Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

goma da yan minutes aka kawo amarya, abokan ango sukayi_sukayi akan amarya ta taso suje d'akin uwar gida su gaisa amman tak'i, ganin haka yasa akace d'aya daga cikin abokan ango suje su bama khadija hak'uri tunda tak'i zuwa



Usman yaje ya sameta tare da fad'in "Uwar gida ran gida dan allah kiyi hak'uri da y'ar k'anwar nan taki tace bazata zo ba amman nasan ai dole zaku had'u" Haka ta fad'a? Khadija ta tambaya " Eh" Okay muje d'akin nata ai duk'ama wada baya hana ka taso da tsawon ka................................


Suka nufi d'akin fuskarta d'auke da murmushi, k'awayen amarya da abokan ango sune a d'akin tashi bakin ta d'auke da sallama, "Amarya mai butum hankali in tayi wata tazam wagila" Khadija ta fad'a duka d'akin aka d'au dariya, sadik da tunda ta shigo ya kafe ta da ido ganin irin kyawon da tayi ko shakka babu tafi amarya had'ewa

Muga fuskar amarya, ta fad'a tare da d'aga mayafin amarya ta lok'o fuskarta " Aah wai ke ce ?" Ta fad'a dan tasan yarinyar y'ar unguwarsu ce " Kai ma sha Allah gaskiya mijina kayi dace to allah ya kawo yan biyu kwanan fari" duka d'akin aka d'auki shewa sunata dariya, k'awayen amarya suna mata murna ganin ta samu abokiyar zaman da ba ruwan ta gata da sa mutane nishad'i

Khadija ta mayarda dubanta ga sadik tare da fad'in " To mai gayya idan ka kama ina neman ka daki" Jin ta fad'i haka sai da gabansa ya Fad'i ya dai d'aure tare da fad'in "To " ta fito tayi d'akin ta


K'awayen amarya suka wuce abokan ango kawai suka rage suma harsun kama hanya su fita sadik ya dakatar dasu tare da fad'in " Ni wallahi lamarin khadija ya fara bani tsoro ku duba fa kugani wacce na sani da kishin tsiya amman ace tunda aka yi auren nan ba'a abinda tayi wanda za'a ce na kishi ne anya kuwa ku Kuna ganin ba matsala" Wallahi nima al'amarin nan na bani mamaki " ballo ya fad'a" To ba tace tana neman ka ba ko kaje ne? Usman ya tambaya" Aah banje ba ku jirani naje na dawo" To yayi


Ya kama hanya yayi d'akin ta, kwance ya sameta tayi ashe_ashe saman gado,ganin sa yasa ta tashi zaune tana kallansa tare da fad'in" Sannu adali uban adallai" Khadija menayi ? Ya fad'a cikin k'asa_k'asa da murya " Au har tambaya kake mekayi" Dan Allah kiyi hak'uri "Hak'uri ai dama sai an gama cutar da kai za'a baka hak'uri, Mik'ewa tayi tsaye yayi saurin ja da baya kad'an tasa hannu ta cukunkume wuyan rigar sa tare da fad'in" Macuci mayaudari wai sadik harni zaka cuta na baka kud'i ka k'ara a jarinka sai ka rasa dame zaka sakamin sai da kishiya saboda kana macuci harda yakan da ake bama mata idan za'a k'ara aure baka bani ba na hak'ura na gyaleka kud'i ka bani nayima mutane na abinci ka hanani kace baka da amman ai kasa an dafa maka abincin yan d'aurin aure macuci kawai" ta fad'a tare da k'ara shak'ar wuyan rigar" Dan Allah kiyi hak'uri nasan ban kyauta ba ki yafemin "Wani irin k'arfi taji yazo mata sai da ta dai_dai ta rigar biyu taja ta har k'asa ta rabata biyu ( allah sarki sadik sabon d'inkin sa an masa fatafata da shi)


Sakin sa tayi tajuya tana dube_dube can ta hango wuk'a, taje ta d'auko ganin ta nufosa fuskarta babu alamar wasa a ciki yasa yayi saurin rik'e hannuwan ta duka, can suka fara ko kuwa ta samu ta yanka masa ita a hannu allah ya taimakesa kad'an ne, ganin wallahi da gaske take yasa ya fara kiran suna abokan sa dake waje, Jin yana kiran sunayen su yasa suka shigo d'akin da gudu " Subhanallah! subhanallah meyake shirin faruwa ne subhanallah khadija" Usman ke wannan maganar, dak'yar suka samu suka kar'be wuk'ar

" Kuma wallahi ka sani mata ni ka auroma ita dan wallahi baza ka kwana a d'akin ta ba idan kuma kana ganin wasa nake kaje ka kwana kadai san unguwar nan akwai yan black market da yawa wallahi zan fita naje ta samo fetur na k'ona ku sai dai naje gidan yari wallahi mata ni ka auro ma ita baka da ikon cin ta nizan cita dan da kud'i na ka auro ta " Haba khadija dan allah kiyi hak'uri zance bazai cita ba duk bata taso ba amarya ce fa wannan daren shine dare mai daraja a garesu" To ina ruwa na kaji na rantse billahillazi'lah'ilah'ha illahuwa bazai cita ba idan kuma yana ganin wasa nake yaje wallahi sai na bari ya tube ya fara zan shiga na shar'be๐ŸŒsa " sadik kamar maraya haka ya koma a wajen


"Wallahi sadik duk laifinka ne meyasa zakayi aure da kud'in ta" Ahh to idan yana san matar sa ya bani kud'i na yanzu yanzun nan" akwai kud'in ne? Usman ya fad'a tare da kallan sadik " Girgiza masa kai yayi alamar babu.............................




" Khadija dan allah kiyi hak'uri kinga yanzu dare yayi " To ina ruwana da dare yayi ni kud'i na na jama ya bani kud'ina yanzu salin alim na kyalesa " Kud'inan basu yanzu amman da safe duk yarda za'a yi koda rabi ne za'a samosu a baki"Rab! rabi fa kace to wallahi gabaki d'aya nakesan kud'ina ni da zan basa rabi na Basa? " Hak'uri zakiyi " Dallah kun isheni da wannan kalmar hak'uri! hak'uri to bazan hak'ura ba aheeeeeeeeee " Allah ka muna maganin wannan masifar" Au nice ma masifar? Ta fad'a tare da nuna k'irjinta, to wallahi wannan soma ta'bine idan har baka bani kud'i na ba"



Amarya jin hayaniya tayi yawa yasa ta fito tare da tunkarar d'akin tun kafin ta isa bakin k'ofa d'aya daga cikin abokan sadik yayi aurin fitowa tare da fad'in" Wallahi juya ki koma d'akin da mijin ki bayada gaskiya tun abun bai shafeki ba" amarya jin haka yasa tayi saurin juyawa tayi d'akin ta



Su Usman sai hak'uri suke ta bata, dak'yar suka samu tace yaje d'akin, Usman yace" To kin amince ya kwanta da ita" Hmmmmmm wallahi bazai kwana da ita ba dan bazai cita ba " Khadija ki yi hak'uri su raya daren nan" Usman wai kafira ka d'auke ni ne nayi rantsuwa bazai yi ba Hmmmmm"



Bello yayi 'bangaren mama dan ya sanar da ita halin da ake ciki, duk da kusan duk abinda ke faruwa tanaji tak'i zuwane dan tasan idan taje abun zaiyi muni da yawa dan basa da gaskiya, bello na zuwa tun kafin ya kai ga magana ta tare shi da fad'in " Yi hak'uri kawai ka juya Dan bansan abinda zan fad'a ba" Mama da dai kinzo muje nasan zataji Maganar ki " Tabbas haka ne amman idan naje ban mata adalci ba amman ga waya ka duba number sadiya nasan idan tazo in Sha Allah komai zaiyi sauk'i" To mama, wayar ya amsa ya lalubo number kira biyu ta d'aga ya sanar mata abinda ke faruwa tace gata nan tafe,


Sadiya yayar sadik ce, khadija na ganin girmanta sosai,


Cikin k'ank'anin lokaci aunty sadiya tazo, zaunar da ita tayi tare da bata hak'uri da kalamai masu taushi tana kwantar mata da zuciya, Sannan ta hak'ura, Usman yaje gidan sa ya auno abinci aka fitarma da khadija kolo na rantsuwar da tayi, koda suka wuce ukun dare harta gota, ko wannen su ya bama matarsa labarin abinda ya faru, matan matsuwa sukayi safiya bata waye ba suzo gidan



Hadari ne ya taso khadija ta bud'e d'akin ta tayi shimfid'a dai_dai bakin k'ofa tayi kwanciyarta iska na kad'a mata,


Sadik zaune yake gefen gado yayi tagumi, amarya baccin ta kawai take cikin kwanciyar hankali, zuciyar sadik cike take taf da tsoro dan har yanzu bai lamun ce da hak'urin da khadija tayi ba,





Washe gari
Tun da safe yayi wankan sa ya baro gidan, khadija tayi wankan ta ta had'e cikin wata atamfa da ita da d'akin ta sai k'amshin suke zubawa, mutane ta antaru mai kid'i aka sake kira musu suka sa dije, rawa kawai suke tik'a.............................




Sun tik'i rawarsu bil'hak'k'i, anci an sha,an watse, da dare sadik bayan ya dawo yaje ya gaida Mahaifiyar sa ya dawo yayi d'akin khadija, fuskarsa d'auke da murmushi ya shiga d'akin,


wani k'amshin dad'i ne ya kaima hancin sa ziyara sai da ya lumshe ido, zaune ya ganta saman sallaya da alama sallah ta ida " Ahah uwar gida sarautar mata sai kinyi goma yaro zaiyi d'aya uwar gida ran gida, uwar gidana addu'a akeyi to a rok'a harda mu "ya fad'a tare da samun waje ya zauna, ya tsina baki tayi taci gaba da addu'ar ta sai da ta gama, ta juyo ta gaidasa, ya amsa, hannu yasa aljihu ya ciro kud'i ya sake sa hannu d'aya aljihu ya ciro, ya Mik'a mata, tasa hannu ta kar'ba tare da fad'in " Nawa ne anan?" Dubu d'ari da hamshin ne" su na baka? " Haba khadee ta kiyi hak'uri in Sha Allah zan cika miki saura wallahi wad'an nan ma dak'yar na samesu" ya fad'a cikin mairairaice murya hmmmmm kunsan tsakanin mata da miji sai allah, tausayin sa taji ya kamata, ta tashi taje ta d'auko masa farfesun kayan ciki da inna ta aiko mata, yana ci yana zuba mata albarka, bayan ya gama ta kawo masa waje ya wanke hannun sa yasha ruwa ya Mik'e dan dare yayi, ya nufi d'akin amaryarsa balkisu


Yana fita taji hawaye na mata ambaliya a fuska da ta goge sai taji wasu na k'ara zubowa, ga wani k'ololon bak'in ciki da take Jin yana taso ma, wai yau sadik d'in ta ne zaije d'akin wata mata, fashewa tayi da kuka mai ban tausayi, sai da tayi mai isanta Sannan ta tashi ta haye gado tayi kwanciyarta tare da karanta addu'ar bacci





Bayan sati d'aya da aure
Khadija zaune bakin k'ofar d'akin ta tana d'aura zobo a leda sadik na zaune daga gefe, balkisu ta fito daga wanka d'aure da wani guntun zane, tunda ta fito ta ajiye bokiti tayi tsaye sai ta d'aura zane ta kunce, tana wani tallabe_tallaben nono, khadija ta lura da abinda takeyi ta juya ta kalli sadik taga wandama takeyi dan shi baiko san tana yi ba, wata shewa khadija tayi tare da fad'in "Hhhhhhhhh allah kashe mijin mai kyawo ko bai kashe ba aure ya mutu yo wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwar sa " Ta fad'a taci gaba da k'ullinta, balkisu ta gyad'a kai tayi d'akin ta, sai gata ta fito sanye da hijab tazo tayi tsayen kan khadija ta rik'e k'ugu tare da kad'a kafa


