Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*Yusra super market* wanda yahadu iya haduwa. Parking tayi suka fito suka haura sama.

Hafiz ne da Mubarak cikin mota, Hafiz yace "wace super market din zamu je ne" Mubarak yace "wadda muka saba zuwa mana" Hafiz yace "kai ni yau naji duk banason zuwan can, kawai muje *Double 7* mana" Mubarak yace "Allah yanzu ancin masu hurin kaya masu kyau muje can" Hafiz yace "yau kaida super market dinka kamanta kanaji da *Double 7* Mubarak yace " Adaba" Hafiz yace "to bari muje kawai" afili ama azuciyarsa kamar ana dakamai ganga a cikin ta" Mubarak ne yakatsemai tinani da cewa "wai ma baka sanarmin mizakai acanba? Kuma wazakaima shopping" Hafiz yayi yar ajiyar heart yace "Aure zaniyi a wannan week din" Mubarak dake driven baisan randa yasaka birki ba yakalle Hafiz daya tsorata ganin Mubarak nason kashesu yace "Hafiz lafiyarka kuwa? Mi Safna tamane dazakai aure a wadannan shekarun?" Hafiz yadan kallai irin kallon ban waje, yace "aure nakeso nayi ku zaka hanani ne? Mubarak yace " haba Hafiz duk kwata-kwata yaushine kai auren fari dazaka koma wani sabon auren" Hafiz yace "kai banason shishshige a lamarina kuma aure ba fashi kasani a wannan week din" Mubarak yace "Wacece zaka aura ne" "Amina" yabashi amsar kai tsaye. Mubarak yace "Badai ta gidanku ba Hafiz" Hafiz yace "Kaiiiii ya isa hakan idan zaka min fatan alkhairi kamin idan kuma zaka cigaba da min wadannan banzayin maganganun to kaficemin a mota tun muna sheda juna" ya kauda kai. Mubarak yasan halin mazan nashi yace "ba haka nake nufiba kayi hakuri Allah yabada sa'a ina ma fatan alkhairi" Hafiz yace "anan zamu kwana ne ko sai sarkin zama ya iske mu?" Mubarak yace "mazahh zama dakai sai ni" yana mai jan motar suka dau hanya.....

Safna dasu Ayman sai yawo suke acikin super market din adauko wannan a dauko wancan. Saboda Hafiz yabasu kudi isassu. Malik ne ya ce"Momy baki sayamin ball ba" Safna tace "oh namanta wlhy malik but muje nadauko ma" suka koma wani lungu dake cike da kayan wasan yara.

Basui parking ba sai *Yusra super market* fitowa sukai a tare a dai-dai inda Safna tai parking da motatta shima nan yayi parking dintasa, bai kula da motar bama sam bale number motar kasan cewar motocin sunada number's. Cikin super market din suka haura.

Kaya suka fara kwasa kamar ba gobe. Safna bayan ta daukoma malik ball da wani doki mai kyau, Ayman tace itama asayamata teddy Safna ta dauko mata duk suna rungume da abinsu. Jiyowa sukai gun night gown zata sayama kanta. Ayman ce a gaba Safna na jeye da hannun malik dayan na jeye da basket dasukai mai uban lodi. Hafiz da Mubarak kuwa suna tsaye a hurin night gown suna kwasa. Mubarak ne yace "Kai Hafiz wannan amaryar kuwa zata sha kaya, wannan kayan hak-" dai-dai su Safna sun kawo hurin, Ayman ce ta watsa da gudu ta rungume Hafiz tana Abi " Hafiz dayake rice ta wata sleep gown maroon jin anrungume shi yasa yadago kai dan ganin ko wanene , wazai gani.......😳 Ayman datai mai wata wawuyar runguma. Hafiz baki na rawa yace "Ayman keda wa" tace "nida Momy mana" tafada tana mai juyuwa ta kalle Safna. Sai sannan Hafiz ya lura da Safna da tai mutuwar tsaye kasancewar taji maganar Mubarak sarai a kunnenta, sai dai neman gasgatawa da take but zuciyarta taki ta yarda, duk da dinbin sayayyar da tagani a basket tasan sarai ta macece gasu inner wears dinnan datagani. Hafiz duk da ya tsorata ama dayake namijin duniya ne sai ya faske sai kallun safna dayakeyi, ita kuma kallunsa takeyi tana kallun basket dinnan. Mubarak shumane kawai baiba a hurin sai gumin daya ketomasa.

Saboda bakin ciki Safna batasan randa taja hannun su malik ba suka bar wajan. Batareda ta idar da sayayyar ba ta fice. List din kudin akai mata ta biya ta fita. Inda tai parking motar ta takoma nanne talura da motar Hafiz da aka sakawa *H NA MAKKA 02* takara tabbatar da motar Hafiz ce, wani bakin ciki yakara lullubeta tashiga motar taja ta bar wurin duk motanin hurin kallunta ake yanda ta tada kura a hurin sai cika take. Wasu suce tayi iska ne da ita wasu suce kuma tayu rasuwa akai mata. Titi tahaura sai kwasar gudu take

Hafiz wayan cewa yayi duk da Mubarak ya gano tsintsar rashin gaskia a taredashi. Suma batareda sun kammala sayayyar ba suka fice. Bayan sun kama hanya ne Mubarak yace "Hafiz duk da bakaso a gayama gaskia a cikin wannan maganar sai dai kayi hakuri, ama a matsayina na amini a gareka zan gayama gaskia komai dacinta kuma duk lokacin danaga ka kauce, saboda shine zama na amana kuma zaman tare. Hafiz ko kallunsa baiyiba yace " idan dai gameda aure na ne to ni shawarar da zanbaka karufama yahunka asiri ka tsai dasu karka wahalar dasu, saboda ba tasiri zasuyi a guna ba" Mubarak yanisa yace "Hafiz tsakani da Allah baka kyautawa Safna ba, wannan abun daya faru yanzu a super market dinnan shiya tabbatarmin da baka sanarwa Safna zakai aure ba sannan duk wannan dinbin sayayyar damukayi ba na Safna a ciki, shin Hafiz miye ribarka idan ka sakawa Safna da wannan abin? Katunafa Safna tasoka randa kaf danginta suka tsaneka! Safna tama halacce dataji zata iya baro IYAYENTA da fanginta a dominka Hafiz haba kayi tinani man-" shitttt! "Ya isa haka Mubarak idan kasan wannan maganar ce will you get out form car pls" Mubarak yace "dole na gayama gaskia Hafiz kokaso ko ka'k-" "I say get out in my eyes" a tsawace Hafiz ya fada. Mubarak yabude motar dareda fita yace "hmm man kenan zakazo kasaman" Hafiz ya fige mota yabar wajan ba ko kunya. Haka yabar Mubarak a tsaye gwanin ban tausai. Waya Mubarak yayi a gida yace a aiko da driver ya dauke shi. Nidai manshat ysbani tausaye kamar nayimai lift kuma dai nace bazanyi ba tunda Mubarak akwai naci. LoLolzzzzzzzzzz


Kubiyone danjin ina Safna zata hauraπŸ˜‚.

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatttπŸ’…πŸ½

Kuyi hakuri typing wahalaπŸ˜ͺ

*INA SONKU 'KAWAYE NA*😘😍
[10/23, 3:15 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~😘✍🏻
{3⃣4⃣}

*Assalamu alaikum*
*Zanyi amfani da wannan dama dan bawa makarantan wannan 'kan'kanin luttafin mai suna ~BAKIN IYAYE~ hakuri saboda rashin typing danayi kwana-da-kwanakki, hakan tafarune sakamakon wani mashahurin uzuri da ya gittomin amma insha'allah yanzu zamuci gaba daga inda muka tsaya da fatan kuna biye dani kuma zakuyi hakuri kuyimin uzuri. Nagode*

```K'ok'arinku ne My Aunty's @Rash kardam &Billy n. Abdul ```


Safna! A gidana yafurta a fili. Ita kuwa Safna duk da gaban ta yayi wawan bugawa amma ta daure ta gyara perkin din mota tana 'kokarin fitowa. Dady ne ya 'katseta a tsawace yace
"keee! Wlhy karki sake 'kafafuwanki su tako wajannan. Inaso kafin na kirga ukku kinbar gidannan kuma har abada bake ba gidannan.
Kukane yaci 'karfin Safna tana
" dan Allah Dady kayi hak-" sheeee!!! Yafurta a jidalance yace "banason jin muryarki Safna banason ganin ki a kusadani da kaf zuria ta, kifita daga gidannan kafin nakira police sufitarmin dake".
Momy ce ketafe tana ta'ko irin nasu na manya. Wayoyin Dady dayabari kan kujera tazo kawomai sakamokon kiran da akemai jimi-jimi. Alhaji! Alhaji!! Ta furta tana mai duban rumfar da Dady yake a tsaye. Tsaye tayi tana kallon bakuwar motar datagani kuma taga mamalakin ta bai fitoba, Dady tagani fuskarnan kamar ya hade sabulu. Gabantane yafadi sakamakon Safna data hango acikin motar sai zubda kwalla take. Da hannuwa biyu taa nunata dashi tana Safna! Wani irin abu taji yayo mata a zuciya saida ta dafe 'kirjinta, Dady yace "haj bar hurinnan kejiko" Momy da jikinta sai rawar dari yake tace "Alh kayi hakur-" haj nace kibar hurinnan. Dady yafada a tsawace sai da nima Manshat narazana. Momy jiki ba kwari tajuya amma inaaa!!!!! 'Kafafuwanta basa daukar gangar jikinta chak taja tayi tsaye tana zubarda kwalla.
Dady yace "zaki bar gidannan ko sai na kira police?" Safna da hawaye sungama wanke mata fuska da har sitarin motar ta sai da ya wanke da hawayen dake zubar mata. Tafito amotar ta kai gaban Dady tana mai durkusawa tace "Dady dan Allah kataimakeni wallahi kune gatana a duniya banida wanda yafiko idan kun k'ine Dady waye zai so ne?" Dady yace "yanzu kikasan haka sai yanzu da duniya tajuye mike kika tina da mune gatanki? To kisani mu bama buk'atarki a garemu munyafewa duniya ke kije can ki 'karata, kuma bakiga komai ba ma Safna yanzu kika faragani idan duniya ce wanda baizoba ma tajirasa bale mu bake ciki, ai duniya kawai ta isheki wa'azi" Momy kam zubewa tayi a 'kasa somammiya! Safna tayi gunta da gudu tana kwalla mata k'ara. Dady shima can ya nufa, da isarsa ya wawaso kwalar Safna ya wanka mata wani hadaddin mari dani kaina Manshat saida na rufe kunnuwana saboda kukan marin. Yace "wallahi idan har matata ta mutu to kitabbata kema kin mutu, idan kuwa tasame wata matsala to kisani sai nayi k'ararki" yayi wurge da ita sai da kanta ya buke motar ta. Yace "Abdullahi!!!" Mai gadi yazo da gudunsa. Dady yace "kafin na kirga uku kafitar da waccan k'azamar daga gidannan ko karasa aikinka, kuma idan kasake nakuskura nakoma ganin ta a gidannan abakin aikinka" yanufi Momy da har yanzu ko motsi batayi yadauketa yashiga ciki da ita. Mai gani jiki na bari yace "ke ke tashi bar gidannan kafin na hadamiki kokarar nan tawa" Safna da har yanzu tana kwance inda Dady ya wurgar da ita tayi yunkurin tashi amma jikinta duk a mace yake, ga kirjinta sai bugawa yake zuciyarta kamar tafito saboda bak'in ciki. Mai gadi ne yabuga mata tsawa yace "kee wallahi bazaki min hasarat aikina ba kitashi kifita tun kan Alh yafito" Safna taja motar tabar gidan tana kuka mai ban tausayi. Dady side dinta yanufa ya ajiyeta yadau waya yakira family doctor dinsu wato *Doc I.S marnona* yace mai gashi nan zuwa yanzunnan.

Safna tafiya take sai kuka take nan taji wani abu ya buge zuciyarta nan tasake titi motar ta buge wani icce. Ba kowa a hurin kasan cewar marece tayi duhu yafara saukowa.

Alh Kabir ne shida matarsa Haj Fatima suke tafiya a mota. Suna dan taba fira. Can Haj Fatima ta hango wata mota kamar ta sake titi ga alamu anyi accident ne. Da sauri tace "Alh kamar anyi accident a wajannan duba kaga" Alh kabir yace "accident koma Haj?" Haj Fatima tace "da alama fa waccan motar akwai mutun acikinta" Alh kabir yace "to ko zamu duba ne" Haj Fatima tace "mizai hana Alh" duk suka fito suka nufe motar, ga mamakinsu sukaga mutun aciki. Haj Fatima ce tace "Alh akwai mutun aciki kuwa kuma ga alama macece" Alh kabir yace "hakane wallahi, to yanzu miye mafita?" Haj Fatima tace "mafita dayace mu taimaketa" Alh kabir yace "kamar ya kenan?" Haj Fatima tace "mukaita asibiti mana" Alh yace "to to kidaukota muje bari najahu mota" tace "to" ta bude marfin motar tajawo Safna da ko motsi batayi, suka sakata a mota suka nufe *Specialist* da ita. Haj Fatima duk a tsorace take tace "to kuma miye yasameta ko wanine yabigeta ya gudu oho" Alh yace "ai sai tafarka tukunna musan dalili" Haj Fatima tace "Alh anya wannan boyar Allah tanada rai kuwa?" Alh kabir yace " allahu a'allam" sai dai mun isa asibitin zamuje daga likitocin" Haj Fatima tace "Allah kasa ta rayu dan daganinta tana cikin wani hali" Alh kabir yace "Ameen".

Kubiyo ni kusha labari✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatπŸ’…

I miss u all friends😘
[10/23, 3:17 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~
{3⃣5⃣}

Da wannan suka iso asibitin. Wani Dr suka sama suka gayamai yatai makesu sunkawo patient ne. Yace to yana zuwa. Dr I.s ne ke famar tattara takardun dake kan table sai sauri yake saboda kiran da Dady yamai. Dr imran ne yashigo office dinsa yace "Dr pls a patient is just brought to the emergency room nd she need an urgent attention" yafada yana mai dubin Dr I.s dako kallonsa baiyi ba. Dr I.S yabuga hannuwansa kan table din dake gabansa tare da furta "oh good! To be honest I am currently busy cuz, I was just called to attend another emergency. But I will be back shortly" Dr I. S yafada yana mai bin hanyar fita. Dr imran ne yace dasauri " look Dr please, this patient need an urgent attention, she may lose her life if nothing is been done. See how she is bleeding" Dr I.S batareda ya jiyoba yace "please imran wait for me now" yafita batareda ya wai-wayo ba. Dr imran mamaki ne taf a fuskarsa yasan Dr I.S bashida wannan halin to why not zaiyi wa wannan patient haka? Yatambaye kansa.

Dr I.S da fitarsa motarsa ya nufa yaja sai gidan Alh Hashim, da zuwansa mai gadi yaji horn sai da ya rega yagansa kasancewar yasan ko waye Dr I.S ya bude masa gate ya haura ciki. A falo yayi sallama amma ba kowa yadau wayarsa ya kira lambar Dady, a take yadauka yagayamai ya iso yana a falo Dady yace ya karasa daga ciki.

Side din Momy yanufa yatarad da Dady zaune. Tashi Dady yayi suka gaisa da Dr yace "bissimillah kafara aikinka kawai" Dr I.S yace "OK" kan Momy yahaura yafara gwaje-gwajensa bayan kamar 30mints yadago kansa yakalle Dady dayake zaune kan bed sheet yace "Amma Alh akwai abinda yafaro ko saboda naga zuciyarta ce ta buga sakamakon wani abin firgitarwa data gani" Dady yace "eh to akwai abinda yafaru but now bashine abun saniba inaso nasan mike damunta Dr?" Dr yanisa yace "to har yau dai batada matsalar komai sai jininta daya hau, shine dalilin faduwar da take samu idan taga wani abunda yake tadamata da hankali ko abin tsoro ko na firgitarwa. Kuma idan hakan bata daina faruwa ba to gaskia zan iya cema matarka zata iya kamuwa ciwon shanyewar barin jiki wato (strokes)" Dady yace "Subhanallah shanyewar jiki koma?" Dr yace "sosai kuwa sai dai bama fatar hakan amma gaskia sai ankula da bacin ranta" Dady yace bakomai Dr nagode" maganukka yabata tareda musu fatan samun lafiya, kuma yasanarwa da Dady nan da 30mints zata farka insha'allah. Dady yayimai godiya sosai yafita.

Asibitin yakoma yasame Dr imran a office ya buga tagumi. Dr I.S yace "What happens my man?" Dr imran yace "Nothing, kawai ina compas din wannan patient ne wlhy" Dr I.S yadan tabe baki kan yace "oya muje" Dr imran yashiga gaba Dr I.S yabishi a baya suka kama hanyar emergency room da Safna take a cikin tun tuni. Dr I.S ne yace "Subhanallah hakan take zubarda jini? Dr imran ya watsamai harara. Dr I.S yahau kanta yana fadin "daukomin wancan box din" Dr imran yadaukomai, yayi treatn nata agun da Dady yayi hurgi da ita, saboda tsananin bakin ciki batamasan taji ciwo a gunba gashi sai jini yake mata zuba gashin kanta duk ya wanke da jini harma da goshinta da tabugu ga glass din motar daya watsu a fuskanta duk tayi jina-jina da jini, kowaye kai idan kaga Safna a wannan lokacin bazaka shedata ba saboda jininda ke zuba a fuskanta,duk jikinta raunine. Plasta yasakamata a fuskar ya rufe ko ina da yayi raunin sa'annan yajuyo kan Dr imran yace "ina wadanda suka kawo wannan patient din?" Dr imran yace "Suna waje".

Alh kabir ne da Haj Fatima suketa sake-sake ko wannan boyar Allah tanada rai kuwa? Suna cikin hakane Dr yafito yace " Kone kukawo wannan patient wacce tai accident?" Alh kabir yace "eh mune Dr" Dr I.S yace "To patient dinku tana bukatar jini sakamakon zubar da jininta yayi" Haj Fatima tace "jini kuma Dr" Dr yace "sosai kuwa, nanda 30minta" Alh kabir yace "Innalillahi yanzu Dr yaza'ai" Dr yace "zaka iya bayar da naka agwada idan zaiyi ko na wasu yan uwan kafin nan da 20mints" Alh kabir ya dube matar sa Fatima. Haj Fatima ta d'aga masa kai alamar "Yes!" Alh kabir yace "bakomai Dr" Dr yace "yanzu zaka biyoni office domin a gwada ko zaiyi" Alh kabir yace "to Dr" Dr yajuya yabarsu a tsaye. Alh kabir ne yajuyo yakalle Haj Fatima yace "kinaga ba matsala Haj" Haj fatima tace tace bakomai Alh ai tunda muka kudiri niyar taimaka mata ai yanada kyau mu isa nufinmu, kumaduk wanda yataimake musulmi dan uwansa Allah zai taimakesa. Saboda haka na amince abayar da jininka asakama wannan matar" Alh yace ba komai nagode Haj Allah yasaka miki da aljannah" Haj Fatima tace "Ameen" yafice office din Dr".

Cikin ikon Allah jininsa yayi dai-dai da jinin Safna kamar an tsaga kara. Haka aka dibe jinin Alh kabir gora biyu aka sakawa Safna.

Hafiz kuwa bayan yakira Mubarak bai dagaba yayi watse da wayar kan bedsheet yacigaba da sabgarsa. Can kira yashigo a wayarsa mlm Salman yaga ansaka yadauka yanamai sallama. Tsan bangarin aka amsa bayan sun gama gaisuwa ne mlm salman yace "Hafiz kamanta da yaranka ne yau a mkrnt?" Tuma yayi daga kan bedsheet din yakai zaune, sai a lokacin yatina da Safna bata gidan kuma baiji motsin kowa ba, a mamakinsa ina Safna zataje har 8:30pm bata dawoba?" Mlm salman ne yakatsesa da cewa "bakace komai ba" nanfa Hafiz yashiga sosa kai kamar agaban sa yace "eh...eh ina busy ne shiyassa koma Momy'nsu tayi tafiya ne sam na manta da nakaisu a makaranta duk na sha'afa" mlm salman yace "ok dama nayi mamakine nagansu a bakin gate shine na wuto dasu gidana" Hafiz yace "OK nagode fa mlm gani zuwa yanzu in daukosu" mlm salman yace "to bakomai sai ka shigo".

Kashe wayar Hafiz yayi yana maijin wani bakin ciki. Mtwss yaja tsaki yasaka tufafinsa, key din motarsa yadauko element yadau hanyar *Bado* yana tafiya yana mamakin ina Safna taje? Can wata zuciyar tace dashi " kaida baka kula da lamarinta miye naka idan ma tabar duniyar ai kama samu damar cin amarcin ka cikin kwanciyar hankali" wani murmushi yayi wanda bashida maraba da dariya yakara gudun motarsa sai *Bado*.

Kubiyoni danjin labari✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatttπŸ’…

Luv u all friends😘😍😍
[10/23, 3:17 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~😘
3⃣7⃣

Gidan Ummi ya huce dasu Ayman. A falo sukaci karu da Safiyya, gaisad dashi tayi tare da rungume su Ayman tana murna. Hafiz kuwa fuskar nan turmuke yace "Ina Ummi?" Safiyya tace "Ummi tana ciki" yace "ok Amina fa?" Kallon tuhuma tamai tareda amsa mai a dakace "tana ciki" ta juya kansu Ayman tace "Ayman ina aunty Safna ne?" Ayman tace "Muma bamusan inda tajeba daga islamiyya muke" Safiyya tace "islamiyya kuma Ayman? Yanzufa 9:30pm ake magana" Ayman tace "ingaya miki aunty safiyya?" Hafiz yayi tsaki yabar wajan. Safiyya tace "kuzo muje daki" tajasu suka shiga dakinta tareda kunshin ledar da aunty Aisha tabasu.

Hafiz sama ya haura, kan gado ya taradda Ummi sai waya take tace "jirgen safe zaku shigo ko Haj? Yakamata kam saboda inason idan kun iso da huri kuka huta sai mu fara shirye-shiryen bikin tun huri" can kuma tace "to..to sai kun iso Allah yakawo ku lafiya" ta katse wayar. Duk abinda take Hafiz na kan kujerat mirror yana dannar wayarsa. Ummi tajuyo tace "son yanzu kake tafe gidan namu? Yadan sosa keya yace " eh Ummi bama ni kadai ba harda su Ayman" Ummi ta kai zaune tace "to ina uwar tasu taje?" Hafiz yace "nima Ummi bansan inda tajeba, kawai koda na koma dazun na tarad ba kowa a gidan" Ummi tace "bata gayama zataje wani gu ba?" Hafiz yace "eh Ummi bata sanar minba suma su Ayman sai yanzu na daukosu daga islamiyya, na dauka ma taje dauko su ne" Ummi tace "lallai ma yarinyar nan wato abinda take shirin yi kenan, amma karka damu kabar yaran a nan har idan ta gama gantalinta ta dawo gidan dan nasan batada gidan daya kai mata nan. Ni dama haka nakeso" Hafiz yace "to Ummi ni zan koma mu kwana lafiya" Ummi tace "Allah yasa" ya fita. Yaso ya hadu da Amina amma hakan bata faruba, baiso hakan ba dole ya tafi.

Washe gare da safe, Haj Fatima ta shirya kayan breakfast ta bawa lukman ya kawo asibiti. Ladi mai aiki ce ke jinyar safna. Har yau bata farka ba. Sallama akai ladi ta amsa tare da cewa "sannu da zuwa lukman" ta karbe kayan. Lukman yace "yawwa inna ladi ya mai jikin?" Ladi ta amsa da "da sauki amma har yau bata farka ba" lukman yadan yamutsa fuska saboda lukman a rayuwa tai bayason irin rayuwar iyayensa na kwaso wannan kwaso wancan, su ala dole taimako, shi ko a gida saida Haj Fatima tayi arangama dashi akan karya sake ya nunawa wannan boyar Allah halin rayuwar sa idan ba hakaba ransa zai bace. Yamutsa fuska yayi tare da cewa "to Allah yabada sauki" tareda dubin ta yana mata kallon ukku saura. Kasan cewar Ladi mai aiki tasan ko waye lukman tace jiki na bare "ameen..ameen " yabanke kofar dakin ya fita. Ladi wata sassanyar ajiyar heart tayi tareda gode Allah da yasa lukman baimata abinda yasaba ba wato fada.

A dakin safiyya kuwa ta saka su Ayman gaba sai labar tamata abinda yafaru suke har bacci yafara daukar Malik, safiyya tace "bari na dubu ko Ya Hafiz yananan nagayamai kuna jin bacci ko za'a barko nan" nan take Ayman ta fara murna tana tsalle, sakamakon bakin jinin Safna yajaza musu har Ummi yanzu bata son su kamar da. Safiyya falo ta fito a tunaninta ko su Ummi suna fira amma kuma bata tarad dasu ba. Side din Ummi ta nufa ta haura sama, Ummi ta tarad tana batun fitowa saboda Hafiz yace suna gunta. Safiyya tace " Ummi Ya Hafiz fa?" Ummi tace "ya tafi, ina su Ayman yace suna gunki?" Safiyya tace "eh nan zasu kwana ne? Ummi tace "eh su kwanta a dakinki ma" Safiyya tace "to Ummi sai da safe" Ummi tace "ok mutashi lafia"

Safna bata farka ba sai 12:00pm idanuwanta ta fara bodewa kafin nan takai zaune, wani matsanancin sarawa ne kanta yayi wanda yasa ta komawa kan gadon ta kwanta hawaye na zuba a idon ta. Ladi dake zaune gabanta tace "sannu boyar Allah kin tashi ne?" Kallo kawai Safna ta bita dashi. Ladi tace "ina zuwa" ta fita. Office din Dr I.S ta nufa ta tarad ya bode kofar kenan tace "likita ta farka yanzu" Dr yace "alhamdulillah yanzun ma zan duba tane muje" dakin suka karaso Dr yace "sannu kinji" nan ma kallo kawai tabi Dr dashi tana zubar da hawaye. Dr I.S Allah Allah yake akan lamarin wannan patient din, saboda yana tunanin tayi loosing memory nata, can kuma yace "Ya sunanki?" Safna ta kallai kallon tuhuma still bata amsa ba., Dr I.S ya girgiza kai tareda sake tambayarta "zaki iya tina da waye kikai accident?" Nanma bata canza zane ba, "oh good" yafada tareda juyowa ya dube Ladi yace "idan su Alh sunzo kice dasu su sameni a office" Ladi tace "to likita" ya juyo kan Safna da har yanzu kukan take yace "sorry stop crying please, zaki jazawa kanki matsala yanzu bakya bukatar kuka, saboda kanki kinji ko" nanma dai haka take Safna ko uffan batace ba. Dr yace "Allah ya kara lafiya" yafita.

Kubiyoni danjin labari✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Takun daiπŸ‘ŒπŸ»
Writer
πŸ’ManshatπŸ’…

{Luv u all sweet friend}😘😍😍
[10/23, 3:17 PM] β€ͺ+234 703 632 4075‬: πŸ™†πŸ˜­πŸ‘„*BAKIN IYAYE*πŸ‘„πŸ™†πŸ˜­
*Na*
~Mrs phareesy~
3⃣6⃣

Alh kabir ne shida Haj Fatima a zaune kan wasu fararin kujeru. Alh kabir yace "Haj ya kamata muje gida sai a turo mai aiki tazo ta kwana da ita zuwa gobe sai musan mafita" Haj

Please Login or Register in order to submit comment