Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ

πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†
SANADIN LINK
πŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈ


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```
____________________________________


_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_ πŸ–‹

*Short story*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*



```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA WADDA TA RAINENI TA KULA DANI JINJINA GAREKI MAHAIFIYATA```




Page_1

Kwance take bisa makeken gadonta, tana sanye da ash colour night wear, earpiece ne manne a cikin kunnanta tana jin wakarasu DJ-AB mai taken DA SO SAMU NE, hankalin ta kwance babu abunda yake damunta a rayuwa,chatting take yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da alamu chatting din yayi mata dadi shiyasa hankalinta baki daya ya karkata agun chatting din, Allah sarki Safiya kenan...


"Sofy! Sofy!! Sofy!!!, oho ni Fiddausi wannan wata kalar rayuwace yarinyar nan ta daukarma kanta, ace shi mutun baida aikin da ya wuce jin wakokin sai kuma rige waya aikin kenan ba dare ba rana, ke Sofy wai baki jinane, ta buganmata baya sanna ta juyo cikin firgice da tsoro,"Mami, wallahi Mami kin bani tsoro sosai, bansan kin shigo ba sai kawai naji kin bigeni, "ai dole kice haka Sofy, yanzun sofy abunda kika daukarma kanki kena sabo da Allah, wannan ba hali bane mai kyau,"haba Mami, yanzun ke kullun saboda Allah ni mai laifi ce, baki san ki ganni cikin farin ciki, yanzun Mami maiye aibun chatting? Kuma ni yanzun ba yarinya bace tunda har degree nagama, haba Mami ai ya dace ki duba man mana...


"Sofy, yanzun ni kike gayama haka, to nidai a matsayina na mahaifiyarki ba zan fasa gaya maki gaskiya ba, kuma tun wuri ki dawo cikin haiyacenki wallahi Sofy, haka za'ayi maki auren kina wanann MUMMUNAR DABI'AR, ai in ba shi Aliyun ba, ba wanda zai iya rayuwa da ke, dan haka ki tashi daga wannan dogon baccin naki, ina ma fatan kinyi sallahr isha'i? "Aah daman yanzun nike da niyar tashi nayi sallahr kike shigo, "Innalillahi yau naga ikon Allah ni Fiddausi yar-malan, yanzun Sofy har sai yaushe zaki ringa yin sallah kan lokaci? Ke kullun baki sallah sai nace maki kiyi, kinsan ko karfe nawa yanzun? "Eh duka yanzun karfe 10 fa Mami, kuma ai isha'i har gabannin asuba duk cikin lokacinta ne, "To shikenan tunda haka kika ce, tashi kiyi sallah, salan kuma inkin gama sallahr k ikoma bisa network din...


Allah sarki uwa, Nan fa Sofy ta tashi tana gunguni tashiga toilet tayi alwarla sannan tayi sallah tana gama wa ta tashi, ta cigaba da chatting dinta, kuma bata fasa jin music dinta itace bata sauka online sai 1:00am, sannan ta kwanta, babu adu'ar kwanciya bacci babu komai, itadai kawai tayi kwanciyarta, haka Mami tazo da asuba taita aikin Tara Sofy bacci, Amman taki tashi wai ita abarta ta huta, duka duka yaushe ta kwanta har asuba tayi, Sofy bata tashi tayi sallah ba sai wajen 7:30 sannan ta tashi tayi sallah, tana gama sallah ta tashi ta koma baccin safe, ba ruwanta da aikin gida tunda suna da mai yi masu aiki, ita a cewarta,bata tashi bacci ba har sai 11am sannan Sofy ta samu ta tashi, tayi wanka tasa wasu English wears riga da sicket dinta,sunyi mata kyau sosai, daman Sofy bata harka da manya kaya namu na hausa...


"Mami, ina kwana, "lafiya lau Sofy, an tashi lafiya? "Lafiya lau, Mami mai kukayi mana yau breakfast? "Doya da kwai mana, tashi kije kice ko,"To Mami, yauwa Mami, daman yau Aliyu yace man zai shigo gida ya gaidaki, "To shikenan Allah ya kaimu anjima, ai sai ki shiga kitchen keda Asabe ku samu abunda zaku girka mashi, "haba Mami yanzun harda ni za'ashiga kitchen din? Nidai gaskiya ya kamata Mami ki duba man, "To wallahi Sofy sai kin shiga Kitchen dinna kin ma Aliyu abinci, ba bakon ki bane, ina tunanin saura wata uku a yi bikin ku, in anyi bikini ubawa zai ringa yi maki sauwar? Dole ki shiga kitchen kuwa, "To shikenan Mami, zan shiga yi hakuri..


Bayan Sofy ta gama yin breakfast, ta shirya taje aka yi mata kunshi da kitso, ta biya ta anso dinkinta, sannan ta wuce gida, sallah tayi sannan suka shiga kitchen ita da asabe, suka yi ma Aliyun nata girki mai rai da lafiya, sannan ta shiga wanka tayi kusan 40min tana wanka sannan ta fito, ta fara daukar kwaliya kuma, daya ke Sofy kyawkyawace ta karshe ga fara kuma, ga dara -daren idanu masha Allah, hanci har baka,gashi kuma har gadon baya, kuma Sofy tana son gayu, yar gayuce sosai, bayan ta gama yin make-up, sannan ta dauko atamfarta super hollond mai ratsin ash, dan ta Sofy tana son ash colour sosai, dinki ya hau jikin Sofy Sosai ta kuma murza daurin dan-kwalinta wanda ake yayi yanzun, ta dauko gyalenta pink colour tasa dayake jikin atamfar akwai pink a jiki, sannan ta dauko turare ta fara barinshi a jiki kamar ba gobe, bayan ta gama shirya wa Aliyu yace mata ya iso, nan tasa Idi mai dadi ya kanshi dakin baki, sannan tasa Asabe takaimai kayan matsa baki,sannan Sofy ta wuce gun Mami tace mata ita ta wuce wajen Aliyu..


"Sallama Alaikum, Amincen Allah ya tabbata agareka ya kai ma'abocin murmurshi, wani handsome guy ne naga ya juyo yana yi ma sahibar tashi murmurshi, Aliyu yana da kyau sosai shima fari ne, yana barin suma, sumar ta kwanta tayi lub-lub da ita ga idanu da hanci sai kace shiyayi kanshi tsabar kyau da aji,"Amin wa'alaikum sallama, yake sanadarin rayuwata, bissilmilah mana kizo ki zauna, kinsan dai nayi missing dinki sosai, "To Habibi, nan fa Sofy tazo, ta zauna kujerar dake opposite dinshi tana yi mai murmushinrta Mai tafiya da imani mutum..


"Habity, ki tausayaman, wallahi sonki yana shirin kasheni,baki ji yanda na kosa ba, ji nike kamar na janyo wannan wata ukkun ya dawo kwana 3,habity Allah ya saman sonki, ina yi maki son da koni kaina bansan adadinshi ba, "Habibi kasan nima ina yi maka son da bansan adidinshi ba, sonka yayi man mugun ila, bani fatan abunda zai shiga tsakanin mu, "shsssss, Habity, bani fatan abunda zai shiga tsakanin mu, nidai Habity bani son ina ganin ki always online, wallahi raina na baci kuma ina Kishinki sosai, "Habibi karka sama kanka damuwa, bani chatting da kowa sai kai, nidai kawai kabarni nayi chatting dinna a group, kasan dai inason karanta Novel, shiyasa duk wani group din dai na novel ne nike shigarshi, "To shikenan na yarda Habity, yanzun dai je ki man iso gun Mami naje na gaisheta sai na wuce gida,"haba Habibi tun yanzun? "Sorry Habity wallahi zan biya nayi magana da wani, na taho Abba ya yi man waya karfe shidda naje Company zaniyi magana da wani customer din mu shiyasa, "to Habibi, Allah ya tsareman kai, "Amin Habity, kiyi sauri ina jiranka, "To shikenan...


"Mami kuje ku gaisa to zai wuce, "To gani nan zuwa, bayan Sofy taje tace ma Aliyu ga Mami nan zuwa sun dan Kara fira sannan Mami tazo suka gaisa, sannan Aliyu ya tafi gida...






Jameelah jameey πŸ–‹


Share and comment pls



πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†
SANADIN LINK
πŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈ


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```
____________________________________


_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_ πŸ–‹

*Short story*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*



```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA WADDA TA RAINENI TA KULA DANI JINJINA GAREKI MAHAIFIYATA```




Page_2


Wacece Safiya


Safiya Ibirahim Bello, kenan, sunan Mahaifinta Ibirahim, haifenta dan jahar kano ne, a unguwar hotoro, ya taso cikin kulawa ta uwa da uba, mahaifinshi Alhaji Bello baban dan kasuwa ne a cikin kasuwar kwari, yana da babban shigon atamfofi da shadodi su materials duk wasu kayan sawa India dikasu za'ayi to akwaishi a shagon Alhaji Bello, sunan matarshi Safiya itama yar unguwar hotoro ce a garin kano, Ibirahim yayi makaranta ta arabi da boko, yayi degree din shi a bangaren mass communication a nan BUK kano, ya fara aiki a gidan radion FM kano, sanann shima ya shiga kasuwa suna gudanar da business din babanshi a tare, ya hadu da matarshi Fiddausi a nan cikin unguwarsu, sun kulla soyayya cikin aminci da kaunar juna, Fiddausi tana gama makaranta Secondary aka sa bikini su wata hudu, da yake ita mahaifinta baya barin a wuce makarantar gaba da secondary, anyi biki nagani na fada, inda aka kai Fiddausi dakin mijinta...


Bayan anyi walima kowa ya watsa ya kama gabanshi, nan aka bar Fiddausi daga ita sai halinta, tayi kuka kamar ba gobe, bayan kowa ya kama gabanshi nan ango ya shigo shida abokanshi, bayan anyi budar baki, suka yi masu fatan alkhari kowa yasan inda dare yayi mashi..

Bayan Ibirahim ya dawo daga rakiyar abokanshi ya shigo dakin amaryarshi bayan sunyi sallah raka'a biyu, sun gode ma Allah daya nuna masu wanann lokaci main albarka, yayi mata tambayoyi kamar yanda addini ya tsara sannan suka ci kazar amarcin su,bayan sungama cin kaza Fiddausi tafara shiga wanka sanann Ibirahim, kafin ya fito Fiddausi tuni tagana shirin yawa ta kwanta, shima bayan ya gama shirinyawa ya kwanta asuba tagari...


Washer gari Fiddausi ta daure ta kara gasa jikinta sosai, ta shirya ta shiga kitchen ta hada masu abunda zasuyi breakfast dashi, haka dai rayuwa ta kama ta fiya tsakaninmu Fiddausi da mijinta Ibirahim zama suke cikin kalawar juna...


Soyayya suke main karfin gaske, baka jin junansu koda wani abu ya hadasu tsakaninsu suke sasanta kansu basai sunje gida ba, a kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Allah ya azarta su Fiddausi da karuwar ciki, sunyi farin ciki da murna sun reni cikin sosai, dan harta aiki Fiddausi daina yinshi tayi saboda likita yace sai ta rage yin aiki sosai wanann dalilin ne Ibirahim ya hanata yin aiki, inko Fiddausi tayi aiki to Ibirahim ya tafi wajen aiki, sanann take samu tayi aiki kafin yadawo...



Bayan cikin ya cika watan haihuwa Fiddausi ta haifo shentaleliyar yarinyar ta kyakyauwa da ita, ranar suna yarinyar taci suna SAFIYA amman ana kiranta sa SOFY, tunda Sofy ta taso babanta baya barin ayi mata fada, koda kuwa tayi abunda ba dai-dai ba,, sai yace yarinya ce nan gaba bata yi ba...


Wanann dalilin shine yasa Sofy ta taso cikin shagwaba da gata, duk abunda take so shi ake yi mata ba main ye mata fada shidai Maminta, itama da Dadynta yadawo zata gaya mashi Mami tayi mata fada, nan fa ya ringa yin fada kenan, yana cewa abarma shi yarinyarshi tayi abunda take so a gidan ubanta...


Haka dai rayuwa taciga da tafiya, Hajiya Fiddausi tana ji tana gani amman abu yafi garfinta, bata da ikon hana Sofy yin abu, kuma bata da ikon sata yin abun, da Alhaji Ibirahim yaga matarshi ta matsama yarshi sai yaje wani dan kauye ya dauko yar aiki mai suna Asabe, dan shi baya son ana sa diyarshi aiki main yawa...


Sai da Hajiya Fiddausi tayi da gaske, sannan ta samu Alhaji Ibirahim ya yarda a koya ma Sofy sauwa, daga bayan sauwa bai yarda a Kara koya mata wani abuba, haka dai Hajiya Fiddausi tayi kokarinta gani ta gyara ma diyar tata tarbiyarta amman ina ta MAKARO, amman duk da haka ta dan guard wata...



