Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabanki dakuma yadda kika bani labarinki
naji cewar kin rabu da daya 'yar taki wato usainar
Dabira wacce kika bayar da ita ga 'yar uwarki Nuzaira.
Tun daga sannan na ji na kamu da tsananin
tausayinki da kuma kaunar dabira, shiyasa na rokeki
akan cewa komai dadewa kada kisanar da dabira
cewa bani ne na haifeta ba har sai bayan shekara
ashirin alokacin da zatayi aure murabu da ita an nuna
mini a mafarki cewa a gobe-gobennen allah zai kawo
wani sadaukin jarumin musulmi daga can nashiya
daban wanda yafi Dabira jarumtaka kuma suna
haduwa zasu kamu da son junansu akan wannan
daliline na yi kundun bala na shirya wannan haduwa
tamu domin na bayyana miki sirrin zuciyata. Idan
harkin amince da tayina ina son a daura aurena da ke
gobe".
Koda jin wannan batu sai humaira ta fashe da kukan
farin ciki taji kamar ta rungume sarki raihan humaira
ta budi baki domin tace wani abu sai kawai suka ga
dabira ta fito daga cikin turakar humaira idanunta
sun yi sharkaf da hawaye. Cikin firgici da matukar
mamaki sarki raihan da humaira suka mike tsaye
suka kura mata idanu. Dabira tasa hannu ta share
hawayen ta sannan ta dubesu daya bayan daya tace,
"me yasa kuka buye mini wannan sirri tsawon
shekara da shekaru ? Na rantse da girman allah duk
inda 'yar uwata take sai na tafi nemanta! Waye ya
kashemini mahaifina? Kuma ko waye ya kashe
mahaifina sai na bincikoshi duk inda yake na
hallakashi! Ina tabbatar muku da cewa bazan taba
yarda nayi aure ba face na cika wadannan burika ".
Koda gama fadin haka sai taji ta tsani birnin kisra da
duk mutanen cikinsa saboda jin cewa asalin
mahaifiyarta humaira daga can take.
Koda sarki raihan da humaira suka ga dabira ta fashe
da kuka sai han kalinsu ya dugunzuma suka yunkura
zasu je gareta domin su rarrasheta amma saita ruga
waje da gudu ta nufi turakarta. Da zuwa sai ta shiga
can cikin dakinta mai kofa ta rufe ta sake fashewa da
sabon kuka.
Cikin sauri humaira da sarki raihan suka karaso kofar
dakin dabira suka yi ta rokonta akan ta bude kofar
amma taki, duk suka hakura suka koma turakar
Humaira suka zauna.
Tsawon lokaci duk su biyun sukayi tagumi basu
ce komai ba. Daga can sai sarki ya mike tsaye ya
dubi Humaira yace, "yanzu muna cikin tashin
hankali da damuwa saboda haka sai gobe naji
amsar tayin dana yi miki "
Koda gama fadin hakan sai sarki yajuya ya fice
daga cikin falon gaba daya. I ta kuwa Humaira ta
bishi da kallo kawai cikin damuwa da tunani.
Har dare ya raba sosai Humaira bata rintsaba
saboda fargaba da tunani bisa jin abinda Dabira
tafada cewar duk inda 'yar uwarta take saita tafi
nemanta kuma sai ta nemi wanda ya kashe
mahaifinta. Shima shi.
Abinda ya tayar wa da humaira hankali shine,
tasan irin bala'in sarki Daksur da sadauki Zaihar
da irin sadaukantakar da karfin tsafinsu,don haka
yana tsoron karonta da su don tana ganin cewa
zasu iya hallaka farat daya muddin ta kai kanta
inda suke.
Haka dai humaira ta kasance acikin tsananin
tashin hankali ta kasa zaune ko tsaye ta dinga
kai komo acikin turakarta. Tana cikin wannanhali
ne ta tuno da batun tsoho kasim au yi ` yar hira
nan take ta aiyana zuwa dakin tsoho kasim ta
tasheshi koda kuwa barci yake yi. Batare da bata
lokaciba humaira tafito daga cikin turakarta
acikin dare da durfafi bangaren da dakin tsoho
kasim yake duk inda ta ratsa sai taga dakaru a
tsaitsaye suna kan aikinsu na gadi kuma gaba
dayan gidan sarautar a haskake yake da fitilu
gwanin ban sha awa duk inda tazo giftawa sai
dakaru su ratse su bata hanya babu inda aka
dakatar da ita har ta iso kofar dakin tsoho kasim.
Da zuwanta sai ta iske kofar dakin a kulle take
ruf. Haka ma gaba dayan tagogin dakin. Koda
ganin haka sai jikin humaira yayi sanyi ta tuna
cewa yau fa tsoho kasim acikin matukar gajiya
yake sakamakon artabun da yayi da kurayen nan
har maya sami raunika saboda haka bai kamata
ta tasheshi daga barci ba nan take humaira ta
juya da baya da nufin ta koma turakarta. Amma
sai ta jiyo sautin kuka acikin dakin tsoho kasim
kuma sautin na muryar mace ne. Al amarin daya
matukar bata mamaki ke nan domin ita a saninta
ai tsoho kasim ne aciki wannan daki to mene
neya shigar da mace cikin dakinsa ? Cikin
fargaba da sanda ta koma izuwa kofar dakinta
leka ta cikin kafar kubar ai kuwa tana lekawa ta
hango zabgegiyar kyakkyawar budurwa ta gaban
kwatance zaune akan kujera tana faman sharba
kuka a gefe daya daya ga wadannan tufafi na
tsoho kasim ajiye a gefe daya wadannda akansu
an dora layu da guraye na tsafi humaira ta
kurawa fuskar budurwa idanu kawai sai ta lura
da idanunta taga iri daya ne sak! Dana dabira.
Koda ganin wannan al amari sai zuciyar humaira
ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayenta
biyu ta juya baya cikin ajiyar numfashi tace a
ranta. ” Duk yadda aka yi wannan yata ce
ussainar dabira tazo mana a cikin kamannin
tsoho kasim mene ya kawota garin nan ? Shin
tazo neta cutardamu ko kuwa ta gano cewa mu
jininta ne ta zo domin mu sadu ? ”
Nan fa humaira ta kasa baiwa kanta amsar
wadannan tambayoyi cikin tsananin fargaba da
tashin hankali humaira ta koma dabaya don ta
koma turakarta. Lokacin da ya rage saaura kiris !
Ta iske kofar turakarta sai kawai taga dabira
tsulum ! A gabanta kamar daga sama ake jefota
kafin humaira ta budi baki tace wani abu sai
dabira ta dubeta tace. Yake ummata menene ya
kaiki dakin bakonmutsoho kasim ? Kai sani sani
cewa nida sarki duk bamu yarda da tsoho kasim
Ba kuma na funkanci cewar akwai wata alaka
tsakanin da shi. Da shi saboda haka gobe kafin
na bar garin nan zaki yi mini cikekken bayani
akan rayuwarki kafin ki baro birnin kisra ki da
dawo nan misra da wannan kalami nake miki
sallama allah ya tashe mu lafiya ” koda gama
fadin hakan sai dabira tajuya ta koma izuwa cikin
dakinta tamai da kofa ta rufe nan fa humaira ta
sake rudewa ta kidime ta rasa abin da ke mata
dadi a duniya domin bata san bayanin daya
kamata ta yiwa dabira da sarki ba a goben. Da
kyar humaira ta koma cikin dakinta ta kwanta
taci gaba da tunani da zullumi. Har aka yi
assalatu bata sami damar yin barciba. Kamar
yadda humaira ta kasa barci hak shima sarki
raihan ya kasa barci saboda tsananin damuwa
har yaje masallaci da asuba. Ya dawo turakarsa
bairintsaba. Itama dabira bata rintsa ba wato dai
duk su ukun basu yi barciba amma wani ikon
allah ita jaruma yazila batasan saadda barci
yasace taba daf da lokacin daza ayi sallar asuba.
Lokacin da aka idar da sallah a masallaci sarki
ya waiga ko ina bai ga tsoho kasim ba sai jikinsa
ya sake bashi lallai akwai wani boyayyen al amari
a kansa don hak sarki na baro masallaci sai ya
tura aka kirawo dabira yace da ita ta tafi izuwa
dakin bako tsoho kasim ta fada dakin cikin
shammace taga a halin da yake ciki domin baizo
masallaci sallar asubaba lallai akwai wani abu na
shin gaskiya a tare da shi. Domin tun da ya garin
babu wanda ya ga yayi sallah koda jin wannan
batu sai dabira tatafi izuwa dakin tsoho kasim a
fusace wadansu dakarunta guda biyu na biye da
ita. Tana sanye da hularta ta karfe.
Da zuwan kofar dakin tsoho kasim sai tasa
kafarta guda ta daki kofar. Take kofar ta burma
ciki ta fadi kasa. Karar dukan kofar na yasa
yazila ta farka firgigit! Kafin tayi wani yunkuri sai
kawai taga jaruma dabira tare da dakartunta biyu
tsaye akanta rike da makamai koda su dabira
sukayi arba da yazila sai suka cika da tsananin
mamaki. Gashi dai agefe daya kuma suka ga
wannan tsufaffun kayan tsoho kasim ga layu da
gurayen tsafi akansu sai al'amarin ya daure musu
kai.
Nan fa Dabira ta kurawa yazila ido tana tunani a
zuciyarta. Abinda ya fadomata a rai shine, ta san
fuskar yazila tun da sun gwabza yaki ba sau
dayaba, amma bata taba yimata kallon kurilla ba
sai yau. Tabbas dai yanzu ta gane cewa abokiyar
gabarta ce tayi bad-da-kama ta shigo birninsu
domin ta cutar dasu. Amma kuma me yasa a
bokiyar gabar tata take kama da ita? Anya kuwa
yazila ba ita ce 'yar uwarta ba? Ai waka abakin
mai ita tafi dadi,bari naji daga bakinta.
Nan take dabira ta dubi yazila tace, "wace ce ke,
kuma meyasa kika batar da kamanninki kika
shigo birninmu?".
Koda jin wannan tambaya sai yazila ta bushe da
dariya tace, "Nice jaruma Yazila babbar abokiyar
gabarki! Kuma na shigo wannan birnin naku ne
domin kawai nayi yakin karshe dake mu
bambance tsakanin aya da tsakuwa!!!".
Da jinhaka sai itama Dabira ta bushe da dariya
sannan ta hade rai tace, "ke tsohuwar abokiyar
gaba kiyi sani sani cewa kinka wo kanki GIDAN
MUTUWA! Lallai bazamu kashekiba da azaba ko
taron dangi ba, lallai nida ke zamu raba raini a
yau dinnan. A matsayin ki na mai laifi, dole ne
yanzu nasa a kamaki akaiki kurkuku a tsare ki
inyaso yau da farkon yamma yammaci afito dake
izuwa filin fada inda zamu fafata yakin karshe ni
dake inda za arufe mu a cikin keji har sai
dayanmu ya wanda duk ya rayu sai ya bude kejin
ya fito. "
Koda gama fadin hakan sai dabira ta dubi
dakarunta dake tare da ita tace dasu su sawa
Yazila ankwa sannan su tafi da ita kurkuku,
Bisa mamaki sai dabira taga yazila ta tsaya
kyam! Ansa mata ankwa a hannayenta da
kafafunta batare da tayi wani yunkuriba sai
murmushi kawai take har aka tusa keyarta a
gaba aka tafi da ita. Al'amarin daya matukar
jefata cikin tsananin mamaki kenan da wasi-wasi
domin a sanin dabira yazila jarumace ta gaske ko
ita kanta bata isa tasa mata ankwa ba cikin
sauki, amma sai gashi dakarunta sunsa mata
ankwar sun tafi da ita.
Abin dabata saniba shine yazila tana sane ta saki
jiki aka kamata saboda dalili uku. Dalili na farko
shine tana son su fafata yaki domin dabira ta cire
mata wannan laya dake wuyanta dalili na biyu
shine tanason takai dabira kas har ta cire wannan
hular karfe ta kanta domin taga kamanninta dalili
na uku shine bata son dabira tace zata bita sutafi
izuwa birnin kisra don daukar fansa akan sarki
daksur shiyasa taki gayamata cewa ita yar
uwartace ta jini
Bayan an tafi da yazila izuwa kurkuku sai dabira
ta tattara wadansu layu da guru na tsafi ta kunna
musu wuta nan take suka kune kurmus ! Suka
zama toka. Har tajuya zata fita daga cikin dakin
sai taga jakar guzurin yazila a rataye ajikin bango
kai tsaye ta nufi inda jakar take zata dauko ta
duba abin dake ciki sai kawaitaji an kira sunanta.
Tana waigowa sai taga ashe sarki raihan ne a
tsaye da kansa. Sarki raihan ya dubeta fuskarsa
babu walwala yace " yan zu kin daina fushi
damuzaki iya sauraron bayanin dazan yimiki ?”
Koda jin haka sai idanun dabira suka ciko da
kwalla. Tace. ” Ka gafarceni yakai abbana. Kayi
sani cewanima nayi nadamar nuna muku fishina.
Ina fatan zaku gafarceni ? ” Koda jin wannan
batu sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Babu
komai yake. Yata yanzu dai kizo muje fada akwai
wani gagrumin abu daya taso wanda zamu zauna
mu tattau tare da sauran yan majalista hukuncin
da kika yanke yanzu akan wannan abokiyar gaba
tamu dataso ta yaudaremu yayi kyau ”.
Koda jin haka sai dabira ta taho wajen sarki
raihan ta ruke hannunsa suka jera suka fice daga
cikin dakin ya zamana cewa gaba daya ta manta
da batun wannan jaka ta yazila.
Ita dai wannan jaka babu komai a cikinta face
wadansu kayayyakin tarihi wadanda da zarar
humaira tayi arba zata shaidasu. Domin kaya
nena yar uwarta nuzaira wanda ayanzu haka tana
da irinsu aajiye kuma kullum sai ta kallesu don
tunowa da yar uwarta ta. Banda wadanda kayan
tarihi kuma. Akwai rigarda aka sawa yazila
aranda aka haifeta kuma dabira ma tana da irin
rigar wacce har yanzu humaira nanan da ita
aajiye don tarihi. Dabira ta sha ganin humaira
tana dauko rigar tana kallenta kawai har tana
kwallah amma duk saadda ta tambayeta dalili sai
tace da ita kawai ta tuno wahalar data sha ne a
lokacin data sami cikinta saadda ta haifeta.
Lokacin da sarki raihan da jaruma dabira suka iso
fada sai suka iske gaba dayan yan majalistar a
zaune. Suna jiran karasowarsu al amarin daya
razana dabira kenan domin ta san cewa duk
saadda taga yan majilista sunyi irin wannan taro
ya zamana cewa kowa ya zo to lallai akwai wani
abu gagarumi al amari daya taso. Ko dai annoba
ta barko. Ko kuma yaki zaayi.
Da shigowar dabira da sarki cikin fadar sai suka
je suka zauna inda suka saba zama. Zaman su
keda wuya sai wazirin sarki Raihan yayi kyaran
murya sannan yace, "yaku 'yan majalissar
wannan birni namu mai albarka, da yawa daga
cikinku sun san dalilin taruwarmu anan. Ga
wadanda basu saniba, yanzu sai su sani.
Wannan al'amari ba komai bane face a yau
dinnan kimanin sa'a daya data shude mun sami
rahoton cewar abokan gabarmu mutanen birnin
kisra sun taho da zugasama da dakaru miliyan
dari hudu da hamsin domin su yakemu.
Wannan zuga ta hada da dakarun gudummawa
daga sauran kasashen kafirai na wannan nashiya,
kuma sun taho da alwashin cewa wannan karo
adan za a shekara ana wannan yaki bazasu
janyeba har sai sun tabbatar da cewa sun baje
birnin mu sun kashe mazajenmu sun kama
matayenmu da yaranmu a matsayin bayi sun
kwashe dukkan dukiyoyinmu.
Ku sani cewa adadin wadannan dakarun abokan
gaba ya ninka namu sau goma, wato gaba
dayanmu bamu wuce kaso daya ba a cikin kaso
gomansu ba. Yanzu menene abinyi? Tabbas idan
muka ce zamu fita mu tari waddannan abokan
gaba za su iya murkushemu a cikin dakika kadan.
"
Sa'adda waziri yazo nan a jawabinsa sai Jaruma
Dabira ta mike tsaye zumbur! A fusace, kuma ta
zare takobinta a lokacin da jikinta ya kama
tsuma. Cikin fushi ta dubi waziri tace, "yakai
waziri kayi sani cewa bamu da wani karfi wanda
yawuce karfin allah katuna cewa bayau ne karo
na farko da muke fita yaki da abokan gaba da
kuma ya zamana sun fimu yawa, amma sai kaga
mun yi RAGAS dasu kokuma musami nasara
akansu. Duk bawan da yayarda da allah kuma ya
sallama al'amuransa a gareshi tabbas allah zai
iya masa abinda ya gagareshi. Ina tabbatar muku
da cewa koda abokan gaba yawansu ya kai cikin
duniyar nan gaba daya idan ni kadai ce na rage
musulma a wannan birni na rantse da girman
Allah sai na fita na yakesu dan kare martabar
addinin allah koda kuwa zasuyi gutsin-gutsin da
sassan jikina. Na sani nan dagobe wadannan
abokan gaba zasu iso kofar birninmu don haka
zan jagoranci dakarunmu mufita mu yakesu
wanda duk yake ganin zai bi bayana yabi, wanda
ba zai bi ba yayi zamansa!".
Koda dabira tazonan azancenta sai sarki Raihan
ya zare takobinsa yace, "Ina bayanki ya ke 'yata,
lallai dani za ayi wannan yaki gobe!".
Koda ganin haka sai fiye da rabin 'yan majalissar
ma suka yi abinda sarki raihan yayi. Kalilanne
daga cikinsu basu yi hakan ba, domin sun gama
tsorata da wannan yaki daza ayi, kuma imaninsu
ya raunata.
Wannan shine a binda ya faru a fadar sarki raihan
bayan 'yan majalisar kasar sun yi taro na
musamman.
Al'amarin yazila kuwa, lokacin da aka kaita kurkuku
aka kulleta sai taji ko kadan bata damu ba face kawai
tana zumudin yamma tayi a fito da ita a kaita filin
fada inda zasu yi yakin keji ita da jaruma Dabira.
Har rana ta take Yazila ta kasa tsaye ta kasa zaune a
cikin kurkukun. A lokacin ne aka kawo ma ta abincin
rana. Ko kallon abincin batayi ba bare ma taci.
Ai kuwa bayan an idar da sallar la'asar da kimanin
rabin sa'a sai aka bude kofar kurkukun aka tasa keyar
yazila izuwa fada. Tana tafe tana jan sarkar da aka
daure kafafunta da hannayenta, dakaru na biye da ita.
Lokacin da aka iso filin fadar da jaruma YAZILA sai
taga filin fadar ta cika makil da jama'a fiye da kullum,
harma mutane sun rasa inda zasu tsaitsaya sai akan
katangau.
A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wannan katon kejin
karfe mai tsawo da fadi wanda aka yi masa 'yar
karamar kofa ta shiga.
A can gefe daya kuwa, sarki RAIHAN ne da 'yan
majalisarsa a zaume kuma daf da shi JARUMA
DABIRA ce a tsaye cikin gagarumar shigar yaki
fuskarta a rufe cikin hular karfe kamar kullum.
Koda aka ga anzo da YAZILA sai aka yi sauri aka bude
kofar wannan keji. Cikin hanzari aka kwancewa yazila
sarkokin dake hannayenta da kafafunta aka bata
takobi sannan aka ingizata izuwa cikin kejin. Nan take
Jaruma Dabira ma ta baro inda su sarki suke ta nufi
inda kejin yake.
Koda ganin haka sai fadar ta rude da kabbara aka
rinka yiwa Dabira Jinjina har ta shiga cikin kejin aka
rufe kofar kejin.
A sannan ne aka yi tsit! A fadar gaba daya tamkar
mutuwa ta gifta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin
jaruma Dabira da Jaruma YAZILA.
Jaruma Dabira ta dubi yazila cikin murmushi tace,
"yau mun hadu a inda babu damar gudu, kuma babu
yankewar yaki face dayanmu ya sami nasara akan
daya.
Ina so ki sani cewa tuni na kona gaba dayan layoyinki
da gurayenki na tsafi yanzu dame kuma za kiyi
dogaro?".
Koda jin wannan tambaya sai Yazila ta bushe da
dariya tace, "ke yarinya, aikin kashe micijine baki sare
kansa ba. Kin ga wannan laya dake wuyana wani
malami ma'abocin addininku ne ya bani ita bayan an
bashi dukiya mai tsananin yawa. Kuma ya tabbatar
mini da cewa in dai ina tare da ita babu wani
mahaluki daya isa ya sami nasara akaina ".
Koda jin haka sai Dabira ta fusata ta zare takobinta ta
afkawa yazila suka ruguntsume da azababben BAKIN
ARTABU wanda ya dugunzuma hankalin kowa a
wajen, domin su biyun babu wanda ke da alamun
samun nasara akan abokin gwaminsa.
WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GAGARUMAR
HADUWA DA AKAI ?
SHIN DABIRA ZATA CIRE LAYAR WUYAN YAZILA
ITAKUMA TA CIRE HULAR KANTA?
IDAN SUN SAMI NA SARAR HAKAN ME ZAI FARU ?
YAUSHE ZA A KWABSA YAKI TSAKANIN RUNDUNAR
BIRNIN KISRA DA RUN DUNAR BIRNIN MISRA?
A WANNE HALI HUMAIRA MAHAIFIYAR DABIRA TAKE
CIKI?
SHIN DABIRA DA YAZILA SUNA GANO CEWA SU 'YAN
UWAN JUNANE ? IDAN SUN GANO ZASU JE DAUKAR
FANSA ABIRNIN KISRA AKAN SARKI DAKSUR?
Muhadu a littafi mai suna BAKIN ARTABU don jin
cigaban wannan kasaitaccen labari
Alham dulillah a yau na kawo karshen littafin jaruma
yazila 1-2-3 kamar yadda nagaya muku tun farko
shine a hannuna ban sami cigaban saba amma idan
na sami cigabansa zan kawo mukushi. Na ku
BASHEER ISHAQ TOKARAWA
BASH I TKRW
08105808371
JARUMA YAZILA
Littafi na Uku
Na Abdul'aziz sani madakin gini
Created and design by:- Shuraih Usman
Publishing shuraih 99%
From http://shuraih.wapsite.me
To download more Ebooks follow this link http://shuraih.wapsite.me

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

1 Comments On JARUMA YAZILA
avatar
gaskiya

12 months ago

Reply

Inajin dadinaa sosai

Please Login or Register in order to submit comment