Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za'a
sami ciyawa da ruwa domin dabbobinsu su sami
abinci.Shugaban wadannan makiyaya ya kasance
dattijo dan kimanin shekaru saba'in da 'ya'ya ana
kiransa da suna Atiyar.Kallo daya mutum zai
yiwa
Atiyar ya gane cewa da can anyi GWARZON
JARUMI,domin gaba dayan surar jikinsa irin ta
sadaukai ce,amma tsufa ya sauya masa siffa ya
tauye masa kwarjini.Shugaba Atiyar yana da 'ya
guda daya,wata kyakkyawar budurwa ta gaban
kwatance mai suna Sulaira.Duk da cewa Sulaira
ta
kasance bakar fata amma kalar fatar
jikinta ta bambanta data sauran bakaken
mata,domin ita wankan tarwada ce,sannan tana
da
yalwar gashi mai santsi da sheki tamkar na
mutanen kasar Hindu.Tana da dara daran idanu
farare sol masu daukar hankali gami da dogon
siririn hanci da dan karamin baki.Tana da
kananan
hakora a jere reras kuma masu haske wadanda
duk
sa'adda ta bude bakinta mutum yayi arba dasu
sai
yaji kamar ya kwashesu ya maida su nasa
bakin.A
duk sa'adda Sulaira tayi murmushi kuwa mutum
na iya jin kamar an bashi SARAUTAR DUNIYA
domin take zata zare masa dukkan bakin cikin
dake cikin zuciyarsa.Kai kyawun diri kuwa a
wajen
Sulaira tamkar ita ta kera kanta,kwatance da
baki
bazai yiyuba sai abinda ido ya gani kawai.(Hmm
Kyakkyawa).Gaba
dayan mazajen wadannan makiyaya sun kasance
zakwakuran mayaka masu dakawa maza gumba
a
hannu.Asalin wannan makiyaya dangine mai
yawan
zuri'a wadanda adadinsu yakai dubu uku,amma a
yawon kiwon da sukeyi ne 'yan sumame ke kawo
musu hari don rabasu da dabbobinsu aka rinka
karkashe su har ya zamana saura su dari uku
kacal.Fiye da shekaru goma baya ba'a sake
kashe
koda mutum daya daga cikinsu ba.A wannan
shekarar ne shugaba Atiyar ya shirya gasar
neman
auren 'yarsa Sulaira a tsakanin samarin wannan
zuri'a tasu,kuma an yanke hukuncin cewa sai
anje
dajin dake da iyaka da birnin Hirtoliya sannan
za'a
fara gasar.Yanayin gasar shine za'ayi kokawa ne
a
tsakanin samari ashirin da hudu ya zamana cewa
kowa ya kara da kowa,wanda duk aka kasa kaishi
kas har aka gama gasar shine zai auri Sulaira.Su
Atiyar na cikin harhada kayansu kenan a lokacin
da Sulaira ke taya mahaifinta debo kaya daga
cikin
bukka suna dorawa akan rakumansu sai kawai
suka hango kura daga yamma ta turnuke sararin
samaniya.Al'amarin daya dugunzuma hankalinsu
kenan gaba daya.Nan take shugaba Atiyar ya
yiwa
jama'arsu tsawa yana mai basu umarnin a tusa
dabbobi a gaba da gudu domin ya fahimci cewa
wani gagarumin AYARI ne na yan sumame suka
danno wadabda ba za'a iya tsayawa ba a
tunkaresu har a fafata.Abinda ma bai sani ba
shine
abinda ke zuwa yafi karfin Ayari,RUNDUNA ce ta
gaban hankali.Nan fa jama'ar Atiyar suka sa
dabbobinsu akan gaba matansu a tsakiya suka
sakarwa dawakansu kaimi suna masu tsala
gudu.Koda suka waigo baya sai sukayi arba da
rundunar mayakan su Sharkas sun taso su a
gaba
cikin matsanancin gudu suna neman kuresu.Babu
abinda ya firgita Atiyar da jama'arsa face ganin
tsananin yawan wannan runduna dake kokarin
tarar
dasu da kuma kwarjininsu.A wannan lokaci
dakarun Sharkas ihu suke suna karawa
dawakansu
kaimi,suna cin burin su kurewa mutanen Atiyar
gudu su ragargajesu su kama na kamawa su
kashe na kashewa kuma su kwashe
dukiyoyinsu.Saida su Atiyar sukayi gudun sa'a
guda amma duk sa'adda suka waigo sai suga
ABOKAN GABAR sun kusa cimmusu,kawai sai ya
ja
linzamin dokinsa yai turjiya ya tsaya cak,cikin
tsananin razana sauran mazajen kabilar sukayi
tirjiya suka tsaitsaya.Daya daga cikinsu ya dubi
Atiyar cikin firgici yace ya shugabana me yasa
ka
tsaya alhalin kasan cewa ba zamu iya da wannan
muguwar runduna ba?Kafin Atiyar ya budi baki
yace wani abu sai ya fara zare takobinsa sannan
ya
dubi wannan jarumi da yayi masa tambayar yace
yakai Kufaru kayi sani cewa wannan gudu da
mukeyi gudun banzane domin bamu isa mu
tserewa wadannan yan sumame ba,dole ne su
kure
mana gudu kuma su karkashemu su wulakanta
matanmu,su debe dukiyarmu.Da hakan ta faru
salin alin gwara mu tsaya ko mutum dubu muka
kashe daga cikinsu ai mun rage asara tunda dole
ne su tafi da bakin cikin barnar da mukayi
musu.Sa'adda Atiyar yazo nan a zancensa ne
yaga
'yarsa Sulaira ta zuba masa ido hawaye na zuba
a
idanunta.Kawai saiya dubeta yayi murmushi yace
yake 'yata yaune ranar da zan tafi izuwa inda
mahaifiyarki ta tafi,saboda me zakiyi bakin ciki
maimakon ki tayani farin cikin zan sadu da
MASOYIYATA.Dajin Haka sai Sulaira ta zare
takobinta sannan ta share hawayenta kuma ta
yiwa
Atiyar murmushi tace nima ina fatan na bika inda
mahaifiyata ta tafi a yau domin banga amfanin
rayuwa ba a duniya muddin babu MASOYI.Atiyar
yace a'a yake 'yata bana fatan kema ki
gushe,domin idan kika gushe shike nan babu
sauran zuri'armu kenan.Na sani cewa abu ne
mayuwaci wadancan yan sumame dake
durfafarmu
su kasheku a matsayinku na mata.Lallai inason ki
rayu domin nan gaba kiyi aure har ki bar
baya.Gama fadin hakan keda wuya sai Atiyar yaji
gaba dayan sauran matan Ayarin nasu sun fashe
da kukakn bakin ciki domin sun san cewa yaune
ranar da zasu rabu da mazajensu.Adaidai wannan
lokaci ne ya zamana cewa tazarar dake
tsakaninsu
Su Atiyar da da Rundunar bata da yawa sai ya
daga takobinsa sama yace mu kare mutuncinmu
mu bada jikinmu da jininmu ga kasa.Kawai saiya
zaburi dokinsa da gudu ya tari abokan
gaban.Koda
ganin haka sai sauran yan uwansa mazaje suka
rufa masa baya.Kaico!Kaji maza wadanda suka
san
hakkin zuri'arsu da dukiyarsu kuma suka sallama
rayuwarsu domin su.Babu abinda zai baiwa
mutum mamaki face yadda ko kadan babu wani
tsoro ko fargaba a cikin zukatan su shugaba
Atiyar
duk da ganin tsananin yawan dakarun
Sharkas,amma suka taresu,duk da sun san cewa
ruwa ba sa'an kwando bane.Burinsu kawai shine
a
kashe su suna kokarin kare mutuncinsu in yaso a
yiwa kasa ado da jikinsu da jikinsu.A cikin gaba
dayan matan Ayarin su Atiyar Sulaira ce kadai ta
bugi kirji ta shiga cikinsu Atiyar domin ayi
wannan
yaki tare da ita saboda itama tana da Jarumtaka
ta
ban mamaki domin barewa batayi gudu ba 'yarta
tayi rarrafe.Koda aka gwamutse tsakaninsu
Atiyar
da dakarun Sharkas sai aka rincabe da
AZABABBEN YAKI.Karar karafa gami da
haniniyar
dawakai da dudufniyar
kofaton dawakan suka cika dodon kunne,kura ta
tashi ta baibaye wajen gaba daya,sai gashi dan
hakin da aka raina yana neman tsone ido,domin
rukunin farko na dakarun Sharkas wadanda suka
fara isowa gaban su Atiyar sun kasa aiwata
komai,kaifi kawai suka sha saidai kaga sassan
jikinsu na yawa a sama suna fadowa kasa.Jini
kuwa ya rinka fantsamuwa.Koda sauran yan
uwan
dakarun Sharkas suka hango abinda ke faruwa ga
yan uwansa sai suka karawa dawakansu kaimi
suna ihi mai firgitarwa.Nan da nan kuwa suka iso
kansu Atiyar sukayi musu rubdugu.Wayyo!Hakika
sarkin yawa yafi sarkin karfi.Nan da nan aka fara
yiwa dakarun Atiyar MUGUN KISA,saidai kaga an
zabtarewa jarumi kafadarsa ko hannunsa ko
kuma
a filla masa kansa gaba daya ya bingire kasa
matacce.Koda Atiyar da sauran sukaga irin
barnar
da ake yiwa yan uwansu sai suka ZAGE DAMTSE
sosai suka cigaba da BAKIN ARTABU suna yaki
suna kuka saboda takaici da bakin ciki.Kafin
cikar
rabin sa'a an gama kashe gaba dayan dakarun
Atiyar ya rage saura su biyu kacal,wato shida
'yarsa Sulaira suna ta namijin kokari.Gashi dai
miliyoyin dakaru sun kewayesu suna kai musu
hari
ta ko ina,amma sun kasa kaisu kasa.Su kansu
dakarun sunyi matukar mamaki bisa ganin irin
jarumtakar wadannan mutane biyu.Ana cikin
wannan bakin gumurzu ne sadauki Sharkas ya
karaso wajen bisa dokinsa a sukwane.Koda
ganinsa sai aka bude masa hanya,gaba dayan
dakarun nasa suka ja da baya aka daina yakar su
Atiyar akayi cirko cirko.A wannan lokaci baka jin
sautin komai face sautin sawayen dokin sadauki
Sharkas.Tun daga nesa kadan sadauki Sharkas
ya
kurawa Atiyar da Sulaira idanu yana mamakin
yadda akayi har suka iya shafe kusan rabin sa'a
suna fafatawa da dakarunsa ba tare da an kaisu
kasa ba.Fuskarsa a murtuke ya kurawa Atiyar da
Sulaira idanu.Koda ya gama nazarinsu yaga ma
su
biyu ne kacal kuma harma da mace a cikinsu sai
ransa ya baci ainun.Atiyar da Sulaira kuwa suna
hango Sadauki Sharkas sai jikinsu yayi sanyi
suka
tabbatar da cewa babu sauran wani kokari da
zasu
iyayi domin da gani ba tambaya,Kura zata ci
Mutum!Tunda Atiyar yazo duniya bai taba ganin
mutum mai fadi,tsawo da kirar karfi ba kamar
Sharkas.Koda sarkin birnin Hirtoliya wato sarki
Garzub da ake ta zancensa a nahiyar gaba daya
yasan cewa baifi rabin wannan sadauki ba.Kafin
Sharkas ya karaso garesu sai Atiyar ya dubi
Sulaira yace da ita yake 'yata ki dubi gawarwakin
yan uwanmu gasu nan birjik a kas.Ina murna
nima
zan bisu inda suka tafi.Kiyi mini alkawari bayan
tafiyata daya daga cikin wadannan azzalumai
bazai
amfani jikinki ba.Koda jin wannan batu sai
hawaye
ya zubowa Sulaira tayi jifa da takobin hannunta
sannan ta zare wata sharbebiyar wuka daga
jikinta
ta dubeshi tace yakai Abbana nayi maka alkawari
da zarar naga ka tafi nima zan tuta kaina inda ka
tafi.Koda jin haka sai Atiyar ya yiwa Sulaira
murmushin karshe sannan ya juya ya fuskanci
sadauki Sharkas wanda saura kiris ya iso
gabansa
ya rike takobinsa da hannu biyu.Lokacin daya
rage
saura taku uku kacak sadauki Sharkas ya iso
gaban Atiyar sai ya daka tsalle sama daga kan
dokinsa tamkar an zukoshi da kugiya ya kawowa
Atiyar mummunan sara.Atiyar ya kare saran da
dukkan karfinsa amma saida takobin Sharkas ta
raba takobin Atiyar gida biyu kuma ta tsarga
kafadar Atiyar ya bingire kasa matacce.Koda
ganin
abinda ya faru sai Sulaira ta tsandara ihu ta
daga
wannan wuka dake hannunta da nufin ta caka a
cikinta.Karar sukuwar dawakai ce mara adadi a
bayansu tasa Sulaira ta fasa idda nufinta.Cikin
firgici Sharkas da gaba dayan dakarunsa suka
waiga sukayi arba da wata runduna mai yawan
gaske ta durfafosu.Mayakan sun zare
makamansu
suna ihu suna haddasa karamar girgizar kasa a
dajin gaba daya.Koda ganin wannan runduna sai
Sharkas ya bushe da dariya duk da yaga cewa da
kadan nasa dakarun zasu fi wadancan yawa.Ba
komai ne yasa Sharkas yin dariya ba face ganin
cewa dakarun dake zuwa gaba dayansu bakaken
fata ne,shi kuwa rundunarsa duka ta sadaukan
larabawa ce wadanda ya yarda da jarumtakarsu
gami da bakin nacinsu da kwarewarsu a yaki.Ita
dai wannan runduna dake zuwa ba tasu kowa
bace
face su Sarki Garzub wadanda suka fito domin
kare kasarsu da dukiyarsu bisa jin cewa su
Sharkas na nan tafe.Nan take Sharkas ya
dakawa
Dakarunsa tsawa yace maza su tari ABOKAN
GABA.Ai kuwa sai duk suka sakarwa dawakansu
linzami suka durfafi abokan gabar.Wohoho!Wanda
duk bai ga sa'adda wadannan rundunoni biyu ke
kokarin haduwa da juna ba yayi asarar kallo
kuma
baiga mummunan tashin hankali ba a rayuwarsa
domin lokacin da dawakansu suka rinka kartar
kasa suna azababben gudu kuma mazajensu
dake
kansu suka zare makamai suna ihu saida dajin
gaba daya ya hautsine kamar sama zata rikito
kasa.Ai kuwa ana haduwa aka kacame da
masifaffen yaki tamkar mayakan duniya ne kaf
suka
hade.Nan fa wuri ya yamutse komai kallon
kurillar
mutum bai isa ya tantance bangaren da ke
samun
nasara ba,saboda jama'a gaba daya jikinsu da
dawakansu ya rine da jini.Da zarar mutum ya
daga
kansa sama saidai yaga hannaye,kafafuwa da
kafadun bil'adama na shawagi a sararin
samaniya.Shi kuwa jini daya fara fantsamuwa
yana
zuba a kasa tamkar teku ta balle.Kai ko daga
nesa
mutum yaji ihun da mazaje sukeyi a wannan filin
yaki dole ne ya kidime,mai karamar kwakwalwa
ma
zai iya zautuwa.Duk wannan bakin gumurzu da
akeyi babu mutum biyu a ciki wato babu sadauki
Sharkas da Sarki Garzub domin duk su biyu suna
tsaye a gefe daya bisa dawakansu kowa ya zuba
ido yana kallon bakin artabun da akeyi.Saboda
bala'in wannan yaki da akeyi Sharkas ya manta
ma
da batun Sulaira wacce ke tsaye a bayansa
kamar
gunki.
TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Daya (1)
Part C
Wacce ke tsaye a can bayansa kamar gunki tana
kallon wannan azababben yaki da ake
fafatawa.Sa'adda Sulaira ta fuskanci haka sai ta
rinka ja da baya a hankali har tayi nesa dashi
sosai taje can bayan wani katon dutse ta labe
tana
hangen abinda ke faruwa kuma tana kuka bisa
tunowa da mutuwar mahaifinta da dukkan sauran
zuri'arsu.Har izuwa wannan lokaci tana rike da
wannan wuka kuma hannunta nata karkarwa tana
shawarar ta kashe kanta ko kuma ta
fasa.Lokacin
da akayi yini ana wannan yaki ya zamana cewa
ana ta asarar rayuka a kowanne bangare ba
adadi
kuma an kasa gane bangaren da ke samun
nasara
sai hankalin Sharkas dana Sarki Garzub ya
dugunzuma suka rasa abinda ke musu dadi.Da
yake duk su biyun sun hau kan duwatsu ne masu
tudu suna iya hango juna kuma kowannensu yana
yiwa kowa kallon shakka,duk da cewa Sharkas
yafi
Garzub kwarjini da cika ido.Ashe duk wannan abu
dake faruwa Sarki Garzub ya lura da Sulaira
wacce
ta buya a can bayan dutsen da Sharkas ke bisa
kansa.Shi kuwa Sharkas yama manta da
al'amarinta.Lokacin da sarki Garzub ya fahimci
cewa idan rana ta fadi duhu ya soma za'a iya
tsayar da wannan yaki.Idan kuwa aka tsayar da
yakin Sharkas zai iya tunowa da batun Sulaira
yasa
a farautota a duk inda take a cikin dajin.Tun
sa'adda sarki Garzub ya kyallara ido ya hango
Sulaira yaga irin tsananin kyawunta sai nan take
yaji ya kamu da tsananin SONTA.Nan take Sarki
Garzub ya kada linzamin dokinsa ya sauko daga
kan dutsen da yake,kawai saiya zare takobinsa
ya
zaburi dokinsa da gudu ya nufi kan Sharkas yana
ihu da kururuwa.Koda ganin haka sai shima
Sharkas ya zare tasa takobin ya zaburi
dokinsa.Dokin ya daka tsalle daga kan dutse ya
duro kasa ya fita da gudu don haduwa da
takwaransa wato Dokin Garzub.Sai gashi duk su
biyun suna ihu da kururwa irin wacce ke firgita
mazaje.Kai inda ace a lokacin da suke wannan
dabbobin dajin na kusa da sai dukkaninsu sun
dimauce,na rami sun kama fitowa,na waje na
kokarin komawa rami su kuma na kan bishiya na
tarwatsewa.Yayin da Sharkas da sarki Garzub
suka
kusan haduwa ya zamana cewa saura baifi taku
biyar ba a tsakaninsu sai Sharkas ya daka tsalle
sama daga kan dokinsa ya kaiwa Garzub
mahaukacin sara irin wanda ya yiwa Atiyar
mahaifin Sulaiara ya tsargeshi gida biyu.Cikin
zafin
nama Garzub ya goce kuma ya kare saran da
takobinsa.Saboda karfin saran da kaifin takobin
Sharkas wacce ta kasance tsafaffiya saida
takobin
Garzub ta rabe biyu,takobin Sharkas ta datsa
bayan
dokin Garzub ya rabe biyu tamkar an yanka
lemon
bawa a tsakiya,dokin ya zube kasa matacce.A
lokacin da Sharkas ya duro kasa bisa
kafafunsa,shi
kuwa Garzub ya mike zumbur da sauri.Maimakon
Garzub ya fuskanci Sharkas sai kawai ya falfala
da
matsanancin gudu gaba ya nufi wannan dutse
wanda Sulaira ta buya a bayansa.Koda ganin
haka
sai Sharkas ya cika da mamaki ya bishi da kallo
kawai yana tunanin ko guduwa yake so zaiyi bisa
ganin abinda ya faru ga takobinsa da
dokinsa.Wata
zuciyar kuma sai tace da Sharkas haba ya za'ayi
sarki guda kuka GWARZON MAYAKI kamar
Garzub
wanda aka bashi labarinsa ace zai gudu a filin
yaki
alhalin ya jagoranci wadannan miliyoyin mayaka
kuma gashi har yanzu yakin ake ta fafatawa
wanda
babu alamar nasara ga kowanne bangare.Sadauki
Sharkas na cikin wannan tunani ne ya hango
Sarki
Garzub ya isa inda wannan dutse yake kawai sai
ya
sake hango Sulaira ta mike tsaye zumbur.A
tsorace
bisa ganin Garzub ya taho gareta.Nan take
Garzub
ya gaya maya wata maganar tunda Sharkas
nacan
nesa baya jiyo abinda suke tattaunawa.Kawai sai
yaga sun kama hannun juna sun kara falfalawa
da
gudu izuwa cikin daji.Koda ganin hakan sai
Sharkas ya juya da sauri da nufin ya kamo
dokinsa
ya hau ya bi sawunsu amma sai yaga ma dokin
nasa nacan baya don haka zai bata lokaci kafin
ya
isa inda dokin yake,kawai sai shima ya falfala da
gudun tsiya domin ya cimma su Garzub.Duk da
cewa sun bashi tazara mai dan yawa sai gashi
yana neman ya cimmasu saboda azababben
gudun
da yakeyi ya wuce nasu.Adaidai wannan lokaci
ne
Sulaira ta fafi kasa.Kafin Garzub ya sunkuya ya
tasheta tsaye tuni Sharkas ya dako tsalle ya dira
a
gabansa.Kawai sai yasa kafa ya naushi Garzub a
kirji.Tamkar ya daki tamoka haka Garzub yai
sama
ya fado kasa a galabaice,amma saboda naci da
juriya irin ta mazajen kwarai sai sarki Garzub ya
mike tsaye zumbur yayi sauri ya zare wadansu
tsofaffun Adduna guda biyu dake jikinsa suka
fara
kallon kallo suna zagaye juna.Ita kuwa Sulaira sai
ta koma gefe daya kawai ta zuba musu idanu
jikinta nata kyarma saboda tsoro.Sharkas ya dubi
sarki Garzub cikin kallon raini sannan ya budi
baki
cikin harshen larabci yace yakai wannan sarki
mai
taurin kai kayi sani cewa baka isa ka gujewa
balai
na ba.Ina tabbatar maka da cewa kafin gari yayi
duhu mayakan sun gama karkashe gaba dayan
mayakanka.Kai kuma yanzu zanyi maka kisan
gilla
a gaban wannan Kyakkyawar yarinya irinka
BAKAR
FATA sannan itama nayi mata fyade na kasheta
kamar yadda na kashe ubanta.Daga nan bazan
tsaya a ko ina ba nida dakaruna sai a cikin
birninka na Hirtoliya.Da zuwa zmuje mu baje
birnin gaba daya mu kame jama'arka a matsayin
bayinmu sannan mu kwashe dukiyoyinmu kuma
mu tona kasa mu debe albarkatun cikinta
wadanda
aka kabarta mana.Lokacin da Sharkas yazo nan a
zancensa sai yaga sarki Garzub yana duru duru
alamar cewa baya jin yarensa.Kwatsam!Ba zato
ba
tsammani sai sukaji Sulaira ta fara fassara
bayanin
da Sharkas yayi a cikin nasu yaren na bakaken
fata.Koda Sarki Garzub yaji jawabin sai zuciyarsa
ta kama tafarfasa kamar zata kone kawai saiya
ruga izuwa
8 hours ago
kan Sharkas suka ruguntsume da azababben yaki
suna masu kaiwa juna SARA DA SUKA cikin
tsananin ZAFIN NAMA,juriya da bajinta.Bisa
mamaki sai Sharkas yaga takobinsa ta kasa
lalata
addunan Garzub.Nan take ya gane cewa suma
addunan tsafi ne.Duk da cewa Garzub yana
matukar kokari wajen kaiwa Sharkas hari gami da
kare nasa harin amma yaji a cikinsa cewa ruwa
ba
sa'an kwando bane domin Sharkas ya fishi zafin
nama nesa ba kusa ba kuma karfin saransa ya
ninka nasa sau uku.A duk sa'adda Sharkas ya
kawowa Garzub sara ya kare sai yaji kamar zai
fadi
saboda karfin saran.In badon Garzub ya kasance
mai tsananin juriya ba da naci da tuni Sharkas
yayi
masa kisan farat daya.Lokacin da aka sami rabin
sa'a ana wannan gumurzu tsakanin Sharkas da
Garzub ya zamana cewa babu wanda ya sami
nasarar komai sai Sharkas ya fusata ainun ya
sauya salon yaki ya zamana cewa ya hada da
kaiwa Garzub NAUSHI DA BUGU da hannu da
kafa.Da yake yana da matukar zafin nama sai
kawai ya shammaci Garzub ya gabza masa
wawan
naushi a kumatu.Saboda karfin naushin saida
wani
gudan jini yayi fitar burgu daga cikin bakin
Garzub
ya kife kasa rub da ciki.Kafin ya yunkura ya
tashi
Sharkas ya soka masa takobi a bayan
kafadarsa.Garzub da Sulaira suka tsandara ihu a
lokaci guda.Shidai Garzub ihun da yayi na
tsananin
jin zafi da zogi ne.Ita kuwa Sulaira ihu ne na
firgita bisa ganin an sami lagon wanda ke kokarin
kare rayuwarta.Sarki Garzub ya sake mirginawa
kasa a matukar galabaice lokacin da jini ke
bulbula
a kafadarsa.Sharkas ya tsaya a kansa yana
kyalkyala dariyar mugunta.Duk da cewa idanun
Garzub sun fara lumshewa yana gani dishi dishi
sai ya tuno da bakin jawabin da Sharkas yayi
dazu
wanda Sulaira ta fassara masa.Nan take ya
yunkura da dukkan karfinsa ya mike zumbur suka
cigaba da fafatawa.Ai kuwa suna farawa ne
Sharkas ya sami nasarar sake cakawa Garzub
takobi a gefen kirji.Take takobin ta lume a cikin
kirjin ta faso ta gadon baya.Sharkas na zare
takobin jini yai tsartuwa.Saida Garzub yayi
katantanwa a tsaye sau uku ya tafi kasa luu!Zai
fadi amma saboda tsananin juriya saiya daka
tsalle
sama kamar sufurin ya zabgawa Sharkas naushi
a
fuska iya karfinsa.Saboda mugun zogin da
Sharkas
yaji bai san sa'adda ya saki takobinsa ta fadi
kasa
ba kuma yayi taga taga da baya kamar zai
fadi,amma da yake giwa ba wasa bace saiya
mike
zumbur ya cafi wuyan sarki Garzub ya rinka jera
masa naushi a ciki kamar ana doka tabarya a
cikin
turmi.Nan da nan ya lugui-guitashi,Garzub ya
zamo tamkar tsumma.Sharkas ya warbar dashi a
kasa tamkar yayi jifa da gawa.Kawai sai ya juya
izuwa inda takobinsa ta fadi da niyyar ya daukota
ya gididdiba Garzub.Har ya sunkuya yakai hannu
zai dauko takobin sai idanun Garzub suka bude
ya
hango abinda ke shirin faruwa.Daga kwancen
Garzub ya dafa kasa da hannayensa biyu kawai
yayi tsalle tamkar an cillashi daga cikin kwari ya
fada kan Sharkas suka kife kasa tare suka
rukunkume juna da kokawa gami da naushi suna
murgin murgin.Ai kuwa basu ankara ba suka
tsinci
kansu a sama wani tsauni mai matukar tsawo.A
firgice Sulaira ta bisu da gudu izuwa kan tsaunin
amma kafin ta riske su sun sallamo kasa izuwa
kasan tsaunin dukkaninsu suna masu tsandara
ihu
domin sunsan cewa dukkaninsu karshen su
yazo.Ai kuwa suna fadowa kasan tsaunin sai
kowannensu kansa ya bugu da dutse duk suka
sume,amma sai ruwa ya tafi da Sharkas,shi kuwa
Sarki Garzub sai wani dutse ya tokareshi.Yayin
da
Sulaira ta leko kasan tsaunin ta hango Garzub a
baje kamar gawa sai ta jua da baya da gudu ta
gangaro izuwa kasan tsaunin tayi kundunbala ta
daka tsalle ta fada cikin kogin ta kama iyo har ta
isa inda sarki Garzub yake.Da kyar da sidin goshi
ta janyoshi daga cikin kogin izuwa gaba.Koda ta
kara hancinta daidai nasa sai taji yana numfashi
kadan kadan,amma data dubi mugun raunin dake
kirjinsa da bayansa sai ta karaya ta fara tunanin
abune mayuwaci ya rayu.Har izuwa wannan
lokaci
tana iya jiyo ihun mazaje daga inda suke a can
inda aka wannan bakin yaki kuma a sannan ne
gari
ya fara yin duhu.Sulaira ta dubi Garzub taga kato
ne ba zata iya daukarsa ba kawai sai ta kama
jansa a kas tayi ta jansa har saida tayi nesa da
wannan kogi ta kaishi har cikin wani kogon dutse
mai zurfin gaske.A sannan ne ta juyo an buga
gangar tsaida Yaki.Kamar daukewar ruwan sama
haka ta daina jiyo karar MAKAMAN YAKI da ihun
mazaje.Nan take Sulaira tayi tsafi sai kofar
wannan
kogon dutse ta rufe ruf da dutse tamkar babu
wata
kofa data taba wanzuwa a jikinta.Ta sake yin
tsafi
ta kunna wuta a jikin itatuwa kogon ya haskake
da
haske.A sannan ne ta bude jakarta ta guzuri ta
debo garin magani ta rinka cusawa a cikin ramin
raunikan Garzub har saida ta cike ramukan jini
ya
daina zuba.Har izuwa wannan lokaci numfashin
Garzub baya fita daidai akwai lokacin ma da
numfashin ya dauke gaba daya tayi zaton ya
mutu
sai daga can kuma numfashin ya dawo.Cikin
matukar farin ciki ta cigaba da sa masa magani
a
kansa inda ya sami rauni lokacin da suka rikito
kasa shida Sharkas daga kan tsauni.Bayan
Sulaira
ta gama sawa Garzub magani sai ta sake bude
jakar guzurinta ta dauko wani abinci ta ci ta
koshi
ta daga salkar ruwanta wacce ke cike fal ta
kwankwada.Gama shan ruwan keda wuya sai ta
bingire ta kama bacci saboda tsananin
gajiya.Wannan shine abinda ya faru tsakanin
Sarki
Garzub da sadauki Sharkas bayan sunyi bakin
gumurzu har Sulaira ta ceci rayuwar Sarki
Garzub.
*** *** ***
A can filin yaki kuwa ana buga gangar tsaida
yaki
sai kowanne bangare suka ja da baya.A sannnan
ne aka lura da irin mummunar barnar da akayi.A
bangaren
bakaken fata kuwa,wato dakarun sarki Garzub an
kashe sama da mutum miliyan ashirin,wato
wadanda sukayi saura basu kai miliyan goma
ba.A
bangaren fararen fata kuwa wato labarawa
Dakarun
Sharkas mutanen da aka kashe sun kai miliyan
goma sha biyar,wato suma wadanda suka rage
basu fi miliyan ashirin da biyar ba.Nan take
kowanne bangare suka kwashe gawarwakinsu
kuma aka baiwa juna tazara mi yawa sannan aka
kafa tantuna.Har sai bayan an gama binne
gawarwaki sannan kowannen bangare suka
fahimco cewa basu ga shugaban su ba,wato
larabawa basu ga Sharkas ba,suma bakaken fata
basuga sarki Garzub ba.Nan fa hankalin kowanne
bangare ya DUGUNZUMA aka fara shawarwari
akan
a tafi neman shugabannin.Amma kuma da aka
fahimci yin hakan yana da matukar hadari tunda
gari yayi duhu kuma yakin zai dade kaurewa ayi
tayinsa ba tare da an fahimci inda aka dosa ba
sai
kowanne bangare suka hakura da batun tafiya
neman shugabansu har sai gari ya waye ido na
ganin ido.
*** *** ***
A can cikin kogon dutse kuwa tunda Sulaira ta
bingire ta kama barci bata farka ba sai da dare
ya
raba.Tarin Sarki Garzub ne ya tasheta yana mai
ambatin ruwa.A firgice Sulaira ta farka,koda taji
Garzub na ambaton ruwa sai ta ruga da gudu ta
dauki salkar ruwanta tasa masa a baki yayi kurba
uku da kyar sai tari ya sake turnukeshi.Al'amarin
daya dugunzuma hankalin Sulaira kenan ta fara
kokarin ciccibar kafadunsa domin ta tayar dashi
zaune amma sai taji yayi kara saboda zafin da
raunikan jikinsa sukayi masa.Cikin sauri Sulaira
ta
mayar dashi kwancen a lokacin da idanunsa ke
lumshewa.A sannan ne tayi tunanin cewa Garzub
na bukatar abinci.Amma inda matsalar take shine
ba zai iya cin irin abincin guzurinta ba dole ne ta
samo masa abu mai ruwa musamman ma
madarar
shanu.Koda gama aiyana hakan sai Sulaira ta
tuno
da dubunnan shanunsa da ragunansu da
tumakansu wadanda aka kadasu cikin daji
sa'adda
aka hango dakarun Sharkas sun kawo harin
Sumame.Nan take Sulaira ta mike ta nufi bakin
kofar kogon ta shafeta da hannu sai kofar ta
sake
budewa ta fice.Tana fita ta sake yin tsafi kofar
ta
sake shafewa.Cikin sanda Sulaira ta nausa cikin
dajin tana hange hange da waige waige cikin
alamun tsoro.Haka dai ta cigaba da tafiyar har ta
hango inda rundunar mayakan biyu suka kafa
sansanisu suna makotaka da juna.Sulaira ta
ratsewa hanyar da zata kaita izuwa inda
sansanin
rundunonin biyu suke ta falfala da gudun tsiya
izuwa wata hanya daban wacce dabbobinsu suka
bi tana gudu tana duba sawun dabbobin
nasu.Saida Sulaira ta shafe sa'a uku cur tana
gudu
a cikin daji ko alamun dabbobin nasu bata gani
ba,a sannan ne kuma taji ta gaji likis yayi data
iso
gaban wani katon dutsw mai tsawon gaske da
madaidaicin fadi.Sulaira ta fadi gaban dutsen
tana
haki cikin alamun karayar zuciya.A wannan
lokaci
ne ta tuno da mahaifinta Atiyar da sauran
zuri'arsu.Kawai saita fashe da matsanancin kuka
tana mai aiyanawa a ranta cewa menene
amfanin
rayuwarta a duniya tunda bata da kowa.Nan take
Sulaira ta zare wannan sharbebiyar wuka tata ta
daga sama zata kirba a cikinta sai ta tuno da
batun sarki Garzub wanda ta kaishi can cikin
kogon dutse ta barshi a cikin mayuwacin hali
wanda rayuwarsa ke tsakanin RAI DA
MUTUWA.Nan fa Sulaira taji bai kamata ace ta
kashe kanta ba ayanzu,zaifi kyau ta koma kogon
dutse tayi iya kokarinta wajen ceto rayuwar
Garzub.Ita kanta Sulaira sai ta cika da mamaki
bisa dalilin da yasa ta damu da rayuwar Garzub
alhalin ta rasa ma mahaifinta.Wata zuciyar sai
tace
da ita ai dole ne ki ceci rayuwar Sarki Garzub
domin inba don shi ba da tuni yanzu an miki
fyade kuma anyi miki KISAN GILLAH.Ashe kuwa
dole ne kiyi masa halacci kuamar yadda ya siyar
da rayuwarsa ya tari sadauki Sharkas don
kubutar
da taki.Lokacin da Sulaira tazo nan a zancenta
sai
tamike tsaye da nufin ta koma da baya.Ba zato
ba
tsammani sai kawai ta jiyo kukan shanu a bayan
wannan katon dutse da take.Cikin sauri ta ruga
izuwa bayan dutsen ai kuwa sai tayi atba da
dukkanin dabbobinsu a bakin wata katuwar
korama
suna ciki ciyawa da shan ruwa.Saboda farin ciki
Sulaira batasan sa'adda ta bushe da dariya
ba.Duk
da cewa dare ya raba a wannan lokaci kuma
duhu
yayi amma akwai hasken sararin samaniya kadan
don haka sai Sulaira ta ruga izuwa inda dabbobin
suke.Wani abin mamaki daya faru shine dabba
daya bata gudu ba daga wajen har Sulaira ta
karaso cikinsu ta tsaya tana dube dube tana
neman wata farar saniyar mahaifinta wacce tayi
matukar sabo da ita.Kawai sai Sulaira taji an
dungureta ta baya,a tsorace ta waiga da sauri
sai
taga ashe wannan farar saniya ce.Cikin matukar
farin ciki Sulaira ta rungume saniyar ta fashe da
kuka.Tsawon yan dakiku Sulaira na rungume da
saniyar tana kuka.Daga can sai ta shiga
karkashin
saniyar ta fara tatso nononta tana zubawa cikin
battar ruwanta har saida ta cika battar sannan ta
mike tsaye ta juya da baya domin tabar wajen.Ai
kuwa sai taga wannan saniya ta biyota a
baya.Sulaira ta kora saniyar baya domin ta daina
binta amma taki.Abinda ya daurewa Sulaira kai
kenan musamman dataga cewa gaba dayan
sauran
dabbobin babu wanda ya biyota sai wannan farar
saniya.Tun Sulaira na dada cigaba da korar
saniyar har ta gaji ta kyaleta suka jera tare
sukayi
tafiya a cikin dajin ya zamana cewa Sulaira ta
kama wata karamar igiyar dake wuyan saniyar ta
cigaba da janta suna tafiya.Duk wannan tafiya da
sukeyi Sulaira a tsorace

1 Comments On TSIRA DA HALAKA 1 and 2
avatar
hafeez-dalhatu

9 months ago

Reply

Godiya

Please Login or Register in order to submit comment