Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

my fans .

Ga mai buƙatar karanta littafinnan tundaga na ɗaya zai iya samunsa ta wattpad momislam2020

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

EPISODE 31 & 32

Ganin rana tayi kuma Maimunatu bata fito ba yasa mama miƙewa ta nufi kitchen ta kunna risho kasancewar bata iya kunna gas ba , ruwa ta dora da wake a haɗe dan da alama shinkafa da wake zata girka , fitowar Maimunatu daga ɗaki kenan ta leƙa ɗakin Haisam taga babu kowa ya fita , kitchen ta nufa hango mama tana gyaran shinkafa yasata cewa sannu , washe baki mama tayi cikin rawar jiki tace "sannu ƴar albarka."

sai da Abdallah ya sami nutsuwa da Afnan sanan ya shafo fuskarta tare da manna mata kiss a goshi , Allah yayi miki albarka duk da wani ya rigani amma dole nayi alfahari da wanan rana gaskiya Afy kin shayar dani zuma , Afnan dake kwance tana kallonshi yana sumbatu ta rungumeshi tare da raɗa masa a kunne tace "karka damu mijina koda wane lokaci ina tare dakai , wanan maganar ta Afnan tasa shi jin daɗi sosai ya miƙe ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwa , wankan tsarki ta fara kana yayi na sabulu ,Afnan miƙewa tayi ta ciro masa boyel mai laushi baƙi da farar hula da farin takalmi kasamcewar akwai wasu kayan nasa a ɗakinta ..


Yana fitowa ta shige itama wanka tayi tare da na tsarki ta fito kanta ɗaure da towel na tsane ruwa ,

Samunsa tayi har ya shirya sai zuba ƙamshi yakeyi ga wani sihirtaccen kyau da yayi mata ..

Kamo hanunta yayi tare da ɗorata kan cinyarsa yace "gaskiya zanje in dawo ki kularmin da kanki ,

Ƙara marai rai cewa tayi ta ce "gaskiya nagaji da fitarnan inace hutun two weeks ka ɗauka ,

Buɗe baki Abdallah yayi yace "wane ni yazanyi da jama'ar da suke jirana in dawo ?"

Uhm to yanzu ina zaka ?"zanje duba Sadiq ne wai sun dawo gida ..

Kishi ne ya tasowa Afnan amma dole ta danne dan tanason samun fada a zuciyar Abdallah ,ka gaishe shi shida momyn 'nashi oky Abdallah yace "yana ɗaura agogo a hanunsa,

Shafa fuskarta ya ƙarayi kana yace "natafi Allah ya tsare Afnan tace "fuskarta ɗauke da murmishi ."

da isarshi gidan takalma ya gani a ƙofar ɗakin zasukai na mutum huɗu ,nazari ya kamayi dan lokacin magrib ta farayi , jiyo surutun su yayi suna cewa ai wlh hajiya ki kaɗa ƴar banza ...

Kina zaune da mijin zata fara kawo miki cikas nifa dama bason aurannan da yayi nakeba duk da bani ke zama dashi ba ...

Momyn Sadiq ce tace "uhm ni yanzu ma kullum sai nayi kuka sbda ya sabarmin da komai nasa , wata daga gefe tace "uhm nidai banida ta cewa tunda tun farko baki ɗauki shawarar mu ba ....

Akwai wani hatsabibin malami wanda yataɓa yimiki aiki har kika samu cikin Sadiq .

Tagumi ta zuba alamar tunani , momyn Sadiq ce tace "wlh wanan karon bazan aikata zina ba inaji ina gani ,

Nice ban jira lokaci ba ai likitoci sunce akwai lokaci dagani har mijina muna aihuwa ,

taɓe baki sukayi tare da miƙewa sukace to kizauna ta kasheki karkuma ki neme mu , fashewa tayi da matsanancin kuka ta miƙe tsaye tana takowa gabansu tace ...

To ni mezan sa boka yayi mata ?" sallamar da sukaji ne yai sanadiya faɗuwar gaban momyn Sadiq ta dafe ƙirji suko sauran ko a jikinsu sukayi waje kowacce na kallon Abdallah ."

Zama tayi jugub a kujera tana share gumin da yake karyo mata tare da mai maita innalilahi a zuciyarta .

Abdallah wayarsa ya ciro yafara danne danne amma inka lura dashi sosai hankalinsa a tashe yake ,

Ko kaɗan bata ƙaunar taji yayi mata magana hakan yasata miƙewa ta nufi hanyar da zata sadata da bedroom ɗinta keee!!! taji Abdallah yace " cikin tsawa juyowa tayi batare da tace "komai ba ,


Kuma maida hankalinsa kan wayar dake hanunsa yayi a zahiri kukan zuci yakeyi dan nafili yaƙi fitowa .

Takai wasu mintuna a tsaye a gurin dan yanzu tsoransa ma takeji kar tayi ƙwaƙwaran motsi ya yanke mata mumunan hukunci,

Tashin hankali gami da rashin ƙaunar maman sadiq ya darsu a zuciyar Abdallah ,mai maicin da zuciyarsa take yimasa shine zina ?zina tayi kenam ba ɗana bane ?" ya ilahi ya riƙe kansa da yake sara masa."

Ya ɗago kansa ya dubi maman Sadiq yace "naji duk abinda kuke ta taunawa akai dame na rageki ci ko sha ko tufafi kokuma haƙinki ne bana saukewa kiji tsoron Allah ,

Yaci gaba da cewa kin cuceni kin cuci ɗanki dan bazance ɗana ba ,


Momyn Sadiq jira take taji kalamin Abdallah na ƙarshe yace ya yafe mata sai taji akasin hakan yace " na sakeki saki biyu inkin sami miji kiyi aure kuma ki tafi da ɗanki banida alaƙa dashi.....✍️.

Fans kuyi haƙuri kwana biyu kunjini shiru nayi tafiya ne amma na dawo ganin sharhinku shine zai sa kusami pagin gaba amma in bangani ba sai bayan sallah gaskiya 🤗.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*



*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 33 & 34

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Kasa tsayuwa tayi a gurin saboda wani jiri dake ɗibarta ta durƙusa kan guwaiwar ta tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu oh ni ƴa su ina zansa kai na ,rarrafowa gabansa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace "dan darajar iyayenka ka yafemin wlh ba 'ason...!!! wani wawan mari ya wanketa dashi kana ya miƙe tsaye yace "kar in dawo in samu kina gidannan wlh sai kinyi dana sani , ya fice zuciyarsa na suya , driving yakeyi amma hankalinsa a tashe yake ,ikon Allah ne ya kaishi gida , ko horn baiyi ba ya buɗe murfin motar ya fice tare da buɗe get ɗin , mai gadi dake zaune a wata farar kujera ta roba ganin Abdallah ya shigo a fusace ya miƙe yana cewa Alhji barka dai ywwa kawai yace ."


Bai jira ƙara jin wata maganar ba ya shige ciki , mai gadi ne ya jinjina kai ya ƙwalawa driver kira da sauri ya taho sabda shima ya lura da yanayin Alhajin ."

Wangale get ɗin yayi ya shigo da motar, sukazo suka zauna kafa hirar shigowar uban gidan nasu ,

Bai sameta a palo ba ya nemi guri ya zauna , kashe tv da yaketa ƙararsa shi kaɗai yayi , ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya abubuwan da suka faru tsakaninsa da momyn Sadiq suka fara dawo masa ..

Cikin zuciyarsa yace " ko kaɗan banyi dana sanin rabuwa dake ba dan bansan ko bada ni kaɗai kike taraiyya ba .

Shigowar Afnan ce ta sanyashi katse tunanin tare da faɗaɗa fara'arsa irin karta gane yana cikin wani hali , takowa takeyi cikin isa da ƙasaita ,
kai kace ƴar wani sarkin ce ."

Zama tayi gefensa tare da ratayo hanunta a kafaɗarsa tace "lafiya mijina ? naga kamar kana cikin damuwa " a'a Afy kaina ke ciwo yanzu ma so nakeyi na ɗan kwanta ..

Badan ta yarda ba ta ƙyaleshi amma ta fuskanci akwai abinda yake damunsa jikinta a sanyaye tayi bedroom ɗinta ta fashe da kuka ,

jiyo kukan yayi lokacin da zaiyi hanyar bedroom ɗinsa ya dawo zuwa ɗakin nata , dole ya jata gado ya rungume ta yana jijiga ta kamar baby har bacci yai gaba da ita .

Ajiyar zuciya ya sauke can kuma sai wasu zafafan hawaye suka sauko daga idonsa , kallon sa ya kai ga Afnan dake ta bacci hankalinta kwance amma fuskarta duk alamun hawaye gasunan ..

In ya tuna Sadiq ba ɗansa bane sai ya saki wani mahaukacin kuka mai ban tausayi , yana cikin hakan ne yaji ring ɗin wayarsa ..


Kasancewar ya bar wayoyinsa a palo ya miƙe a hankali ya isa gurin wayar da ɗaga warsa, my son yagani sai da yakuma zubar da hawaye sanan ya ɗaga wayar, kafin yayi magana yaji Sadiq yace "dady na koma school fa gashi yanzu banida wasu kuɗi a hanuna , jimm Abdallah yayu can kuma yace "zan tura maka zuwa anjima inna fita , nagode dady Sadiq yace " lokacin da Abdallah ya jiyo ƙarar tafi da dariyaku ya kashe wayar , kirane yakuma shigowa a karo na biyu Abdallah ya ɗaga a fusace yace "wai lafiya ?am dady wayar momy ce tun jiya a kashe dan Allah in kuna kusa ka bata , bana kusa Abdallah ya bashi amsa a taƙaice ya kashe wayar duka ma."

Lefin momynsa yana neman shafarsa ko da yake yanata shawara da zuciyarsa akan ya fito ya faɗawa Sadiq ba shine ubansa ba sai kuma ya kawar da tunanin , ya shafe mimtuna a gurin yanata tunani iri iri amma babu wata mafita da yaga ta dace , kwanciya yayi a doguwar kujerar tare da ɗaga kansa sama , yau ɗinnan a tunani ya ƙare , bayan Afnan ta tashi tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga baƙa mai adon faraten dutsina ba ƙaramin kyau tayi ba , samun Abdallah tayi kwance a palo bacci ya ɗaukesa gashi lokacin ƙarfe shida na yamma , kasa tashinsa tayi kwai ta miƙe tayi hanyar kitchen,

Abinci mai sauƙi ta yi doya da miyar ƙwai dan yau tunda taga mai gidan babu walwala take jinta babu daɗi , tana gamawa ta dawo palo ta zauna gefensa tana shafa fuskarsa a hankali , buɗe ido yayi yana salati "ana kiran sallah fa , oky yace "tare da miƙewa ya nufi hanyar toilet , bin bayansa da kallo tayi tana mamakin sayawarsa daga fitarsa zuwa yanzu , kodai wani ya ɓata masa rai ne ? ta tambayi kanta , dawowarsa ce yasata ɗago kai tare da cewa Allah ya tsare amen yace "yasa kai ya fice....✍️.


Babu sharhi 🤨?.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*



*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 35 & 36

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Washe gari safiyar litinin (monday) Maimunatu ta tashi da wani matsanancin ciwon mara da baya , jin shiru har ƙarfe takwas bata fito ba yasa mama nufar ɗakin , jiyo nishin Maimunatu yasa hankalinta mugun tashi ta shigo a guje , ganinta tayi durƙushe tanata juyi idanunta sunyi ja , subhannallah mama tace " tare da kamo mai munatu ta gyara mata tsuguno , yau kam babu magana kuma bata yiwa mama musu , ganin abin ya wuce tunani gashi dai alamun aihuwar ce amma har yanzu shiru , sake Maimunatu tayi ta wuce ɗakin Haisam dake bacci ..

Bugun ƙofar takeyi tana ƙwala masa kira , a tsorace ya taso ya buɗe ƙofar yace "lafiya mama?" inafa lafiya maza fito kazo ka ɗauko mashin ɗinka muje asibiti wanan yarinyar inaga aihuwa ce , ai dajin tace aihuwa ce yasashi azamar sauya kaya ya fito da sauri mama ta kwaso kayan yaro , kasancewar ba zaman daɗi sukeyi dashi ba amma yana siyo kayan jarirai , kai tsaye suka nufi asibiti ,da isarsu aka wuce ,da Maimunatu ɗakin aihuwa ..

Mama da Haisam sun zuba tagumi kawai jira suke suji ance ta aihu ,

Ɓangaren Maimunatu likitoci ne zagaye a kanta sunata aiki ,itako batasan inda kanta yake ba ,adu'a sukeyi duk wacce ta faɗo musu amma kaf ɗinsu hankalinsu ya fara tashi , tun ƙarfe tara na safe gashi yanzu ƙarfe biyar na yamma , wata likita ce ta fito fuska babu walwala ganin hakan yasa mama miƙewa da sauri Haisam da bai san ko mai ke faruwa shima ya miƙe , hango likitar yayi ta doso gurin su ...

Tun a zuciyarsa yafara mai maita innalilahi haka mama itama , likitar ce tace "waye mijin Maimunatu a nan ko kai ne ? ta nuna Haisam ,cikin tashin hankali yace " nine ok "kazo office munason ganinka , to Haisam yace "jin ba abinda yake tunani bane yasashi sakin fuskarsa ,

Da sallama ya shiga ya nemi guri ya zauna likitar da tazo ta kirashi ne takuma cewa malam muna mai baka haƙuri akan rashin matarka , a razane Haisam ya miƙe daga zaman da yayi yace " ban gane ba ?".

Kina nufin Maimunatu ce ta rasu ? wani doctor dake gefe tunda Haisam ya shigo bai ce komai ba yace " abokina kayi haƙuri kulli nafsin za'ikatull maut kayi haƙuri adu'arka take buƙata ..

Da zamuyi maka magana kasa hannu ayi mata aiki to muna tunanin aihuwar da saura amma Allah da kansa ya ƙarɓi abarsa ."

Mama jin Haisam shiru bai dawo ba yasata neman gurin zama amma tanajin yawan faɗuwar gaba , hangoshi tayi yana share hawaye kamar ƙaramin yaro , a saninta Haisam bai cika zubar da hawaye ba inba babban abu ne ya faru ba , lallai akwai abinda ya faru mama ta faɗa a fili ".

Yana isowa gurinta yace " mama ta mutu !!zaro ido mama tayi tanajin abin kamar a mafarki ƙarya kakeyi Haisam ,waye ya mutu ?Maimunatu ya bata amsa innalilahi ta bazama cikin asibitin da gudu , binta Haisam yayi yana ƙwala mata kira amma ina sai da tayi ɗakin da gawar Maimunatu take ta bude gawar da aka lulluɓeta da farin mayafi , salati ta dinga rafkawa tana surutai marasa amfani ..

Ashe tafiya zakiyi kintafi da ciki , tsayawa Haisam yayi a bakin ƙofa idanunsa cike da hawaye yana share wa wani na biyo baya , haka likitocin suka shigo suka samesu suma sun tausaya musu amma dayake lamarin na Allah ne da yafi kowa so ya karɓi abinsa suka cigaba da yiwa su Haisam nasih.

Haka 'asibitin suka bada mota aka sa gawar Maimunatu suka nufi gida , tun a hanya Haisam yafara sanar da ƴan uwansu dana Maimunatu , mahaifiyarta ko kuka tasa tana ihu ,

Kafin su ƙaraso an ɓalle ƙofar gidan mutanen kusa sunata shigowa , da shigarsu aka wuce ta gawar ɗakinta aka ɗibi ruwan ɗumi aka yimata wanka aka karɓo likafani a masallaci , aka suturce ta, kasancewar iyayenta duk sunzo ana fito da gawar ta mahaifiyarta ta miƙe tana ihu wani malami ne ya fara yimata wa'azi da ban haƙuri , kuka kam ansha haka aka kaita makwancin ta rai kenan baƙon duniya.

Gida ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi mama kam hauka ne batayi ba amma tadingi kuka sosai ga cikin babu tadinga mai maitawa a cikinzuciyarta...✍️.


Follow me on wattpad momislam2020

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com

*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*

*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*

*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*



*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 37 & 38

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Duk abinda Sadiq ya nema Abdallah ya tura masa harda kuɗi masu yawa , washe gari yayi sammakon zuwa gidan su momyn Sadiq ,samu yayi ta kwashe duk wani kaya nata durƙusawa yayi a gurin ya saki wani kuka mai cin rai a fili yace " ina sonki wlh ina sonki amma soyayyar da nake yimiki bazai sa inkasa yanke hukunci dai dai da abinda kika aikata ba , fuskarsa tayi shaɓe shaɓe da hawaye kamar ƙaramin yaro , miƙewa yayi ya nufi bedroom ɗinsa ya kwanta zuciyarsa fall baƙin ciki da haka bacci mai nauyi yayi nasarar ɗaukarsa , ya daɗe yana baccin tare da mafarkai iri iri na ban tsoro rin ɗin wayarsa ce ta tashe sa daga bacci salati yayi kana ya janyo wayar ya danna ya kara a kunne ,wlkslm naji yace " daga ɗayan ɓangaren akace ango hutun ya isa haka ma'aikata nada buƙatar ka kuma kasan gobe za'ayi taron cika shekara biyar da buɗe ma'aikatar mu bamuyi wasu shirye shirye ba? innalilahi Abdallah yace ".

garin ya hakan ta faru kash mutumin da yakira ne yace "bye zai zuwa goben , tom kawai Abdallah yace " kana ya shige toilet ya watsa ruwa yana fitowa ya cigaba da tunane tunanen sa , da sauri ya saka kaya ya fice daga gidan yaukam kowa ya gansa yasan babu lafiya kasancewar ko mai bai shafa ba , abubuwa sun taru sun yi masa yawa ga matsalarshi da momyn Sadiq ga gurin aiki .

Washe gari tunda ya dawo daga masallaci da asbha bai koma bacci ba ,shirye shirye yaketa yi na inda lamarin taron zai kasance , dan ma abinka da mai kuɗi kira yakeyi a waya a gudanar da komai , bayan Afnan tayi sallah asbha ta nufi ɗakinsa da sanyin jiki , samunsa tayi a zaune da wasu takardu a gabansa da alama na aikin ne , zama tayi dab dashi can kuma ta durƙusa tare da cewa ina kwana "lpy Abdallah yace "ya kike ina lpy sai dai tunanin ka , riƙe kai yayi yasan ko kusa bai kyautawa Afnan ba , naƙin kulata kwana biyu janyota yayi kusa dashi tare da rungumeta , hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba , dan tana tunanin ko tayi masa laifi ne ? amma yanzu ta gane uzuru ruka ne sukayi masa yawa ."


"Afy zoki shirya , Abdallah yace "lokacin da yake fitowa yana sanye da shadda ruwan toka sai ɗaukar ido takeyi , ganinan zuwa sweety Afnan tace " kasancewar tun ɗazu ya gaya mata sunada taro , itama shaddar tasa kalar tashi ta ɗauko mayafi da takalmi marar tudu da jakarta fara kalar takalmin da wani glass baƙi ta sanya a idonta , wow gaskiya Afnan tayi kyau dayake ɗinkin doguwar riga ce ba ƙaramin fito da ƙyan dirinta tayi ba kallonta ya tsaya yi sbda shima tayi masa kyau , turare ya ɗauko ya fesa mata yana sakar mata murmishi , suna gamawa suka rufo ƙofar suka nufi gurinda aka tanadar domin ajiye motoci , da ganinsu driver ya taso da sauri ya buɗe mota suka shiga back side ya rufe , shikuma ya shiga gaba , hira sukeyi jefi jefi a motar , amma fuskar Afnan da alamun damuwa , Abdallah sam bai lura da yanayin ta ba kasancewar yanata amsa wayoyi na mutane , faɗuwar gaba takeji a kamar akwai wani abu dazai faru a gurin taronnan , wata zuciyar tace "ki koma gida kawai ' ina babu halin yin hakan yasa ta daure zuciyata tare da mai maita innalilahi."


Sunyi tafiya mai nisa sannan suka iso tsararren gurin taron , misalta tsaruwar gurin ma ɓata lokaci ne gurin yashe gyara kasancewar hidimar ta manyan mutane ce abin ya birge , bayan angama bada kyau tutuka Abdallah ya tashi yayi jawabi akan cigaban kamfaninsu dakuma inda zasu dinga tafiyar da al'amura cikin sauƙi , Afnan dake gefe sai murmishi takeyi , hango wata farar budurwa nayi tana sanye da riga da sikel ɗan kanti ta yafa wani tsdadden mayafi mai kyau fuskarta dauke da kwaliya tanada manyan idanu farare ga gashin kanta dogo , dan anyi mata kitson gaba , cikin yanga take takun hanunta ɗauke da farar takarda dakuma flawoyi ta isa gaban Abdallah , ganin haka yasa Afnan jin wani mugun faɗuwar gaba kamar an caka mata kibiya , lokaci ɗaya murmishin ya ɗauke daga fuskarta hango wanan budurwa suna gaisawa da mijinta kuma hannu da hannu har tana lumshe masa idanu , kuma duk da haka bata bar gurin ba , baƙin ciki ne ya cika zuciyar Afnan ta miƙe tabar gurin , gurin da sukayi parking motarsu ta isa ta buɗe motar ta shige ciki , kuka ta fashe dashi kamar wacce aka aikowa da mutuwa,


Maiyasa maza suke haka ne ? .


wayarta ta ciro tafara dannawa amma hankalinta yana gurin wanan budurwa to wacece ita ?" babu mai bata amsar tambayarta a halin yanzu yasata yin shiru tare da ƙara fashewa da kuka.


Leƙenta Abdallah yakeyi amma sam bai ganta ba , budurwar dake gefensa ta lura da akwai abinda yake nema tace " maiya faru big boy ?" murmishin yaƙe yayi kana yace " nup bkm ina duba wani friend ɗina ne naga ma kamar ya tashi , oh budurwar tace " ina matarka ne ? batanan amsar data fito daga bakinsa kenan , hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa budurwar ba , tace "zamuje shan is cream ?sai da yayi jim kafin yace ”to babu matsala yarasa mai yasa baya iya yimata musu ko kad'an , fad'ad'a murmishinta tayi tace ”big boy har yanzu kak'i bani amsar tambayar da nayi maka shekara d'aya data wuce ko ?".


Jiyo alamun tashin taro sukayi hakan yasa hankalin Abdallah komawa gurin Afnan ya ilahi , yace " lokacin da ya tuna da ta dad'e da tashi a gurin gashi ko kiranta a waya baiyi ba , dafe da goshi ya yi hanyar fitowa ganin baiga motar tasu ba yasashi jin tsoro kardai Afnan ta tuk'a motar nan ne tayi gida ? yana tsaye yanata tunani kala kala har mutane suka fara fitowa suna mik'o masa hannu suna gaisawa annan ma sai da ya k'ara bata lokaci , janye jikinsa yati ya koma gefe guda ya danna number driver ✍️.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

ZAINAB HABIB
(mom islam)

My wattpad momislam2020

My telegram link

https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713gmail.com



*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦

EPISODE 39 & 40

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ring d'aya driver ya d'auka tare da sallama yace ”ranka shi dad'e na dawo d'aukarku nasamu babu mota ? dafe kai yayi tare da cewa "innalilahi yanzu ina Afnan ta shiga oh Allah driver ne ya k'ara magana a karo na biyu yace " mai gida wani gurin tayi ? shut up your mouth wlh zan sa6a maka , kana yaja wayar ya kashe , budurwar nan mai suna Husna ce ta tako har kusa dashi tace " hi my man mutafi ko ? juyowa yayi a fusace zai yimata masifa ya kasa , shafa k'eyarsa yayi yace ”mutafi , wani irin murmishi tayi wanda ita kanta tasan ma'anar hakan , motarta suka shiga tana driving shikuma yana gefenta , Afnan na zaune a cikin mota a can gefen titi kasancewar gabas sukayi ba lallai su ganta ba amma ita ta gansu musamman lokacin da Husna ta rik'o hanun Abdallah

Please Login or Register in order to submit comment