakesa kafi....Amma ammi ta yaya kenan bacin kinsan sotake taga bbushi aduniya..jirani Mana Hafiz"cewar ammin.
Ai yanzun zanmasa allurar zaiyi kusan 30 or 35 minit kafin tafara aiki ajikinsa"
Na biyu...shine byn yanxun kamaidasa gd "zamuje Gurin liman me tsaran makabartar dake k'arshen g r a,nida kai muyi Masa bayani in ankai Abdallah anbinnesa zaka koma ku hak'osa kaidashi"sai dare yyi kaje ka daukosa ka maidosa nan gdn"na ukku shine in anyi sadakar 7 Zan canza Kama na nuna nice yayar mahaifiyar riyan naje na cewa hjy hafsat Zan tafi da ita gd tayi ta kaba,nasan zataso hakan"dana tafo da ita nan sai kawai ,mujabgoransu nidakai zuwa k'auyen karaye gdn baffanka MLM HABIBU(masanin kur'ani mai girma,Yana karya sihiri yayan mahaifin Hafiz ne) nasan insha ALLAH Abdallah komai Daren dad'ewa zai warke sbd da alama sammu aka Masa "kaga dg nan inya warke sai ya fito ya yak'i hjy hafsat,Amma tunkararta yanxun gsky bashine mafitaba sbd shikanshi mahaifinsa tagama dashi....na hudu shine duk jawabin nan kusanar da matarsa (riyan) sbd gobe in ALLAH ya kaimu zatafito tana kururuwa byn sallar asuba ta nufi part d'in hjy hafsat tasanar da ita Abdallah baya numfashi ko motsi...munsan dama burunta kenan ,Kuma baza a bincika ba sbd tagama da Abbansa,inkuma riyan ta ji ana cewa za'a bincika aga ya mutu ko kuwa to tayi hanzarin kiranka !kaikuma ka kirani.....

Ajiyar zuciya Hafiz yyi had'e da kallon Abdallah cike da tausayawa abd ganin za'a sa yyi mutuwar wucin gadi...

Ahankali yace AK kaji duk jawabin ammi ko?"

"D'aga Kai yyi "alamar eh.

Hafiz yace ka amince da shawarar ta?"

Abdallah ya d'aga Kai hawaye masu zafi na zubar Masa akumatu...ba tausayin kansa yasa Kashi kukaba,ah ah tausayin mahaifiyar sa da aka rabashi da ita tsawon wasu shekaru... lallai ya tafka kuskure "Yana zaune duk baisan hakan ba..wata zuciyar tace K'ADDARA ce tayi sanadin hakan..


Muryar Hafiz ce ta katse Masa tunani gun cewa to ammi kusanar damu wacece HASSU TSIYA TSABA?"

Ammi ta ce Zan sanar da ku,Amma lokaci ya kure yanxun Hafiz ,muyi abinda ke gaban mu..

Hafiz yace to shikenan....

Kamar yadda ammi tace haka akayi tayiwa Abdallah allurar(bazan fad'i sunantaba sbd kada anema acutar da wani)

Sannan Hafiz da body guards nasa suka maidasa gd gab da magrib , Hafiz be bar gdn ba Saida yyiwa riyan bayanin komai gameda shawarar da ammi ta basu,yakuma sanar da ita tayi taka tsan tsan Dan kubutar da rayuwar Abdallah ,sbd yau da isha'i mom zatazo ta kawowa Abdallah frash milk,kada ta yarda yasha..

Bayan Hafiz ya koma gd sunyi magrib da isha'i,yaja ammi amotarsa ,sukaje gun liman me tsaran makabartar,suka Masa bayanin komai sbd sun San insunkoma basu sanar masaba ,da matsala za'a zargesu ne...da farko liman ya nuna be yardaba ,Amma dasuka Masa bayani sosai suka nuna Masa photo na Abdallah sai ya amince ,yyi musu fatan samun nassara.

Bangaren su riyan kuwa.

Suna cikin tashin hankali da faduwar gaba har akayi magrib zuwa isha'i.

Zaune riyan take kan kujera, yyinda Abdallah ke kan kekensa zaune jigum Yana jiran zuwan mom.. had'e da tunanin Wai shine gobe zaa binne da ransa....oh shin mi wasu suka dauki duniyane Wai?"

Sallamar mom ta kashe Masa. Tunani... Wani mugun faduwa gaban su yyi shida riyan.

"Cikin ambaton ALLAH riyan ta amsa"tana kallon frash milk din dake hannun mom cikeda cup.....

Zama tayi fuska asake ,ta amsa gaisuwar riyan,kafin tace yamai jikin?

Riyan tace gashinan da sauk'i...

To madallah"ga frash milk sabon yayi,abashi Dan tafi waccan dakuke bashi,ta fad'a had'e da cewa to gata abashi mugani kota Masa dad'i...

Karb'a Riyan tayi hannu na kirma..

Mom ta matsa ta shafi kan Abdallah had'e da cewa sannu my son kaji"ALLAH ya tashi kafad'ar ka "dakai nake kwana nake tashi azuciyata sbd tausayin ka Abdallah kana cikin wannan hali,bbu jiii bbu mgn Amma aikomai yakusa zuwa karshe tunda za'a fita dakai waje... fad'a had'e da kukan munafurci Wanda bbu hawaye.

Azuciyar riyan tace shaid'aniya kenan,afili kuwa sai taita rarrashinta gun cewa kiyi hakuri mom ki yarda da k'addara insha ALLAH zai Sami sauk'i.

ALLAH yasa riyan "
Ameen mom"maza ki basa mugani kozai shnye ne...


Daukar cup d'in riyan tayi tana latsa wayar Abdallah dake hannunta had'e da kokarin Zama kusada keken Abdallah Dan tabasa...

Bata kaiga zamaba aka d'auke nefa ta gdn Baki daya...

Mittsss mom taja tsaki hade da cewa Kai Yan nefa bbu tabbas Yanzun ai ya'u direba zai tada Jan...

Kafin riyan tayi mgn haske ya gauraye parlourn...

Murmushn samun nassara mom tayi had'e da cewa yauwa anmaido"maza kibasa yasha aje akaisa ya kwanta...

Kallon mom kawai Abdallah keyi,jiyake kamar yashaketa sbd tsanarta,sai yau ya yadda da ake cewa wasu dg cikin Mata shaid'anu ne,Kuma dangin shaid'an...Ashe duk abin nan da mom ke Masa ba Dan ALLAH bane...cup d'in da riyan ta Kai bakinsa yadawo dashi tunaninsa....

K'uri da ido mom tayi tana dubarsu har Abdallah yashanye tas , riyan ta dubi mom had'e da cewa Kinga kuwa ya shanye duka bara na Kai cup din kicin natafo Masa da fura ya k'ara....

Ajiyar zuciya mom tayi aboye, yyinda fuskar ta fal da farin ciki tace to shikenan jeki dawo nima na wuce,namaji Alh shiru baidawoba bare yazo yaduba my son...riyan ta fice dg parlourn da cup a hannunta....

Tana fita mom ta kece da dariya had'e da cewa banzaye ,wawaye daku kaida ita... lallai Abdallah dg yau kagama numfashi... matsiyaci na tsaneka bana kaunarka kokadan ,ko rungumeni kayi ,jinake tamkar na shakeka,naso ace ka auri zeenat nasakata ta kashemun kai....

Duk abinda take cewa Abdallah najinta Amma be dagoba balle ya nuna alamar yaji,yyidai shiru...akuma dedenan Abba yyi sallama yashigo cikin parlourn.

Amsawa mom tayi , had'e da maida fuska kalar tausayi,tace Alh yakamata fa amaida Abdallah hospital kafin zuwan ranan da za'a fiddasa waje....

Zama Abba yyi hade da cewa,eh wlh nima naso hakan Amma k'ila amaidasa gobe....kafin tayi mgn riyan ta shigo.

Nan suka gaisa da Abba,kafin yakoma Gurin Abdallah Yana shafa kan sa, Yana Masa fatan samun lfy...dg bisani sukayi sallama ,atare da mom suka fice.

Byn sun fita ne.... Saiga ammi ta fito dg bayan kujerar da riyan ke zaune tana ajiyar zuciya. ..riyan tayi ajiyar zuciya tace hankalina fa yatashi danayita ma yaya Hafiz flashing,amma anki adauke nefa...sai yanzun Dana kirasa akicin yacemun ai akan idonsa mom ta shigo parlourn nan..

Ahankali ammi tace nikaina wlh ,hankalina be kwantaba Saida aka d'auke nefa na canza Miki frash milk d'in na karb'i me maganin.

.gata maza kije kiyi floshing nata ,nibara natafi gd zanbi ta inda Hafiz ya shigo Dani,yanacan Yana jirana.ALLAH yashige Mana gaba ,ki kula sosai kiyi yadda komai zai tafi daidai...

Insha ALLAH ammi ,riyan ta fada had'e da nufar bed room d'in ta.

Ammi ta kalli Abdallah dake sauronsu Yana kallonta da ido yanason yin mgn sai bakinsa ke motsi.

Murmushi tayi had'e da babu godiya tsakaninnu kaji Abdallah dakai da Hafiz duk d'aya me aguna,ta fada sbd talura abinda yakeson fad'a Ken.

Saida riyan ta dawo , sannan ammi ta fita....

Washe gari.......


Share

BY
MMN FAREESA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾



Story & written by
mmn fareesa

Kuyi hakuri my fans dajina shiru Ina da uzurirrikane🙏🏼 sannan Ina godiya ga wadanda suka kirani da Kuma masu turo sakuna" nagode sosai d kulawarku... sannan duk week end gsky bazaku samuba🤣


Not edited❌

p 41

......Matarka!hjy hafsat tana d'auke da cuta mai karya garkuwar jiki H I V....nine Kuma na lik'amata ita"
In kana kokwanto zanturo maka video d'in da nike kusantarta! Kana sone?"sannan nasan tamaka asiri tana juyaka bacin ta rabaka da iyalanka...kada kasake ka kusanceta Koda ta bukaci hakan "sannan inta maka kwarjini ka ambaci sunan ALLAH insha ALLAH zakaji tsoron yarage "
Niii..na tuba yanzun ,inhar kana bukatar jin sirrin Matarka ka turo sako ta wannan number 09087671240..... Ka Kuma goge sakon sbd zata iya dubawa....iya nan Alh kabir girma yakaranta" zuface keta keto Masa dukda acikin AC yake d fanka" yyinda zuciyarsa ke tambayar sa cewa ta rabaka da iyalanka? To suwaye kenan...wani faduwar gaba yaji had'e da mugun sarawa kansa yyi "da k'arfi yyita ambaton sunayen ALLAH...ji yyi zaman office d'in ya ishesa,hakan yasa yatafi gd "zuciyar sa nason tuna Masa yau kimanin wata 3 kenan rabonda yakusanci mom tun kafin marigayi Abdallah yarasu..lolx..yakuma aiyana aransa Dole yaga video d'in, sannan bazai yarda wani Abu yashiga tsakanin suba "Kuma Wai da aurenta take aikata Masha'a ,inda gske ne to tun yaushe ta Fara aikata hakan?"

Koda ya iso gd "har part nata yaje Amma bbu ita bbu alamarta"yakira wayarta akashe"to Ina ta tafi?yatambayi kansa dukda Bata tambayar sa zuwa anguwa...wasu hawaye ne masu zafi suka zubo Masa sbd tuna Abdallah da yyi"ahankali yace ALLAH ya jikanka da rahama...gaba d'aya sai yaji yatsani rayuwarma gaba d'aya...

*********
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU'UN!shine abinda umma ke maimaitawa had'e da nuna photon Abba da hannu tana hawaye had'e da cewa shine!shine!!shine!!!wlh shine mijin yayata HAJARA data Bata shekara 25 kenan...cikin zaro ido had'e da mamaki riyan da Abdallah keyiwa umma kallon tambaya...da sauri ta d'aga Kai had'e da nuna Abdallah tace Ni jininka ce Riyan k'anwarkace! shin ya akayi hakan yafaru ?"tafad'a cikin kuka da shashsheka"dama hassu itace kishiyarta?"ni dama bansantaba alokacin da akace mahaifinka zai k'ara aure sbd alokacin ko aure baa munba"Kuma bayan AUREN abbanka da wata2 mukaje kano gun mahaifiyar ka kace sun tashi...

Cikin mamaki had'e da al'ajabi Abdallah yace umma ke k'anwar mahaifiyatace?"

Tace k'warai da gske "sbd ga sheida nan,na photon mahaifinka da Kuma yadda Naga kuna yanayi da Yaya HAJARA"sbd Kai jinintane,gashi sunanka Abdallah ,hakan ne sunan d'an data Haifa...umma na yarda !Ashe dama ko Yaya zanga jinin mahaifiya ta kafin nabar duniya ?

Yafad'a Yana hawaye"kafin yad'aga hannunsa sama Yana wa ALLAH godiya"
Mlm yyi gyaran murya had'e da cewa Masha ALLAH Alhmdllh lallai kunga rayuwa"ubangiji yabaiyanata aduk inda take yasa tana raye....da ameen suka amsa kafin mlm yafita Dan basu guri...
Riyan kuwa tamkar gunki tayi sbd ganin abun tamkar almara!Wai Abdallah jinintane?"
Yayanta ne! Shiyasa haba take yawan jin tausayinsa dakuma kin mom tunda tagane ba itace mahaifiyar sa ba"sannan inya Mata wulakancin batajin zafinsa ,ga yawan damuwa dashi datayi ,Ashe D'an uwantane... lallai ikon ALLAH beda k'arshe... d'ago kanta tayi ta kallesa saitaga yyi saurin janye idanunsa dg nata...

Shikuwa Abdallah kunyace fal da Dana sani aransa! lallai yaga rayuwa"tabbas Hafiz ya Sha fad'a Masa yadena wulakanta mutum bakasan meyimaka ranaba ,gashi Riyan ta Masa Rana dg k'arshe Kuma Ashe ita d'in jinin sa ce"yayantane"lallai Hafiz bazai tab'a mantawa dashiba"sai yanzun yagano dalilin dayasa mom Bata kaunar Hafiz"
Wato Dan taga Yana fad'a Masa gsky "tabbas bazai manta da AUREN WATA SHIDDA ba !gashi sanadinsa yasan abubuwa da yawa"wad'an da ko a mafarki bai sansuba"inama ace ana maido baya"yadawo da rayuwarsa ta baya "ya gyara kuskuransa...
Sai yanzun ya tuna da tunatarwar malaminsa na addini(a ingila) dayake cewa kuguji k'in Abu"Amma kunemi zabi agun ALLAH"ma'ana in wani Abu yashige maka to Rok'i ubangiji yazaba abinda yafi alkhairi...sbd da yawa abinda kuke k'i,sai yazama alkhairi agareku"abinda kukeso yazama sharri agareku!to gashi yak'i AUREN WATA SHIDDA Ashe shine sanadin warwarewar matsalar sa,fatanshi ALLAH ya bashi lfy yagyara abinda yabata agurin Riyan d'in shi ...wani murmushi yasaki daya tuna irin farin cikin da Hafiz da ammi zasuyi....Amma Wai duk ta Yaya hakan tafarune ?ya akayi kukazo nan Kuma ita hassun tasan Kuna nan??"


D'ago kanta RIYAN tayi ta shiga warwarewa umma komai"sbd abaya akwai abinda ta boye Mata,saidai ko yanzun Bata Fadi aurensu na WATA SHIDDA bane...

Saida umma tasake yin wasu koke koken, sbd tausayinin wannan al'a mari musammun dayaji cewa RIYAN k'anwar Abdallah ce,"
Cikin farin ciki yace gobe my man Ina hanya insha ALLAH dukda wannan watan my feedo take haihuwa,Amma zamuzo tare da ammi insha ALLAH goben..

D'akin Inna mairo umma ta nufa danta kwana,dukda bada niyar kwanan tazoba,jin Abdallah jinintane yasata kwana...
Tabar riyan da Abdallah ad'akinsu Dan su sake ...
Bayan fitar umma Abdallah ya dubi riyan had'e da yin k'asa k'asa da murya yace Mrs Abdallah zoki kamani na kwana pls...cikin ko inkula tace ai mlm ne ke kwantar da Kai ko inyakamaka addua ko"hmm Nike nakeso yau,inkuma bakyayi nasanar da umma bakyajin mgn ta...da sauri ta tashi , cike da tsoro ta nufesa.
Ahankali ta mik'a Masa hannunta yakama ta dagosa dg kan kujerar"kasancewar gasu ga katifar"hakan yasa yyi saurin riketa Gam ajikinsa ,suka fad'a kan tatifar atare"ckin mugun tsoro riyan ke kokarin kwacewa ,amma sai yasaka hannunsa ya gyaramata kwanciya akan faffad'an kirjinsa" cikin murmushi yace matsoraciya anan Zaki kwana yau ,nima naji dumin jikin matata ,Koda yaushe saiki barni Ni daya na kwanta saikace wani gwabro ko" bacin inadake... eh d'in Nika cikani konamaka ihu ALLAH kuwa tafad'a tana son kwacewa dg jikinsa..
Murmushi yyi had'e da cewa so what?" Inkinmun ihun ne"garama ki kwanta Dan bazan cikakiba...sai zille zille take da koke koke,Wanda duk Wanda yagani zai gane shagwaba ce zalla take" hakan Kuma sai ya saka mutumin nata cikin wani yanayi....


Daskarewa Abba yyi agurin,me maganar ta kenufine?"
Ta aikasa lahira inda na mik'a D'ansa"
Zuciyarsa tace....


Share


BY
MMN FAREESA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾



Story & written by
mmn fareesa


Wannan shafin nakune Queen minart & pretty Ina mugun yinku, irin sosai d'in nan🥰🥰


Not edited❌

P 44
.... Zuciyar sa tace kanada wani d'anda ya wuce Abdallah ne!tuni gabansa yyi mummunan faduwa...Amma sai yaita ambaton sunayen ALLAH azuciyarsa"meke Shirin faruwane Dani ?" yatambayi kansa"ita takashe Abdallah Kuma ta keson ganin bayansa"
Dakewa yyi ,yyi sallama had'e da boye damuwarsa da al'ajabin dake cikin ransa"itama amsawa tayi fuska asake"Zama yyi agefenta ,Yana cewa yau bazaiyi dinner ba ,da wuri zai kwanta..
Mik'a tayi had'e da cewa nima da wuri Zan kwanta muje ko"Ina Kenan ?"yatambaye ta sbd ba gu d'aya suke kwanaba ! bed room d'in ka Mana acan Zan kwana..
Kallon ta yyi had'e da hmmm Aida bacan kike kwana ba ,Amma inzaki iya muje Amma fa kisani banida lfy "
Cike da mamaki had'e da zaton ko Suraj ya sanarda shi wani Abu "tace banganeba kamun bayani,kamar ya bakada lfy??"
Tashi tsaye yyi Yana nufar bed room d'in sa Yana cewa ,

Please Login or Register in order to submit comment