Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki kama ruwa,gashin dama ai shine dai-dai tunda muna son ruwan ya shiga ciki ya gasa miki ciwon,to kodai ɗan ƙaramin tiyo zamu samu a zira a bakin botar sai kema kisa ko ruwan zai shiga? Kai nan ma ba dabara bace,kinga kawai kawo butar a zuba kar ruwan ya ƙone".
Ita dai Laraba kanta a sunkuye Batace komai ba,har Sai da akace ta miƙo buta ta shiga ta ɗauko.Sai da umma ta haɗa mata ruwan ta sanar da ita yadda za tai sannan ta bata ta nufi ban dakin.Ita kam umma al'ajabi take tayi,a haka har larabar ta kuma dawowa ta haɗa mata wani ruwan ta ƙara watsawa😂.
**********************
Suna nan zaune ba wata hira suke ba a tsakaninsu,sai ga malam ya aiko da Isma'il da kayan miya da ledar taliya, kasancewar yasan su salame sun koyo azzalumin rashin mutunci,yasan bazasu bawa uwar albarka koda ruwa ba.Duk yadda Laraba take ji,haka ta daure ta tashi ta ɗora musu taliyar,maman Maryam ta so ta bari amma tace zata iya.Koda ta kammala a kwano mai kyau nan ma aka zubawa malam,suma Baban Maryam nasu daban aka zuba musu shida malam Garba.Maryam kam ɓatan dabo tayi,sai da kowa yaci ya ƙoshi sannan ta dawo gidan.Isma'il ya gama cin abinci kenan,ya ɗago ya kalleta ganin ta faɗo ɗakin a guje ko sallama babu tana haki"Ke Maryam shi ne kika gudu kika barni kin san ban san gari ba ko?, Badan gidan nan bai da wuyar ganewa ba ai da na ɓata".
Humm yaya Isma'il ai dan baka san ina naje bane shi yasa,da ko cewa nayi kazo muje bazaka ba,Anty Laraba ai kin san gidan su maraba da wari ko?"
"Eh mana gidansu Iro mahaukaci".
"Yauwa can,to dama rannan ne fa da na je ta wajen layin,kin san wai ɗaureshi ake yi,ni ban sani ba sai naga an ɗaureshi jikin bishiya, ina zuwa nace mishi sannu yaya,sai naji yace min yauwa,nace laifin me kayiwa me gari yasa aka ɗaureka?sai yace min babu komai,tsabar zalunci ne,shine nace masa idan na kwance ka nawa zaka bani? Shine yacemin biyar,Nikuwa na kwance shi,ina kwance shi kuwa ya riƙe Ni,yaita zabgamin igiyar nan,da kyar aka kwaceni,shine ban faɗa wa kowa ba nace saina rama,dana san yau zan tafi shine nace nasami bulalar malam ƙatuwar nan dayace yana dukan masu kunnen ƙashi da ita na ɓoye,yauma ina zuwa na tarar dashi a ɗaure, na kuma cewa in kwance ka? Yace "eh" na ce,idan na kwance ka nawa zaka bani? Yace ɗari,shi ne nace masa Ni kuma zan baka ɗari biyu kana so? Ya cemin "eh" shin Ni kuwa na fito da bulalata na shiga zabga masa,Allah yau ba kalar kukan da Iro baiyi ba,da farko ba wanda ya fito sai daga baya baban su kandala ya fito shi ne ya ganni ya biyo ni,wallahi da kyar na sha" ta ƙara sa maganar tana mayar da numfashin gudun datayi.


"Na shiga uku na lalace! Dama har yanzu Maryam baki daina halin ba? Malam fa cewa yayi kin kintsu kin zama kamila mumina,ashe ƙarya ne,ai ni dama nasan da kamar wuya wannan matsayaciyar ace cikin ƙanƙanin lokaci wai ta nutsu,to wallahi yau sai dai abin ya ƙare akanki,mahaukacin da kika tsokano abin sai dai ya tsaya akan ke da kika jawo,ni kinga ma tafiyata, in an gama lallasa ki a kawomin ke nayi jinya,'yar iska kawai".

Laraba dake tsaye jin abinda umma ke faɗi,dan haka ta tattaro jarabar ta ta da ta can tace"Ai wallahi indai ina nan ba wanda ya isa ya taɓa maryam,ba dai Iro bane kawai,to yazo ni zan lallasa shi,Ni na ma warke,Maryam jeki ki ƙara tsokano shi,yazo wallahi saina ci hancin babarsa".

"Oh Ni Huwaila ! Nikam naga abinda yafi ƙarfina, ah kice malam mazahabar caskale ya kawo ki bawai ki shiryu ba,kidai ƙara tambaɗewa da lalacewa,dan haka tashi maza gara ma mu koma gidan nasan yadda zanyi ki daina wannan hatsabibancin,tunda gashi har da masu ƙirar katafila ke tare miki faɗa,ba dole abu yaci gaba ba tunda kunsa zalunci a harkar, kije ki tsokano ƙananan ɗiba,ita kuma ta markaɗe miki su,to kinga tashi maza musan nayi".
Haka tá kama hannun Maryam tana faɗin taso 'yar jaraba ai banga ta zama ba tunda kika tsokano motsatstse".

"To ai ban ɗauki jakata ba umma"

"Ba buƙata ki barwa wasu almajiran ita,tunda baza'a rasa masu buƙata ba".
"Dan Allah Innar Maryam ki barta karki tafi da ita kinga itace ƙawata,kuma ita ke bani shawara a komai,na rantse ki kyaleta duk wanda ta tsokano Ni zan tare mata".

Numfashin takaici umma taja sannan tace,"kice Maryam ba koyon tarbiyya aka kawo ki ba kawai an kawoki koyon CASKALE,to wallahi bada ni ba,gara ki koma gabana duk abinda zakiyi kiyi shi da a gaban idona".


Da matsiyacin gudu sukaga malam ya shigo,yayin da ya buga wani uban tsalle ya ketare kan Maryam ya afka ɗakin Laraba ji kake bamm ya banko ƙofar.Salame da Zuwaira na zaune kofar daku nan su su na aikowa su Laraba harara a fakaice dan suna jin duk abinda suke faɗa.laraba ta buɗe baki da niyyar tambayar malam sai ji tayi anyi ciki da ita amma bata faɗi ba sai dai ta motsa daga inda ta ke.Malam Garba ne da baban Maryam suma a guje yayin da duk suka ruɗe suka shiga laluben inda zasu ɓoye,daga can malam Garba ya shiga faɗin"yo ta nan Shu'aibu,biyo nan ɓangaren Inna salame".Suma su salame ganin mazan na gudu yasa suka shiga wurga ido dan ganin meke faruwa,aikuwa a guje malam Garba ya bangaje salame ,itama Zuwaira dake tsaye tana son ganin meke faruwa nan baban Maryam yayi gaba da haɓarta,wadda saida tayi wani juyi kafin ta kifa saman randar ruwanta nan kuma kowanne ya shige ɗaki ya banko batare da la'akarin ko wanne ɗakin suka shiga ba.

Da nufin yin bala'i Zuwaira ta ɗago,amma sai me.Ido biyu tayi da Iro daya shigo a guje yana muzurai hannunsa riƙe da wata sharɓeɓiyar adda tsirararta,na ya shiga raba ido.Ganin hakan da sukayi duka hankalinsu ya tashi, kafin kace me salame duk da tsufanta ta kama katanga ta haura,Zuwaira dayake tanada ɗan jiki kaɗan ta miƙa mata hannu itama tana faɗin "yaya taimakamin nima na haye dan Allah kinji 'yar uwa".

"Yau babu wannan zumuncin zuwai ,kowa yayi ta kansa ta ina na zama 'yar uwarki kedai nemi mafaka kinga nayi nan" Salame na kaiwa nan ta dira ta baya.Zuwaira na ganin hakan ta kama duru-duru,kawai saita nufi ƙaton rumbun gidan ta buɗe duk ƙaiƙayin dake cikin gero batayi tunani ba ta faɗa ciki.


Idon Iro ne ya sauka akan maryam,aikuwa ya zaburo yayo kanta,ta fice a miliyan ya rufa mata baya.Jikin Laraba ne yakama rawa,nan umma ta kalleta tace"ke kuma ɓultuwa me kika tsaya jira,ba ke kika ce duk wanda ya taɓa Maryam zaki bashi kashin bala'i ba,to yau gata nan taje ta tsokano motsatstse sai ki je ki tare mata ai,dan wallahi Ni yanzu gida nayi ta taho daga baya tunda ita tajawa kanta,in Kuma kin kwatota ma tafi tare".Tana gama faɗar hakan ta nufi ɗakin da taga mijinta ya shiga.....


*Pls managed*



*Alƙalamin khady* ✍
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*'YAR CASKALE*
( _Sanadin bakin uwa_)

*Na*
*KHADIJA USMAN*
(Real tame gari)

5⃣9⃣-6⃣0⃣

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*____________________________________*

Maigari ne zaune a gindin bishiya,tare da mutanensa ana gudanar da harkokin mulki irin nasu na masu sarauta.😂

A guje Maryam ta tunkaro su,da yake gurin a kan kwana ne ya sa ita ce a kan gaba,dan haka ita suka fara hangowa.Ita ɗin ma tsallen ta yi kamar yadda malam ya yi,ai kuwa sai ga ta ta tsallake maigari tare da tuge rawanin dake kansa.

"Kaga irin marasa tarbiyya"cewar wani bafade da ya yi tozali da rantal ɗin kan maigari.Maigari da ya kumbura yana shirin zartar da hukunci akan wannan mai babban laifin,kawai sai idonsa ya hasko masa Iro ya nufo su da adda tsirarar ta,kafin ma ya ƙarasa magana tuni Iro ya iso inda suke,Hakan ya sa maigari faɗowa daga kujerarsa.Iro ko ta kansa bai bi ba ya tsaya raba ido yana son ganin inda Maryam ta yi.

Ya jima tsaye yana zare idanu,su kuwa duk gurin jikinsu mazari yake yi.Cikin tsawa Iro ya ce "waye ubanta a nan?"

Maigari duk da bai san wa ake nufi ba amma haka ya daure yace cikin rawar murya"ai ita ɗin shegiya ce"

Zare ido Iro ya kuma yi,cikin wata tsawar yace" To waye baban babanta?"

Wannan karon wani ne ya yi caraf ya ce "ai shima uban shege ne".

"To shikenan tunda duk shegu ne,kai wannan" (ya nuna mai gari),kai ne babanta,kai kuma baban baban babanta".cewar Iro.

" Mun ji mun amince mun karɓi wannan kyautar" duka suka haɗa baki.

"To wa zan fara yiwa yankan rago a cikinku? Dan dama na ce tunda ta dakeni sai na yanka uwarta ko ubanta".

Jin abin da ya ce ne ya sa su maigari ƙara tsurewa suka shiga roƙonsa a kan ya yi haƙuri.Ganin kamar suna daɗa tura shi ne ya sa maigari yin wata dabara domin ya zuwa yanzu ya fuskanci wadda ta tsokano Iro.

"Kaga Iron Lantana ba dai kace harda uwarta ka ke nema ba?"

"Eh ɗin"Iro ya faɗa yana zaro ido.

"To maza shiga ciki,tana can ta goyata duk ka haɗa ka yanka su gaba ɗaya". Ai kuwa a guje Iro ya bi wata hanya ya shige wani gida.Su kuwa su maigari ba tare da ya sallami kowa ba suka hau kwasa a guje, shi ma bai damu ba ya tashi da sauri ya nufi bakin kasuwa ,a ransa yana me ayyana sai ya sa an nemo masa iyayen wannan yarinyar ya ci su ta ra.

*************************
"Baban Isma'il buɗe ƙofar mana ni ce"cewar Umma dake tsaye tana bugun ƙofar ɗakin da ta ga mijinta ya shiga.

"Ke dai in kin kuɓuta ki yi ta kanki ,amma ni ba zan fito ba wallahi"

Ƙara bugawa ta yi ta ce "haba malam,yanzu dan abin kunya ɗakin tsohuwar mutane ka shige,to ni dai wallahi na yi nan,dan ga shi nan a saman rufin ɗakin da kake yana ɗaye kwano zai shigo".ji kake kararaf ana kiciniyar buɗe ƙofar duka ɗakunan,yayinda jin maganar da umma ta yi ya sa har malam Garba fitowa ba shiri.

Dariya umma ta sa duk da halin da suke ciki ta ce" ba gashi yanzu kun fito ba,da ina ta magiya abu ya faskara,to ni dai malam na yi gaba sai kun taho dan wallahi ba zan zauna a ɗauki rayuwa ta a garin da ba nawa ba,dan haka ni nayi nan" Ta ƙarasa maganar tana nufar ɓangaren Laraba dan ta ɗauki jakarta.

Turus suka yi dukansu, ganin Laraba tsaye tana ta rokon malam a kan ya buɗe ƙofar amma ya ce ba zai buɗe ba.Maryam da tun ɗazu tana maƙale a soro da sauri ta ƙaraso tana faɗin"Baba malam yi sauri ka fito gobara a ɗakinka na zaure"

Ba shiri malam ya buɗe ƙofa har yana tuntuɓe dan sauri,saboda ajiyar sa da duk kadarar sa suna wannan ɗakin, su ma jin abin da Maryam ɗin ta ce ya sa suka rufawa malam baya.Zuwai dake cikin rumbu jin an ce wuta itama tayo tsalle ta fito🤣.

*************************

Dukan su zaune suke an sanya Maryam a tsakiya sai raba idanu take.kowa huci yake yi musamman malam da ya zuwa yanzu duk wata martaba da Maryam ta samu a gurbin zuciyarsa ta goge,dan haka ya kalli su baban Maryam har da zabga musu harara a fakaice sannan ya ce" Da farko dai ba sai na ce komai ba game da wannan yarinyar, dan ku iyayenta kun fini sanin matsalarta sannan kuka yayibo ta kuka kawomin ni wato ga mai matattarar 'yan iska kangararru.Dan haka ina son kafin na yanke hukunci mai zafi a kanta inyi muku wata tambaya".

Baban Maryam ne ya samu zarafin cewa
" Allah gafarta malam ai mana afuwa dan Allah,dan wallahi zaman yarinyar nan a nan ya fi mana kwanciyar hankali,domin mu mun ga ci gaba a zaman nata".

Malam ne ya ƙara muskuta zamansa sannan ya ce
" tabbas kam an samu ci gaba da lalacewar ta ba,domin yarinyar nan tunda ta zo ban taɓa ganin ta yi wani abun arziƙi ba,kullum da kalar bala'in da za ta jawo".

"To amma Abban Maryam ba kai kace min malam ɗin ya faɗa maka an samu ci gaba ba Maryam ta nutsu?" cewar maman Maryam.

"Tabbas haka ya kirani ya faɗamin".

"To inaga lokacin aljanuna maƙaryata sun hau kaina,dan haka nake wani zubin in suka zo yini nake bana cikin hayyacina,amma yanzu abu mafi sauƙi shi ne,ku tattara ta ku tafi da ita gida,nayi muku alƙawari daga nan zan dinga jifanta da addu'a, dan ita bata faɗuwa ƙasa banza,kuma ko ina akwai Allah".

Maryam da daɗi ya kasheta ta ce" Baba malam Allah Ya yi maka albarka idan na tafi zan yi kewar ku wallahi,amma zan dinga mafarkin ku".

Da sauri zuwai dake zaune ta kasa cewa komai tun ɗazu saboda aikin susa da take yi ta ce" Bama sai kinyi mafarkin mu ba, mu ma dinga yin naki".

"Ai ba ma wanda zai dinga yin mafarkin wani a tsakaninmu,sai kace wasu mayu,kunga ku tashi kai Garba kar dare yayi muku a hanya" cewar malam.

Laraba dake zaune jikinta a sanyaye tace"to amma yallaɓai inta tafi ni kuma da wa zan dinga hira kuma wazai dinga bani shawara?"

Dariya zuwai ta sa tana faɗin" abin dariya wai yaro ya tsinci haƙori,sai ki koma saida ɗanta malele ko zaki kuma samun wata sha-sha-shar irinki"

"Ni kike cewa sha-sha-sha?"

"Ke ɗin mana ,ko da wata ne bayan ke". Zuwaira ta faɗa cike da masifa

A harzuƙe kuwa Laraba ta hunƙura,ba tare da tunani ko tsammani ba zuwai taji an fyaɗe ta da kasa ai kuwa ta hau ihu,domin zauneta kawai Laraba ta yi ta fara murzar ta".

Malam dai ya san ƙarfi bazai kwaci zuwai ba,kawai sai ya kama roƙon Laraba amma ta ƙi ji.Ganin haka yasa Maryam matsowa ta ce" Allah Anty idan baki ɗaga ta ba zansa Baba malam ya sake ki".Da sauri suka ga Laraba ta zame daga kan zuwai.

Kowa da kallo ya bita,yayin da malam a ƙufule yace"ka ga irin tsiyar tata ko? Matata ma ita ke iko da ita bani ba tunda ita ce ta haifeni za ta sa na sake ta,to tun kafin ma lokaci ya ƙure ku tashi ku tafi,ke kuma in ta tafi kada ki sake jin maganata kiga idan ban sake ki ɗin ba da gaske".

Maryam kam bata ƙara bi takan kowa ba taje ta ɗauko jakarta tana faɗin"Baba zuwai sannu ki gasa jikinki sosai.Anty Laraba ni tafiya zanyi sai mun kuma zuwa,ina addu'a Allah yasa ki haifi 'yar kululluɓar yarinya me kama dake,itama ta dinga ɗirkar mutane".

Ba irin haƙurin da baban Maryam bai bawa malam ba,amma ya ce bai san zance ba sai an tafi da maryam.Haka suka fito da ita da kayanta,yayinda mutan gidan dake nan duk suka rakosu bakin mota.Ɗalibai irin su maryam kuwa duk sunji ba daɗi da wannan tafiyar ta Maryam ,Laraba ko kuka ta kama yi amma ita Maryam ko a jikinta suka shige mota ita da Isma'il da mamanta,wadda take jin kamar ta kama Maryam ta yi ta ɗirka.

*************************

Suna gab da fita gari suka ga tawagar mai gari buguzun -buguzun sun nufi hanyar gidan malam.Su dai basu juyo ba suka ɗauki hanyar Kano.

Sun shigo Kano da yamma baban Maryam ya ce da malam Garba ya ɗan tsaya zai siye wani abu,aikuwa ba jima da fita ba sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da zabgegiyar dorina mai baki biyu.Ita kanta Umma ta yi mamaki amma ganin fuskar nan tashi a haɗe ta tabbatar ransa ɓace yake.Su ma kansu su Maryam da Isma'il sun tsorata da ganin wannan bulalar ,amma haka dai kowa ya haɗiye ƙin jinshi har suka isa gida,yayin da Baban Maryam ya shiga yiwa malam Garba godiya nan suka shiga gida.

Ba ƙaramin farin ciki Maryam ta shiga ba ganinta a gida,ai kuwa da sauri ta shige ɗakinsu da umma ta buɗe yanzu.Sai da ta sha birgimar ta akan katifarta sannan ta tashi taje kiran da ummanta ke mata.

Yau kam umma an nutsu,domin nasiha ta shiga yiwa Maryam da ta nutsu ta daina rashin ji, aikuwa Maryam ta zama kamar mumina,yayinda take ta Allah-Allah umma ta gama ta je ta kama ummita ta yi mata dukan da ta yi alƙawarin za ta yi mata.

********

Sam ba ta samu sami hanyar fita ba sai bayan magariba da babanta ya fita Masallaci daga can zai wuce gurin sana'arshi,sai mamanta kuma ta shiga sallar magariba.

Ko da ta shiga ɗakin umma ta iske ba ta ciki ashe tana kicin,aikuwa idonta ya sauka kan bulalar da babanta ya siyo nan ta sureta ta fito a guje.Umma ba ta lura da ita ba sai Isma'il,shima hanya yake nema ya gudu dan kar ya je makarantar dare shiyasa bai tona asiri ba.

******

Direct gidansu ummita ta nufa.Cikin sa'a har ta shiga ba ta gamu da kowa ba.A tsugunne take da hijabi a jikinta tana ɗibar ruwa a randa tana zubawa a buta.Sai da ta daddage iya ƙarfinta ta shimfiɗa mata bulalar.

Da sauri ta ɗago tare da furta "wayyo Allahna! dan azabar saukar bulalar da ta ji,ta waigo dan ganin waye ya yi mata wannan aika-aikar. Aikuwa suka yi ido huɗu da maryam,ita ma Maryam ɗin waro ido ta yi dan ganin wadda ta daka wato Rakiya.......🙄

*Alƙalamin khady*✍
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*'YAR CASKALE*
( _Sanadin bakin uwa_ )



*Na*
*KHADIJA USMAN*


6⃣1⃣-6⃣2⃣
*__________________________________*



*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan na kasa_*

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*


Ganin Maryam tsaye yasa Rakiya faɗin"kam bala'i,yau ga naman danake jira ya kawo kanshi har gida,na rantse da Allah yau bamai kwatar ki a gidan nan wato annoba ta dawo ko? " Hahaha! Rakiya ta saki dariyar mugunta,bayan ta shafo inda Maryam ta zarkwaɗa mata bulalar taji kamar ma gurin ya ɗaye.
Itako Maryam ba ƙaramin tsorata tayi ba,dan harga Allah ko da ta saba da duka da kuma tsokana, to abin nata bai kai ta daki manya ba,dan haka cikin karayar murya tace" dan Allah Baba Rakiya kiyi haƙuri, wallahi ba ke nayi niyyar duka ba,ummita nayi niyyar zanewa dan nayi alƙawarin dukan ta duk lokacin da muka haɗu,da naga hijabin jikinki na ɗauka itace,ban san cewa anko kukayi ba".

"Ai kinga maryam,idan zaki dinga gwagwiyar dutse kina ɓantara kina ban haƙuri wallahi bazan haƙura ba.Marabin da a dakeni yarinya tun ina rigimar yaye,sai gashi yau da 'ya'yana zagada-zagada kin shaulamin tsumagiya,to wallahi yau kisa a ranki mai ƙwatarki ko cikin uwarsa ba'ayi ba bare asa ran haihuwarsa".

Maryam na shirin magana baban ummita ya shigo yana gyaran murya"Assalamu alaikum.wai duk ina yaran suke ne aka bar gidan kaca-kaca,kullum ina faɗan wannan ƙazantar taku amma kunƙi ragewa bare insa ran zaku daina,ke Asiya ce nan ko ummita? Maza kawar da turmin can gefe dan Allah".

"Ai malam ba Asiya bace ba ummita bace, yarinyar nan ce tamba ɗaɗɗiya wadda muke nema ruwa a jallo,itace ta shigo dan tsabar tsaurin ido wai zata zane ummita shine ni tahau lodata kamar ta sami 'yar ta".

Haska fitilar hannunshi yayi da kyau,aikuwa yayi ido huɗu da maryam shima.Jikinsa har rawa yakeyi dan tuna abinda yarinyar tayi musu,wanda silar hakan har sai da suka kai ƙara gun me unguwa sannan suka sami salama ga tsokanar da mutane ke musu,dan ko sararin fita basu da shi.Dan haka batare daya ce ƙala ba ya nufi ƙofa dan ya rufe,nan yayi kaciɓis da duka yaran nashi zasu shigo kamar sun san abinda ke faruwa.
Sai da suka gama shigewa kafin ya mayar da ƙofar ya rufe,domin dukansu basu san abinda ke faruwa ba.Shiyasa ganin babansu na rufe ƙofa sun ɗauka halin ne ya motsa,dan haka ba wanda yayi yunƙurin cewa wani abu dan sun san hali.Ganin Maryam da sukayi tsugunne gaban mahaifiyar su dan an kawo wuta haske ta ko ina yasa Asiya faɗin"wa nake gani kamar Maryam ɗin Huwaila?"
Cikin sanyi ta furta "Ni ce Anty Asiya".

"Bala'i,wato yau ni ɗin ce Anty? Lallai ma yarinya,har kinyi laushi tun baki karɓi hukunci ba, Inna ko kin fara azabtar da ita ne?"

"A'a ni ban taɓata ba,dama ku nake jira kowa yazo ya fanshe haushin shi na tsawon lokaci,ku ɗaukar mana fansar abinda tayi mana".

Jamilu babban ɗan gidan Rakiya yace"Ni dai abinda nake so in mata shine:A samomin manyan ƙusoshi da guduma zan buga su a jikinta shikenan".

Caraf Raliya mai bi masa tace,Ni kuma bayan ka buga ƙusar zan bi in zazzaro su sai in buga mata allurai sannan nasami adda na sassare kan alluran tsinin kuma na jikinta".

Asiya ce ta gyara tsayuwar ta itama tace" a'a Anty da yaya,ku bari saina feɗe fatar ta tukun tsokar ta bayyana in samu cokali nasa a wuta inbi naita ɗona mata a sassan jikinta".

"Ummita ce tace bayan duk kunyi wannan ni kuma inta cizonta har sai ta suma ta farfaɗo".

Rakiya ce tace yauwa 'ya'yan albarka,ni kuma bayan duk kun kammala waɗannan abubuwan,sai in samo buhun ƙanƙara a ɗebe rabin ƙarnƙarar sai a sata a tsaƙiya a loda mata ƙanƙarar a samanta shikenan".

"Ni kuma zan ɗauketa na kai ta bayan gari na jefar a bola kunga mun fanshe haushinmu".cewar baban su ummita.

Tunda suka fara ambato nau'ikan azabobin da zasuyi mata ta yankewa kanta shawarar mutuwa tun kafin su kashe ta,dan iya tsurewa ta tsure.

Rakiya ce ta nufota tana faɗin" dan ubanki taso jamilu yafara nasa aikin amma sai me? Ga dai Maryam riƙe da bulala amma shuru kake ji bata ko motsi,a ɗan razane Rakiya ta kamo hannunta sai ta jishi a sake,dan haka cikin alamun tsoro ta juyo ta kalli sauran dake tsaye tace" malam ina ganin fa kamar yarinyar nan ta mutu fa".

Zaro idanu duka sukayi kafin baban ummita yace"ta mutu kamar yaya ? Ya faɗa yana me ƙarasowa inda Maryam ɗin ke kwance.Hannunsa yasa saitin hancinta yaji babu alamun iskar numfashi dan haka a kiɗime yaja baya yana faɗin"shikenan Rakiya kun kashe 'yar mutane,dama ni tun shigowa ta na lura yarinyar bata numfashi ban dai faɗa bane sai yanzu dana tabbatar,dan haka kun jawa kanku masifa ni wallahi ba ruwana" ya faɗa yana me ja da baya.

"Ah ah malam,wallahi sai dai ko in tsorata tayi zuciyarta ta buga lokaci ɗaya to amma ai bamu ji ƙarar fashewar komai ba,kuma ma ai lokacin daka shigo da ranta da lafiyarta malam kada ka jaza mana laifi mu kaɗai,kawai asan abin yi tunda imu-imune".

"Ke Raliya maza kinga goyata kiga yadda za'ai".
A firgice ko Raliya ta juya baya aka kima mata Maryam sannan Rakiya da sauri ta ɗauko zani aka tare kanta dake reto."maza sa hijabinki ku Kaita soron gidansu ku ajiyeta,dan gidan su babu yawan shige da fice maza kuje Allah ya rufa mana asiri".

"Inna to ya za'ayi da azumin da akeyi idan an kashe mutum?" Cewar ummita.

"Ke rabu da ni,ai rabawa za'ai kowa yayi nasa kuje dai ke Asiya ki raka Raliya".

Ko nauyin Maryam Raliya bataji ba haka suka buɗe gidan suka fita, kasancewar an shiga sallar isha'i yasa ba wasu mutane a wajen har suka ƙarasa ƙofar gidan su Maryam.

Sai da suka tabbatar babu wanda ya lura dasu sannan suka shiga zauren,da sauri suka kamata suka sauke tare da kwantar da ita,wanda har yanzu bulalar na hannunta suka juya suka fice da sauri.

Suna ficewa Maryam ta buɗe idonta dan tabbatar da ta kuɓuta,ganinta a zauren gidansu yasa ta miƙe ta shige gida.wannan karon ma bata sami umma a tsakar gida ba,dan haka ta shige ɗakinsu ta kwanta tayi luf tana tunano irin azabar dataji su Rakiya na faɗin zasuyi mata,lallai mutanen nan basu da imani,kenan da ta mutu da gaske haka zasuyi mata,aikuwa saita san yadda tayi ta koya musu hankali.

Tana nan kwance taji umma na kwala mata kira,alamun tunda ta fita umma bata nemeta ba kenan,hakan yasa taji wani sanyin daɗi na ziyar tar ta.

Haka ta tashi ta fita,umma tace tazo ta ɗauki abinci taci(kuskure na biyu damu iyaye mata kiyi,yakamata ace mahaifiyar Maryam ta nemeta tun ɗazu danta gabatar da Sallah kasancewar takai munzalin da in batayi ba za'a iya dukanta,amma kunji ta abinci ma takeyi).haka ta fito taci ta ƙoshi tana ta tuna abinda zatayiwa

Please Login or Register in order to submit comment