Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dear, me ke damun ki?”
“Bana iya barci, zuciya ta tana min wani irin ciwo, ido na baya gani sosai, in dare yayi sai da lalube nake shiga bandaki”.
Daya daga cikin malaman mu yace "you need to see a doctor Hasna, if possible za’a kai ki babban asibiti ki ga ophthalmologist”.
“Kafin nan za’a kai ki clinic ki ga Dr. Saheeb ku tattauna shi zai san likitan da ya dace ki gani, da asibitin da ya dace a kai ki a yi miki glasses”.
“SAHEEB! SAHEEB! A ina na taba jin wannan sunan???
“Haba shiyasa naga tana copying note ba daidai ba” inji Malam Lawal.
“Short-sightedness is part of their defect ai, da wuya ka ga zabiyan da ke da cikakken gani” inji Uncle Salisu.
Mr. Samson wanda malamin bautar kasa ne kuma kabila amma mai kirkin gaske da kula da daliban sa, shi ya sa ni a gaba ya kai ni har clinic din makaranta da kan sa.
Dan asibitin namu karami ne wanda yafi dacewa a kira shi dispensary. Su biyu kacal ke aiki a cikin sa shi da Nurse Saratu, sai kuma cleaner mai tsabtace asibitin.
Lokacin da muka shiga rubutu yake a cikin wata folder, nurse din kuma tana sakawa wata student karin ruwa, da alama ita ya gama dubawa.
Ko da Samson yayi masa sallama alamar ya zauna yayi masa da biron hannun sa ba tare da ya dago don ganin masu shigowa ba. Sai da ya gama rubutun sa tsaf, sannan ya dago ya dube mu.
Wasu irin idanuwa gare shi masu sheki da haske (sparkle) da suka sa na kasa dauke ido a kan sa ba tare da na san kallon sa nake ba. Ina jin Mr. Samson yana gaya masa matsaloli na tare da cewa “ina jin tausayin zabiyar nan, don Allah Saheeb ka duba ta sosai”.
Dago kan sa da kallo na da yayi da sparkling eyes din sa, da kuma kallon haushin da ya watsawa Mr. Samson saida suka sa na kusa narkewa a kujerar gaban sa da na ke zaune sabida tsoron idanun sa masu matukar kwarjini.
“Ita ta ce ma ita abun tausayi ce? Don kawai tana exceptional child? You are to be encouraging her on her defect, not to weaken her. Words like yours are not encouraging at all". Mr. Samson ya ce “I’m sorry Saheeb, Hasna is among my favourite students, dawowar ta kasa a aji ya dame ni, i don't mean to devalue her." Ya ce “ka je zan yi Magana da ita”.
Bayan fitar Mr. Samson cigaba yayi da rubutun sa, har sai da ya gama sannan ya aje biron ya dube ni, a cikin idanun sa concern ne da kulawa tsantsa.
“Hasna’u zan iya sanin abinda ke damun ki? Da yasa har malaman ki suka yi noticing cewa kin yi kasa sosai a karatu?”
Hawaye suka cicciko ido na, amma ban san meyasa ba na ji shi kam zan iya gaya masa hakikanin damuwa ta, na samu confidence a tare da shi tun lokacin da ya taimake ni ya bani abinci, ya kuma ce da mahaifiyar sa da ta kira ni 'zabiya' Ubangiji da ya halicci kowanne dan adam ya karrama shi”. Tun daga wancan lokacin na ji ina respecting din sa sannan ya dade da zama cikin rai na na kasa manta shi.
“Uncle Saheeb, so nake na koma baka (black), ina nufin kalar 'yan Africa, don Allah idan akwai maganin da zai maida ni baka ka bani, ina da ciwo a cikin raina, babu inda yake min ciwo sai zuciya ta tun lokacin da na gane fari na abnormality ne ba kyau bane.
Uncle ko kawa banida ita a makarantar nan sabida ni zabiya ce…. A gidan mu su Hassan da Hussaini ba mai alaqa da ni sai mahaifiya ta, ban taba ganin mutum iri na ba a garin mu bakidaya, meyasa ni kadai ce zabiya? Kuma meyasa aka haife ni haka? Ji nake na tsani kai na bana ko son ganin fuska ta a mudubi”.
Zuciyar Saheeb ta yi wani irin nauyi, ya dade bai manta yarinyar ba, sabida ita duk sanda ya ga zabiya sai ya waiwaya ko ita ce. Ya dora fuskar sa akan tafukan sa ya soma Magana cikin lallashi.
“who told you ke kadai ce zabiya a duniya? There are millions of Albinos around the world wadanda nasu yafi naki muni. In kin duba ke kam naki da sauki akan wadanda ko kuda ne ya sauka akan fuskar su sai yayi musu tabo.
Amma a haka suke rayuwar su cikin godiyar Allah. In kina so ki rayu kamar kowa, sai kin cire damuwar abnormality din ki daga ran ki, kin sa a ran ki cewa haka Allah ke son ganin ki, ki fidda maganganun mutane da damuwar su a ran ki domin ba duka keda imani akan Ubangiji ke halitta yadda yake so ba.
Me yasa kike son komawa baqa? Hasna you are special a yadda Allah ya yi ki. Wasu makafi ne, wasu kurame ne basu ji basu gani. Wasu kuwa duk an hada musu rashin ji da rashin gani. Wasu kuwa guragu ne basu da kafa. Su kuma su ce me Hasna? Sai su ce lallai sai sun bawa kan su abinda Allah bai ga damar basu ba? Hasna’u ki karfafa imanin ki, in ba haka ba zaki karawa kan ki lalura, kwakwalwar ki ta tabu da damuwa. Kin ga lalura ta karu kenan. Ni na gaya miki in kika cire wanan damuwar a ran ki, kika tsaya ki kayi karatu mai nagarta AN AMAZING HUSBAND na zuwa, wanda ba zai taba kallon abnormality din ki a matsayin nakasa ko abin kyama ba”.
Murmushi nayi, murmushin da ban taba yin irin sa a tsayin rayuwa ta ba, babu wanda ya taba gaya min maganganu masu dadi da karfafawa irin na Uncle Saheeb. Koda kuwa ace ya fada ne kawai don ya faranta min, ba hakikanin gaskiyar kenan ba, na yi alkawarin bin duk abinda ya ce don tsira da lafiya ta, ba zan so kam in zamo mentally-retarded bayan zama albino ba kuma. Na alkawartawa rai na daga yau zan so kai na, zan koyawa kaina (self-love and self-determinatio) tare da rungumar kaddarar da Ubangiji ke so na da ita.
Maganar da ya ambata ta cewa amazing husband na zuwa idan na tsaya na yi karatu ita kadai nake da inkari (ja) a kan ta.
“Na ji duk abinda ka ce Uncle Saheeb, na kuma yi alkawarin bin duka shawarwarin ka, amma ka cire maganar amazing husband na riga na sa a raina har abada bazan yi aure ba.
Karatun kadai zanyi ta yi har sai naga karshen sa (idan ana gani), amma bazan taba yin aure ba uncle, ban taba sanya raina ba”.
Uncle Saheeb, sai ya kura min ido, zuwa can ya ce “if that is your decision I must say it’s a WRONG decision (idan wannan shine hukuncin ki sai in ce gurbataccen hukunci ne). Wanda ke nuna still kina kalubalantar Ubangijinki da halittar da yayi miki.
Aure sunnah ne kuma Allah ya halatta shi akan kowanne musulmi mai lafiyar da zai iya aure. Don haka Hasna’u ki cire wannan doctrine din daga zuciyar ki, ki sa a ran ki duk sanda Allah ya kawo miki miji za ki yi aure. Uncle Samson ya gaya min kina da issue da idanun ki”.
“Eh Uncle bana ganin rubutu dai-dai akan allo, kuma in dare yayi sai da lalube nake shiga bandaki”.
Uncle Saheeb ya dube ni cikin ido, duk da haka babu alamar tausayi na cikin kwayar idanun sa. Wani yanayi ne a cikin idanun sa wanda ya sha gaban in kwatanta shi da komai, sabida da ban taba gani a tare da kowa ba.
“Now, tell me about yourself, ‘yan wane gari ne ku kuma meyasa Innar ki bata zo visiting ba?”
“Rashin zuwan Inna ya kara min damuwa don bata taba fashin zuwan ba tun da na fara makaranta. Mu ‘yan garin nan ne amma asalin Babana dan Kabo ne”. Na gaya masa tarihi na bakidaya. (Uncle Saheeb tun daga wancan lokacin har zuwa yau bai daina tunanin hanyoyin inganta rayuwa ta ba).
“Go to your class Hasna’u. In an yi hutu tunda saura sati biyu zan zo har gidan ku na kai ki asibitin Murtala ki ga ophthalmologist. Insha Allah you will have a fitted glasses wanda zai taimaka miki.
“kin min alkawarin daga yau kin cire damuwar halitta daga ran ki ko? Zaki komawa karatun ki yadda kike yi a can baya? If possible har ma ya fi na baya?”
Ina murmushi na gyada masa kai.
"Madallah Hasna, now go to your class, an kusa kada kararrawar tashi”.
Na juya na fita daga clinic bayan nayi masa godiya mai yawa. Da gaske na ji zuciyata ta yi wasai daga kuncin data ke ciki. (Counselling pays).
******
Hasna’u na bada baya ya janyo system din sa, ya shiga internet sai ya samu kan sa da kasa cigaba da yin aikin da yake yi,sabida tunanin Hasna’u, ya hau yin kyakkyawan bincike a kan albinism. Ko akwai treatment din sa a likitance?
Abinda ya fara cin karo da shi shine “Albinism is inheried condition (wato gadon sa ake yi cikin jini) amma Hasna ta ce ita ba gada ta yi ba. Zai iya yiwuwa cikin ancesstors din ta wani ke da shi bata sani ba.
Binciken sa ya cigaba da gaya masa cewa;
“It happens beacause they have less MILANIN than usual in the body. Melanin gives skin, hair, and eyes their colour. Except for vision problem, most people with albinism are just as healthy as anyone else”. (Yana faruwa ne a sakamakon rashin melanin yadda ya kamata a cikin jikin dan adam. Melanin shine abinda ke baiwa fata, gashi da ido kalar su. In kika dauke matsalar raunin gani, yawancin zabiya lafiyayyu ne kamar kowa).
Sai ya koma tambayar menene MELANIN?
MELANIN is the pigment that is responsible for our beautiful variety of skin tones and shades, eye colours and hair colours.
Not only melanin provide pigmentation for human skin, hair and eyes, it also provides protection against the harmful effect of ultraviolet (UV) rays.
Sai ya koma binciken menene treatment din sa a likitance?
“Because albinism is a genetic disorder it cannot be cured, treatment focuses on getting proper eye care and monitoring skin for signs of abnormalities”. (Tunda ya kasance gadar sa ake cikin jini, to ba shi da magani, treatment dinsa daya ne kula da lafiyar ido yadda ya kamata da kula da fata koda zata samu sabon sauyi) Darmatologist and ophthalmologist sune professionals wadanda Zabiya ke gani akai-akai.
Saheeb, sai ya hada kai da tebirin sa, yana tunanin hanyar da zai bi ya tallafi rayuwar zabiya HASNA’U. Hasna’un da ya fahimci bata da wani cikakken gata bayan mahaifiyar ta, wadda itama bata da karfi.
Abu na farko daya tsayar cikin ran sa shine tsayawa lafiyar idanun ta da fatar ta for any abnormality sign, don kada ta rasa ganin ta gabadaya, ta hanyar kai ta ga kwararren ophthalmology Dr. Abubakar Turaki Abdullahi, sannan da zuwa ya binciko halin da Innar ta ke ciki, wanda ya hana ta zuwa ganin ta. Daya al’amarin dake sakadar ruhin sa yaki yake da shi ko ta halin kaka da karfin tsiya don bai ga ta ina yiwuwar sa zata kasance ba in ya tuna an ce “It’s a genetic disorder!”
-TAKORI
*****


BANGO ABIN JINGINA (ME YA HANA INNA ZUWA?)
A duka kwanakin da suka biyo baya da Hasna’u yake kwana yake tashi a ran sa. Don haka bayan kwana uku da zuwan Hasna’u clinic ya bi kwatancen da ta yi masa ya shiga cikin garin Kachako. Karo na farko da ya taba shiga garin tun fara service din sa. Gwamnatin Tarayyah ta turo shi asibitin ‘Unity College Kachako’ domin hidimtawa kasa, a matsayin sa na wanda ya karanci MBBS.
Da tambaya da kwatance kuma dama aka ce zabiya baya taba buya a cikin mutane, musamman a karamin gari kamar Kachako, don haka bai sha wahala ba ya gano gidan Kawu Sama’ila.
Ya sauka daga kan machine din okada da ya kawo shi ya taka zuwa kofar gidan sannu a hankali, abinda ya dau hankalin sa shine cincinrindon mutane kamar ana daurin aure, sai da ya lura kuma ya gane fuskokin su duka babu walwala kuma kowa alwala yake yi, alhalin ba lokacin kowacce sallahr farilla bane, ba jimawa kuma kafin ya yanke shawarar abin yi ya ga an fito da gawa cikin makara an fara daidaita sahu.
A matsayin san a musulmi sai ya ambaci “innalillahi wainna ilaihi rajioun” duk da bai san waye ya rasu ba, ya kuma bi sahu don dama da alwallar sa, akayi sallahr jana’izar tare da shi. Koda aka idar kowa ya wuce makabarta banda wani dattijo da ya zauna akan kututturen iccen darbejiyar kofar gidan. Sai ya karasa gare shi yayi masa sallama.
“Sannu samari, daga ina? Wa kake nema?” Dattijon ya tambaya cikin mutumtawa.
“Na zo neman gidan su Hasna’u-Zabiya, wadda take makarantar kwana”.
Dattijon sai ya dube shi da dukkan alhini ya ce “nan ne gidan, bari maigidan ya dawo sun tafi makabarta kana gani” “Allah ya jikan musulmi Allah ya bada hakuri, ai ba wurin sa na zo ba, na zo ne wajen Babar Hasna’u in isar mata da sakon diyar ta, ni likitan su ne na makaranta”.
Dattijo sai ya ce “Allah sarki dan nan, Allah sarki Hasna’u – Zabiya. Da rabon bazaku gana da Inna Zulai ba, ita aka tafi kaiwa makwanci, yau watannin ta biyu kenan a kwance tana jinya sai yau Allah ya hutar da ita”.
Saheeb sai ya durkushe a wurin yana fadin “Innalillahi wainna ilaihi rajioun”. Ya nemi waje gefen dattijon nan ya zauna ya rasa abinda ke masa dadi. Tausayin Hasna’u ya kara ninkuwa a ran sa and he vowed to himself to become her guardian and also a shoulder to lie on (bango abin jingina) ko da wannan shine abu na karshe da zai gabatar a rayuwar sa.
Yayi hawaye ya share har babu adadi. Ba jimawa su Kawu Sama’ila suka dawo. Dattijon nan yayi masa nuni da Kawu Sama’ila “ga Yayan ta can ya dawo, je ka yi masa taaziyya”.

Ya karasa har gaban Kawun ya tsugunna ya gaishe shi yayi masa gaisuwa, sannan ya gabatar da kan sa matsayin likitan ‘Unity College’ da abinda ya kawo shi wato duba ma Hasna Innar ta da kuma abin alhinin da ya tarar. Ya kare da yi masa ta'aziyya. Kawu Sama’ila ya ja shi suka zauna tare a gindin bishiya yana ta gode masa tare da sanya masa albarka.
“Wato dan nan ina tausayin Hasna’u, bata saba da kowa ba sai uwar ta, ga ta da kebe kai daga cikin al’umma (alienation), idan ka ga irin shaquwar da suka yi sai ka ji cewa lallai Hasna’u yanzu ne zata yi maraici na baya ba komai bane tunda ko sanin uban bata yi ba.
Ko barci baya raba su, sai in ta koma makaranta.
Kullum zancen ta shine, “ranar da babu ni, Yaya Sama’ila ko yaya Hasna’u zata yi?” Sai in ce mata Allah da ya halicce ta shi zai bata yadda zata yi”.
Hirar mu ta karshe bayan masassara ta kwantar da ita shine ta ce ta san Hasna’u na cikin damuwa na rashin zuwan ta ganin ta a makaranta, tunda bata taba fashin zuwa ba, nace mata ni zan je in gano mata Hasna’u” sai cewa tayi "yanzu ta kusa cika shekaru sha bakwai, na san ba miji zata samu ba, ko yaya rayuwar ta zata kare?” Nace mata “Zulai ki daina irin wannan tunanin Allah shi yake komai, kuma muddin ina raye Hasna’u zata yi aure kamar kowa tunda dai na haifi ‘ya’ya maza, in ‘ya’yan kowa sun ki ta ‘yan uwan ta Hassan ko Hussaini bazasu ki ta ba.
Sai ta yi murmushi tace “gara kowa da su in dai a kan Hasna’u ne”
nikuma nayi mata alkawarin muddin ina raye, to Hassan ko Hussaini wani cikin su zai auri Hasna’u”.
Tunda Kawu ya fara bayanin sa yake saurare attentively har Kawun ya dasa aya. Bai ce komi ba, don bai da abin cewar amma hakika Hasna ta gaya masa Hassan da Hussaini ‘ya’yan Kawun ta sun fi kowa kyamar ta. To ina ga an aura musu ita? Amma su kadai suka dace da auren nata ko babu komi jinin ta ne ‘yan uwan ta ne, but Hasna is talented a karatu despite her disability, talent din da ke bukatar nurturing ba wai auren wuri ba, auren da za’ayi ne kawai don a rufa mata asiri ba don ana son ta ba.
To amma shi wanene da zai hana Kawu yi wa ‘ya’yan sa aure in shi ba auren ta zai yi ba?
Rasss! Ya ji gaban sa yayi mummunan faduwa. Abu daya zai yi in har yana so ya taimaki rayuwar Hasna’u shine YA AURE TA!!!
To amma ya aureta ya kai ta ina? What of the genetic factor? Mama will NEVER allow him to bring ALBINO to her family talkless of matar data riga ta yi masa wato Fa’izah diyar aminiyar ta.

“Kawu ina rokon alfarmar kada a fadawa Hasna mutuwar Innar ta sai ta dawo hutu, saura kwana goma su dawo”. Ya fada da wata murya kamar ta wanda ya sha duka hawaye na kundumbala cikin idanun sa. “Sannan ina neman alfarmar a bar ni in kaita asibiti a yi mata gilashi ranar da suka yi hutu ni da kaina zan dawo da ita har gida cikin amana, idan har ka amince da ni. Gilashin zai ceci ganin ta da take gab da rasawa”.
“Samari na amince maka ka ji? Ka kaita ayi mata ka dawo min da ita, Allah yayi maka albarka, in iyayen ka na raye Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana, idan kuma sun rigaye mu Allah ya kai ladan taimakon da kake da niyyar yi wa Hasna’u kabarin su”. "Amin ya Allah Kawu, ubana ya rasu mahaifiyata ke raye, sai kanwata daya Nusaiba.
Sunana Abubakar Saddiq amma ana kira na SAHEEB”
“Sannu ka ji Sahabi? Sahabi abokin Manzo, Allah ya baka masu yi maka kai ma”.
Da wannan suka yi sallama da Kawu Sama’ila, yana shirin barin kofar gidan wani saurayi na tahowa dukun-dukun da shi idanun shi jajawur, in ba shaye-shaye ba ba abinda zai maida idon namiji haka, ya kalli Saheeb ya watsar, yasa kai zai shige cikin gida.
“Kai Hassan don jakar ubanka baka san kanwata ta rasu bane? Ban ganka a makabarta ba kuma yanzu zaka wuce mu baka yi mana ta’aziya ba, ga bako kana gani amma ko ka gaishe shi?”

Bai tsaya ba ya cigaba da tafiyar sa yana fadi cikin kunkuni “to Baba ina ruwa na don uwar zabiya ta kwanta dama? Bakon ka kuma meye gami na da shi? Garin kwashe-kwashen ka sai ka janyo wadanda zasu yi kidunafun din ka”.
Da haka ya shige cikin gida, kunya kamar ta kashe Kawu Sama’ila, sai da ya gwammace bai kula shi ba. Saheeb yayi kamar bai ji su ba ya sa takalmin sa ya wuce don gab yake da fashewa da kuka da ya gane wannan ne mijin Hasna’u. Mijin da sai wani babban ikon Allah ne zai hana ta auren sa.

Mr. Samson ne a cikin ajin yana bada darasin sa na lissafi. “Set Theory” is our today’s topic. Who can tell me what is set in mathematics?”

Kamar ko yaushe ya san ita kadai ce zata daga hannu, kasancewar ta masoyiyar darasin sa na lissafi, saboda tsabar son ta ga subject din kafin a yi musu topic ta je labirare ta dubo shi ta yadda in ya zo ya fara koyarwa sai dai ya zama kamar tishi a gare ta. Amma ga mamakin sa yau bata daga hannu ba. Ta hada kai da tebir bata ma san me ake a ajin ba.

Har Mr. Samson ya zo gaban tebirin ta ya tsaya, ya kuma kira sunan ta bata ji shi ba. Sai ga sallamar Saheeb wanda baya zuwa classes area sam, amma yau sai gashi har ajin su Hasna’u, gabadaya a hargitse yake kamar bai samu barci sosai ba kuma bai yi wanka ba, bayan ya dauki iznin hakan daga principal ya kuma gaya mata abinda yasa yake son ganin Hasna’u din, ba wani abu bane lafiyar ta zai bincika don tana gab da fadawa depression kuma ga rasuwar mahaifiyar ta ba tareda ta sani ba. Ya gaya mata Kawun ta shi ya bashi iznin kulawa da ita har zuwa asibitin Murtala da zasu je ranar hutu.
Principal Haj. Maimuna Dikko, ta yi mamaki kwarai, what is special a kan zabiyar nan da kowanne malami bai da zance sai nata? And now Dr. Saheeb, yayi tattaki har cikin kauye sabida Hasna’u zabiya, lallai ne there’s something unique, something special associated with Hasna’u Dabo, wanda su Malamai da suke tare da ita suka yi noticing.
“Samson what’s wrong with her?” Ya fada hannayen sa biyu zube cikin aljihu, sounding worried, gaban sa na faduwa, cike da tsoron ko wani yayi masa riga malam masallaci ya gaya mata mutuwar Innar ta.
“I don’t know Dr. But she’s absent-minded”.
“Hasna! Hasna!!”
Saheeb ya kira sunan ta da dan karfi, tare da kwankwasa tebirin nata. Firgigit ta tashi ta hada gumi kashirman idanun ta sun kada sun yi jazir. Mafarkin da ta yi jiya da inna shi ya daga mata hankali. Sai ta ji uncle Saheeb na fadin.
“taso ki biyo ni clinic”.
Duk attention din ‘yan ajin sai ya dawo kan su, masu kyabe baki nayi, masu mamaki nayi. Dr. Sahib Bello Wamakko, ya kasance mai farin jinni a wurin ‘yammatan Unity Kachako duk da kasancewar bai dade a makarantar ba kuma ba mai sakin fuska bane. A rashin sanin sa 70% na ‘yammatan unity masu ji da kan su yana matukar burge su.
Ya riga ta shiga ofishin sabida tafiyar data ke yi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Nurse Saratu na gyara kantar magunguna ta gan su sun shigo. A yadda ta ga Hasna’u sai ta tabbatar ba lafiya ba, ga fuskar ta kara yin jajawur kamar da ka taba jinni zai yi tsartuwa.
“Have a seat” in ji Saheeb. Ya fada yana gyara mata kujerar gaban sa. Ta zauna, amma ta kasa ko duban sa.
“What happened Hasna’u?” Girgiza kai ta yi alamar babu komai. Shi kuma ya cigaba da lallashi yana tambaya. “Ni ba Yayan ki bane yanzu? Baki san har gidan ku na je ba? Kowa da kowa yana gaishe ki, ga wannan Inna ta ce na kawo miki” ya fada yana mika mata wata katuwar Ghana must go shake da kayan masarufi na alfarma. Kallo daya ta yi wa kayan ta hau girgiza kai.
“Ba Inna ce ta aiko da wadannan kayan ba”.
“Why do you say so?” ya tambayeta cikin rashin jin dadi, feeling somehow yau yayi karya don ya farantawa Hasna’u.
“Ina ta gan su? Da dai kanzo, kwaki da kuli da mai da dunkule ka kawo shine zan yarda Inna ce ta aiko” “to naji na yi karya Hasna’u, shikenan, har zuwa gidan ku dana yi shima karya ne ko? In baki sani ba har Hassan na gani da malam Audu makocin ku da Kawu Sama’ila da ita Innar kan ta”.
A take fuskar Hasna’u ta washe, jan ya ragu, har ta yi murmushi. Ganin hakan ya cigaba da yi mata bayani.
“na je na karbo iznin Kawu ne na in kaiki asibiti ranar hutu, daga nan in maida ke gida. So ki shirya da wuri ranar hutu don mu samu ganin likita a cikin Kano”.
Bata san meyasa shi ta yarda da shi ba, bata san me ya sa kome ya gaya mata sai zuciyar ta ta yi amanna ba, haka bata san me yasa shi SAHEEB take da kyakkyawan confidence da trust a kan shi ba.
Ta ji ta yarda zata iya bin sa ko Birnin Sin ne, ba tare da ta ji ko darr ba, ta amince ba zai cutar da ita ba. Ta kuma yarda ya je gidan su, wadannan kayan ne dai bata yarda daga hannun Inna suka fito ba, they are solely from Saheeb, yace inji Inna ne don yayi mata wayo ta karba.
“Kai dai uncle ka gaya min gaskiya, cewa kai ka yi provision din nan, ai ba zan ki karbar kyautar Yaya na ba. Amma ina kudin surfen Inna zai sayi wannan? Jarin abincin ta ya dade da karyewa”.
Ta fada with so

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment