Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fatanshi keyin wani bororo dahar wani motsi suke yasa yace “a chanzamai kayan jikin nan nashi maza, ku goggogemai jiki with clean towel, allergy ke damunshi, he’s allergic to dirt da kazanta right from small, kuyi sauri pls” fita kowa yayi daga dakin akabar Munir da Mom, Waziri da sauran duk suka zauna a falo yace “wazai attacking yaro daga durowan shi kasan nan?” Anatse Wambai yace “call the police I think sai anbincika airport din maybe ta CCTV za’a gani” faduwa gaban Kabeer yayi amman yadaure yaranshi always do a clean job he hope bazasu kwofasashi ba, fitowa Munir yayi yace “Dr an gama” dukansu komawa ciki sukayi Kabeer sai tsaki yake aranshi shida yakeso kowa yaji haushinshi amman jibi yanda kowa ke nan nan dashi, attention yakoma kanshi ma infact, skin nashi gabaki daya yakoma so red, drip akamai fixing da allurai ciki Dr yakalli Mom datafi kowa damuwa adakin yace “anjima kadan zai farfado don’t worry” dan murmushi tayi tareda gyadamai kai Waziri yace “ki zauna dashi” Gwaggo tace “nima ina nan kome za’a kawomai kowa zaizo yadubashi saina ganshi inga uban waye keso ya cutar mini da jika, bangama kukan mutuwan d’ana ba yanzu halakamin jika za’ayi wlh jinina yasha karfin kowa” kallon Munir Mom tayi ahankali tace “thank you Munir” gyadamata kai yayi yawuce yafita daga dakin hakan yarage daga Gwaggo sai ita, dafata Gwaggo tayi tace “ki tsare yaron nan ki dage da addu’a akanshi, tun ranan da aka haifi Riyad akace yanada taurari masu kyau kuma babban mutum ne shi, kiduba kigani yaran marigayi maza shidda amman shi kadai akeso ahalaka tun yanzu kenan bama asan waye zai gaji kujeran sarautan ba kenan amman so ake akasheshi balle kuma ace shine zai gaji sarautan ki tashi tsaye Maryama, saikin tashi tsaye, kinyi zaman gidan nan basai na fadamiki hadarorin dake cikinsa ba, inde kalubale ne yanzu Riyad yafara gani, idan kuma yazama Sarki yadinga ganin kalubale iri iri kenan har abada, ki tsare yaron nan, kizama idanunshi kunnuwanshi uwa uba kizama inuwarsa dakuma lullubinsa” gyadama Gwaggo kai Mom tayi takama hannun Riyad tarike gam tana kallonshi tace “Gwaggo meya musu Riyad dako zaman gidan nan baiso, na tabbata baimason ya gaji kujeran nan, dan bata gabanshi” Gwaggo tace “kwarai” Mom tace “shi kadai Allah yabani, shi kadai gareni, Riyad kadai Allah yabani yau ana kokarin rabani dashi” kankame hannunshi tayi tace “Gwaggo zan iya zuwa bangon duniya sabida Riyad! Kuma nayi alkawari duk Wanda yace zai cutar da yarona saidai yafara dani dan daga yanzu zan zama shamaki tsakanin Riyad da komi na duniyan nan, zan zama inuwa hazo zan lullubeshi nakuma kareshi daga duk wata hari” sosai Gwaggo take kallonsu sai kawai tai murmushi tadauki charbi ta tacigaba da ja itama bini bini tana tofama yaron addu’a aka.


JOIN GROUP DANAKE POSTING NOVEL DIN NAN


https://chat.whatsapp.com/CrKHphXCxK09RvYbrO1cCU
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: 💫 SANYI DA ZAFI 💫


EPISODE 3️⃣



✍🏻M SHAKUR

WHEN WAS THE LAST TIME KIKA SAYI SABON PANT?🤭 TALK TRUE

BRA DINKI SUN KOMA RUWAN KASA TSABAGEN SAWA KULLUM😒

TO IDAN NACE YAU NAKAWO MIKI HABISHMA UNDERWEARS FA👙💃 SUNA SAIDA PANTS, BRAS, NURSING BRA, MATERNITY GOWNS, NO LEAKAGE PANTS NA PERIOD, KAYAN BACCI DA SAURANSU🔥
SUNADA MOST AFFORDABLE KAYA GA VERY CHEAP DELIVERY NATIONWIDE GO AND BUY NOWWWW!!!

https://www.tiktok.com/@habismaunderwears?_t=8lzVAMnAhgk&_r=1

4 daidai tashiga wani babban kanti na abinci irin local restaurant din nan, wata katuwar mata dake zaune a tsakiyan shagon kan kujera ga lalitan uban kudi a hannunta tana kirgawa ne ta kalleta tace “Allah yasoki baki latti ba” batace komiba kai tsaye tace “ina wuni Maman Miwa” batare data amsaba tace “nidai je ga wanke wanken ki chan na jiranki” bata damu da yanda tamata maganan ba dudda akwai mutane a shagon sunacin abinci tace “bari nai salla naje nayi” bata jira amsanta ba tawuce ciki chan bayan gidan shagon bayi taje tacire kayan jikinta tafito da dogon riga na abayan dake jakanta tana neman gyalen ta tuna tabawa mutumin nan tsayawa tayi chak sai kawai taja gajeren tsakiya saurin datake tazo nan yasa ta manta bata amsaba, karamin farin hijabin tasaka ta dauro alwala tafito tasami waje tai salla sannan ta cire hijabin tasa kan igiya fari ne batason ruwan wanke wanke ko mai ya bata mata taje gaban makwarara, ga wanke wanke zaka dauka na gidan biki ne ga manya manyan tukunyan abinci, omo ta dauka ta tara ruwa abaho dukta kawo sannan ta dauki wayanta kirar vivo duk taci screen tasaka earpiece ta danna waka ta soke wayan aljihun dogon rigan tashigayin wanke wanken da sauri sauri dan tanada kuzari sosai batada kasala ko son jiki.
Wata yar budurwa ce tazo wajen ganinta tana wanke wanke tana waka kasa kasa like zero worries dinnan yasa ta harareta tajuya tafito tadawo cikin shagon tazo gaban mahaifiyarta dahar lokacin take kirga kudi tace “wai Mama Yar gidan HIV dinchan kikesa take mana wanke wanke har yanzu banace ki sallameta ba gashi gashi abinda ake cewa ita da Mamanta sunada shi” batare da maman ta kalletaba tace “koyar gidan kanjamau ce ba HIV ba ina ruwana ko kinada wanda zaki samo dazatamin wanke wanken nan ta share ko’ina har zuwa katon shagon nan akan dubu biyu kullum aduk fadin garin kanon nan?” Baki yarinyar tabude zatai magana Maman Miwa tace “kinga ki kyaleni fa, nagadai nace kiyi aikin nan bayi zakiyi ba” dasauri yarinyar tace “Mama ni kyamanta nakeji wlh, sunada HIV tana mana wanke wanke” dasauri Maman Miwa tace “wai sau nawa zan gayamiki Maman ta kedashi ba itaba yarinyar datake karatun likita, to koma tanadashi me ruwana nagadai ciwon nan ajini yake kuma baya kwarara acikin ruwan wanke wanke ko? Miwa dan Allah ki barni na kirga kudin nan kinatasa ina mance abinda na kirga” tsaki yarinyar tayi tawuce tafita daga shagon cikeda bacin rai.
Kafin 1hr tagama wanke wanken nan tass, tukunyoyin har bayansu ta wanke kal sai kyalli suke ta share ko’ina tashigo shagoma ta share tsaf tai mopping lokacin biyarda rabi sannan takoma baya tasa hijabinta tadauko jakanta ta goya abaya tafito tazo gaban Maman Miwa tace “nagama” kallonta Maman Miwa tayi tace “ohh kudinki ko”? Gyadamata kai tayi, kudin hannunta Maman Miwa tashiga kirgawa taciro 10k tabata tace “gashi na litinin zuwa yau juma’a” murmushi tayi for the first time dan gaskiya she hardly smile kaganta tana murmushi ko dariya to sai in tana tareda Mamanta, takirga kudin tass dubu goma chip chip tace “nagode Allah yabiyaki” tajuya tawuce kallo Maman Miwa tabita dashi ance duk muguntan ka kaji an maka wani addu’an saikaji ranka ya sosu harta fita waje Maman Miwa tace “Rasheeda!” Dasauri yarinyar tajuyo jin an kirata, komawa cikin shagon tayi tace “na’am gani” kallon sales girl dinta Maman Miwa tayi tace “samata shinkafa da tuwo a takeaway takaima Mamanta” wani kalan murmushi tayi dayasa wani hot dimples suka lotsa a kumatunta Ya Allah! She looks damn beautiful dasauri tace “nagode sosai, nagode nagode” Maman Miwa sai kallonta take dan wlh today is the first time in almost 3months data fara musu aiki take ganinta tana murmushi, yarinyar kam badai kyauba, ta tabbata badan cutan su ba da tuni wani babban Alhaji ya aure ta, kawomata abincin akai a leda ta amsa wannan karan saida ta duka tace “nagode sosai Maman Miwa” murmushi Maman Miwa tamata tace “sai Allah yakaimu gobe” gyadamata kai tayi tafice Maman Miwa tabita da kallo wani zubin she wants to be wicked amman kuma indai kai ba shaidan bane u can’t be wicked to this girl cus zata maka aiki tsakani ga Allah dabazaka taba ganin abinda zakai complain akai ba, wanke wanke take maka tsaf, tai shara tai moping kaga ko ina na kyalli, banda haka daidai da tsinke bata taba sata a shagon ba wlh ko kwayar magi bai taba bataba dudda ko basudashi, kowa ya tsaneta kowa kyaranta yake sabida Mamanta but if u look at it ciwo nakan kowa, zata gudu tabar mahaifiyarta ne sabida tabada HIV? No, ba HIV ba ko HIVVV uwarta kedashi uwarta ce, dudda ma taji labari ance mai kudi mahaifiyarta ta aura but taje tai fasikanci tasamo HIV yakorota yace cikin ma ba nasa bane, hmmm tasauke ijiyan zuciya tace “Allah ya kyauta dai”.

Tafiyan datayi zaiyi nisan tafiyan inda zakaje kabiya 200 ko 300 kan adaidaita sahu amman akafa tai tafiyan nan tana shiga layinsu ta tsaya gaban wani chemist ta kirga 6500 tabashi tace “ga kudin maganin nagode” karba yayi yace “an dawo daga aikin Rashy” gyadamai kai tayi batace komiba ya karbi kudin yana kokarin kirgawa daidai ta juyo zata fito wasu maza guda biyu na zuwa wajen daya daga cikinsu yakalli mai shagon yace “kai Bala nagaya maka idan kana bari yarinyar nan na shigowa shagon ka bazaka taba yin ciniki ba ni nama fasa sayan abinda nazo saya mtswww yawa kake wlh gaye” yajuya harya fara tafiya Rasheeda tace “ko dabba yafi jahilin namiji mara ilimi daraja tirr, adaije makaranta akaro ilimi katon banza” chak saurayin ya tsaya saikuma ya juyo yanuna kanshi yana kallonta kur itama Rashida ke kallonshi yace “dani kike”? Dasauri Mai chemist din Bala yazagayo yana daga marfin kanta yafito yace “badakai takeba Rashida tafi gida kudin sun cika nagode” wani kalan kallo tama mai chemist din tace “akanme zakace badashi nakeba Bala? Inba dashi nakeba waye yamaka kama da jahili awajen nan”? Wani tahowa gayen yayi azuciye zai daketa yace “zan sumar dake wlh ke” dasauri Bala yatareshi yace “me haka kai Sani dukan mace zakayi”? Wani kalan dariyan daru Rasheeda tayi tasauke jakanta dake goye abayanta ta ijiye ledan abincin hannunta duka akasa tanuna kanta tace “nizaka daka?” Tasake dariyan keta tace “billahillazi yauka tabani saidai uwarka ta haifo wani zan gwada maka ni dakake gani kaman maza dari ce anan, try me I will make sure namaka abinda baxaka so ka karabin hanyan danake bi ba” tai maganan azuciye cike da fushi da masifa da rashin tsoro, dasauri Bala mai chemist yakalli abokin Sani yace “please rikeshi ku tafi dan Allah Kamal” kamashi abokin yayi yace “muje Bros shareta pls ba riba a fada da mace” Rasheeda tace “kasan Jahili baida ilimin sanin hakan wannan dahar yanzu ake raba shayin safe dashi agida” haba wani kalan fizge kanshi yayi yakawo mata duka da duka karfinshi kaucewa Rashida tayi da sauri yasami bango batai wata wataba ta daga kujeran dake wajen na zaman mutum plastic chair ne ta rapkamai a fuska kafan kujeran ya yakushi bakinshi haba bakinshi sai jini ganin jini abakinshi yayo kururuwa zaiyo kanta da sauri abokinshi da Bala mai chemist suka rikeshi, itama Rasheeda cikeda fitina ba tsoro azuciye tace “ku sakeshi yazo bakaga komiba duk bakin dazai kokarin bullying dina wlh saina fasa bakin, kai kayi kadan kahanani sakewa agarin nan sabida ka ganka namiji, akan wani dalili zaku hanani sakat bazan iya zuwa nasai abubu? Shaguna nawa nadena zuwa na layin nan? Wannan danake zuwa yanzu shima kuce ban isaba sabida wani dalilin ku na banza da wofi, cuta nakan kowa, babu wanda yasan karshen shi, yes Mamana nada HIV and so what? Kubi duniya a sannu kai kanka bakafi karfin kasami cutan ba dakiki kawai mahaukaci, katon banza wanda ake gutsurama buredi agidansu har yau akasa dashi da kannenshi sabida baida zuciyan nema, kar Allah yasa ka kara zuwa shagon siyan abu, jahili kawai” cika shagon akayi da mutane sabida yanda Rashida ke zubamai zagi shikuma yana kokawa dasu Bala asakeshi ya daketa ganin yanda ta fasamai baki, cikin taron mutanen wani dan tsoho ya leko ganinta sai kawai ya shigo cikin shagon yakai hannu ya karbe kujeran ya ijiye gaisheshi mutanen wajen sukahau yi. “Barka da yamma Baba Liman” cikeda hikima na manya ya dubi Sani yace “ayakuri Sani, kekuma wuce mutafi” hannunta yakama yace “wuce mutafi” batai musu ba akumbure cikeda taurin kai tace “ni jakata” sakinta yayi yana kallonta taduka tadauki jakanta ta goya abaya da ledan abincin tarike a hannu tana nishi kaman kirjinta zai fashe sabida fushi saikuma ta dago azuciye dan tanada naci wani zubin kaman mayya, takalli uban mazan dake wajen duk ana kallonta tace “Baba Liman kagayama yan anguwan nan su kiyayeni nida mahaifiyata, bamu shiga gidan kowaba munyi sata, Mama harni baya shiga gidajensu sabida yanda kowa ya kyamace mu, bamu rokesu kudi ba, banzo nacema kowa yabani kaza zankai mahaifiyata asibiti ba dan haka su fita daga rayuwata dana mahaifiyata Baba, sufita na gayamusu, I am enough for Mamana! ni kadai zan iya kula da ita, nayi girma kuma Alhamdulillah inada karfin yimata komi kowa yafita harkana, ban nemi fadan kowaba ban shiga hurumin kowaba dan haka duk wanda yashigo tawa koshi waye wlh sai inda karfina yakare kagaya musu Baba Liman” tayi maganan with a sound warning, ahankali tsohon yace “ya isa!” wucewa tayi fuuuuu tafice daga shagon kowa na wajen jikinshi yayi sanyi wani dakeda shago kusada na chemist yakalli yaron yace “kudaina abinda kukeyi mutanen nan ba akanku suke zaune ba, wlh Allah zai iya saka musu, shidai cuta nakan kowa, yau dauka fasikanci matan tayi tasamu Allah masani amman ina mai tabbatar muku, gulma, keta, rashin mutunci da sa’ido da menene menene kukema matan da yarta kadai ya kore zunubansu” anatse Baba Liman yace “muji tsoron Allah, mun kyamaci mutanen nan shi kadai ya isa wlh kudena takura musu kar Allah yakamaku, kar Allah yakamaku” yawuce shima yatafi, dasauri Bala yace “nima kada ka kara zuwan mini shagona kaje wani chemist din” tsaki Sani yayi yace “ka dinga shiganmata ko zaka mutu iyayyenka dai damuka sani bazasu taba barinka auren tijararriyan yarinyar me kanjamau dinchan ba” yayi maganan yana ficewa dağa shagon abokinsa na binsa.

Gidansu na wajajen karshen layin, wani dan karamin gidane sosai ciki da falo daya ne sai bayi ba kitchen a tsakar gidan suke girki, ko’ina kal kal agidan, maida kofan tayi tarufe tasa sakata tasauke ijiyan zuciya sannan tai murmushi dan bataso Mama tagane ranta yabaci daganan zaure tai shouting “Mamaaaaa, Mama nadawo” tai ciki da gudu labule ta daga Maman na zaune kan dadduma kaganta kamansu daya sak da Rasheeda itama tanada haske but ba kaman Rasheeda ba, batada kiba ko kadan ta rame ta bushe sosai, duka duka bazata wuce 40 ba but she looks kaman wacce ta tsufa, tana zaune kan dadduma tanajan charbi, ijiye kayan hannunta Rasheeda tayi saikuma tai tagumi tana leka fuskan Mama tace “Mama kiyi sauri kigama kimin sannu da zuwa niii” tafadi a shagwabe, hannu Ammi tasa ta shafe addu’an datakeyi sannan tajuyo kawai saita kama kunnenta ta saman hijabin jikinta tace “dan kaniyanki ba alwala yakamata kiyo ba kizo kiyi salla ba” dariya sosai tayi tana yarfe hannu tace “wayyooo kunnina Mama zai cire” sakin kunnin Mama tayi tana murmushi looking so happy tace “imaza to jekiyo alwala kafin lokacin magrib yafice baki salla ba” tashi tayi tafito tsakar gida alwala tayi tadawo tai salla kusada Mama sannan tadauki jakanta tabude taciro kudin tasa a hannun Mama tace “Maman Miwa tabiyani, hotel din nan gobe suma zasu biyani kuma manager tace nakawo zanen tagani idan na iya sosai zasu saya” karban kudin Mama tayi tana kallo tana murmushi Rashida tashiga fito da abincin tace “nabiya nabawa Abdul kudinshi Mama ga abinci Maman Miwa tace nakawo miki” bubbude komi tayi ta tashi tafita dasauri tadauko ruwa a bowl tadawo tazauna takama hannun Ammi tasa aruwan tace “wanke hannun muci” wanke hannunta Ammi tayi ta ijiye kudin agefe ta gutsuro tuwon instead takai bakinta bakin Rasheeda takai dasauri Rasheeda tace “Ammi ke kici” ahankali tace “ni naci abinci namana shinkafa, keko nasan tun safe bakici abinci ba banda karin dakikayi ko kinci wani abu”? Hadiye tuwon bakinta tayı tana fikifiki da ido most of the time idan tana aiki mantawa da abinci take, hararanta Ammi tayi tace “bude bakin, kidena wasa da abinci kinji Doctor” gyadama Ammi kai tayi tana murmushi Ammi nasa mata tuwo abaki tace “ko biscuit ne buy and eat kinji” sake gyadamata kai tayi, haka Ammi tadinga feeding nata kuma sosai taci ita bama tasan takusan cinye tuwon ba saida takalli takeaway dasauri tace “Ammi nacinye miki tuwon” murmushi tayi tace “haka nakeso dama Doctor” tass tacinye tuwon Ammi kuma taci shinkafan ba sosai ba dan batajin yunwa, sannan ta tashi taje tayo wanka da alwala tareda Mama sukai salla ta shiga tattara yan kwanukan zata wanke Mama tace “kibarshi jekiyi zanen ki zanyi wanke wanken” dasauri tace “Mama ni kidaina aiki, bayawa yanzun nan zanyi nagama zanyi zanen” kafin Mama tai magana tafice daga dakin biyota Mama tayi dudda haka tana wankewa Mama na dauraye wa suka gama suka dawo daki tayata Mama tayi ta kwaso board na zanen da colors nata da pen ta zuzzuba tafara zanen kome takeso Mama na mikamata suna cikinyi aka dauke wuta torch light Mama tadauka ta kunna Rasheeda tai murmushi tacigaba dayi sai wajajen 12 tagama tabarsu su bushe gobe zata sasu acikin frame, zama tayi anan danta huta kafin suje su kwanta sai bacci itakuma Mama na tattare brushes din tana dauraye mata su aruwa, munsharin ta da Mama taji yasa tajuyo takalleta ganin yanda take baccin azaune kanta na lilo.


KINASON MAGANA DANI M SHAKUR??? CLICK ON THIS LINK AND CHAT ME UP
wa.me/+2347012181461
[5/18, 10:18 PM] +234 708 918 4042: 💫 SANYI DA ZAFI💫



✍🏻M SHAKUR

JOIN INTIMACY CLASS TODAY WITH JUST 5k MY PEOPLE LEMME TEACH YOU YANDA AKE HAVING AMAZING LOVE MAKING DA YALLABAI! YANDA AKE ENJOYING SEX! YANDA ZAKI TASHI KANSA KIKUMA KWANTAR MAI DA HANKALI.
YANDA ZAKI KWANKWANCE KAN MEGIDA DA MAGANAN BANZA🔥

I AM THE BEST IDAN DAI HARKAN KARATUN NAN NE A HAUSANCE😎

Kimin magana a watsapp +2347012181461






EPISODE 4️⃣


She just wished all this ayyukan wahalan da suffering da yarinyarta yar karama keyi just to take care of her itane keyi mutane bazasu gane rahama ne Allah yamaka lafiya sannan yabaka karfin nema ba gashi tana neman wannan karfin ita tafita tayo aiki ta kula da diyarta daya tak a duniya tarasa, Rasheeda ce zuwa ayyukan shara da wanke bayuka, da wanke wanke just to get paid suci abinci ga school duk ita kadai dan yanzu ma suna hutun school, yarinyarta batasan menene dadin rayuwa ba tunda ta taso sai wahala, Rashida doesn’t deserve to be born like this, ta zaman ma yarta bakin tabo arayuwanta waye zai taba auren Rashida yanzu? Ko anzo ma gulman yan anguwan nan koransu suke, babu kalan sherin da ba’a musu, kowace budurwa irin Rashida nada kawaye ita batadashi kota fara kawance iyayen yaran zasu raba abotan sabida ansan diyar mai HIv ce, yar fasika ne gantalalliya dan haka babu iyayen dakeson yaransu suyi mu’amala da yarta, hawaye masu dumi ne suka gangaro daga idanunta dasauri takai hannunta ta share fuskan tass tareda sauke ijiyan zuciya ahankali tace “Allah na yarda ka kasheni da ciwon nan, Kama karomin cuta daban daban duk na yarda, amman Ya Allah kabama diyata farin ciki arayuwanta, Ya Allah ka kawomata karshen wahalan nan, Ya Allah idan mutuwata zai zamto abinda zaisa Rashidana tadena aikin wahalhalun nan just to take care of me Ya Allah ka dauki raina dudda banson na barta, Ya Allah spare my daughter this harsh way of living and take me instead” tasake share hawayen dasuka zubomata sai kawai tadaura kasan rigan atampanta kan fuskanta tai shiru takai 2min ahaka sannan ta mike taje inda take tallabota tayi tace “Raudah oya muje ki kwanta” ina batamasan anayiba baccin yayi nisa gajiya kuma kesata baccin kaman tamutun nan, kamata Mama tasakeyi tace “tashi muje kinji Rish-rish din Mama” Mama tai maganan tana dagata da kyar ina bamata iya tafiya kaman matatta, kakkamata Mama tayi tasata ajikinta tana tafiya da ita ahankali tanajan kafa kaman irin wacce tasha giya tai tatil din nan, uwar dakin babu komi banda wata yar katifa datake a gyare akasa sai kuma manyan ganamasgo guda biyu na kaya sai dan rio na kayan kwalliya da wasu kodaddun hodon makeup da gorunan turaren humra suke ciki saikuma wata benci haka da littafai ne cike na school akai saikuma lab coat da aka makala a nail na bango jikin aljihun an rubuta Dr Rash ajiki Mama ta kwantar da ita ahankali.


Karfe 4:30 daidai tabude idanunta adduan tashi daga bacci tayi sannan takalli Mama wacce taganta kan dadduma idan da sabo ta saba agurguje ta tashi waje taje tahura wuta tadaura ruwan wanka sannan tashare tsakar gidan taje ta wanko bayi ta watsa ruwan sanyi ita tafito tai alwala tazo ruwan yayi zafi tahadama Mama a bucket tadawo daki dan kaita bayin dan kafafunta na bala’in damunta tace “Mama muje kiyi wanka” tana rike da Mama har bayi Mama tace “karki jirani jeki salla” batai musu ba salla taje tayi sannan tafito ta daura tuwo a wuta ta kwashe kayan da Mama tasa sharp sharp ta wanke ta shanya tasake wucewa hanyar bayi tadawo da Mama dakin dahar ta gyara tafita waje takarasa tuwo tai miya tazuba komi a kula takawo daki sannan ta shirya cikin wani dogon rigan abaya baki wanda stones din duk sun ciccire tadau gyalen zata yana kenan ta tuna jiya saitahau dariya Mama dake shafa mai tace “ke lafiyanki kike dariya ke kadai?” Dasauri tajuyo ta taho wajen Mama tace “Mama wani dan gayun mutumi nasa a bola na zuzzubamai shara bakiga yanda yake makyarkyata ba kaman da zinare aka yishi ba kasa ba” yanda take murmushi tana dariya yasa Mama tace “wa kikasa a bola Doctor?” Dan tsagaita murmushin tayi tabama Mama labari kunnenta Mama taja tace “Rauda wai mesa bakiji ne inda sun kasheki ke fa dakike musu rashin kunya ina kikeso nasa raina why mesa you are always putting yourself in trouble ne eh? Mesa bakiji wai kin dauka wani karfi gareki wai sabida wani baitaba chasaki ba ko” kaman zatai kuka tace “Mama yakuri to kisaki kunnena” sakejan kunnenta Mama tayi dudda bada karfi sosai ba tace “saina cireshi duka, wai mesa bakiji eh? Why wat if wani abu yasameki?” Ganin yanda takeyi da fuska kaman zatai kuka alamun jan kunnen namata zafi yasa Mama tasaki kunnen ahankali saikuma takama kafadanta cikeda damuwa sosai tace “Doctor kinason duk idan kin fita yanzu hankalina yadena kwanciya ne?” Dasauri ta girgizakai, ahankali Mama tace “to yimin alkawari u will not put kanki in any trouble again” murmushi tayi tace “I promise Mama bazan karaba” ijiyan zuciya kawai Mama tasauke dan tasan is impossible cus Rashida and trouble are besties, tashi tayi tawuce takarasa shiryawa ta yana gyalen akanshi ta kwashi uniforms nata tasa ajakan ta sannan tazauna tahada zanen tasaka musu frames Mama sai kallonta take kawai saida tagama tass sanan tazo kusada Mama lokacin 7 daidai tace “Mama maganin safe” tadauko magani bama Mama maganin tayi sannan tacire yar wayanta daga chaji tadauki earpiece dinta tace “Mama bari inje” cikin kudin data kawo jiya Mama tazare 1k tace “ga wannan kihau abin hawa kidena tafiya da kafa hotel din nan da nisa” dasauri ta girgiza kai tace “Mama ki ijiye duk nazuwa asibiti ne next week ni dakafata zan taka ai ba nisa ko ciwon kai kikaji ki kirani zanbar kome nakeyi na dawo zanyi aiki a hotel har karfe daya biyu yau ba airport zandaiga alert, sai karfe 4 ina wajen Maman miwa bye Mama na” dasauri Mama tace “to baxaki daure ko Lipton kisha ba tunda baki iyacin abinci dasafe” dukowa tayi ta rungume Mama tace “Mama zanyi latti ne nakai zansha a hotel din ai ana bamu coffee da biscuit bye Mama kinji” ta shafa fuskan Mama tana kallonta saikuma ta manna ma Mama kiss a goshi tace “Mama kinyi kyau wlh atampan nan zaki bani ita” dan maketa kadan Mama tayi tace “ba Dr yace kidena min irin abubuwan nan ba saina shafamiki ciwo” haderai Rashida tayi sosai tai sauri zata tashi hakan yasa Mama tarike mata hannu tace “zo to fushi kikayi banso kibar gida da fushi yakuri bazan kara miki maganan ba” hawaye idanunta suka tara saikuma tahadiye hawayen saikawai ta rungume Mama tsamtsam kaman yar yarinya tace

Please Login or Register in order to submit comment