Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

UWAR MIJI


Da sunan Allah ne rahama me jikai

Gargadi

Banyar da wani ko wata yayi amfani
Wani shashi na littafina ba batare da
Izina naba ko mai da shi document
Ko masi YouTube channel su mai
Da shi audio

In kunne yaji......jiki ya tsira
Wannan labarin ƙirƙirar rene duk
Yaga yayi dai-dai da rayuwar sa
Ya dauka armashi ne......



Bisimillahir rahamanir rahim


*🍁🍁UWAR MIJI🍁🍁*






PAGE 1





*BY AISHA YAHAYA TANKO✍️*





~Wannan labari ba wai na rubuta shi dan cin mutuncin wata ba, kawai nayi shi ne saboda nishadanarwa da kuma ɗaukar darussa akan abinda ya kunsa~

*Ina neman addu'arku masoyana akan FATIMA IBRAHIM MUHAMMAD Allah ya yaye mata lallurai da take damunta😭 ga dukkan wanda ya karanta pls ya taimaka sadaka ce Allah ya bata lafiya da dukkan musulmin duniya baki daya* 🙏🏻🙏🏻


Hajja Sarai ce zaune a ɗaya daga cikin kujerun dake katafaren falonta cikin kasaita take magana tana kurbar lemon gwangwani tana ajiyewa ta ajiye lemon tana bin ko waccen su da kallo,yayin da suke zube akan kafet ɗin falon magana tayi da cewa.


"nasan baku san dalilin da yasa na taru ba koh, to inaso Ku bani hankalinku Ku buɗe kunnuwanku ku ji abinda zan faɗa muku,da farko dai kunsan zaman aure shi ya kawo Ku gidan nan kuma kun san koni wace a wajenku ni dai UWAR MIJI ce ba uwar Ku ba ina da sharadan wanda zan kafa muku game da zama da ƴaƴan na duk wadda tabi su zata sha romo kuma haka duk wadda ta ki binsu zata fada cikin rijiyar me zurfi bani da farin cikin daya wuce farin cikin su nasan kun auresu ne dan so da kauna kuma nasan ko waccen Ku bazata rasa buri ba na ganin ta mallaki wani abu daga wajen mijinta to inaso ku kiyaye ku san zaman aure bauta ne ba wai hutu bane kar kuga kun shigo daular da ko wace ƴa mace take mafarkin samo sannan ku dage da yiwa mazajenku biyayya da kuma yi musu fatan alkairi sannan kunsan dole ku dinga yiwa kanwarsu zahra biyayya itama tare da faranta mata rai da kuma gujewa bacin ranta nazo gareki Khadijah karki dauka dan mahaifiyarki aminiyata ce shi zaisa na raga miki to ba wannan maganar a wanna lokacin ki manta da wannan alakar ki yi amfani da aure kika zo".


Ta kara kurbar lemon sannan ta kara gyara zama tace.

" ke kuma Salma karki duba dan gantakata dake na ƴar kanwata ki cireta acikin ranki na dawo gareki Amina kema zaman aure kika zo ba wai ki nuna gidan wan mahaifinki bane dukkan ku cire alakar sanayya kuyi amfani da ni UWAR MIJIN ku ce fatan kun gamsu da bayanai na daga karshe inai muku fatan alkairi sannan ku zauna lafiya ko akwai wadda bata gamsu da bayani na ba to tayi magana tun kafin na shiga daki naga dare ya fara.

Gaba daya suka amsa da Aa ko wacce ta mike ta nufin sashenta.

Salim da Adam da Aminu suka shigo a tare suka rusuna agaban Hajiya suna gaisheta ta amsa cike da nuna jin dadinta ta sawa auren nasu albarka sannan ta musu kashedi akan su kiyaye dan yanzu bata shirya karbar jikoki ba.


Gabaa ɗaya suka zaro ido lokaci guda Aminu ya yi gyaran murya ya soma magana.

"Amma Hajja karki manta mutum baya shiryawa kansa rayuwa kuma duk wanda yai aure burinsa ya tara zur'ia tunda ya raya sunnar ma'aiki".

Baka da kunya ne Hajjan kake fadawa irin wadannan kalaman to wallahi idan baka bata hakuri ba yanzu zaka fuskanci hukunci .

Aa ku rabu dashi ya fada min abinda yake bakinsa ai yau yayi aure dole yaga kamar kanmu daya amma inaso ya sani duk abinda zai fada baze sa na janye kudirina ba.


Dan Allah Hajja ki gafarce bawai na fada dan na saba miki ba sai dan na tunasar dake amma ki yafemin kimin afuwa na tuba yana gama fada be jira yaji abinda zata ce ba ya shiga sashensa cikin sauri.

Nan ya iske Salma tayi tagumi hannu biyu hawaye na zuba ta kuncinta cikin sauri ya karasa inda take hannu yasa ya fara goge mata sannan ya ajiye mata ledar a gabanta..



```Ya kukaji wannan page ɗin, comment ɗinku shine ze bani ƙarfin gwiwar da zan ƙara sa muku```




🍁🍁UWAR MIJI🍁🍁




PAGE 2 ✍️




*BY AISHA YAHAYA TANKO🥰*






Salma kiyi hakuri nasan rabuwarki da umma akwai damuwa amma ki sani dama wannan ranar zata zo ko ba dade ko ba jima tunda dole za kiyi aure aike gida kika dawo tunda Hajja uwace a gareki ko da ban aureki ba.

Nifa ba wai rabuwa da Ummata ne yake damuna ba kawai dai ina tuna wani na daban da kuma irin rayuwar da zan fuskanta ta zaman aure.


Duk ki bar wannan maganar ki tashi muje muyi alwala muyi sallah muci abinci dan ni rabon dana sa wani abu a cikina tun a wajen dinner shima ke kika bani 2 spon ɗin nan,nan ya fara kici kicin cire babbar rigarsa yai wurgi da ita gefe guda suka mike a tsaye a tare suka nufi Toilet.

Tun bayan tafiyar Aminu Hajja ta kasa zaune da tsaye a cikin falon ta dubi su Salim da Adam tace kar kuyiwa Aminu komai Ku kyaleshi zan zauna da shi na fahimtar dashi dalilina na yin haka nasan ze gane manufata

Ta tsaya a tsakiyar falon hannu tasa tai musu nuni da su tafi wajen amarensu,suka mike cikin sanyin jiki kowannesu zuciyarsa cike da sake-sake ya doshi wajen amaryarsa.

Shigar Adam dakin ke da wuya ya tarar da khadija ta manne da bangon dakin tana faman sharbar kuku tamkar wadda akai mata auren dole turus yayi abakin kofar yana mamakin ganinta cikin wannan halin ya soma kiranta.

"Khadija! Khadija!!khadija!!! ko ba kece wadda muka shiryawa kanmu rayuwa ba kina tuna kin min alkawari adaren da muka tare zaki shayar dani zumar soyayya amma sai gashi tun kan aje ko ina kina zubar da hawaye pls ki dakata haka kin wannan ranar tana cike da daraja da kuma dumbin alkairai".

Ya karaso inda take hannu yasa ya yaye mata mayafin dake jikinta yana dubanta haba kanwata saboda kin rabu da Abbanki shine zaki sa kanki cikin wani hali ko dan ke shalelansa ce kin san dai nan ma gida ne tunda Hajja uwace garemu yanzu ki bar wannan kukan haka zan kira miki shi Ku yi magana kinji.


Ta dago Kai cikin sauri ta dakatar dashi karka kirawo shi bana bukata ka kyaleni da radadin da zuciyata takeyi na....

Ya saurin rufe bakinta me kike shirin fada ne ki tashi mu shiga ciki ki samo kici kazar nan ki huta nasan kina tare da gajia ya kama hannu suka shige cikin daki.

A can bangaren su Salim kuwa tun bayan shigarsa wajen amarya yaci karo da kwandon masifa duba daya yai mata yace inaso kiyi hakuri be kamata a irin wannan ranar mu sami matsala ba kin san dai Hajja sarai mahaifiyata ce dan haka ya zama dole kibi dukkan sharadin data kafa muku idan har da gaske kina min soyayyar da baki taba yiwa kowa ita ba koda ban aureki ba nan gidan wan mahaifinki ne inaso ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya ya zamana munfi kowa jin dadi kinga yanzu idon kowa yana kan gidan nan tun bayan rasuwar Baban mu mutane suka zuba ido suka yadda zamu kasance da ke kin fi kowa sanin wace Hajja sarai ba sai na fada miki ba kiyi hakuri kisha koda ruwana ne dan zuciyarki ta sami sauki.



Washe gari ne Amare suka sha ado suka nufi sashen Hajja Sarai anan ne zasu dimga cin abinci an shirya musu abinci iri daban daban Hajja Sarai ta dubesu tace.


"Ko wace zan sa mata ranar da zata dinga girki a gidan nan da kuma lokacin yinsa sannan bazan sallami su karime ba, zansa su dinga taimakon kon wajen gabatar da girki sannan zasu dinga nuna muku abinda baku gane ba zaku su sanar daku irin abincin dana fi so fatana anan ku bani hadi Kai mu gudu tare mu tsira tare".


A yanzu Amina ce zata zubawa kowa abincin da zaici amma inaso ko wacce ta fadi irin wanda take sanci .

Nan da nan Amina ta fara kokarin buɗe katafaren plas da aka shakareshi da zabi ta fara zuba Hajja Sarai ita dai kawai tana binta da kallo bayan an gama cin abinci ne Hajja Sarai tace.


"Inaso nan falon ya zama wajen da ku dinga zama kuna hira bana san ku yawaita zaman daki kuna shirman banza da mazajenku idan ba kwanciyar bacci ba ba abinda zai dinga mai da ku dakunan ku".

Cikin isa take maganar ta kara gyara zama ta dubesu tace.

"kuma gobe da yamma jirgin su zahra zai sauka inaso ku san abinda ya dace ai mata na taryarta".



KO wacce zuciyarta ta cika da sake sake



Mu hadu a page 3

🍁🍁UWAR MIJI🍁🍁*



PAGE 3




*BY AISHA YAHAYA TANKO✍️🌷*



Gaba daya suka amsa da cewa Allah ya sauketa lafiya tunda kin bamu wuka da nama zamu san abinda ya dace ai mata.

Cewar khadija.

Hajja ta fara kwallawa karime kira nan da nan ta amsa tare da zubewa kasa a gabanta.


gani ranki ya dade ai min afuwa banji kiran da wuri ba ina can gyara inda wajen mukai girki ne.

Hajja ta ya tsine fuska ta soma magana cikin isa inaso ki tsara musu ranakun da ko wace zata dinga girki a gidan nan sannan kuma ke zaki dinga kula dasu kina taimaka musu saboda abin yafi tafia dai-dai ita kuma Hanne zata dinga shirya mana nan falon a yayin da zamu ci abinci idan mun gama kuma ta dinga kwashewa da fatan kin fahimceni.

Ta kara rusunawa tare da jinjin mata to ranki ya dade duk abinda kikeso shi za'ayi da girman kujerarki tana magana ta mike ta fara kwashe plas din abincin.

Hajja yanzu nasan ko waccen Ku tana bukatar kebewa da mijinta to inaso Ku sani bawai zaku dinga shagaltar dasu ba Aa nima ina da bukatar san kasancewa da ya'ya'na tare muke gudanar da kasuwan mu.

Zan bawa ko wacce awa daya da mijinta nasan bazaku rasa abinda zaku tattauna dasu ba Ku tashi Ku tafi na sallame Ku suma yanzu zasu biyo bayanku.

Haka kuwa akai suka tashi a tare ko wacce jiki a sanyaye zuciya cike da sake-sake

Tafiya suke ba waiwaye sannan suka hade waje guda nan fa ko wace ta bayyana abinda yake cikin ranta daga karshe khadija ta ce amma fa mu hade kanmu ta nan ne zamu iya samun biyan bukatun mu tunda ko wacce tana san mijnita.


Salma ta bude baki tace ni duk ba wannan ba kun san kuwa abinda Hajja tace musu.



Suka amsa da Aa
Tab to cewa tai ita yanzu bata shirya karbar jikoki ba ai kunga tazo da bidi'a da kuma san rai tunda ba itace zata bamu haihuwa ba da bata san karbar jikoki ai da sai bari kar tai musu aure yanzu sai ranar da taso karba sai tai musu kawai.

Tab! di jam da sake ni kam bazan lamunta ba saboda dukiyar data ke takama da ita ai darajar wan Mahaifina ta sameta daya mutu ya barta nifa a shirye nake da aiwatar da komai acikin gidan nan tunda tace ita uwar miji ce to ni kuma matar ɗan ce tace yanzu mu zamu dinga girki agidan nan mun amince sannan ta kafa wasu dokoki marasa amfani da hujja duk dan nata ra'ayin.

Hajja ta kara gyara zama tana kurbar lemo kamar kullum tace.

" Ku sani ina nan akan bakana sai nan gaba zan fayyace muku abinda nake nufi tasa hannu ta dauki wayarta ta kunna ta kunna camera idonta ya gane mata surukan nata a yayin da suka taru waje guda murmushin mugunta tayi tace a fili nasan haka zata kasance amma muje zuwa ni Hajja sarai bame ja dani sai ikon Allah tana gama gani ta kashe wayar tai wurgi da ita gefe guda taja tsaki.

"Ku tashi Ku tafi wajen matayen Ku kar amanta da lokaci".

Sai kun fito nima zan koma daki na huta kafin rana tayi Salim ya miko mata sandanta ta karba ta nufi cikin daki.

Salim da Adam da Aminu suka tattauna akan matsalar Hajja da kuma irin dokokin data kafa musu Aminu yace nifa gaskiya Yaya zan iya dauke matata mu bar kasar nan in yaso ma dinga waya daku nifa nayi aure ne dan na sami nutsuwa da kwanciyar hankali ba wai dan nasha wuya ba kuma gaskiya inaso ya'ya'

Haba Aminu haka zakai mana kar na kara ji kace zaka bar kasar nan muyi hakuri da Halin Hajja ita haka nata tsufan yazo dashi .

Duk abar wannan maganar kun san yadda tana daki amma duk abinda da muke idonta yana kan mu dan nasan yanzu ta gama ganin mu ga kuma wani babban tashin hankalin gobe zahra zata dawo ta kammala karatunta kun san kuwa akwai babban kalubale Allah dai ya kyauta inji Adam nan kowa ya kama gabansa ya nufi inda matarsa take.


Amina ce zaune gefan gado ta hade rai kamar wadda akaiwa sakon mutuwa tana jin sallamar sa ta mike tsaye ta nufo shi ta tsaya a gabansa tace.

" Yaya Salim dama haka zama yake da uwar miji......"

yai saurin dakatar da ita kin san kwa abin da kike fada UWAR MIJI fa kike ce wato Hajja ba uwarki bace kenan tun daren jiya na fara ganin take takenki zan lamunci komai amna bazan zuba ido naga kina raina min uwa ba saboda duk duniya bani da kamarta ki iya bakinki .

Hawaye cim mata hannu tasa tana gogewa cikin kuka ban san haka zaman mu zai kasance ba Yaya salim na aureka dan so da kauna da kuma dangantar dake tsakanin mu nasan da Baba yana da rai zai fi kowa murnar hakan kuma zai daukeni tamkar ya'r cikinsa sai gashi yau na auri ɗan daya haifa kuma matsala zata kunno kai.

Salima jikinsa yai sanyi nan ya san akwai dalilin da yasa Amina ta fadi haka to shi yanzu bashi da abin cewa sai dai ya kwantar da kai bata hakuri kawai dan yana mutukar kaunar matarsa.

Nan ya fara rarrashinta yana bata hakuri Har ta hakura aka ci gaba da gudanar da amarci.

A can bangaren Hajja kuwa tun bayan data ga su salim sun tsaya suna tattaunawa tasan akwai abinda maganar dasu kai amma dai bazata ce musu komai ba ita dai tana nan akan bakanta.

Tana magana tana duban lokaci nan ta fara kokarin kiran wayar cikin gida ne taji sallamarsu sun shigo a tare ko wanne fuskarta cikin annuri ga kuma wani kamshi da sukeyi nan tace musu kun cika alkawari hakan ya nuna min bazaku tsallake dokata ba ganin yadda lokaci ya karato ku tafi kasuwar idan kun dawo sai musan abin yi ina matan naku duk ba wadda ta iya rakoku balke tai muku addu'a.

Salim ya fara sosa keya yace ai Hajja kar hakan ya zama laifi shi yasa muka dakatar dasu kafin su karaso nan.

Tayi murmushi amma salim kayi kyan kai kuma ka cika Babban dan Alhaji Mudi Baba kana gudun bacin raina sannan baka taba yi min karya ba amma a yanzu zuciyata ta fara gasgata ka inaso kai saurin dawo da gaskiyar Ku tashi Ku tafi Allah ya tsare.

Salim ya buɗe baki zai magana tai saurin dakatar dashi.



UWAR MIJI🍁🍁*



*PAGE 4 and 5*




*BY AISHA YAHAYA TANKO✍️*



*AMAZING WRITER'S ASSOCIATION💦*




Haka suka fice daga falon cikin ba wanda yayi kowa magana har suka isa inda aka tanada domin ajiye motoci kowa ya zaro key dinsa ya fara cicin buɗe motarsa cikin hanzari bala ya nufi get dan buɗe musu ya lura yau basa cikin walwala dan alkairin da su masa yau wanda ya dube shi balle shi, bayan sun fita ne ya koma kan bincinsa ya zauna ya kunna redion sa yana sauraron labarin duniya.

A can bangaren su Amina kuwa tun bayan fitar Salim ta fara tunanin yadda zata aiwatar da girkin nan to amma tunda karime zata taimaka min komai zai zo min cikin sauƙi, ji tai ana kwankwasa mata kofar tai zumbur ta miƙe ta amsa da shigo mana.

Karime ce ta shigo tana cewa.

"Sannunki Hajiata yau ta kanki za'a fara tun ɗazu nake tsumayinki ki fito muyi girki naji shiru shine Hajjajuna taban umarnin kiranki fatan dai bazaki damu ba,kar mu bata lokaci kin san idan taga na jima zata iya zargin mu saboda ko ina a gidan nan zagaye yake da camera".


Karki damu bari nazo mu tafi Karime ta bawa Amina hanya ta wuce tana gaba da ita har suka nufi wani baban kicin wanda aka kawata shi da kayan girkin zaman tsayawa tai tana tunanin shin ta ina zata soma ita dai a saninta bata taba sanin abincin da Hajja tafi ci ba.

Amma ta tuna wata rana suna hira da Yaya Salim yake bata labarin irin abincin da Hajja tafi ci bari wata zuciyar tace Aa ki tambayi karime ta fayyace miki komai mana karki tsaya batawa kanki lokaci.

"Karime karki damu ni zan miki komai Hajiata rigima ce irin tata ta yaya daga zuwanku za'a ce Ku fara da girkin gidan nan me wahala wanda duk iyawarka baka gwaninta kin san Hajja tana fama da ciwon hawan jini dole sai kinyi taka tsantsan wajen sarrafa abinda zakiyi amfani dashi zan baki shawara idan kikai amfani da ita zaki tsallake duk wani tuggu da makirci bazan manta dubin alkairan da mahaifin yai min ba dashi da marigayi wato me gidan nan ki dinga kokarin zuwa barin Hajja kina gaisheta sannan ki gujewa bacin ranta tunda kina san Yayanki ki kuma danne duk wata damuwa da zaki fuskanta sannan karki nuna gajiyawa ko kosawa ki ki jikinki ita din maca ce me san kanta da kuma san ya'ya'nta kuma kinsan gobe Auta zata dawo to shima wannan dawowar ta akwai babban kalubale tana da iyayi gashi kuma duk abinda za'a mata baya burgeta hatta yan'uwanta basan zamanta agidan nan saboda rashin mutunci ga wulakanta mutane bata san darajar kowa ba, ke zata iya raga miki tunda kun hada jini da ita kuma kunyi wasa tare lamarin ba'a cewa komai.

Amina naji kince ko ina na gidan zagaye da camera amma naga kinai min bayani ba tare da fargaba ko jimami ba .

Ta daga kai ta dubi ko ina tace ai nan babu camera shi yasa na saki jikina yanzu me kike sha'awa Hajja taci .

Ni ina zan san abinda zata ci ki dai taimaka min muyi girkin tare bazan sakar miki ba.

Nan da nan kamshin ya cika gidan hatta hajja dake kashinhide a falonta ya cika mata hanci ta girgiza kai ta matsa remote din dake hannuta nan da nan Tv dake manne jikin bangon falon ta kawo hoto da sauti ta kwallawa hanne kira ta amsa cikin sauri ta gurfana gabanta gani ranki ya dade ko akwai abun da kike bukata ne.

Cikin isa take magana.

" inaso ya haɗa min kayan marmari yanzu san ki shirya mana wajen da zamu ci abinci ki kunna turaren wuta kiyi amfani dana wajen yar barno idan kin gama kije dakin auta ki kar kaɗe ko ina ki gyara mata shi tab ki mu kunna mata turaren wuta ki tabbata kinyi yadda ya kamata tashi kije".

To ranki ya dade duk abinda kikeso shi za'a yi na barki lafiya Uwar dakin mu me runbun alkairi taji dadin yadda Hanne tai mata saki murmushi.

An kammala komai an kuma jiresu a kinda ya kamata ne kowa ya hallara a falon Hajja hatta su Salim sun dawo gida da wuri yau abinci ne iri-iri Amina ta fara zubawa Hajja sannan ta zubawa Salim shima ta zubawa kanta,ta koma ta zauna.


Yanzu kuma ko wacce ta zubawa mijinta da kanta ita ta gama nata aikin na dare kuma Karime da Hanne su zasu dafa mana.

Nan fa Khadija da Salama suka fara ƙoƙarin aiwatar da abinda Hajja ta umarce su, wajen yayi tsit kowa da alama abincin Amina yayi daɗi ga kamshin ya turare da wajen yake kowa ci ya sha yayi kat bayan an kwashe kayan an Kuma gyara waje yayi tas kamar ba'a bata ba.

Hajja tace da Salim.

"Inaso ka kirawon Musa me hoto dan inaso zanyi hotuna da surukai da kuma ya'ya'na da kuma Autar Hajja kuma uwata ta kaina sannan inaso a haɗa mana walimar dawowar ta gida zan bawa ko wanneku damar ya gayyato mutane biyar dan suzo suci su sha su kuma taya Auta murnar kammala karatunta, sannan inaso idan ko wacce zata tafi a bata naira dubu 50 duk saboda murnar dawowar Zahra".

Kowa ya buɗe baki cike da Mamaki Salim yace.

" Gobe kike san ayi walimar ko yaya?".

Hajja cikin isa tace.

"Kar ka manta irin tarin dukiyar da muke da ita ya isa ace muyi amfani da ita a duk lokacin da muka ga dama bawai sai mun batawa kanmu lokaci ba duk na raba kwangilar abincin da za'a dafa,sannan kuma su Karime zasu soya kaji da kuma abinda ya sauwaka, ku kuma ku

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment