Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar ta a dakin zuciyar kowannen su na tafasa, ya nufi dakin Nusy ganin har zuwa lokacin Hasna bata fito ba.
Ya duba cikin dakin bai gan ta ba, ya karasa kofar toilet din yana kwankwasawa, shiru ka ke ji, babu Hasna’u babu alamar ta.
Da sauri ya fito waje yana tambayar mai aikin su Tani dake shanya ko ta ga wata farar yarinya da uniform? Tace ta fice tun dazu. Da sassarfa ya karasa wajen maigadi yana tambayar sa mintuna nawa da fitar yarinyar? Maigadi yace tafi minti biyar da ficewa.

Sai ya koma ya fada mota ya kunna yayi reverse ya durfafi get da mugun gudu, tuni maigadi ya wangale get din don bai taba ganin Saheeb cikin gaggawa haka ba tunda aka haife shi. Domin kuwa a kan idon sa aka haife shi a gidan.
Tafiya yake a gefen titi yana mamakin meyasa Hasna’u zata yi masa haka? Daga ki yi sallah ki fito? Sai ki kama hanya alhalin baki san kowa ba cikin gari irin Kano? Ba mamaki bacin ran abinda Nusaiba ta yi mata ne yasa ta ga gara tayi tafiyar ta.
Gumi ya shiga barko masa da ya tuna ya karbo amanarta ne wajen Kawun ta, in bai ganta ba me zai ce masa? Ko daure shi aka yi bashi da hujjar kare kan sa, tunda har principal ta san suna tare.
Bai kai karshen fita daga layin su ba ya hange ta tana tafiya a gefen titi tana ta zuba sauri kamar zata tashi sama, yayi maza ya sha gaban ta da motar ya sauke glass daga ciki yace.
“Hasna’u”.
Yadda ya kira sunan ta da rauni, sai zuciyar ta ta idasa karyewa, dama idon ta jike yake da hawaye.
“In kin yarda ni Yayan ki ne Saheeb kuma bazan cutar da ke ba, taimakamin ki shigo motar nan in maidawa Kawu Sama’ila amanar sa dana dauko, daga nan ki yanke hukuncin duk da kike so akan alaqar mu, ni dai ta fanni na ba gudu ba ja da baya wajen zamowa bango abin jinginar Hasna’u, kiyi hakuri ko me ya faru ni na jawo miki, saida ki ka ce min bazaki je ba sabida gudun hakan, ni kuma ba don komai na takura kije ba sai don ina so ki saba da karbar kalubale kowanne iri daga mutane mai dadi ne ko mara dadi? Rayuwa bata taba yiwuwa without challenges from people koda kuwa a ce ke kika fi kowa kyau a duniya sai an samu wanda zai ce kyan nan naki ba alkhairi bane, shaidan zaki zamewa mijin ki.
I want you to Open your heart and mind and learn how to accept critcsm no matter how bitter, shigo mu tafi kin ji Hasna’u?”.
Idan ta ce zuciyar ta bata ragargaje da dadin kalaman sa ba ta yi karya, haka idan tace bata yarda da duk abinda yace ba ta cika butulu. Amma abinda bai sani ba shine ba abinda Nusaiba ta yi mata ne yasa ta barin gidan su ba wutsiya a zage ba tare da ta jira shi ba, sai don tana so ta kawo karshen wannan alaqar, alaqar da ta fara lura bazata haifar mata da Da mai ido ba kuma karshen ta nadama zai zama.
“Ki nemo majanyi da zanin goyo kifara shirin goya ALBINOS domin wannan zabiyar itace uwar ‘ya’ya na, Insha Allahu”.
Wadannan sune kalaman da suka fiddo ta daga gidan Wamakko helter-skelter, ba tareda second thought ba. Domin bai yi kalaman da sigar da za’a ce wasa yake ba, haka intonation na muryarsa a lokacin da yake furta su kaifin sa yafi na takobi, domin maganar ta fito ne kai tsaye daga karkashin zuciyar sa ba tareda shi kansa ya san ya yi ba.
Amma a maganar sa ta yanzu yace zai bata zabi akan alaqar su, fatan sa kawai tayi masa alfarma ya maida amanar da ya dauko. In har zaya bata wannan damar, to yau ce rana ta karshe da alaqar tasu zata kare. Allah ya kai su gida lafiya.
Da kansa ya fito ya bude mata kofa ta shiga, ya maida ya rufe silently sannan ya koma nasa mazaunin. A yadda yake tukin motar tamkar tayoyin ta sun yi faci, kuma a gefen titi don ma kada ya sha zagi daga motocin gaban sa da bayan sa.
Ji yake kamar kada ya maida ita wannan gidan nasu da ba abinda zata fuskanta a cikin sa sai wahala, tunda babu sanyin idaniyar ta Inna, to in bai kaita nasu gidan ba wanne zai kai ta? Ko dai kawai ya gudu da ita ne ya nema mata shelter? Anya in yayi hakan Kawu Sama’ila zai taba yafe masa? Ya yarda da shi ya amince masa bari ya tabbatar da wannan yardar, ya tabbatar masa har yanzu cikin ‘yan adam akwai masu amana.
Sai da suka hau babban titi dodar ya tuna bata son A|C sai ya kashe, ya kunna mata sautin Khusairi cikin Suratul-Al-Imran. Kamar ya san surar da take matukar so kenan kuma a ita suke a islamiyyar su ta cikin UNITY wato daga ita sai Baqarah sai saukar su, wanda zai zo daidai da kammala SSCE din su.

Sai ta hau bin karatun a zuciyar ta wata irin nutsuwa na shigar ta, tsoron Allah na kara samun gurbi a ran ta. Ta ji dama su dawwama suna wannan tafiyar ita da Saheeb, watakila daga yau bazata kara ganin sa ba, don ta riga ta yankewa kanta kawo karshen alaqar su, kada tausayi da jin kai irin nasa su sa ya saki layi ya hau kan turbar wanda su duka ba zai bulle dasu ba.
Suka tsaya a Wudil ya je ya sayo mata soyayyen kifi ragon ruwa da ruwan sha, daga shi har ita an rasa mai Magana, zukata kadai ke kiyasi, kowanne kuma da abinda yake kiyastawa daban da na dan uwan sa. Ita tana tunanin hanyar kawo karshen alaqa, Saheeb yana tunanin hanya mafi dacewa ta maida alaqa infinite. Sai a lokacin da ya ajiye mata kifin ne ta ji kamshin sa ta dan motsa kadan tace .
“Bana cin kifi, inada allergy da cin kifi”.
Ya dube ta a hankali da lumsassun idanun sa yace.
“Dama shi yasa na so tafiyar nan, don in san likes and dislikes din ki, and I know a lot in one day, ga tsoro kamar farar kura”.
Murmushi ta dan yi ta juya kan ta ga taga, bata ce komai ba.
Ya cigaba da tuki har suka kusa albasu, lokacin shidda na yamma ta yi, ya tsaya a garin albasu ya saya mata lemun La-Casera mai sanyi guda biyu sannan ya shiga wani shago ya dinga sayayya.

Sabulun wanka dana wanki, omo, maclean, brush, deospray, hypo, Dettol soap, Vaseline da sababbin panties, always pad, indomie, kayan tea da kuma slippers ya sayo cikin katuwar bagi ya zo yasa a kujerar baya.
Ya je ya bi jam’in sallahr magriba a kofar shagon sannan ya zo ya tadda Hasna’u ya tada motar.
“I’m sorry for keeping you waiting Yayan naki akwai kailula”
“Sallah fa ka yi, to ai dole in jira ka don Inna ta ce it ace sama da komai”. Saheeb ya juyar da kai kamar bai ji ta ba, zuciyar san a kokawa da hawayen idon sa.
Daga nan basu kara Magana ba har suka shiga Kachako, kawai ta ga yana daukar hanya babu tambaya domin tuni ya rike gidan Kawu Samaila.
Kugin karshe da motar ta yi a kofar gidan Kawu Samaila ne. Ga yara suna ta wasan dare an kunna aci bal-bal wasu kuma na gefe suna sayar da soyayyar gyada marau-marau. Hasken motar yasa duk suka dare suna ihu. Duhun dare da ya shigo yasa basu san su waye a cikin motar ba don Saheeb ya kasha fitilar.
Ta juya da zummar yi masa godiya ta fita sai ta hango idanun sa cikin hasken farin wata suna wani irin sheki da maiko kamar na hawaye amma dai basu gangaro kan kundukin sa ba. Tace.

“Yaya Saheeb bani da bakin gode maka, sai dai in ce Allah ya yi maka sakayya da aljannah madaukakiya ya ji kan ka kamar yadda ka ji kai na. Allah ya shige maka gaba a kan dukkan al’amuran ka ya baka duka binda kake nema a rayuwar duniya”.
Ta murda handle din kofar da zummar ficewa, amm sai ta ji shi gadagau (a kulle). Ta juyo tana duban sa da idanun bidar dalili? Sai y langabar da kai yace mata.
“Abu daya nake nema yanzu a rayuwa ta, ki taya ni rokon Allah to make it easy for me wurin mallakar sa, ta ko’ina na juya na hanga na hango it is not easy, duk da haka ban fidda rai ba kuma ban ja da baya ba, sannan gaba na bai fadi ba. Tunda Allah ya ce “La taqnadou min rahmatullah…”.
Hasna’u tayi murshi, he’s always bold, kuma dama ita ta tsani ragwan ta, tana son mutum mai yarda da kan sa da jajircewa bisa ra’ayin sa.
“Idan alkhairi ne a gare ka Allah ya baka, idan ba alkhairi bane Allah ya musanya maka da mafi alkhairi sa. Ka dinga sanya tagociya a addu’ar ka sabida ba duka abinda muke so bane yake zame mana alkhairi ba”.
Ta sake kokarin bude mota amma ko gezau. Da ta juya saida tayi nadamar juyawar a karo na biyu.

His eyes are sparkling tamkar hasken wata dan daren goma sha hudu. A cikin su wani yanayi ne mai wuyar fassarawa wanda bata taba gani cikin kwayar idon kowa ba.
Muryar ta na dan rawa tace “ka bude min in fita Yaya Saheeb, nan kauye ne, bai kamata muyi ta zama cikin mota ba”.
Da wata irin murya kasa-kasa yace.
“Idan kuma na fito na tsaya a zaure a ce na zo zance ko?”
“ZANCE?”
Hasna’u ta maimaita Kalmar cikin sigar tambaya don kuwa da gaske bata gane mata ba.
“Eh mana, idan na fito zauren ku muka tsaya muna Magana ya zama zance irin na saurayi da budurwa”.
Da sauri Hasna’u ta lullube fuskar ta da hijabin ta tana fadin ‘’ka bude min kofa Yaya Saheeb”. “An ki a bude, sai kin gaya min sunan saurayin ki?” “Ya ilahi!” Hasna’u ta fada a fili amma ta kasa sauke mayafin da ta rufe ido da shi, shi kuma yace bai bude kofa sai ta gaya masa sunan saurayin ta.
Da ta ga lokaci yana ta ja, sannan yaran gidan su sun fara taruwa suna shafa motar sai tace masa a hankali kamar cikin rada.

“Banda abun ka waye zai so zabiya ne? Ni fa ka san Allah ban taba yin Magana da wani namiji ba bayan malamai na a class ko staff room. This is out of my vocab-bank (vocabulary Bank)”.
“And it must be included in your vocabulary bank, because at this stage da kike ciki na gab da kamala makaranta its either ki zabi miji ki gabatarwa Kawu, ko ya aura miki duk wanda ya ga dama”.
Hasna’u a ran ta tace “ashe kuwa zamu shata babban layi ni da Kawun, nan kusa ban ga ranar aure na ba, daga ni har Inna karatu muke so na yi”.
Murmushi Saheeb yayi, domin shi mutum ne mai karfin ji, abinda take zaton a zuciyar ta ta fada ya gama shigewa kunnen sa. Ya kuma gamsu da abinda tace din na bazata bari a yi mata aure yanzu ba, kafin nan zai tunanin mafita ga rayuwar su, koda kuwa hakan na nufin….
Ya dauke ta ne ya gudu da ita inda basu da kowa a daura musu aure. Idan Mama ta ki.
“Ka yi wa Allah Yaya Saheeb ka bude min kofa in fita”.
Ta fada kamar zata yi kuka.
“Sai na gama kallon mata ta!”.

Hasna’u bata san lokacin da ta bude light blue eyes din ta tana kallon shi ba, kallon mamaki da tsoro, hadi da firgici.
Wadannan sune kalaman da har abada bazata manta ba, domin sune mabudin littafin kaddarorin ta masu dadi da marassa dadi. Sune kuma suka maida zarar bunu…. ta zama babbar maganar da ta kai ta har matakin da take kai a yanzu.
Ya lura da irin kallon da ta ke yi masa na firgici da tsoro, sai ya lumshe mata lumsassun idanun sa tare da daga girar sa guda daya. Ya saki lock din motar ya fita ya zagaya ya bude mata, amma sai ta kasa fitowa tamkar an sa glue an manne ta a kujerar.
Bai takura mata ba, ya koma booth yana sauke kayan ta yana baiwa yaran suna shiga dasu gida. Suna ta ihu “ga zabiya ga zabiya ta dawo”.
Wani bakin ciki yazo ya tokare Saheeb a kahon zucci. Why not al’umma bazasu kira mai nakasa da sunan yankan sa ba? Sai dai a kira shi da inkiyar sunan nakasar sa?”
Suna gama shiga da kayan sai ga Kawu Sama’ila ya fito da sauri da far’a yana “maraba lale da mutanen Kano, ya bashi hannu amma Saheeb sai ya tsugunna akan gwiwowyin sa bai bashi hannun ba yana gaishe shi with due respect.
“Ayi hakuri kawu mun yi dare, hakan ya faru ne a bisa layin ganin likita” Kawu yace “babu komai Sahabi, ai na san yadda ake ganin likita a Kano, kwanaki da ido ya matsa min ai can naje, Murtala, kada ka so ka ga wahalar da na sha sai I yanzu na dawo gida”.
Ya maida duban sa ga Hasna’u tana fitowa daga mota jiki a mace kmar wadda ta sha duka. Ya ce “ka gaya mata ne?” Da sauri Saheeb ya girgiza kai “a’ah Kawu, gara kai ka gaya mata da kan ka” “to babu laifi ka je, Allah ya kiyaye hanya nagode Allah yayi maka albarka. An yi gilashin?” “Eh an yi, ji bi zan karbo in kawo maka, insha Allah”.
Babbabn abinda yake burgeshi da yaron kenan, komai zai ce sai ya hada ta da Kalmar “insha Allahu”.
Daidai lokacin da Hasna’u ta karaso tana gaida Kawu, ya dube ta da tausayawa yace “shiga gida gani nan, kicewa Hajjo ta baki abincin ki”.
“Ai ya saya min abinci na ci Kawu, Sallah dai zan yi in kwanta in huta” Kawu y ace “to maza ‘yar albarka, shi din kun yi sallama ne?” Hasna tayi maza ta shige gida bata tankawa Kawu ba. Ya yi murmushi yace “ai Hasna’u bata son Magana Kawu, in ma nayi mata sai ta ga dama take tanka ni” Kawu yace “haka take fa, uwarta ma Allah ya jikan rai haka take, sai su wuni basu kula kowa cikin gidan nan shiyasa sam basu da abokin fada, basu da abin yi sai sana’ar sayar da abinci da surfen su”.
“Kawu a gaya mata ta lallashi, ta kyakkyawar siga, a nuna mata dukkan mu na haka ne Inna bata yi gaggawa ba muma duk jiran tamu muke”.
Kawu yace “je ka kada kayi dare da yawa, na san yadda zan bi da ita, gashi ba iya kwanan zaure zaka yi ba da ka kwana dakin su Hassan in ya so da sassafe ka tafi”.
Murmushi yayi ya juya yan fadin “ba kwanan ne bazan iya a nan ba, watarana zan zo na kwanan, yanzun ina kan uzuri Kawu”. Kawu ya ji dadin abinda yace masa yayi ta saka masa albarka.
Kawu Samaila bai koma gida ba sai da Saheeb ya ja motar sa ‘kia-picanto’ a hankali ya bar harabar gidan sa.
Sannan ya juya ya nufi gida, zuciyar sa cike da kaunar yaron da kuma alhinin abinda zai gayawa Hasna’u.
******




MUTUWA MAI TONON ASIRI..... (WANDA YA RASA UWA SHI KE DA KUKA).
Hasna’u na shiga gida kai tsaye bangaren su ta nufa da sassarfar ta, Hajjo matar Kawu na zaune kofar dakin ta tana kallon ta ta shige bata ce mata komai ba, kayan ta da aka shigo da su duk Hajjo ta sa an tule mata a kofar dakin Innar ta. Don ma kada a fara cewa a dakin ta zata zauna.
Tun daga kofar sassan take kwada sallama tana fadin.
“Inna kina kusa? Inna gani na dawo!”
Ta sa kai a rumfar, duhu dudum, ya bakunci idanun ta, Inna bata kunna aci-bal-bal da ta saba kunnawa ba, ko mai yasa?.
“Inna lafiya kike zaune cikin duhu haka? Wai kina ina ne ko gyaran murya bazaki min ba in sallah kike yi?”
Ta fada tana lalube a cikin dakin. Sai ta jiyo gyaran muryar Kawu daga bayan ta, yana haska tocilan yana tahowa. Yace “Hansai dakko kayan ki ki biyo ni” cikin damuwa tace “Kawu ina Inna ne? Ko bayi ta zaga?” Kawu yayi gaba bai kula ta ba, sai ta bishi da gudu-gudu cikin alamu na fara shiga rudu, har ta riga shi shiga dakin nasa. Saura kadan ta bangaje shi.
Ya zauna yana haska 'light blue eyes' din ta wadanda sai sheki suke yi kamar idon mussa (mage) yace. “Zauna Hansai ki bani hankalin ki kin ji? Hakika Ubangiji baya dorawa rai abinda ya san bazata iya dauka ba. Ya san ZAKI IYA! Shi yasa ya dora miki”.

Hasna’u ta fiddo iyakacin 'yan kananun idanun ta da iyakacin girman su tana kallon Kawu Sama’ila. Ya cigaba dacewa “Kullu nafsin za’ikatul maut, daga ni har ke bamu tsira ba, jiran ta muke yanzu ne? Gobe ne? Anjima ne? Tana tafe bazamu taba iya guje mata ba sai fa in lokaci bai buga ba”.
Hasna’u dai kallon sa take tana jiran ta ji karshen wannan wa’azi da bata ga dalilin sa ba. Daga tambayar sa ina Inna? Kawu yacigaba da jawo aya da hadisi yana fassarawa akan muhimmancin yarda da hukuncin Ubangiji mai dadi ko mara dadi wajibi ne ga dukkan musulmi. Wanda ya yarda Allah shine mai bayarwa kuma mai karba a duk sanda ya so. Ya kasa fitowa fili ya fadi maganar dake kunshe a bakin sa, sai dawurwura yake, a ran sa yana fadin "da na sani na shigo tare da Sahabi, na ga ya fini kaifin harshe", ita kuma bata katse hanzarin sa ba sai da ya rasa sauran hadisin fade sannan ya nisa….

Ya ce “Hansai Zulai ta sha jinya ta wata biyu, masassara ta kwantar da ita, ba irin maganin da ban sayo mata ba, an yi jike-jike har ba adadi a karshe na kaita asibiti a birni.
Kwanan mu biyu da dawowa daga asibiti jikin ya dan yi kyau, kuma likita ya ce tayifot ce ta kama mata hanji, an dora ta akan gwaje-gwajen da suka dace, kafin akai ga yi, da safe na shiga don in kai mata koko, sai gani na yi rai ya yi halin sa…”.
Hasna’u ta runtse idanun ta kafin ta ce.
“Kawu menene rai yayi halin sa?”
Yace “halin sa na bakon kan hanya mana! Ya tafi inda aka turo shi, ta rasu!”
Zai cigaba da wa’azi sai gani yayi Hasna’u ta mike ta fita da gudun gaske, dakin su ta koma tana lalube tana kiran sunan Inna! Da iyakacin muryar ta. Da iyakcin makogaron ta. Wanda hakan ya janyo hankalin al’ummar gidan duka aka taho sassan. Kawu ya zo ya kamata ganin tana buga kanta da bango har goshin ta ya fashe. Yace “Hansai kice “Innalillahi wainna ilaihi rajioun…. Kada Allah yayi fushi da ke”. Ina! Hasna bata ji me yake cewa ba, jinni ke fita daga goshin ta a lokacin. Duk da cewa fatar zabiya tana da karfi amma ta buga kan sosai da bango hoping itama Allah ya dauki ranta kafin abinda Kawu ke fada ya zama tabbatacce. Kawu ya rike ta tamau yana ta ambata mata.
“Ina lillahi wainna ilaihi rajioun…. " Bai gushe yana yi ba sai da ya ji ta kama. Kuma bai saketa ba, sai da ta sulale da kanta ta yi kasa.

Koda ya duba sai gane bata numfashi, Hajjo tace "Hassan maza kawo ruwa kada ‘yar ma ta mace mu shiga uku” Hassan yace “Hajjo don Allah ku bar ta ta karasa, kowa ya huta, in ta rayu me zata yi mana banda karawa Baba nauyi? A bar shi ya ji da mu, mu lafiyayyu da muka zame masa dole, ku barta tabi Uwar ta”. Kawu ya saki Hasna’u yayi kan Hassan da mugun duka Hassan ya gudu, Kawu ya fadi, sabida babbar rigar sa da ta tadiye shi, ya bugu sosai, Hajjo ta ce.
“Oh ni Hajjo! Duk akan zabiya zaka hallaka kan ka? To wallahi ‘ya’ya na basu shirya zama marayu ba, in ka mutu kuma ka san inda zaka kai zabiyar ka”.
Kawu bai san sanda ya fashe da kuka ba ya dawo kan Hasna’u yana dingishi. Atika ce ji tausayin Kawu ta kawo ruwa a kofi wato autar Hajjo ya hau shafa mata a fuska yana kiran sunan ta.
"Hansai, Hansai, Hansai diya ta!"

An dauki lokaci kafin Hasna’u ta yi ajiyar zuciya, shima Kawun yayi, ya kwance dankwalin dake kanta ya daure goshin ta. Daga nan ta mike zaune, sai kuma ta ja gefe ta sanya kai a tsakanin cinyoyin ta ta soma kuka….
Hakika kuka rahma ne ga dan adam a lokacin da zuciyar sa ba ta da sassauci. Hasna’u tayi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita, kuka irin wanda bata taba yi a rayuwar ta ba. Kukan sabo da kewa… kukan kauna da soyayya, kukan da ba zai dawo da UWA ba, balle UWA irin tata da ta sadaukar da rayuwar ta domin inganta tata. Hajjo da ‘ya’yan ta suka yi tafiyar su, amma Kawu akan Hasna’u ya kwana, don ya kasa tafiya ya bar ta cikin wannan mawuyacin halin, shima sai a lokacin mutuwar ‘yar uwar sa ta doke shi ta dawo masa sabuwa. Suka hadu su ka yi ta kuka shi da Hasna'u.
Bai fita ba saida aka kira sallahr asubahi, bayan ya zuba mata ruwa a buta, ya roke ta tayi sallah ta yi wa uwar ta addu’a. itace kadai tsakanin su yanzu.
Hasna’u tayi alwala ta tada sallah amma koda tayi sujjada bata iya addu’ar ba sai kuka. Kullum Inna ce ke tada ita sallah suyi tare. In ta tuna wai bazata sake ganin Inna ba ko yin Magana da ita sai taji zuciyar ta kamar zata fito ta bakin ta.

Koda gari ya waye ba wanda ya bi ta kanta a gidan. Kowa harkar gaban sa ya shiga yi yadda ya saba. Ko gaisuwa babu wanda yayi mata. Tana can takure akan gadon bonon Inna ta dauki zanin atamfar Innar ta lulluba ta rungume rigar ta, hawaye na bulbula. Hawayen da basa dawo da UWA a lokacin da DA ya rasa ta. Koda Kawu ya fito don tafiya kasuwa yace da Hajjo dake rabon dumame da koko.
“Hajjo in ce ko kin mikawa Hansai nata?”
Hajjo ta aje ludayin da take damun kokon da shi ta jefa masa harara ta ce “da can ni nake basu?” Yace “ai yanzu ba mai batan, dole duk abinda kika baiwa ‘ya’yan ki ki bata”.
Hajjo tace “tabdijam! Dole fa ka ce! Hakan kuwa ai ba mai yiwuwa bane tunda kuwa su talla suke da sayar da Rake su kawo min, ita ko ‘yar makaranta ce bazai yiwu ‘ya’ya na su sha rana su nemo abincin su in dauka in bata ba, sai dai in itama in dinga dafa mata Rogo tana kaiwa kasuwa kamar yadda Atika ke yi”.
Kawu ya ce “amma kin san Zabiya baya son rana ko? Uwar ta ko surfen data ke wuni yi kina gani bata bata ko sau daya ta ce ta taya ta ba, wane talla wannan halittar Allah zata iya yi miki?” Hajjo tayi mirsisi tace bata bada dumame saidai yaje ya sayo mata a waje.
Kawu yace “sai aka yi rashin sa'a sunana Samaila amma ba sauna bane, da za’a gindaya min yada zan yi da gida na, dole kullum kika dafa ki bata ko ni a cire min kwano a gidan a dinga bata nawa, ai nima ina fita in nemo in kawo to a bata wanda na kawo.
Hajjo tace nayi rantsuwa kuwa daga yau na cire ma kwano a gidan nan har sai ta koma inda ta fito”.
Duk abinda suke yi din nan a kunnen Hasna’u. yanzune ta tabbatar ta zama marainiya ta kowacce fuska amma a baya babu wanda ya kai ta gata. Yanzu ne ta tabbatar wanda ya rasa uwa shi ke da kuka kuma mutuwa TONON ASIRI GARETA.
Kawu ya shigo da kwanon dumamen yana kiran sunan ta “Hansai kin tashi?” Ta daga masa kai “ga nan dumame to ki ci” ta girgiza kai alamar bata ci. Yace “kada ki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment