Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da Amiru wani sati biyun mns beym
nan ya sake dawowa a lokacin nan kawa baifi kwanaki
biyar sulkz saura a fara bikin ba.
A Ciki wadannan kwanakin kuwa babu abin da
Yalkubudi bata yi min ba wanda suke yi wa amarensu ko
da yake ma kamar karasawa ne don tafi kwanaki talatin
tana min jike-jike, hayake-hayake, tsime-tsimw, gogo
goge, gyare gyare, kuilum kuma ta kan yi ne tare da yi
min bayami wannan uban zirga-zirga da wamuiea yro
yake yi ai gara a kara gyara mishi ke ya sameki.. kin san
ance wai ko kana da kyau to ka kara da wanka kar ki
yarda ki zauna bakya gyaran jikinki don shi namiji da
kike kallonshi.... ta danyi shiru kada katin ta ce, uhuyy
ke yanzu yarinya ce ba za ki gane yanda alamarin yake ba tukunna.
Ana cikin haka kwanakin biki suka iso jama'a suka
yi ta haduwa fiye da duk yanda ake ko daga gida
mutanan da sulka zo bikin ko kadan banyi zaton ganinsu
haka ba Umman Mubarak, Yakumbo Halima, baba
Sumaye, baba Lami, manyan dattawa wannan yan
matasa yaran mata kuwa akwai anti Asiya aminiyar yaya
Dija da malamata malama Basma akwai yar anti Safara
96

ga wasu mata su uku da suka gabatar min da kansu a
matsayinsu ne angwaye alamar ko dai kanne ko kuma
abokan wasan Mubarak sai dai ban san ta ina ba maza
kam babu adadi don kuwa naji ana ta maganar yawan
nasu abokan Mubarak da yawa sun zo daurin auren ga
samarin unguwa irin Isiyaku su ma ba a barsu a baya ba
don kuwa shi mai mu'amala da na kasa da shi ne abokan
babana irinsu baba Baidu da baba Hodijo kasuwar
timatir su ma ance mota guda suka zo abin dai gwanin
dadi gwanin sha'awa.
Ina kwance a dakin da nake zaman lalle ina lullube
da kaina na ji an shigo an zo an durkusa a jikina a
hankali na bude ido don ganin waye hakan? Inna na gani
da sauri na saki wani lallausan murmushi yaya Dija ta zo
ne? Ta ce a'a babanmu ne ya zo da mu ni da Abba,
sannunku da zuwa na mike na zauna ina nunam ata
kwanukan da na san akwai abinci a ciki don taci ta
girgiza kai nuna alamar ta koshi.
Buki baba Abba Gana ya yi irin wanda yake yiwa
ya'yan da ya haifa a cikin shi kona ince fiye da haka
dno kuwa yayi hidima ya ciyar da jarna'a abin ba a
magana, bayan san kowa daga jama'a ne aka yi daurin
auren bai yarda an dauki amarya kamar yanda abokan
Mubarak suka so su yi ba sai ya ce tafiyar tayi nisa baza
a dibi mutane masu yawaa yi irin wanan tafiyar da su
ba a cikin dare.
Don haka aka bari sai washegari a waunan lokacin
ango baya zuwa wurin daurin aurenshi don haka
Mubarak bai zo Gaidan ba yana Kaduna wurin
harkokinshi.

97

Washe gari ana gama karyawa akayi ta shiri ana fita don shiga motocinda zasu dibi jama'a ganin da Baba Abba yayi kaiyade masu zuwan zai iya kawo bacin rai yasa shi yin shiru yace su angwayen su debi adadin abinda suka ga zasu iya diba su kuwa su Amiru da Abdulhamid suka ce duk wacce take son tafiya kawai ta fito, mata kuwa sukace me za su yi ba tafiyar ba.
An fito da ni aka kaini wurin Abba Gana a lokacin nan kuwa yana tare da dan uwanshi Baba Goni alamar da tafiya ta zo ke nan kuka nakeyi sosai daga kuma cikin zuciyata kukan ke fitowa saboda tausayin abubuwa a yanzu kuma sa naga zaa tafi sai naji bana son tafiyar cikin dangin ubana.
Yakumbo Halima ta shigo dakin ga alama kuma kiranta akayi suka gaisa da baba Abba a cikin yanayi na mutunci da girmamawa, kece uwartasu? Tace eh Mallam suka dan yi hira kadan a cikin hirar tasu ta sake jaddada mishi ita da inna mu uwa da uba daya suke ita ta sha nono ta bar mata, to Ubangiji ya jikansu da Rahamarsa in tamu tazo kuma yasa mu cika da imani aka amsa amin amin, to mun gode fa mun gode mun gode yayi ta nanata godiyar tamkar dai wani abin akayi mishi sai da suka soma yi mishi sallama zasu tafi sai ya ce, to ungo ana Kabudi mika musu wannan sadakin da uban mijinta ya zo dashi ne wannan kuwa ni na bayar in kunje ku sai mata abinda kuka ga ya dace Yakumbo tasa hannu biyu ta karba tare sa yi mishi godiya me yawa.
Motar amarya itace motar da ta tashi a karshe kenan duk sauran motocin sunyi gaba kafin ita daga ni sai

98

Yakabudi ne kuma a bayan motar yiuyin da Amini da
wani wanda ban sani ba suke gaba.
Kafceciyar wayar cellular da ke hannun Amiru tayi
kara ya dauka tare da anmsewa, ran ango ya dade ban ji
abinda Mubarak ke gaya mishi ba na dai ji shi Amirun
ayna ce mishi, gabn daya jama'a dai sun taso suna ka
hanya amma mu garu nan a kofar gida ba ma taso ba
saboda shi warnan baban na ta da kake bani labari ya ki
bada ita.
s Mutumin dake tukin ya yi murmushi, kai Ahlaji
Amiru kar ka se ango ya shide kai in banda Allaji
Adbulhamid ya dage ai da cewa ya yi wai shi ma zai
biyo mu in yaso ko a Goabe ya tsaya shi nc ya ce sai dai
ya taho mu mu zauna.
Kai dai muna hanya amma mn biyo bayansu ne, ban
san abinda yace ba naji Amirun ya sake ce mishi to amin.
Muna zaune a bayan motar ni da Yakabudi bacci
takeyi saboda gajiyar hidima da kuma sanyin AC da ya
ratsaya, ni kuwa tunanin al'amura da yawa nake yi
Innata na fara tunswa 'yar rayuwar da mukayi tare dan
sanin da nayi mata mu'analar da nakeyi tunawa a
tsakanina da ita, rasuwarta da yanda hakan ya zama
sanadi na la'amura masu yawa, zamana da babana,
mu'amalar da ta gudana tsakanina da shi, na tausayawva
da kulawa har kawo zuwan baba Lantana gidanmu
al'amuran da aba Lantanat ayi mana sanadinsu a
Zuwanta gidanmu tausayin babana ya kama ko ncc ya
kara kamani musamnan da na tuna yanda ya bar gida ya
bar danginshi ya fito ya soma rayuwa tare da lanaia
rayuwar da da kunnena, na ji shi yana tabbatar mata da
99

cewar ita ce banagre mafi dadi da rayuwarshi ta dandana
yazo ya rasata a lokacin da bai zata ba ya yi bakin ciki
irin wanda bai misaltuwa bai gama wattsakewaa daga
rashinta ba da kewarta ya zo ya fada hannun baba
Lantana, alamuran da sukayi ta faruwa har kawo
wannan lokacin da muke ciki, wata rana sai labari ai
babu wani abinda yazo ya tabbata in dai ba kudurar
Ubangiji ba ne, wannan jimlar jimlace da mutane
daban-daban suka yi ta furtamin ita a lokuta daban-daban
bisa faruwar al'amura edaban-daban sai dai ban taba kawo
tsammanin wucewar tasu za ta zo min a haka ba saboda
tsananin daci da ciwon abubuwan da sukayi ta faruwar
sai na rinka ganin tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin
tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin tamkar nawa
mas'aloli da damuwowin ba masu wucewa ba ne masu
dawwama ne don haka şai na zamo a duk lokacin da
wani babba ya tabbatar min da cewar zasu wuce wata zai
wuce har ki ganki kina bayar da labari sai in samu kaina
da tambayar kaina to yaushe ne? Yaushe ne wata ranar
da zai wuce? To gani a yau sai na samu kaina da yarda
da cewar tabbas mutum mai gaggawa ne mai sauri ne a
kank al'amuranshi, saboda ganin da nayi tamkar daurin
aurena da Mubarak da akayi kawai ya kawo karshen
al'amuran duka zamana da baba Lantana da ma shi
baban nawa a gida daya ya kare, lissafin da ake tayi min
na dadewar da nayi babu aure a ce nan kusa babu sauran
sa'a ta shima ya kare a yau ni din matar aure ce, matar
ma kuma ta Ahmad Mubarak wanda duk kwaramniyar a
kanshi aka yi ta yi haka na zurfafa cikin tunani mai tsawo
nayi nazári mai zurti kan al'amuran rayuwa da kai
100
kawon al'amuranta abubuwan da na shiga da wadandA
idona ya gane min sai na kara tabbatarwa kaina da cewar
rayuwar gaba daya wata rana zata kai ga kaaewa, tausayi
ya yi matukar kamani har na kasa hana idanuwana zubar da hawaye.
Sannu a hankali sai gashi ahr mun iso garinmu har
gamu muna shiga unguwarmu, bude ido ki gani Maryan
nisan tafiyar da kika sanyamu ta kare gamu mun iso
gida, Amiru ne ya ke yi min wannan magana,r ban tanka mishi ba.
Babana na hanga a kofar gida cikin kwalliyar da ban
taba ganin yai irin ta ba, habbar riga da 'yar ciki da
wando ga kafceciyar hularshi ta zanna a kanshi, bakin da
ke fita daga cikin motocin dake tsayawa yake yiwa
sannud az uwa wadanda yan uwanshi ne da suka biyo
motocin amarya sai dai nasan 'yan daidaiku ne kawai zai
iya shaidawa a ciki sauran duk sai anyi mishi bayaninsu,
tunanin babana ya sake dawomin ban taba yin kwana
bakwai ban ganshi ba don ban taba zuwa wani wurin da
na bar shi na abr unguwaru da aka haifeni da gidanmu
naje na kwana bakwai ban dawo ba, to inama nake
zuwa? Gidan yaya Dija ne sai ko Yakumbo Halima da
sauran dangin Inna nan din kuwa bana iya zaman da
zanyi kwana bakwai nake gudowa in dawo gida sai
wannan karon de nayi tafiyar dana kwana sittin da daya.
Ganin da nayi za a wuce kofar gidanmy bayan nayi
zaton nima a nan za'a saukeni yasa nayi maza na cewa
Amiru, a'a a'a ba a nan za a saukeni ba? Gaba daya shi
da mai tukin suka hada baki wajen tambaya ta gidanku?
Ai furta kalmar na bayar na karar mishi da baba sukayi
101

tare da baba Abba Gana ya rabaki da shiga gidanku ba
tare da izinin angon ba yarinya shi kuwa tuntuni aikina
jin wayoyin da yake tayi jaddadawa yake yi lalle ne a
wuce da ke gida kar a ce za a tsaidake a ko ina, ban san
dalili ba ina jin bayanin na Amiru na soma yin kulka
hawaye suna ta gudu a kan fuskata, a hakan aka shigar
da ni gidansu Mubarak sashin Umman shi aka fara kaini
itace ma ta jagorance mu ta wuce gaba muna biye da ita
a baya zuwa inda tace can din ne wurina muna tafiyar ina
tunanin shekaru biyar ne cif har da wasu watanni ban
shiga gidan ba da nake shiga irin shi tafiyar da mukeyi
kafin mu isa inda zata kaimin ya sani fahimtari rin canjin
da gidan ya samu a shekarun da nayi ban shiga ba.
To ga nata wurin nan bismilla ina jin ta fadi hakan na
soma karanto addu'o'i iri-iri ko dama can kuwa tun
isowata kofar gidan nake addu'ar ban fasa ba man tarar
da su anti Kubra, anti Hindu, Hasiya Jibrin da mutane da
yawa wadanda ba zai yiwu in yi ta lissafinsu ba, aikin
jere suke ta yi daga ganin jama'ar dake wurin dai kai ka
san ba karamar gaiyata yaya Dijat ayi ba.
Mun kuma shigo. ne muka sama su Yakumbo Halima
da su baba Sumaye da suka rigamu isowa suna fadni, kai
masha Allahu tubarakallahu Ubangiji ya yiwa Hadiza
albarka mafi yavwancin mutanen dake wurin sukayi a
amin, amin, ita kam ai uwa ce ba ya ba.
Wani daki da babu komai a ciki daga labule sai
katifar da aka yiwa shinfida mai kyau aka kaimu ni da
Yakubudi ina shiga anti Kubra ta biyomu ta yiwa
Yakubudi sannu da zuwa ni kuwa kallona tayi ta tsuke
fuska kafin ta ce min, maza share hawaye ki hadiye
102

kukan da kikeyi ya ishen haka na gani a wurin Hadiza
jiya tun da akayi waya akace an daura auren ki da Alhaji
Ahmad take kuka tun ina rarrashinta ina bata hakuri har
sai da ta kureni nayi mata kaca kaca nace ina dalilin da
za ki tara jama'a irin wannan ki yi t skuka a cikin su, to
maza kema sharesu ni ma ina nan kika tuna in na naki
kukan na dadin ganin burinki ya cika ne kin auri mijin da
kike so duk daya kar in sake ganin hawaye a idonki
Ban tankawa anti Kubra ba iyaka dai dama nasana
halinta na kuma san tana cilkin mutanen da suke sen yaya Dija.
Hasiyan Jibrin ta shigo na lama ji dadin shigowar
tata, kin gani abokan tasowarki har sunyi salla suna cin
abinci ke kina zaune wanan doguwar tafiya ai ko mura
kike ya rage ga ruwan zafi na zube miki ki yi wanka si
ki yi alwala ki yi salla ki dan ji dadi, nace mata to kafin
in idar har ta tanadar min abubuwa masu saukin ci
wadanda ba za su gunduren da sauri ba irinsu strawberry
grabus citrus da apple masu ban sha'awa wadanda ko
don kyansu zaka iya 6ata lokaci mai tsawo kana cinsu
basu gundureka ba, itama Yakabudi ta kai mata tare da
abincinta tana ci ita kuma ta dawo wurina muna hira, ai
naso in zo her Gaidan din nayi maza nacem ata gara daa
bakije ba Hasiya da Walid yasha wahela tafiyar tayi
tsanani da yawa, ta yi murmushi ta Ce, to ba biki uwarshi
akeyi ba, na yi murmushi a karo na farko tun bayan da
bikin ya fara na ce, ai kuwa da uwar tashi bata kyauta
mishi ba don da ta wahalar da shi.
Hira kadan aukayi sai naji ta soma tambayata ina ata
dai kin shigo ne da shirinki shiri kamar yaya Asiya? A
103

hankali cikin muryar rada ta soma yi min bayani, shirin
rike mijinki a hannunki mana ko kin san yau kwana hudu
kenan da dawowar uwargidanki daga yaji, gabana ya yi
mummunan fadiuwa saboda a anzu zaman lafiya nafi so
ba fitina ba, duk da ta gane faduwar gaban da na samu
bata yi shiru ba sai ta ci gaba da bani labarin da take son
bani alamar dai ta matsu sai ta gaya min, ai rikici mai
yawa akayi bayan tafkiyari ta ja ta tsaya kan in dai Alhaji
Ahmad zai aureki to ita ya sauwake mata saboda wai
kina waje ma baki bar aurenta ya zauna latiya ba balle
kuma a ce kin shigo gida gaba daya kuna daga ita har
yan uwanta sun mara mata baya.suna fadin ai da aurenki
gara a ce wasu kishiyoyin ya kawo mata su zama hudu,
wajen kwana talatin ta yi bata nan shi da abokanshi suka
yi ta zuwa biko ana yi musu wuiakanci wasu abokanshi
har suka fusata suka ce ya saketa ya ce a'a ashi ba zai yi
aure don ya rabu da ita ba ne dukanku yana sonku ya
kuma yi alkawarin matukar ba ita ta tsoma kanta cikin
abinda bai shafeta ba zai yi iyakacin kokarinshi wajen
ganin yayi adalcin da zai tsarevwa kowa hakkinshi.
Na yi ajiyar zuciya mai karfi ba tare da na ce mata
komai ba baya ga Ubangiji ya bashi ikon yin hakan
saboda iyakacin gaskiyata nake nufi nafi son zaman
lafiya a kan gutsiri tsoma.
Sau biyu anti Kubra ta kawo min kan wayar
telephone din dake dakin wai in kar6a zai yi magana da
ni ban kara ba saboda sai nafi son ya kyaleni kawai in
zauna shiru ko zan samu natsuwar da nake bukata a tare
da ni, tunda na soma gane cewar nan gidan nashi dana zo
ma zai yi wuya in har zan samu zancan shirun da nake
104


Dukata don ina daga kwance na jiwo baba Sumaye tana
cewa, kun ga dangin uwargidan nan babu abinda suke
nema in banda a yi rikicin da za a yi kaca-kaca a bikin
nan to na rokeku kar in ji wani cikinku ya kulasu.
Tana fagfin hakan na ji mutanen dake wurin su na ta
bayaninai mu ma kaza mu ma kaza tun jiya suke yi.
mana wulakanci abu kaza da kaza har suna gori wai..
Yakumbo Halima ta katse masu kokarin yin bayanin kan
irin gorin da suke yin tare da fadni, abin dai bai yi dadi
ba da kwabar yarsu suka yi suka nuna mata

muhimmancin zaman lafiya da yafi musamman ma da
yake akwai sanaiya mai karfi a tsakanin mu da su,
haduwarsu karkashin miji daya kuma wannan kaddara
ce su dukansu biyun matan shi ne in banda haka ai da
Mero ya fara aura da ya aureta a wancan lokacin kuma
da ba ma zaton zai koma auren 'yoarsu to kaddara don
haka mu ba ma fada da ita sai dai mu yi mata addu'a,
yanzu ita wacce tayi sanadin abin ina take? Itama ba
ance shekaranjiya ta tafi ba itama ta yiwa kanta sanadin
nata auren saboda sharrinta, shi mutum duk yanda ka kai
da kinshi ai baka iya hana shi samun abinda kaddararshi
ta rubuta mishi in da hakan yana yiwuwa ai da auren
Mero da Alhaji Mubarak bai yiwu ba.
Na zaro ido ina kallon Hasiya Jibrin don son jin karin
bayani kan maganar da na ji Yakumbo Halima ta fada na
wacce tayi sanadin da aurena da Mubarak bai yiwa ba a
wancan lokacin itama ta yiwa kanta sanadin nata auren
na kuma san da baba Lantana take nufi, sai Hasiya Jibrin
ta gyara zama ta ce min, ei ai ranar da ake shirin tafiya
daurin aure baba yasa a yiwa 'yan kasuwar timatir dinsu
105

abinci na musamman ya ce su ci a kuma zuba nmusu a
kula a sa musu a motar da suka yiwo shata saboda nisan
tafiyar sai baba Lantana ta ce zata yi wannan tana kai
kawo tana hidimar girki ana raha ana barkwanci da ita
har muna cewa a'a kaga baba Lantana abin mamaki ta
sake sai hidima ake ta yi da ita, ashe ashe baba Lantana
da abinda ta shirya, kamar baba ya sani ya ki fita daga
cikin gidan nan har muna ganin kamar ya daan takura
mana ashe ashe in bali labari sai kawai idonshi ya kai
kan baba Lantana tana zuba wani abu a cikin abincin nan
bayan an gama shi ai kuwa dai nan da nan ya isa wurinta
ya tambayeta me take zubawa a çikin abincin? Ta ce bata
zuba komai ba ya yi yayi ta ki yarda da cewar ta zuba
wani abu ya ce to ta diba tayi nan ma ta ki.
Hannu biyu na saka na dafe kaina saboda sarawar da
yakeyi a dlai in tsoratar da nayi ban iya barinta ta kai
karshen baya iin ba na tambayeta me take zubawa a ciki
Hasiya? Sai ca ta kuramin ido kaíin ta ce, guba su ci su
mutu ko ince duk wanda ya ci ya mutu, salati na rinka yi
ina karawa kr fin daga bisani na shiga yin hamdala ina
godiya ga Ub.ngijin da ya yiwa babana wannan rufin
as rin bai barta ta ja mana wannan abin akin cikin ba ko
me muka yiwa baba Lantana ni da babana ta ki mu irin
wannan kiyaiyar? Akmar in tsaya yin wannan tunanin sai
kawai ma na kavwar da shi na kalli Hasiya na ce, to sai
aka kare a ya ya?
Ta ci gaba da takaicin abinci ta kama kuka da zage-
zage wai zai kulla mata sharrin da ya saba kulal mata, ya
ce a'a ai babu sauran sharri je ki na sauwake miki auren
ya isa haka, za ta yi rashin mutunci su Anti Kubra suka
106

fitar da ita daga gidan aka dauki abincin aka je aka tona
rami aka juyeshi aka rufe don kar wani abu mai rai ya ci,
na ce hodijan na kame bakina nayi shiru.
Rannan dai da daddare bacci ya gagara ta yayi gaba
daya mutanen dake dakin sunyi bacci amma ni idona
biyu.
A baya a duk lokacin da na kan zauna in yi tunani a
kan yin aure na kan ga kamar yin auren hutu ne amma
tunda auren ya gabato ni na samu kaina cikin wani irin
yanayi da yanzu da wadannan al'amuran suke ta faruwa
sai na gane lalle akwai wani babban al'amari a cikin don
haka maimakon in yi ta juyi idona biyu ni kadai saboda
bacci ya gagareni sai na koma karanta kalmar Lahaula
wala kuwwata illa billa kalmar da Manzon rahama ya
tabbatar mana da cewar tana maganin musibu kala
daban-daban har guda dari daya babu wato casa'in da
tara mafi kankantar musibun nan kuwa shi ne bakni ciki
har gari ya waye ban daina ba da na idar da sallar asuba
ma komawa nayi na kwanta na ci gaba da karantawa.
Ina cikin haka sai ga anti Safara ta shigo dakin da
nake nayi maza na mike na zauna na tare ta da murmushi
cikinta ya fito ta kuma kyau ba kadan ba.
Amarya ta ango, anya da wata amaryar dá ta fiki
morewa kuwa Yahcuwuna? Nayi maza na katse
murmushin da nake yi kafin na tambayeta, wacce irin
morewa kuma anti bayan duk wannan kwararmniyar? Ta
ce kin auri mijin da yake sonki ban taba ganin so irin
wanda Alhaji Amadu yake yi miki ba kwaramniya kuwa
ina ruwanki da ita tunda dai kinyi sa'a Ubangijin mu ya
107

rufa muku asiri ke da babanki duk abinda akayi nufin ya
same kun bai sameku ba.
Nayi maza na ce haka ne anti, to zuwa nayi yanzu
don in ganki in gaya miki kisa hannu biyu ku karbi
al'amarin mijinki kar ki yarda ki tsaya sakarci ko tunanin
wai ko ke amarya ce a'a yi hidimar aurenki kawai ke ko
iya shegen nan amare a yi ta tsiya ana wani iface-iface
ban yarda ki yi mishi ba kin ji na gaya miki, hannu biyu
na saka na rufe idona tare da fadin ki yi min irin tuwon
da kike yi min jiya anti. Zanyi miki ma yafi na jiya dadi
ki ci tare da angonki don nasan ba wuya ace ya wuce yau
din nan bai dawo ba, kisa hannu biyu ki karbe shi in yaso
babu kuma ruwanki da kwaramniyar da take cikin
gidanshi kar ki daga ido ki kallesu balle su ganekin san
abinda suke ciki, ita mace da kike gani ko wace da
halinta tak Zama, nace to na gode anti, tayi min sallama
ta tafi har cikin zuciyata sai naji dadin iin kalaman da ta yi min.
To haka akayi wunin bikin ranar cikin wani irin cikar
da ba zai ki atantu ba ta wurin mu ma dai muna da yawa
ga yan uwn babana da suka rakoni daga Gaidan ga
dangin Inna ta wadanda su ma masu yawa ne babu laifi
ga gaiyar yaya Dija na kawaye da dangin mijinta masu
kara nan gidan su Mubarak ma ba a magana uwargida
kuwa kai kace tamkar da gadara yan uwanta suka zo
don su nuna su din masu yawa ne.
A wancan lokacina marya 6oye kanta take yis aboda
k unya da kawaici ba kamar yanzu ba da amarya ke kai
kawo a tsakanin yan bikinta sai dai hakan abi hanani
tsala ado, wuni nayi ina kwalliya ta burgewa kwalliya
108

kuma mai tsada da kowacce nayi sai kaga kamar kar in
cireta saboda ina tare da gwanayen kwalliyar irinsu
malama Hindu da malama Basma ga uma anti Asiya
wacce ita dama babbar sana'arta kenan gyaran amare ciki
da waje, in nace ciki da waje kema sai ki gane abinda
nake nufi.
A gaba daya sashinmu a wancan lokacin bakina ne
bikin farko da mutanen mu suka sheda video coverage
ana daukar su ana kuma yi musu tambayoyi, me zaku ce
game da wannan aure na Alhaji Mubarak da amaryarshi
Maryam? Wasu su yi magana wasu kuwa kunya da
rashin sabo ya hanasu cewa komai in banda kyalkyalewa
da dariya wasu kuwa da abin yayi matukar burgesu duk
da sun kasa cewa komai fadi sukeyí yau ku zo ku gani
bin mutnae akeyi ana yi musu tambayoyi da irin abin nan
na masu rahoto.
Malama Basma itace tayi magana ta ilimi har ta samu
jan hankulan mutane gaba daya aka koma sauraron
bayanin nata tayi magana ne a kan matsayin aure da
kuma' menene kishi a musulunci, tayi magana sosai ta
kuma karfafa magangnaun nata da ayoyi da hadisai tare
da kawo misalai na manyan mata magabata yanda suka
tafiyar da rayuwarsu tsakaninsu da mazajensu da kuma
kishiyoyin nasu duk da ba wai basa kishin bane ya sa
suka yi hakan a'a sai dai su fahimtarsu a kan kishin
daban mu ma a yau tamu fahimtar daban.
Da ta kawo karshen jawabin nata sai tace ya ku yan
uwanam ata ina kira garemu da mu yi gyara a kan yandaa
muke tafiyar da al'amuran da suka danganci kishinmu a
yau mu daina kishi na jahilci kishi na rashin sanin ya
109

kamata mu koma yin kishi irin na shari'a wanda shi ne
ibada.
Wassalamu alaikum wa rahamatullah, gaba daya
wuri ya kaure da kabbara malama Ubangiji ya saka miki
da alheri abinda kowa ke fadi kenan.
Ana gama wannan aka shiga yin hotuna wai duk
ribibin da kaeyi nayin hotuna da amarya ita Rumasa'u da
kyar ta yarda aka yi mana hoto guda daya ni da ita da
aka kawoni dakinta kuwa kamar yanda aka saba bisa
al'ada na kai amarya wurin iyayen miji da uwargidanta
in har tana da ita yan uwanta basu ji kunyar fadin babu
wata amana tsakanina da ita ba tundai ta din ba wan
girmana tayi ba banda haka kuma ai banbancin dake
tsakainta da ni kadan ne iyaka ita tana ciki ne ni ina waje
ba manyan dattawan da suka kaini ba wadanda
shekarunsu suka kai fassara musu al'ar ari ko da kuwa
da kafa ka iadeshi ba da baki ba ko ni da nake lullube a
gabansu na gane abinda suke uui, to balle kuma su a
haka muka tashi muka fito aka dawo da ni dakina tunda
dama sai d aka kaini wurin Umma kafin a kawo ni
wurinsu mun dawo' daki nuka ci gaba da harkokinmu sai
a wata yar uwarta ta shigo wai ga kudin sayen bakina
marya an manta ba a bayar ba, anti Astya ta ce, aki haba
a1 babu komai mayar masu kawai, ita wannan amaryar

Please Login or Register in order to submit comment