Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne na haɗu da Anwar tsawon shekara huɗu muna tare da shi.

Mahaifinmu Alhaji Sani Sa'id, yana nuna mana ƙauna fiye da tunanin kowa, shi yasa mu ma muke ƙoƙarin yi masa abin da zai ji daɗi, balle ga girma ya tunkaro shi, saboda mutum ɗan shekara sittin da takwas a duniya,ai mun san dattijo ne, sai dai jin daɗi yasa ba'a gane tsufan jikinsa.

Ina da ƙyau,ko ni na sani, sai dai farina irin na Larabawa ne wato fari mai haske. Structure ɗin jikina kuwa na burge ni,ga manan ƙirjina daidai ne, yawancin ƙawayena suna cewa ina yanayi da ƴar ƙasar Indiyar nan wato Pretty Zeenta,sai dai wai na fita fari mai ƙyau, kuma gashinmu ba iri ɗaya ba ne,ni irin mai laushi ne irin na Larabawa, ita kuwa nata mai tauri ne,ko kuwa a ce bazar yake.

A unguwar Refin Rizont gidan iyayena yake,gani ƴar gata gaba da baya, saboda ƙauna da ake nuna mini,balle kuma ni ce auta.

**** **** ****

Hidima kamar ta yi mini yawa, balle yau ne ranar walimar iyaye da abokan arziki (Dinner party). Rana ce wacce da iyaye da ƴaƴa da abokanan arziƙi ke haɗuwa, to balle hidima irin ta manya haka.

Yau ne mahaifin Fatima, wanda yake abokin wasa ga Dad yake yin party ɗin ɗiyarshi ta uku, wacce take ƴar'uwata, Aminiyata ga ta ƙawata. Biki kuwa irin na manya, kowa ya san shuwagabannin kasashe ke taruwa ban da Sarakunan duniya.

Tabbas sun taru a yau. A hotel ɗin jero wanda shi ne Hotel na biyu a Jos a duk faɗin Jos. Ƴan gidajen rediyo da talabijin kuwa ba zan iya ƙirga yawansu ba, ballantana kuma dama kowanne shugaba in zai zo da tawagarshi, zai taho ne da ƴan ɗaukar hotansa, ban da ƴan ɗaukar hotan kaset (Camera man) da ƴan gidan rediyo na garinshi.

Shi hall ɗin kuwa,an jera masa kujeru na alfarma, amma za a iya cewa duk tebir ɗaya mutum uku ne zagaye da shi, suna kallon saman ɗakin taron, manyan sarakuna da shuwagaban ƙasashe kuwa su ne irin lafiyayyun kujerun nan da ake keɓewa (VIP Cushion).

Kowa ya san in an haɗo irin wannan taro a kan ɗauki lokaci ana gabatar da shirye-shirye tun da akan gayyato mawaƙa kala-kala, da ƴan wasan ƙwaiƙwayo na Turanci, da na yare, sai an gama irin wannan shaƙatawa sannan ma ake buɗa fili da ƴan surutai, da kuma sannu da zuwan baƙi wanda uban ango da na amarya ke yi.

Da waɗanda aka ɗora a matsayin baƙin taro,a kan ba ango da abokinshi fili su yi godiya. Ango kenan abokin ango ya gabatar da halayen ango masu ƙyau, haka ƙawar amarya ma takan yabi ƙawarta. Amarya kuwa godiya kawai take yi da nuna murnarta.

Yau ne duk ranar yin haka, wanda tuni ɗakin taro ya cika maƙil da jama'a, kafin komai ya fara bayyana kaset ɗin kiɗa mai fitar sauti a hankali (Slow music) a lokacin kuma ƴan mata masu rabon abinci ke ratsa mutane suna ajiye masu ƴan kayan lasawa, kafin a gama a fara kawo abinci.

A cikin ƴan matan kuwa har da mu ƙawayen amarya, wanda muka dinga yawo da ƴan farantai a hannu muna raba madara mai ƙanƙara da lemun ƙwali da ruwan doguwar roba (Ice Cream,Lemon juice, and Swan water).

Ni kaina na san duk ɗakin taron nan mutum ɗai ɗai ne wanda hankalinsa ba ya kaina, shi ma sai dai in bai hangoni ba, saboda ƙyau da Allah ya yi mini. Riga da wando ne a jikina, amma ruwan baƙaƙe, sannan kuma masu ɗauke idanuwa, saboda yadin mai sheƙi ne tamkar madubi.

Wando ne har ƙasa, amma daga ƙasa a buɗe yake, sai rigar kuwa ƴar iya ƙuguna, wanda hannunta kuwa na shimi ne, ɗan siririn gaske, amma doguwar riga mai buɗaɗɗan gaba da dogon hannu ita ce a saman shimin nan, wanda ɗan abin ɓalle doguwar rigar dai dai saman cibiyata yake.

Gashina ya sha gyaran kanti, wato (salon), amma na taje shi gaba ɗaya ya bi bayana, sai sheƙi yake,dama Tubarakallah! Ga shi baƙiƙƙirin, tamkar izgar baƙin doki,dama asali ni ba mai ɗaura ɗanƙwali ba ce ba, saboda haka ma baya cikin tunanina, sai dai na ɗan yanko ƙalilan daga cikin gashina ya sauko gefen fuskata, wanda yake ɗan saka ni aikin gyara shi idan na duƙa ajiye ƴan kayan lasawa a gaban mutane.......



*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 3


Fararan takalma ne a ƙafata, sannan sarƙa da ƴan kunne ne a wuyana, amma na (Diamond), wanda duk sun ƙunshi agogon hannuna da zobunan hannuna guda huɗu, baƙin fenti ke liƙe a farcina na (Lamp paint), haka baƙin jam baki ne manne a leɓɓuna na, wanda ke sheƙi.

Lallai ni kaina na san na yi ƙyau, wannan ƙyau nawa kuwa ina taƙama da shi,ga takalma na masu tsinin gaske ko'ina na kai (Ice Cream) ɗin nan sai sun yi mini magana,ni kuwa dama ba mace ba ce mai son magana, wannan yasa sai dai in yi musu murmushi wanda ƴar lotsawar gefen kumatuna ke bayyana (Dimple).

Ina cikin rarrabawa ne kuwa har na kawo wani tebir a tsakiyar ɗakin taron, na ajiyewa na gabana,na ajiyewa ɗayan na kusa da shi, sai na ji mutanen nan biyu na cewa.

"Allah ya ja da ran Gimbiya,Yarima na gaishe ki."

Na samu na gyara gashin da ya rufe mini fuska. Gabana ne naji ya yi mummunan faɗuwa a daidai lokacin da na ɗago kaina na ga mutumin da motarshi ta bige ni,a tsakiyar titin unguwar Ahmadu Bello way,wanda tamkar ya banke akuya shi ne kishingiɗe a cikin kujera ko motsi ma ya kasa yi don mulki zan ce ko ƘASAITA.

Na yi masa kallo wanda ya kai na minti uku, a inda na ƙara karantar fuskarshi,a cikin kallon da nake yi masa ne naga da ƙyar yasa hannu ya cire farin gilashin da ke manne a saman idanuwanshi, sannan na ga ya lumshe idanuwansa duka biyu, sannan ya buɗe.

Da hannunsa mai gilashin nan ya ɗan yi masu nuni kaɗan, sai naji sun ce, "Yarima na amsa gaisuwar ki."

Nayi murmushi da ke bayyanar mini da asirtaccen ƙyauna, wanda na yi shi ne don haushi da takaici da nuna masa cewa nima fa na isa,ƙyau yake taƙama da shi, nima aƙwai wanda ya fi nasa a jikina.

Na rausayar da gashin kaina, ya shafi fuskarshi, sannan na sunkuya na ɗauke kayan lasawata,ice cream da lemuna har ruwana, na mayar a gaban na kusa da shi, sannan na miƙe na yi gaba abina,a zuciyata na ce, sai dai wata ta kawo maka ba dai ni ba, nima nan da ka ke ganina sarauniyar kaina ce, iyayena kawai nake wa shagwaɓa sai kuwa yayyena.

Tsakanina da Dad da aƙwai nisa, sannan ga shi cikin jama'a yake, waɗanda suke manyan mutane ne. Wannan ne ya hanani in isa wajen Dad in nuna masa azzalumin mutumin da ya kaɗe ni, sannan ga tsoro ina ji, kada in tafi wajen tsurkun nunawa Daddy shi, wani ya ce yana sona a cikin mutanen da yake tare da su,ni kuwa sai angona Anwar.

Bayan ɗakin taro ya nutsu ne aka bayar da umarnin cewa amarya da ango su shigo ɗakin taron, cikin mintina goma (Martina Desginer) jikina da ƙwalliyar dark blue les mai dige-ɗigen fari, musamman domin ta gyarawa ƴan matan amarya jiki aka ɗauko mana ita.

Gwaggwarona kalar fari, haka takalmana, da jaka ƴar sagale a hannuna,ƴar siririyar sarƙa ce mai kalar fari a wuyana, wacce zamu iya kiranta da suna Diamond, gashin kaina kuwa nannaɗe shi na yi waje ɗaya, tamkar naɗin da Indiyawa ke yi wa gashinsu.

Wetlips ne kawai a laɓɓana, sai dai zagayan saman laɓɓan nasa masu jagira mai kalar fara. Kowa ya hango ni, sai ya yi zaton ni ce amaryar, sai dai don ita amarya ta sha bamban a duk inda take, gefen amarya nake, shi ma abokin ango a gefen angon yake, kenan mun jera layi a kan mutane huɗu-huɗu, maza biyu mata biyu.

Dole ɗakin taron ya kaure da surutai don ma dai taron manya ne har ihu ma sai anyi, saboda ni kaina nasan mun yi ƙyan da za a iya ɗaukarmu a matsayin (Magazine) Ɗinkunan zamani ne a jikinmu in ka ganmu tamkar an shirya mu ne domin a sa a Magazine ɗin (Ovation Magazine).

Fitowarmu ke da wuya, sautin kiɗa ya canja a hankali ya soma tashi, wanda har muka isa wajen zamanmu,saman ɗakin taron daga gefe ɗaya, saboda gefe ɗaya an bar shi ne saboda ƴan wasa.

Abin ka ga garin da ya tara yarurruka kala-kala, wannan yasa kusan yare ashirin suka yi raye-rayensu da waƙoƙin su, sannan aka koma wasan ƙwaiƙwayo, inda ƴan Legas suka yi nasu a kan zamantakewar auratayya da tarbiyyar yara.

Ƴan wasa kuwa shahararru ne, irin su Pate Odochi,Sam Loco,Ramsy Noah,Geneve Nneji,Liz Benson,Mama G. Gaskiya wasan ya yi ƙyau, dole ne ma fili ya ɗauki tafi,abin ka ga mutanen da ba su da Addini duk da ita ma Jos da sauƙin Addinin, amma yanda suka shirya shi ne kamar da gaske, shi ya burge ni. A nan take na ji ina son yin auren, saboda rayuwar da suka nuna.

Kamar an ce in ɗaga kaina, sai na hango wannan sakaran mutumin wanda ya kaɗe ni ya wani ƙwanta a kujera sai fizgar kai yake yi, kowa ya kewa, Oho. A zuciyata na ce yau ka faɗa, da Dad zan haɗa ka,kasha dukan tsiya.

Bayan fitarsu ne sai fili ya ɗan ruɗe kaɗan da hayaniya,in ɗan kalla sosai sai na ga ashe shahararrun ƴan wasan Hausa ne na jahar Kano waɗanda muke gani a cikin talabijin yau ga su a fili, kamar su Iyaye Alhaji Ibrahim Mandawari, Alhaji Hamisu Iyantama,Kabiru Na Ƙwango, Shehu Hassan Kano,Usaini Sule Ƙoƙi,Kabir Mai Kaba. Tare suke da ƴan fim ɗin su maza da mata. Sai iyayen fim din su mata na biye da su kamar su Hajara Usman salihar mace,Saratu Giɗaɗo macen da kowa ke so, Jamila Haruna kin fi kama da matar Gwamna da dai sauransu.

In na tsaya lissafawa ba zamu gama ba,sun yi wasan ƙwaiƙwayonsu a kan samu da rashi sannan da mutuwa da kuma ƙaunar iyaye da ƴaƴansu, wasan kuma ya sanyayar da zukatan mutane, wanda a take kowa ka kalla ya yi la'asar, tamkar yana jiran Mala'ikun mutuwa su iso kanshi.

Bayan nan kuma ɗaya bayan ɗaya aka dinga tashi ana magana da ƙoƙon fitar da sautin magana da ƙarfi (Microphone), iyaye,abokan arziƙi, shuwagabanni,a inda har wani shugaba a nan Jos ya baiwa ƴan wasan Kano ƙyauta ta motoci guda biyu, saboda yawon wasa da suke yi.

Wannan ne ya buɗe fili aka dinga yi musu ƙyaututtuka. A ƙarshe abokin ango ya fara faɗin halayyar abokinsa, ya kuranta shi, inda ni ma na tashi na yi, duk fa da harshen Turanci,dama su ni an iya turancin hanci (Slang) shi nayi a wajen. Ni kuma na san duk wanda ya ganni a tsaye ya ji turancina kuma ba zai taɓa ɗaukar ni bahausa ba ce ba, sai dai ƴar ƙasar tsallake.

Ango ya yi godiya, amarya ma haka, daga nan sai aka dinga rarraba abinci wanda duk ka ke so, sai ma an tambaye ka wanda nan kuma masu raba abincin Hotel ɗin ne ke aikinsu (Waiters).

Ƙarfe biyu da rabi na dare aka tashi ba wai watsewa ba, saboda in na tashi ne ake samun damar gaisawa da jama'a na nesa da na kusa. A lokacin ɗakin taron da wajen ya baje da jama'a ana ta gaisawa tare da yin hira da su a gidan talabijin.

Da ƙyar na samu na je na gayawa Dad cewa na ga mutumin da ya kaɗe ni, kafin in waiga in nuna masa shi ya ɓace mini,wannan yasa na yi saurin jan ɗaya daga cikin ƙawayenmu na fita wajen Hotel ɗin, domin in samu damar ɗaukar lambar motarshi.

Cikin ɗan sauri-sauri muke tafiya, a inda na ci karo da wani, wanda har sai da muka haɗu da juna sosai, turaren da ke jikinsa kuwa, irin mai sanyaya zuciya ne, ina jin ƙarar faɗuwar jakata da wani abu a ƙasanmu, duk wannan bai fi cikin sakan uku ba, maimakon in kalli ko waye sai na duƙa don ɗauko masa wayar hannunsa, wacce ta faɗi tare da jakata.

Ɗagowa ta kuwa ta yi daidai da duƙawarsa ya ɗauko mini jakata yana ɗagowa ina shirin ba shi haƙuri, saboda a zatona ya yi tsaran iyayenmu, sai kawai haushi ya kama ni a take kamar yanda na lura al'ajabi ya kama shi mutumin da nake faman nema in nunawa Dad ɗina,shi ne muka yi karo da juna.

Na rasa me zan ce masa, na yi tsaye da wayarsa a hannuna, shi ma da jakata, ganin shi ba shi da niyyar yi mini magana, saboda tsananin girman kai, yasa nima na ƙi tanka masa, sai dai na fizge jakata da ke hannunsa ta ƙarfin tsiya, sannan na jefe shi da wayar da ke hannuna, ta faɗi ƙasa ta tarwatse.

Wannan ta yi daidai da tahowar wasu gungun shuwagabanni, za su wuce gamu mun tsare hanya,ƙawata Uwani ita ta janye ni cikin sauri sannan na ga ta sunkuya ƙasa tana tsince masa tarwatsatstsiyar wayarsa, wanda ta bi shi da sauri don ta bashi, saboda gungun mutanen sun yi gaba da shi.

Wai sai da na ɗauki mintuna biyar a tsaye sannan na yi saurin tunowa da lambarshi fa zan ɗauka ta mota. Na fita cikin zafin nama ina ta waige-waige, amma ko kalar mai rigar sa ban hango ba.

Na gaji da waigena har na juya zan koma ciki, sai na ji Uwani na ƙwala mini kira na yi saurin waigawa domin in gano inda take, saboda na ma san na gane mutumin nan, amma sai na ganta ita kaɗai, na yi saurin taryar ta, ina tambayarta.

"Ina yake, ina yake?"

Wai tambaya take wa? Na ce mata wanda ki ka kaiwa waya. Sannan ta nuna mini motar da yake ciki wacce ta kusan fita daga hotel ɗin, ba kuma za a iya hangen lambar jikin motar ba, balle a ɗauka.

Haushi ya kama ni na dinga yi mata faɗan masifa a taron nan,a haka har aka tashi wannan taro, ina cikin ɓacin ran rashin ɗaukar lambar motar nan.

Bayan mun je gida na sanar da Dad abin da ya faru,nan ya ce inyi ƙoƙarin ɗaukar masa lambar in na yi haka, to shi kenan in sa ido, na amsa masa tare da ƙudirin sai na ɗauke ta in Allah ya yarda, amma har muka gama biki ban ƙara ganin ko mai kama da shi ba. Wannan kuwa ba ƙaramin takura ni ya yi ba.

**** **** ****

Bayan ƙwanaki arba'in da huɗu da gama bikin Fatima da mijinta Ibrahim, wacce take da mahaifinta da Dad abokan wasa suke. Ni kuwa bayan bikin ban ƙara zuwa inda take ba, sai yau ranar Asabar saboda in samu Ibrahim a gida shi yasa na bari sai Asabar.

Cikin isa nake jan motata zuwa unguwar Ring Road,domin kai wa Fatima ziyara, daidai wajen bada hannu ne wajen unguwar Ahmad Bello way,na tsaya bai fi mintuna biyu da tsayawa ta ba ina jiran a ba ƴan layinmu hannu, sai kawai na ga ƙato ya buɗe murfin motata a gaba ya shigo, ina ƙoƙarin yi masa magana na ji buɗewar baya,waigawar da zan yi sai naga ƙarti uku zaune a cikinta, sun nuna mini bindiga, wanda na gaba ya ce mini.

"Kiyi shiru,ki ja mota kawai muke so!"

Ban tsaya gardama da su ba na mayar da hankalina ga tuƙina inda aka ba mu hannu.

"Titin hannun ki na dama za ki bi."

Haka ɗayan ya ce mini. Ni dai na san ba zan ɓata ba a garin nan sai dai in kashe ni za su yi, saboda haka ban razana ba.

Duk inda suka ce in nufa,nan nake bi da motata, har zuwa wani mahaukacin gida, wanda yake ɗauke da yawan fitilu, duk da safe ne ba kunna su aka yi ba, amma ganin su a tsaye shi ya nuna mini yawansu.

Titin get ɗin gidan muka miƙe, tamkar za mu wani garin, bayan mun shiga get ɗin gidan waɗanda yake ɗauke da sojoji sun kai goma sha biyar,ni kuwa ganin sojojin ma ya ƙara mini ƙwarin giwar in sakin jikina ma, sai da muka dinga wuce gidaje zan ce ko gine-gine, sun kai baƙwai sannan suka ce in tsaya a ƙofar wani gida mai bene,wanda saman shi yake zagaye da barandar sama.

Da gani zagaye yake kamar ƙwano kenan circle ta can sama na hango ƙyallin wani mutum ta labule ya ɗan ɗago masu hannu, daga nan sai suka ce in yi gaba na ja mota muka nausa cikin wani daji, duk fa a cikin harabar wannan gine-gine. Bayan tafiya ta kai ta kilomita uku, sannan na ga mun iso wani gida mai dogon gini kamar ginin Choci.

Nan aka umarce ni da in tsaya in fito daga motar, ba wanda ya taɓa ni cikin su, suka nuna mini hanya har cikin gidan nan. Mun wuce wurare da dama, sannan na dinga ganin ragar ƙarfe da mutane a ciki, wannan ya nuna mini gidan yari ne aka kawo ni,abin da ban gane ba,shin ziyara aka kawo ni inyi ko kuwa ganin wani,ni dai na san ban yi laifin komai ba......


*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 4


Abin tausayi na gidan (Yarin) gidan maza, saboda duk sun bi sun rame, sun ƙare,ga su nan da ƙyar suke magana, masu ɗan ƙarfi ne ke miƙewa su zo su kama ƙarfen suna yi mana magana wadda bana ganewa.

Matattakalar bene muka haye ni da su, wanda nan naga mata birjik a ɗaure a zuciyata na ce laifin me suka yi waɗannan bayin Allah, har da masu tsohon ciki da masu ƴaƴa, ga su nan a kukkulle,ni dai ƴar kallo ce har aka kai wani ɗaki na ga an buɗe shi wai in shiga,ban musu gardama ba muka shiga tare da su.

Gado ne ƙarami irin na ƴan makaranta amma wanda bashi da sama, sai ɗaya a kusa da shi da wata ƙwance tana bacci. Ba su yi mini magana ba ɗaya daga ciki ya buɗe wata ƙofa,nan na ga ashe banɗaki ne, ɗaya ya buɗe famfo a kusa da ni, na ga ruwa ya zo, duk dai ban yi magana ba.

Sai da na ga duk sun fita suna shirin kulle ni a ciki, sannan na yi masu magana da harshen Turanci.

"Baku gaya mini komai ba har za ku tafi."

Ɗaya daga cikinsu ne ya ce, "ki zauna za a neme ki."

Ya juya ya tafi ban ce masu komai ba,nima na ɗan kalli gidan nan na zauna.

Tsayin awa ɗaya, sai na ga matar nan ta tashi, tana ganina ta taso a hankali ta iso wajena ta zauna.

"Yaushe aka kawo ki?"

Naji ta faɗa da Hausa. Na kalleta sosai.

"Ko baƙya jin Hausa?"

"Ina ji,ɗazun aka kawo ni."

"Me ki kayi?"

"Ba komai"

"To Allah ya taimake mu"

"Musulma ce ke?"

"Eh."

Daga nan muka dinga hira da ita.

Ina nan har ƙarfe tara na dare, sannan naga waɗannan mutanen sun buɗe in da muke sun shigo, ɗaya daga ciki ne ya ce in taso, na yi wa wacce muke tare sallama mai suna Mabaruka. Tana kuka na bar ta tausayinta ya kama ni. A motata muka kuma shiga na ja har gaban gidan da muka tsaya da rana.

Muna tsayawa na ɗaga kaina sama sai na hango mutum zaune a barandar saman bene ya miƙe tsaye sosai ya juyo tare da dafa majinginin barandar, cewa suka yi in fito, na fito na kalleshi sosai, cikin sakan uku na gane mutumin da ya kaɗe ni watanni huɗu da suka wuce.

Me zan ce masa ni kuma yanzu bai yi magana ba, nima ban yi masa ba. Na girgiza kaina na juya na koma motata har na tashe ta ɗaya daga cikin ƙartin nan masu sanye da fararan T.shirt, ya sunkuyo ta gilashin da nake tuƙi ya ce.

"An baki last warning saboda haka yana gargaɗinki da kada ki ƙara shiga layin gonar shi, balle har ganganci ya kai ki kice za ki ratsa tsakiyar ta, ina fatan kin fahimta?"

Na ɗaga masa kai kawai, na ja motata har na yi nisa na tsaya na leƙo da kaina na ɗaga masa babban ɗan yatsana ma'anata a nan za mu haɗu wata rana.

A mota ne na yi tunanin ba zan gayawa Dad kome ya faru da ni ba, amma ni da kaina zan ɗauki mataki wanda ko a hanya ya hango ni sai ya ce a sake wata. Har na isa gida ina tunanin hanyoyin da zan bi, amma na rasa su, saboda haka na ajiye lamarin, na dangana shi da ba aikin gaggawa ba ne.

Sai da Mamee ta ɗan yi mini faɗa a kan nayi dare, goma saura kaɗan, na san banida gaskiya na dinga ba ta haƙuri,gudun kada ta gayawa Dad shi kuwa ba wasa a lamarin sa, idan har ka taɓo shi. Kun san iyaye dai.

Bayan na yi wanka na shirya jikina ne na gabatar da sallolin da ake bina, daga nan ban iya yin bacci ba, saboda tunanin hanyar ramuwar gayyar da nake son haɗawa Yarima.

Wannan dalili ne yasa na tunano da litattafan novel na Turanci na shahararren marubucin nan (James H. Chase). Na san a cikin litattafan sa akwai idea zan iya samun wata hikima a ciki. Daɗi, murmushi, dariya, suka saukar mini a lokaci ɗaya, wannan ya sa na kashe fitilar gefen gadona na koma na ƙwanta, tare da tabbacin yanzu bacci zai zo mini. Haka aka yi kuwa,sallar Asubahi ma Mamee ce ta tashe ni.

Da ƙyar na shawo kan Mamee ta amince na fita, shima don na ba ta tabbacin iyakata Bookshop na nufa domin neman wasu littattafai, cikin saurin da bai fi na mintuna talatin ba na dawo,lode da litattafan James, sun kai goma sha biyar.

Tun da na haye sama ɗakina ko motsi na kirki ma bana son yi, abincin rana kuwa sai da la'asar na samu na ci shi. Sai da na ɗauki ƙwanaki goma ina nazarin litattafan nan da birona da zungureran littafina a gefe,in ta kama in rubuta in kuwa tawa muguntar ta faɗo in rubuta.

Wani lokaci a falon Dad,nake shigewa saboda kada a dameni, sai na ji dawowarshi, sannan in koma ɗakina, na gama karantawa saura haɗa ayyuka. To yaya kenan?.

Ƙarfe taƙwas saura na safiyar Litinin wacce ta yi daidai da ƙwanana biyu da gamawa, na je na samu Katung Maigadi nan na zauna na gaya masa buƙatata, a take ya ce ai wannan duk abu mai sauƙi ne, tunda da akwai shi, sannan akwai abokanansa,in zan tura da kuɗi kawai su zasu kawo mini aikin da suka shirya. Na yi murna ƙwarai da gaske, sannan na ce ya bani ƙwana ɗaya.

Saboda na jima ban fita ba, shi ne na tambayi Mamee zan je gidan Aunty,ta amince mini. Ina isa gidan na ce mata kuɗi nake so, na dinga narke mata kamar zan yi kuka, har sai da ta bani dubu goma, na bugawa Yaya Habib waya na ce masa kuɗi nake so ya ce zai turo ta account ɗina wato banki.

Sai da na haɗo dubu talatin, sannan na ɗauki ashirin a nawa (account) ɗin na haɗa, na zo wajen Dad kuma na dinga fadanci cewa litattafai zan siyo, ya bani, saboda ganin da yake ina yawan karanta su, ya bani talatin. To saura Mamee, na girka mata kuka tun da ita ba wasa.

Ganin duk ranar kuka kawai nake, shi ne ta tausaya mini ta dinga lallashina, har tana tambayar me nake so, shi ne na gaya mata cewa account ɗina ba komai a ciki, shi ne nake son kuɗi in siyi litattafai, shi ne Dad ya bani kaɗan ,nan ta ce nawa ne? Na ce ashirin, ta ƙirgo ta ba ni.

Bayan ƙwanaki tara, ya zo ya ce mini komai ya haɗu, amma aikin farko kenan,yau wajen ƙarfe biyar na yamma in bi ta hanyar Bank Road saboda ruwan da ake yi na san yanzu zai kai har nan da tsayin lokaci a yanda (weather forecast) ta nuna.

Cikin ruwan sama mai tsanani na bi hanyar Bank Road,hanyar da bata cika

2 Comments On KASAITA 1
avatar
khadijat-6-8

4 months ago

Reply

Thanks

avatar
khadijat-6-8

4 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment