Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sami na
sarar yaki a kan mutanen birnin kisra, kuma duk
saurayin daza ta aura sai ta tabbatar da cewa
yafita ilimin addinin muslunci.
Al'amarin daya matukar firgita samarin kenan
guiwowinsu sukayi sanyi domin sun san cewa
Dabira tasa sharadin abin da ba zai taba yiyuwa
ba domin a kasar gaba daya ana ganin cewa
babu mai irin iliminta. Hatta manyan malaman
kasar ma shakkar ta suke domin tun sa'adda
tana yarinya 'yar karama ta rinka kure su yayin
da a ke musabaka ta karatun Al'qur'ani da
fassararsa.
A bangaren ilimin taushidi da fighu kuwa' dabira
ta na zarci littattafai da dama. Wasu ma jama'a
da yawa basu taba nazarin suba saboda tsananin
yawon neman iliminta da bincikenta da kuma
baiwarta ta saurin daukar karatu. Duk abin da
aka biyawa dabira ko aka gaya mata ta haddace
shi kenan har abada tamkar a littafi aka rubuta
shi, komai tsaurin karatu da yawansa kuwa. Kai
da yawan mutanen kasar misra sun daina kiran
ta da dabira sai dai suce da ita "YAR BAIWA"
saboda al'amarinta ya wuce yadda kowa ke
tsammani.Lokacin da jaruma yazila ta hango kofar birnin kisra
daga can nesa, dabara ta fadomata na yadda zata
shiga cikin birnin bisa batar da kamanninta koda
wannan dabara tazo mata sai ta tsayar da dokinta ta
sauka, sannan ta daure dokin agindin wata bishiya.
Dama awannan lokaci rana ta kwalle gashi ta gaji
ainun kuma guzirinta ya kare har ta fara jin yunwa da
kishirwa. Ka wai sai yazila ta shimfida darduma a
karkashin wannan bishiya ta kishingida akai tana
tunanin yadda zata shiga cikin birnin misra. Tana
cikin wannan hali ne kawai sai ta hango an bude
kofar birnin, sai ga tawagar wadansu dakaru kimanin
su arba'in sun fito bisa dawakai a cikin shigar yaki
kuma sun durfafo inda take zaune.
Cikin hanzari jaruma yazila tayi girgiza, nan take ta
rikide ta zama tsohuwar mafarauci sanye da walki da
rigar fata, kuma. A rataye da kwari da baka. A kafarsa
yana sanye da ta kalmin fata. A kan dokinsa kuwa
tsuntsayene kala-kala kimanin guda bakwai duk
matattu alamar cewa harbosu yayi.
Nan take dardumar dake shimfide a kasa itama ta
rikide ta zama buzu. tsuhun yana ki shingida akan
buzun yana hutawa
A dai-dai wannan lokaci ne wannan lokaci ne wannan
tawaga tazo za ta gifta ta gaban mafarauci. Koda
ganin wannan mafarauci sai shugaban tawagar yaja
linzamin dokinsa ya tsaya a gabansa. Bawani bane
shugaban tawagar face jaruma dabira. Tana sanye da
kayan yaki, kuma tarufe fuskarta da hular karfe,
kofofin idanunta da hancinta da bakinta kadai ake
gani.
Jaruma dabirA ta dubi wannan tsohon mafarauci
sama da kasa tare da karemasa kallo cikin nutsuwa
sannan ta daka masa tsawa tace, "yakai wannan
tsohon mafarauci wanene kai, kuma daga ina ka fito
sannan menene ya kawoka nan kusa da kofar
birninmu?".
Da jin wannan tambaya sai tsoho yakama
makyarkyata cikin alamun tsoro yace, 'ki gafarceni
yake shugabata sunana kasim kuma ni bakon
mafaraucine na fitone daga kasar rum. Na shigo cikin
dazuzzukan dake kusa da iyakar kasarku ne da tamu
ina farauta sai guzurina da ruwan shana suka kare
shina na zonan na zauna ina hutawa idan rana tayi
sanyi na shiga kasarku na sayar da 'yan tsuntsayen
dana harbo na sami abin da zan sake yin guzurin na
koma kasata".
Koda jin wannan batu sai jaruma dabira tayi
murmushi saboda jin cewa tsohon daga kasar rum
yake domin birnin rum ma'abota addinin
musuluncine a wannan lokaci, kuma akwai alaka
tsakanin mutanen birnin Rum da mutanen birnin
Misra.
Dabira ta dubi tsuntsayen da tsohon ya harbo
wadanda ke kan dokinsa taji sha'awarsu domin babu
irinsu a cikin yankin dazuzzukan kasar misra don
haka sai ta dubi tsohon ta ce "yakai kasim nayi
sha'awar wadannan tsuntsaye naka saboda haka ni
zan siyesu nawa ne? Kuma inaso karamu izuwa dajin
daka harbo irin wadannan tsuntsaye domin nima na
farauto irinsu domin a halin yanzu farautar muka fito.
Zan biyaka da lada na musamman idan kayi mana
wannan rakiya "
Koda jin haka sai farin ciki ya lullube tsoho kasim yayi
godiya. Nan take jaruma Dabira tasa aka bawa tsoho
kasim abinci da ruwa sha ya cika cikinsa ya koshi,
sannan ya hau dokinsa ya wuce gaba yayi musu
jagora izuwa cikin daji.
A wannan lokaci zuciyar tsoho kasim daka take kamar
zata tsaga kirjinsa ta fado kasa domin bai san dajin
da zai kai su dabira ba su sami irin wadannan
tsuntsaye na sihiri da ya samar dasu.
MEZAI FARU TSAKANIN YAZILA DA DABIRA A CIKIN
WANNAN TAFIYA TA SHIGA DAJI DOMIN FARAUTA?
@SHIN JARUMA YAZILA ZATA CIKA BURINTA BISA
ABIN DA YA KAWOTA BIRNIN MISRA?
@YAUSHENE DABIRA ZATA GANE CEWA YAZILA 'YAR
UWARTACE TA JINI, KUMA IDAN TA GANE HAKAN
MAIZAI FARU ?
@SHIN IDAN HUMAIRA TA HADU DA YAZILA ZATA
SHAIDATA A MATSAYIN 'YAR CIKINTA KUWA ?
@YAUSHENE ZATA KOMA BIRNIN KISRA KUMA IDAN
TA KOMA MAI ZAI FARU?
Muhadu a JARUMA YAZILA littafi na uku don jin
cigaban wannan kaya taccen labari.
Daga ni BASHIR ISHAQ TOKARAWA
08105808371
.
JARUMA YAZILA
Littafi na biyu 2
Na Abdul'aziz sani madakin gini
Created and design by:- Shuraih Usman
Publishing shuraih Usman
From http://shuraih.waphall.com
.



JARUMA YAZILA
Littafi na Uku
Na Abdul'aziz sani madakin gini
Created and design by:- Shuraih Usman
Publishing shuraih 99%
From http://shuraih.wapsite.me
.
.
Lokacin da tsoho kasim yayiwa dabira da dakarunta
jagora izuwa cikin daji domin yin farautar irin
wadannan tsuntsaye da ya harbo sai ya ci gaba da
wucewa kan gaba zuciyar sa nata. Bugawa da karfi
domin baisan inda yakamata ya kaisuba har a sami
irin wadannan tsuntsaye.
Haka dai suka wanzu suna nausawa cikin daji har
tsawon sa'a daya da rabi bai tsaya a ko ina ba.
Al'amarin daya sa jaruma Dabira ta kosa kenan ta
dubi tsoho kasim ta daka masa tsawa tace "ya kai
wannan maharbi ina zaka kaimune haka, har yanzu
bamu isa dajimba ne?"
Koda jin wannan tambayar sai tsoho kasim yaji
kamar hantar cikinsa zata fito ta baki. Cikin karkarwar
bAki yace, "ya shugabata ai muna dab da shiga dajin
da tsuntsayen suke".
Koda gama fadin hakan sai ya sunkuyar da kansa kas
yana tunanin yadda zaibi ya sulale yagudu ya barsu a
dajin tun da asirinsa yana daf da tunuwa.
Hakika allah shine mai rufawa bawansa asiri, idan
kuwa ya tona masa, tofa koda duniya kaf zata taru
babu wanda ya isa ya rufamasa ba.
Kwatsam! Bazato ba tsammani sai ga irin wa dannan
tsuntsayen sak! Suna shawagi a saman su dabira.
Tsuntsayen sun kasance masu yawan gaske tamkar
shagalin biki suke, Koda ganin tsuntsayen sai dabira
da dakarunta suka tsaya cak a waje daya suka dana
kwari da baka suka dinga harbo tsuntsayen suna
fadowa kasa shima tsoho kasim sai ya faki ido ya
watsar da wadannan tsuntsaye guda bakwai na kan
dokinsa. Suna zubowa kasa sai suka bace bat cikin
hanzari ya harbo wasu guda bakwan ya dora akan
dokinsa. Dayake su dabira sun shagala da harbin
tsuntsayen basu lura da abinda tsoho kasim yayiba.
Bayan an sami nasarar harbo tsuntsayen da yawa sai
sauran tsuntsayen suka tsere. Nan take kowa ya debi
nashi tsuntsayen ya dora akan dokinsa cikin mutukar
farinciki jaruma Dabira ta dubi tsoho kasim tace,
"madallah da wannan tsoho mai bayani na gaskiya.
Yanzu sai mukoma da baya mukoma birnan mu
domin nacika maka alkawarina agareka kuma zanso
na baka masauki agidana da kaina domin kayi koda
kwana biyune rak a gidana kaga irin yanayin
rayuwarmu ta birnin misra".
Kodajin wannan batu sai tsoho kasim yayi godiya
yana mai nuna matukar farin ciki
Nan take jaruma Dabira ta kada linzamin dokinta
baya ta wuce kan gaba tana mai jerawa tare da tsoho
kasim suka bi hanyar komawa birnin misra sauran
tawagar na rufamusu baya
Haka dai akaci gaba da tafiyar inda hira karde
tsakanin Dabira da tsoho kasim inda taringa
tambayarsa tarihin rayuwarsa dakuma irin gwagwar
mayar da yasha a rayuwarsa a cikin daji bisa wannan
sana'a ta farauta.
Koda jin wannan tambaya sai tsoho yai tashara karya
kala-kala haryana ta bayani irin gumurzun da yayi da
manyan dabbobin daji yana samun nasarar kashesu.
Kodajin wadannan labarai sai mamaki yakama
jaruma dabira ta dubi tsoho kasim taga babu alamar
sadaukan taka atare tashi saita aiyana aranta cewa
duk yadda akai wannan tsoho da kuri yakeyi kawai
donhaka sai tace aranta, "Nikuwa in allah ya yarda sai
na kure wannan tsoho na gwada iyakar jarumtakarsa
na gani lokacin da yarage saura tafiya kadan a iso
kofar birnin misra sai jaruma Dabira ta sake nausawa
cikin wani dajin daban al'amarin da ya baiwa kowa
mamaki kenan daya daga cikin dakarun dabira
yadubeta yace "ranki yadade meyasa kika komar
damu cikin daji alhalin gashi farautar tayi kyau
munsamo abinda muka fito nema, koma kinsani
cewa wannan daji dakika shiga damu dajine mai
hadarin gaske wanda ke dauke da mugayen
dabbobi?"
Koda jin wannnan tambaya sai dabira tayi murmushi
ta dubi mai tambayar tace , tace """ai ganinayi mun
fito bamu sha wahalar komai ba mun sami tsun tsaye
ai yana da kyau mu dan motsa jini?".
Dajin haka sai hankalin sauran dakarun ya
dugunzuma domin sunsan halin dabira idan tace
tana son motsa jini dai-dai yake data ce tana son tayi
yaki.
Shikuwa tsoho kasim ko gezau baiyi ba sai kawai
yakara kaimi ya wuce kan gaba ma a cikin dajin.
Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan har ita
kanta dabira kuwa tce a ranta "yanzu shi wannan
bushashshen tsohon gani yake zai iya wani
abukenan ? To ai inda bakasa anan ake gardamar
kokawa. Zamuga iya kar koka rinsa
Abinda ya kara baiwa su dabira mamaki shine tsoho
kasim ya sakarwa dokinsa kaimi ya zabureshi da
gudu ba tare da shakkar komaiba
Kwatsam! Sai gasu sun iso tsakiyar wani babban fili
dazuwa sai suka ga wadansu manyan kuraye ayari
guda akan bishiya. Tsoho kasim ne yafara farga da
dabbobin don haka sai yaja linzamin dokinsa yayi
turjiya ya daga hannu yana mai yiwa su dabira nuni
da su tsaya.
Nan take kowa yaja tunga ya tsaya. Nan fa aka fara
kallon-kallo tsakanin kuraye da tsoho kasim
Kurayen sun kasance manya-manya masu matukar
kwarjini da ban tsoro sai gurnnani suke yi suna
wangame baki gami da dalalar da yawu kamar suci
babu. Kai dagani kasan cewa yunwa sukeji kamar suci
babu. Nanfa kuraye suka fara motsa jikinsu alamar
cewa akoyaushe zasu iya daka tsalle su fado kan
kasim
Tsoho kasim ne yafara zare takobinsa daga cikin
kube. Sannan sauran sauran dakarun dabira ma suka
zare tasu takobbinsu itakuwa dabira komotsi batayiba
daga kan dokinta sai murmushi take yi kawai tana
kallon kasim da dakarunta alamar cewa tayarda da
kanta su takeji.
Koda kuraye sukaga su tsoho kasim sun zare
takubbansu sai suka dako tsalle gaba dayansu alokaci
guda asama suka fado kanu aka rugun tsume da a
zababben yaki. Sai gashi kuraye sun jeho yaran
Dabira daga kan dawakansu su duka kuma suka
turmushe su suna kokarin cinyesu. In badamma
dakarun sun kasance zakakuran gaskeba da farad
daya kura yen zasu gama dasu. Nan fa akacigaba da
bakin artabu ya zamana cewa kuraye sunfara yiwa
dakarun Dabira rauni suna kartar jikinsu da faratan
hannayensu da kafafunsu kuma suna kai musu cizo
suna kaucewa da bugun bakunansu da takobi.
Al'amarin tsoho kaasim kuwa, abin al'ajabin
dayakeyine yasa Dabira takasa motsawa daga inda
take ta kaiwa dakarunta dauki kawai sai tabude baki
tana kallonsa cikin tsananin mamaki.
Tunda kurayen suka afkawa su tsoho sai yazama
kamar shaidani a tsakiyarsu ya dinga ra gargazarsu
da takofinsa yana kaftara musu sara yana tarwa tsasu
suna faduwa kasa, amma saboda naci da taurinkai
irin na kurayen saikaga suna dada tasowa suna
afkawa tsoho kasim duk da cewa jikinsa yai fata fata
da jini. Nan dai tsoho kasim shika dai ya zamewa
kuraye alakakai alokacin da suka gallabi sauran
dakarun Dabira.
Yayinda kuraye. Suka ga tsoho kasim yana yi musu
muguwar barna sai duk suka bar da karun dabira
suka yiwa tsoho kasim rubdugu gaba dayansu suka
lullubeshi. Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi sai
nan da nan kuraye suka fara ruda tsoho kasim
saboda suna kai masa muggan hare-hare ta kowane
bangare. Inbadan ma yana yana da tsananin zafin
namaba da tuni sun ya galgala shi. A nan cikin
wannan gumurzu ne wadansu kuraye guda uku masu
mugun naci suka shammaceshi suka karci jikinsa da
faratan hannayensu lokaci guda. Daya ta dankara
masa sara akirjinsa waje uku, wajen ya dare har jini
yai tsartuwa daya a gadon baya taimasa saran iri
daya dana kirjin nasa, dayar kuma a cinyarsa, saboda
tsananin zafi da zugin da tsoho kasim yajine ya kwala
ihu kuma ya fusata ainun kawai sai yadaka wawan
tsalle sama na bammamaki sannan ya sallamo kasa
kafafunsa na sama kansa na kasa. A haka ya dinga
gididdiga kurayen. Duk wadda yayiwa sara daya sai
kaga ya fille mata kai ta fadi kasa mutacciya nan fa
jinin kurayen ya dinga fantsama har yana. Bata jikin
Dabira. Kafin ta ankara jikinta gaba daya ya rine da
jini. Babbar jarumtar da tsoho kasim yayi shine
tunda ya fara sare kan kurayen a sama hannunsa ko
kafafunsa basu taba kasaba asaman yayi shawagi a
kan kurayen tamkar tamkar tsuntsu mai fuka fukai sai
da ya gama kashe kurayen gaba daya ya zamana
babu guda daya mai rai sannan ne ya duro bisa kasa.
A sannan ne dabira ta lura da wadansu tsofaffin
manyan raunika a jikin tsoho kasim wadanda tuni
sun warke abin da fara fadowa Dabira a rai shine ta
yaya wannan tsoho yake irin wannan jarumta irin ta
masu jini a jika wato matasa masu karancin
shekaru ? Nan take taji cewa lallai akwai a yar
tambaya akan tsohon.
Abu na biyu wadannan tabon data gani a jikinsa da
gani kasan gumurzu yayi da wani gagarumin
sadaukin da ya illatashi. Dabira ta kudurce a ranta
cewa lallai sai ta tambayi tsoho kasim yadda akayi
yasami wadannan raunika.
Bayan tsoho kasim ya gama kashe kurayen nan sai
yaji Dabira tayima tafi gami da jinjina nan take dabira
ta sakko daga kan dokinta ta taho izuwa inda tsoho
kasim yake. Sai da tazo daf dashi har suna jin numfa
shin juna sannan tatsaya cak tadube shi tace "ya kai
wannan gwarzon jarumi kasani cewa rabon da naga
jarumta irin taka tun sa'adda nayi gumurzun karshe
da babbar abokiyar gabata Jaruma Yazila ta birnin
kisra".
Koda jin wannan batu sai tsoho kasim yaji zuciyarsa
ta buga da karfi ya tsorata ainun domin ya zata
Dabira ta gano ko wanene shi. Kawai sai yaji dabira ta
kyalkyale da dariya sannan tace, "ka gafarceni yakai
wannan jarumin tsoho, ka sani ina sani nace a shigo
wannan dajin domin na gwada iyakar jarum takarka
bisa labarin daka bamu kan hanyarmu bisa irin
gwagwarmayar Da kayi. Tabbas yan zu na yarda kai
jarumine a bin kwatance. Amma duk da haka zan
sake yimaka wata jarrabawar ta karshe wadda ina
ganin asannanne zanga karshen jarumtakar taka.
Koda gama fadin han sai jaruma dabira ta bude
jakarta ta guzuri ta dauko wani magani ta mikawa
kasim tace, "ga wannan sai kasa a cikin raunin naka ".
Nan take kasim ya karbi maganin ya shafa a raunikan
da kurayen suka jimasa. A sannanne suma da karun
dabira suka yiwa kansu magani bayan kowa ya kimtsa
sai aka hau dawakai aka nufi hanyar birnin misra.
Humaira na zaune a cikin harabar gidanta tana
hutawa wadansu kuyangi hudu sun zagayeta suna
tayata hira kawai sai ta hango Dabira da tsoho kasim
sun taho gareta, wani bawa na rike da tsuntsayen da
suka farauto. Tun daga nesa da Humaira tayi arba da
idanun tsoho kasim sai taji zuciyarta tabuga da karfi.
Ba komaine ya haddasa hakan ba jface jida tayi a
jikinta cewar kamar ta taba ganin irin idanunnan
arayuwarta amma sai ta kasa tuno a inda ta taba
ganinsa.
Shima tsoho kasim tun daga nesa ya kurawa Humaira
idanu ko kiftawa bayayi. Koda suka iso daf kuwa sai
yaji idanunsa sunkico da kwalla suna neman su zubo
da hawaye. Babu shiri kasim ya sunkui da kansa kas.
Nan take Humaira taji kaunar tsoho kasim ta shiga
zuciyarta tamkar dama can tadade da sabo dashi.
Cikin fara'a Humaira ta dubi dabira tace "yake 'yata
wannan kuma wanene haka kika zo mini dashi?"
Kafin dabira ta budi baki tace wani abu sai tsoho
kasim ya zube kasa gaban humaira yace "Ni bakone
daga birnin rum yake wannan matar sarki. Na zo
gareku da salama kuma da yardar allah zan barku a
cikin salama da karamci ina fatan zaku karbi bakun
cina na kwanaki kadan cikin jin dadi?"
Koda jin haka sai Humaira ta sunkuya. Da sauri ta
kama kafadun tsohon kasim ta tashehi tsaye a lokacin
da ta sake kura masa idanu tace, "haba ya kai
wannan tsoho saboda me zaka durkusa min alhalin
ka haifeni a haife?"
Koda jin wannan tambaya sai idanun tsoho kasim
suka sake cikowa da kwalla ya dubi Humaira yace, "ai
duk inda 'ya mace take dole ne namiji ya girmamata
tun da kune kuka haifemu. Duk da cewa shekaruna
sunfi naki ina ganinki na tuno da ainahin mahaifiyata
wadda kaddara taa rabamu".
Dajin haka sai hankalin Humaira ya dugunzuma ta
kasa sakin kafadun tsoho kasim tace, "wacce kaddara
ce ta rabaka da mahaifiyarka?" Sa'adda kasim yaji
wannan tambaya sai hawaye ya zubo masa yace,
"makiyane suka rabamu tun ina jaririya har yau har
gobe bamu sake saduwaba. Babban abikin cikina
shine yanzu idan ma haifiyata na nan araye ko mun
sadu ba zamu shaida junaba tunda bata sanni ba
nima ban santaba".
Koda Jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
Humaira tace, "ya kai wannan tsoho kayi sani jininka
jininkane har abada. Ina tabbatar maka dacewa koda
mahaifiyarka bata shaida kaba indai kukayi arba da
juna saikun ji wani abu ajikinku, tabbas na tausaya
maka matuka bisa jin labarinka domin al'amarine
mai ban mamaki"".
Lokacin da HUmaira tazo nan a jawabinta sai Dabira
ta cika da tsananin mamaki domin a iya rayuwarta
tare da humaira bata taba ganin ta zubar da
hawayeba sai yau. Abin daya kara daure mata kai
shine Humaira ta sha jin labarai na abubuwan
tausayi wadanda ma suka fina tsoho kasim amma
bata yi kukaba. Menene dalilin daya sa Humaira tayi
kuka a yanzu bisa jin labarin tsoho kasim?"
Tambayar da Dabira takasa bawa kanta amsa kenan.
Nan dai dabira ta baiwa humaira labarin yadda ta
hadu da tsoho kasim da duk abubuwan da suka faru
a tsakanin su a daji. "
Koda jin haka sai humaira ta kamu da tsananin farin
ciki ta sake yiwa tsoho kasim barka da zuwa sannan
ta umarci wata kuyanga safina ta tafi da tsoho kasim
izuwa dakinsa kuma a kai masa ruwan dumi yayi
wanka gami da abinci.
Nan take kuyanga safina tatafi da tsoho kasim suka
nufi bangaren da ake saukar baki. Har suka kuLe
tsoho kasim bai daina waigowa ba yana kallon
Humaira tamkar baya son rabuwa da ita. Kai kace 'yar
uwarsa ce ta jini. Ita kanta Humaira sai taji bata son
tsoho kasim yayi nesa da ita amma sai ta rasa dalilin
hakan, mussamman a duk sa'adda ta dubi idanunsa
wadanda take ganin cewa basu dace da shiba domin
idanune irin na matasa masu karancin shekaru
dabasu kai ashirin ba shi kuwa gashi ya kasance
tsoho dan kimanin shekaru tamanin da doriya.
Bayan kulewar kuyanga safina da tsoho kasim sai
dabira ta dubi Humaira ta Baiyana mata sakon sarki
cewar yana son a dafa masa wannan tsuntsu kuma
zai zo da kansa bayan magariba yaci naman tsuntsun
a turakarta.
Koda jin wannan sako sai Humaira taji zuciyarta ta
buga da karfi kuma ta cika da tsananin mamaki
domin ita a zatonta sarki bazai taba zuwa kusa da ita
ba sai bayan cikar shekaru ashirin da zuwanta birnin
misra.
Cikin sanyin jiki da yake HUmaira ta dubi Dabira tace,
"shi kenan zan cika wannan umarni na abbanki"
Nan take Humaira ta juya ta nufi turakarta itama
dabira sai ta nufi tata turakar zuciyarta cike da tunani
da wasi-wasi. A bin da yafara fadomata a rai shine
wai shin menene ya kawo sauyin al'amura ne a yau
tsakanin mahaifiyarta Humaira da abbanta sarki
Raihan alhalin hakan bata taba faruwaba ? Anya kuwa
sauyin al'amarin ba shi da nasaba da zuwan wannan
bakon tsoho? Koma dai menene zan gani da idanuna
kuma zan yi aiki da shawarar abbana nasa ido sosai
akan wannan bakon tsoho don kada ya mamayemu
ya cutar damu duk da dai yace shi musulmine, ai dole
ne mu tabbatar da musuluncin nasa da kuma
amanarsa.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin jaruma Dabira
da iyayenta bayan ta tsinto tsoho kasim a can bayan
gari.
Al'amarin tsoho kasim kuwa lokacin da aka kaishi
masaukinsa aka shigar da. Shi cikin wani daki mai
kyau aka kai masa ruwan wanka kewaye kuma aka
kawo masa abinci sai ya mike tsam yaje ya rufe kofar
dakin yasa sakatu sannan yarufe duk tagogin dakin
gaba daya suma ya samusu sakatu. Bayan ya
tabbatar da cewa babu ta inda za a iya hangoshi daga
waje sai yayi girgiza nan take ya rikide ya dawo izuwa
ainahin siffarsa ta gaskiya, wato siffar JARUMA
YAZILA. Nan take yazila ta shiga kewaye ta cire tufafin
jikinta gaba daya sannan ta shiga cikin baho tayi
wanka. Bayan ta fito daga wankane taje gaban
madubi ta tsaya tana kallon fuskarta. Koda taga irin
kyawun da allah ya bata kuma ta tuna yadda ta
sauyawa kanta kamanni ta zama tsoho tukuf ta boye
ainahin kamanninta ga mahaifiyarta Humaira sai ta
fashe da kuka.
Dama tun sa'adda yazila ta taho izuwa birnin misra
tayi bincike a cikin tsafinta har ta gano cewa lallai
mahaifiyarta na nan a raye a cikin gidan sarauta
kuma.duk wadda tayi mata jagora izuwa wajenta
itace 'yar uwarta ta jini wadda aka haifesu tare. Bisa
haka ne yazila ta gane cewar lallai Humaira ce
mahaifiyarta kuma Dabira ce 'yar uwarta wadda take
dokin gani. Yanzu gashi tana son taga fuskar Dabira a
matsayin 'yar uwarta ba akan matsayin abokiyar
gabarta ba tana son dabira ta gane cewa ita 'yar
uwarta ce ta jini. Tayaya zata biya duk wa dannan
bukatu a cikin kwanciyar hankali?
Sa'adda yazila tazo nan a zancenta sai ta fashe da
kukan bakin ciki kuma hankalinta ya dugunzuma
ainun domin ta sancewa a koda yaushe a sirinta zai
iya tonuwa idan kuwa asirinta ya tonu kafin humaira
da dabira su gano cewa ita jininsuce tata takare wata
kila ma zata iya rasa rayuwarta a wannan lokaci.
Koda yazila ta aiyana haka a cikin zuciyata sai ta sake
fashewa da matsanancin kuka.
Bayan an yi sallar isha'i sai Humaira ta caba ado
sannan ta shirya kasai taccen abinci akan teburin
dake falonta wanda aka yi shi da farfesun irin wannan
tsuntsayen da su dabira suka farauto a daji.
Lokacin da Humaira ta gama wannan kintsi sai ta
sallami dukkan kuyanginta suka fice daga cikin
turakarta gaba daya sannan ta zauna tasa wannan
abinci agabanta tana kallonsa kawai a lokacin da
jikinta ya kama tsuma saboda mamaki da fargabar
zuwan sarki Raihan.
Tana cikin wannan hali ne taji anyi mata sallama. A
razane ta amsa sallamar ta dago kai tayi arba da sarki
Raihan a tsaye shima ya caba ado na kure a daka
fuskarsa Cike da annuri. Nan take kamshin turaren
jikinsa ya cika falon gaba daya.
Koda ganin sarki Raihan sai Humaira ta mike tsaye
zumbur a lokacin da jikinta yaci gaba tsuma, yayinda
sarki raihan yaga Humaira a cikin wannan hali sai
shima ya kasa bude baki yace wani abu har ya zo
kusa da ita ya tsaya.
Tsawon 'yan dakiku suna tsayen dayansu baice uffan
ba kuma kowannensu kansa na sunkuye suna kallon
kas, sai sarki Raihan yayi gyaran murya sannan yace,
"ya ke ummul Dabira shin na iya zama akan wannan
kujera?".
Koda jin wannan tambaya sai Humaira ta dago kai ta
dube shi cikin mamaki gami da murmushi tace, "ya
shugabana ai da wannan kijera da kuma wannan
dakin duk a karkashin ikonka suke. "
Koda jin haka sai sarki raihan yayi 'yar karamar
dariya sannan yace, "A'a ina shakka. Na yarda cewa
da wannan kujera da wannan daki a karkashin ikona
suke amma banda mai dakin. Ya ke Humaira ki tuna
cewa tun da kika zo garinnan tsawon shekaru goma
sha takwas ban taba umartarki da wani abuba sai
yau, kuma yau ne karo na biyu da muka taba kebewa
tare. Kin ga kuwa ashe ke ba a karkashina ikona kike
ba, kina dai karka shin alfarmata. Na san zaki yi
matukar mamaki bisa ganina ayau na kawo miki
ziyara har cikin turakarki, kuma bama keba hatta
gaba dayan hadiman gidannan suna mamaki don
gudun zargin wani abu shi yasa ban rufe kofar
wannan daki ba leka bayanki ki gani".
Cikin sauri humaira taleka bayan sarki sai ta hango
wadansu dakarunsa mutun biyu a tsaye suna hangen
duk abin dake faruwa tsakaninta da sarki amma
kuma basa iya jiyo abin da suke tattaunawa koda
ganin haka sai humaira tayi murmushi sannan tace. ”
Haba ya shugaba ai shi kansa shaidan ba a ko ina
yake samun nasara ba na yarda da imaninka da
tsoron allahnka don haka ina da yakinin cewa babu
wani mugun abu da zai shiga tsakaninmu face
alkhairi yanzu sai ka zauna kaci wannan abinci wanda
ka umarceni da na dafama maka ”. Koda jin haka sai
sarki raihan yayi murmushi yace. ” Na yarda zan
zauna naci abinci amma bisa sharadin cewa zaki cire
dukkan tsoron dake ranki ki daina tsuma haka”.
Da jin haka sai humaira tayi yar karamar dariya tace.
” Na amince amma ai bai kamata kaga laifina ba
domin kwarjininka ne da mamakin wannan ziyara
taka ta bazata su suka janyo mini lokaci guda duk su
biyun suka yi dariya sannan suka zauna a tare
zamansu ke da wuya sai sarki ya bude kwanukan
abincin dake gabansa kamshi ya doki hancinsa ya
shaki kamshi cikin farin ciki koda ya wanke hannunsa
acikin bakinsa ya yanko loma guda ta abinci ya sa
acikin bakinsa ya tauna ya tsaya cak ga barin cin
abinci ya kurawa kwanon abinci idanu kawai al
amarin da ya dugunzuma hankalin humaira ke nan
tayi zaton ko abincin ne bai yi dadi ba.
Dag cai saita ga hawaye ya zubowa sarki raihan cikin
kaduwa humaira ta dubi sarki kuma ta dubi baki da
kyar tace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi
kuskurekomai ba a cikin wannan girki ?” Koda jin
haka sai sarki raihan ya gyada kai sannan yasa daya
hannun nasa ya share hawayensa ya dubi humaira
yace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi
kuskure komai ba acikin wannan girki kuma tsananin
dadin girkin ne yasa na tuno da matata marigyiya da
kuma yar uwarta ina so ki sani cewa rabona da cin
abinci mai dadi irin wannan tun daga ranar dana rasa
wadannan masoya nawa saboda bakin ciki rabuwa
dasu. Ina so ki sani cewa nuni da cewa idan har ban
zo bana baiyana miki wata muhimmiyar magana dake
raina tsawon shekaru a yau bato har abada ba zan
sami damar hakanba.
Yake ummul dabira kiyi sani cewa tundaga ranar da
mutane suka zo dake tare da jaririyarki dabira naji
ina matukar kaunarki a zuciyata, amma sai naji bazan
iya furta miki ba saboda tausayinki bisa ganin halin
da kike ciki na bakin ciki rashin mijinki wanda aka
kashehi a

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

1 Comments On JARUMA YAZILA
avatar
gaskiya

12 months ago

Reply

Inajin dadinaa sosai

Please Login or Register in order to submit comment