Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mishi murya shi kuma sai zirga-zirga
yake yi yana kaiwa da kawowa don ya gane abinda take nufi.
Amiru ya ja tsaki kafin ya saki wani lallausan
murmushi ya ce, ban ga komai ba Alhaji kai ne kaga
hakan ni dai na san a halin da Maryam take ciki a yanzu
in ma kaga tayi wani abu makamancin hakan to sai dai
tayi don ya zama dabi'arta amma ba don ta burge wani
ba don haka kayi hakuri ka rage sa mata ido ku fuskanci
juna kai dai ta don ku f jin dadin mu'amala a
tsakaninku.
Kai kam ai dama baka son laifinta ban taba kawo
maka zancenta kan abinda take yi min ka goyi bayana ba
sai ka ce wai sa ido nane ya yi yawa.
Bai sake tanka mishi ba sai ya juyo gareni, ke rabu da
shi kin ji Maryam daina kuka ki share hawayenki kin ji?
Ni zan tafi. Nayi naza ma share hawayen nawa kamar
50


yanda ya bani umarni na kuma yi mishi godiya, Mubarak
yabi bayanshi nayi maza na koma wurin babana. ai n
sBa a wani dade da yin hakan ba sai na hango shi
yana dawowa alamar rakyar ba mai yawa ya yi mishi ba
don haka na yi maza na sake fitowa daga dakin na tare
shi a dan dogon falon da kofofin dakunan ke ciki a
hankali cikin natuswa ta yanda babu mai jin abinda nake
fada na ce mishi, ko zaka daina zuwa ne don kar mu zo
muna batawa juna rai? A yanayin da nayi mishi maganar
a irin shi ya bani amsa, ranki ya zo yana baci dai amma
ni me zai 6ata min rai? Aiina ganin so mi somin hakan
na daga wurinki zan yi maza in yi maganin abin don
gaba daya zan hanalki zuwa asibitin kamar yanda kika
hana matan gidanku zuwa. Gabana ya yi mummunan
faduwa na yi amza na daga ido don in kalleshi saboda
mamakin maganar tashi in ga irin karfin halin da ke
gareshi da zai yi min irin wannan hukuncin alhalin ni da
mahaifina ne, wani irin lalataccen kallo naga yana yi
min, kina nufin kinfi kowa kusa da shi ne ko kinfi kowa
sonshi ne? Ki yarda in ga wani abinda bai yi min ba ki
gani? In gani in zan hanaki zuwan ki zo ki ga wulakancin
da zan yi miki baki iya rashin kunya ba? Kar ki dauka
kuma wai kishinki nake yi kamar yanda Amiru yake fada
ko daya.
Rasa abinda zance mishi nayi na soma yi mishi kuka
saboda sanin da nayi cewar zai iya aikata abinda ya ce din.
Sakarya kawai sokuwa wacce ko ciwon kanta bata
sani ba sai rashin kunyar tsiya.
51

Ya wuceni zai tafi nayi maza na ce mishi, to bana son
aikin da kake son sawa a yi msihi. Maimakon ya ce min
to kamar yanda nayi zaton ji daga gareshi sai naji ya ce
min to ai bake ke da shi ba yana kuma da bakinshi dona
cikin hankalinshi yake. Ya wuceni ya shiga ciki na share
hawayena nabi bayanshi a kan kujerar da nake zama na
sameshi yana tashe da babana da ke kwance yana fama
da kanshi.
Sannu baba ya soma yi mishi gaisuwar cikin natsuwa
da yardar Ubangiji zaka samu saukin wahalar numfashin
nan nan ba da dadewa ba tunda likitoci sun gano kan
al'amarin sun kuma yi bayani da cewar dan karamin abu
ne ya sameka don haka za su yi aiki su gyarashi in aka
gano kan ciwo baba to ai shi kenan magana ta kare sai
kawai a yi addu'a Ubangiji yasa a dace da abinda za a yi
don haka nake so in rokeka ka yi hakuri ka kuma
kwantar da hankalinka kar ka ce zaka sanyawa ranka
wani damuwa don kar jininka ya zo ya hau aikin da za a
yin ba wani mai wahala bane. Ya zubawa babana ido tare
da saurarona binda zai ce, yayin da nima na yi hakan tare
da fatan in ji ya ce baya son aikin tunda mu kam ni da
yaya Dija ba ma so gashi kuma ba shawara da mu ya yi
ba kafin ya zartar da hukuncin sai kawai na ji babana ya
ce mishi na gode Ubangiji ya yi maka albarka. Ya ce
amin, ya mike ya fita ba tare da ya nuna alamar ya san da
tsayuwata a wurin ba.
Wulakanci irin na Mubarak yawa ne da shi ga
dukkan alamu kuma watakila shima ya san shi din gwani
ne tunda shi da kanshi ma yana barazanar zai yi shi don
haka sai nà kudurawa raina in ma za a yiwa babana aikin
52

to ba shi ne zai dauki nauyin abinda za a kashe ba kamar
yanda na lura yake nufin yi yan kadarorina zan sayar da
na samu na tara da kudin da nake samu a sana'ata ta
dinki zan sayar in baiwa yaya Dija kudin ta hada da
abinda ke hannunta ta mikawa mijinta ya hada tunda
naga alamar aikin zai ci kudi masu yawa.
Yaya Dija ta iso na bata labarin duka binda ake ciki
da wanda ya faru tsakanina da Mubarak, fada ta rufeni da
shi a kan wai ai ni nake jawoshi ta hanyar sakar mishi
fuskar da nakeyi mishi amma in ba haka ina ruwanshi da
mu da har zaizo yana yi mana irin wannan shisshigin?
Aje ya ji da harkokinshi ya barmu mu ma mu yi namu
sannan ta riga ta gaya min bata son aikin ba za a yi ba
ban ce mata komai ba har ta yi ta gama har ma ta tafi
iyaka dai kawai addu'a nake yi da kara gayawa Ubangiji
halin da mahaifina yake ciki wanda kuma nasan ya fini
sani.
Ana idar da sallar magariba sai ga Amir ya sake
zuwa dubamu na ji, dadin ganinshi saboda ganin shi
kadai ne ya zo ya duba babana ya juya zai fita nayi
amfani da baccin da ya tarar baban nawa yana yi na
biyoshi waje muka tsaya a dan tsaye a wajen da muka
tsaya da Mubarak.
Cikin natsuwa na soma yi mishi magana wanda roko
ne na ya taimakeni ya gayawa Mubarak cewar ya fita
hanyar jinyar da babana yakeyi ya daina zuwa asibitin
bana kuma son duk wani taimako nashi.
Wani dan siririn murmushi ya yi mai hade da ajiyar
ciya a hankali cikin natsuwa ya tambayeni, wai ni in
sani mana me Alhaji Ahmad yake yi miki ne? Ni dai
53

basan tunkina yar kankanuwarki yake tare da ke tun
baki isa komai ba tun baki ma san ke wacece ba, amma
har zuwa yau din nan bai samu matsayin da ya dace
dashi ba a wurinki.
Nayi maza na kalli Amiru cikin ntusuwa saboda jin
kalaman nashi kan in san abinda zan budi baki in gaya
mishi sai naji ya ci gaba da cewa, saboda kawai kin san
yana sonki saboda kin gane ba zai iya fita harkar ki baa
duk motsin da za ki yi idonshi yana kanki iyayenshi sun
bashi aure amma kin hanashi natsuwa da zai zauna lafiya
da iyalinshi lafiya ya iya jaruntaka kan komai amman in
akan ki ne sokancinshi yawa ne da shi, ni da kaina na sha
bashi shawara kamar yanda nasha yi mishi gori a kan ki
wai dan ya yi zuciya ya kawar da kai daga gareki amma
ya kasa ya yi aike gidanku ace an hanashi yafi a kirga
kullum kuma ya zo kusa da ke sai kin san abinda kika yi
kika 6ata mishi rai amma yana biye ba zan ce mishi ya
fita harkarku ya daina zuwa ba don ko na gaya mishi ba
ji zaiyi ba don haka in ya zo ke da kanki ki kara gaya
mishi in ya ji shi kenan in kuma bai ji ba sai ya yi tayi na
dai san har da alhakin abubuwan da yake yiwa matarshi
uwar 'ya'yanshid a take matukar sonshi cikin wadannana
bubuwan da kike yi mishi. Ya wuceni ya yi tafiyarhi ba
tare da ya tsaya ko da don yi min sallama ne ba.
Na koma dakin da babana yake kwance na jawo
kujerar robar da na saba zama a kanta cikin natsuwa na
zauna zuciyata cike da tunanin kalaman da Amiru ya yi
min nice mai yawan batawa Mubarak ko shi ne mai
yawan bata min a sanina kullum a cikin kaffa-kaffa da
shi nake matukar yana wuri bana sakewa in yi abinda na
54

ke so kai ko baya nan bana iya saba dokarshi saboda
tsoro ko gudun bacin ranshi da nake yi amma a hakan
bana tsira sai ya san abinda ya ce na yi wanda ya yi min
wani abinda zan raina kaina ko in zubar da hawaye a
dalilinshi amma ka ji irin kalaman da baokinshi yakeyi
min to babu laifi.
Har dare har washegari Mubarak bai dawo ba
maimakon in sake in ji dadin rashin ganin nashi sai na
zama ko iya amsa gaisuwar likitan nan bana yi saboda
tsoron kar mu na cikin gaisawar ya shigo ya ganmu ya ce
ba a yanayin da nake amsa gaisuwar sauran mutane nake
amsa mishi ba.
Wunin ranar nan har dare bai shigo ba sai wajen
karfe goman dare a lokacin nan kuwa babana yana cikin
wani hali da ya yi dalilin da sai da naje na kirawo likitoi
saboda kei kawo mai tsananin da numfashin nashi kc y1,
a-hankali ya turo kofar ya shigo bai nufi wajensu don
gani ko jin abinda ke faruwa ba wurina ya zo ya tsaya bai
yi wata magana ba har sukayi abinda za su yi suka gama
suka tafi, da sauri muka isa inda baban yaku wance don
ganin halin da yake ciki gaba daya ya jike da gumi cikin
Zuciyata na ce ya wahala, hawaye suka sake zuba daga
idanuwa na sharr, bance mishi komai ba haka nan shima
Mubarak din ya juya ya fita ya barmu a dakin, na kai
guiwowina kasa na durkusa yayin da na kwantar da
kama a gefen gadon nashi hawaye suna ta zubo min,
jimawa kadan na sake dagowa na kalleshi saboda
yanayin numfashin nashi da naji ya sauya bacci ne ya
daukeshi na dan ji dadi kadan saboda tunanin yanayin da
zai sake farkawa a ciki.
55

A hankali naji an turo kofar an shigo na waiwaya don
ganin wanda ya shigo Mubarak na gani cikin zuciyata na
ce, ashe ba tafiya yayi ba, to dawo daga nan mana tunda
ya samu ya runtsa. Ban yi musu ba na koma daga nan din
da yace na zauna, a hankali ya mikomin ledar da ya
shigo da ita, bude ki cinye abinda ke ciki ba hilkima bane
don kana jinyar mara lafiya ka yi ta zama da yunwa in ka
yanke jiki ka fadi sai jinyar ta zama ta mutum biyu
maimakon da ana yin na mutum daya.
Na sa hannu na karba ina ci shi kuma yana yi min
nasiha shi mutum hakuri yakeyi ya koyi jaruntalka idan
al'amari irin wannan ya sameshi ba ya yi ta kuka yena
kin cin abinci ba kinga irinr amar da kikayi kuwa? Na
maida ledar na ajiye saboda koshin da nayi na bude robar
ruwa ina sha, sai da yaga itama na maida ita na ajiye
sannan ya tambayeni, amma yanzu ai kin gane ya zama
dole mu tsaya wajen ganin an yiwa baba aikin nan ko?
Na yi maza na daga ido na kalleshi saboda jin dolen da
ya ambata sai naji ya ce min, to zai yiwu ne mu barshi a
cikin wannan halin? Kin ga haka zai yíwu? Sannan ba
zai yiwu a cireshi daga nan a kaishi wani wuri ba domin
nan teaching hospital ne. Kalamai da mabayani masu
yawa yayi min a natse har dai na bude baki na ce mishi,
to ai yaya Dija ma ba ta son aikin.
A hankali ya ce min to ai baban naki ne Maryam kin
fita iko da shi ke lika fi kowa shan wahalarshi in yana
cikin rashin lafiya kamar kina ciki ne dubi yanda kika
zama a dan tsakankanin nan, kece kuma baki da kowa sai
shi in aka rasa shi kinfi kowa rashi ita tana aure tana da
mijinta da iyalinta ga ya'yanta ke ce baki da kowa sai
56

shi, Ina jin ha tadi hakan na soma kuka'saboda yarda da
zuciyata tayi cewarni ce bani da kowa sai babana in aka
Pasashi ni nafi kowa rashi. Kukan da nake yi bai hanashi
ci gabs da yi min magana ba, ke madadin da namiji ce a
wurin shi duk kuma abinda da namiji ke yiwa uban a
laulawa da taimakawa shi kikeyi mishi ke kinfi wani da
namijin ma jaruntaka don haka tsaya kawai a matsayin
da ya dace da ke ki taimaki mahaifinki ya samu lafiya in
kuma ailkin ya zo da akasi to kar ki ji zafin kanki ki
dauka kawai kaddarar kenan kin kuma rasashi ne a
kokarin da kikeyi na nema mishi lafiya.
Kalaman Mubarak sukayi matukar shigata ta yanda
har naji na yarda da magamar yin aikin nan take kuma sai
naji zuciyata ta daina tsodo addu'a kawai nake yi a yi
aikin a sa'a.
Da safe yaya Dija tana isowa ita da mijinta a
gabanshi nayi mata maganar ina ganin mu bar neman
sallama don komawa wani wuri mu tsaya a nan a yi
msihi aikin kawai don ba zai yiwu ya yi ta zama a cikin
wahala irin wannan ba.
Tayi maza ta ce min, a'a ba zai yiwu don ba zai yiwu
mu yi abinda zaum sanyashi cikin hatsari ba ban taba
ganin inda akayi irin wannan aikin ba ba kuma zai yiwu
a fara a kanshi ba.
Ai hatsari bai wuce ciwo ba yaya Dija gardama mai
tsanani ta shiga tsakaninmu, saboda taja ta tsaya a kan
bata son aikin tunda itace babba kuma itace zata fadi
yanda za a yi, nace mata a'a ni ya kamata in facla saboda
nice tare da shi a wuri faya ni nafi ki tsoron rasashi
saboda nasan zan fiki maraicinshi ni ce ni kadai bani da
57

Uwa bani da... ban iya karasawa ba kuka na soma yi
mata.
Yaya Ibrahim ya kalleni cikin natsuwa ya ce min,
kece mai fadin abinda za a yi mishi Maryam tunda kina
so a yi mishi aikin za a yi ké Dija ki yi akan wannan
ra'ayinta za a yi.
Karo na farko a rayuwarmu ai da yaye Dija da
jayaiya irin wannan ta shiga tsakaninamu bata taba cewe
gAma yanda zaa yi nace mata a'a ba, hankelina ya yi
matukar tashi da abinda ya farun musamman da na ganta
tana ta kuka saboda ta riga taki aikin da za a yin sai
karfinta kawai akayi bata yarda ta zauna ba ma a asibitin
kamar yanda kullum take yi kama hanya tayi ta tafi,
To in ailkin nan bai yi nasara ba me cewa yaya
Dija? Tambayar da na yiwa Mubarak kenan a lokacinda
ya zo don jin yanda mukayi da ita, bata fuska ya yi sosai
kafin ya ce min, to in kama ska yi nasarar fa? Ke ba a i
yi addu'ar yin nasara b sai ki zausa kina abrin zaciyarki
tana raya miki mnanan abubuwa? Da wani wanda yake
rike da rayuwar wani ne ko kuwa da wata hikima ne da
za ta sa mutum ya tsallake wa'adinshi? Da irin wadannan
kalaman na yarda na sanya hatmm a kan takerder ailkin da
Za a yiwa babana.
Cikin tsananin tsoro da fargaba ina gama sanya
hannun na koma gefe ina kuka yana rarrashina.
Yanda babana ya wuni karfashin dokar lilkita na bar
ya ci komai ko da kuwa ruwa ne baka nima na wuni ban
iya sanya komai a bakin nawa ba gashi babu yaya Dija
sai Inma yarta babban da dama take zuwa tayani zama
in ita bata zo ba saboda aiki ko wani aikin sai dare suka

58

zo ita da yaya Ibrahim idanuwanta a kumbure alamar tayi
kuka har ta gaji ban iya ce mata komai ba na daga hannu
ko bayanin likita na cewar za a shigar da shi Dtiyata da
misalin karfe goma da rabi na dare ba.
HASBUNALLAHU WA NI'IMAR WAKL' abinda
kawai nake karantowa kenan a bakina da kuma zuciyata
suka gama abinda sukeyi suka tas.
Wajen Rarfe taran dare Mubarak ya iso babu abinda
bai zo min da shi ba wanda ya san ina so amma ban iya
cin komai ba saboda tashin hankali sai kaduwa nakeyi
tamkar awcce sanyin hunturu ke kadata.
Ana cikin haka har lokacin ya iso gadon likita naga
an fara kawowa cikina ya bada sautin kulululu ban iya
daurewa ba sai da na ruga da gudu na shiga bandaki
kafin in fito na samu har an canza mishi kayan jikinshi
da rigar likiten na raca yaada zenyi da raina na rinka jin
tamkar ince na fasa abar yi mishi aikin kawai, shi da
kanshi babana za gane ya shiga wani hali saboda jinshi
da nayi yana cewa, Mubarak na gode Ubangiji ya yi
muku albarka in har ban fito ba kuma to ka rike min
uwata amana. Maimakon Mubarak ya ce misbi to ko ya
gaya mishi wata magana da zata yi mishi dadi sai kawai
naji ya ce mishi, a'a baba ni kar kace ka bar min amanar
Mero don ba zan karba ba in zaka bani aurenta kawai ka
bani ga mutane can a wancan dakin inka yarda in yi
hanazrin kiran mutum biyu kawai ko uku don su tayan
shedawa.
Haushin Mubarak da takaicinshi suka kamani har a
halin da babana yake ciki yana iya yi msihi musu da
sauri na ce mishi, a'a baba daina cewa ka baiwa wani

59

amanata ai lafiya zaka shiga ciki ka kuma fito lafiya
babu abinda zai sameka sai alheri, kai në zaka fito ka ci
gaba da kula da ni mu ci gaba da zamanmu babu abinda
zai sameka sai alheri, babu abin da zai sameka sai alheri,
nayi ta nanate fadin hakan tamkar dai shi ne abidna zai
sa hakan ya zamo ya yiwu.
Ni da shi muka bi bayan gadon da ake tura habana,
babana yana ta salati ni kuma sai kuka nakeyi shi kanshi
Mubarak ya shiga wani hali, watakila don ganin babu
kowa a wurin daga ni sai shi saboda batta su anti safara
da na tuntubesu kan aikin basu bani goyo baya ba balle
inji daiin gaya inusu cewar vau da daddare za a a yi, don
haka babu wani wanda yake: da cikakkiyar masaniya na
abinda ake ciki.
Suna tafiya muna biye da su har muka kai inda aka
tsaidamu shi kurna aka wuce da shi ciki.
Kwanciya nayi a kasa ina kuka, tashi-tashi ki gani?
Tashi ki zauna, kin taba ganin inda kuka ya yiwa wani
amfani ko ya zama sanadin samun biyan bukatarshi?
Addu'a ai itace ta kamace mu tashi ki zauna.
Da irin wadannan kalaman nashi ne na mike na
zauna kan daya daga cikin kujerund a ke wurin shi, kuma
ya fita ban san inda ya je ba jifa jif dai yakan shigo ya
zo ya sameni ya gaya min kalmomi na karfafa zuciya da
kara tuna min muhimmancin tsayawata kan addu'a
maimakon kuka ko yawaita damuwa ba zan iya tuna irin
addu'o'in da nayi a ranar ba, fatana da burina da a yi
nasara ne a fito da shi yana raye don in aka samu akashi
kan hakan to ban san abinda zan cewa yaya Dija da

60
sauran wadanda suke da hakka kan rayuwar tashi ba
gaba daya
Saboda tsananin kidima da damuwa bana iya
tantance dadewar da sukayi a ciki gaba daya in banda
duk abinda ake yi a cikin duhun dare ne guda daya da
Dayi zaton anyi adadin kwanakin da basu kidayuwa
saboda dadewarsu da na gani.
Mubarak ya sake shigowa ya sameni a inda ya barni
a zaune.
Sannu Maryam, da kyar na iya buda bakina na ce
mishi, yauwa saboda jin da nakeyi tamkar la66an bakin
nawa a manne suke, cikin yardar Ubangiji za a yi nasarar
aikin da ake yiwa baba Ubangiji kuma zai yi miki
sakaiya kan al'amuran rayuwarki gaba daya bance mishi
komai ba ya nemiw uri ya zauna yana kallon agogo in
dai komai ya tafi daidai ai sun kusa fito da shi.
Cikina ya sake bada wani sautin na kuluulu saboda
jin da nayi ya ce in komai ya tafi daidai kenan in bai tafi
daidai ba ma an kusa sanin abinda ake ciki kenan.
A haka muka ci gaba da zama a wurin babu mai cewa
wani komai, idona yana kan agogo in banda tafiyar
lokaci babu abinda nake dubawa, zuciyata kuwa tana ta
karanto addu'o'i haka, a haka a irin wannan yanayin da
awowi suka zama tamkar kwanaki a hakan kuma dai har
muka kai lokacin da suka ambata na kammala aikin da za
8u yiwa baban nawa sai kuma gashi an fito da shi kwance
a kan gadon babu wata alama ta motsi a tare da shi, muka
Sake biyo bayansu zuwa dakin da dama muka bari aka
dorashi a kan gadonshi aka kwantar da shi, abu guda
daya kawai da ya dan kwantar min da hankali shine
61

tabbacin da naji suna ta baiwa Mubarak ina anyi nasarar
aikin da aka yi mishin.
Amma ban samu natsuwa a tare da ni ba har sai kwanaki biyu bayan nan da naga babana ya soma wattsakewa daga mummunar wahalar da ya sha har kuma gashi numfashin nashi ya daidaita saura ya samu karfin jikine kawai.

Mutane sukayi ta zuwa duba babana saboda jin labarin aikin da aka yi mishi kai kace ahi kadai ne mara lafiya a asibitin nan, ina jin wani daga cikin yan kasuwar tumatirin nasu yana gayawa abokin tafiyar tashi, kaga ja'irar yarinyar nan yar gidan Malam Habu mai tumatir, kai wannan yarinya da jarumtaka take bata gajiya da hidimar mahaifinta kullum a cikin kai kawo da dawainiyarshi take shi yasa duk iya shegenta sonta yake yi.
A to ba dole ya sota ba Malam ko da na mijine ya ke irin hidimar da yarinyar nan take yi akan mahaifinta ai yaci a yaba mishi balle ita yara irin wadannan ai haka suke sunada halin tsiya da na arziki, kai ba duka ba inji wani da bansan ko waye ba ita dai wannan anyi dacentane Ubangiji kuma zai saka mata ya shiryar da ita ya bata mijin da zai sota ya riketa duk da iya shegen nata.
Babana bai cika kwana biyar da yin aiki ba sai da kowa ya gamsu da aikin da ak yin ya kuma ce gwara da akayi hakan ciki kuwa harda yaya Dija.
Tun kwana biyu da aikin babana sanda ya soma dawowa cikin hayyacinshi Mubarak ya dauke kafa ya daina zuwa asibitin baya zuwa da daddare balle kuma da rana, ko dama can kuwa mafi yawancin zuwan nashi kan
62

zamo cikin dare ne lokacin da zirga-zirgar dubiya tayi
sauki in dai ba wani dalii mai karfi ne ya kame na yazo
da ranar ba.
Rannan da safe ni da yaya Dija ne kawai a tara da shi
bayan mun goggoge mishi jiki mun gyarashi mun
tsabtace komai na dakin sai kamshi yake yi yaya Dija ce
a kusa da shi tana bashi ruwan tataccen kabeji da karas
yana sha a hankali yayin da ni kuma na gama tattara
kayan wanke-wanken mu na mikawa Inna nace taje ta
wanke sai kawai mukaji an turo kofar dakin a hankali
tare da yin sallama, gaba daya muke amsa sallamar tare
da maida hankalinmu wajen kofar.
Gabana yayi mummunar faduwa saboda ganin mai
sallamar, Umma ce ko ince Umman Mubarak tare da
Rumasa'u da Rukaiya, kadan ya rage in dibibice in rude
saboda rabon da muyi gaba da gaba da su haka an dade
ko ince tun daga ranar da abinda ya faru tsakanina da
Mubarak na samuna da akayi a dakinshi da al'amuran da
suka biyo baya wa ta mu'amala bata sake hadani da wani
daga cikin mutanen gidan ba, wacce tayi dalilin
haduwarmu a wuri daya kamar hakan ba dan gara-gara
Rukaiya in ta kure mana a makaranta mukan gaisa
saboda munyi karatu tare.
Sannu da zuwa Umma yaya Dija ce ta fara yin
gaisuwar daidai tana mikawa Umman kujerar zama, na
mika hannu don karbar yarinyar da take hannun
Rumasa'u duk da yanayin dake fuskarta tamkar dai ace
mu din ba wasa tare muke yi ba, gaba daya aurenta da
Mubarak ya canza al'amuran dake tsakaninmu ni da ita
kowa ya fi jin zafin wani oho?. Ko da yake dai nikam can
63

cikin zuciyata na sani bana jin zafin Rumasa'u kamar
yanda nake jin zafin Mubarak da wadanda suka sashi
aurenta.
Gaba dayansu na bisu na gaishesu kamar yanda naga
yaya Dija tayi, yaya jikin na malam? Yaya Dija ta sake
amsawa Umma zancensu ni kuma na dawo da hankalina
wajen sauraron abinda Rukaiya ke gaya min naga Hasiya
jibirin shekaran jiya ta tabaye ni ke na gaya mata tace in
gaisheki itama zata zo, nayi murmushi na ce mata ai jiya
tazo nan ta kusa wuni muna zancenmu ban sake Juyawa
na kaili Rumasa'u ba saboda bata bani fuskar da zan iya
fuskantarta in kakalo wata naganar da zanyi da ita don
haka na ci gaba da wasa da 'yarta da kuma hira da
Rukaiya, kc kadan dai banji dadin sammakon da sukayi
mana ba an saukin abiıma sun zo sun samu babana da
kuma dakin da muke ciki cikin tsabta.
Bayan tafiyarsu yaya Dija ta kalleni tayi murmusbi ta
ce, kai kishi babu kyau mata suna kokari, ban tanka mata
ba balle zancen ya yi nisa na kalli knna na ce mata, jeki
ki yi mana wanke-wanke kin ji? Ta ce to ta tashi ta fita
ba fa zuwansu bane ina jin Alhaji Mubarak ne ya turosu.
Na sake kin amsawa don kuwa ban san dalili ba sai naji
bani da ra'ayi a kan zancen nasu.
Sati biyu da aikin babana aka sallatmo mu muka dawo
gida bisa dokoki da aka jaddada mana binsu. Ranar wuni
nayi ina aiken Inna gidajen mutanen da sukayi ta zirga-
zirga suna ta dawainiya da mu irinsu Jumare gidan baba
Hodije Yakubo Halina, Hasiya Jibrin, malamaina ua
Markas irin su Malama Basma da Hindu abokan
karatuna na makarantar mu ta ilimi addini mai zurfi
64

musamman wadanda mukayi aji daya da su wadanda har
karo-karon kui suka yi suka kawo min don taimakawa
Zumunci irin wanda mutane suka nuna mana a

Please Login or Register in order to submit comment