Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yai
tsartuwa daga cikin raunin.Sharkas ya zaro
wukar
ya sake daba masa ita a saman kirjinsa
bangaren
hagu.Garzub ya sake rusa ihu,shi kuwa Sharkas
saiya bushe da dariyar mugunta ya dada zare
wukar ya soka masa ita a saman kirjinsa
bangaren
dama a karo na uku.Nan take Garzub ya sume
ya
zama kamar gawa.A wannan lokaci Dakarun
Sharkas na ta ragargazar dakarun Garzub
tamkar
suna sassabe a gona.Komai rashin tausayin
mutum idan yaga irin kisan gillar da akeyi
musu
dole ne hankalinsa ya DUGUNZUMA.Sharkas ya
tsaya akan Garzub har saida yaga ya farfado
daga
suman da yayi kawai sai ya sunkuyo da nufin
yayi
masa yankan rago.Ba zato ba tsammani sai
yaga
Garzub ya mirgina ta karkashin kafafunsa izuwa
bayansa.Kafin Sharkas ya juya Garzub ya daka
tsalle tamkar dan biri ya dira akan wuyansa
kuma
ya caka masa yan yatsunsa a cikin
idanunsa.Take
kwayar idanun Sharkas suka fashe jini ya
kwararo
daga ciki Sharkas ya fadi kasa yana birgima da
kururuwa wacce ta cika dodon kunnen kowa a
wajen tasa aka daina yakin akayi cirko cirko
ana
kallonsa.Kawai sai Garzub yazo kansa ya tsaya
yasa takobinsa ya sare hannun Sharkas na
dama
hannun ya fice fit yai tsalle gefe daya.Sharkas
ya
kwarara uban ihu wanda yafi wanda yayi da
farko a
lokacin da jini ke malala daga cikin dungulmin
hannun nasa.Koda ganin haka sai Sarki Garzub
ya
dubi Sarkin Yakinsa Zamud wanda ke tsaye daf
dashi yana layi saboda jinin dake zuba a jikinsa
sakamakon yawan raunika ya daka masa tsawa
yace maza ka daure dungulmin hannun Sharkas
ka
tsaida jinin dake zuba don bana son ya
mutu.Cikin
sauri sarkin Yaki Zamud ya kwabe rigar jikinsa
ya
cika wannan umarni.A wannan lokaci shima
Garzub layi yake kamar zai fadi kasa domin jini
ne
keta zuba daga cikin wadannan raunika nasa
guda
uku wadanda Sharkas yayi masa.Garzub ya nufi
kan Sharkas yana tangadi kamar wanda yasha
giya
ya bugu sannan yasa kafa ya take kirjinsa ya
dubeshi a lokacin da idanunsa ke rufeqa da
budewa da kyar yace yakai Sharkas wakilin
sarki
Madarus ka koma izuwa kasarka ka gayawa
sarkinku cewa ka kasa idda aikin daya turoka
domin ka kamu da gamonka.Idan har yanason
burinsa ya cika to yazo da kansa ya cika
wannan
aiki.Ina sauraron isowarsa a ko yaushe.Ka sani
cewa kai taka ta kare domin na gama da
rayuwarka,tunda na maishe dakai makaho
kuma
musaki,baka da idanu kuma naka da hannu
guda.Ina mai matukar farin ciki da sa'a ta fado
a
kaina ka kasa idda mugun nufinka a kaina da
matata.Gama fadin hakan keda wuya sai
Garzub
yaji Sharkas ya bushe da mahaukaciyar
dariya.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki
kenan a
filin dagar.Daga can sai Sharkas ya hade fuska
yace yakai wannan sarki mai taurin kai kayi
sani
cewa inda kasan irin sadaukantakar sarki da
karfin
mayakansa da bakayi wannan furuci ba.Tabbas
zaka san cewa ka tsokano GUGUWAR ANNOBA
wacce bata da magani,kuma ka shafawa sauran
dukkanin kasashen dake makoftaka da kai
kashin
kaji.Ina tabbatar maka da cewa da zuwan
sarkina
wannan nahiya taku gwara a saukar da
muguwar
Annobar gobara daga sararin samaniya da
kuma
kasan kogi ta babbake ku gaba daya..Kafin
Sharkas ya gama rufe bakinsa sai Garzub ya
naushi fuskarsa da kafarsa ya baje kasa
sumamme.Sannan Garzub ya juya ya nufi cikin
dandazon mayakansa yana tafe jiri na dibarsa
har
zai fadi kenan akayi sauri aka rirrikeshi aka tafi
dashi izuwa cikin tantinsa.Su kuwa jama'ar
Sharkas sai sukayi sauri suka daukeshi suka
shiga
yi masa magani.Kafin cikar sa'a guda jama'ar
Sharkas sun gama hada nasu inasu sun bar
dajin
gaba daya.Al'amarin sarki Garzub kuwa kafi a
shigar dashi cikin tantinsa tuni ya suma,don
haka
cikin gaggawa shima likitan ya kama aiki
akansa.Har likitan ya gama aikinsa Garzub bai
farfado ba sai bayan sa'a uku.Yana bude
idanunsa
yaga Sulaira zaune a gabansa ta kura masa
idanu
tana zubar da hawayen farin ciki.Da kyar
Garzub
ya yiwa Sulaira guntun murmushi saboda
tsananin
zogi da radadin da yakeji a jikinsa.Saida suka
shafe wata tara cif ana jinyar sarki Garzub a
cikin
wannan daji da akayi wannan bakin gumurzun
yaki
sannan ya warke.A ranar daya warke ne ya
gamu
da mummunan bakin ciki a rayuwarsa wanda
bazai
taba mantawa dashi domin a ranar ne matarsa
Sulaira ta mutu sa'adda take nakudar haihuwa
ta
haifi santalelen jariri mai tsananin kyawun
gaske.Saboda tsananin bakin ciki bisa ganin
Sulaira ta mutu saida Sarki Garzub ya zamo
kamar
mahaukaci domin ihu yayi tayi da kuka DARE
DA
RANA.Sarki Garzub bai baro wannan daji ba da
akayi yakin saida ya kara kwana arba'in kullum
yana yini a gaban kabarin Sulaira yana kuka da
begenta cikin rera wakoki masu baitoci na ban
tausayi wadanda duk mahalukin dayaji su sai ya
zub da hawaye.Bayan cikar kwana arba'in din
ne
su sarkin yaki suka lallameshi aka bar dajin aka
nufin birnin Hirtoliya.Tunda aka fara tafiyar
Sarki
Garzub na rungume da jaririnsa baya rabuwa
dashi
face idan za'a shayar da jaririn madara,kuma
da
wannan farar Saniya ta Sulaira aka tafi ana
tatsar
nononta ana shayar da jaririn har aka iso
birinin
Hirtoliya.Duk sa'adda sarki Garzub ya dubi
jaririnsa
saiya tuno da Sulaira ya fashe da kukan bakin
ciki.Wannan shine asalin tarihin rayuwar sarki
Garzub da yadda yayi aure har ya sami dansa
guda daya jal ya zauna a cikin shirin ko ta
kwana
yayi ta zuba ido yana sauraron martanin sarki
Madarus na birnin Darul Nusur,amma har
tsawon
shekaru ashirin da 'ya'ya baiga komai ba kuma
bai
sami sakon komai ba.Lokacin da sarki Garzub
ya
gama tunanin wanann al'amari daya faru
shekaru
ashirin da biyar da suka gabata sai ya kamu da
tsananin bakin ciki ya fashe da kuka.Yana cikin
wannan hali ne yaji an turo kofar
turakarsa.Cikin
sauri ya dago kai sai yaga ashe yarima Uzaima
ne
ya shigo idanunsa sunyi sharkaf da
hawaye.Al'amarin dayai matukar baiwa sarki
Garzub mamaki kenan ya mike tsaye ya tari
Yarima Uzaima yana mai rike kafadunsa yace
yakai
dana ina dalilin zubar wannan hawaye a
idanunka?
Koda jin wannan batu sai Yarima Uzaima ya
risina
a gareshi yace yakai Abbana kayi sani cewa ba
komai ne ya sani zubar da wannan hawaye ba
face
nayi nadama bisa bata maka rai da nayi a baya
domin ka bukaceni da nayi aure amma naki.A
dalilin haka ne na kamu da tsananin bakin ciki
har
ka daina zaman fada na tsawon yan kwanaki
kuma
kullum ka rinka kulle kanka a cikin turakarka
kana
kuka.Ina fatan zaka gafarta mini wannan laifi
da
nayi maka kuma ina tabbatar maka da cewa
yanzu
a shirye nake da nabi dukkanin umarninka don
ganin farin cikinka.Sa'adda Sarki Garzub yaji
wannan batu daga bakin Yarima Uzaima sai ya
cika da tsananin mamaki gami da farin ciki
sannan
ya rungume Uzaima yana murna.Jima kadan
saiya
janye jikinsa daga cikin na Uzaima suka
fuskanci
juna,Sarki Garzub ya dubeshi yace yakai dana
inason ka fada mini iyakar gaskiya,kai kuwa
mene
ne yasa kayi nadama bisa wannan ra'ayi nawa
daka bijire masa?Dajin haka sai Uzaima yasa
hannu ya share hawayen dake zuba a idanunsa
yace ba wani abu bane yasa nayi wannan
nadama
ba face a jiya da daddare sarkin yaki Zamud ya
bani labarin yadda akayi ka hadu da mahaifiya
har
kukayi aure aka haifeni bayan kun fafata
gagarumin
yaki da mutanen Kasar darul Nusur sa'adda
kayi
jarumtakar da baka taba yin kamarta Ba.Yakai
Abbana me yasa ka boye mini wannan labari
tuntuni?Na rantse da darajar kaunar da kake
yiwa
mahaifiyata inda nasan da wannan labari da
tun
farko bazan taba bijirewa umarninka ba na son
nayi aure.Koda sarki Garzub yaji wannan batu
sai
ya sake rungume Yarima Uzaima a kirjinsa ya
fashe da kukan farin ciki.Kashe gari da sassafe
sarki Garzub ya tashi manzo ya aikeshi izuwa
wata
kasa da ake kira Karyabu inda sarki Rakalu ke
mulki.Sarki Rakalu aminin sarki Garzub ne
kuma
yanada wata kyakkyawar 'ya wacce babu
kamarta
a gaba dayan nahiyar,ana kiranta da suna
Gimbiya
Izaima.Sakon da sarki Garzub ya aikawa sarki
Rakalu shine ya hanzarta ya taho birnin
Hirtoliya a
gobe tare da yarsa Izaima domin ayi baikon
'yarsa
Gimbiya Izaima da yarima Uzaima.Tsakanin
Birnin
Hirtoliya da birnin Karyabu tafiyace ta kwana
uku
kacal.Lokacin da manzon sarki Garzub ya isa
fadar
sarki Rakalu ya isar da sakon sia sarki Rakalu
ya
cika da tsananin farin ciki mara misaltuwa.Ita
kuwa
gimbiya Izaima sai da tafi mahaifin nata ma
farin
ciki ta rinka tsalle da rawa domin ta dade tana
begen yarima Uzaima a zuciyarta kuma babu
abinda batayi ba domin ta sami soyayyarsa
amma
bata samu ba.Duk sa'adda Gimbiya Izaima takai
ziyara birnin Hirtoliya sai ta bukaci ta gana da
yarima Uzaima ko sau day bai taba yarda sun
kebe
ba bare suyi hira.Kai tun Gimbiya Izaima tana
yarinya karama mahaifiyarta ke zuwa da ita
gidan
sarki Garzub kuma tun a sannan ne tahi tana
son
yarima Uzaima amma ko magana bai taba yi
mata
ba,idan ma tazo kusa dashi saiya tashi ya ruga
da
gudu ya bata wuri.Har suka girma akan haka
al'amuran ke tafiya.Gimbiya Izaima tayi kuka
sau
ba adadi akan yarima Uzaima saboda tsananin
son
da take masa yana wulakantata.Shi kansa
Yarima
Uzaima saida takai cewa yana tausaya mata
amma
a zahiri bai taba nuna mata yana tausayin nata
ba.Cikin gaggawa Sarki Rakalu yasa aka
shirya masa tafiya izuwa birnin Hirtoliya tare
da
'yarsa Gimbiya Izaima ya debi dukiya nai yawa
gami da makada da mawaka,dakaru dubi dari
uku
sukayi masa rakiya.A cikin kwana uku daidai
kuwa
suka isa birnin Hirtoliya.Tun kafin su shigo
cikin
garin labari ya riski sarki Garzub yayi hawa da
kansa yazo ya tarbesu cikin farin ciki suka
dunguma gaba daya izuwa gidan
sarautar.Abinda
ya baiwa Gimbiya Izaima mamaki shine yarima
Uzaima bai biyo sarki taryarsu ba amma sai ta
aiyana aranta cewa wani uzuri ne ya hanashi
zuwa.Har su Izaima suka isa gidan Sarautar aka
kaisu masaukinsu bataga Yarima Uzaima
ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan
taji babu abinda takeso sama da ganinsa.A
wannan lokaci da suka iso birnin Magriba tayi
don
haka sai sarki Garzub ya gaya musu cewa su
bari
sai gobe da safe ayi wannan shagalin biki na
baikon Yarima da Gimbiya.Domin har a sannan
ma
bakin da ka gaiyato basu gama zuwa ba.Har
dare
ya raba gimbiya Izaima bata sami sukuni ba
kuma
sau bakwai tana aikawa ayi mata iso wajen
yarima
Uzaima amma duk sa'adda akaje sai a tarar
yarima
Uzaima baya nan yana can turakar mahaifinsa
suna ganawa.Haka dai Izaima ta hakura ba don
taso ba taje ta kwanta amma sai bacci ya
gagara
saboda Farin ciki da dokin ganin gari ya waye
anyi
baikonta da Yarima Uzaima.Ai kuwa tunda
duku
dukun safiya Izaima ta tashi tayi wanka ta kure
adaka.Sa'adda ta tsaya a gaban madubi tana
ado
saida ta bata sa'a biyu tana kwalliyar.Duk
abinda
tayi sai taga baiyi mata kyau ba sai ta sakeyin
wani.
Al'amarin Yarima Uzaima kuwa ko kadan baya
farin ciki da zuwan wannan rana domin a
rayuwarsa bai taba ganin wata 'ya mace data
burgeshi ba bare har yaji yana son ya
aureta.Yanzu ma ya amince ayi masa baiko da
gimbiya Izaima ne don kawai ya farantawa
mahaifinsa rai kuma ya kwantar masa da
hankali
ya daina yawan kuka da begen matarsa
marigayiya
Sulaira.Lokacin da fadar sarki Garzub ta cika da
batse da manayn baki da sauran jama'ar gari
sai
makada da mawaka suka fara aikinsu ya
zamana
cewa fadar ta cika da hayaniya anata
shagali.Jim
kadan saiga sarki Garzub da Sarki Rakalu sun
fito
daga cikin gidan sarautar suna rike da hannun
juna suna tafe suna ta hira cikin nishadi da
farin
ciki,Gimbiya Izaima na biye dasu a baya.Kai
tsaye
suka nufi inda karagar sarki take suka
zauna,nanfa
Izaima ta kama hange hange da waige waige
domin taga Ta inda Yarima Uzaima zai fito.Ai
kuwa jim kadan da zamansu sai ga Yarima
Uzaima
ya shigo fadar yana sanye da tufafi koraye
masu
tsananin kyau irin na sarakai.Abinka da mai
kyau
kuma ya sanya mai kyau sai gashi Uzaima ya
zamo tauraro mafi haske a cikin taurari wato
ya fita
daban a cikin dukkanin samarin dake cikin
fadar
sai haske yake da kyalkyali.Mata kuwa basu san
sa'adda suka wangame baki ba suna kallonsa
kawai kamar su ruga su daukeshi.Cikin
murmushi
Yarima Uzaima ya nufi inda gimbiya Izaima
take
zaune.Koda ta hangoshi ya nufota saita cika da
tsananin murna ta kasa nutsuwa ta rinka
muskuce
muskuce jikinta nata tsuma.Koda Uzaima yazo
daf
daita sai ya kama hannunta ya sumbaceshi
yace
lale marhaban da ABOKIYAR RAYUWATA.Koda
jin
wannan batu sai hawayen farin ciki ya
subutowa
Izaima bata san sa'adda ta sumbaci goshin
Uzaima ba tayi masa rada a kunne tana mai
cewa
lale marhaban da rabin jikina abin begena dare
da
rana.Uzaima yayi murmushi baice komai ba
sannan ya zauna a kusa da ita suka fuskanci
tsakiyar fadar inda wadansu yan mata su goma
sha biyu keta faman tika rawa sunyi wata shiga
irin ta siffar dawisu mai ban sha'awa suna
debewa
kowa kewa a fadar.Saida masu rawar suka
shafe
rabin sa'a sunata aikinsu sannan aka sallamesu
suka fice daga tsakiyar fadar.A wannan lokaci
ne
sarki Garzub ya mike tsaye cikin farin ciki yayi
jawabin barka da zuwa ga manyan baki kuma
yayi
bayanin dalilin wannan gagarumin taro da aka
shirya.Bayan ya gama wannan jawabi ne aka
kirawo Gimbiya Izaima da Yarima Uzaima
domin yi
musu baiko.Lokaci guda duk su biyun suka taso
daga inda suke zaune suka nufi tsakiyar
fadar.Nan
take fadar ta rude da shewa da tafin
jama'a.Bisa
al'adar mutanen birnin Hirtoliya inda akayiwa
mace
da namiji baiko to har abada dayansu bai isa
yayi
aure ba da wani daban idan dayansu ne ya
mutu.Yanayin yadda akeyin baikon shine za'a
zuba zuma ne da madara a cikin kasko sai
masoyan su sa cokali su rinka diba suna sha
har
sai zumar da madarar sun kare sannan sai a
fasa
wannan kasko.Nan take aka kawo wannan
kasko
wanda ke cike da madara da zuma aka ajiye
akan
wani tebur dake tsakiyar fadar.Uzaima da
Izaima
sukazo suka tsaya agaban Kaskon suka sashi a
tsakiya suna masu fuskantar juna.Ba tare da
bata
lokaci ba aka kawo musu cokali na duma suka
fara
diban wannan madara da zuma ta cikin kaskon
suna sha.Sannu a hankali suka kusan shanye
madarar ya zamana cewa saura baifi cokali uku
ba.Kwatsam sai ga wani bafade wanda ya
kasance
daya daga cikin dakarun da suka kewaye bayan
gari don tabbatar da tsaro ya shigo cikin fadar
a
guje yana haki rike da wata wasika a
hannunsa.Da
zuwansa gaban karagar sarki saiya zube kasa ya
kwashi gaisuwa ya mika wannan wasika ga
sarkin
yaki Zamud.A wannan lokaci gaba dayan
mutanen
fadar sun kame kamar gumaka sun kasa kunne
su
ji sakon da aka zo dashi.Yarima Uzaima da
Gimbiya Izaima ma sai suka tsaya ga barin
cigaba
da shan wannan madara.Cikin sauri sarkin yaki
Zamud ya warware wannan wasika ya fara
karantata a fili kamar haka:-Takarda daga
hannun
SARKIN SARAKAN duniya mai daraja ta daya
wato
sarki Madarus na birnin Darul Nusur.Zuwa ga
makaskancin sarki Garzub na birnin
Hirtoliya.Yakai
wannan sarki kayi sani cewa

TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Daya (1)
Part G
Ya kai wannan sarki kayi sani cewa ba'a ramuwa
ranar gaba.Idan baka manta ba kimanin shekaru
ashirin da biyar baya da suka shude na aiko sarkin
yakina Sharkas ibini Tauwab domin yazo nahiyarku
ku bashi bayi da dukiya mai yawa amma saika
bijirewa umarninmu ka shirya mayaka ka fita ka
kashe mana dakarunmu kuma ka maishe da sarkin
yakina makaho kuma musaki.Kayi sani cewa a iya
rayuwata duniya babu wanda ya taba yi mini irin
wannan wulakanci dacin mutunci sai kai.Naso tun
a wannan lokaci na fito da kaina nazo na rushe
kasarka na kwashe komai naku amma danayi
bincike a tsafina sai naga babu nasara a sannan
dole sai bayan shekaru ashirin da biyar.Tofa!Yanz
u
lokaci ya cika daidai wato shekaru ashirin da
biyar,yanzu haka maganar da nake maka saura
kwanaki uku kacal na iso birninka tare da dakarun
yaki guda miliyan Tamanin wato ninkin wadanda
na turo a wancan karon.Ina mai sanar maka da
cewa gaba dayan kasashen dana iske akan
hanyata duk na cisu da yaki na sami fiye da
adadin bayi da dukiyar da nake bukata.Zan karaso
kasarka ne kawai saboda kawai nayi ramuwar
gayya wacce tafi ta gayya ciwo.Na rantse da
girman mulkina da daukakata ko beran birninka ba
zan barshi da raiba,sai an kashe dukkanin
mazajenku manya da kanana,yara da tsofaffi.Gava
dayan matatenku saina kamasu a matsayin bayi
bayan anyiwa dukkaninsu fyade.Duk wani abu na
dukiyarku koda tsinke ne sai mu kwashe shi
sannan mu bunkawa birnin naku wuta har sai
komai ya kone ya zama toka.Ko ku shirya ku fito
ku taremu ko kuma mu iso mu riskeku,Mune
GUGUWAR ANNOBA kuma GOBARA DAGA KOGI
wacce bata da magani!.Sa'adda sarkin Yaki Zamud
ya gama karanta wannan wasika sai hankalin kowa
ya dugunzuma a fadar masu kuka suka kama
kuka,masu ihu suka kama ihu,masu gudu suka
kama gudu.Nan da nan fadar ta yamutse,ita kuw la
gimbiya Izaima saboda firgitar da tayi gami da
bakin ciki domin tasan cewa har abada burinta ba
zai cika ba.Cikin tsananin fishi sarki Garzub ya
mike tsaye ya daka tsawa kowa ya shiga taitayinsa
sannan ya dubi sarkin yaki Zamud yace aje a
shirya mini sulken yakina ni da kaina zan jagoranci
mayakanmu mu fita mu tari wadannan abokan
gaba.Koda jin haka sai Zamud ya dubi sarki
Garzub cikin matukar tsoro yace ya shugabana ka
tuna da irin tsananin masifar da muka shiga a
wancan karon da mukayi yaki da wadannan
mutane.A sannan nefa da miliyan goma kacal suka
fimu yawa.Yanzu kuwa ina tabbatar maka da cewa
sun fimu yawa da adadin miliyan arba'in da
biyar.Babu yadda za'ayi mu sami nasarar wannan
yaki.Bugu da kari da da yanzu fa ba daya bane.Ni
da kai yanzu duk girma ya fara
kamamu.Jarumtakar da mukayi a da yanzu ko
rabinta ba zamu iyayi ba.Tabbas ba zamu tsira ba
a wannan yaki,gaba dayanmu sai mun
hallaka.Kafin Zamud ya gama rufe bakinsa sai
yarima Uzaima ya tari numfashinsa yace idan ku
kun tsufa ai mu yanzu muke kan ganiyar
kuruciyarmu kuma mun gaji komai naku.Uzaima
ya dubi sarki Yace yakai Abbana kayi mini izini
naje na jagoranci mayakanmu.Koda jin wannan
batu sai sarki Garzub yayi murmushi yace da kyau
'dana tabbas yanzu nasan cewa banyi asarar
komai ba duniya tunda na haifi kamata.Tabbas kai
NAMIJIN DUNIYA ne wanda bai san tsoro
ba.Hakika matsoraci bashi zama gwani kowane
ne.Na yarda da jarumtakarka kuma nasan
zuciyarka a dake take.Ka tafi da albarkacinmu data
mai girma Larratu,nylayi maka izini ka jagoranci
wannan yaki.Koda jin haka sai Yarima Uzaima ya
juya ya fice daga cikin fadar.A wannan lokaci ne
sarki Rakalu ya lura da halin da 'yarsa gimbiya
Izaima ke ciki,wato ya ganta kwance a kas a sume
sai ya rusa ihu ya kara firgicewa dama tuni ya rude
bisa jin cewa sarki Madarus ya ratso ta cikin
birninsa ya gama da birnin.Cikin gaggawa sarki
Garzub ya bada umarni aka dauki gimbiya Izaima
aka shigar da ita izuwa cikin gidan sarautar kuma
aka ruga domin a kirawo likita ya dubata.Nanfa aka
fara shirye shiryen yaki aka rinka fito da
makamai,dawakai da guzuri.Kafin rana ta fadi tuni
an gama shiri tsaf.Idan kowa yaga irin shigar da
yarima Uzaima yayi ta yaki a wannan rana dole ne
ya firgita dashi domin daka ganshi kaga
mahaifinsa,bambancinsu kawai shine shi matashi
ne mai ji da SAMARTAKA.Shi kuwa sarki Garzub
ya fara manyanta domin shekarunsa sun haura
hamsin.Lokacin da yarima Uzaima ya gama
shirinsa tsaf ya fito filin fada inda miliyoyin
dakarun yaki ke tsaye suna jiransa sai kawai yaga
sarki Garzub,Sarki Rakalu da sarkin Yaki Zamud a
cikin mayakan.Al'amarin dayai matukar bashi
mamaki kenan ya dubi sarki Garzub cikin tsananin
mamaki yace yakai Abbana saboda me kuka fito
wannan yaki alhalin yanzu lokaci ne daya kamata
ace kun zauna a gida kun huta bautar da kukayi a
baya,in yaso mu mu wakilceku?Koda jin haka sai
Sarki Garzub ya dubi Uzaima yayi murmushi
sannan yace yakai dana kayi sani cewa wannan
yaki da zaka fita ya wuce dukkanin tunaninka,kuma
ina tabbatar maka da cewa ba'a taba yin
gagarumin yaki irinsa ba duniya a baya kuma har
anan gaba ma baza'ayi irinsa ba.Kai kadai ba zaka
iya jagoranci ba.Basirarka,tunaninka da hangenka
sunyi kadan dole ne ka bukaci gudunmawa irin
tamu ta tsofaffin hannu.Tabbas wannan yaki da
za'a fita ne na TSIRA KO HALAKA.Uzaima ya jinjina
kai domin wannan bayani ya ratsa shi
sosaimsannan ya dubi sarki Rakalu yace yakai
sirikina kai kuma saboda me ka fito wannan yaki?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
sarki Rakalu yace yakai Yarima Uzaima kayi sani
cewa a halin yanzu babu wani abu daya rage mini
a duniya face 'yata gimbiya Izaima domin a halin
yanzu nasan na rasa kasata,mulkina da
jama'ata.Idan har
. ban fita wannan yaki ba na taimaka maka an sami
nasara ba,indai ka mutu tabbas 'yata zata kashe
kanta domin a duniya babu abinda take so sama
dakai.Ni kuma babu abinda nake so sama da
ita.Indai ka hallaka a wannan yaki tabbas nima zan
kashe kaina.Koda jin wannan batu sai hankalin
Yarima Uzaima ya dugunzuma ainun ya rasa
abinda ke masa dadi a duniya.Cikin sanyin jiki ya
zaburi dokinsa ya fita da gudu.Nan take kuwa su
Sarki Garzub suka rufa masa baya suka nufi kofar
fita daga birnin Hirtoliya gaba dayansu.Idan mutum
yaga adadin dawakan wadannan mayaka da
mahayansu wadanda suka kasance ZARATAN
JARUMAI masu kamar zasu ci babu dole ne ya
firgita.
WANE IRIN AZABABBEN YAKI ZA'AYI IDAN
RUNDUNAR SU SARKI GARZUB TA HADU DA
RUNDUNAR SARKI MADARUS?
KUMA WANE BANGARE NE ZASU SAMI NASARA?
SHIN INA LABARIN SHARKAS WANDA SARKI
GARZUB YA MAYAR MUSAKI KUMA MAKAHO?
SHIN WANE IRIN AZABABBEN KARFIN DAMTSE
DANA SIHIRI SARKI MADARUS YAKE DASHI?
SHIN YARIMA UZAIMA ZAI DAWO GIDA A RAYE
HAR YA AURI GIMBIYA IZAIMA?
Mu Hadu TSIRA DA HALAKA littafi na Biyu don jin
cigaban wannan kasaitaccen kayataccen labari.
End Of Book 1.

TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part A.
LOKACIN DA UZAIMA ya jagoranci mayakan su
gaba daya suka fice daga cikin birnin sai suka
wanzu suna tafiya ba sassauci.Saida suka yini
suna tafiya har rana ta fadi sannan Uzaima yaja
linzamin dokinsa ya tsaya ya bayar da umarnin a
yada zango.Nan take kuwa aka shiga kafa
tantuna
da kokarin dafa abinci.Wannan karon ma ba'a fita
wannan yaki da mace ko guda daya ba kuma
yarima Uzaima ne ya kaddamar da dokar hakan
yayi koyi da mahafinsa bisa yadda yayi wancan
yaki dasu Sadauki Sharkas wato shekaru ashirin
da biyar baya da suka shude.Hadimai Hudu kadai
sarki ya taho dasu,daga mai dafa masa abinci sai
mai kula da shimfidarsa sai kuma shamakinsa
sannan kuma liktansa daban.Bayan an kafa
tantuna
har an kawowa Uzaima abincinsa yana shirin fara
ci kenan sai ga wani badakare ya
shigo.Bakadaren
ya zube kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya
shugabana sarki ne yace kaje ka sameshi a cikin
tantinsa domin kuci abinci tare.Koda jin wannan
batu sai yarima Uzaima ya cika da tsananin
mamaki domin shi a rayuwarsa kuma a iya
saninsa bai taba cin abinci ba tare da sarki ba,to
menene dalilin da sarki keson cin abinci tare
dashi
a yau?Haka dai yarima Uzaima ya mike zumbur
yabi wannan badakare suka fita tare.Da zuwansa
kofar tantin sarki Garzub sai wannan badakare
yaja
gefe daya ya tsaya a kusa da yan uwansa dakaru
wadanda suka yiwa tantin kawanya don tabbatar
da tsaro.Dama sun riski shamakin sarki a tsaye a
kofar tantin.Tun kafin su karaso bakin tantin
shamaki ya shiga ciki yayi busharar zuwa yarima
sannan ya fito.Kai tsaye yarima Uzaima ya kunna
kai cikin tantin.Ai kuwa yana shiga yayi arba da
mutum uku a zaune.Cikin tsananin mamaki da
fishi Yarima Uzaima ya tsaya cak!Ya kura musu
idanu kawai yaji kamar ya koma da baya.Ba
komai
ne ya haddasa hakan ba face Yarima yaga sarki
tare da abokinsa sarki Rakalu da 'yarsa gimbiya
Izaima.Cikin tsananin damuwa yarima Uzaima ya
durkusa a gaban sarki Garzub yace yakai Abbana
kai da bakinka ka gaya mini cewa mai girma
Larratu ya goyi bayan dokar dana kafa cewar
baza'a fito wannan yaki tare da mace ba koda
guda daya.saboda me yanzu aka taho tare da
gimbiya Izaima?Koda jin wannan batu sai sarki
Garzub yayi murmushi kuma ya mike tsaye ya
kama kafadun yarima Uzaima yace yakai dana
hakika duk abinda ka fadi gaskiya ne amma ka
sani cewa Izaima ba haifaffiyar birnin Hirtoliya
bace
dama dokar tana aikine akan macen data
kasance
haifaffiyar birninmu.Abu na biyu na yanke
shawarar
a taho da gimbiya Izaima ne domin idan muka
barta a gida zata iya shiga wani mugun hali bisa
tunani da fargabar halin da muke ciki gwara dai
ace tana kusa damu.Ina tabbatar maka da cewa
kasancewar Izaima tare damu bazai haifar da
wata
matsala ba facema karin guiwa.Akwai karin
bayani
idan mun kadaita ni da kai.Sa'adda Yarima
Uzaima
yaji wannan batu sai jikinsa yai sanyi bai kara
cewa komai ba kawai saiya koma gefe daya ya
zauna.Nan take gimbiya Izaima ta mike tsaye
taje
ta zubawa sarki Garzbu da sarki Rakalu abinci
sannan ta zubawa Uzaima nasa daban taje ta
ajiye
a gabansa.Izaima taje ta debi nata abincin itama
ta
koma gefe daya ta zauna.Ba tare da bata lokaci
ba
duk su hudun suka kama cin abincin.Duk sa'adda
Yarima Uzaima ya daga kai sai yaga ya hada
idanu
da gimbiya Izaima tana yi masa wani irin
TATTAUSAN MURMUSHI.Ko kau da kai batayi
kuma bata jin kunyar su sarki ma.Al'amarin dayai
matukar baiwa Uzaima mamaki kenan a lokacin
da
kunya ta isheshi ya kasa sakewa yaci abincin
sosai.Abinda Uzaima bai sani ba shine tsananin
farin ciki ne ya jefa Izaima a cikin wannan hali
saboda wannan ne karo na farko data taba
samun
dogon lokaci tare da Uzaima a iya rayuwarta
dashi.Hakika idan mutum yayi zurfi a cikin son
wani tofa baya ganin laifin wanda yake so
din.Shekara da shekaru Izaima tasan cewa
Yarima
Uzaima bai damu da ita ba kuma bai taba nuna
mata wata alama ba wacce ta nuna cewar yana
sonta amma duk da haka bata taba damuwa
ba.Abinda tayi imani dashi shine duk ranar data
mallakaeshi ya zama mijinta to da sannu shima
zai sota saboda tsabar kulawar da zata ta nuna
masa da TSANTSAR SOYAYYA.Haka dai su
Uzaima
suka gama cin abinci har suka kare gaba daya.A
sannan ne Yarima Uzaima ya mike yaje ya wanke
hannunsa a cikin wata kwatarniya da aka tanada
sannan ya dubi sarki ya nemi izinin tafiya.Sarki
Garzub ya mike tsaye ya kama hannun yarima
Uzaima ya jashi suka fice daga cikin tantin suka
koma can gefe daya domin tattaunawa.A wannan
lokaci dakaru da yawa sun yiwa sansanin
KAWANYA don tabbatar da tsaro.Sarki Garzub ya
dubi Uzaima yace yaka dana ka sani cewa in
badon wannan yaki ya taso ba da tuni yanzu kai
da Izaima kun zama MIJI DA MATA.Na sani
cewa
baka son Izaima amma yanzu zaka sota ne don
kawai ka faranta mini rai.Lallai ka sota saboda ni
don domin bani da wata bukata a wajenka wacce
tafi hakan.Lallai nasan cewa zaka so Izaima
anan
gaba da sannu.Bani da tabbacin wannan buri
nawa
zai cika kafin ganin karshen wannan yaki tunda
dole sai bayan yakin ne burin nawa zai cika wato
ganin aurenka da Izaima.Yakai dana inason a
yanzu kayi mini alkawarin cewar ko bayan raina
zaka auri Izaima indai kai da ita kun
rayu.Sa'adda
Yarima Uzaima yaji wannan batu sai hankalinsa
ya
dugunzuma,nan take idanunsa suka ciko da
kwalla
ya dubi Garzub yace yakai Abbana ka sani cewa
ni
mai ladabi ne da biyayya a gareka saboda haka
babu yadda za'ayi na ketare umarninka har
abada.Lallai na dauki wannan alkawari indai ina
raye bayan wannan yaki kuma Izaima ta rayu
lallai
zan cika maka burinka.Koda jin wannan batu sai
farin ciki ya lullube sarki
Garzub ya rungume Uzaima cikin tsananin murna
a
lokacin da duk su biyun hawaye ke zuba a
idanunsu saboda tunanin cewa abu ne mayuwaci
duk su biyun su rayu a karshen wanna gagarumin
yaki wanda basu san yadda karshensa zai
kasance
ba.A cikin tanti kuwa bayan sarki Garzub da
Yarima Uzaima sun fita sai Izaima ta ruga da
gudu
izuwa wajen mahaifinta ta fada kan kirjinsa tana
ta
kyalkyala dariyar farin ciki.Cikin matukar mamaki
Sarki Rakalu ya kama kafadun Izaima suka
fuskanci juna yace yake yata ke kuwa menene
dalilin wannan farin ciki naki haka?Izaima tace
yakai Abbana kayi sani cewa hakika yanzu ne na
fara ji a jikina cewar burina zai cika.Mafarkin
dana
dade ina faman yinsa dare da rana yana daf da
tabbata gaskiya.Koda jin wannan batu sai sarki
Rakalu yayi ajiyar zuciya sannan yace yake yata
hakika abinda kika fada gaskiya ne in ba don
wannan yaki daya taso ba bakatantan ai da tuni
yanzu buri ya cika.Ina so ki sani cewa ban fito
wannan yaki ba don kishin kasata ko jama'ata ba
sai domin ke kadai.Ki tuna cewa a halin yanzu

1 Comments On TSIRA DA HALAKA 1 and 2
avatar
hafeez-dalhatu

9 months ago

Reply

Godiya

Please Login or Register in order to submit comment