Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Fatima tanisa tace "to alh hakan ma yayi yayi ko yarannan hankalinsu zai tashi tunda munce musu muna hanya" Alh kabir yace "hakane, yanzu bari naje na sanarma Dr".

Ya kama hanyar office din Dr. Wayar sa ce ta fara rura, ya daga yayi sallama tare da cewa " Yaya ya gida?" Can bangaren aka amsa "lafia lau Kabir, ya ankayi na tambaye Lukman yace kun gayamai kuna kan hanya tun 6:30pm amma yanzu har 9:30pm baku iso ba, lafia kuwa?" Alh kabir yace "eh hakane yaya amma ansamu wata matsala ne shiyassa, yanzu haka muna asibiti wat-" asibiti kuma? Lafiya? Miya faru? Alh kabir yace "ka kwantar da hankalin ka yaya wata fa boyar Allah ce tayi accident muka sameta a gefen hanya ko motsi batayi, shine muka taimaka mata" yace "ayya to ya jikin nata dasauki?" Alh kabir yace "to da sauki za'ace amma saida aka sakamata jini ma" Alh Aminu ya jinjina al'amarin tareda mata fatar samun sauki. Yace "ai yakamata ku dawo gida zuwa gobe kunsan fa yaranku na kewarku kunyi 1mouth bakwa gida" Alh kabir yace "ai yanzu gidan zamuje kafin zuwa gode musamu mafira" Alh Aminu yace "to Allah ya kawoku lafia" yace "ameen" ya karasa office din Dr ya sanarmai. Dr yace bakomai zasu iya tafiya tunda patient dinku tana bacci kuma zata iya kai gobe saboda batason hayani" Alh kabir yayi godia sosai suka fito asibitin.

Momy bata farka ba sai bayan sallar bagrab ta farka tana tunano abinda yafaru. Allah ta nema sauki akan al'amarin tareda da tashi ta nufe toilet ta yo alwallah. Fitowarta ta tarad da Faisal kan gado a zaune ya zuba tagumi, Momy tace "kai Faisal lafiya? Yace " Momy ba aunty Safna bace tazo gidannan dazu ba? Kuma har da kuka ta fita tayi accident" sai ya fashe da kuka" gaban Momy ne ya fadi tace "Kai Faisal waya gayama wannan maganar?" Cikin kuka yace "da muka dawo taga islamiyya ne driver ya daukomu na hango motar kuma kamar aunty Safna ce acikin motar" Momy tace "ba ita bace sai idan mai kama da ita ce, kasanfa ana kama duniya kaima yanzu zaka iya ganin mai kama da kai" Faisal yayi dariya yace "a'a ni Momy dake kawai nake kama" Momy tayi murmushi na takaici a zuciyarta tace "da gaskiyar Faisal insha'allahu itace tayi accident ya Allah ka hadata da hannu na gari" Faisal ya katsemata tinanin data zurma da cewa "yanzu Momy kenan ba aunty Safna bace?" Momy tace "eh aunty'nka tana gidanta" Faisal yace "ni Momy wlhy inason zuwa gidan aunty Safna ko dan naga yaranta amma nasan Dady bazai barniba" Momy tace "kar nasake jin zancen zuwa gidan Safna ga bakinka idan ba haka ba zan hadaka da Dady'nku" Faisal yace "na bare Momy dan Allah karki gayamai kinsan inason yasaimin mota idan na gama prmry" Momy tayi dariya tace "to kadaina, wai ma kayi sallar magrib ne Faisal?" Faisal yace "tare da Ya Jabbar ma" Momy tace "yazo kenan?" Faisal yace "tun tuni ma tare mukayi sallah yana dakinsa" Momy tace "to kaga tashi kaje parlor ni zanyi sallah idan na idar zan fito muci abinci" Faisal yatashi yana dariya yana "ashema Momy kece bakiyi sallar ba" Momy tace "zan kamaka ai" ta karbarta sallar.

Hafiz daya kama hanyar gidan malam baiyi parking ba sai gidan a waje ya tsaya yakira mlm salman yace ya iso gidan. Mlm salman yace "to gani nan" mlm salman ne ya shigo ya tarad suna wasa da Aisha matar sa yace "lallai kinsamu yara yau wannan wasar haka ko abar miki su ne?" Ayman tayi saurin ciwa "eh abarmu a nan" Aisha tayi dariya tace "eh idan Momy'n su zata barmin mizai hana naso ko kuwa malik bakace komai ba ko bakaso abarka a nan?" Malik yace "inaso aunty" mlm salman yace "kunga kuzo muje ga abbanku can yazo" Ayman tace "yeeh ga Abi yazo malik zo muje" Aisha tace "lallai Ayman tunda Abi yazo zaku barni ko" Ayman tazo dai-dai kunnin Aunty Aisha tace "zamu dawo ai zan cewa Momy adinga kawomu a nan duk ran weekend" aunty Aisha tace "Allah Ayman promise?" Ayman tace "I promise aunty" aunty Aisha tace "to kuzo kuji" ta jaho hannunsu duka suka shiga daki. Mlm salman yace "to nidai idan kun gama ina waje kizo dasu" yafita. Side dinta ta shiga dasu ta dauko wata leda tace "Ayman karbe wannan" Ayman ta amsa ta buda, wowwww! Ayman ta furta tace "chocolate nd sweetπŸ˜‹ kai aunty mungode fa" aunty Aisha tayi murmushi tajaho hannunsu suka fito. Su Ayman sai hannu sukema aunty Aisha, Hafiz yajasu suka bar wajan.

Kubiyoni kusha labari✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatttπŸ’…

{ luv u all sweet friend😘😍😍}
[10/23, 3:17 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„
*BAKIN IYAYE*
πŸ‘„πŸ˜­πŸ™†
*Na*
~Mrs phareesy~😘
3⃣9⃣

Zainab ce ke zaune kan kujera a parlor da cikin ta wata 6, tana kallon wani film a *Arewa24* wanda sukeyi shirin na matu'kar burgeta wato *Dadin kowa*. Haj saratu ce ta shigo tana waya da Alh. C,,R,,O. Bayan tazo da zauna kan kujerat da zainab take zaune tada cewa "angama ranka ya dade" ta katse wayar, tana cewa "sister kenan, kinanan kina kallon mutumin naki sallau ko" ta fada tana dari. Zainab tace "Aunty kenan kinsan jiya ina school bansamu damar kallon saba shine yau suke mai-mai nake dan kallawa" Haj saratu tace "hm lallai wannan cikin da kwazabar kallo yake" tafada tana mai nuna cikin zainab na yamata kyau sosai kamar ka dauketa ka guduπŸ˜‚.

Zainab tayi dariya tace "aunty kenan" Haj saratu tace "nidai ma ba wannan ba, Alh ne yace yanaso amai kunun geda" zainab tace "ok bakomai aunty bari naje kitchen na dafa masa" Haj saratu tace "a'a zauna kisha kallo lafiya" zainab tace "ai da kibarshi kawai nayi zan iya ai" Haj saratu tace "kinsan Alh bayason aikin masu aiki, da hajara ma zata iya, bari kawai naji yanzu zan gama nadawo" zainab tace "to aunty adawo lafia" Haj saratu ta fice kitchen.

"Assalamu alaikum, Honey!!!!" Hafiz ya fada yana shigowa. Amina tace "lafiya ake kwalamin kira tun a waje?" Hafiz yace "sorry Honey, Allah nadawo ne a gajiye" Amina taja tsaki ta cigaba da latsar wayarta. Hafiz yace "Honey yunwa nakeji wlhy" Amina ta yamutsa fuska tace "acan din dakaje bakaci ba ne?" Hafiz yace "eh wlhy kinsan banason cin abincin waje" Amina tace "Allah ko?" Hafiz yace "kinga nifa wannan wasar badani ba yanzu kibari idan na waske sai muyi amma yanzu yunwa nakeji sosai" Amina tace "Bangirka da kaiba" Hafiz yace "haba Amina kamarya ina matsayin mijinki kice bakiyi girki daniba haba" tsawa Amina tayimai tareda da cewa "kaii Hafiz vari kaji nagayama nifa ba boya bace dazan dinga ma girki da sauran aikin gida, ni ko a gidanmu ba'a sani aiki sai dai a dafa a bani, tun yaushe nake gayama bazan iya dawainiya da kuba kaida wadannan kucakan yara? To kasani tun huri kasan inda dare yayima kaje ka nemo masu aiki dazasu iyama bauta amma ba Amina ba" rungumu ta yayi, yayi kiss dinta yace "haba Amina kinsan fa bana cin abincin masu aiki dan Allah ki tausaya min. Zan nemo miki masu aikin but bada girki ba" kwace kanta daga jikinsa tayi tamike tsaye tace "wllhy wlhy wlhy Hafiz sau nawa na rantse ma ? Wallahi bazan iya girkin gidannan ba" wayarta ta dauka ta fice fuuuuuh.....

Hafiz a inda tabarshi ya kusan 20mints yana dogon tunani. Cikin sa ne ya motsa yatuna da yaransa. A dakin su ya shiga ya tarad dasu a kwance gwanin ban tausai, yunwa tacisu. Da sauri ya nufesu ya. Malik ne ya sakarmai wani murmushi, Ayman tace "Abi dan Allah a maidamu gidan ummi gun aunty safiyya nan ba dadi" Hafiz yace "to Ayman" malik yace "Abi yunwa nakeji sosai" Hafiz yace "bakuci abinci bane?" Ayman yace "tunda muka dawo daga school bamuci komai ba" Hafiz ya tausayawa 'ya'yan sa (Hafiz yama manta da akwai Safna a duniya kwata-kwata baya maganar ta) yace "kuzo muje" wanka ya musu tare da shiryasu suka fito parlor. Anan suka tarad da Amina tana waya da Momy mamar ta kenan. Tana cewa "ai mom komai yana tafiya dai-da-" katse wayar tayi sanadiyar ganin Hafiz tareda su Ayman. Hafiz ne yace "Honey zamu gidan Ummi" kallon sa tayi ta zubar a kasa tace "a dawo lafiya" Hafiz yace "Allah yasa" suka fita.

Amar ne yashigo tareda cewa "Aunty amarya ananan ana kallon?" Yana dariya ya zauna kusanta. Zainab tace "eh Amar ya aikin?" Yace "Alhamdulillah wlhy yau ke kadaice a parlor ina momcy? Zainab tace " tana kitchen tana acikin kunu kasan babanku da sun kunun geda" Amar yace "Hakane wlh ai dad akwashi da sun kunun nan kuma fa ko dadi bashida" ya yamutsa fuska. Zainab tace "Kaine dai bakasan dadin sa ba" yadan kifa Kansa kan hannun kujerat yace "kawai abune dai irin na dad ai kuma banga kuna shaba".

Sadiqa ce ta shigo dawowarta daga school kenan. " Yaya Amar ina huni?" Tafada tana mai kama hanyar dakinta. Amar yace "kee zo nan" sadiqa tatako tana murguda baki tasan maganar daya ce. Amar yace "akaina zaki tsaya ne?" Yana mata tsawa. Da sauri sadiqa ta zauna tana yamutsa fuska yace "ni kadai kika gani a parlor'n? Ita wannan bazaki gaida ta bane?" Sadiqa ta murguda baki tace "banganta bane Ya Amar".

Tassssss..kakeji mari. Zainab tace " haba Amar miyassa ka mareta?" Amar yace "aunty Amarya kibarni da ita kawai wlhy saina gyara musu zama a gidannan itada Rahma" Zainab tace "ai da baka mareta ba kabarta kawai" Sadiqa anan ta dinga kuka, Amar yace "zaki bar gurinnan kosai ba tattakaki? Stupid kawai". Tashe tayi zata tafi sai ga Haj saratu tace " Mike faruwa ne inajin yaya tun a kitchen kamar harda k'arar wani abu?" Amar yace "Momy wannan yarinya idan vatai hankali ba saina gyara ta a gidannan" haj saratu tace "wai minene? Amar yace " Rashin kunyar da sukema aunty amarya yayi over a gidannan ita da Rahma, yazata zo ko gaishe da ita bazatayi ba wai har ni zatace ma bata ganta a parlor'n nan ba" Haj saratu tace "kamin dai-dai Amar. Ke kuwa idan kun fasa ba halattatun 'ya'ya bane. Kuma zan gayawa mahaifinku idan yazo" Amar yace "Momy basai ma kin sanarwa Dady ba ni nan zan gyara musu zama wlhy" Zainab dai tana zaune batace komai ba. Haj saratu tace "Zainab kiyi hakuri da duk abinda yarannan zasu miki kar ki sake ya shiga a ranki" Zainab tace "ba komai aunty Nima ina Baku hakuri" Amar yayi tsaki ya fice dakinsa.

Uncle Usman ne zaune a office yana rubuce-rubuce. wayarsa ce tayi ring akan screen din an rubuta *Dr I.S* dagawa yayi yana mai cewa "Dr ya aikin?" Can bangarin "Alhamdullah" yace ya aikin Yaya Hashim fatan an dace?" Whatt😳 innalillahi wa'innailaihirraji'un!!! Wasu zufane suka karyo masa sharkaf, w gegece yace "Sun mutuuuuu??????????????????".


Kubiyoni danjin amsar✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatπŸ’…

{luv u all friends}😘😍😍
[10/23, 3:17 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„
*BAKIN IYAYE*
πŸ‘„πŸ˜­πŸ™†
*Na*
~Mrs phareesy~😘
3⃣8⃣
*Amadadin yan wannan group nawa mai taren albarka wato πŸ’ManshatπŸ’… NovelsπŸ“š ZallahπŸ‘ŒπŸ» Muke muku murnar kammala novels dinku ~Dear Afrah~ JUMAYMA (yar bincike) nd ~Sis Nuceey luv~ OMAR KO FAROOQ❓ hakika munyi k'okari sosai Allah yabiyaku ya kara basira da zakin hannu😘*

Washe gare tun da asuba su Dady suka fito domin tafiya England. Dady ne shida zuri'ar sa kaf a harabar gidan.

Dady yace "to mukan zamu tafi" uncle Usman ne yace "Yaya Allah yakiyaye hanya, yakuma sa ayi a sa'a" uncle Farooq ma haka yafada. Duk hurin aka amsa da Ameen. Bayan duk su Umma matar uncle Usman kenan da Ammi matar uncle Farooq. Duk sunyi bankwa na da momy tare da hugging din junansu. Momy tace "har yau wa gobe dai ina mai dad'a baku amanar auta na Faisal, dan Allah kukular min dashi bisa amana".

Mota biyu ce suka shiga dayar Dady da yan uwansa uncle Usman da uncle Farooq wacce driver ne ke ja. Sai dayar kuwa itace Momy take ciki tareda Jabbar da Umma matar uncle Usman.

A haka suka kai airport, acan suka tarad da Dr I.S basu jima ba jirginsu ya tashi sai England.

A gidan Ummi kuwa yau shirin biki kawai akeyi anyi komai da komai da yake ba wasu event bane za'ai.

Safiyya ce itada su Ayman sai shirya su take zasu je school, su Ayman duk da juriyar su amma sun kosa suga ummar su wacca har yanzu ba'a ko maganar ta a gidan sbd Ummi tace abarta har ta gaba abinda take,tayu ma yaji ne tayi takoma gidansu. Ayman ce tace "aunty Safiyya har yanzu Momy bata dawo bane" wadansu hawaye ne suka zubu mata lokaci guda tace "Ayman zata dawo ne gode karki damu kinji" Ayman tace "ni aunty safiyya inaso naga Momy" Safiyya ta rungumo su duk har malik da shi harya barma Allah ya daina kuka yanzu tace "kuyi hakuri Allah zai saka muku akan wannan al'amarin" malik yace "aunty miyassa kike kuka?" Safiyya tayi saurin share hawayen ta tace "ba komai karkuyi latti bari na shirya ku" tufafi tasaka musu tareda dauko school bigs dinsu ta dauko musu suka nufo dinning.

Amina ce a kan dinning tana breakfast kasancewar akwaita da ci kamar garaπŸ˜‚ shiyassa take rigan kowa breakfast a gidan.

Isowa sukai a dinning table din can dayar chairs dake gewaye da table din ta aje musu school bags dinsu, ta zaunar dasu kan sauran kamar yadda ta saba saboda itace ke lura dasu sosai a gidan. Chicken pepper soup ne sai tea nd bread da kuma sweet patato ball, bayan Safiyya ta bode kulolin da ke a jere kan table din tayi wani wawan tsaki tare da cewa "wayyo Allah na manta da indome din Malik wlhy" Ayman tace "Nima aunty safiyya zanci indomen yau" safiyya tace "harda me Ayman?" Tace "eh aunty banason wannan" ta nune abincin da Amina keci. Safiyya tace "karku damu yanzu zan hado muku ita kinga ba huyane da ita ba yanzu zan dafa cikin 20mints" mtwzss Amina taja tsaki ta ce "aikin banza adaiyi agama da wadannan agololin" har safiyya ta juya ta nufe kitchen ta dawo tace "kee waya saka wannan k'azamin bakin naki? Ubanwa yayi dake dazaki sakomuna baki acikin magana? Wai ma to dakike cewa agololi acikin ke da su waye agolan?" Amina tace "kinsani ai kuma" safiyya taja tsaki tace "ke kinsan sunfiki a gidannan SBD su gidan babansu suke kuma gidan kakarsu gidan kakansu, kefa? Ba dangin iya bale na Abba, banza kawai" ta juya ta nufe kitchen tabar Amina a tsaye tana famar jidali. Can kuma tajuyo gun su Ayman tace "kuko dan ubanku zan hadu daku wallahi sai na gyara muku zama" taja tsaki tabar wajan.

Yau dai ta kama ranar assabar inda jama'a da dama sun halacce dauren auren *Hafiz Abubakar Mai Makka* da *Amina Sulaiman Mai Makka* akan sadaki dubu hamsim.

Ansha biki an rak'ashe wanda a dare aka dauke amarya zuwa gidanta da yake a *Mabera* daga can ne aka huce party. Basu da dawowa ba sai karfe 1:00am bayan sun dawo gida kowanne ya huce dakinsa ya watsa ruwa. Amina kuwa wani mayen wanka ne ta dauka cikin night gown iya gwaiwarta ta tsaya ta hau gado ta kwanta bata jima ba Hafiz ya shigo shima yayi shirin bacci. Nidai Manshat a nan na rufo musu k'ofar na tattara yan komatsaina na fice.

Safna kuwa tana gidan Alh kabir ba uhm bale magana, kowa kallo kawai take biyarsa dashi Haj Fatima ce ke dawainiya da Safna.

Zaune suke itada mai gidanta wato Alh kabir tace "Alh ya zamuyi ma wannan boyar Allah?" Alh kabir yace "Haj bamuda mafita wacce ta huce mu rungume wannan boyar Allah abisa yar uwa a garemu tunda bamusan taba bamusan kowa nataba yar nan garin ce ko ina oho" Haj Fatima tace "yawwa Alh ina jakar kayanta da muka tsinta a motar ta inajin baza'a rasa wayarta ba kaga sai mukira muji" Alh kabir yace "hakane kuma fa Haj kinzo da shawara mai kyau" suna a dakin ki nace ladi ta saka a waldrop je ki dauko" haka Haj Fatima ta tashi taje waldrop ta dauko handbag din safna, akai rashin sa'a ba waya a ciki ba wata sheda da zata taimaka musu hurin gane yan uwan Safna.

A gidan Hafiz kuwa soyayya ake zubawa zallah inda Hafiz duk ya zauce akan Amina ita kuwa sai nuna isa take tana batsewa. Yan aiki aka samo mata SBD tace ita baxata iya aiki ba dan ko a gidansu bata aiki. Haka Hafiz jiki na rawa yaje yasamo mata yan aiki.

Kubiyoni✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatπŸ’…

{luv u all friends}
[10/23, 3:17 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„
*BAKIN IYAYE*
πŸ‘„πŸ˜­πŸ™†
*Na*
~Mrs phareesy~😘
4⃣0⃣

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" kadai uncle Usman ke nanatawa. Office din yafito agegece yashiga mota.
Gida ya koma can ya sanar musu da mutuwar su dady da momy a hadarin jirgin sama. Wannan shine sakon da Dr I.S ya gayawa su uncle.
Bakin ciki da tashin hankali marar adadi ne ya bayana acikin wadannan family ganin mutuwar Dady da Momy. Wanda yasa Jabbar harda kwanci a asibiti, su uncle ma sunyi koka wanda bai misiltuwa, sunji bakin cikin rasuwar dan uwansu da matar sa.

Hafiz kuwa tafiya yayi da su Ayman gidan Ummi acan sukaci abinci basu dawoba sai dare.

A gidan Alh kabir. Safna har yau bata canza zaneba idan kaganta bakace tana cikin wani hali ba. Haj Fatima abu duk yabi ya dameta.

Safna ce zaune a parlor tana kallon TV ta maida hankalin ta akan TV'n kamar mai jin abinda suke fada. Ganin shigowar Lukman ya huce fuuuuuh! Yasata juyawa kallon sa. Bayan sun kammala labarin su sai kuma suka fara sanarwar kamar haka:

*A yau muka samu labarin rasuwar babban dan kasuwar nan wato Alh. Hashim Al'ameen da matarsa sakamakon faduwar jirgin sama ayanyar su ta dawowa daga England. fatan Allah yayi masa rahama*

Juyowar da Safna zatai taga an nunu pic din *Dady* wani iho ta saki wanda koni kaina Manshat saida na tsorata.....

Haj Fatima na a daki tajiyo ihon Safn, jikinta na bari kamar zata zame ta hauro kasa Allah ne kadai ya tsare ta da faduwa kasa..

Safna ta tarad a tsaye kan TV tana nunin TV'n tana kuka mai ban tausayi nan aka dauke huta. Haj Fatima bataga pic din ba.

Dai-dai ita ta tsaya tarugumo ta tana lafiya? Safna kuwa ta kara zubewa kanta tana wani kuka tana kiran "wayyo IYAYE na" gaban Haj Fatima ne ya fadi tareda godiya ga Allah tace "iyayen ki kum-" Alh kabir ne ya shigo yace "Haj kinanan kina aikin ko" ganin Safna na kuka mai sauti yasa yakaraso. Haj Fatima tace "Alh ta warke, tayi magana yanzu sai dai kuma batakoma cewa komai ba" Alh C,,R,,O ne ya shigo tareda sallama yace "Kabir kabarni a tsay-" ganin Safna yasa mai ida maganar saba. Tsaye Safna ta tashi ta nuna C,,R,,O tace "C,...R... kaiπŸ‘‰πŸ»πŸ‘‰πŸ»πŸ‘‰πŸ»" luuuuuu ta zube kasa somammiya.

Haj Fatima tabita a kasa tana "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un""""" Alh kabir shima ya rikice but yace "Yaya ban gane ba, dama kasan ta ne?" C,,R,,O yace "dama itace wanda kuka taimakawa kabir" "eh itace kasanta ne?" C,,R,,O yace "to ai itace yayar Zainab wacce nacema ta bata yau tsahon wata biyu ba labari" Alh kabir yace "Allah mai iko itace wlhy yaya, to amma mi yasa ba'a nrmeta ba har tsahon wata biyu Yaya"? Alh C,,R,,O yace " yanzu dai ba wannan ba idan ta farka zakuji komai" ruwa aka dauko aka juye mata a jikinta, wani sassanyar ajiyar heart tayi tareda farkawa tana hawaye. Haj Fatima tace "Safna ki kwantar da hankalinki ki daina kuka ki gaya muna labarinki idan kina neman taimakon mu, muku insha'allah zamu taimaka miki, munaso muji labarin rayuwarki" wasu hawaye ne kuka kwararo mata ta fara da cewa:

*Da farko nidai sunana Safna Hashim Al'ameen.............* har zuwa karshe ta kwashe komai ta gaya musu.

Sun jinjinama al'amarin kuma sun tausayawa Safna sosai, Haj Fatima harda hawaye akan tausayen Safna.

Alh kabir yace "hakika acikin labarinki akwai abun ban tausayi da al'ajabi da kuma cin amana hadeda wa'azi, lallai tabbas kema kanki kin tafka *babban kuskure* na bijirewa umurnin iyayenki, suma IYAYEN naki sunyi *kuskure* na yimiki *BAKIπŸ‘„* hakika *BAKIN IYAYE* yana tasirantuwa ga yaransu. Kuma ke kanki kinga illar kin bin umurnin IYAYE, tabbas ba wata riba da mutun zai samu a duniya matu'kar ya bijirewa umurnin IYAYEN sa iyaye abin bine saboda aya tazo acikin alkur'ani cewa: *Uban gijinka yayi umurni kada ku bautawa kowa sai shi, kuma IYAYE mu kyautata musu* saboda haka su IYAYE akuda yaushe umurnin su akebi ko kanason abinda sukeso ko bakaso. Sa'annan insha'allah zamuyi bakin kokarin mu na ganin mun dai-dai taji tsakanin ki da iyayen ki, haka shima mijin naki dan ki koma gidan mijinki uban 'ya'yanki". Wani tausayinta ya kama C,,R,,O na ganin yanzu ta zabe iyayenta akan mijinta amma kuma yanzu ne lokaci ya k'ore mata saboda iyayenta basa raye.

Alh kabir ya cigaba da cewa" "Safna munan da kike gani mu muka tsintoki ne a kan titi kinyi accident muka kaiki asibiti watanki biyu a gidannan, kuma wannan da kike gani wato Alh Aminu Yaya nane shi uwa daya uba daya kuma shine mijin kanwarki Zainab"

Kukan da take boyewa ne yaci karfinta. Haj Fatima tace "kiyi hakuri Safna insha'allah komai yazo karshe kinjiko ki daina kuka" Safna tayi musu godiya sosai haka Alh C,,R,,O ma tamai godiya.

Alh kabir yace "ba komai ai duk wanda ya tai make wani sai Allah ya taimake shi, yanzu abinda ke akwai Haj kije kushirya ku fito muje gidan nasu".

Haj Fatima tace " to Alh " haka suka shiga itada Safna sai sharar hawaye take. Suka shirya tsaf, suka fito.

Mota suka shiga Alh kabir ke a mazanin driver sai Alh C,, R,,O a mazaunin bai vima driver sai Haj Fatima da Safna a baya.

Haka suke tafiya ba mai cewa uffan. Sai ma Alh C,, R,,O dayake ta tinanin abinda Safna zataje ta tarad a gidan nasu a yau.

Basuyi parking ba sai gate din gidansu Safna, daya cika da parking-parking din mototi na alfarma, hankali Safna yayi mugun tashi amma ta daure. huri suka samu suma suka Parker motar tasu. Fitowa sukayi safna sai kallon mototin take kamar wadda ta fito daga rugga. Tana tunanin wa ake ma aure a gidan nasu? Can ta tuna da *intisar* diyar uncle Usman kenan, tace "kai makuwa intisar ba domin kuwa bata isa aure ba to waye?" Ta tambaya kanta.

Haj Fatima tace "Safna mikikewa tinani haka" Safna tace "ba komai mama" cikin gidan suka shiga. Nanma hankalin safna ya tashi ganin dubban mutane a zaune kai da ganin zaman basu kasan ba lafiya ba. Alh kabir ya dube dan uwan nashi dubin tuhuma ganin hankalinsa bai tashiba da ganin wadannan mutanin.

Haj Fatima da Safna suka isa cikin gidan. Ganin kowa azazzaune ya kara tabbatar mata da ba lafiya ba, duk hankalinta a tashe.

Zainab da tsulun cikin ta tataso ta rungume Safna tana kuka mai ban tausayi nan ne fa Safna ta gidime tana "lafiya Zainab fada min mike faruwa na ga mutane a ko'ina wasu na kuka pls n pls Zainab" takarasa maganar da wani iho, Zainab ta kara sautin kukanta tace "aunty Safna Dady da Momy sun mutu a hatsarin jirgin sama" Safna tace "innalillahi

Please Login or Register in order to submit comment