Haka dai Sofy ta cigaba da rayuwa cikin son da kauna, bata aikin komai sai shiga kitchen, shima kitchen din ba ita daya ba, ita da su Mami, ahak dai har Sofy tayi JSCE, ta shiga secondary school, Sofy bata son san manyan kaya ace warta manya kaya sa zafi garesu a jiki, shiyasa duk inda Alhaji Ibirahim yaje yakan dawo ma da Sofy English wears kala kala..

Bayan ta gama Secondary school,tayi jamb kuma taci dan haka tasamu addimission a BUK kano, kana karanta BCH, wato BIOCHEMISTRY, tana level 3 ta hado da Aliyu ya shigo cikin unguwarsu nan fa suka hadu, Aliyu yasha wuya kafin ya shawo kan Sofy ta soshi, shi kuma Aliyu dan GRA ne, da sannu Aliyu ya tusama Sofy Soyayyarshi a zuciyarta, taji baya son kowa sai shi,suna soyayya main kyau da shi'awa, shi kuma Aliyu ya gama MSC din ya karanta COMPUTER SCIENCE, yana aiki a campany Abbanshi...

Sofy tana son chatting sosai, kullun tana online, bata da aiki sai chatting, duk LINK din da ta gani ana talla sai ta shiga, amman bata shiga kowa ne inba group na novel ba, tana karanta novel sosai, saboda yawan karatun novel, Sofy bata sallah kan lokaci, har sai Mami tayi magana sannan take tashi, indan kuma ta gayama Alhaji sai yace ai yarinya ce nan gaba komai zata daina, sai dai Mami tayi shiru, tana yima mijin nata adu'a Allah ya nuna mai gaskiya, sanann wannan duk ba gata bane yake nuna ma Sofy ba, domin yana bata mata rayuwa...



Sofy nagama university a kasa ranar bikinta da Aliyu wata shidda, saboda Alhaji Ibirahim zaiyi wani course na wata biyar, shiyasa aka bikini wata shidda, sai ya dawo daga SUDAN , sannan za'ayi bikin su..





CIGABAN LABARIN




Jameelah jameey πŸ–‹







Share and comment pls


πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†
SANADIN LINK
πŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈ


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```
____________________________________


_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_ πŸ–‹

*Short story*



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*



```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA WADDA TA RAINENI TA KULA DANI JINJINA GAREKI MAHAIFIYATA```





Page_5-6









"Mami ni zan shiga daki, sai da safe, "To shikenan Sofy, dan Allah karda ki kai sha biyu a kan network din nan, "To Mami, byeee, tunda Sofy ta shiga room dinta, ta fada toilet tayi wanka tayi shirin bacci, as usual dai ta dauko wasu night wears dinta suma ash, amman masu gajeren wando tasa, sannan ta hau kan bed dinta, ta dauko wayarta ta fara chatting da kawayenta na wani group mai suna HAUSA NOVEL ONLY, suna ta yin SHIRHIN NOVEL DIN NANA JAWAHEER, na marabuciyarnan mai suna jameelah jameey, suna ta yaba NOVEL din suna cewa yayi dadi sosai, kawai sai wata daga cikin members din group , ta turo wani LINK MAI SUNA HAUSA NOVEL MATA ZALLAH, nan fa Sofy ba tare da tayi tunani ba kawai tayi joining din group din, bayan tayi joining admin din group din ta fara magana kamar haka..


"Sannunku yan group din nan, baki da wanda suka jima a cikin group, muna san kowace bakuwa tayi introduction din kanta amman fa ta voice note, dan mugane da gaske mata kawai suka yi joining, sannan kuma sai kowace ta turo mana hotonta duk dan mukara tabbatarwa da natane suka yi joining banda maza...



Nan fa suka kama yin introduction kamar yanda ta bukata, duk wanda tayi sai tayi posting din hotonta, nan ma Sofy tayi itama ta turo wani hotonta, tayi bala'in kyau sai kace ba yar Nigeria ba, sai ayi tunanin yar makka ce tsabar kyaun da tayi, bayan sun gama introduction din kansu, nan fa admin ta fara gaya masu ROLE AND REGULATIONS din group din..



"Duk wanda tasan tana cikin group din nan dole tabi abunda group ya tsara, sannnan inka shigo group din nan ka shigo kenan ba fita, dan haka wannan group din ba na NOVEL bane...


Nan Sofy tace "bata gane group ba na novel bane inba na novel bane na maiye? "Eh bana NOVEL bane, group din yan LESBIAN NE, kuma ko kina yi ko baki yi ya zaman dole kiyi shi, ko kiyi shi cikin kwanciyar hankalina, ko kuma mubuyo maku ta wata hanya, duk wanda kuka gani cikin group din nan to rabinsu LINK suka shigo....


"Amman mai yasa kuka sama sunan group din HAUSA NOVEL? "Ha haha haha, yarinya kenan, Safiya ko ana kiranki da Sofy, gaskiya Sofy kinyi man, ina sonki sosai, naji dadin shigowarki group din nan, domin ko ba komai zamu amfana da juna..


"Dalilin da muka sama group din HAUSA NOVEL, saboda kallarku masu son karatun NOVEL, in dai kana son group dinka ya cika har ba waje to kayi mashi suna da HAUSA NOVEL, to zaka ga ana shigo ba Kama hannun Yaro, saboda yanmatan yanzun suna karanta novel sosai, ke harda Mayan aure da zawarawa, shiyasa na bude group da wannan sunan,amman a badili ba haka yake ba..



"To nidai, fita zanyi ba zan iya zama a cikin wanann group din ba!!!



"Ke yarinya dakata kiji, ko kin manta gidan nan ba'ayi mana gardama, dan haka ki bini a hankali domin ko bani da IMANI ko kadan,koni kai na bansan iyakar Ada din matan da na lalatama rayuwa ba...


"Dan haka kinyi man, kuma ya zama dole na dandani zumanki yarinya, kinsa a banza nace duk ku turoman hotonan ku? Dan haka ki bani hadin kai cikin saukin rai, a hankali zaki saba kema da kanki zaki nemi mai dabemaki kewa..


Nan fa fada ya kaure tsakaninmu yan group dasu Sofy, kuma sunyi sunyi suyi left a group din, amman yaki fitowa, ba arziki Sofy ta sauka online tun 11:00pm abunda bata yin a rayuwata, inta sauka da wuri to shine ta sauka 12:30,amman yau da yake ta shiga cikin tashin hankali shi yasa ta sauka tun 11 sannan ta kasa yin bacci tana shawar ko ta ga yama Habibinta halin take, amman Kash Sofy ta MAKARO, tunda har tayi joining din group din..



Haka dai Sofy ta kasa bacci tana ta yin tunani, daga karshe ta tuna bama tayi sallah ba, ta tashi tayi sallah, nan tayi dan adu'oi first in history da Sofy tayi sallah ta tsaya yin adu'a, sanann ta samu ta kwanta bacci...









By jameelah jameey πŸ–‹


Share and comment pls



πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†
SANADIN LINK
πŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈπŸ™†β€β™€οΈ


*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»```
____________________________________


_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey_ πŸ–‹

*Short story*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*



```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA MAHAIFIYATA WADDA TA RAINENI TA KULA DANI JINJINA GAREKI MAHAIFIYATA```







Page_7-8






Tunda gari waye Sofy ta tashi daga bacci, tayi sallah, as usual wanka tayi, ta shirya sannan ta fito ta tadda Mami a kitchen suna hada breakfast, nan fa tashiga ta taya Mami aiki sannan suka yi breakfast, koma room dinta ta bude data, tana hawa online taga wata number tayi mata magana ta PC...



"Hy, masoyiya ta, fatan kin tashi Lafiya? Sunana Hajiya Zulai Amman anfi kirana da zuly baby, naso jiya muyi magana amman sai ki kagudu kin banni da kewarki da tunaninki....



"Dan Allah can Malama karki sake yiman magana, inks yar'iska ce, to ni ba yar'iska bace kinji dai na gaya maka, Sofy take cema Zuly baby ta voice..




"Wooow, nice voice inasan ki ringa yi man magana da muryan nan taki mai zakin sarewa, kinsan jiya kafin nayi bacci sai da nasake jin muryanki, kafin nayi bacci yanzun kuma ga ta breakfast nan kin turoman...



"DlAllah can yi man shiru, banza kazama marar mutunci, in ba kina

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment