Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita tabarshi shi kad'ai, kuma tana tsoron kar azo a ganta matsala ta sake faruwa wanda ita kuma bataso.


Haka tanaji tana gani tai waje tana waiwayen d'akin.




_Kauye_


Yau tun safe su maman Hanne suka shirya ita da Datti akan lalai yau ya kamata suje ganin muhalin Nafi saboda ai dama bai kamata suje daga farko ba.

Sun fito suka tarar da D'an Litti a inda sukai zai jirasu, Kowa ya kalli D'an litti sai ya kara saboda tsananin gayun dayasha, riga ce ta shadda mai dogon hannu yasa wando jeans ya tutura rigar a cikin wandan sannan ya kwama takalmi sau ciki ba safa, ya kawo hula irin tamu ta hausa ya saka, sannan ya kwama glass dinsa, gefen aljihun wandon kuwa ya ajiye wata zargab'ebiyar wuka.


Tsayawa yai ya wani karkace, su Datti suka karasa, maman Hanne na rike da gari yai zafi, wanda 'yan uwan Nafi suka harhad'a mata tarkace su fura ne, kayan mata ne, gayayyaki na magani, su daddawa ne, kub'ewa busassa da sauransu.



Datti ya kalli D'an litti yace " kai amma wannan yaron kana burgeni, ni kam dama kaine ka auri Nafi ba wannan ba. "

Dan Litti ya juyo cikin gayunsa yace "Haba Malam ni ai nafi karfin Nafi sannan ni abinda yasa nake san zuwa rakiyar nan ba komai bane ila I want me to see Ashaf. "

Datti ya juya kai tare da tab'e baki yace " mu tafi nikam ba turanci ne a gabana ba. "


Sun isa Gwaram suka samu wata bus anata lodi masu zuwa kano nan suka shige, Datti yai dariya yace " Ashe ma abin ba wuya."

Me ruwa ne ta leko tana asai ruwa, Dan Litti ya kobare cikin salonsa yace " ke me ruwa Me too want water one. "

Ta kalleshi tace " Dan boko banajin turanci. "

Maman Hanne tace "Kayi mata da hausa D'an litti kasan ba iyawa tai ba "

Yai murmushin kasaita yace " okay, bani ruwa d'aya. "

Nan ta bashi, Datti yace "lalai yaro muna zaune dan rashin d'a'a sai ka sai ruwa kai kad'ai ba tare da ka sanmana ba? "

Dan litti ya kara gyara zaman glass d'in sa yace "gatannan ka siya kaima."



Datti ganin inya siya sai ya saima maman Hanne hakan yasa ya gwara shima ya hakura.

Nan mota ta tashi suka fara tafiya..........




_Gida_

Kawu ne ya kalli Mumy wacce ke zaune cikin damuwa, yace "Hajiya lafiya kuwa? "

Kallansa tai cikin kulawa tace " Tunani nake yaushe ya kamata asa lawyer d'in mahaifin Ashraf ya kawo sakon wasiyyar nan? "

Kawu ya mike zaune tare da dafata yace "Hajiya karki damu da wannan, ai shima Yayan cewa yai abama wacce Ashraf ya fara aura, sai mu bari sai anyi auren kenan ko? "

Tai d'an dariya tace "I am really curious akan me ya ajiyema Matar Ashraf wanda ba wanda ya sani sai shi daya tafi. "

Kawu yai dariya yace "nikaina na k'osa naga menene wannan, da yace lalai matar Ashraf ta farko ya umarta abama. "

Nan suka shiga tattaunawa akan al'amarin wanda ba su kad'ai ba kowa ya kosa yaga menene wannan abun......


To nima daban taba ji ba sai yau na k'osa na gani sai dai ina ta tambayar kaina, Wacece matar Ashraf ta farko??????


*🗣🗣🗣🗣🗣🗣My Beely Badaru, duk Amarcin ne🙈?*


*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*Where are u my Cwt Nafeesa? Ur page is here!!! Hope banyi late ba? Happie Birthday dear wish u long life and prosperity.....*


1⃣8⃣


Duk yanda Nafi taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, ganin azahar tayi tai sallah dan yanzu ba laifi Little ta koya mata duk da suratul Iklas kawai ta iya ko hijab d'in datai sallah bata cire ba tai waje da sauri, knocking tai ganin ba'a bud'e ba yasa tasa makuli ta bud'e.

Ko kofar bata rufe ba ta shiga da sauri tana fatan Allah yasa ba wani abun bane ya sami Ashraf.

D'akinsa ta nufa kofar nanan a bud'e kai tsaye tai nufin shiga sai dai me? Aneesa ta gani zaune kusa da Ashraf ta rike plate a hannunta ta d'ebi Faten dankali tana kokarin kai bakinsa, da sauri ta matsa daga kofar ta tsaya a jikin bango, hannu.
Ashraf yasa da niyar amsar cokalin ta noke kafad'a tace " ni zan baka Hubby. "

Kallan mamaki ya mata, ta kashe mai ido cikin salo tace " daga yau na daina cema Yaya tunda bikinmu ya matso, Hubbyna zan dinga kiranka. "

Ashraf baice komai ba sai kula da hijab dayai a bakin kofa, Nafi wacce ke lab'e tad'an leko kad'an jin abinda Aneesa ta fad'a.


Idanunsu ne suka had'u juyawa tai da gudu tai waje, baice komai ba haka kuma bai mike ba sai murmushi dayai.

Aneesa ta d'auka cemai Hubby datai shiyasa yai murmushi, ta kalleshi cikin kauna tace "ahhh! "

Amsar cokalin yai, ta turo baku cikin shagwab'a tace "Hubby ya maganar sakon Abbanka? Sai yaushe za'a bani. "


Kallan mamaki ya mata yace "me? "

Ta d'an mai hararrar wasa tace " haba Hubby na kagu inga menene. "

Fuska Ashraf ya canza, cikin takaici ya kalleta yace " Get out."

Mikewa tai cikin mamaki tace "me kuma nai? "

Yace "what? Me kikai? Ina kwance ba lafiya amma ki rasa me zaki ce sai zancen wani abu? Fita nace. "

Idanu ta fara canzawa zatai alamun kuka, yace "wlh Anisa kika min kuka anan sai kinyi bala'in dana sani. "

Ta kalleshi cikin tsoro tace "Tayaya zaka iya abu kai kad'ai bayan kafad'ar ka a kumbure take? "

Ya juya kai yace "da sanda kika gani a mace kika ganni? Fita nace ko? "

Aneesa ta mike ta fita cikin takaici.

Tsaki yai sannan ya tuno sanda Nafi take hawaye sanda taganshi haka da sanda takesamai magani, tsaki yaja kawai.


Nafi kam tana fita d'aki ta koma ta rasa me yasa takejin zafin Ashraf, Hubby? A fili tace ko meye hakan oho....

Harta zauna ta mike tai kitchen.




_A Mota_

Tunda suka isa birnin kudu aka tsaya aka ajiye mutane sannan aka d'ebi wasu, kowa ya kalli D'an litti wanda ke sanye da wuka a katara sai ya matsa, sai kuma yasha jinin jikinsa, duk mutane sunyi tsit a mota duk tunaninsu d'aya wancan me zaiyi da wuka? "

Haka dai akai ta tafiyar kurma shikam yana nan kwame da glass d'iinsa baicewa komai, haushinshi ma su Datti da suka isheshi da zancen wai gaskiya sun gaji har yanzu ba'a iso ba? Wani gida ne kano haka?

Sun isa kachako anan kwandasta ya kalli kowa yace "a kawo kud'in mota."

D'an litti yace "nawa ne? "
"dari 700."
A zabure Datti yace "me? Dari 700?hauka kuke? Kunsan ma miye d'ari bakwai? "

Wani ne wanda ke gaban d'an Litti ya d'an mike yace "To wlh anmin sata. "

Gangarawa mai mota yai, parking yai sannan akace kowa ya fito, wanda akama sata yace wlh an d'auken kudina a dunkule.

D'an litti yaja tsaki yace "kudai kawai baku ajiye kudi ba yanda ya kamata zakuzo kuce am d'auke muku. "

Nan aka fara hayaniya kwandasta da kansa yake tambayan kowa ko ya d'auka har akazo kan d'an litti yace "Kai Tsakanin ka da Allah kaika d'auka? "

"I am the one. "abinda d'an litti ya fad'a kenan cikin gadara da takaici, shi harga Allah ya dauka i am the one yana nufin ba i am not ne.

Nan aka shiga zaginsa wasu na cewa dama su basu yadda dashi ba, hannu yasa ganin ana mai hayaniya da jiyar fito musu da aljihun sa akan su tabbatar ba komai a ciki, da sauri Driver ya rike hannun sa ta baya, yace " me kake shirin d'aukowa? "

Mamaki ya kama d'an litti zai magana sai ga 'yan sanda, nan suka fad'a musu, su kansu suna kallan yanda d'an litti yasa wuka zargab'ebiya a gefen riga suka tabbatar da lalai da alamar tambaya.

Cafkeshi sukai sukace sai sun kaishi office an charge shi, Datti a zabure yace "Aradun Allah baku isa ba rakamu gurin 'yata fa zai. "

Kallansa sukai sukace "sai dai ku koma in ya dawo ya rakaku amma wannan dole me ya bimu."

Dan litti sai kokawa yake akan a kyaleshi amma ina...ankwa aka garkama mai akai gaba dashi sai ihu yake yana cewa Wallahi Allah bani bane, Allah I am the one. "


Su Datti kam abin duniya ya damesu, maman Hanne tace "Yaya aikam dole mu koma ina mukasan zamu? "


Mai mota yace sai sun bashi dari 1000 su biyu, da kyar aka laluba datti aka samo dari 500 cikin takaici suka barsu agun sukai gaba.

Datti kam duk ya rikice, shida yakesan suje gun Nafi wannan yaran ya d'an bashi kudi dan yaga da alama akwai kudi a jikinsa.

Maman hanne ta kalleshi tace " Yaya wlh ba karamin kuskure kai...... "

Tsawa ya daka mata dama yana takaicin bai samu wani kudin ba ga nashi ya kare uta ficika ba a d'auka nata ba yace "ke ni gafara bani guri, banza kanwar mai satan saniya duk ba yayarki bace taja duk abinda ya faru? Zaki wani bud'en baki kice wai nayi kuskure? Nayi kuskuren 'yarki ce? "

Maman Hanne tace "Allah ya baka hakuri.... "
Nima nace Ameen

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

*I Sincerely Dedicated This Page To You Billy S. Fari and My Samrah.... ILYSM*

1⃣9⃣


Dakyar Ashraf ya iya watsa ruwa a jikinsa, wajen sa kaya kamar yai ihu, haka dai ya daurw yasa riga, makuli ya d'auka ya nufi hanyar waje da niyyar zuwa asibiti.

Yaje fita Umma ta kirashi hakan yasa ya karasa gunta, falo suka shiga bayan sun gaisa ya kalleta yace "Umma ya akai? "

Ta d'anyi murmushi tace"Dama tun jiya nakesan magana dakai. "

Kallanta yai kawai baice komai ba, ganin haka yasa tace " yanzu saura wata d'aya da sati biyu bikinku da Aneesa shiyasa nake tunanin kamar ya cancanta a bata sakon mahaifinka..... "

Wani kallo ya mata wanda ita kanta batasan ke yake nufi ba, sannan murmushi ne ya biyo bayan fuskarsa ya kalleta yace " Ashe har na bada sadaki an shaida kenan? "

Umma tace "mene? "
Yai wani murmushin rainin hankali yace "a iya sanina wanda ya bada wasiyyar nan cewa yai matata ta farko, banaji yace matar dana kusa aura. "

Ta kalleshi sannan ta motsa baki zatai magana, mik'ewa yai sannan yace " inada abinyi Umma sai anjima. "

Tabishi da kallo cikin maimaita kalamansa, asanda yai maganar sam kwakwalwarta kullewa tai amma yanzu kam datake maimaita kalaman ta fahimci banda tsananin rainin hankali ba abinda Ashraf ya fad'a mata.

Shikam cikin tsananin b'acin rai ya shiga mota, yayi tunanin zai iya tuki sai dai jin zafin da kafad'arsa take yasa ya na driver d'in mumy magana, ba'a dad'e ba ya karaso nan ya jashi suka fita.

Kansa ya kwantar akan kujera ya lumshe idanunsa, menene dalilin dayasa mutane suka damu da abinda mahaifinsa ya bari? _Fatiha an d'aura auren Ashraf da Nafisa yar gidan Datti_

Abinda ya fad'o mai a rai kenan, kallan driver yai yace " Adamu kaini wajen malam Yunus "

To abinda driver d'in ya fad'a kenan tare da murd'a kan sitiyari, sunyi tafiya sosai kafin su isa wata katuwar makarantar islamiya, nan yai parkin Ashraf ya fita, wani babban office ya nufa ya kwankwasa, daga ciki aka ce shigo, Ashraf ya murd'a kofa ya shiga.

Malamin na ganinsa ya mike cikin tsananin farinciki ya karaso kusa da Ashraf tare da mikamai hannu alamar musabaha, shi kanshi Ashraf d'in ya saki fuskarsa sosai, nan shima ya mikamai suka gaisa cikin girmamawa.

Nan ya nunama Ashraf guri ya zauna, sunyi gaisuwa tare da tambayan juna bayan rabuwa, dattijon Malami ya kara washe baki yace "Muhammad sam ka daina ziyartata. "

Ashraf yai murmushi yace " wlh malam uzuri ne ke hanani zuwa. "

Sunjima suna gaishe gaishen su kafin Ashraf yai gyaran murya yace "Malam ina cikin wata 'yar matsala ne wacce duk duniya ba wanda na sanar ma kuma ba wanda zan sanarwa sai kai. "

Malam yunus ya kalleshi cikin tsananin kulawa, yace" Inajinka."

Ashraf yai shiru, yana tunani.
Malam yace "Muhammad karka b'oyemin komai. "

Ashraf yai kasa da kai nan ya zayyane mai kaf abinda ya faru sannan ya d'oramai da wasiyyar mahaifinsa.

Malam Yunus hankalinsa ya tashi dajin wannan al'amari ya kalli Ashraf yace" Tausayi da Taimako ne yasa ka aureta sai dai Muhammad inasan tunasar dakai aure ko a wasa akayishi indai har anyi auran yanda musulunci yace to fa tabbas wannan auran ya d'auru sannan hakkin matarka na wuyanka. "

Kallan Malam yai cikin tsananin damuwa yace " da ina tunanin saki..... "

Da sauri Malam yace " kul Muhammad akan me? Ba taimako kakesan yi ba? Meye amfani taimakon kenan? "

Ashraf jiki a sanyaye ya kalli Malam yace " me zanyi da ita? A kauye fa take ko ince a riga, yarinyar da banaji sallah cikake ta iya, batasan komai na rayuwa ba, infact shekarunta ma inaji basufi 16 ba Malam me..... "

Malam yai murmushi yace " naji duk bata iya komai ba, kamin alkawari d'aya nikuma zan taimaka ma. "

Ashraf yace "Name kenan? "

Malam Yunus yai murmushi yace " Inaso kasa ta a makaranta inma taa kwana ko ta jeka ka dawo ka kula dacinta da shanta da suturarta har ta kai shekara 20 zuwa da d'aya, inhar aka kai lokacin Bakaji komai a tattare da ita ba inaso ka bata takardarta ita kuma sai ta nemi wani ta aura. "

Cikin rashin damuwa Ashraf yace "nama wannan alkawari. "

Malam yai murmushi sannan yace " game da wasiyar mahaifinka kuma kasan yanda zakai a rabu lafiya dan kuwa wannan wasiya ta matar daka aurace ba wacce zaka aura ba. "

Shiru Ashraf yai yana tunanin lalai akwai chakwakiya inhar yace bazai ba Aneesa wannan wasiyar ba, Malam yaji yace " zaka iya jinkirtawa zuwa sanda ka rabu da matarka."

Ashraf yai shiru, sai dai yasan wannan shawarar itace daidai,sunyi Sallama Ashraf ya ajiye mai kud'in talafi na makaranta sannan ya tafi.

Mota ya koma nan sukai hanyar Asibiti.





*Dan Allah kuyi Hakuri da wannan wallahi rasuwa aka mana shekaran jiya.*
Nagode!


*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

*_Hakika bani da bakin da zan muku godiya, nagode kwarai da so da kaunar da kuka nunamin, ina kara godiya ga masu min ta'aziya ta waya, ta text, da ta chat nagode kwarai Allah ubangiji ya barmu tare......_*




2⃣0⃣


Shiru Ashraf yai a mota bayan sun fito daga Asibiti, tunani yake mai zurfi ina zai sa Nafi a makaranta? A kalaa dai shekarunsu d'aya da Little banbancinsu dai Little nada d'an jiki sai dai Nafi siririyace sosai sai tsayi, ko alphabet bata iya ba.

Ya d'an juya kai, ina zai sata? Yarinyar nan dai bamai ansarta ko Js1 ne to a hakan ma Js1 ya mata kankanta saboda ita ba yarinya bace, yai d'an karamin tsaki lalai Malam dama wahala ya d'auramai.

Sam baiji sanda Driver yake ta cemai Oga ina zamu?
Can bayan ya gama tunani ya kalli Adamu yace "Adamu me muke jira kuma? "

Adamu ya dan saki fuska yace " tun d'azu nake tambayar inda zamu banji kace komai ba. "
Tsaki ya kara ja sannan yace "Mu tafi gida, tunani ne suka min yawa. "


A gida kam kan kace me kowa yasan abinda Ashraf yama Aneesa akan wasiyyar da za'a bata, duk ta yad'ashi tana fadama mutane tana kukan sakalci, anyi carko carko a waje kowa nata fada'an albarkacin bakinsa, sai dai kaf Ashraf suke bama laifi gani suke ai ta cancanci abata ta gani, dan ankusa d'aura musu aure.

Mumy kam tana d'aki abin duniya ya dameta itakam ba abinda ta tsana irin taji ance Ashraf yayi abu.

Tun da suka shigo Ashraf ya fuskanci da matsala sai dai har sukai parking ya fito bai nuna komai ba, ba kuma yasan ya san meke faruwa, direct hanyar banharensa ya nufa, suna daga tsaye ko kallan inda suke baiyi ba, Ga Aneesa da su Umma suma daga d'an gefe.

Asim ne cikin kuluwa yace " Ashraf bakaga dan kai muke tsaye ba? "

Kallansu yai ya saki wani mugun smiling na rainin hankali yace " Da alama tsayuwar domin ni tana muku dadi ne. "
Ya ci gaba da tafiyarsa, a xabure Asim da kannansa suka matso inda Ashraf yake, Asim ya tafi a zuciye zai shake Ashraf, saura kiris ya karaso Ashraf yace " D'an daba muka samu a gidan? Ka tabbatar kasan me kake shirin yi kafin a samu matsala. "

Jin haka yasa kannensa sukai saurin tare Asim d'in shikam sai hucci yake, ya nuna Ashraf yace " Dan kut........ Kai har ka isa kasa kanwata kuka?"

Kallan inda su Umma suke yai sai a lokacin ma ya kula da su, cikin zuciyarshi kwarai takaici ya lulube shi sai dai murmushi ya sake saki yace " Kanwarka? Sai kai azama ka bata hakuri sannan kai gaggawar yi mata kashedi akan zubar da hawaye akan wani bare. "

Ran Asim ne ya kara dugunzuma, yanzu kam har kannansa abin ya kular dasu, Aneesa ta matso, Ashraf ya d'an buga mata wani kallo sannan ya kalli Asim fuskarsa a sake sosai kamar ba'amai komai ba yace " Ya? Gatannan sai ka tambayeta me baren nan ya mata. "

Asim ya kalli Ashraf cikin masifa yace " kai dan rashin mutunci baza ka bata wasiyyar mahaifinka ba? Ko dan tsabar mugunta rikewa zakai? Oh andaiji jiki uba ya mutu ya bar wasiyya amma d'a ya kasa......"


Kasa karasawa yai saboda ganin Ashraf yana murmushi harr hakoransa suka fito, cikin tsananin takaici ya kalli Ashraf yace " kut! Dariya ma na baka? "

Ashraf ya juya kai tare da shafar kasan kansa da hannun da baya mai ciwo yace " Uba? Sai kuma ka manta wannan Uban nawa ne ko? Sannan banaji a wasiyyarsa yace inba matar da ban aura ba ko? "

Aneesa ta matso kusa dashi tace " Yaya?"

Matsawa yai daga kusa da ita baice musu komai ba ya juya ya fara tafiya, sai dai abin mamaki kasa cemai komai sukai sai Aneesa data bishi da sauri, tana kiranshi.

Ko Kallanta baiyi ba, ransu Umma ya sake b'aci, yana shiga falonsa ta bishi itama tace "Hubby? "

Matsowa ya farayi inda take harta isa jikin bango yasa hannunsa ya matseta har sai datai dan kara, sannan yace " wlh ki shiga hankalinki, inkikai wasa Wlh kinji na rantse duk sanda nake miki sai in ajiye maganar auranki, kinfi kowa sannin ni Ashraf nafi karfin mace ta wulakantani ko ta juyani. " saketa yai sannan yai d'akinsa.

Da kallo ta bishi dashi, wani mugun tsoro ne ya shigeta,A tsorace tai waje.

Ashraf kam yana shiga d'aki ya durkushe agun, kafad'arsa har kasan hannunsa banda azabar zafi ba abinda yake ji, d'ayan hannun yasa da niyyar sa magani, sai dai ina jin gun yai ya kara kumbura, ya tuna abinda likita yace mai.

"Ashraf a ina ka bugu haka? "
Da mamaki yace" ni ban bugu ba kawai da daddare ciwo ya tashi min."

Likitan yai shiru can yace " A 'yan kwanakin nan baka bugu ba? "

Ashraf ya kalleshi yace " na dai d'an sanu karamin accident to daga nan ina d'anjin gun ba dadi to amma bawai ciwi ya kemin ba. "

Likitan yai d'an ajiyar zuciya yace " Ashraf ya akai haka? Me yasa bakazo checkup ba bayan abin? "

Ganin bashida niyyar magana yasa ya mik'e ya bashi magunguna, sannan yace " a sa tsuma a ruwan zafi a dinga matsewa ana gasa ma gun, sai a shafa wannan. "

Asharf ya amsa, yacigaba "wannan kuma na had'iya ne. "

Nan ya bashi kud'inshi Ashraf ya mike, har ya fara tafiya likitan yace " Ashraf ka tabbatar an gasa ma sannan karkai amfani da jikinka sosai. "

Nan yai gaba, ta ina zai iya gasa gun da kansa? Gashi sunyi fada da waccan yarinyar, shikuma kaf mazan gidan bayaji akwai wanda zai iya kira.

Wayarsa ya d'aga ya dannan number Little yana fatan Allah yasa ta dawo.
Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga, bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. "

Abinda ya fada kenan ya kashe, little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai dai ita batasan meke damunta ba, ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo.

Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. "

Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " taya zan tafi in barki? "

Little tace " naji muryar yayan ma kamar......"

Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu, tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda kawai tasa a ranta kenan.

Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike, dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi, Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne?

Nafi kam jikinta ya fara tsuma ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. "

Asim ya d'ago da niyyar masifa, sai dai me? Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita.



1 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

Please Login or Register in order to submit comment