"Khadija! Khadija!" Balkisu ta fad'a khadija ta d'ago tana kallan ta, Shima sadik ya d'ago, taci gaba da cewa " Idan kin isa ki sake maimaita abunda kika fad'a d'azu" Okay so kike na maimaita kenan? Khadija ta fad'a tare da Mik'e wa tsaye" Eh " tun kan balkisu takai ga rufe bakin ta khadija ta d'auketa da wasu irin zafafan maruka guda biyu Wanda yasa ta ganin walk'iya tayi saurin ja baya ta dafe kunceta, hawaye rata_rata , sadik yayi saurin tasowa tare da fad'in " Subhanallah meyake faruwa ne wai? Khadija akan me zaki mareta ? " Au bakaji abinda take fad'amin bane saboda tsabagen ta raina ni, wallahi bama laifin ta bane kai ka bata fuskarda zata rainani acikin gidan nan to wallahi kisani, ta fad'a tare da maida dubanta ga balkisu wacce hawaye ke mata ambaliya a fuska dan haryanzu rad'ad'in marin takeji , dai_dai nake dake dan zan saitamiki hanyarki naga tunda kika zo gidan nan kike min wata hikirkitar iskanci to wallahi mai gyaran miki zama ce anan mtsssssssssssssssssssssss" ta fad'a tare da zama taci gaba da aikin ta, juyawa tayi lufff ta shige d'akin ta, sadik har ya kama hanya ya bita yaga wani kallo da khadija ke masa, hkn yasa ya juyo ya koma ya zauna " Hmmmmmm ayi dai mu gani in tusa na hura wuta" khadija ta fad'a







Tun da sadik yayi auren nan duk wata hanyar da yake samu ta tushe ko kasuwa yaje haka zaita zama babu kasuwa, ita kuma khadija kamar kar yayi auren nan bud'i ya rik'a zuwa mata kyautukka taketa samu har inda batayi zato ba, yau ma tashin ta daga bacci kenan wani abokin baban su ya aiko mata da buhun d'angote guda biyu da katin d'in taliya biyu da dubu hamshin akai






Kalarta biyu na tufafin da ta cire da d'auko zata wanke, balkisu ta taso tare da fad'in " Aunty khadija wanki zakiyi? " Eh" Zauna ki huta kawai kawo na wanke miki" Aah barshi kawai nagode " Nifa nace ki kawo na wanke miki ai ba rok'ana kikayi ba" Ganin ta nace akan sai ta wanke mata yasa ta bar mata................................






*Addu'ar Wanda Al'amari Ya Tsananta A Gare Shi*

ุงูŽู„ู„ูŽู‘ู‡ูู…ูŽู‘ ู„ุงูŽ ุณูŽู‡ู’ู„ูŽ ุฅูู„ุงูŽู‘ ู…ูŽุง ุฌูŽุนูŽู„ู’ุชูŽู‡ู ุณูŽู‡ู’ู„ุงู‹ ูˆูŽุฃูŽู†ู’ุชูŽ ุชูŽุฌู’ุนูŽู„ู ุงู„ู’ุญูŽุฒู’ู†ูŽ ุฅูุฐูŽุง ุดูุฆู’ุชูŽ ุณูŽู‡ู’ู„ุงู‹.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.
Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki


Idan ta wanka ita kuma khadija ta d'auraye ta shanya har suka gama, bayan sun gama khadija ta nemi waje ta zauna dan ba aikin da zatayi balkisu a da girki,


Kusa da ita ta tazo ta zauna tare da fad'in " Aunty khadija yau me za'a dafa ne" To, khadija ta fad'a tare da mata kallan mamaki " Ki tambayi mijin ki mana" Haba aunty ai babban yatsa ko bayacin tuwo yana kyauwo a miya ai idan baya nan kece matsayin sa a gidan nan. gashi wallahi koda ya fita yace bayada ko sisi bare ya bada kud'in cefane "To ki jira ya dawo"Wallahi aunty ba girman ki bane ace muna da kamar ke a gidan nan amman ace wai sai mun tsaya jiran har ya dawo aunty ki dai duba "Hmmmmmmmmmm naji je ki samo waje ki auno shinkafa" Yawwa aunty ko kefa Allah dai ya biya" ta fad'a tare da Mik'ewa taje ta d'auko wajen da zata zuba tashi d'akin khadija ta auno shinkafar, ta fito



"To aunty khadija gashi nan me za'a yi allah ya gani na gaji da cin shinkafa kullum shinkafa " To kiyi muna dambu" Wallahi gashi na jima banci shi ba " To sai kiyi muna " Aikuwa, to kud'in markad'e da kayan Had'i" Ahhh wai kina nufin komai ni zan bayar " khadija ta fad'a" To aunty ni wallahi bani da ko sisi dole kece zakiyi hak'uri ki bayar allah ya baki lada " uhmmmm d'auko jaka na baki kud'in" To, ta d'auko jaka ta Mik'e mata naira dubu tace "gashi a siyo kayan miya da kayan ciki tun da akwai sauran kaya kayan miya ne kawai babu" kar'ba tayi ta fita taje mak'otansu ta samu wani yaro ta aike sa ta dawo takai redar shinkafar, nan tayin su






Tun daga lokacin suka shirya, muddin khadija na aiki to balkisu sai tazo ta tayata itama hakan take, sai dai abu d'aya wanda khadija ta lura dashi shi ne, balkisu nada shegen kwaud'ayi, sannan idan taga anata zuwa siyan kaya wajen khadija sai taga tana wani ciccin magani, alamar hassada





Sadik ne ya shigo gidan, d'akin khadija ya shiga yaga bata nan, d'akin balkisu ya shiga, yatsina fuska ya rik'a yi tare da bin d'akin da kallo, wai d'aki kamar ba mutum a ciki ya fara k'ura ga wani hanamin bashi_bashin da yake tasowa, ga kaunukan da akaci abinci nan zube tsakar d'aki har sun bushe, balkisu na kwance tana sharar baccin ta, girgiza kai yayi tare da jan tsaki mtsww ya fito daga d'akin, yana fitowa sai ga khadija, kallan ta yayi daga sama har k'asa sanye take da hijab har k'asa




Daga ina kike na duba ban ganki ba? " Daga wajen mama"okay, muje ki zubamin abinci " ka manta ba fa girkina bane " ina sane nidai muje " Bata nan ne? " Wani kallo yayi mata bata sake cewa komai ba ta wuce ya biyo bayanta, tana shiga d'aki ta kau'be hijab d'in ta, sanye take da riga da wando, Wandon ya matseta sosai sai rigar y'ar guntuwa idan ta d'aga hannun ta ana ganin cibiyarta, rigar kawai ce a jikin ta ko bre bata saka ba, wasu irin yawu sadik ya had'a, ya kasa jurewa sai da ya taso ya rungumota ta baya tare da zura hannayensa gaba ya d'ora akan na shanunta yana..................... juyowa tayi suna fuskantar juna, ta d'ora hannun ta a kafad'arsa tare da zagayowa, shi kuma hannayensa na kan k'ugunta, gira ta d'aga masa tare da fad'in " Yane nayi kyau" Sosai sosai kayan nan sun miki kyau" ya fad'a yana shin_shinan daddad'an k'amshin dake fitowa a wuyan ta, bakin su ya had'e waye d'aya ya shiga tsotsa ita ma ta biye masa sun d'au yan minutes a haka, ganin yanan san cire rigar da ke jikin ta yasa ta kaunce kanta daga gare shi tare da dai_dai ta natsuwar ta tace" Zauna na kawo ma abincin" wayyoooooooooo sadik ba haka yaso ba.................................








*ZUWA GARE KU MATA โœ*
Kishin da bazai qara miki..........................
martaba da kima a idon miji ba, kishin da bai sa kin samu qarin kusanci a wajen miji ba, kishin da ba zai sa ki qoqarin gyara da kyautata dabi'un ki ba, kishin da ba zai sa ki qara kusantar miji da mahaliccin ki ba, kishin da zai sa kimar ki ya zube, miji ya nisance ki ko ki nisanci miji da mahaliccin ki ko ki koma bibiyar 'yan tsubbu

Tabbas wannan ba kishi bane rashin hankali, rashin sanin daraja da mutuncin kai da qarancin tsoron Allah da son zuciya ne, muddin kika biyema irin wannan kishin tabbas zai kai ya baro ki duniya da lahira ko kiyi asarar duniya da lahirar ki.

*๐ŸคฒYaAllah sa mu gane gaskiya ya bamu ikon binta*









_-_Perfectly Pen's_-_~*โœŠ 2024


*~_-_Perfectly Pen's_-_~*๐ŸคŸ


*Team One.*


*๐ŸŒน perfectly Pen's together with five Talented's โœ๏ธโœŠ*


*Our Ongoing Book's...โœ๏ธ*


*1_PRINCE ASAD.*
*Free Book. BY: Zieey Dodo.*

*2_SHIRYAYYIYAR ฦ˜ADDARA.*
*paid 500*
*Season one Free. BY: Queen Kainaat.*


*3_TSANTSAN SO.*
*Paid,500. BY: Nainarh KD Nkd's.*


*4_MU ZUBA MU GANI.*
*Paid,300. BY: Oum Yasmeen.*



*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daษ—aษ—an littattafan mu masu cike da ilmantar wa faษ—akarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaษ—antar wa.๐Ÿ’*



*๐Ÿ”ฅKada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters ๐Ÿ”ฅ



Abincin ta kawo masa yaci ya k'oshi, Sannan ya tashi ya koma kasuwa duk da ba ciniki, daya fito ko d'akin balkisu bai sake lek'awaba ya wuce, har yanzu ko tana nan tana sharar baccin ta,

Koda ta tashi daga baccin taga lokacin zuwan sa cin abincin harya wuce ta Mik'e ta fito khadija ta zaune tana gyaran waken suya " Aunty sadik bai dawo cin abinci ba ne? " Ya dawo mana ai har yaci ya koma" Okay shine bai tashe ni ba" To kinsan ba dad'i mutum na bacci a tadasa" Uhmmmmmm" ta fad'a ta koma d'aki, bud'e kulolin abincin tayi taga ba abinda aka ta'ba a ciki, ta sake fitowa " Aunty " Naam " kin ce ya dawo yaci abinci? " Eh " To ai ni banga anci komai ba cikin abincin " Eh dayake ba anan yaci ba wajena yaci " Bangane ba" balkisu ta fad'a a tsatstsaye " Kamarya kenan? Khadija ta fad'a tare da ajiye waken da ke hannun ta " Ahh to naga dai bake ke aiki ba taya zai je wajenki yaci abinci ai wannan salon munafurci ne " Yau ga ikon allah shin yazo kina bacci kuma yunwa yakeji yace nazo na saka masa abinci shikenan sai nace masa aah ko tunda ba girkina ba ne sai nabar mijina da yunwa bayan Kuma ina da abincin to wallahi ki sani koda bani da shi yazo wajena yace na saka masa sai naje na nemo masa rainin wayon banza kawai " Ah ah naga kina wani zazzaburomin sai kace wani abun na fad'a bancin kuma gaskiya na fad'a ke idan girkin ki ne namiki hakan zakiji dad'i? " Me zai Hana wallahi dan kinyi haka bazan ga laifin ki ba daga ma kin taimaka min kin basa wallahi ni nace balkisu muddin yazo gidan nan ranar girkina ya tarar da ina bacci wallahi jashi d'akin ki ki basa abinci ke har ruwan wanka kai masa abu d'aya kawai nasan bazan lamunce ba ranar girki na yace ya kwanta dake, bare nasan bazai aikata hakan ba dan yasan haramun ne bancin wannan wallahi ni ba abinda zai damuna " To nidai ban lamunce ba ehhheeeeeeeeeeee kowa yayi aikin sa ranar girkin sa " Ke balkisu wai ma da kika zo kika tasani gaba ni nace kije kiyi bacci sannan ki bari shi wanda ya aika tan idan ya dawo sai ki tasasa a gaba kiyi masa fad'a kar ya sake yin haka " Ai ni bashi yamin laifi ba bare kice na masa fad'a" Ohh wato ni ce nayi laifin ko" khadija ta fad'a tare da Mik'e wa tsaye" Ke naga kina son gayamin magana to wallahi bazan d'auka ba dan mai maganin ki ce a wajen nan ina san muzauna lafiya gidan nan amman daga alamun ke bakyada buk'atar haka muje a hakan duk yada ki ka zo nima dai_dai nake da ke a gidan nan " Magana dai ceee na fad'a ba uban da ya isa ya hanani fad'an abinda nayi niyya" To tsaya daga nan dan bana jurar zagin iyayena idan ba haka ba wallahi yanzu na ma mutum hailar baki " Hmmmmm wai hailar baki" To idan tantama ki ke kiyi ki gani wallahi bakin ki sai ya cika da jini " Balkisu ta bud'e baki ta sake magana khadija ta fere hannun ta wanka mata mari sai da ta fad'i, ta taso tayi cikin khadija, khadija ta samu taja k'afafuwan ta sai k'asa, balkisu ta fad'i khadija ta haye Samanta ta shiga dukan ta, da taji azaba ta fara ihu na neman taimako,



Mama da taji ihun balkisu yayi yawa yasa ta taso tayo wajen su, khadija ta gani ta kai balkisu k'asa ta haye sai dukan ta take da sauri ta k'arasa tare da fad'in " Subhanallah! Subhanallah khadija meyake faruwa ne? " Dak'yar mama ta samu ta raba su, balkisu ta koma gefe hawaye da majina sai ambaliya suke a fuskarta " Dan Allah gobe ki k'ara"khadija ta fad'a " Wai meya had'a ku ne ? Mama ta tambaya" Mama wai................................................. khadija ta zayyano mata duk abinda ya faru " Gaskiya balkisu bakya gaskiya ai dan ma abun bai miki dad'i ba ba ita ya dace ki yima magana ba shi zakiyi ma maga cikin hikima amman gashinan yanzu wa gari ya waya bakin ki harya fashe " Eh ina ruwan ki bak'ar muna fuka ai daman nasan goyon bayan ta zakiyi" khadija da mama suka Kalli juna mama ta girgiza kai, khadija tasa hannu zata janyo ta tayi saurin rugawa tayi d'aki tare da rufewa " Ai da kin tsaya k'aramar mara kunya kawai" khadija ta fad'a tare da juyowa tana bama mama hak'uri akan abinda balkisu ta fad'a


" Karki damu, amman kema ya kamata ki rik'a hak'uri ki rik'a sassauta zuciyar ki " To mama in Sha Allah...........................










Washe gari
Balkisu zatayi girkin rana, khadija ta kar'bi girki, gashi sadik bai bata komai na girki ba, da ya riga da ya rabar da khadija zata bayar dan yanzu bayada k'arfin da zai iya ciyar da gidan khadija ke ciyar dasu gabaki d'aya, dan haka yana tashi yayi tafiyar sa, zaune take bakin k'ofar ta tana maganar zuci, Hmmmmm gashi mun samu sa'bani jiya bani da daman da zance naje na kar'bo shinkafa na dafa to ya zanyi mtsssssssww kowa ya ci da kansa to koda ma ance haka ita me zata ci?



Ita dai khadija na nan na faman aikin tarbon miji ana had'a

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment