Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara kallon jikina sosai, ban ga abin da na manta ba.

"What?" Na faɗa cikin jan aji.

"Mayafi,ko kin manta yanzu ke matar aure ce?"

Na tsaya na ƙare masa kallo, amma shi ko motsi bai yi ba,a hankali na nufi inda na san zan ga su Mansura, sannan na yafito ta, ta iso da gudun saurinta, sannan na umarce ta da ta ɗauko mini mayafi wanda yake iri ɗaya da takalman da jakata, cikin rawar jiki ta ce to.

Ko kallon inda yake ban yi ba, na wuce zuwa waje abina,bai ce ƙala ba, shi ma na ga ya taso ya biyo bayana. Wani abun al'ajabin kuma shi ne dakarun tsaron shi suna nan tsaye ƙam suna jiran shi, a zuciyata na ce lallai wannan mutumin da mulkin masifa yake.

Limousine motar nan mai ƙofa uku, wacce ta bugeni a titin Ahmad Bello Waya, ita aka buɗe mini na shiga cikin takaicinta, ta gefe ɗaya na ga ya shigo shi ma,a inda bai fi sakan biyu da zama ba, na ga labulaye baƙaƙe sun sauka da kansu, kenan an rufe mu,ko direban ma bana gani.

Kujerar gefenmu ba kowa, sai tsakiyarta naga ƙaramar talabijin na aiki,sanyi na ji ya sauka a lokaci ɗaya, tare da wata fitila mai kalar duhuwa ita ma a zuciyata na ce lallai dole a dinga kaɗe ƴaƴan talakawa ba a sani ba.

Yanda ya shige ƙwanar kujerar da yake,ni ma haka na ƙwanta linkif a cikinta,tsawon mintuna goma sannan na ga ya cire gilashin fuskarsa da ƙyar, sai ga wani ɗan tebir ya ɓullo daga ƙasa da ƙwalaban lemu amma ba irinsu fanta ba,da kofunansu, wasu ƙwalaben ne abin kallo, don ma ina ƴar gidan masu da shi, da sai in ce giyoyi ne ba lemo ba.

Ya ɗora gilashinsa a sama, sannan yasa hannu ya janyo gaban tebirin, sai na ga ashe ɗan firji ne ya zaro robar Ice Cream da Chukulat, ya ajiye a gabana, sannan ya ɗaga ƙwalba ya tsiyaya lemo a kofi, ya ajiye a gabana, sai na ga shi ma ya tsiyaya.

Sai da ya kurɓa sau biyu, sannan ya ajiye ni kuwa sai bin shi nake da kallo ta wutsiyar idanuwana.

"Na aiko da gaisuwata ɗazu, amma ban ji gamsasshiyar amsa ba, wanda ke ce mace a ƙarƙashina ki ke,ke ya cancanci ki aika mini da ita,ko kizo ki gaishe ni." Ya yi shiru ya ƙara ɗaukar kofin ya kurɓa lemun.

"Ki sha mana,sarkin shan zaƙi."

Na ɗago na kalleshi a zuciyata na ce wa ya gaya masa ina son waɗannan kayayyakin, ban amsa masa ba sai naga ya ɗan sunkuyo kaɗan ya ɗauki Ice Cream ɗin ya buɗa ya miƙo mini.

"Karɓi."

Na girgiza kaina alamar a'a, saboda mamaki da al'ajabi ya hana ni motsi, ashe ya iya magana mai sanyin gaske ko don bai cika yin magana ba.

"Yasmin!"

Na juyo sosai na kalle shi domin mamakin yanda aka yi yasan sunana, ya ɗan yi murmushin ƘASAITA, ya ƙara miƙo mini,na sa hannu zan karɓa, sai na ga yasa ɗayan hannunsa ya riƙe hannuna, ya kama ƴan yatsuna, sannan na ji ya yi magana.

"Daga yau don Allah kada ki ƙara shafa irin wannan fentin, ina son kisa a yanke miki faratan gaba ɗayansu,ni ba na so, Allah ma baya so."

Na zame hannuna, "Dole ne ki bi umurnina, saboda ina mijinki, ba ki da wata hanyar rabuwa da ni, tunda kin zo hannuna."

Na yatsina fuska. "Ka manta da ina da abin da zan iya tona maka asiri da shi?"

Ya yi murmushi, "Ai yanzun kan ki zaki tonawa asiri, tunda duniya za ta kira ni da mijin Yasmin ne ɗan iska mai bin mata. Amma duk da haka ina roƙon ki ƙonasu,bana so mu ɓata ran mahaifanmu."

Na yi murmushi na juyar da kaina gefe ɗaya.

"Zan ƙona su, amma sai ka bi dokokina."

"Bama za ki same su ba,ki yi shiru kawai."

Bai yi wata magana ba, na ga ya koma ƙwana ya ƙara gyara ƙwanciyarsa.

Ni dai ƴar bi ce kawai, saboda ban san ko'ina ba a gidan, har muka iso wani falo. Wata ƙyakƙyawar mata ce kishingiɗe a saman wani tudu kamar na katifa, wanda ya sha shinfiɗun dardumai wanda kalolinsu ba sa ƙirguwa. Sai da muka isa kusa da matar, sannan na ga na ma taɓa ganin ta. Ƙasa na ga Yarima ya zauna cikin ladabi, nima sai na yi yanda ya yi.

Cikin ɗan lokaci ƙanƙani, na ga matan da ke zagaye da ita suna kawo mana gaisuwa,suna ficewa waje.

"Barka da yamma Mama."

"Barka ka dai yarona."

Nima sai na faɗi yadda ya ce, "Barka da yamma Mama."

"Ɗiyata barka da yau, ya baƙunta, ina fata baya ɓata miki rai?"

"A'a Mama, lafiya ƙalau."

Sai na ga ya tashi ya haye shinfiɗar ya zauna, ya fara wata magana irin ta shagwaɓa, mamaki ya kama ni,nan take na ce lallai iyaye, iyaye ne ashe da wanda Faysal ke wa magana lafiya ƙalau ba taƙama.

"Mama ni har yanzun Sarki ya hana ni zuwa Malesiya,Mama don Allah ki sa baki ya bar ni in tafi gobe."

"Ba fa zai yiwu ba,in dai ka tashi zuwa Honey Moon ne to na san ba zai hana ka ba."

"Mama don Allah." Ya ƙara matsawa kusa da ita har da riƙe mata hannu.

"Kana da naci Yarima a kan abin da ka san ba zai taɓa yiwuwa ba. Yanzun ka tashi ka je ku gaisa da Sarki naji an ce ya shigo, kuma na san saboda kai kawai ya shigo. Baby Yasmin ku je ku gaishe da Babanku, ga shi can ya shigo gida,ki ƙyale wannan shagwaɓaɓɓan mijin naki,kin gan shi nan kullum bai girma ji yake kamar a mayar da shi ciki ma."

"Mama, kada ta raina ni,ni bana yi mata wasa."

"A'a,lallai ni tashi ka wuce ka ba ni waje,marar kunya."

"Mama." Ya faɗa a daidai lokacin da shi kuma ya sauko muka tafi.

Tabbas sarauta sai ɗanta, Sarki kam yana mugun ƙaunar Faysal, saboda yanda ya nuna lokacin da muka shiga. Mun shiga Faysal ya sunkuya har ƙasa ya gaishe da Sarki,a inda ni ma na yi yanda na ga ya yi, sannan muka zauna gabansa.

"Faysal na ji aikenka har karo biyu, amma na bayar da amsa ɗaya, ita ce a'a, yanzun ma a gabanka na ce a'a, ba wai don in ɓata maka rai ba, a'a saboda yanzun ba da bane ba, yanzun kana da nauyin iyali a kanka, ya kamata a ce ka tsaya ka kula da su na tsawon lokaci kafin ka yi wata tafiya.

Faysal ban haɗa ku aure da sunan in zalunce ku ba,mu iyayenku mun haɗa ku aure ne, saboda muna ganin ku ƴaƴa ne nagari masu tarbiyya, hakan yasa ni nayi tunanin wacce ta dace da kai ta ɓangaren ko'ina rayuwar duniya nan, har izuwa lahira, na ga ba wacce ta dace sai wannan yarinya.

Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Ɓacin ranta zai iya shafar tsakaninmu da kai,ko da kuwa labari na samu,ka riƙe ta tsakaninka da Allah, shi so da ka ke gani, a hankali yake shiga cikin zuciya, har ya ratsa gangar jiki,in kuka yi haƙuri da juna, wata rana sai kun yi murna. Saboda mu ma duk haka aka yi mana,ga shi yanzun ya zame mana alheri."

Daga nan ya ci gaba da yi mana nasihohi, sannan ya sallame mu.

Muna fitowa daga ƙaton falon Sarki,Yarima ya yi gaba ya bar ni a baya,a zuciyata na ce ni dama cewa ka yi in tafi gidanmu,ni ya fiye mini alheri, tunda nima saboda mahaifina kawai nake zaune a gidanka.

Ina isa falon mahaifiyarsa na ga ban gansu ba, sai na nufi wata ƙofa nima in nemi inda suka shiga sai na jiyo muryar Yarima.


*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 11


"Mama wallahi yarinyar nan ba ta sona ƙwata-ƙwata, nima har yanzu ban ji ta ƙwanta mini ba sosai. Mama taƙama gareta ga jiji da kai."

"Kai ka fara yi mata,ka manta labarin da ka ba ni a baya cewa yi fa tana burge ka,tun ranar da ka fara ganinta."

"To Mama ai burgewa ba so bane ba."

"To yanzun me ka ke so inyi maka?"

"Mama ki yi mata faɗa, ita ma ta rage jiji da kai."

"Kai ka yi mata."

"Wallahi Mama tun da ki ka ce kada in yi mata wallahi ba na yi mata."

"Haba Faysal na san ka fa."

"Mama ko yanzun fa da zamu zo nan ni na je har ɗakinta, sai da ma na jira ta tashi daga bacci. Mama ai kuwa na yi."

"Shin wai waya gaya maka rana ɗaya so ke shiga,a hankali in kuna tare zaka ji kana sonta, amma na gaya maka dole kai ne za ka yi ƙasa ka dinga lallashinta,ƙiyayyar mace ba ta da tsanani."

"Mama ni wallahi da an bar ni nayi tafiyata kawai."

"Bana son haukan nan naka fa,kullum ana koya maka hankali, amma ka ƙi ka koya." Jin kamar ta yi ɗan shiru yasa na yi saurin yin baya na samu ƙasa na zauna.

"Haba Yasmin!"

"Na ji an faɗa, na yi saurin ɗaga kaina. Mama ce, "Nan fa ya zama gidanku,ki saki jikinki."

"Na yi murmushi, ta zo ta zauna kujerar kusa da ni, sannan ta kama hannuna ta sa mini awarwaraye da zobe.

"Na gode Yasmin,ki je kuyi ta haƙuri kin ji ko, balle ma na san za ki samu kulawa sai na kawo muku ziyara."

Nayi godiya, sannan muka yi sallama. Ai tunda muka shiga mota ban kalli inda ma yake zaune ba, saboda baƙin ciki,wai ni Yasmin ce yau ake tambulan da ni ga ɗa namijin da ba na ƙauna,wai har ba shi baki ake yi da lallashi a kaina dole ne in zo in tayi masa abin da zai ji haushi, har ya haƙura da ni,a raba auran don dole.

Safiya na yi na sa aka kira mini jakadiya,na tambaye ta wa ke tsaran gidan yari? Ta amsa mini da Sarkin tsaron gida, na ce ta sa a kira mini shi, shi da mai kula da basu abinci, wanda ta ce mini sunanshi Ma'aji.

Suna zuwa na umarce su da su shiga dafa abinci mai ƙyau kamar wanda suka san ana ci su dinga ba ƴan gidan yarin, kuma sau huɗu a rana. Da wadataccen ruwan sha, sabulun wanka,wanki,kayan sakawa, na tabbatar zan yi masu ƙyautar da ba su taɓa kawowa zuciyarsu ba, sannan tabbas zan iya kai masu ziyarar bazata,a duk lokacin da na so. A take na ce masu idan Yarima ya tambaya suna iya ce masa ni na saka su, na ɗaga filon ɗin da yake kusa da ni, na ɗauko bandir ɗin ƴan ɗari biyar guda huɗu na basu na ce su raba.

Na kawo guda shida na basu na ce a siyi duk abinda aka san babu. Nan Ma'aji ya tabbatar mini aƙwai komai, ya ba ni labarin irin kayan abincin da ke gidan nan,ya tabbatar mini za su iya ciyar da mutanen Jos da ƙauyukansu har na tsawon shekaru goma, mai ƙyau mai daɗi.

Bayan sati biyu ta cika ne,a daren ranar sai ga jakadiya da mace ɗaya tana biye da bayanta,a inda ta tsugunna ta gaishe ni. Ni kuwa ina kishingiɗe saman kafet ina hutawa su Mansura na gefena, ana ta ba ni labarurrukan ban dariya da nishaɗantarwa.

Na ba ta iznin ta faɗi abin da ya kawo ta, shi ne ta ce Yarima ne ya turo ta tunasar mini na lokacin da na ɗiba ya cika, ta ajiye mini farantin hannun matar nan ɗaya,tana buɗewa sai na ga manya-manyan kaji ne har guda uku, na ɗan yi shiru na tsayin mintuna biyu, sannan na nisa.

"Ki koma ki sanar da shi cewa ni ma na san lokaci ya cika, amma ko a wancan lokacin na baya, cewa na yi ƙila, saboda haka ki mayar masa da waɗannan kaya ki ce na ji saƙon shi, amma idan ya samu dama ina son ganin shi yanzun, anjima, gobe,ko duk lokacin da ya samu damar zuwa,ki gaishe shi."

Ta ɗan ɗauki lokaci, sannan ta miƙe, shi ma kamar ba za ta tafi ba, na juyo na kalle ta.

"Shi kenan." Ta tafi tana kiran,"To, to,ai ba gardama."

Mun samu sama da awa uku muna hira ni da ƴan matan gidana,ganin sha ɗaya na dare ta yi yasa na sallame su,ni ma na nufi ɗakina, domin kayar da kafaɗata saman gado. Al'adata ce yin Sallar nafila kafin in ƙwanta bacci, sannan in kawo wutirina, wanda nake ƙin yi dama sai dare ya yi. Sam ban wani tsaya tunanin zuwan wani Yarima ba na haye gadona.

Ƙarfe goma na safiyar juma'a na shirya tsab na fita,a inda na samu motocin da na bayar da umarnin a shirya mini su tun jiya. Motoci ne guda huɗu, ɗaya ta maza ce ƴan rakiyata, ragowar kuwa ƴan matana ne, ba wani waje za mu ba,illa gidan yari zan kai masu ziyara in ga ko ana yi masu yanda na umarta.

Bayan na shiga mota ne, na hango Yarima saman barandar ɗakinsa yana kallona, tare da al'ajabin ganin yanda na danna kaina a mota, amma abin ka da sarauta,ko ya nuna alamar ya yi mini magana, balle ya tambaye ni ina zani.

Na ji daɗi ƙwarai da gaske, yanda na ga mutanen gidan yarin nan duk sun fara ƙyan gani, duk da akwai rama a jikinsu, amma ni kaina na san ta ragu sosai, gaba ɗayansu aka tara mini su,a inda na yi masu ƴan nasihohi, sannan na ƙwantar masu da hankali da maganganu masu daɗi.

Da ganin yanda suke nunawa ka san sun ji daɗi sosai,nan take na yi masu alƙawarin kawo masu ƙwararrun likitoci, domin a duba marasa lafiyarsu, da su kansu masu lafiyar, domin tabbatar da tasu lafiyar. Na ƙara jadadda masu cewa abinci mai ƙyau kuwa yanzun ma aka fara ba su.

Sannan na ce masu za'a dinga fitar da su wajen wasanni, amma sai sun yi mini alƙawarin ba za su dinga guduwa ba,in kuma na same su da cika alƙawari,nima na yi masu alƙawarin wani abu, amma ba zan faɗeshi ba, sai idan lokacin ya yi. Bayan gama jawabina, na umarce su da su ja layi za'a raba masu wasu kayan da na zo dasu.

Tun bayan goma na safe nake cikin gidan yarin nan, amma ban fito ba sai ƙarfe uku na yamma. Ina isa gida kuwa sai wanka, ban fi minti sha biyar da fitowa ba sai ga jakadiya ta russuna ta yi gaisuwa, sannan ta ce Yarima na son ganina,na bata amsa da cewa in ya shirya gani, ina nan a gida zaune.

Ƙwana uku tsakani, amma ba Yarima ba dalilinsa, wannan ba ƙaramin tayar mini da hankali ya yi ba,shin wai haka za mu yi zaman auran? Tambayar da nake wa kaina kenan daga ƙwance cikin gadona, wanda tun da na yi sallar Asubahi nake cikinsa, har ƙarfe ɗaya na rana.

Kuka kawai nake yi daga ƙwancan nan, Mansura suka shigo na sanar masu cewa ba na jin daɗi, ƙarfe biyu saura ƙwata na rana sai ga Yarima ya shigo har ɗakina, ina ƙudundune cikin bargo, amma ba ƙudundunar rashin lafiya ba, duk baƙin ciki ne yasa na kasa tashi in yi komai.

Tsaye ya yi a bakin gadona, sai da ya ɗan ɗauki minti ɗaya, sannan ya cire gilashin fuskarsa,ni kuwa ina kallon shi da idanuwana masu fitar da hawaye.

"Ni ban san ba ki da lafiya ba, sai yanzun, sannu da jikin naki." Ya ɗan yi shiru.

"Da zaki daure ki ɗan saka kayanki saboda zan turo miki likita yanzu."

"Ka barshi ma, na sha magani, zan samu sauƙi."

Ya janyo kujerar tebirin rubutu a gaban gado, ya zauna, ya kalleni ina kukana, amma bai iya yi mini magana ba.

Wannan zama kuwa ya ɗauke shi har wajen awa ɗaya, sai dai ya ce mini sannu sau ɗaya kawai.

Bayan nan ya miƙe ya zo ya ɗan dafa goshina, wanda jijiyoyin kuka suka tashi a saman shi, ina kallo yasa ɗan ƙaramin hankici ya goge mini hawayena,amma fa ba tare da ya yi mini magana ba.

"Zan dawo anjima." Ita kawai ya faɗa ya juya ya tafi abinsa.

Haushi da takaici suka saukar mini a lokaci ɗaya, tare da tunano masoyina Anwar na san da shi ne, da naga ruɗewa a yau, amma shi ko a tsokar naman jikinsa ma.

Sallamar da aka yi ta kai uku, sannan na amsa na bayar da umarnin a shigo,a inda nake ƙwancen nan. Na ga Aunty Salwa ta shigo, ban san lokacin da na miƙe da ihu ba na duro daga gado na taryeta,sai dariya take yi ita kuwa, bayan mun zauna ne take yi mini ya jiki.

A inda ni kuma na tabbatar mata lafiya ta ƙalau,baƙin ciki ne ya yi mini yawa a zuciyata,amma yanzun tunda ta iso na warke, na ƙara gyara zama, na kalle ta sosai tare da riƙe hannuwanta, kafin bakina ya motsa har hawayen da ke cikin ƙwayar idanuwana sun gangaro a kumatuna.

"Aunty gaskiya ni ba zan iya wannan zaman ba,ki gayawa Dad, ya zo ya raba ni da wannan rayuwar ƙiri-ƙiri mutum ya ce baya sona,ni ma bana son shi, amma an tursasa mu, sai mun yi zaman dole."

Na ƙwashe labarin duk irin zaman da na yi na tsawon ƙwanaki ashirin da uku a gidan nan amma ba ruwansa da harkata.

"A'a ba ruwanki da harkarsa dai,ai shi ba laifi,yana daurewa yana kula ki,ke ce mai matsalar,ni ba ma ruwana da wannan, tsaya in dawo ga haƙƙinsa. Shin kin san ba abin da yake ci ko sha?" Na girgiza kai.

"Kin san a inda yake ƙwana,ma'ana a nan tsabtar muhallin shi?" Na kuma girgiza kaina.

"Kin taɓa shiga ɓangaren sa ki gaishe shi ya nuna miki baya so?"

"A'a, amma Aunty ai duk yana da masu yi masa."

"Ba ruwana da masu yi masa,ai ke dai haƙƙin ki zaki sauke."

"Ni wallahi Anti..."

"Ke wallahi da me? Haba Yasmin ya ki ke so iyayenmu suyi da ransu,so ki ke su kashe kansu a kanmu?"

"Aunty ki yi haƙuri abin ba na faɗa ba ne."

"In baƙya son faɗa, to ki tashi ki yi wanka ki shirya jikinki,muje ki raka ni wajen Yariman mu gaisa."

"Kai Aunty in je gidansa,ai Kamar na ma zubar da ajina ne, na dai aika a kirawo shi."

"Sannu mai makaranta, saboda ai yanda ki ka ɗauki kan ki ma naga alama ya wuce aji, sai dai makaranta kawai. Wallahi idan ba ki ɗauki kanki da sauƙi ba, zaki sha wahalar rayuwar duniya,su waɗannan mutanen babu abin da Allah bai basu ba, sannan ina ki ka taɓa jin auran gidan sarauta na rabuwa? Da wahalar gaske. Sai dai su auro wata su ƙara,kina kallo ya auro wata ya yi zamanshi lafiya da ita."

"Ni dai Aunty da zai sallame ni,ni ya auro huɗu ma a lokaci ɗaya, har ya haɗo da ƙwarƙwara ma."

Nan take na ga ta daddanna wayar da ke hannunta.

"Zan gayawa Daddy halin da ki ke ciki,in ya so shi sai ya san matakin ɗauka."

Na yi saurin fizge wayar daga hannunta, na kashe.

"Aunty ke daga wasa."

"To tashi ki shirya." Dole ta sa na tashi gudun kada ran iyayena ya ɓaci a kaina.

Riga da zani ne na wani yadi three in one mai ƙyan gaske, ruwan madara ne da dishi-dishin ruwan ƙasa mai duhu a jikinsa,zanan ya sha ado, kamar dai yanda ake yayi ( Wrapper Skirt ) yanzu,takalman da na sa a ƙafata kuwa masu kamar silifas ne (Flat) ruwan madara ne, sai mayafi kawai da na yafa a kaina, ban wani tsaya neman ɗankwalinsu ba, na feshe jikina da turare, amma ba wata ƙwalliya a fuskata, saboda sanyi ma da ake da ko mai ba zan shafa ba.

Farar hoda kawai na gogawa fuskata, sai kuwa man leɓe da na sakawa laɓɓana. Jere muke da Aunty a inda na cewa su Mansura su jira in dawo. Muna isa ƙofar gidansa, mutane ne sun kai goma a zazzaune, suka yi saurin miƙewa suka kawo gaisuwa, muka amsa sannan muka wace ciki.

Mutane ne su huɗu zaune a ƙasa suna ta hirarsu,falo ne shi ma ƙaton gaske, wanda ba zan iya cewa ga abin da ya ƙunsa ba, saboda farkon shigowa ta kenan, mutanen nan suka kawo mana gaisuwa, waɗanda zan iya kiran su dogarawa. Bayan mun zauna da minti ɗaya sai nake ce musu su yi mana magana da Yarima.

*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 12


A take ɗaya daga cikinsu ya ce ai ba a hawa idan har yana sama, sai dai ni ina iya hawa. Na nuna a barshi in ya sauko ma dawo. Amma Aunty ta ce sai na hau saman nan, kamar wacce zata hadu da abin tsoro, haka nake tattaka matattakalar benen, saboda na fahimci yanayin zubinsu ɗaya da gidana.

Duk inda na duba baya nan, har sai da na kai ga ɗakinsa. A hankali na murɗa hannun ƙofar gudun kada ya ji ƙara, na tura ta cikin sanɗa, sannan na yi sallama, amma shiru ba wanda ya amsa mini,sai da na kai tsakiyar ɗakin manufata in isa barandar gidan inda na fahimci ya fi zama.

Kamar an ce in kalli gefen ɗakin, sai na ganshi ƙwance a ƙasa, ya yi rigingine yana bacci ba riga a jikinsa, sai dogon wando, na matso na tsugunna a hankali a gabanshi inda na ƙurawa halittar Allah idanuwa.

Ƙyau kam gashi nan a ƙwance, a take sai na ji dama Anwar ne na samu a ƙwance nan, amma matsala ɗaya ita ce hannuwanshi waje ɗaya ya yi filo da su, da gani kuma ka san abu ne wanda zai iya wahalar da shi.

Wai sai na tsinci kaina da son gyara masa, na miƙe zuwa gado na ɗauko filo, na iso na zauna dirshen, na zare hannuwansa a hankali, abin ka da gefe nake zaune, sai kawai na ga ya yi juyin da ya iso saman cinyata, ya sa hannuwa duk biyun ya zagaye ni.

Kenan ya koma rub da ciki,a zuciyata na ce Allah ya ƙara mini,cikin ƴar dabara na samu na zame jikina nasa masa fili,wai sai na ji ina son taɓa gashin kan shi inji kowanne iri ne, a hannuna na ji wani irin laushi,dama na san hakan za ta iya faruwa, saboda baƙin gashin ya yi yawa, sai dai ba shi da yawa.

Na miƙe a hankali na juya na tafi,a inda na samu Aunty na sanar da ita bacci yake yi,baccin kuma ya yi nisa, haka muka koma sashena muka ci gaba da hirarmu.

Ƙarfe biyar na yamma na dinga haɗa Aunty da Allah a kan ta sa kayan wasa mu je muyi tennis a filin wasa. Siket da riga iya gwiwa na saka,farare ƙal, da ganinsu ka ga kayan wasa, saboda wuyan T.Shirt ɗin kore ne zagaye da ita, haka hannuwanta ma, sai bal ɗin matse gashi wanda na roba ne,koriyar safa ce amma farin kambos ne a ƙafata.

Ita kuwa Aunty Siket ɗin ta har ƙasa yake, sannan ta ɗaura ɗanƙwalin wasa sai dai ita ma farare ne na wasa, na umarci su Mansura da su je su duba mana lafiyar filin wasan, sannan su isa da ruwa da lemo kafin mu isa, wanda tuni nasa an yi gaba da kayan wasan.

Shigar da nayi ita tasa na ji ni tamkar an yi mini albishir da Aljanna, saboda samun kaina da na yi cikin farin ciki da nishaɗi,hakan yasa ma da guduna na isa filin wasan, saboda motsa jikina. Aunty kuwa ta biye mini ne kawai na san don dai ta ja ra'ayina in yi haƙuri in ci gaba da zama.

Wasa kam ya yi daɗi, amma har yanzu ba wanda ya ci wani. Ikon Allah kuwa Allah ya ba ni Sa'a na ci Aunty,ban san lokacin da na dinga ihun murna ba, har da su tsalle. Kamar an ce in kai idona ga barandar Yarima, sai na gan shi a sunkuye ya dafa ƙarfe yana kallonmu, kallon da nayi masa ya kai na minti ɗaya sannan na juyo na yi tsaki,a inda ya ɗago mini babban ɗan yatsa,alamar yabawa da cin da na yi.

Na kira Mansura na ce ta je ta kirawo min jakadiya ta amsa tare da tafiya da saurinta. Ban fasa wasan ba wai saboda ganin Yarima, sai dai jikina na bani kallona yake yi. Tsawon mintunan da ba su wuce taƙwas ba, sai ga jakadiya da saurinta tana zuwa ta zube gefena a inda ina wasana ina gaya

2 Comments On KASAITA 1
avatar
khadijat-6-8

4 months ago

Reply

Thanks

avatar
khadijat-6-8

4 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment