Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zauna bama shida niyar fitowa."

Wata tsawa Abdallah ya daka masa mai firgitarwa , ba ƙaramin firgita Sadiq yayi ba dan a iya saninsa dadynsa baya ko yimasa kallon banza bare wanan tsawar a tsorace ya fito , shima driver dake gefe lamrin ya matuƙar bashi mamaki dubada irin soyayyar da Abdallah ke yiwa ɗan nasa katse tunanin yayi dan yaga sun shige ciki Sadiq ne a baya kamar wanda aka doka , dan ya firgita matuƙa ,



Gidane dai dai misali bazaka kirashi da gidan talakawa ba ,zadai ace gidan masu rufin asiri gidane mai ɗauke da ɗan madai daicin get sai filin tsakar gidan da yake malale da siminti daga can ɓangare hagu wani kasko ne guda biyu masu flawoyi ,ƙofar da zata sadaka da sashe matar gidan itace ƙofar dake kallon ymma kasancewar ƙofofi biyune kusan a jere , babu sashin da Abdallah bai sani ba dan haka ya shige ƙofar dake ɓangaren dama suma suka rufa masa baya , da sallama a bakinsu suka shige matar gidan na tsakar gida tana wanke wanke ta ga su Abdallah , washe haƙora tayi tare da cewa" lalle marhabun barkanku to kai Sadiq ka shiga dasu man jiki a sanyaye Sadiq yayi musu jagora zuwa babban palon gidan , zaune take a cikin ɗaki a gefen katifa taci kuanta ta godewa Allah musamman da sukayi waya da Sadiq ya faɗa mata a hotel ya kwana ta razana sosai , jiyo muryar mamy na kiran sunan Sadia yasata aiyanawa a ranta cewar ai harda Abdallah ma ,


Miƙewa sadiq yayi yahau bankaɗa labule yana duba islam wato autar mamy , bankaɗo na ɗakin da momynsa ke ciki yayi da sauri ya isa gareta ganin hawayen fuskarta yasa shi fara shre mata hawaye ,

Afnan dake zaune gefen Abdallah da sai yanzu ta sami damar yin mgna tace " ina mukazo ? gidansu momyn Sadiq ya bata amsa a taƙaice , jan bakinta tayi tai shiru kana ta zubawa sarautar Allah ido , mamy ce ta shigo hannunta ɗauke da jug na ruwa da food flaks na abinci ajiywa tayi a gaban su Sadiq kana ta zauna kujera mai kallon tasu , sauka yayi daga kan kujerar yace " mamy barka da yamma mamy ywwa barka ya gida ya aiyuka lpy lou Abdallah yace" Afnan ma gaisheta tayi kana shiru ya biyo baya , Abdallah ne yace " nakawo Sadiq ne , da alamun damuwa mamy ta dubeshi tace " Abdallah naji duk abinda ke faruwa yanzu dai inason kayi haƙuri dan Allah banda tone tone , sunkuyar da kai Abdallah yayi yace " mamy momyn Sadiq bata kyauta min ba wlh eh nasani , labarin bashida daɗin sake mai maitawa dan Allah kadubi darajar maraici ka maidata ɗakinta , Afnan sai yanzu ta gano abinda ke faruwa cikin sanyin murya tace "dama bakwa tare da mmn Sadiq? ko kulata bai yi ba shigowar momyn Sadiq da Sadiq ne suka shigo palon ."




Kallonsa ya kai gareta kana ya sada kansa ƙasa dan jiyakeyi kamar yaharbeta amma bashida mafita , kuma yana tausayawa rayuwar mutanen gidan kasancewar su masu ɗan ƙaramin hali , gashi mamy nason matsa masa oh Allah Abdallah yace " lokacin da yakai dubansa ga Sadiq ya kauda kansa gefe , shikam ya tsani zina kokuma ɗan zina ,sake kai dubansa gurin mamy yayi kana yace " da sharaɗi inhar ta amince bazata jemin da Sadiq gidana ba , wata razananniyar ƙara yasa tare da cewa" to waye mahaifina ki nunamin ."

Muryar Sadiq sukaji Afnan ce ta miƙe tare da riƙo masa hannu , cikin kakausar murya Abdalah yace " karki kuma gigina taɓashi ba jinina bane !!! timmm mamy ta faɗi sumammiya , da sauri Afnan da momyn Sadiq sukayi kanta mai adu'a nayi mai ɗibo ruwa nayi ,duk da haka Abdallah bai dena zazzaga bala'i ba , momyn Sadiq ce tace "inhar kazo kawomin shi ne to , inkuma kazo tayar mana da hankali ne sai ka faɗa , Afnan dai lamarin ya ɗaure mata kai ta rasa wane lamari ne ke shirin faruwa da rayuwarta ?" a zuciyarta take wanan batun , eh duk inda kika ɗauka haka ne , cewar Abdallah dan zan temaka na maidake wlh bacin tausayinki da nakeji babu abinda zai sa na maidake !!!, mamy na farfaɗowa ta tsinkayo maganarshi ta ƙarshe , cikin dauriya dajin zafin kalamin nasa tace " Abdallah abin bai kai ga haka ba mungode basai ka mayarda ita gidanka ba , daganan ta shige ɗaki , dukaninsu suna tsaye Sadiq ko yabi mamy ɗakinta
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com


*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION💦*

EPISODE 47 & 48

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Afnan da tun usulinta batason tashin hankali tafara kuka tare da durƙusawa a gaban Abdallah ta riƙo masa hannu , kana tace " dan darajar iyayenka ka kaida ta , bai yi magana ba sai ficewa da yayi daga ɗakin , momyn Sadiq kasa magana tayi sbda baƙin ciki Afnan ce ta rungimeta suka dinga kuka, bayan fitarsa driver ya shigo a guje tare da cewa hajiya mai gida na mota yana jiranki ,sallama tayi musu kana ta rufawa mai gadi baya , buɗe murfin motar tayi ta shiga suka miƙi titi , babu mai cewa kowa komai , shikam zuciyarsa tafar fasa takeyi kamar garwashi gaskiya da ba zina tayi ba zai iya mai data amma tuna abin ya kasance da haka yana ganin sai dai su haƙura kawai , horn ɗin da driver yayi ne ya tabbatar musu da cewar sun iso gida , buɗe murfin motar tayi da sauri ta fice tana kuka , tana shiga palo ta wuce bedroom ɗinta da gudu ta faɗa gado tana wani irin kuka mai cin rai , ita kam tafi tausayin Sadiq ɗin a kan mahaifiyar tasa , can kuma wata zuciyar tace " ke meye naki na tausayin sa bayan bakida alaƙa dasu? gaki a cikin matsala ,


Kawar da zancen tayi ta ɗauko wayarta , lambar momy ta dannawa kira ring ɗaya ta ɗauka , sallama Afnan tayi bayan momy ta amsa Afnan tace "ya dady da anty suna lpy momy tace .

"lafiyarki kuwa Afnan?" naji muryar taki tayi kama da ta mai kuka , kuma dai dai ta muryar tayi kana tace " llah momy wlh ba komai nayi missing ɗinku ne inason zuwa , momy ce tace " to shine zaki ɓata ranki ? ki kwantar da hankalinki muna lpy karki dinga tada hankali kinga ba ke kaɗai bace , waro ido Afnan tayi kana tace " momy nikaɗai ce man au wai kun ɗauka cikine da ni ? eh momy tace " hmm wlh banida komai , cewar Afnan , momy ce tace " Allah zai kawo ki kwantar da hanlalinki kinji , to tace " tayiwa momy sallama , numbar anty ummi ta kira dan tasan tayi laifi yaushe rabon da suyi waya."


Lokacin taga gidan Haisam tana cin azaba gurin mama batada wata uwa banda anty ummi yanzu kuma da ta auri burin iyayenta shine zata watsa mata ƙasa a ido ina , jin an ɗaga wayar ya sata cewa aslamu alaikum , daga ɗayan ɓangaren anty ummi tace " walaikissalam Afnan kinanan? uhm anty da farko dai ayimin afuwa dan Allah , nasan ban kyauta ba , share zancen anty tayi da cewa karki damu yarinyata ,


nan suka kuma gaisawa kana sukayi sallama , turo ƙofar da Abdallah yayi ne yasata kai dubanta ga inda ya ke , tsaye yake a bakin ƙofa ya zura hannayensa cikin aljihu , ya kallonta.


Zaune suka a wani tsararren palo wanda yaji kayan more rayuwa wannan palo shine zakaji ana yiwa kirari da aljannar duniya , hajiya Maryam ce zaune kusada mai gidan nata wato Alhaji Aliyu mai nera , Alhaji Aliyu mai nera shaharaten mai kuɗi ne na ji da gani , sananne ne kowa ya sanshi a babu wanda zaka yiwa kwatancen sunansa yace " bai sanshi ba , shine uba ga Husna ƴa ɗaya tilo da Allah ya basu ,Husna tayi karatu sosai musamman ma na boko , har yanzu taƙi fito da mijin aure da zarar Alhaji yayi magana mahaifiyarta zatace guda nawa take karya takura mata , akwai wata rana tana cikin tafiya a motar ta , sai motar ta sami matsala , tana tsaye bakin titi motar Abdallah tazo wucewa , bayan ta sa masa hannu alamar ya tsaya ta roƙesa da ya temaka ya rage mata hanya zuwa gidansu,


Suna cikin tafiya tana satar kallonsa dan Abdallah kyakyawane in baku manta ba , suna isowa tace " ya bata lambarsa , baiyi mata musu ba ya bata har ya zamo daga wanan rana tana kiransa suna gaisawa , kwanci tashi asarar mai rai , Husna ta fara nunawa Abdallah tsantsar soyayya tun bai san tanayi ba har yazo ya gane , wata rana yazo gidansu badan yaso ba sai cewa da tayi zasu gaisa da mahaifiyarta , yake gaya mata shikam yanada mata , Husna tayu baƙinciki amma kadancewarta wayayya ta nuna babu komai gashi yac" bai shirya yin aure nan kusa ba , itadai a tata zuciyar ta ƙudiri aniyar auransa ko ta wane hali wanan kenan.


Alhaji ne ya dubi Hajiya Maryam yace " lokaci yayi da zan fitarwa da Husna mijin aure sbda lokutan da na ɗaukar mata sun cika , kukan da Husna ta fara ne yasa su Alhaji juyowa kallonta , kuma bai fasa maganar ba , Hajiya Maryam ce tace "a wanan karon ina goyon bayanka ai tanada samarin ruwan ido ne yasa take rainawa mutane hankali , Husna batada zaɓi banda dole ta karɓi zaɓin iyayenta amma kuka yaci ƙarfinta ,tashi tayi da gudu ta haura samma inada ɗakinta yake , ta faɗa gado tare da sakin wani sabon kukan , tunanin Abdallah da yayi mata nisa tafara yanzu yazanyi duk wata hanya da zanbi dan haddasa musu fitina na kasa dole nabi abinda su hajiya sukeso , da haka bacci mai nauyi yayi nasarar ɗaukarta ."


Abdallah ne ya ƙaraso kusa da Afnan ya ɗauketa ya ɗora akan cinya kamar ƙaramar yarinya , raɗa mata yayi a kunne wai two days mai ya sami baby na ne tadena bani kulawa ?" narkewa Afnan tayi kana tace " nikam babu ruwana da kai , mekuma nayi ? cewar Abdallah , Afnan ce tace " dan me bazaka dawo da matarka ba ?" walwalar fuskar Abdallah ce ta gushe ya kalli Afnan yace " zaki iya zama da miji mazinaci ? zaro ido tayi tana kallon Abdallah da idonsa ya ciko da ƙwallah tare da girgiza kai , to inhar bazaki iya ba karki ƙara yimin zancenta akwai maza a duniya bani kaɗai bane autan maza ya kamata kisani babu ni babu momy sadiq!!!!!.


Jin zancen nasa babu daɗi takeyi amma babu inda zatayi dole ta kawar da zance dakuma tinanin momy Sadiq ta rungumi mijinta , rungumota yayi yana shafa mata gashin kanta tare da murza ƴan yatsunta , itama fara yimasa wani salo tayi na daban dama tayi amfani da maganin da momy ta bata , tunda naga Abdallah ya fara harata yasani rufo musu ƙofa nayo waje.

Yau Afnan ta tambayi zuwa gida , daƙyar Abdallah ya barta amma da sharaɗin karta daɗe, tun safe tayiwa momy waya akan gatanan zuwa , kowa na gidan murna yakeyi dan an daɗe ba'a haɗu ba , momy tasa an shirya mata abinci kala kala, dady ma yau bai fita ba sbda yanason su gaisa da ƴarsa ,


Abdallah na fita ta fara shiri tana gyara gado taci karo da kuɗi masu yawaa tunani ta fara ko Abdallah ya mance dasu ne , ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani , Abdallah me mai kiran amsawa tayi tare da cewa ka isa lpy , lpy lou sweety ina kewarki dariya Afnan tasa tare da cewa " kai mijina daga fitarka ? eh man Afy jinake kamar in dawo , zaro ido tayi kamar yana ganinta tasan inhar sukaci gaba da maganar zai iya dawowa yayi mata haramiyar zuwa gidansu , am sorry Allah ya dawomin dakai lpy mijina akwai tanadin da nayi maka so karkaji komai , nidai fatana karka bari ƴan mata su kallemin kai , dariya sukasa a tare kowa ya ajiye wayar , dafa ƙirjinta tayi kana tace " my man rigima , tacigaba da shirinta


💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com


*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION💦*

EPISODE 49 & 50

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Biki ya kankama na Haisam da Uwani kasancewar mama tace " inhar yabarta to yabar mata , badan yaso ba ya amince da abinda takeso tunda bazata fasa ba , fatanshi dai Allah ya sanya musu albarka shikenan , hidindimu akeyi sosai sbda yanzu Haisam kuɗi sun zauna masa ba laifi harya siyi mota mai kyau ya kuma sauyawa gidan nasa fenti komai dai yayi masha Allah ,

Dama tunda iyayen Maimunatu suka zo suka kwashe kayanta ya kulle ɗakin sai yau da za'ayiwa ɗakin fenti ya buɗesa , kowa sai sam barka yakeyi amma ana cece kuce akan amarya ,ranar ɗaurin aure kowanne na dangin mama da magoya bayanta suna farinciki sosai , da yamma za'a kai Uwani tunda taji alamun zuwan motoci tafara kuka ita bazatabi wancan mugun ba , karyazo yana yimata mugunta , kowadai lallaɓata yakeyi tunda Uwani dole sai lallaɓo , tun a mota take rafka salati da koke koke kamar wacce za'a kai gidan yanka , ana isowa ƙofar gidan nanma sai da aka ririƙeta tana neman guduwa ,


Mutane sunga tashin hankali , faɗa aka yimata mai shiga jiki duk rashin kunyarta sai da jikinta yai sanyi , musamman da aka cemata banda yiwa mijinki musu banda yimasa rashin kunya , kasancewar tana tsoron ace wutar jahannama yasata yin laushi da duk wata masifa tata , haka suka tafi suka barta tana kuka , amma a ƙarƙashin zuciyarta tsoron Haisam ne fal.

misalin ƙarfe goma da rabi kowa ya watse sai raba ido takeyi tana daga zaune a tsakiyar gado taji alamun turo ƙofa, shi kaɗai ne sai wata ƙatuwar leda dake hanunsa , gyata zaman ɗan mayafin tayi kana ta kalli ledar Allah yasa kazace , Uwani tace " lokacin da ta haɗiyi wani mugun yawu , zama yayi bakin gado tare da cire agogon hanunsa ya miƙe , Uwani tashi muje muyi sallah sai da taɗan harareshi kana ta miƙe , kunsan dai mai hali baya fasawa amma a tunaninta ta rage rabi ,


Bakinnan kamar wanda aka ja dan fushi ita ba sallar bace damuwarta cin kazar shine matsalar ta , tana yin alwalalr ta dawo ɗaki ta zauna gefen gado , Haisam na shigowa yace " tashi muyi sallah ko kulashi batayiba ta miƙe sukayi sallahr ya shafa kanta yayi mata adu'oi kana yayi mata ƴan tambayoyi game da tsarki dakuma wanka da alwalah , ba laifi tayi koƙari ta wanan fanni.


Jira take sai kuma taga ya miƙe ya ɗauko plet da wuƙa ya baje kazar gata ƙatuwa , wani yawu takuma haɗiya , so takeyi taji yace " mata sakko kuma badan yau sabuwar kunyarshi takeji ba da babu abinda zai hanata daka wawa, sai da ya tsiyaya mata milk a cup kana yace " bismillah har sikel na harɗeta ta sakko ta zauna ko irin yangar nan babu tafara bawa cikinta tanayi tana lumshe ido mamaki ta bashi, sai ya tuno darensu na farko shida Afnan lokacin da ya shigo ƙin buɗe fuska tayi kuma da ƙyar taci kazar bawata mai yawa taci ba amma ita wanan ko na bakinta bata gama ci take ɗaukar wani.


Tsayawa yayi kallon ikon Allah bata damu da rashin cinsa ba sai suɗe hannu takeyi, da ya gaji da dane dannen wayarsa ya miƙe ya nufi ɗakinsa , a gajiye yake hakan yasashi kwanciya 'a madai daicin gadonsa bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi .


Saida takusa cinye kazar sanan ta ajiye ragowa a kan table taje ta faɗa gado tana tsalle ashe haka aure yake tabb shine naketa kuka , yasin danasan kullum haka za adingayi da ban tada hankali ba , naci ta yau saura ta gobe yasin su inna zasu ganni nayi mulmul , dahaka itama bacci ya sureta .


magunguna momy ta haɗawa Afnan sbda momy mace ce mai son taga ta mallaki zuciyar miji bata hanyar boka ba , ta hanyar magunguna da turaruka ,da kissa hakan yasa dady yafi sonta itako anty bata ganewa maganin mata kasancewarta bata jituwa da magani shiyasa take masa kallon ko in kula , wasu zafafan turaruka momy ta haɗawa Afnan a wata ƴar leda kana ta ƙara da ce mata kartayi wasa da shan magani dakuma kula da abubuwan da mijinta yakeda buƙata , karkuma ta zamo mai ɗaga murya akan ta mijinta ta zamo mai tausayi da iya kallo dakuma iya tafiya , ta ƙara da cewa " ta yawaita amfani da turaruka masu daɗin ƙamshi karta dinga barin kanta yana daɗewa batare da ta wankesa da shampo ba .



godiya Afnan tayiwa momyn ta , momy ce tace " bawai na gama bane , abu na gaba inaso kisan wani sirri shi namiji inda kika juyashi haka zai biki tausayi fara'a iya kallo iya tafiya dadaɗan kalami uwa uba kuma ɗaukar wanka da iya kissa ,karki zamo kina zama nesa dashi a yayin da kuke tare ki zamo masa tamkar yayayyar yarinya ina fatan duk waɗannan abubuwan sun shiga kunnenki ,zuwa gaba zan baki wasu muhimman sirrukan , yanzu miƙomin wancan zumar , miƙewa Afnan tayi ta kawowa momy zumar momy ce ta buɗe tare da cewa ki kafa kanki ki shanye ki ɗauko madara a store ki fasata itama ki shanye , akwai dabino a wanan kwanon ki ɗibo kici shima yana temako sosai basai na fayyace miki komai ba.

Kiran Abdallah ne ya shigo wayarta momy ce tace " ɗaga mana amma ki sanyaya murya , gyara muryarta tayi ta kara wayar a kunnenta tare da cewa aslm my man barka da yamma ykk ya aiki , Abdallah dake zaune a office yana shirin dawowa gida yace " baby nagaji , ƙara kashe murya Afnan tayi tace " nima gani a gida nakasa dawowa , whatt Abdallah yace " ya mukayi da ke ?uhm uhm to ba sai ka biyo ka ɗaukeni ba , ganin momy ta fice daga ɗakin yasata cewa banason in koma inga bakanan shiyasa ban dawo ba, ok Abdallah yace " to ki kwantar da hankalinki ganinan zuwa dady ya dawo ne ? eh cewar Afnan gurinshi ma zani , to sai na ƙaraso , Allah ya tsaremin kai , amen y Allah cewar Abdallah,


Momy ce ta shigo take cewa Afnan tashi kije dadynku ya shigo 'ok Afnan tace "tare da miƙewa ta nufi palon dady , da fara'a ya amsa gaisuwarta tare da cewa ya maigidan naki yana lpy Afnan tace sukaɗan taɓa hira ta miƙe domin zuwa shirin tafiya gida ....



Yau kwanan Uwani biyar iyakaci ta dafa indomie shine ya dawo abincinta , tun ranar da Abdallah yace " ta dafa masa ya koya inda zatayi shikenan tasamu shikam yanzu yama haƙura dayin faɗa tunda ba ji takeyi ba ,


Daren talata Haisam ya dawo ƙarfe tara lokacin tana kallo a palo sannu kawai tace "tacigaba da kallonta intaga ana wurga ƙwalo tadinga cewa "banza ka cafe man yawwa nawan , Haisam ya gaji baya buƙatar hayaniya ya fito yana yimata maganar tadena ihu ,harara ta zabga masa kana tace "ni banason gulma kaima zoka zauna ayi kallon dakai."

Ran Haisam ne ya ɓaci yace " ni kike gayawa haka ? bata ƙara kallonsa ba sai cigaba da kallon ta da tayi shiko tunanin hanyar da zai gyara mata rashin kunyarta yafara , murmushin mugunta yayi yazo kusa da ita ya zauna tare da jawota jikinsa , zatayi magana ya haɗe bakinsu tare da sakar mata hote kiss masu zafi , nifa ka dena banason iskanci , Haisam ne yace " biyani kazata , ninace ka siyomin bai ƙara bi ta kan maganar ba yafara shafa mata gashi yana sauke wahalalen nunfashi , jin yafara shiga wani yanayi ya kulle ko ina ya sunkuceta sukayi ɗakinsa , a gadonsa ya kwntar da ita , dukda kukan da takeyi bai hanashi cimma burinsa tare da mayar da ita cikakkiyar mace ba , ya daɗe yana aika mata da saƙonninsa kai kace sabon shiga , Uwani bakifa ya mutu banda kiran wayo babu abinda takeyi sai kuma faɗar Allah zai sakamin ,


Mirginawa gefe yayi tare da shafo ƙirjinta yana ƙara sauke nunfashi tabbas ya sami nutsuwa sosai , yanzu ne ya fara tunanin yarinyar mutane , a razane ya miƙe ya tallafo kanta idanunta shaɓe shaɓe da hawaye , tashi kiyi wanka cikin muryar kuka tace " wlh bazan iya ba tausayinta ya kamashi ya temaka mata sukayi wanka itakam yanzu ɗaukar ɗan iska rayiwa Haisam .





LOKACI NA TAFIYA YAYINDA KOMAI KE SAUYAWA CIKIN WATA GOMA.



Uwani tasami ciki ta haifi yarinya mace mai kamada Haisam yanzu kam duk wani surkule ta rageshi kuma Haisam ya koyat da iya soyayyar sa haka suke rainonon yarinyar mai suna Aneesa wacce taci sunan mahaifiyar Uwani wato HAJARA .




Zaune na hango Afnan a ɗaki da ɗan ƙaramin cikinta wanda zai kai wata uku tayi kyau ta ƙara ƙiba da haske , soyayya a gurin Abdallah sai wanda ya daɗu , Anty wato yayar dady tasami cikon burinta dady ya gina mata gida yakuma siya mata mota da direba sbda mijinta ya rasu tin shekarun baya da suka wuce





Kowane gida ya yalwatu da arziki dakuma farinciki mama kam tana kula da jikanta dai dai gwargwado .





ALHAMDULILH ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANAN LITTAFI ABINDA NA FAƊA DAI DAI ALLAH YA BAMU IKON CIGABA DA RUBUTA DAI DAI AKASIN HAKAN ALLAH KA YAFE MANA ALBARKACIN WANAN WATA MAI ALBARKA SAIKUMA ALLAH YA HAƊAMU A LITTAFI NA GABA .





DOMIN KIRA MAI MUHIMMANCI 08141799224



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau

Please Login or Register in order to submit comment