Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hidima a gidan hidima sannan kuma
matar mai hidima, farin cikin mai hidima, zuciya hasken
annurin mai hidima, zakanya saidai aganki anesa badai a
matso kusa ba,” Wani irin murmushi da dariya falmata tayi
cikin jin dadi, ta daga giranta sama sannan tace “kinga na
kashe da’ saura uwarsa sannan uban gayyan uban gidan,
yusuf[truncated by WhatsApp]

HALACCON SARAUTA 32
 benaxir  October 26, 2015  Hausa Novels
 145 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR jakadiya
tana rusune harta mike ta fice. Bawanda yakai falmata
farin ciki aranan saboda tana ganin wanda zai tare mata
sarautar danta yafadi kasa yamutu, shehu kuwa baiyi
hankalin dazata sashi a sahun masu karban sarautan ba.
Donhaka tuni tafara tunanin hanyan dashi kanshi sarkin zai
mutu, babu tsoron Allah babu tunanin lahira, tunaninta
shine takashe duk wanda tasan zaishiga tsakaninta da
mulkin garin, Sai dare sannan aliya tafarka atake sufyan ya
tallabota yadawo da ita gida yana ganin inna baikulataba
yashige da aliya ciki, saida yatabbatar takwanta ya rufo
kofan sannan yafito inna tana tsaye tana jira yafito,
baikulata ba tana kiransa, inba don babu gun da zaikai
aliya ba da gidan nata saisu tattara subar mata shi, Cikin
dare aliya tayita firgit tana wasu mafarkai, dolenta
tamike,alwala tadauro tafara sallah har asuba tana yiwa
abdullahi addua, tausayin matanshi da abunda zasu haifa
yacikata, Dasafe sufyan nazaune wayansa tayi kara
alh.hamidu ne yake cemasa yazo suna jiransa, baiyi
bacciba tsabar yana tunanin hanyan dazsi bullowa
maganan, motansa yaja yafice gydan alh.hamidu yanufa
suna zaune a tsakar gydan suna jiranshi, sun gaysa
yabasu girmansu sannan yazauna, inda hussieni yake
tambayansa alkawarinsa, sufyan yayi murmushi sannan
yace “komi zaizama naka idan kabani tarihin yadda akayi
ka kashe mahaifina!” Ba hussieni ba har alh.hamidu saida
yabude baki don mamaki,hussieni yagagara cewa
komi,hakan yakara tunzura sufyan, hawaye ne suka fara
zubo mishi yafara magana cikin sanyin jiki “Ashe karshen
duniya zatazo dahar danuwa zaisa hannu yakashe
danuwansa saboda dukiya?saboda mulki?” Bawanda ya
amsa mishi kaman tsoffin barayi da aka kamasu hussieni
kanshi akasa yafara magana “kai mahaifinka ne. Nikuma
danuwana , wlh tlh ba abunda nashirya yafaru ba kenan,
Allah dai yayi zanzama sanadi, tabbas munyi musu da shi
batun mulki anma ban kwallafa raina ba. Nasan na umurta
da amai dukka anma bance sukasheshi ba, bankuma ce
suhada da mahaifiyarka ba. Allah yayine lokaci yayi don
Allah kayi hakuri, karkuma kabari kanwarka taji alokacin
sufyan yayi kukan zuci daya tuna da iyayensa anma tuni ya
watsake saboda ayanzu zucuyarsa tabushe yana tunanun
daukar fansa, recordern dayake recordn yasawa stop
sannan yamike yafice batare da ya ce musu komi ba dama
yakira lawyernsa awaya tuni yadamka masa shaidansa
tareda basa go ahead nashigar da kara kotu, koba komi
yanzu yaji sanyi aransa Aliya kuwa tacanja gabadaya ba
abinci sai ruwan lipton, sufyan yayi lallamin harya gaji
yusuf ma yayi nass Bayan sati biyu alokacin anwatse a gun
rasuwa. Sannan alh.hamidu da alh.hussieni sun shiga kotu
inda zaa fara sauraren karansu Aliya tadan sake, yanzu
hankalinta ya kwanta maganan rama mutuwan iyayenta
anmma abunda yafi bata ciwo shine danuwan mahaifinta
shi yakashe mahaifinta. Abunda ciwo,saidai yanzu tabar
komi agun Allah har lokacin sufyan baya magana da inna ,
aliya tayi iya kokarinta anma yafaskara yusuf na iya
kokarinsa ganin ya farantawa aliya yayinda soyayya mai
karfi tashiga tsakaninsu, tuni yafara maganan aurenta
yasamu falmata da zance atake tace batasan zance ba,
nan yakoma kan yakolo ta yadda takuma sa albarka inda
anan yasako waziri da sarki, dafarko waziri yaki amincewa
acewarsa dole yusuf yadauko yarinya mai asali, nan fa
yusuf yazayyana masa rayuwar aliya tundaga farko
dakuma wahalhalun datasha waziri yayi mamaki sarai
anma yace zai gwada tunkarar sarki, sarki yanajin magana
yatambayi wacece atake waxiri yace yar marigayi
galadima,sarki yaji dadi sosai tuni yafara murna, wannan
yarinyan ai ita keda asali, nan waziri yace “anma akwai
matsala mai martaba, yarinyan tashin hannun mace tayi
dakuma tashin gari” Sarkin yayi shiru don tantance me
wazirin ke nufi donhaka yace “yi bincike mai tsanani
muji”dahaka waziri yabar maganan, falmata taji labarin
abunda ke faruwa donhaka ta nufi sarki da maganan anma
yanuna mata shi ba ruwansa,don shikanshi yanaso yusuf
yayi aure, baitaba tsammani kuma yusuf zaikawo yarinya
yace yanaso ba donhaka tuni tarikice duk tana tunanin
hanyoyin dazata hanashi wanda shi yusuf har daina zuwa
gaysheta yayi tsabar yasan kalan mitanta, Aliya kuwa
tasan bakaramin rikici bane zai afku donhaka tuni tafara
lura da takunta, ga masu nufinta da sharri, ita anata taso ta
tattara tabar garin bata da dsmuwa da gun anma dole
tajira a idar da case din iyayenta a kotu, Waziri yayi iya
bincikenansa akan aliya tuni yakira yusuf “Kana sane da
tayi bauta agydannan?” “Tayine alokacin batasan kowa ba”
“Kasan dai yanayin rayuwarta bai shiga danaka ba”
“Nasani shiyasa nake rokonka daka sa baki, kaikadai ne
inka yabeta sarki zsi yadda, don Allah kataimaka” “Zan yi
iya kokarina, anma kai kasan halin mahaifiyarka”
Dawannan suka rabu inda yaje yagabatar da zancen da
duk wani tarihin aliya agaban sarki, sarki yadannan
approve makake, nima dai benaxir na dannan approve duk
da munsan amincewan mezai jawo, ansa rayuwar aliya
cikin hatsari da damuwa, anma munsan cewa aliya ce
kadai zata iya gyrawa falmata duwawun zama, muje zuwa
gobe[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 33
 benaxir  October 27, 2015  Hausa Novels
 106 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR falmata
kashe kanta ne batayiba domin amincewar da sarki yayi, ta
tura duk wanda take ganin zai iya magana wa sarki anma
taci tura, waliyyim aliya shine alh.hussieni anma sufyan
yayi kif da ido akan bai san zance ba, dole akarshe aka
bukaci alh.hamidu yazama waliyyi, duk soyayyan
dayakewa hassana yayine domin yasamu hankakinta anma
daga karshe yaga sone na gaskiya , hussiena ma tasha
alwashin zaman lafiya kam aliya da yusuf bazasu
sameshiba agydan Anyi zama a kotu inda lawyernsu
sufyan yaci karan, kotu tabawa alh.hussieni zaman prison
na shekara ashirin da daya sannan ta bukaci daya fidda
gadonsu ko kuma kotu taci tararsa, a ranan aliya tayi
kukan farim ciki tunda take bata tabajin kwanciyan hankali
irinna ranan ba, jitayi kaman ansauke mata dutsen badr
akirjinta, tuni ta maida hankalinta kan batun aurenta duk da
tasan tashin hankalin dazata shiga, antyn abuja ne ta
bukaci taje don su samu ayi siyayyanta, ta tattara dan
komatsanta duk da yusuf bai so ba, shi yanzu babban
damuwansa yaga ya aureta, Sunyi sallama tatafi yayinda
yakoma fada, shigansa yatarar da bilkisu da abincinsa,
zama yayi yarike kai yana tunani kansa yamasa nauyi har
yanzu falmata taki yarda da auren, yasan son zuciyanta ne
anata tunanin wai saidai ya auri hussiena, shi haryau
hussiena bata kwanta masa arai ba , bilkisu ce tayi tari
hakan yadawo dashi daga tunaninsa yakalleta sannan yace
“meke faruwa acikin gyda gameda aurena” kanta a kasa
tace “Gimbiya yakolo tafara shiri, yayinda gimbiya falmata
bata fara ba, ita shirinta da hussiena takeyi” Baice komi ba
yatashi yafice sannan yanufi fannin falmata anma sa iso
sannan yashiga daga ciki tana zaune akan kujera yazauna
akasa abinda bayayi, hakan yatabbatar mata da bukata
yazo dashi, bata kulashiba yasa kanshi akasa sannan yace
“Ina neman amincewarki na auren aliya” “Ban bayarba,
kuma ko bayan raina ban sa baki ba” “Inaso kibani hujjanki
wanda addini ta haramta min auren aliya” “Yar kan titi!!
Yarinya tagama gantalinta agari! Kowani dan iska ya
kwasa! Kainan tayi fitsari tabaka kasha ba dole kabiya
kaman agwagwa ba!” Ga mamakinta taga yamike yafice ,
baikuma cewa komiba, tunda shi mahaifinsa yasa albarka
hujjanta ba kwakkwara bane dazatace masa kar ya auri
aliya, fannin yakolo yaje, yasami hauwa tana ganinsa tafice
don haryanzu tsoronsa takeji, yakolo tayi murmushi tareda
masa iso, bayan karasowarsa yazauna dum a kasa, nan da
nan tagano alfarma yazo nema, yagaysheta ta amsa masa
sannan yace “Naje gun gimbiya na nemi ta amince min
auren aliya taki yarda, kuma hujjojinta ba ingantattu bane,
kitaimaka ko zakisa baki” “Bakomi yusuf, kasan mahaifinka
inta sa rai akan abu, kai yakamata ka lallabata anma zan
gwada kokarina kaji” “Nagodr Allah yasaka da alheri”
Ficewa tayi, tuni abdullahinta ya fado mata arai, tasan
yarinyar dayakeso aketa rikici akai, gashi cikin mata yafara
fitowa duk da sunriketa tana fadan akan saita haihu tukun
zasu barta tafita, Yakolo tayi iya kokarinta don fahimtar da
falmata anma falmata kaman ana zuba mata man fetur,
dahaka biki ya matso kusa aliya tadawo gari saidai
tagagara zama, rokon yusuf tayi akan ko zai taimaka
yabata aron bilkisu, haka kuwa akayi , tuni bilki tafara
taimaka mata, jin aliya zata auri dan sarki tuni dangin nesa
da wanda aka manta dasu suka fara bayyana kowa
saiyace yazo auren marainiyan Allah, Ran jumaa aka daura
auren aliya da yusuf, inda akayi dinner daredare nagani
nafada, munsha gwaggori munsha rawa,yusuf na makale
da matarsa, hannunsa gam anata shi yanzu gani yake duk
duniya bawanda yakaishi hakuri da juriyan dayayi, angama
dinner inda aka kai amarya fanninta side guda aka ware
mata a fada, dakuna uku da falo biyu,tabbas tasamu kaya
tasha gata, sufyan yashare mata hawaye tayi kukan rashin
iyaye anma batayi maraici ba, kowa yayi mamakin ganin
yadda falmata tasake ranta da maganan biki, harwani jan
aliya take ajiki, acewarta komi yawuce,anma aliya tagagara
sakewa da ita, randa aka kaita an watse aliya tana kunshe
jikin gyalen kyabban da aka rufata dashi duk ta kagu tana
jiran angon nata,don tsoro takeji dakin ya mata girma
sosai, kukan kare tafaraji, dafarko bai dametaba anma
datayi tunanin gydan babu inda aka ajiye kare, tuni tafara
tsorata kodai yusuf yasiya ya ajiye a fanninta ne? Toh
anma matsalanta shine jin kukan take kaman agabanta
yakeyi, hannunta ne yafara bari tafara salati da dan karfi
sannan taji shiru, can kuma takarajin kukan karen daga
nesa saikuma karan kofa, saura kadan tasake fitsari
awandonta taji anbude kofan, yusuf ne batasan lokacin
data rungumoshiba, jikinta na bari jinhaka yasa shima ya
kamata, sunfi mintoti ahaka kafin yajawota yazaunar da ita
akan lallausan gadon, “leeya meya sameki?” Bata bashi
amsaba, tafarajin wani kukan karen wannan karon harda
kulya, salati takeyi jikinta na bari, tuni jikinsa yayi sanyi
domin bata cikin hayyacinta, alwala yadauro yace itama
tayi anma dole saida yarakata toilet din don tsoron
datakeji. Tafito yajasu sallah yakamo kanta yatofa mata
addua, sannan yafara tambayanta akan littafai daga kan
fiqhu, hadiths da dan tauhid, yayi mamaki sosai dayaga
tanada sani, baitaba zaton tasani sosaiba, daganan ne yace
“mezakici?” “Babu kabarshi” Cire mata kallabin yayi,
sannan yarikota naman ya yaga kadan yafara bata tana
tauna ahankali yabata da soya milk haka taci takoshi
sannan yace tadan kwanta, tana kwanciya taji kukan karen
zumbur tamike kaman an tsira mata allura, rikota yayi yana
tofa mata addua, atakaice haka suka kwana a zaune har
asuba, dazaran zata kwanta sai kukan kare ko qulya,
asuba nayi sukaji shiru, hakan yabashi daman fita
masallaci, tana sallah bata fitoba saboda baccin daya
kwasheta, karfe shida daidai saiga umma uwar tsoro
falmata ta turota buga mata kofan tayi can dai tabude, bata
tasheta ba ta nufi kan gadon taja bedshit din tafice, kaiwa
falmata tayi wanda tana zaune tana jira ganin babu komi
akan bedshit din yasa ta salati, tana cewa “saida na
gayawa yusuf wannan yarinyan tagama gantalinta, yaki
yarda, kue kudauko min ita,” Dauko aliya cak akayi aka
wurgata akasa. Jiri ne yake dibanta anma tuni ta warsake
don ruwan sanyi tas falmata tasa aka watsa mata, alokacin
yakolo tazo ranta yayi mummunan baci, inba raina darajan
dan adam ba yazaayi matar danki dan cikinki zakina
wulakantawa? Tuni fa gyda ya hargitse, nima benaxiratu
idona na rufewa anma dole nabude[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 34,35
 benaxir  October 29, 2015  Hausa Novels
 110 Views
[10/29, 7:11 PM] Adda Bena: [10/29, 6:45 PM] Adda Bena:
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya bata
iya daga kai ba, tarasa meyake mata dadi, ayayinda
falmata da yakolo ke magana, anma falmata tayi kif da ido
tareda “cewa tunda ba danki bane saikiyi hakuri” yakolo
taji zafin kalman dakinta takoma don abun yafi karfinta,
Yusuf nafitowa daga masallaci yaga shehu wanda yayi latti,
donsai alokacin zaishiga masalaccin [10/29, 7:10 PM]
Adda Bena: Ganin yusuf yasa ya tarbesa tareda cewa “kayi
sauri kashiga ciki kaga ikon Allah hakan yasa yadada sauri
jikinshi nabashi wani abu yafaru ne,aikuwa idonsa kan
aliya yayi tana zaune a kasa , Allah sarki marainiyar Allah
dasauri yaje yadauketa falmata nakiranshi bai kulataba
fanninsu yanufa da aliya daki yakaita yaga babu bedshit
nan da nan yagane me akayi mata ajiyeta yayi yaje
yadauko kettle yahada mata ruwan zafi sannan yace “tashi
kishiga,” da taimakonsa tashiga bandakin tarufo, jin ta
dade baikuma ji motsin ruwa ba yasa yabude bandakin
tana zaune acikin bathtub din tana kuka, tausayinsa
yakamata bata rai yayi sannan yace “zanmiki wankan”
kallonshi tayi adan tsorace anma bai kulata ba, yarufo
bayan gidan yakamota, tagara yimasa gaddama, haka
yacire kayan yakunna showern kunya duk yarufeta,
tagagara motsi haka yacudeta kaman jaririya sannan
yadaukota ya ajiye, ya shafa mata mai yaciro mata kaya
marar nauyi wani dogon riga ne haka, daya ciro yasamata,
yahada mata tea a falo yazo yazauna ya lallabata tasha,
itakam sai ganin ikon Allah take, mutumin datake masa
kallon soko yau gashi soko na aikinsa,saida ya tabbatar
batada matsala sannan yashiga yadau wanka, yafito fannin
bayi yanufa, yasa akira masa wanda suka dauki aliya ,
sannan yafara fada akan me zasu taba mishi matarsa
nemo dogarai yayi yasa aka basu jikinsu, saidaya tabbatar
kowacce taji jiki sannan yanufi fannin yakolo yagaysheta
anan tadada basa hakuri yanuna bakomi , yanufi gun
falmata wacce tacika fam tana jiransa, zuwansa tafara
masa fada akan me zai hukunta bayi sannan yafara gayda
kishiyanta kafin ita, tunda tafara magana baice mata uffan
ba harta gama,hakan yakara tunzurata tuni ta kullace aliya
aranta, gani takeyi ta mallaka mata da, fitowarsa yanufi gun
mahaifinsa suka fara gaysawa, kafin yakoma fanninsa, tare
suka wuni har dare alokacin aliya tafarajin wannan kukan
kuma, tuni tafara tsorata [10/29, 7:39 PM] Adda Bena:
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR haka suka
kara zama adaren basu runtsa ba, tuni aliya tafede rashin
bacci yafara takurata. Ga ciwon kai ita saitana jinta asama
itabaa kasa ba, baa sama ba, kaman jira kaman ana yawo
da ita, Ga rashin kwanciyan hankali haka suka jera sati
ahaka bata bacci daredare dasafe kuma inta kwanta
saitahau mafarki,ganin abun banayi bane yasa yusuf yakira
sufyan suka gayamasa abunda yafaru tunda yake baitaba
shiga tashin hankalin ba, nan yafara dana sanin amince
mata ta auri yusuf, bai kawo kowa aransa ba anma yasan
akwai wanda basuson aliya da yusuf, akwai wani malamin
da sufyan yasani donhaka ya umurci yusuf da aliya suje
gunshi, Babban malami ne yanada almajirai nan yusuf
yabukaci ganinsa, aka musu iso a zaure, malamin yashigo ,
aliya sanye takeda babban gyale yarufe fuskanta hannunta
ne kawai awaje, malamin nazama, yace “subhanallah, ciro
abun hannunki” dasauri tafara ciro zobunan, yace “a a. Na
azurfan” cirowa tayi tamika masa, yakarba dasauri ya kira
almajiri daya yamika masa sannan yace yaje ya sa awuta,
sannan yajuyo yakalli aliya tareda cewa “baiwar Allah
kinata yawo da tsafi ajikinki, ai kurwanki ake yawo dashi
asama, ” tuni jikinta yafara bari, yusuf yakalleta tareda
cewa “waya baki zoben?” “Acikin kayan aurena nagani”
baice komi ba inda malamin yace sutafi meke tafe dasu,
tamishi bayani zalla zallah Yace “dafarko jirin dakikeji
wannan zoben ne, shiyake jawo haka yawo ake da
kurwanki asama,, nabiyu kuma asiri ne akamaki mai suna
janduks, shi wannan sihiri anayine wa mutum inda mutum
zaisa ranshi a tsaka,” daga yusuf har aliya gyra zama
sukayi don kowannensu yagama tsorata jikinsu na bari,
musamman aliya, duk dabarun sihiri data karanta bata
karanto dawannan ba, “Sihiri ne akewa mutum na kwana
ashirin, dafarko akan dauki hoton mutum kowani abu
dakika mallaka a yi amfani dashi, sannan wannan sihiri
shine zakina jin kukan dabobbin dakikafi tsoro, inkin
kwanta kuma zakina mafarkin kura, shiwannan kura zaina
binki ne,har kwana ashirin idan kuran ta yakeki zaki mutu
acikin kwana ashirin, idan kuma ke kika yaketa zata koma
kan wnda yayi sihirin, kinada wani tabo ajikinki dakika
samu a mafarkin?” Ta gyada kai tareda cewa “kuran
danake mafarkinsa kullum inna tashi sainaga cizon ajikina
yayi baki”. Yace “haka sihirin take, yanzu zanbaki dabarun
karyawa, inbaki karyaba zaki iya rasa ranki Allah ya
sauwaka” aliya da yusuf jikinsu na bari sukace to inda yaci
gaba da bayani yana cewa “Akofar dakinki ko kuma tsakar
gydanki kinemi rami akwai inda aka birne laya kiduba, dole
sai an birne laya medauke dasunan wanda akeso ya mutu
din, kinemo acire, sannan inzakiyi bacci kikaranta yasin,
fatiha, falaq, nas, da suratul jinni, kikaranta kikwanta zakiyi
mafarki anma zakisamu karfin yakanta, donhaka kisamu ki
kashe wannan kuran hakan kadai zaisa kizauna lafiya,
sannan dalilin ganin wannan kuran wanda yayi asirin
kowani dare yana kona laya da takarda me dauke da
sunanki donhaka saiki dage da addua wani lokacin mune
bama nemawa kanmu tsari, munsan sihiri nakama mutum
anma zamu iya karyawa,ki kasance kina bacci da alwala, ki
kasance kin rike hisnul muslim,ki guji zama cikin najasa,
Allah yana taimakawa wanda ya taimakawa kansa ne”
Sunmasa godiya sosai sannan suka mike sukafito dakyar
aliya take tafiya jin ance kwana ashirin, acikin kwana
ashirin taci bakwai, ashe dama haka abdullahi yaji daya
bata kodanta yasan zai iya mutuwa kowani lokaci, ashe
haka yaji? Innalilah kuka tafarayi yusuf harya tukata gyda.
Sannan yafara lallabinta, dakyar tashanye kukan tafito
bilkisu takira tareda cewa tanemo dogarai, suna isowa
tafito itama tace sufara tone gun duk inda sukaga laya
kowani abu na alajabi su kawo, tana tsaye akansu tana jira
nima benaxiratu nadau gatari daya nafara dube du[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA (THE END)
 benaxir  November 1, 2015
 Hausa Novels  126 Views
[11/1, 7:04 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR (First of all, m sooo sorry kunjini shiru
kwana biyu nd i couldnt explain myself, y’all should find a
place in ur hrts to forgive me,bikin one of my closest frnds
nayi. Sunyi kokarinsu don ganin sunsamu laya kowani abu
makamancin haka don samun babban kyauta kamar yadda
aliya tamusu alkawari, basu sami komi ba haka suka
hakura har dare ana abu daya, aliya duk tashiga damuwa
da tashin hankali, anki abarta tahuta da mijinta ankuma ki
abarta tazauna lafiya, Daredare takaranta surorin kamar
yadda akace tayi takwanta zuciyanta cike da son kama
kowacece, acan tafarajin kukan kulya da kare nan da nan
tafara Allahumma ajirni fi musibati waakrijhi khailriha,
tanayi tana hadawa da auxubillah, ahaka tazauna yusuf na
gefenta yana tayata addua yagagara bacci duk da taso yayi
anma yaki, hakan yasa suka zauna suna ta addua ahaka
har asuba, asuba nayi yafice masallaci itama tayi sallolinta
sannan tawuce kan gado , tana addua harta jira bacci ya
kwasheta Tayi dan mafarkan Allah kuma yabata nasara ta
jiwa kuran ciwo, itama ta ji ciwo bata tashiba sai karfe
daya. Inda tayiwa yusuf bayani yace tacigaba dahaka har
na sati kamar yadda malamin yace zata kashe kuran inhar
tana kokarin fada dashi, [11/1, 7:35 PM] Adda Bena:
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR kullum tana fada
dashi kuran yadawo baida ishashen karfi, aranan tafito
tana son zuwa fannin yakolo ko zasu gaysa, wani bakin
abu tagani rana ya hasko mata, harta wuce takoma
tadauka ga mamakinta laya ne, hannunta na bari tadauka
tana addua, harta isa dakinta tana isa tanemi babban
container tazuba sannan tarufe, wayanta tadauka takira
yusuf yana dauka muryanta na rawa tace “kayi sauri kazo
gyda, don Allah kayi sauri” yadda yaji magananta tuni ya
tsure dama yashiga kasuwa ne babu shiri yadawo fada,
tana zaune a falo yashigo anan tanuna masa shima ya
mugun tsorata anma dole yadanne nasa don karta rude,
wurin malamin suka nufa dashi, yadauki layan sannan yace
tayi addua ta tofa ajikinta ta kona layan agun, aikuwa tana
haka yace toh yanzu saura takarasa nakasa kuran inhar
tayi haka toh ba tabbas wacce tamata wannan sihirin,
asiranta zai tonu dahaka sukayi sallama dashi. Sunkoma
gida sukaga fannin falmata a cike arude yusuf yashige
aliya na biye dashi abayanta, falmata ce adaki tana kwance
sai kuyangu akanta, dakuma yakolo su umma uwar soro,
mutane dayawa dai haka, hankalinshi tuni yafara tashi,
yaleka ta dakyau ga mamakinsa ganinta yayi kaman ba
itaba, kamanninta duk yacanja, tacanja wasu manyan
kuraje ne suka fito mata, ga doyi kuma, kowa hannu na
hanci tuni yakai nashi hannun , anan akace kowa ya watse
aka barsu kadai adakin umma uwar soro tace takai awa
daya ahaka, don tunda jakadiya tazo tamusu bayani akan
falmata nakwance kawai saiga kurajen sunfara fitowa abun
kuma bai tsayaba, shiru yayi zuciyarsa na masa zargi,
anma duk dahaka yazauna, duk iya kokarin da akayi
dawasu likitoti abu yaki tafiya wari yaki tsayawa, falmata
acikin dakikai kadan tadawo abun tausayi, wanda hakan
tuni yafara yawo a fada, falmata tayi sihiri yadawo kanta
acewarsu kenan, kowa sai Allah kara yake, dama ta addabi
kowa acikin fadan, kowa yanata farinciki, yayan cikinta ne
kawai suke kukan abun, suma ni benaxir na tabbata don ita
tahaifesu shiyasa, inbahaka ba babu yadda zaayi suji
haushin abunda yake samunta, yusuf dai zama yayi
agefenta yana kallonta yarasa ma yazaiyi sannan kuma
mezaice mata, [11/1, 8:01 PM] Adda Bena: HALACCIN
SARAUTA NA BENAXIR OMAR dahaka tana kallonshi tana
zubda hawaye, aliya ma tana daga gefe tayi tagumi duk
tsanar falmata datayi yaukuma tausayinta taji, tamike
tadauko ruwa sannan tabata, tana jingine a kujera, tana
kallon aliya yusuf ma nagefe, Wani abun mamaki shine tun
ranan aliya tadena jin kukan kare da kulya, sannan tafara
baccinta abun ya matukar bata mamaki hamdallah
tarinkayi wa Allah tana godiya, tayi salollinta, Falmata
ankaita asibiti anma sunbada shawaran ayi maganin gida
nan da nan aka nemo mai maganin gargajiya, yusuf kuwa
yahado da wannan malamin bayan dan magana dasukayi
sai malamin yace mishi tabbas itace, yusuf jikinshi yayi
sanyi donhaka dakyar yakira aliya malamin itama yamata
bayani kuka tayi sosai jikinta yayi sanyi, tanata tunani
duniyan shinawa yake? Da girmanka da mutuncinka zaka
nemi gun boka , me boka zaimaka wanda Allah baimaka
ba? Mezaka tanadar wa kanka agun boka? Daya wuci
wulakanci da dizgi, duniyar kanta nawa take da mutum zai
sa rayuwarshi ta kaskance, ta zama wulakantacce, Takoma
gun falmata anma bata canja mata fuska ba, tacigaba da
zama tana jinyarta da bayin dasukenan, Wannan hali na
aliya yasaka falmata jin kunya, taji inama tunfarko bata
kullaceta ba, bata mata asiriba, sannan bata musguna
mata ba, tana kuka taroki gafaran aliya takuma nuna
nadamarta a fili, aliya tanuna mata bakomi hakan yasa
tacire komi aranta, mijinta kuwa tuni tasamu kanshi duk da
dafarko yana fushi da halin mahaifiyarsa aliya tayi iya
kokarinta ta gwada masa muhimmancin mahaifiyarsa
dakuma hatsarin fushi da ita, tabbas yayi alfahari da aliya
domin kuwa tazamto masa garkuwa, itace macen da
annabi yace a aura wacce zata gyra maka yayinda kashiga
hatsari wacce zata zamo maka garkuwa,yana alfahari da
aliya yana kuma tausayinta a matsayin marainiya, Falmata
ahankali tafara samun sauki da yusuf yahado malamai
anata addua da saukan qurani, domin sarkin yayi tashi
harya gaji, Allah cikin ikonsa tasamu sauki duniya takoya
mata hankali ta nutsu tazama mutumiyar arziki domin
kuwa hatta bayi darajasu take, kansu yazama ahade da
yakolo Yayinda aliya tahade da mijinta, abun
alfahirinta,garkuwan jikinta sannan sanyin idaniyanta
Sufyan yazo ya auri hassana wacce ta tare a gydan da
sufyan ya kare mata,zaman lafiya alhmdlh nima benaxir
omar ina jinjina muku dakukayi hakuri dani duk da
matsalan dana rinka samu bansamu na karasa muku da
wuriba dakuma rashin cigaba akan lokaci, nagode sosai
Allah yabar zumunci Ina gayda rukayya bayero for helping
out, yu really made me do dix, Kausar nd ummi aisha na
sadaukar da littafinnan agareku don nuna godiyata
agareku, Tom ni benaxir omar nagode muku saikunjini
asabon labarina dazanyi anan gaba


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment