Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO( FINANCIAL SECTARY OF THE ASSOCIATION OFFICIAL )




Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK


___________________
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect writer's together we stand 🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*pen 🖊️ is mightier than the sword 🗡️*
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣


Wani matsakaicin gida ne gidan talaka bawan allah, d'akuna uku ne a jere waje daya,sai wani waje da aka zagaye da alama akwai mutum a 'bangaren,Wata kyakkyawar mata ce na hango tsakar gida hannunta rik'e da tsintsiya,ita ba fara ba ita ba bak'a ba irin dai tsaka_tsakar nan ce ga hanci ga idanu bakinta dai_dai ga diri gareta mazaunan ta mutum zai iya d'ora Kofi a kai ba tare da kofin ya Fad'i ba sanye take cikin wata atamfa,tana tsaye tana daddaga tasharar a hannunta irin mutum yayi shara ta d'an saki, wani mutum ne ya fito daga d'aki hannun sa rik'e da hula, fari ne soll ga hanci, yana sanye cikin wani yadi bak'i " Wai harka fito? " Matar ta fad'a,ya bata amsa da "Eh yau ina san naje kasuwa da wuri "Gashi ko naso muyi magana amman ba komai idan ka dawo sai muyi" Okay to yayi" Muje wajen mama" To" ta fad'a tare da ajiye tsintsiyar hannunta suka nufi wani 'bangare da aka zagaye na cikin gidan, a tare sukayi sallama suka ciga cikin d'akin, wata dattijiya ce zaune saman sallaya tana jan carbi, ganin su yasa ta saki murmushi, bayan sun zauna kowannen su ya gaidata ta amsa musu cikin sakin fuska " Auta har an fito?" Eh wallahi mama yau ina San naje kasuwa da wuri ne "To ubangiji Allah ya taimaka ya kawo kasuwa mai albarka" Amin ya rabbi " su duka suka amsa da amin, ya tashi suka fito hannunsu sark'e cikin na juna har bakin k'ofa ta rakasa tace" zuwa yaushe zaka dawo?" To sai munga yarda yanayin kasuwar ta kasance "Okay ka kulamin da kanka allah ya kaimin Kai lafiya ya dawo da kai lafiya ya kawo kasuwa"Amin amin matata "Bakinta ya d'ora a nata ya tsotsa, Sannan ya bud'e gida ya tafi.............dawowa tayi taci gaba da shararta bayan ta gama ta d'auki tsinke da mashaci tayi 'bangaren mama bakin ta d'auke da sallama




"Washhhhhhhhhh" ta fad'a tare da d'ora kanta saman k'afafuwan mama "Sannu "Yawwa mama yau me kike son a dafa ne?" Khadija duk abinda kika dafa "Aah ki za'ba "Aah kiyi kawai"Gaskiya ni sai kin za'ba"ta fad'a tare da bubbuga k'afa irin na shagau'bar nan" To kiyi muna tuwo dan na kwana biyu banci shi ba" To shikenan mama allah nima yau d'in nan da San tuwon na tashi "To kinga shikenan sai kiyi muna shi"Ai kuwa bara na kunce kaina sai naje nayo cefa ne dan ba sauran kayan Had'i "Okay bayan zakiyi ?kawo na kunce miki"Gashi wllh kamar kinsan banasan kunce kitso shiyasama ban cika son yi ba " Ai dan dai kinada gashin ne yasa Baki cika yin kitson ba da bakyada suma dole kije kiyi " Ko mamarmu haka take cewa wai "Ai haka ne ma" ta ciren d'ankwallin sai ga gashin ta ya zuba har a gadon baya manya kitsone ma a kanta kuma ba wani dadewa yayiba, mama ta kar'bi tsinken ta fara kunce mata, ta kunce mata gaba ki d'aya ta shace mata ta kame mata shi........


Bayan sun gama taje tayi Shirin zuwa kasuwa , tazo ta bama mama mukullin d'aya d'akin wanda firij d'in ta suke ciki, dan mace ce mai san Sana'a duk unguwar ita kad'ai keda firij ai kuwa koda yaushe cikin ciniki take, tana siyarda ruwa, zobo, kunun aya,k'ank'arar zak'i........................kuma mace ce da bata dogar ga miji sai ya bata zatayi Abu ba cikin kud'in ta take fitarwa ta siya har cefanen gida ita keyi wani lokaci, ba ruwanta idan ya bata ta amsa tayi godiya idan bai bataba ba ruwanta haka take gareta, yana d'aya daga cikin abinda yasa sadik ke k'ara k'aunar ta,sannan tana bama Mahaifiyarsa girman ta su zauna suyi wasa da dariya wani lokacin idan kaga suna wani abu zaka rantse kace tobassai ne akan shak'uwarsu, yayun mijinta har fad'a suke da mama aka ganin irin sagartar da take mata, sai dai abu d'aya wanda yake damun mama da sadik shine rashin haihuwarta har yanzu kusan shekarar su uku da watanni da aure amman ko 'bari bata ta'bayi ba, ga matar da akayi auren su tare mak'otansu har ta haifi yara biyu amman ita haryanzu Shuru ka ke ji.......



Bayan ta kaimata mukullin ta fito ta samun abun hawa tayi kasuwa, cefanen ta tayi mai rai da lafiya, har ta gama cefanenta ta joyo kenan sukayi kaura da wata mata "Subhanallah yi hak'uri dan allah ban ganki ba" matar tayi mata kallan sama da k'asa tare da cewa" Bangane nayi hak'uri ba saboda wawanci kana tafiya bazaka Kalli hanyarka ba "Yi hak'uri dan allah"Khadija ta sake fad'a"Mtsssssssssssssssssss to idan nace bazan hak'ura d'inba fa" yi hak'uri dai" ta sake fad'a duk da ranta ya 'baci na ganin sai faman bata hak'uri take tana gaya mata maganar banza duk da ma ba laifin ta bane dan ita ta jiyo ne ita kuma matar tana tafiya tana dannar waya, " To bazan hak'uraba" Matar ta fad'a irin cikin izzar nan tare da rik'e k'ugu "Bazaki hak'ura ba? "Eh bazan hak'ura ba" khadija ta aje cefanen hannun ta tare da cire nik'ab d'inta ta jefa cikin ledar ta shak'o wuyan matar ta yarfa mata mari tare da fad'in "Dan kutumar ubanki idan kika hak'ura allah bai godeba bura ubar banza kawai dan ma kin samu ana baki hak'uri shi ne harda k'ara botsarewa to ubanki yaci ubansa idan kin hak'ura" nan take idanun matar nan suka kawo ruwa ga Marin da Tasha ga matsarda take sha, ko kafin kace me tuni mutane anzagayensu ana 'ban'barar hannun khadija amman ankasa,wani mutume da yake gefe yana kallansu mussaman ma khadija yana kallan mazaunanta yarda suke rawa akan jijjigar hannunta da akeyi, ya tako a hankali ya tsaya bayan khadija ya zuro hannuwansa ta gaba a yarda ya tsaya yanajin yarda tudun mazaunanta suke sai ki ci niyar rik'o hannuwanta yake wai shi yazo raba fad'a, khadija jin namiji a bayan ta yasa ta saki matar tare da saurin juyowa ta d'auke sa da mari tare da fad'in " Da aure na da yagiyata uku akai dan kana d'ebabben albarka zako kana ta'bani wallahi yanzun nan sai na kullah ma sherin da ba ubanda ya isa ya fitar da Kai dan iskan banza da wofi asararre"ta sake juyowa ta Kalli matar wacce banda Maida numfashi ba abinda take tace" Dan Allah gobe ki k'ara banza y'ar tasha " ta duk'a ta d'auki kayanta tayi gaba abun ta.....................








Idan naga anyi comment mai yawa zan rik'ayin typing mai tsawo




Bayan ta dawo,ta fara aikin ta,tana aiki ana ta zuwa siyen kaya, duk wanda yazo sai dai tace yaje ya d'auka robar kud'i na ciki ka kad'a kud'i ka d'auka, wasu su kad'a wasu kuma su k'i kad'awa kuma su d'auki kaya............


Cikin k'ank'anin lokaci ta kammala girkin ta sai k'amshin miyar keyi, ta d'auki na mama taje ta kai mata ta dawo ta kai sauran abincin d'aki, ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga,mai kyau,bayan ta gama bada jimawa ba,sai ga sadik ya dawo cin abincin rana, ta tarbesa irin yarda ya dace ta kai masa ruwan wanka a bayi yaje yayi wanka ya fito ta d'auko masa wasu kayan, ta kawo masa abinci, lomar farko sai da ya runtse ido tare da kyad'a kai "Allah dai ya miki albarka ya k'ara miki zak'in hannu kiyita yimin irin wad'an nan girkin mai dad'i" Amin Amin mijina" Yawwa wace maganar ce kika ce kina son muyi?" Daman akan maganar gadon nanne da aka raba aka bani nawa shi ne nayi wani d'an nazari akan mezai hana na arama kud'in ka k'ara cikin Sana'a ka ka juya,tunda ni kaga ina da sana'a bare nace jari zan ja "To matar sadik amman kina ganin ba matsala " Ba matsala" kinyi shawara da inna ne" Aah ai Wannan kud'i na ne ni keda ikon yin duk abinda nake so da su bare kuma nasan inna zata goyi bayana akan wannan abun "To shikenan allah yasa musu albarka"Amin" ta fad'a tare da Mik'ewa taje ta bud'e wardrobe d'in ta ta d'auko wata leda bak'a, tazo ta zauna ta kunce ledar ta fara fito da kud'in " Ga sunan dubu d'ari uku ne"To matar sadik allah ya miki albarka yasa ki gama da duniyar nan lafiya ya k'aro muna zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman takewarmu" Amin ya hayyu ya qayyum " sai da yaci abincinsa ya k'oshi Sannan ya tashi ya wanke hannun yayi shirin komawa kasuwa ya d'auki kud'in yasa aljihu,' bangaren mama ya nufa shi kad'ai ba tare da khadija ba ya barta zata gyara wajen da yaci abinci



Da sallama ya shigo wajenta ya gaidata bayan sun gaisa yace" Mama na samu sadakin in Sha Allah da na fita yanzu zan biya na kai musu" Kai ma sha Allah ya sanya albarka, ina k'ara fad'a maka kar ka kuskura ka bari tasan da aure zakayi kadai ji na fad'a maka" Haba mama ai bazan bari ba " To da yafi kam" Ni zan je" To a dawo lafiya "Allah sa" Amin" ya fito ya wuce,


Bayan ya wuce khadija ta Had'o kayan da suka cire ta wanke

bayan ya fito da gidan ya kira abokinsa usman ya sanar masa ya samu kud'in sadaki yazo ya rakasa suje sukai, usman ya tambesa inda ya samu kud'in bai 'boye ba ya sanar masa inda ya samu kud'in, usman yace" Kana ganin babu matsala kuwa" ba matsalar komai " To shikenan ganinan zuwa

Bada jimawa ba usman yazo suka je suka kai kud'in, sadik wani farin ciki yakeji kamar wanda akama bushara da aljanna





AFTER TWO DAYS
Akasa ranar aure nan da sati d'aya,saboda daman an dad'e da had'a komai sadakin kawai ake jira,ganin ya kawo sadaki suka ce kar a 'bata lokaci ayi a gama, ranar asabar bayan sallahr azahar sadik ya shigo tare da mai gyaran sili, khadija na d'aki,suka wuce suka shiga d'aya d'akin dake manne da nata d'akin ana gyara wajen da ya hude, khadija na d'aki jin motsi yayi yawa yasa ta fito tashiga d'aki,ganin tayi ana gyaran sili ta rik'e k'ugu tare da karkad'a kafa, wata uwar tsawa ta dakama mai gyaran sai da ya tashi Fad'owa saman katakon da yake, hanya ta nuna masa tare da fad'in "Fitar kabar gidan nan tun kafin nakai ga lahanta ka " Mai gyanan jikinsa na rawa ya sauk'o ganin fuskarta ba alamun wasa a tare da ita Sannan da ka ganta kaga zubin majiya k'arfi shiyasa Bai tsaya 'bata lokaci ba ya sauk'o tare da kaushe kayansa ya fito


Dubanta ta mayar ga sadik tace" Me nake gani ?"cikin inna inna ya fara fad'in " Daman naga silin ya lalace ne nace yazo ya gyara sa " Kai Kai sadik ba k'aramar yarinya nake ba sili tun yaushe yake haka baka tashi gyaran sa ba sai yanzu to wallahi idan ma wata niyya ce dakai ka cireta daga ranka " ke khadija wai ke ke aure na ne ko ni ke auren ki " Kai ka sani sai ka bama kan ka amsa hmmmmmm" tana gama fad'in haka tayi d'akin ta, harta kwanta ta Mik'e ta fito ta d'auko ta'barya da kujera mai d'an tsawo ta shiga d'akin da sadik ya kawo mai gyara, hawan kujerar tayi tasa ta'barya tana k'ara hude silin sai da duk ta lalata sa sannan taji zuciyarta ta mata sanyi ta...........................









🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO( FINANCIAL SECTARY OF THE ASSOCIATION OFFICIAL )


Wannan shafin naki ne aunty khadee (Oum sharifat ) Allah ya baki lafiya idan kuma..................ne to allah ya raba lafiya muzo mu caskare waii ai da ranar idan muka fara kausan shoki sai an rik'emu🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 masoyiya koya kika ce?😂

Yan amana
Oum sharifat
Maryam Naseer Ibrahim ( Jagabar royal star) love you 🫶💔♥️❣️♥️♥️





Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK


___________________
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect writer's together we stand 🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*pen 🖊️ is mightier than the sword 🗡️*
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣

Dare yayi ta kama ledar d'akin ta daidai wajen da tasan sadik zai kwanta ta nad'e ledar tabar wajen hok'on siminti, ta k'ara gyara gadonta ta haye, daman tuddin sukayi fad'a to bata bari ya hau mata ledar d'aki bare kuma gado, har ya Saba da haka, shigowa yayi ya d'auki babbar rigarsa ya shimfid'a a k'asa wajen da ta nad'iye ledar, yayi kwanciyarsa

Washe gari
Ta gama had'a karin kumallo ta kawo masa, amman ba mai cema d'an uwansa ko uffan, yaci abincinsa ya tashi yaje ya gaida Mahaifiyar sa ya wuce, bayan ya fita tayi 'bangaren mama har sun fara fira aka fara zuwa siyan kaya dole ta koma gefensu




Sadik shirye_shiryen auren sa kawai yakeyi, amman tun ranar da ta Kori mai gyaran sili bai sake kiranyo kowa ba,gashi lokacin aure na matsowa bai gyara d'akin ba


Ana sauran kwana hud'u aure abokinsa usman yazo gidan bayan sun gaisa yace"Khadija wani babban al'amari na Shirin faruwa ba tare da sanin ki ba wanda niko naga idan har aka miki hakan ba'a miki adalci ba shiyasa nazo na fad'a miki" To baban abba wane irin abu ne ke Shirin faruwa da har aka 'boyemin?" Sadik zai k'ara aure in tak'aice miki yau sauran kwana hud'u a d'aura aure amman fa kar kiga laifin sadik Mahaifiyarsa tace kada a sanar dake " Hhhhhhhhhhhhh "khadija tayi wata irin dariyar takaici Wanda ba kowa zai gane ba " Ya naga ina fad'a miki mijin ki zai k'ara aure amman naga kina dariya" Hhhhhhhhhh to baban abba idan banyi dariya ba kuka kake so nayi " Aah" To ka gani badai aure ba allah ya kawota lafiya ya basu hak'uri da juna " Amin ya allah daman haka akeso " ya mata sallama ya wuce, d'aki ta koma ta zauna tare da fashewa da kuka,sai da tayi kukanta mai isarta sannan ta tashi

Da rana da yazo cin abinci bata nuna masa komai ba,har suka d'an sha love d'in su ta tambesa tana san taje gida anjima, ya bata izini


Bayan ya koma kasuwa ta yi duk aikin da gareta ta shirya tayi gida, ta samu Mahaifiyar ta a d'aki da kuka " Subhanallah khadija lafiya ?meya faru?" Cikin sheshshek'ar kuka take bata amsa da " Inna wai yanzu sadik aure zai k'ara" To dan zai k'ara aure shi ne kike kuka " Inna ni bama auren sa ne yafi 'batamin rai ba kamar irin na k'in sanar dani da basu yi ba wai ma abun takaici Mahaifiyar sa ce tace kar a sanar da ni " Khadija kiyi hak'uri ki barma allah kayanki kada ki wani damu kanki" Haba inna yanzu ace ko kayan fad'ar kishiya bazaimin ba" Kai khadija ana baki kina rok'o tashi ki shirya muje wajen yan koli ki za'bi duk abinda kike so ni zan siya miki" To inna" ta fad'a tare da goge hawayen ta" Yawwa har kinsa na manta daman amina nake jira ya dawo tallah ta je ta sanar miki idan mijin ki zai barki kije " Ina kenan?" Wajen bikin sahura" Wai har bikin ya kawo" Eh gobe za'a fara kinga idan har zai barki kiyi tafiyarki, kije cikin Yan uwa zakima manta da wani zancen auren da zaiyi" To inna in Sha Allah zanje "Allah sa" Amin




Zuwa sukayi ta za'bo atamfa manya guda biyu da lace da material guda_guda sai takalmi da sarka, sannan suka dawo tayi gida, bayan taje gida taga dare baiyi ba ta d'auko kud'i ta sake zuwa kanti tasiyoma kanta kala biyar na atamfa da yadi,ta dawo ana gama sallah magrib ta je ta kaima mai d'inkin ta kayan kala tara, sukayi jinga ta biyata



Da ta tambayi sadik maganar tafiya bai hanata ba dan har wani murna_murna taga yana yi, ta dai sharesa, tun da safe ta siyo kolin cingum sukutum dan khadija akwaita da jama'a ita kowa nata ne,ta riga rabama mutane tana cewa kishiya za'a kawo mata sai sunzo dannar k'irji

Zuwa marece suka tafi wajen bikin sahura ba'a garin ba ne.
Sadik jira ce yake da ta tafi dan har cemata yayi tayi zamanta ta kwana a can,taji dad'in hakan duk da tasan ba banza ba, tana wucewa ya kirawo mai gyara aka gyara d'akin akayi fenti har bakin k'ofar ta akayima fenti, khadija ana can ana shan biki tama manta da wani auren mijinta...............................







Ango sadik zumud'i kawai ake ana ta shirye_shirye, sabon d'inkin da yayi ya kai d'akin mama ya ajiye kayansa a can, khadija ana gobe d'aurin aure ta dawo,


bata iso gida ba sai da taje ta kar'bo d'inkunan ta sannan tazo gida, tana zuwa taga anyi fenti d'aya d'akin Kuma a rufe da alama har anzo anyi jere,taga harda k'ofar ta aka sakema fenti ta yatsina fuska tare da fad'in "Aikin banza wa kare wanka dan nace anmin gaunan ta da ka sanima kabarmin kayana a haka" ta fad'a tare da jan tsaki tayi d'akin ta, wata akwauti ta d'auko ta bud'e tufafi ne a ciki kala hud'u sababbi wad'an da sadik ya ta'ba d'inka mata bata saka ba ga wad'an da inna tayi mata kala hud'u ga wad'an da tayi kala biyar ga kuma k'ananun kayan da ta siyo garin da taje tare da turaruka masu k'amshin dad'i..............................sai da ta gyara kayanta sannan ta fito taje 'bangaren mama suka gaisa ta bata kayan biki ta dawo k'ofar ta,yanzu harda firar da suke zama suyi ta rage zama



Washe garin d'aurin aure
Tun da safe sadik keta zarya a filin gidan ya rasa ta yarda zai tunkarar khadija da maganar auren nan,wata zuciya na fad'in yaje wata kuma na fad'in kar yaje haka dai ya d'aure ya shiga d'akin ya tarda ta zaune gyaran murya yayi tare da fad'in "Khadija ina san muyi magana" wani kallo tayi masa tare da fad'in ina jinka" Ina san na fad'a miki yau d'in nan za'a d'aura min aure" D'agowa tayi tare da kallan sa ta saki wani murmushin takaici tace"Ina tayaka murna mijina allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin mu allah ya kauda sharrin shaid'an

Sadik wani irin kallan mamaki yake mata tare da nazarin maganganunta,ya numfasa tare da fad'in "Nagode mama ta allah ya miki albarka" Amin, ka tashi kaje ka shirya kar lokaci yak'ure a tsaya jiran ango " Haka ne fa bara na d'auko kayana wajen mama"Okay, ya tashi ya nufi wajen mama


"Hmmmmmmmmm wato ma kayan baza'a ajiyesu a nan ba kaji rashin gaskiya"

Zuwa yayi ya d'auko kayansa ya shirya cikin wata shadda fara babba rigar tasha kaud'o na mutumci hularsa da takalmi kusan kala d'aya ya fito khadija ta tsare sa da ido ganin irin kyawon da ya mata" Tabarakallah ma sha Allah mijina wai kama kalli madubi kuwa? Kaga irin kyaun da kayi? Ma sha Allah allah nagode ma " allah ko mamata" Allah kayi kyau sosai" Nagode " yawwa nace ka d'an bani wani abu wanda zan yima mutanena girki " Wallahi ko sisi banada kiyi hak'uri" Hmmmmm to shikenan l" Aha sai na dawo" Allah ya taimaka " Amin


Bayan ya fita ta kira inna a waya tana kuka ta fad'a mata harda kud'in abincin da zata dafama mutanen ta yak'i bata yace bayada, inna tayi murmushi irin nasu na manya tare da fad'in" wallahi k'arya ce zance yace bayada kud'i duk Bai taso ba kawai dai yace bazai baki ba, amman karki damu zansa a dafa muku abinci anan amina sai takawo muku" To inna nagode" Karfa ki sama damuwa a zuciyarki taje ta miki illah "ba ruwana inna"Yawwa haka nake San ji sai tazo " To"




Koda akace k'arfe goma gayyatar khadija an fara zuwa, taja wanka ko amarya albarka duk inda ta wulga k'amshi ne ke tashi, mutane zuwa kawai suke zuwa shabiyu aka kawo abinci manya_manyan kuloli guda uku da bokitayyen da aka zuba zo'bo, kulolin d'aya dambu d'aya jallop d'in shinkafa d'aya jallop d'in taliya da makroni


Khadija tasa aka kiranyo masu kid'i ansha rawa sosai kamar ba gobe, khadija tayi mutane sosai dan ko ango baya nuna mata jama'a, anci ansha an watse k'awayenta biyu suka rage sunce sai an kawo Amarya zasu wuce, kafin a kawo amarya ta sake wani wanka ta had'e cikin material d'in ta mai shegen kyau tayi kyau sosai,

k'arfe

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment