Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne bayan bilki? Kokuma gaskiya ne ba ita
takashe shiba? Hakadai yazauna agabanta ganin tadamu
batasan yazo gunba yabuga kanta kadan tuni takaleshi yayi
murmushi tareda cewa “waya taba minke yanzu na ajiye
tarbiya ta da rawani na Nazuba mai farillai da
mustahabban rashin mutunci” kallonsa tayi tareda cewa
“kaifa asalim dan tasha ne ko baa taba gayamaka ba?” Yayi
dariya tareda cewa “gashi kinfadamin? Bazaki kira bilki kiji
daga gareta ba?” Jin yafadi haka ta tabbatar gwadata yake
donhaka Allah ma yataimaketa bata fara fadaba, donhaka
tace “a a bani da abun fada mata”* tuni yaji sanyi aransa
don yatabbatar da ita tasata zata bukaci taji wani abu tadin
mutuwan suka farayi inda tabugi cikinsa taji abunda
takesonji , tabbas wanda yasa maganin daga kicin yafito
tadaisan yayanta bazai je as bawa ba don bawanda zaiyi
tunanin haka , toh yazama kenan yana da mai taimaka
masa bata idar da tunaninta ba yacigaba dacewa “yanzu
inaga bikin abdullahi zaa daga saboda rasuwannan, ”
“Wacece budurwarsan nan?” “Yar galadiman yanzu” “Ni
naganshi ma dazu dawani da na tambaya akacemin dan
galadima marigayi ne” “Toh bantambaya ba wani
galadiman ba, tunda san ke kadaice agun wanda yarau da
ko?” Gabanta yayi mummunan fadi anma tadaure takirkiro
murmushi zuciyanta na bugawa dakarfi tace “ae! Nikadai
suka haifa saidai dayan galadiman, wat a bad luck duk
sauran masu sarautan basu mutuwa sai galadima!” Ya
jinjina kadan sannan yace “yanzu gashi wazirin yarasu
shima ai Allah dai ya dakatar ahaka” “Ameen” “Sarki yasa
ayi bincike sosai you have to be careful sosai, don nasan
wannan bazai dauka dasaukiba acikin fadansa akashe
mutum” Duk ta kagu yabar mata dakin tayi tunani donhaka
tafara baccin karya, ganin haka yasa yace “opps! Harkinyi
bacci barin koma ” Yana fita yarufo mata kofan tawaje tuni
tamike tazauna dakyau, yayanta yaje as mutumin arziki
yana shuka tsiya daga kasa, lalle toh ai babu marabansu
da ita, gashi batama san sunan yayan ba, yanzu yazatayi?
Tunani yazo mata tunda yusuf yace suna yawan zama tare
dole ta ziyarci fada, Taci wanka tasha kyau sosai abaya ne
bski ajikinta tafice tsum tanufi fada ganin fadawan suka
fara tsareta tanuna musu cewa tazo gaysheda gimbiya
yakolo, dolenta tajira aka tambayo gimbiya sukace ai aliya
ce. Nan tabada dama aka shiga da ita, Tagama survey
dinta kafin tanufi fannin yakolo tana isa yakolo tagwada
farincikinta sosai takuma ja ta ajiki, aliya tagwada mata
yau tazo gari don tagaydata nan da nan yakolo tace “toh
dole nabaki masauki, zaki zauna a fada harsai lokacin
dakika ga daman tafiya” [10/4, 6:11 PM] Adda Bena:
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Aliya tanuna jin
dadinta tareda cewa “barinjr hotel din dana ajiye kayanna
nadebo tukuna” dahaka suka danyi tadi aliya ta musu
taaziya inda yakolo ta amsa, fitowa tayi tanufi fannin da
aka kaita taroki bayin da su kira mata bilki don Allah sunji
dadin ganinta suma dahaka suka kira bilki itama magana
ce acike a bakinta, nan ta zayyana ma aliya cewa bawanda
yasan waye , aliya ta tambayeta waye abokin da abdullahi
ke shigowa dashi tace ” awh dan gidan galadima marigayi
ne , sunanshi sufyan, tun wancan satin yazo” “Kisa masa
ido! Sosai fa” “Toh” Suna rabuwa tafito tanufi gydanta
tadibi kayanta na sati biyu hade da kayan sallahnta sannan
tadawo fadan, tuni ta makale wa fannin yakolo tunda taji
labari cewa sufyan da abdullahi suna yawan shigowa” tuni
shakuwa tashiga tsakaninsu domma duk yaranta mata
sunkoma makaranta saura abdullahi ne shehu ma
bayanan, aikuwa an idar da sallah sai gasu sunshigo tana
zaune akan kujera suma suka shigo abdullahi na ganinta
yafara murmushi “aliya ce yau agydannan?” “Yarima na
gaydaka” nan tajuyya takalli sufyan saida gabanta yafadi
shima kallonta yake, kammaninsa daya da babanta, tabbas
yayanta ne babu tantama ta amince, Allah mai iko anma
yadda yayi ta tabbata bai ganeta ba, taji dadin haka
donhaka sai suka gaysa sunadan tadi, yakolo tashige daki
tabarsu inda sukasha hiransu sosai anan tadansan wasu
abubuwan akanshi, nacewa ashe kasar waje aka tafi dashi
tun primary yaje gun kanin babansu a cyprus anan yafara
makaranta harya gama, jitakeyi kaman taje ta rungumi
yayanta anma babu dama,koba komi tanada danuwan
dazata kishingida ajikinsa idan tashiga damuwa, basu tafi
ba sai karfe 10 sun sake sosai abdullahi ma baida matsala
har cewa yayi washegari zasuje gun matar dazai aura
takuma amince, , donhaka washegari dasuka shirya
tashiga mota abdullahi na gefe sufyan na tukawa, suka isa
yarinyan tanada kyau ga kamala da mutunci da dattako,
tana kallom aliya da sufyan tace “anma kai yayanta ne ko?
Kuna kaman sosai” gabanta yayi mummunan fadi bashiri
taji sufyan yayi dariya yana cewa “tsabar soyayya ne muka
dawo kama, budurwa tace fa” tace “awhh gaskiya kam,
Allah bar soyayya” Yabar aliya da tunani tuni shima
abdullahi yafara tsokansu Yusuf yaje gidan aliya yaji shiru
yabude da extra key dinsa anma duk dahaka baiganta ba,
akwai kayanta donhaka saiyayi tsammani kotaje wani
gurine ganin har karfe sha daya yatabbatar masa da
bazata kwana a gida ba, aduk zamansa da ita baitaba jin
takira sunan wani ko taje gun wani ba balle yayi tsammanin
zataje, tuni yafara tunani lallema tayi sabon saurayi, tafita
dashi kishi duk yabi ya turnukeshi dahaka yadawo,
washegaru ma yakoma shiru bata dawi ba dayagaji
yakoma shigowansa gida kenan yaganta tafito a mota
tareda abdullahi dakuma sufyan, tunaninsa tadaure kayan
jikinta yatabbatar masa da ba baiwa bace tadawo, toh
metazo yi? Wannan yarinya da kwainane. Suna tafiya
yakamota tabaya tajuyo tareda fuzge hannunta menene!
“Mekikazo yi anan? “Meruwanka?” “Bazaki fadaba?”
“Ziyara nazo na sati biyu, kuma karka kuskura kanuna
muna tare don zan dizga ka” Yayi mugun tsorata lalle
yarinyannan munafuncinta ko sallah bayayi, Aliya da
sufyan da abdullahi sun shaku sosai don ran sallah saidata
fita tagansu suna hawa, duk da ta kalli masoyin nata
wanda bakin ciki yasa yanzu yake shareta yakoma ruwa
tsundum ba shan giyansa, Satinta biyu cif tasamu tahada
duk wani info din dazata hada, ayadda taga sufyan bai
ganetaba ita aganinta tagama dashi duk wani hanyoyinsa
zata toshe, sunmata goma na arziki kafin ta tafi gydanta
takoma ta zauna tana tunani tabbas yakammata tamike
tsaye jin datayi abdullahi da sufyan suna magana a mota
ya tsaya mata arai tagagara ganewa kuma ” toh wanda
bashida laifi ya mutu dalaifin wani” Sallah tayi takwanta
acikin barci taji kaman ana shafa kafanta bude ido tayi
mugun figita tayi don ganin wanda ke gabanta, sufyan ne
sanye da kananun kaya, tajuya takalli dakin ta tabbatar
dacewa ae gydanta nefa sannan ta kalleshi “sufyan
mekazo yi anan?” “” hello little sister! Long [truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 15
 benaxir  October 5, 2015  Hausa Novels
 103 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR “So am d
fool here” yadanyi murmushi sannan yace “Kinda” zama
yayi agefen gadon yayinda itama tamike tazauna, “meyasa
kika kasheshi? Kinsan hukuncin kisa?” Kallonshi tayi a
harzuke sannan tace “meye zakawani ce nakasheshi?
Sharri zakamin?” “If bake kika kasheshiba toh waye?, yayi
daidai ma domin kuwa bashi yakashe baba ba!, bakuma
sarki bane” zare ido tayi jin yace bashi yakasheshiba ,
sannan jin kuma bashi yakashe mahaifinsu ba toh waye? ,
“keda kike zaune anan fiye da watanni ni acikin sati naxo
nasamu lbrn dakika garara samowa,” “Yoo toh ai kai namiji
ne ka manta? Zaka iya shiga ka fita duk inda kakeso,
nikuwa mace inada limits,” “ba abunda ke tafe dani ba
kenan, gidannan zaki tattara kibarshi acikin satinnan,
kikoma gydan inna nagayamata zaki koma,kina ya’mace
kina zaune ke kadai, in wani abu yafaru fa, kinje kin koyo
halin yahudawa,” “Nifa zaka takuramin wlh, kaida kaje can
wani bariki ne baka koyo ba, angayamaka bana lura dakai
da abdullahi ne? Kuma akanme zanje gun inna? Nasan da
ita ai naki zuwa” “So kike kizauna saboda wannan katon
yusuf din yana zuwa kuna rufe daki kubiyu ko? Mekuke
ayyanawa?” “Awhhhsh yayah kanada zato, nifa ba abunda
yataba hadani dashi!” “Ki rantse baitaba rike yatsanki ba”
“Ae baitaba ba” tana fada tana murkuda baki, hannu yasa
ya riko kunnenta tareda cewa “ko ki tattara ko namiki duka”
“Wayyo yayah sakemin kunne zafi,” yasake tacigaba da
murguda masa baki tana tattare wayoyinta “nikam ka fita
wlh, duk kazo ka takurani” “Ba inda zanje, ki zauna ki
sauraren, waziri baya gari lokacin da akayi kisan baba,
wanda hakan yana nuna baisan da labari ba, alokacin yaje
taaziyan mahaifin matarsa, dole mukara tsananta bincike,”
“Toh naji katafi sai anjima”mikewa yayi yafice tareda
murmushi rufo kofan tayi, tazauna tana tunani tasan yadda
yafara maganan nan bazai barta ba saiyasamu biyan
bukata, duk yana nema yatakurata tana zaman lafiyata,
yusuf ne yashigo fuska a murtuke ganin yazauna bai
kulataba tace “meye kashigomin kaman gunki” Bai
kulataba sai haki dayakeyi ganin zai bata mata lokaci
tadauko jakanta sannan tafito harzata wuceshi yamike
yarufo kofar, ganin yatsaya kaman gunkin gasken, ta
harzuka sosai tabugeshi da zummar tawuce hannu daya
yasa ya bangeta, saigata a kan gado, yakoma yazauna
akan kujera sannan yafara “Aliya kinsan inasonki, kuma
bana danganta soyayyanki dakomi, aliya meyasa kike min
haka? Meye tsakaninki da sufyan yanzu naga yafito daga
gydannan? Dama dalilinki nazama a fada kenan don ku
shaku dashi? Meyasa kike haka aliya? Kina wahalar min da
zuciya” Dariya tayi tareda cewa “sufyan fa kace,” Mikewa
yayi yabuga table din dake gabansa dakarfi sannan yafice
binshi tayi da kallo don mamaki take harta mike tafito
saigashi yadawo rike kanta yayi dakarfi, yaki sakewa,
gashinta nazafi tanacewa “yarima ka saken, dazafi nace
kasaken

HALACCIN SARAUTA 16
 benaxir  October 6, 2015  Hausa Novels
 110 Views
[10/6, 7:05 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR Bai saketa ba baikuma kulataba, kan
kujera yakaita tazauna zuciyanshi na kuna yaja tsaki
yafice, duk da zafin datake ji bashi zaisa tagagara yin
dariya ba, tadauko ribbon ta tace kan sannan tafara hada
akwatinta,wayanta taji yana kara tadauko tareda dubawa
antynta bashiri ta dauka tasa a kunnenta “Anty ina wuni
inashirin kiranki” “Bakomi yakike? Kinhadu da yayankin?”
‘Ae yatakurani wlh” “Hehe amfaanin yayan kenan “Cewa fa
yayi intattara inkoma gun anty kuma wlh banaso, don
bazan sake nayi abunda ke gabana ba,” “Ai yafi kina ya
mace ba daidai bane kizauna a gyda ke kadai, shiyasa
tunda nake gayamiki banaso ai bayadda na iyane dake da
taurin kanki “Kai anty ni yanzu mene ne lbr?” “Lbr shine ki
lallaba danuwanki kimasa biyayya, shikadai gareki shine
gatanki, maganan ramakon nan kibarshi haka, kifito da
mijin aure” “Hahahahaha anty zakisa cikina yayi ciwo,
cewafa kikayi aure, nida ko mashinshini bandashi” “Kedai
kikaki sauraransu, bari zantura miki adduoin dazaki nayi
kingane?” “Toh anty sai anjima” Kallon wayan ta tsayayi
tana daria, ita sai yanzu tunanin aure yazo mata, bayan
tadan kimtsa kayan ta tattara tafito don zuwa siyayyan dan
abunda baa rasaba, tsintar tsohuwa tayi ahanya sukayi ta
tadi ta shagala sosai, komawanta gyda tasamu dakinta
fanko sufyan yasa an tattara dakin tsum, haushi taji kaman
ta tashi sama anma babu yadda ta iya, wayanta tadauka
da zumman kiranshi saita tuna batada numbanshi, tsaki
taja rike da ledodin hannunta tanufi gydan inna tashiga da
sallama inda innar taketa murna kaman ta hadiyeta, ga
kayannan kwartaye sunfi goma suna shigarwa hakan yasa
tadaina mamaki domin kuwa ita tasan cewa Dan zuwanta
kasuwa da bata wuce awa uku ba baikai ace an tattara
mata kayanta ba, wato ya nemo kwartaye don su samu
suyi sauri kartahanasu kwashewa, tana tsaye tana
gantsaran goruban data saya tana kallonsu harsuka kimtsa
mata kayanta tsaf, harzasu tafi tace “ai baku gama ba”
takarbi tsumma da tsintsiya agun inna tabasu suka share
suka goge, taciro musu zanin gado suka gyra, sannan tayi
murmushi tareda cewa nagode! Koba komi sunji jiki,
tashiga dakin yaji komi tsaf kunna a.c tayi tasaka turaren
wuta sannan tashiga wanka, fitowarta tasamu inna ta aiko
mata da abinci ,tabude taga tuwon shinkafa ne da miyan
agushi yasha kasusuwa, bude ciki tayi sosai don bata cika
girki ba, inzatayima bata yin tuwo Bude ciki kawai tayi taci
tayi nak tayi gyatsa sannan ta mike akan gado, Yusuf kuwa
hanyan gydanta yanufa yaga babu kowa, hankalinsa tayi
kololuwan tashi,domin kuwa duk a tsammaninshi abunda
yamata ne yasa tacanja gydan yasan bakaramin wahala
zaisha ba kafin yakara samota, haushin sufyan da
takaicinsa yamasa yawa, gashi a ranar anfara bikin
abdullahi wanda da har andaga saboda mutuwan waziri
anma sarakunnan suka nuna badamuwa adaura kawai don
matan makaranta zata wuce daganan, fada tacika makil
yana tunanin ta ima zaiga sufyan don yatambayeshi,
saanshi daya zaaje dinner duk da baiyi niyyan zuwa
dinnern ba anma haka yashirya tsum yaja mota yanufi gun,
duk iya kokarinsa na son ganin sufyan bai ganshiba, haka
yahakura yazauna kanshi akasa, matan dake gun duk
hankalinsu yayo kanshi dn yusuf bana zubarwa bane saidai
shiyana ta tunanin masoyiyarsa ba, sufyan ne yafito manni
wa amarya da ango [10/6, 8:35 PM] Adda Bena: Yusuf na
ganinshi yamike yanufi kansa cikin bakin ciki da takaici har
wani duhu duhu yake gani, yana isowa ya damko sufyan
dakarfi sufyan yajiyo tareda matsowa yana dan taka rawan
shakiti bobo, yusuf yace “Ina taje?” “Bangane ina tajeba?”
“Bata gayamaka inda zatajeba?” “Tafadamim, baikamata
kasaniba, inaso kafita harkanta, kafita hidimanta, ba saar
yinka bane,” Yusuf daya kara damkoshi sai tunkudr shi yayi
akasa dakarfi wanda saida hankalin mutane yadawo kansu

HALACCIN SARAUTA 17
 benaxir  October 7, 2015  Hausa Novels
 100 Views
[10/7, 9:02 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR sufyan yamike yana karkade kayan jikinsa
tareda kallon yusuf, yusuf baiji kunyan wani abuba yakara
nufa kanshi ya damko shi dakarfi abdullahi wanda ke filin
yanufi kansu don rabasu, anma yayi latti domin sufyan
yasha naushi, yusuf tsakaninsa da Allah ya mammaujeshi
alokacin dakyar abdullahi yasamu ya kufce sufyan sannan
yashiga tsakaninsu, wasu ne sukaja yusuf don yadena
abun kunyan dayakeyi wanda magana tuni ta yadu, yarima
yana fada ,sufyan mota aka nufa dashi don yawuce
masaukinsa gogan naku kuwa fada aka wuce dashi
alokacin zuciyarshi tafasa take duk ya rikici a gigice aka
kaishi fanninshi falmata ce tanufo kanshi don labari ya
isota cewa fada yake akan liya, cikin fushi wanda bai taba
ganinta aciki ba ta umurci kowa ya watse yabarta da danta
“yusuf mekakeso namaka? Kai ba karamin yaro ba yusuf,
wani irin rayuwa ne haka yusuf? So kake ka kasheni?daga
yau acemin kasha giya, jibi mata, yau kuma akan baiwa
kake fada? “Kidena cemata baiwa saboda a yanta ta, rabon
dakiji anganni da wata tun yaushe? Tun ran da nahadu da
aliya!, giya fa? Tun yaushe???” “Da Allah min shiru da
bakinka da rimi rimi abun arziki kadena sha, meyasa
kadawo sha?” “Saboda narasa wacce tahanani sha” “Kana
nufin kacemin ba don Allah kabari ba sai don ita?” “Dazan
bari dana bari tuntuni, anma don ita nabari Allah nagani
donhaka karkiga laifina. Kinaso in nutsu kema ya kamata
kidena musgunawa yaran wasu, kidena neman batanci da
yaran wasu” Hannu tasa ta gaura masa mari, wanda
saidayaga walkiya a fuskansa.”ina magana kana magana?;
yaushe nahaifeka? Kai wato mace dadi ko, kaje ta tusaka
kasan pant dinta,” “Nifa ko tabata bantabayiba” “Yimin
shiru munafiki, duk duniya bawanda karaina kaman ni,
nagaji zangayawa sarkin saimugani ko shi zaka ji
maganansa!” [10/7, 9:09 PM] Adda Bena: Bata saurari
mezai ce ba tafice, fanninta tanufa, gaskiya yakamata
tadauki babban mataki akan aliya, jakadiya takira tareda
cewa ” kinemomin duk inda aliya tashiga ki kawomin ita
nan” Aliya kuwa tana zaune akan gado tana game din
candy crush bacci yaki daukanta, sufyan ne yakirata awaya
tadauka “Kekuma kina tareda mahaukaci ne bansaniba?”
“Waye mahaukacim?” “Mahaukacin saurayinki mana,
zaimin hauka a bainar jamaa, total yarinta?” Tana kwance
ne saidata mike, ita duk tunaninta hala yusuf yasha wani
abune yaje da zafin kishinsa yayi wani yarintar, “Yaya
meyasameshi? Yana ina? “Anma zanmiki rashin mutunci,
bazaki tambayi jikina ba saina wani kato? Nidana sha
duka?mtsw” “Kayi hakuri bazai karaba, anma don Allah
yana ina?” “Gidan ubansa” “Shikenan don Allah kana hakuri
dashi” Bai saurareta ba yakashe wayansa don yaga itama
giyan soyayyan ke dibanta [10/7, 9:29 PM] Adda Bena: Ta
kashe wayan takira wayan yusuf wanda ke kashe ahaka
taketa tryn har bacci ya kwasheta, bata juyaba sai asuba,
Har rana tana tryn numbansa baya shiga ta tattara
sallayanta tanufi tsohon gidanta a kofar gydan taja kujera
tana zaune tayi hakane dan yusuf ko zadu hadu, wasu
yanmata ne guda biyu kana ganinsu kaga yan biyu don
inka cire kayan jikinsu dasuka saka daban daban kominsu
na siffar jikinsu iri daya ne, suka nufo kanta daya sanye da
abaya daya kuma sanye da atamfa Mai abayar takarewa
aliya kallo bisani tayi tsaki sannan tace “yanzu wannan
jaka dabbar ce daman? Baka mummuna kaman kasam
takashi na!? Shikuwa yarima meyagani anan? Mai atamfan
itama takare mata kallo sannan tace “bar munafiki nema
yake yajamin raini da kaskanci, ta ina zaahadani dawannan
gidahumar? Banza talaka!” Aliya zuciyanta na tafasa
musamman datagano maganansu cewa mai atamfar ce
budurwar yusuf. Bata kulasu ba tadanne zuciyanta tanufi
sgiga gidan, coke din hannunta tasaka ta watsawa aliya a
jiki, wani juyowa da aliya tayi ta damko makokoronta “KE
WLH TLH NI KARAMAR MAHAUKACIYA CE!!!ZAN
ZUBAMIKI RASHIN MUTUNCI!!! Kuyi hkr daga yau har
zuwa saturday zakuna samun kadan kadan due to am a
little bit busy,

HALACCIN SARAUTA 18
 benaxir  October 8, 2015  Hausa Novels
 109 Views
[10/8, 8:34 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR mai hijabin wacce itace hussienan takalli
aliya cikin rashin tsoro tasa hannu itama tariko wuyanta,
tareda cewa “ke angayamiki tsoron ki akeji?banza karuwa
jaka dabba!” Aliya tasa hannu ta make bakinta tareda cewa
“ki iya bakinki don banda mutunci” “Dama ina kikeda
mutunci banza” Aliya fuzgan jikinta tayi tareda tattare
komatsanta tafice tabarsu agun, gyda tanufa ta zauna akan
kujera cike da bakin ciki da takaici, yusuf tasan zainemeta,
anma wasu irin dabbobine wannan? Lalle zasugani
shikuma yusuf zaixo yabata labarin suwaye, Sufyan [10/8,
8:59 PM] Adda Bena: Ne yashigo kafanta yatare hanya ya
mauje kafan yawuce hakan yasa ta tashi, tareda kallonsa
“haba yaya dame zanji bakin cikin wancan yanmatan
komeye?” “Wasu yanmata?” “Yanmatan yusuf bansansuba,
kuma baitaba ban lbr ba” “Wannan saurayinkin baiyi kama
da mutum ba, nima haka yamin hauka, bawannan bane
takawoni, angama binciken wanda yayi kissan waziri
ansamu cewa wata baiwa ce tashigo fadan itada
mahaifinta waziri ya kwace gydansu da duk wani abu
dasuka mallaka. Sannan yayi hanyan sanadin mutuwar
matarsa, yanzu dai zaayi hukunci jibi, [10/8, 9:35 PM]
Adda Bena: Kuma abincike na nasamo cewa akwai wani
alh.hamidu shine kanin galadima na yanzu suna tare da
baba randa zai rasu donhaka dole munemi hanyan dazamu
sameshi donjin bayaninsa,” “anma yaya fisabillilah” Bai
saurareta ba yafice don yunwa ne ta isheshi cikin gyda
yanufa yatarar da inna yaci yakoshi sannan yafice, fitansa
kenan saiga yusuf wanda CID dayasaka su suka masa
kwatance ya iso gydan, sallama yayi yashigo suka gaysa
da inna wacce take zaune yadda yamata ladabi taji tana
kaunarshi yatambayi ko aliya tananan, tace akaishi
fanninta, aliya tamike kafafu batasan da shigowanshi ba
hannu yasaka ya mintsineta, “innalilalh ” tamike a razane
wanda hakan yasa yayi murmushi, bata rai tayi kaman
tunda aka halliceta batayi dariyaba tuni yasha jinin jikinsa,
“meya faru don Allah?” Bata kulasa ba tamike tagyra jikinta
tajawo gyale sannan ta yafa sannan tace “meye haka
kashigowa mutane ba sallama, ko kamanta dakin mace
ne?” Yayi mamakin magananta zaiyi magana tace
“kafitamin kuma karka kara dawowa” baice komi ba kuma
bai tashiba hakan yasa ta kwalawa idi kira, almajiri ne idi
kato jibgege, hakan yasa yusuf naganinshi yamike jiki a
sanyaye

HALACCIN SARAUTA 19
 benaxir  October 10, 2015  Hausa Novels
 115 Views
[10/10, 8:04 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR Yana fita tarike kanta domin ciwo yake
mata, itakanta tasan matsananinci so dakuma kishin
datakeyiwa yusuf bana wasa bane,gashi yaje yadauko
maganan yanmata yazatayi da rayuwarta inhar hakanne
dagaske? Shikenan zaidaina sonta? Kawai tazauna tafashe
da kuka, kuka takeyi nanma ta tuno da iyayenta tafara wani
sabon babin kukan, inna ce tashigo ganin tana kuka tafara
lallabinta dakyar tayi shiru. Itakanta tasan cewa aliya tayi
rashin iyaye, saidai batason ta tada mata hankali ne anma
ganin tadamu da ramako gakuma kukan datakeyi, don
itadai tasan cewa dakyar rana yazo yafadi, aliya batayi
kuka ba,a fuska akwai karfi anma zuciyanta mai rauni ne,
saidata tabbatar cewa aliya tayi shiru sannan tace “inaso
ki goge hawayenki ki saurareni, yau zanfadamiki tarihin
iyayenki, tarihin rayuwarki, na boye da wanda ke kanki
bakisaniba hatta yayanki baisaniba” jin haka yasa aliya ta
gyaro zama tashare hawaye sannan tace “inajinki inna”
“Mahaifinki hassan adamu shine galadima na 55 a garin
yombi, kuma ya gada ne kaka da kakkani, sunyi auren
soyayya da mahaifiyarki aisha, wacce tahaife ku rai biyu
dake da sufyan, mahaifinki dan biyu ne haryau baki taba
tunanin kitambaya ba?” Alokacin aliya ta tabbatar batayi
wayo ba, tunaninta yayi nisa a yin ramako har bata hango
kananun matsalan dake gabanta wanda matsalan da ake
samu yanzu kenan, abu yasami mutum maimakon kazauna
kabincika daya bayan daya zuciyanmu sai tayita ta mana
raye raye muje har ga aikata zunubi,anan inna tacigaba
“kekam ko ni kin gujewa kinki zama kinsanni, bayan ni ce
gambon su mahaifinki su yan biyu ne hassan da hussieni,
saini gambonsu, mu uku ne, hussienin mahaifinki yanzu
haka yana raye anma baa garinnan ba, yana can senegal
yana zaune da matarsa, kuma musabbabin tafiya shine
mahaifinki dashi an bukaci abawa dayansu sarauta, sai shi
hussien yagwada yanaso kuma mahaifinki bayaso,
donhaka saiyake taimakawa don abashi bayan rasuwar
galadima na 54 cikin ikon Allah sai mutanen fada sukaki
yadda acewarsu hussieni na da aladun bature. Dawasu
halaye wanda ni bansaniba anma sunfada anyi rikici sosai
a kafin aka yanke bawa mahaifinki, randa akabawa
mahaifinki aranan shi hussieni yabar garinnan bayan dogon
magaanam dasukayi adaki dagashi sai hassan, haryau
bawanda yasan mesuka fada, kuma tunranar hussieni ya
tsani hassan dinsa, yakuma tsaneku, donhaka son yusuf
shiga gydan sarauta inason gayamiki sai me shiryi, wacce
kikeda kyakywan niyya, mace mai ilmi hazaka da karamci,
don sarauta dakike gani yana raba uba da da, balle wa da
kani Bayan tafiyan hussieni munyi jimami sosai, don
mahaifinki har a asibiti ya kwanta don kewar danuwansa,
munyi rashi sosai saidai ya gwadamana baya sonmu,
yagwada mana abun duniya tafi masa mu, dakyar
mahaifinki ya taso daga ciwo, sannan bayan haka yazo
yanuna rashim amincewarsa na karban sarautan, nanma
anyi daga kafin yakarba don inhar sarautar tabar
hannunmu zata koma wani gida ne bazata dawoba, kaka
da kakkani sarautar tamu ce, bayan mahaifinki yahau
tundaga ranan yafara samun barazana, mafarkai kala kala,
gashi ke kanki nasan zaki tuna lokacim da ummanki tayi
barim yanbiyu sau uku, sufyan yazo yafara abu kaman
tababbe bayason makaranta yafara bin almajirai babban
dalilin dayasa hassan yadaukeshi yakai kasan waje kenan
donhaka malamai suka bashi shawaram yadagashi a garin
yombi, dalilin dayasa kenan kikaga anrabaki da danuwanki,
kekuma ba abunda yasameki, wanda hakam yasa mutanen
gari suka fara surutun cewa lallai lallai asiri akayi muku
wanda bayaso babanki yasami magaji, ummanki tadamu
sosai musamman da aka rabata dashi [10/10, 9:06 PM]
Adda Bena: Ana haka shikanshi hassan yafara samun
matsala da yan fada, kinsan ance baasamun mugun sarki
sai mugun bafade, donhaka yalura duk munafukai ne
agefen sarkim saiyazama shikadai mutum dayake kin
yadda da maganganunsu, donhaka tuni tsana da keta, da
hassada yakara shiga tsakani, donhaka rayuwarku gaba
daya tadawo abin hatsari, hakam yasa ya kwasheki yakai
makarantan kwana don kar wani mummunan abu
yasameki, ran mutuwan mahaifinki kuwa ina asibiti mai
gidana yana jinya, aka turomin labarin mutuwarsa, nayi
jimami sosai nabukaci adauko ki daga makaranta
akacemin a a abarki don kuna jarabawa, da sati daya
surukata tarasu munje kaue taaziya kafin nadawo kika
dawo kika tattara kika tafi abuja koda nadawo nayi bakin
ciki anma dana gane gun wa kikaje saina bari kawai nasam
zata rikeki amana, mukan yi waya da ita lokaci lokaci Tana
gayamim awani hali kike ciki, saidai bantaba yarda
tahadamu ba, aganina guduna kike zanbaki wuri, kinji
takaiccecen tarihinki nasan bakisan da hakaba, iya abinda
zan iya sanar dake ayanzu ne, saikuma ina gargadinki da
duk wani magana dakikeyi nacewa zaki dau fansa,
kidenashi na gargadeki daki daina, karkije ki janyo abunda
zai dameki dakuma tashin hankali agareki, abinda yawuce
yawuce, inkuma kinki yadda zaki girbe abunda kika shuka,
domin bishiya kikeso ki tumbuke, dafatan kinjini? (Insha
Allah daga gobe zaku fara ganin dayawa, nagode da
sauraramim dakukayi so[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 20
 benaxir  October 11, 2015  Hausa Novels
 116 Views
[10/11, 7:33 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR Aliya ta gyada kai wanda itakanta inna
tasan cewa baikai har zuci ba, tana tantama dakyar ta
amince anma tana tsoron abunda zaije yadawo idan aliya
tayo bincike, bata cika son bincike ba itakam, tadai mike
tabarta, tana fita aliya ta watsa ruwa tasako dogon riga
tadaura dankwalin sannan tafito, inna ta kalleta “ina
zuwa?” “Kasuwa” ta amsa, inna takare mata kallo , saidai
batace komi ba saikin dawo, aliya tasan mezatace
donhaka ne ma tagodewa Allah datayi shiru, Allah yagani
batason takuri rayuwarta ba tsanani, tafice saidai itakanta
tasan tafita ne don taji gydan ya isheta batada dalilin fita,
ganin me awara tayi tanemi gu tazauna tasiya ta
murmuzashi a cikin ledan yadawo kaman kwado sannan ta
tusa a jakarta, gydanta nada taje haryanzu baa shiga
gydan ba, tashiga tazauna taci awararta ta koshi dama
tana yawo da coke dinta, takora da coke sannan tafito da
zummar takara gaba, hanyan fada tanufa kai tsaye
batareda wani tunani ba, harta yanki kwana taga sufyan
agabanta bai saurari mezatace ba ya damko hannunta ya
wuce da ita basu tsaya ba sai awani lungu, “Meye kuma
yaya?” “Bakida hankali ko? Ina zakije?” “Fada zanje”
“Kimusu meye” “Na ga yusuf” “Mahaukaciya,wuce mutafi”
Fizgan hannunta yayi suka isa bakim titi ya tsari keke
napep suka hau sannan yayi kwatancem gun, “Da kafana
nazo, dakayi hakuri zankoma da kafana!” Bai amsata ba
har suka isa yamikawa mai keken kudinsa sannan suka
shige inna tana tsakar gyda taga yazo yawuce da aliya
donhaka ta dauraye hannunta dama tana wanke kayan
miya ne, tabisu don ganin meke faruwa, “Bakida hankali
ne? Sau nawa zangayamiki aliya sau nawa zangayamiki ki
fita hidimar fada!, kifita rayuwarsu, mutanennen baruwanki
dasu, yusuf dinnan nagayamiki mahaukaci ne ki hakura
dashi kinki yadda wato ga karamin dan iska” Inna tashiga
dakin ganin yana matsifa yaki shiru tace “meyene yake
faruwa? “Inna kiga shigan jikinta, yarinya gaba daya
tadawo inyamura, aladan yarbawa, kinmanta akasan hausa
kike? Kinje kin dauko dabian wasu kina mana anan!” “Yau
nashiga uku zaku kasheni, meye zaka wani ce yarbawa,
agarin yarbawa nazauna? Kaidai inzakayi matsifanka kayi
ai gwara ni kai fa? Wayasan mekake aikawata, dogon riga
ne ajikina meye aibunsa, ?” “Dakikasa dogon rigan shine
zaki cire dankwalin?kin yafashi a gefe ,kokuma kisaka
gajeren wando kina yawo a kasuwa, zanga ta inda zaki
auru a garinnan, dawannan halin tashan kikeson auren dan
sarki? Wazai baki? ” Haushi suka bata itadai tasan ba laifi
tayiba sunbi sunsa mata ido, wacce tasa atamfa ta rataye
gyale awuyanta tarufo

Please Login or Register in order to submit comment