Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabon fada ya
zamana cewa suna kaiwa junansu naushi da bugu da
hannu da kafa....
Page 7.
Zidane kd..
Kaico idan jarumtaka ta hadu da sadaukantaka dole ne
yan kalllo suga abubuwan al ajabi tamkar almara.
Sai da wadannan jaruman hudu suka sake shafe kimanin
daKiku dubu biyar da yaya suna yin wannan dauki ba
dadi batare d dayansu yasami nasarar cutar da abokin
gwaminsa ba.
Al amarin daya fusata su kenan duk su hudun suka kara
kaimi cikin fusata gami da sauya salon fada iri iri.
Hakan ya sa suka fara samun damar cutar da juna..
Nan danna suka fara hadawa da junan jini da majina.
Babban abin mamaki shi ne da zarar dayansu ya sami
nasarar naushin daya kafin yasake kaiwani hannun sai
kaga wanda aka nausa din ya rama..
Haka suka cigaba da gabzar juna cikin juriya da zafin
nama tamkar jikinsu na karfe ne ba na jini da tsoka bane.
Page 8.
Zidane kd.
A wannan lokacin ne hankalin gaba dayan yan kallo ya
dugunzu,a domin babu tabbaccen bangare dazai samu
nasara a wannan gasa sbd dukkaninsu sun fara jigata
ainun ga jini na yoyo a bakunansu da hancinsu kuma
fuskokinsu sun kumbura jikinsu yayi tsami amma sbda
naci kowannensu yaki yarda ya fadi kasa..
Har sai data kai cewa basa iya kai wajunan bugu da
naushi sai suka kaure da kokawa kowa na kokarin kayar
da abkn gwaminsa.
A dai dai wannan lokacine hankalin yan kallo yasake
dugunzuma fiye da ko yaushe har ta kai cewa mutane na
mikewa tsaye daga mazaunansu suna kasa zama sbda
kaguwa firgici da damuwa akan ganin gwanayensu ne
suka sami nasara.
Page 9.
BIRNIN AZZALUMAI 6.
LIttafe na shida.
Na abdul aziz.
Part B.
Type. Suleiman zidane kd.
Whatsapp.
09064179602:
Akan ganin gwanayensu ne suka sami nasara.
Abin da zai bai wa mutum mamaki shine da yawa daga
cikin mutanen garinma suna son suga Husam da Lasmir
Son su ga Husam da lasmir son sami nasara ba don
komai ba sai sbda jarumtakarsu tayi matukar burge su.
A birnin gaba daya babu jaruman da suka kai sarki
zarmus da yarsa Gimbiya Zarisha kuma duk shekara idan
aka yi wannan gasa sune suke lashewa duk dace wa bakin
jarumai suna zuwa daga kasashe makota.
Yau sai gashi an sami zakakuran jaruman da suke neman
karya musu alkadarin da tarihin da suka kafa tsawon
shekaru shida.
Ana cikin wannan haline na rashin tabbas ko kwanto da
fargaba a cikin gasar sai kawai aka ga dukkaninsu
jaruman hudu sun yi wata irin rukunkumar junan ta
bazato da shammace tare kuma a lokaci guda suka fadi
da baya ya zamana cewa duk su hudun bayansu ya taba
kasa.
Page 10.
Zidane kd.
Nan fa yan kallo gaba daya suka dafe kai cikin tsananin
mamaki sanan suka rufe da shewa gami da jinjina.
Ai kuwa sai alkalin gasa ya rugu da gudu ya shigo tsakiyar
filin ya tsaya ya fuskanci jama a ai kuwa sai aka yi tsit
tamkar mutuwa ta gifta.
A sannan ne zarisha ta taimakawa Husam suka mike da
kyar kamar yadda su zarisha sukayi alkalin gasa yayi
gyaran murya yace ya ku mutanen wannan birnin mai
albarka ku yi sani cewa sakamakon wannan gasa shine
ragas.
Jama a su rufe da shewa gami tafi da jinjina alkalin wasa
zai daga hannunsa sama asake yin tsit sannan yace
sakamakon wannan ragas da akayi tafiyar da su sarki
zasuyi izuwa birnin azzalumai babu wanda zai shugabanci
su face wannan bakon jarumi mai suna zaunal wanda
yazo tare da su Husam.
Page 11:
zidane kd.
Dajin haka sai jamaa suka sake rudewa da shewa shi
kuwa jarumi zaunal sai abin yayi matukar bashi mamaki
domin bai ga dalilin da zai sa a bashi shugabanci tafiyar
ba tun da babu shi a cikin gasar da akayi.
Bayan filin gasar yawatse kowa ya kama gabansa sai sarki
zarmus da Husam suka kadaita a cikin turkarsa inda ya
tura aka kirawo lkitoacinsa guda biyu suka shiga duba su
gami da yi musu magani bisa raununka da suka ji a
wannan gasa.
Page 12.
Zidane kd.
Kowannensu ya cire rigarsa ya zamana babu komai a
jikinsa face gajaren wando domin tabbatar da cewa an
duna ko ina a jikinsa.
Ana cikin duba ne Husam ya lura dacewa sarki ZARMUS
na cikin damuwa don haka sai yadubeshin akwai wani
abu ne wanda yabata maka rai a yau?.
Sarki zarmus ya gyara kai yace babu abin dayataba mini
rai amma a cikin firgici da razani bisa gagarumin aikin
dake gabanmu sbda shirin da makiyanmu suka yi akan
mu yawuce duukkanin zatonka da tunaninka.
Ko dajin wanna batu sai Husam ya mike zaune daga
kwance ya dakatae da likitan dake shafa masa wani
magani akan fuskarsa don bajewar kumburi ya dubi sar
zarmus cikin alamun mamaki yace wane irin shari sarki
baskae da boka zarmus suka yi akamu?
Page13
Sarki marzuk ya numfasYace yau saerki wata uku kenan
suna baiwa kansu sababbin horo na yaki kuma sun tanadi
sabbin kayan yaki wadanda ba a taba amfani da su a
wannan nahiyar ba.
Sun dauko sojojin haya kwararru na musamman daga
wasu kasashe dake can gaban nahiyarmu .
Bayan ga haka sun tanadi dukkanin sirrinkan su na tsafi
gami da gudumawar mayan bokayen daga wadansu
nahiyoyin .
Tabbas wannan shiri nasu akwai ban tsoro a cikinsa
wanda idan har kaga mun sami nasara a kansu sai
tsananin sa a da robo.
Lokacin da sarki marzuk yazo nan a jawabinsa sai Husam
yayi doguwar ajiyar zuciya yace yakai wannan sarki msi
irin burina kayi sani cewa raina da dukkan dukuyarya ba
a bakin komai muddin zan dauki fansa akan makiyana
baskar na raba shi da matata jaruma zamirat.
Babban burina shine na sake ganinta ko da sau daya ne
kafin mutuwata .
Page 14.
Burina na biyu shine na ciro tadaga cikin kurkukun da
baskar ya ajiye ta tsawon ya yanke mana farin cikinmu da
soyayyarmu.
Koda Husam yazo nan a zancesa sai sarki marzuk ya
kamu da tsananin tausayinsa har shi ma kwalla ta cika
masa idanu marzuk ya mikezaune kamar yadda husam
yayi kuma ya dafa kafadarsa yace yakai abokina kayi sani
cewa duk duniya babu mutumin da nakeso wacce muka
kasance uwa daya uba daya.
Page 15.
Ita ce kadai nake kalla ta dauke min kewar iyayyena da na
rasa.
A duk sa adda na kalle ta na ji tamkar bani da wata
bukata ko guda daya a cikin duniyar nan.
Ita ce wadda komai mutum yake nema a waje na da
zarar tasa baki take zan bashi ita ce kadai mai bani
umarni na bi kuma bata taba zuwa gareni da bukata na ki
ba.
A tsawon shekaru goma sha da boka zarmus ya rabani da
ita ban tabayin barci sa a uku ba koami tsawon dare sbda
begen ta da tunaninta kuma hakan ne ya haddasa mini
ciwo zuciya kuma ba zan taba warkewa ba face naga na
rabata da bola zarmus kuma na kashe shi da hannuna.
Tun lasmir tana yarinya kara yar shekara bakwai bola
zarmu ya kamu da tsananin sonta a sannan bai fi shekara
sha biyar ba a duniya amma ya ce bawa ne sai ya
bayyana soyayyarsa akanta domin yasan cewa idan ya
mabata kashe shi za a yi.
Bisa wannan daliline zarmus ya dukufa wajen neman
ilmin tsafi domin kawai ya sami damar da zai iya mallakar
lasmir.
Duk sa adda na aike su izuwa kasashe to shi baya yin
komai face ziyarta bokaye a sirrance yana yi musu
hidima kamar zai mutu.
A hakan ne ya sami sirrrikan tsafi d yawa har ya zuwa a
lokacin da ya shekara talatin da uku a duniya.
A wannan lokacin ne ya tara mayaka a sirrance dare daya
ya kawo harin summane izuwa garin nan domin yayi
mini juyin mulki.
Bai sami nasara yi mini juyin mulkin ba kuma mun fafata
kazamin yaki da shi har mana kusa halaka shi amma sai
yayi amfani da karfin tsafi ya sace yaruwata lasrin ya
gudu amma mutum daya daga cikin dakarunsa bai tsira
da rayuwarsa ba .
Babu irin neman da banyi wa boka zarmus da yaruwata
Lasrin ba a wannan nahiya ta mu da sauran nahiyoyi
amma ko duriyarsu ban sake ji ba tsawon shekaru bisa
wannan da
Lilin ne na tara bokaye suka shiga yi mini bincike na
tsawon kwanaki arba in.
.
A ranar kwana na arba in dinne suka zomini da magana
daya.
Maganar kuwa itace bazan taba samun damar karbo
yaruwata ba a wajen boka zarmus face idan wani bakon
sarrki daya rasa karagarsa yazo gareni irin matsalata a
hakan na cigaba bincike na gano cewa kai ne saekin da
zaizo gareni..
Page 18.
Zidane kd
..
Domin haka nayi ta zaman jiran zuwanka sai gashi kuwa
kazo a wannnan lokaci.
Tabbas ni ma yanzu na sallama raina dukiyata da mulkina
don ganin bayan wannan makiyin nawa don haka ba
gudu ba ja da baya.
Kasani cewa a halin yanzu na tanadin dakarun yaki guda
dubu dari..
Uku gami da bokaye dubu arba in wadanda zasu bamu
gudummawa a cikin wannan gagarumin yaki da za mu
tafi kuma nan da cikar kwanaki uku kacal za mu tafi.
Sa adda sarki marzuk yazo nan a lbarinsa sai farin ciki ya
turnuke Husam ya rungume shi suka kana zubar da
hawaye.
Kamar yadda hira ta kare tskanin sarki marzul da Husam
haka mata kasance tsakanin gimbiya zarisha da jaruma
lasmir a lokacin da wata likata ke duba lafiyarsu
sakamakon gumurzun da suka yi a wajen gasa.
Zarisha ce ta fara magana tace yake kawata idan har
kinaso mu samin nasara a yakin da zamu tafi can
birninku to dole ne ki cire kishi a zuciyarki a kai na
dangane da jarumi zaunal.
Page 19.
Zidane kd.
Ina mai shawatar ki da ki cire sonsa gaba daya daga cikin
zuciyarsa sbda ba akwai matar da xzai aura wadda baki
taba zatonta ba.
Ki sani cewa nima ina tsananin sonsa kome ya ke bukata
a wajena zan iya bashi koda kuwa bazai aure ni ba amma
na hkra dashi sbda bai dace dani ba..
Sa adda lasmir taji wanna batu sai hakalinta ya
dugunzuma ta dubi gimbiya zarisha cikin alamun
tsananin damuwa da rashin fahimta tace to wai shin
wacce wannan mace daza ta mallaeke shi anan gaba?
Zarisha tayi murmushi tace sanin hakan a gareki ba shii
da amfani.
Page 20.
Zidane kd.
Zai fi kyau ki sani a loakcin da ya dace gama fadin hakan
ke da wuya sai zarisha ta koma ta kwanta aka cigaba da
duba lapiyarta.
Kamar yadda sar marzuk ya fada haka abin ya kasance
wato sai bayan kwana iki sannan suka yi gagarumin shiri
tare da dakarun yaki da bokayen aka debi kayan yaki
masu yawan gaske gami da bayi da barri aka kama hanya
aka durfafi birnin azzlumai.
KUBIYO MU A LITTAFE NA GABA DON JIN YADDA ZA TA
KAYA....
Kash Saidai kuma naifito.
Amma inyato zamu cigaba..
Muhadu a littafe mai suna sadauki.
Naku har kullu Suleiman Zidane kd.
Whatsapp 09064179602

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment