Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akam gado yana juyi babu
irin tunanin dabaiyiba aransa, yagagara bacci yakuma
gagara tashi yagagara motsi duk tashin hankali na bidansa,
sallarhn magrib ce tasashi tashi ko dayaje masallacinma a
gefe ya kudundunu, for the first time tunda mahaifiyarsa ta
auresa daya mike yayi nafila rakaa biyu yana rokon Allah
yabude masa haske a lamarin daya danno masa, Allah
yasa abunda yake zargi bahakaba, yayi kuka sosai wanda
kowa a masallacin yaji mamaki, abdullahi ne yadafa
kafadarsa tareda cewa “zanyi mamakin abunda zai kawoka
masallaci harkayi nafila, nasan bakaramin abune, Allah
yashige mana gaba, sannan wannan yarinyar aliya!,”
dasauri yusuf yakalleshi jin ya ambaci aliya , yace ” bata
taba maka kama ba? Kaman kasanta abaya?, tanamin
kama da nasanta anma na manta,” dasauri yusuf yace ba
itabace wannan daga wata duniya tazo” abdullahi ganin
yusuf ya amsa da zafin nama yatabbatar da maganansa
don tuni yana zargin yayan nasa da son aliya, shidai babu
keta balle hassada adduanshi tazama sanadin shiryuwan
yusuf, Yusuf nakomawa fada yashiga daki baifi minti goma
ba saiga bilki da aliya sunshigo rike da tire dinsu suka ajiye
akan dinning sannan suka koma gefe, yatashi yazo
yazauna abincin yake kalla anma baya shaawan ci,
asalima baiyi niyyan saukowa daga kan gadonba saidon
yakalli aliya dakyau hakan yasa yazo yazauna, kare mata
kallo yayi wacce itakuma kanta a sunkuye ne batasan
yanayiba, tabbas duk wanda ya tsura mata ido yasan
batayi kama da baiwa ba, kuma duk mai ilmi da wayewa
yasan cewa aliya wayayyiyar macece, ba daga kayaba
kome tasaka wayayyen mutum baya buya , zuciyarsa tayi
nauyi jiyake kaman yayi hauka, zaitona mata asirine don
yaceci mahafinsa? Kokuma zai rufa mata asiri don yana
sonta,duniya tamasa zafi, kansa ya sunkuyar akan table
din tareda cewa “kufita” sunfice saidai aliya jikinta yabata
ba lfy ba, tadai share suka dawo daki, * bilki tana jaje
tareda cewa shekarana goma agydannan bantaba ganinshi
haka ba, toh ko kinmasa wani abune?? Aliya bata kulataba
alokacin shikuwa yarike kansa wacce take matsanancin
ciwo, tunaninsa yarude, bude fridge yayi sannan yaciro
giyansa kwalba guda saidaya shanye a lokaci guda, yakara
ciro wani yakafa kai saidaya shanye, fadi yayi agun sai
bacci, can karfe takwas bayan aliya tagama sallolinta tafito
tayi magana shiru jin baimata isoba tasan meyake
ayyanawa, donhaka tashiga tareda dubawa ga mamakinta
taganshi a kasa kaman matacce, kanshi tanufa tana
girgizashi sai dai yana numfashi hakan yasa ta tabbatar
bacci yake, pillow tadauko masa sannan tasaka masa,
tarufa masa bargon domin a.c na dakin akunnene, tana
zaune ta zura masa ido tana tunani “yarima! Meyake
damunka? Meya sameka kashiga damuwa? Bantaba
ganinka hakaba!” Fuskarshi ta dishe ,zuciyanta na mata
radadi jitayi kaman andaura mata dutse akirji, batasan
hawaye nazuba a idontaba, dawuri tasa hannu tana
gogewa, abun yabata mamaki daga ganinshi haka shine
tafara kuka? “Yooo ni aliya wani irin so nake maka?
Innalilahi, karnazo nagagara cimma burina, zuciya batada
kashi” wasa wasa hawaye nazuba saigashi tanata kuka, oh
ni benaxir abun mamaki dama haka first love din take?, Tun
karfe takwas aliya take zaune akan yusuf bata runtsaba
har karfe uku nadare tana gadinsa, lokaci lokaci dogaran
suna lekowa don tabbatar da babu abinda yasami yariman,
karfe uku tamike tayo alwala tahau sallah, a sujjadda ta
tsinci kanta da rokon Allah ya shiryi yusuf, Allah yabashi
lafiya ya yaye masa damuwansa sannan yanema masa
mafita, sai asuba tahakura bayan sallahn asuba tacigaba
da gadinsa, yusuf bai farkaba sai karfe goma nasafe tana
ganin yabude ido tafara tambayanshi ko lafiyansa lao, yayi
matukar jin kunya bayajin kunyan [9/28, 8:25 PM] Adda
Bena: Mahaifiyarsa bayajin kunyan mahaifinsa anma ya
tsinci kansa da jin kunyan aliya, ta taimaka mishi yaje
bandaki sannan tafito. Wanka taje tayi sannan tacanja
uniform dinta tamike kan gado, bacci mai nauyine ya
kwasheta, Yusuf kuwa fitowarsa yaga babu ita dasauri
yakira dogarinsa daya tareda cewa “ina aliya? Kiramun ita
ai batagama aikin ba” ya amsa da toh, bilkisu ce ta tasheta
anma haka tamike sukaje fannin, tea yasa tahada mishi
yana kare mata kallo, tayi iya kokarints ganin ta danne
baccin datakeji, tahadamai yaci da cake sannan yakoma
kan gado, zata dita yace “dawo ki tsaya harsainayi bacci”
tana tsaye haryafara bacci sannan tafito bacci takomayi,
har azahar alokacin yatashi yaga bilki ransa ba karamin
baci yayiba tareda cewa ina aliya? Kikiramin ita, ta
sunkuyar dakai gami dacewa “bataji dadibane yarima tana
bacci yanzu haka” yazaro ido mai yasameta?” “Babu
baccin dabatayibane yajawo mata, tun shekaranjiya
rabonta da bacci, ” shiru yayi yana tunawa tabbass yatashi
yaganta kenan azaune ta kwana, tsanar kansa yayi yanajin
haushin kansa oh aliya, kiyimini hakuri, shikadanshi kaman
yakashe kanshi, mikewa [truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 9
 benaxir  September 30, 2015
 Hausa Novels  115 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Budewa yayi
yashiga wanda yabawa bayin mamaki domin yaran
sarakunan har matan basu zuwa gun, umma uwar soro ce
kadai me shiga da fice agun, gaba dayansu kowa ya
sunkuyar dakai domin sun gama tsorata, ayadda suka
sanshi sunsan sarai cewa ba lafiya ba, bayada mutunci ko
kadan , yakare musu kallo yaga wani gado ne akwai
mutum kan gadon yanufa, aliya ce tana bacci , yazura
mata ido sosai. Yasa hannu yasa ajikinta yaji yayi zafi
sosai, bayin sunyi mamaki nan da nan kowacce tafara
tsegumi, yafice fanninsa yanufa yadau wayarsa yakira
likitan gydan, bashiri yazo anan yasa bilkisu suka kamo
aliya suka kawota fanninsa aka dubata, likitan yace rashin
hutu ne da wahala, da rashin sabo da wahalan, yabata pain
reliever, da maganin bacci, haka dai yatafi hankakin yusuf
atashe baiyi motsi agefenta ba, yanata kallonta yarasa
wani yanayi zai fassara kansa, Maganan yusuf yashiga
fannin bayi tuni tabaza cikin fada, falmata ranta yabaci
sosai, data bukaci bayani agun jakadiya nan jakadiya ta ce
mata “bayin sunce kwana biyu yana nuna alamun damuwa
wa aliya” falmata tazaro idanu domin ta mugun tsorata,
yanzu yarasa wacce zaice zai kula sai baiwa? Duk neman
matanshi bai kare awaje ba harsai yazo gun bayi?”
Jakadiya tadanyi gyran murya sannan tace ” gimbiya
wannan fa inaga nufinsa daban, don sundade tare, inhar
biyan bukata ne kinsan yarima yanayi sau daya zai
shareta” falmata takara tsumuwa, batasan lokacin data
mike tanufi fanninsa ba, dogarai suna kokarin yimata iso
anma ko jiransu batayiba tafice tashigo, gabanta ne yayi
mummunan fadi ganin yusuf yana zaune agefen aliya, da
alamu yayi nisan tunani tunda baisan tashigo dakin ba,
wani tsawa ta daka masa wanda saidaya firgita ganinta
yasa yadan rusuna, bai idda ba tace “wani rashin hankali
ne wannan? Jakadiya fita da ita!” Jakadiya taje ta tashi
aliya wacce jikinta yayi zafi sosai tarasa yadda zatayi,
donhaka taruketa zasu fice falmata tace “saketa!” Aikuwa
aliya tajita akasa dasauri yusuf yanufeta yadagota zaifice
da ita budan bakin falmata tace “zandaga maka nono
yusuf, wlh inka kuskura kabita zandaga maka nono” cak ya
tsaya ji yake kaman yayi hauka. Alokacin aliya tajanye
jikinta tareda cewa “zan iya tafiya badamuwa karka damu”
fitanta sashimsu tanufa inda kowa kallonta yake alamun
tausayi bata kulasu ba takwanta, alokacin jakadiyar yakolo
tazo ta dubata, acewarta yakolo na gaysheta da jiki, fitanta
kenan alokacin yusuf yabar gydan don baiga amfanin
zamansa ba, gydan aliya yanufa anan yakwanta yasha
giyansa, barci ta kwasheshi, falmata kuwa tarasa yazatayi
gwara tun wuri takauda aliya donhaka ta umurci azo da
aliya, dakarfi aka kamo aliya tana kallonta aliya duk
tacanja kamanni, falmata ta umurci da adauko bulali nan
aka baza aliya ta kwashi dari masu karfi da zafi, tunda
mahaifiyarta tahaifeta bata taba shan wannan azaban ba,
aka kwara mata ruwan sanyi, falmata tace “sakamakon da
ake samu kenan idan mutum yashiga hurumina,” suma
aliya tayi anma haka falmata ta umurci a watsa mata
ruwan sanyi tana farkawa aka daure hannayenta tabaya da
kafafunta aka kwantar da ita akasa,tasa aka dauko
kankara aka jera mata a cinyoyinta,kakkarwa take, duk
tafita hayyacinta burinta baisamu yacika ba zata mutu,
dukka wanda yakegun dole yatausaya mata. Bilki ce taruga
da gudu fannin yakolo tasanar da ita abunda ke faruwa,
bashiri yakolo tafito isowanta gun tace akunceta falmata
takalleta sama da kasa tareda cewa “a matsayinki na
wacece?” Yakolo tace “a matsayinta na baiwa ta!, inbaki
manta ba ai kinkoreta nadauketa!” Faalmata taji kaman ta
makuro wuyan yakolo tsaki taja tare dacewa “zanga wanda
zai daina abunda nasashi,inku jahilai ne takoma tazauna a
kujera; yakolo tayi murmushi dakanta tanufi kan aliya ta
kunceta. Tarungumota sannan tanufi fanninta da ita,
falmata tsaki taja tabar gun tareda zagin bayin, A fannin
yakolo ta aika aka kira likita yaxo yamata dressing jikin
yabata magunguna, abdullahi ne yashigo ya tsorata ganin
yanayin datake ciki, tana bacci anan sukayi shawara da
mahaifiyarsa a[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 10
 benaxir  September 30, 2015
 Hausa Novels  122 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Tana
farkawa tayi mamakin ganinta afannin yakolo anma yakolo
ta gwada mata bakomi, sallolinta tayi a zaune don bata iya
tashiba, abdullahi duk tausayinta yacika sa gashi haryafara
tsanar kansa yasan tabbas yasan aliya anma yamanta
aina ne? Wannan wacce irin mantuwa ne, Yusuf bayan
farkawanshi wanka yayi yacanja kaya sannan yarufo gydan
yadawo fada, atake yafara neman bilki cikin kuka tasanar
mishi da abunda yafaru, ranshi abace yanufi fannin
mahaifiyarsa donjin baasi kamar kullum cemasa tayi
“inzaka shekarana kana neman yanmatan da basu daceba
baxan gaji da koransu ba, kanemo mai tushe mai asali, ”
baice komi ba yafice , fannin yakolo yanufa wanda kowa
saidayayi mamaki yagaysheta sannan yace “nazo daukan
baiwa tace ” tagane meyake nufi anma tace “wacce baiwar
fa?, ” yayi shiru sannan yace “marar lafiyannan aliya” tace
“au! Aibansaniba kamanta mahaifiyarka ta koreta ne? Ni na
karbeta, kuma daga yau na yantata donhaka daga kai har
mahaifiyarka bakuda dama akanta!”. Zaro ido yayi yayin
daya tuna kalmomin aliya na “karka yantani, karabu dani
kuma ka manta dani” subhannalahi ai ta tona mishi asiri
aliya batason a yantata, anma shiyasan yantata shine
kadai hanyan dazai iya soyayya da ita, baice komi ba
yabar gun A haka aliya taringa jinya kullum yusuf na
hanyan gaysheta wani lokacin suhadu da abdullahi wani
lokacin kuma da shehu, wanda baya zama agydan saboda
makaranta wasa wasa saida aliya tayi sati sannan
tawarke, aranan yakolo tabukaci tagayamata gaskiya,
Tagayamata cewa ta yantata , aliya batasoba anma yanzu
kam shine kadai hanyan dazatabi donta rama abunda
falmata tamata, dole tarama saitaji zafi ninkin abunda taji,
zataga itako falmatan wazai juya yusuf, uwace ita tafita
daraja anma namiji kam inkika tsuguna kika haifeshi
aikinsan wa ya mace kika haifawa, domin kuwa komi mace
zaifara yiwa, dadday ne masu fara tuna uwayensu. Shiyasa
bahaushe yace da ki haifi gwamna gwara kinhaifi matar
gwamna domin gwamna matansa zaituna kafin ke, itakuwa
komi uwarta da danginta, sungama magana da yakolo inda
yakolo tabata kayyaki da kudade tace tatafi garinsu don
hakan kadai ne zai tsirar da ita daga gun falmata, abdullahi
ne yazo alokacin yazaunar da ita yace “dani da mahaifiyata
muna tunanin akwai wani igiyan dangantaka a tsakaninmu
dake inbahaka ba kuwa babu yadda zaayi ni kullum ina
tunanin nasanki awani guri yayin da itakuma take tunanin
cewa tana kaunarki haka kawai, toh ko dai babu mudai
iyakacin gatan dazamu iyamiki kenan!” Aliya tayi godiya
sosai tabbas baxata manta da hallacinsu ba, ko agun bayin
kuwa su bilki nata kuka kowa yasaba musamman bilki
tafijin jiki, da kuka suka rabu tafice tanufi gydanta ga
mamakinta taga makullimta baya shiga kuma ba kofanta
bane, tuni tasan aikin yusuf ne don if barawone bazai gyra
kofan ba, tazauna agefen kofan tana tunanin yadda zatayi
saitaji alamun key a gefenta tuni tadauka tabude taga
yabude, dakin warin giya da kwalaben giya hakan yatabbar
mata da cewa yusuf ne yake zuwa dakin, abubuwanta ta
tattars sannan tarufo kofan, tarar machine tayi taje takama
hotel kafin tasamu gida dondai tasan batagama aikintaba
babu abinda zaisa tabar garin, wanka taje tayi tanayi tana
kallon tabon cinyoyinta na dukan da falmata tayi tasake
shower yana zubo mata, tuni tafara tunanin iyayenta kuka
tayu sosai wanda saida yasamata ciwon kai tafito tayi
sallah sannan takwanta wayanta takunna, msgs tagani
dayawa na auntynta kusan kullum saita kirata taji yatake,
tajero mata txt tareda mata adduan samun nasara,
saikuma malaminta yana tambayanta yaya aikin datasa
agaba? Sai daidaikum yan makarantansu dakuma
invitation na bikukunan frnds dinta, bacci ne yakwasheta,
bata tashiba sai bayan magrib donhaka tayi magrib
tasanyo dogon abayanta tafita reception don cin abinci, tayi
ordern fried rice da grilled fish, game take awayanta
saikawai taga mutum yazo yazauna, bata kulashi ba
shikuwa sai kallonta can data gaji da kallon tadauki
wayanta tacanja sit yakara binta tuni taji abincin yafita
mata akai hanyar dakinta tanufa yakuwa bita saidata
fakaici mutane tarikoshi dakarfi hannayensa tawullosu
tabaya tarike kara yasaka. Cikin zafin nama tace “meye
kake bina?” Karan yakeyi babu daman magana anma
yadaure tareda cewa “inason zama abokinki” danna
hannun tayi dakarfi tare dacewa “ni ba saarka bace! Not
interested!” Sakeshi tayi tareda nufa dakinta nan yafara
tunani oh mace dakarfi kaman doki,dahaka yakoma shima
Yusuf kuwa shigowanshi gyda yadan siyo kayan
kwalamansa yashigo fannin yakolo don gayda aliya, ga
mamakinsa tace ” na yantata tunda kasan hakan aikasan
cewa zata tafi duk lokacin dataga dama, toh itama tatafi,”
zaro ido yayi yasake kayan dagudu yafice mukullin mota
yadauko yatuka wani wawan tuki dayakeyi saida ya tsorata
mutane gydan aliya yanufa ya bude yaga bata ciki, yaleka
kasan gado yaga ta tattare kayanta, wani tsaki yaja bakin
ciki nacinsa hannunsa yabude da bango yana magana
shikadai “aliya wlh inasonki, meyasa kikatafi? I[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 11
 benaxir  October 1, 2015  Hausa Novels
 144 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR zama yayi
dirsham babu irin tunanin dabaiyiba aransa, yasan dai
kome yasameta. Bazata taba barin garin batare data
cimma burinta ba a dan sanin daya mata, macece mai
tsayuwa akan raayinta, nan kuma takara bashi tsoro domin
kuwa yasan tabbas bazata bar mahaifiyarsa ba, gida
yakoma yatara dogarai yabasu cikiyanta, har cikiya da
hotonta idan amsamu wanda yaganta zai samu kaso na
dukiya mai soka Aliya kuwa tuni tasamu tanemi hayan gida
ciki da falo, taje tasiya sabbin furnitures, da kayan kallo da
duk wani abu datasan yana wancan gydan tabari, saidata
koma gaba daya sannan hankalinta yakoma kan yadda
zatasamu daman juya fada batareda sungantaba, tayi iya
tunaninta anan ta tuna da bilki, toh tayaya zatayi magana
da bilki babu yusuf? Dole shikadai zai iya dauko mata ita,
inbahaka bilki bazatabar fada ba, ko acikin matan sarkin
bawacce tafi kusanta balle tanemi alfarma, tsaki taja
tasako dan riganta iya gwiwa da jeans, tadaura dankwalin
akanta batayi kama da yaran hausawa ba ko kadan wanda
tayi hakanne donta batar da kammani, yanayin garin
yamata dadi sosai yadda take tafiya duk wanda zai ganta
zai tabbatar da macece marar son damuwa da tashin
hankali, masara tagani ta ciro gudan dubu daya a aljihunta
tamikawa matan, matan tamika mata guda daya da canji
aliya taki karba haka tabar mata canjin, matan tabita da
godiya, hankalinta a kwance tanaci tana tafiya can taga
taro andan cika dasauri tanufi gun, wasu ne suke fada ana
kokarin rabasu ganin mazane ba yadda ta iya tajuya tatafi,
har gyda taje sannan ta kwanta akan kujera taji dadin dan
zaga garin datayi koba komi tayi exercise din kafa, buga
kofa taji anyi batareda tunanin komi ba tamike tabude ga
mamakinta saitaga ysuf, mayar da kofan tayi zata rufe
atake yasako hannunsa bahali dole tabari, tana juyawa
takama kanta tareda cewa “mekazoyi?” Cikin murna da
farinciki ji yakeyi kaman ya rungumota yace “yazaayi
bazanzo ba. Naxo gaysheki ne” tana zama tadauko wani
takarda tana dubawa tareda cewa “mutanen garinnan
munafukai ne, har anje anfadamaka inda nake, fitan danayi
ko awa biyar banyiba” bai amsa ta ba illa zama dayayi
yana kallonta, ta ajiye littafin tareda cewa “taimakona
zakayi, inaso kadaukomin bilkisu akwai maganan
dazamuyi” ganin tadage yace “maganan yadda zaki kashe
babana da mamana?” Ta mugun tsorata anma tadanne
tareda yin murmushi tanacewa “mesukamin? Babu ,
donhaka ni tambayan bilki kawai zanyi!” Yamike tareda
cewa bazaki ganta ba nasan menakeyi, so kike kiyi amfani
dani wurin ramakon ki ko?” Ganin datayi tamkar yasan
komi ta tabbatar dacewa lallai yakaranta littafinnan
donhaka tabata rai tareda cewa “ae!” Baiyi mamaki ba,
dama yasan dole zaa rina, abunda zatace kenan, yamike
tareda cewa “kinemi wani hanyan ramakonki badaniba,
sannan kiyi adduan Allah yarufe bakina akanki” yana fada
yabar gydan, ko ajikinta don tasan bazai fadaba, dazai fada
tun tana baiwarta zaifada, tayi zama tana tunanin hanyan
dazatabi duk iya tunaninta dole yusuf ne hanyan, inbai
taimaka mataba babu yadda zatayi, gashi yariga dayasani
tasan zaibi duk wani hanya domin yaga ya tsayar da ita,
wanda aganinta bazai taba faruwa ba, donhaka dole tabi
hanya daya, wato ta ajiye komi tajanyo yusuf ajikinta har
yasota wanda bazai iya mata musu ba, wani zuciyan tace
toh yanzumman ya aka kare? Donhaka bari tagwada tagani
Kwanansa uku bai lekota ba, tana hankalce anma tana
adduan Allah yasa yazo din, domin zuwanshi ne kadai
mafita agareta, cikin ikon Allah dayamma kamar yadda
takeyi, yau kuma dogon rigane ajikinta tadaura dankwalin
taje cin masara, harta karbi masaran taji murya abayanta
yanacewa shima abashi, juyawan dazayi taganshi, bata
kulashi ba takarba tafara tafiya wanda yana binta abaya
sanye yake da kannanun kaya sunyi asalim yimasa kyau,
kowa kallonsu yake domin ba karamin kyau sukayiba, tayi
kaman batasan akwai mutum agunba har sukaje kofan
gydan tabude tashiga yabiyota, bata kulashiba tacire
dankwalin gashin yazubo tazauna tamike kafafunta alamun
tagaji, tanaji yana kiran sunanta tashareshi tamkar bada ita
yake ba, ganin ta mayar dashi mahaukaci yanufi kanta
kwalban coke dake hannta yakarba yawurga akasa tas
tafashe, aliya bata dago ta kalleshiba balle ta tambayeshi,
ganin zata haukatar dashi yasa yanufi kanta ganin zai mata
hauka tasa kafa ta tokareshi hawaye ne a idonsa ” don
Allah kiyi hakuri duk zuciyan dakikayi dani kiyi hkr, baxan
iya rayuwa ba keba, wlh inasonki aliya kefe madafar
zuciyata, na yadda ko meye zakiyi dani kiyi, kiyi amfani
dani zanyi biyayya inhar zaki gwadamin so, komi kikeso
zanmiki in bilkisu ce barin aika akirata” yamike zai fita tace
“yarima!” Yajuyo yakaleta sannan tace ” kainake son kaje
kadaukota dakanka” ba musu yace “toh (Kuyi hkr nayau
bayawa, nayu latti ne,[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 12
 benaxir  October 2, 2015  Hausa Novels
 122 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Fitanshi
baikai awa daya ba saigashi da bilkisu, tana shigowa aliya
tajata suka shiga daki tabarshi a falo, shigansu bilkisu tayi
mamaki kwarai, kallon gidan takeyi dakuma aliya wacce
taga wautanta na rashin gane aliya tunfarko, tabbas aliya
batayu kama da baiwa ba idan tayi laakari da yanayinta,
aliya ta numfasa sannan tace ” kiyi hakuri bilkisu ke kadai
na yarda inaso kitaimakeni, anma saikinmin alkwari cewa
har mutuwarki babu wanda zaki fadawa” bilki tayi
shiru,azaman duniya idan ana kirga masu sonta tasan dole
aliya tazo aciki, domin ta taimaketa sosai donhaka
batareda wani tunani ba tanuna amincewarta anan aliya ta
fara kissa mata labarinta daga farko har karshe akan
waccece ita, dakuma dalilinta nazuwa fada!, bilkisu ta
tsorata sosai don bata taba kawo haka arantaba, anan
taroki bilki datazama idonta acikin fada, bilki babu gardama
ta amince aikuwa aliya ta mata alfarman komeye takeso
zata mata, dawannan suka fito yusuf na falo har bacci
yafara kwasansa domin sun dade adakin, bilki tafito haka
yamayar da ita kamar yadda ya fito da ita, dawowansa
yasami aliya na kallo shi abun na damunsa toh batada
yanuwane suka barta take wannan garajen? Kayan
kasada? Hakadai yazauna akujera yadurkusa dakanshi
takaleshi ganin yadda yayi tace “meye ka sunkuyar
dakanka kaman shege a rabon gado” abun yabashi dariya
anma yadaure fuska bai tanka ba, ganin haka yasa itama
ta tsuke tareda cewa “alakarmu bazata yiwuba inhar
bakadena shaye shaye ba, daga yau kadena!” Yayi shiru
yana kallonta ko falmata datace yabar shaye shaye tana
masa fada baitabajin yadena ba sai ranan, yasa aranshi
bazaikara shan wani abuba, “insha Allah nadena” jinhaka
yasa tasake masa sukadanyi tadi duk maitarsa nason sanin
meye plans dinta taki fadamishi, anan yake cemata auren
abdullahi bayan sallah, ta ce “ni yakamata nashiga kasuwa
ma saboda banda kayan azumi ko kadan, muje karakani”
aikuwa suka fice tsum dogon riga iya gwiwa dakuma
wando takara sawa sannan sukafito yakalleta dakyau
azucinyanshi yace “wannan yarinyar yar bariki ne wlh”
kaman tashiga zuciyansa tace “karkayi tunanin ni yar bariki
ce, nayi rayuwar kudu” yayi murmushi tareda cewa “kinyi
kyau” dakafa suka taka har kasuwa shikam har kafofinsa
sunfara ciwo yasan yau sai yayi jinyansu amma itakuwa ko
ajikinta tasaba , suka siya komi don inhar zata mika kudi
shiyake mikawa, ganin zai rainata tace “nifa ba irin
yanmatanku bane na zamani dazakuna kashewa kudi
donku siya zuciyarsu” yayi murmushi sannan yace “oh
mata dai, yanzu da bansayaba zakije kice yarima guda dan
sarki anma haka yabarni nasa kudi nasiya tsabar rowa”
abun yabata dariya tace ” toh aiku mazanne hannunku
kaman kuna ajiyeshi agyda kafin inbanda haka ai kasan shi
kyauta yana kara dankon zumunci, zuciya tanason mai
taimaka mata, ko mata da mijine wlh inkana kyautata mata
darajanka dabanne, aanma wasunku sai balain rowan
tsiya, wani lokacin kunsan mace tafi karfin abu duk dahaka
kumata mana, ko bazata karba ba. Anma wai saikuce kuna
gwadata ne, waxaku rainawa hankali, gwara kanayi kana
ihsani,” tabashi dariya nan yakara tabbatarwa macece mai
experience na rayuwa, anma yadanne ransa yace ” samarin
g.s.u marowata ne kenan?” Kut wlh a a, mukam yan
gombe akwai kyauta” “Ta ina kika zama yar gombe????”
“Oho dai gwaramu kaida kagama a.t.b.u samarin atbu ne
da rowa” “Allah kije kiga mu har mota muna saya” “Ae naji
wannan zubairun” Ganin me masara sukayi ta tsaya tana
dubawa tadauko daya tabashi tareda cewa “Ci” yakarba ya
gutsura ” hmmm dadi” Suna tafiya sunaci baisaba ba duk
saiyajishi a tsarge anma yahadu da yar tasha yazaiyi da
rayuwansa?” Gyda suka nufa kicin suka ajiye na ajiyewa
sannan suka fito, yamata sallama yanufi gyda Tun ranan
suka soma shakuwarsu har azumi ta shigo shine yarage
zuwa don yana wuni bacci ne, aliya kuwa alokacin takafa
ibadunta, tanajin labari lokaci lokaci agun bilki idan tasa
yusuf yadaukota, falmata bata canjaba, donhaka aliya ma
bata ajiye kudirinta ba, aliya tayiwa bilki kayan sallah,
yayinda shima yusuf haka yasiyo akwati guda yaciko da
kaya yakawo mata, taki karba anma ya ajiye yafice
yabarta, taji dadi koba komi her first love worth it, ayanzu
son datakewa yusuf yawuce duk wani tunaninta, akullum
addua take Allah yabarsu tare, Yusuf kuwa satin farko shiru
baisha giyaba , ana shiga nabiyu yafara canjawa, kana
ganinsa kaga marar lafiya watarana ansha ruwa yashigo
gun aliya anan yazauna kaman zaimutu tayi tambayan
duniya anma yace mata bakomi, bata rabu dashiba harsai
da ya rike cikinsa yana cewa “aliya ki gafarceni, kishi nakeji
” dasauri tadauko masa ruwa yasha anma ya girgiza kai
alamun bashibane alokacin tagane meyake nufi, babu giya
agidan duk tarude “karka mutu bazaka mutuba, Allah yaga
zuciyarka kaci gaba da danneea” idonsa yayi jajur, duk
yafita hayyacinsa batasan lokacin data fitaba, giyan taje
tasiyo takawo mai tareda cewa gashi kasha kadan, ahaka
harka bari” yakalleta idon jajur yace “nariga nayi alkawari
bazan kara shaba, kibari kawai” hakan yasa ta je toilet
tajuye gaba daya tafito sai karfe goman dare sannan
yasamu kanshi yakoma gyda nanma yaje yakara tarar
dawani tashin hankalin don falmata cewa tayi yaje shan
giya baikulata ba hartagama hargowanta tafice anan kuma
labari ya iso mata cewa kullum ana ganinsa tareda wata,
nan ta bukaci a dubo mata wayene! Dukkan sarakunan gari
ancika makil a fada, donyin council meeting wanda akeyi
kowani laraba, masu sarautan duk kowa yazauna don a
tattauna matsalolin al umma dake faruwa, inda anan aka
shigo musu da kayan sha da ciye ciye, sungama lafiya inda
waziri yasanar da auren abdullahi dazaayi a sati mai xuw,
sannan yamusu barka da sallah, zaikoma yazauna sai
yafara rike wuya yana muzurai, duk hankalin kowa yayi
kanshi anan yakwanta yana muzurai, farin yawu yafara
fitarwa, tuni aka nemo likita anma kafin ya iso, waziri yace
ga garinku Labari tuni yazaga gari aliya wacce ta idar da
karatun quraninta taga yusuf yashigo a birkice idonss jajur
yana cewa “aliya nasan kinzo daukan fansa ne anma kina
mace meya hadaki da kisa?” Takalleshi tareda cewa “wana
kashe? Sannan meyasa zanyi kisan?” “Karki rainamin
hankali waya kashe waziri?” Mikewa tayi zummur tareda
dafa kirji “yarasu? Alhndlh? Amma waye haka yataimaken?
Kenan bani kadai bace me harinsa” “Abunda zakice kenan?
Ke wato kin kwashe kayanki agaban manzo” “Bawani
kwashe kaya. Wlh bani bane, anma inaso nasan waye,
burinmu daya, ni nayi niyan kashe waziri anma bada
hannuna ba, naso nabi hanyar da hukuma zata hukuntashi,
nawa tona masa asiri ne kawai” Ficewa yayi yabarta “Aliya
tuni tafara tunani, azumi na garata anma haka tamike taji
wayam batajin yunwa, duk ta kagu tasan waye mai tayata
aikinnan, Wayarta ce tayi kara daukan dazatayi taga
antynta ne “Aliya ki saurareni kiji yayanki yazo yadamu
ingayamasa inda kike naki fada jin kince kar infada kowa,
anma kuma yanemoki donhaka kizama ashiri zai iya
samunki kibi ahankali don yadau alwashin kashe su ne
acewarsa kina bata lokaci” Aliya tayi kufum kafin tace
“wani yaya? Dama imada yayane? Yaushe aka haifes[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 13 & 14
 benaxir  October 4, 2015  Hausa Novels
 119 Views
[10/4, 5:37 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR Bata amsa ta ba saidai cewa datayi “ina
kasuwa zankiraki idan nakoma gida saimuyi magana kedai
kiduba dakyau zai iyayin wani abu daban, nibansan gurinki
yazo ba sai yanzu dayake kirana” kashe wayan tayi aliya ta
tsaya kallon wayan, bataci ta zamaba gwara tamike
dakyau tanemi mafita duk da tasan cewa yusuf baxai taba
fadawa kowaba, dole tafita neman danuwanta!, dole tabi
diddigin kisan kafin sarki yarigata yasa akamoshi. Murna
zatayu ko bakin ciki? Anma dai koba komi its a relief
tanada danuwa ba ita kadai aka bari ba, tuni tafara
tunanun yadda zataga bilkisu din abakin bilki ne kadai zata
sami lbr, kayanta tacanja tadauko wani katon roba tafita
shago takarbi pure water tajuye aciki ta tusa wayanta
acikin zanin sannan tanufi hanyar fada, ahanya mutane su
tsareta don siyan pure water abun yafara batamata rai ita
tasaka ne don bukatunta daban akan meyasa zaana tareta
don asiya? Dahaka dai tanufi fadan inda ta fara survey din
gurin duk rashin hankalinta da kuma basiranta babu
hanyan bi, katangan ma dogo ne irin dogon da babu dan
adam dazai gwada shiga haka, agun aka siya pure watern
dukka don yanada sanyi sosai roban da kudin tamikawa
wani almajiri tadawo gyda, kwanciya tayi akan gado itakam
zatayi hauka gashi ankusan shan ruwa haryanzu batasami
hanyan shiga fadaba. Tasan dole tabi hanyan daya kamata
tabi wato yusuf,bayan asha ruwa saigashi yazo ganinta
yayi akan sallaya yaga batamasan yazoba hakan
yatabbatar masa dacewa tunani take, shi gani yake kaman
ita takashe waxiri anma yadda tayi dazu tasashi kokonto,
kuma dayaje fada yasami lbrn duk abunda aka kawo aci
daga kicin bilki tana fanninsa a lokacin toh kodai aliya
tanada wani

Please Login or Register in order to submit comment