Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gilas xin gaba ya fi na baya girma. Saboda gaba ake son yawan

kallo ba baya ba.

378.

Abin da ya fi komai daxi shi ne a yabe ka ba ka nan. Abin da ya fi komai haushi

shi ne a yabe ka da qarya a gaban idonka.

379.

Idan kana neman gata ka nemi Uba. Idan kana neman jigo ka nemi xan uwa. Idan

kana neman garkuwa ka nemi aboki. Idan kana son natsuwa ka nemi mata. Idan kana son
su duka ka nemi uwa.

380.

Haquri iri uku ne: Haqurin abin da kake so idan ba ka same shi ba, da haqurin

abin da ba ka so idan ya same ka. Sai kuma haqurin bin dokar Allah.

381.

Macce ta gari ita ce wadda ta san Abin da ya dace ta yi idan mijinta yana cikin

fushi ko yunwa ko gajiya. Sakarai ita ce wadda ake jin sirrin mijinta daga wurin ta.

382.

Namiji sadauki shi ne idan ya samu alheri sai ya nufo gida wurin iyalansa. Sakarai

shi ne mai dukan matarsa.

383.

Mutum biyu ba a gaskata maganarsu: Mai neman aure da mai neman quri'a.
22

384.

A lahira Munafukai su ne a qasan wuta. Amma a duniya sunayensu ne a saman

Jarida.

385.

Mutum uku kana iya biyan su: Wanda ya fara yi maka sallama, da wanda ya ba ka

wurin zama, da wanda ya yo tafiyayya zuwa wurin ka. Na huxu sai dai ka roqi Allah ya
biya shi: Shi ne, wanda yake da buqata bai ga inda ya dace ya nemi taimako ba sai a
wurinka.

386.

Wanda ba shi yawan magana idan ya yi magana ba a manta ta.

387.

Soyayya kamar yaqi ce, hura wutar ta yana da sauqi, amma kashe ta sai an jajirce.

388.

Kada ka damu da abin da mutane suke faxi a kan ka. Domin ka fi su sanin kanka.

Matakin farko na cin nasara ga rayuwa shi ne ka yarda ba za ka iya daxaxa ma kowa da
kowa ba.

389.

Mai hankali yana da alama. Mahaukaci ma yana da alama. Alamar mai hankali ita

ce natsuwa da kyautata ma mutane, da sanin ya kamata. Alamar Mahaukaci girman kai,
da raina mutane da qyamar su. Idan ya yi nisa sai ka gan shi yana dariya babu dalili.

23

390.

Kada ka damu idan kana yi ba a godewa. Magabata sun ce, aikin jama'a ba a

iyawa, ba a gamawa, ba a yabawa. Idan Allah ya yaba aikinka ya ishe ka.

391.

Hasara ita ce ka tsaya kallon wani yana savon Allah. Riba ita ce ka ribaci roqi

Allah gafara a lokacin da ka ga wani yana savo.

392.

A kyauta ake shiga masallaci amma ka gan shi ba kowa. Wuraren shashanci biya

ake yi amma ka gan su maqil da jama’a. Mutane suna barin garavasar aljanna, suna sayen
wuta da kuxaxensu.

393.

Idan kana sallar dare kada ka raina masu bacci. Da yawa ‘yan aljanna waxanda an

fi su yawan aiki amma da tsarkin zuciya suka kere mutane.

394.

Yaro yana faxuwa. Babba ma yana faxuwa. Idan yaro ya faxi zai tashi ne ya zura

da gudu. Idan babba ya faxi yakan waiwaya ne ya ga abin da ya kayar da shi. Idan ba ka
nazarin jiya gobenka ba ta kyawo.

395.

Idan kana fama da ciwon zuciya, ko baqin ciki ya ci qarfin ka, ka tuna fa a duniya

muke ba a aljanna ba. Duk abin da ya ke damun ka a yau zai wuce ya bar ka, ko ka wuce
ka bar shi, watarana sai labari.

396.

Abu biyu ba su haxuwa ga mutum daya: Rowa da jin daxin duniya.

24

397.

Wata tara kake kwance a cikin cikin ta. Shekara uku kake rungume a qirjin ta. A

tsawon rayuwarta kana zaune daram a cikin zuciyarta. Uwa da babu irin ta. Mu darajta
iyayenmu.

398.

Zunubi xaya ne Shaixan ya yi Allah ya kore shi daga aljanna. Zunubi xaya

Annabi Adam Alaihis Salam ya yi aka fito da shi daga cikin ta. Mu kuma da tarin
zunubanmu ne muke son mu koma a cikin ta. Allah ka cece mu.

399.

Abu uku babu daxi idan suna empty: Ciki da Batur da Aljihu.

400.

Duk wanda ba shi da manufar da zai iya mutuwa a kan ta, to ba shi da manufar da

yake rayuwa a kan ta.

401.

Dutsen da ba ya tare maka hanya bai kamata ya dame ka ba.

402.

Tsakanin Bidi’a da Savon Allah: Mai savo a kodayaushe yana iya yin tuba domin

ya san laifi yake yi. Mai Bid'ah ba zai tava yin tuba ba domin ya xauka a daidai yake.

403.

Kada ka faxa ma mutane hizo nawa ka hardace na Alqur’ani. Ka bari su ga

Alqur’ani yana tafiya kawai a cikin jikinka. Kada ka damu da ina ka kai a cikin
Alqur’ani, ka damu da ina Alqur’ani ya kai a cikin rayuwarka.

25

404.

Abu uku wajibin ka ne ka tsare su: Addininka da Mutuncinka da Qasarka.

405.

Abu uku ba su da makawa: Iska da Ruwa da Mutuwa.

406.

Nasararka ba ita ce wadda mutane suke faxi ba. Babbar nasararka ita ce

kyakkyawan aikinka wanda Allah kaxai ne ya san shi.

407.

Matsalarka ba ita ce wadda maqiyanka suke faxi ba. Babbar matsala a gare ka ita

ce wadda ke tsakanin ka da Allah amma mutane ba su sani ba.

408.

Mamaki: Idan muka yi sadaka da Naira 500 sai mu gan su da yawa, amma idan

muka je da su kasuwa sai su dawo yan kaxan. Idan muka yi awa biyu muna ibada sai mu
gan su da yawa, amma idan muka yi su a kallon movie ko wasar qwallo sai mu ga sun
dawo ‘yan kaxan. Idan muna addu'a sai mu kasa daxewa amma idan muna fira sai
bakinmu ya buxe sosai. Idan muna karanta Alqur’ani sai mu qosa nan take, amma idan
muna chatin sai mu rasa sanin inda lokaci ya tafi. Anya kuwa wannan ba alama ce ta
raunin imaninmu ba? Aljanna fa akwai tsada. Mu sabunta imani.

409.

Yin abubuwa guda uku yana sa ayi wasu uku: Kallo yana sa ayi Zina, jayayya

tana sa ayi faxa, fushi yana sa ayi wauta.

410.

Kyauta tana kawo soyayya, kunya tana kawo alheri, tsafta tana ba da lafiya.

26

411.

Ni'imomin duniya guda uku ne: Matar qwarai, da maqwaucin kirki da xa mai

albarka.

412.

Damuwa kamar hadari ce. Idan ta kankama sai ruwa ya sauka.

413.

Idan ka mutu aka xauko ka ba za a kira ka da sunanka ba, sai dai ace a xauko

janaza. Idan an sauke ka cikin qabari ba za a kira sunanka ba sai dai ace a kawo Mutum.
Daga nan sunanka ya vace sai dai a ce “Marigayi”.

414.

Duniya kamar ruwan teku ce. Duk ka qara sha za ka qara qishi.

415.

Wanda duk ba ka da buqata da shi tsaranka ne. Wanda kake da buqata da shi

maigidanka ne. Wanda duk kake kyautata ma sa zai zamo kamar bawanka.

416.

Idan za ka aiki xan saqo kada ka aiki wawa. Nemi mai hankali da basira. Idan har

ba ka samu ba, to ka je da kanka.

417.

Idan mutane suka guje ka a lokacin da ka shiga jarrabawar rayuwa to ka kwantar

da hankalinka. Allah bai kore maka su ba sai don yana son ya ishe ka.

418.

Kada ka damu idan ka yi kuskure sannan ka gyara. Daga kurakuranka ne kake

karanta rayuwar duniya.
27

419.

Idan ka samu alheri, yi godiya. Idan sharri ya same ka, yi haquri. Idan ni'ima ta

girma ya kamata godiyarta ta girma.

420.

Motsin da ya fi kowane sauqi gare ka shi ne motsa harshenka. Amma kuma ya fi

kowane hatsari da cutarwa a gare ka idan ba ka kiyaye shi ba.

421.

Idan ka saki hawayenka a kan filo ka sake su a banza. Tashi ka kwarara su a

tabarmar sallarka. Idan ka yi haka, ka kai qara wurin mai share maka su.

422.

Darasin da ya fi kowanne zafi a rayuwa shi ne sanin cewa, ba dukkan mutane ne

suke son ka da alheri ba.

423.

Kada ka himmatu wajen yawaita abokai. Zavi na kirki ka manta da saura.

424.

Abu uku muna da buqatar su a kullum: Jarunta don canja abin da ake iya canjawa.

Da Haquri don jure abin da ba a iya canjawa. Da Hikima don samar da canji mai ma'ana.

425.

Macce ta fi son ta zama mai kyau fiye da ta zama mai basira. Saboda maza sun fi

amfani da idanunsu fiye da amfanin da suke yi da hankulansu.

28

426.

Sadaka ita ce maganin bala'i. Yi sadaka a yau. Gobe ba za ka iya ba. Domin

likkafani ba ya da aljihu.

427.

An tambayi wani gwani a harkar duniya, me ya fi komai nauyi? Sai ya ce rashin

akin yi.

428.

A lokacin da Allah ya so fitar Annabi Yusuf Alaihis Salam daga kurkuku bai

umurci bango ya tsage ba. Mafarki ne ya sanya Sarki yi, sai ya zama dalilin fitar sa da
xaukakar sa. Allah mai yi ko babu dalili. Amma yana yi da dalili don mu qara karatu.

429.

A addinin musulunci an koya mana cewa, aljanna tana qarqashin qafafun iyaye.

Amma a yau wasu na koyar da cewa, aljanna tana bisa gawawwakin musulmi. Suna
kashe mutane a tituna da kasuwanni da masallatai. Idan ba ka koya ma xanka addinin
qwarai ba zai koyi addini xan jabu.

430.

Ruwa ruwa ne ko a cikin me aka sa shi. Kada ka damu da qyaleqyali, nemi

gaskiya.

431.

Da yawa alherin da ya kubce maka da ka same shi ba zai zame maka alheri ba.

Roqi Allah alherinsa, ka bar zavi a hannunsa.

432.

Kada ka raina qananan zunubai. Da qaramin dutse ake yin tuntuve ba da babba ba.

29

433.

Yahudawa sun zagi Allah. Mushrikai sun zagi Manzon Allah. Idan kana

tsammanin ka tsira daga bakin mutane ka yi wauta. Maganar mutane kamar duwatsu ce;
ko ka xora su a kanka ka sha wahala ko ka take su a qarqashin qafafunka ka haura sama.

434.

Ciwo ba a jiki kawai yake ba. Akwai ciwo a tunani, akwai shi a hali da xabi'a.

Idan ka ga mai kaushin hali ka roqa masa sauqi daga Allah.

435.

Idan kana da ciwo a jikinka rigarka za ta rufe shi. Idan kana da ciwo a tunaninka

bakinka ne yake kware shi.

436.

Mutunta Mutum ba ya nuna kana son sa. Amma yana nuna kana da Tarbiyya. Ba

sai wanda ake so ake mutuntawa ba.

437.

Sau da yawa mutum yake murmushi amma ransa na cikin jin zafi. Domin ya yi

amanna cewa, bayan wuya sai daxi.

438.

Mai ba da haquri ba lalle ne ya zama mai laifi ba. Wani lokaci iya zama da jama'a

ke sa ka ba su haquri alhalin ka fi su gaskiya.

30

439.

Wasu Manya a qasashen waje suke yin karatu. Idan ba su da lafiya a qasashen

waje suke shan magani. A can ne kuma suke shan iska. Abu xaya ne suke yi a cikin
qasarsu, shi ne sata. Kishin qasa shi ma addini ne.

440.

A da, malamai ba su damu da abin duniya ba. Masu duniya na bin su da ita don

neman iliminsu. A yau malamai ke bin masu duniya don neman ta daga wurin su.
Wannan ya sa masu duniya gudu su bar masu iliminsu.

441.

Mutum yakan shiga wani yanayi sai ya xauka cewa qarshensa ya zo kenan. Amma

daga bisani sai ya gane cewa, wannan shi ne farkon jin daxin sa a duniya. Da yawa qofar
da kake zaton ta a kulle idan ka tura ta za ka same ta a buxe tana jiran isowar ka. Kada ka
yanke qauna daga alheri. In da rai da rabo .

442.

Yi qoqari ka mayar da wuninka kyakkyawa duk halin da ka samu kanka a cikin

sa. Idan ka qi ko ka so za ka wuni a cikin sa.

443.

Magana mafificiya ita ce ambaton Allah. Kyauta mafificiya ita ce ka yi ma wani

addu'a. Rana mafificiya ita ce wadda ba ka sava ma Allah ba a cikin ta.

444.

Ababe masu daraja ba su cika maimaituwa a rayuwar xan Adam ba. Shi ya sa

kowane mutum uwa xaya kacal gare shi.

31

445.

Wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Wanda ya sa wani kuka Allah zai

sa shi kuka. Duk wanda ya shuka alheri zai ga alheri a rayuwarsa da bayan mutuwar sa.
Idan kuwa ka shuka sharri to sharrin ne za ka girba komai daxewa.

446.

Kada ka xauka cewa, addu'a makamin raggo ce. Addu'a makamin mumini ce. Da

dare yake wasa wuqarta, a wayi gari ya ga aikinta.

447.

Ba a son Rowa sai a wuri xaya. Idan ka shiga cikin haqqin mutane za su kwashe

ladarka su shige aljanna da ita kana kallo. Yi rowar ladarka.

448.

Idan ka shiga gidan mutane ka mayar da kanka makaho. Idan ka fito ka koma

kurma. Kamar yadda ba ka son a leqi asirinka kuma a yaxa shi, haka su ma mutane ba su
son a leqi nasu ko a yaxa shi.

449.

Mai riqe addini ba jin daxi ne bai iya ba. Macce mai hijabi ba ado ne ba ta iya ba.

Mai kyauta ba kuxi ne ba ya so ba. Kowannen su ya qware ne wajen sanin abin da ke
amfanin sa. Sai ya rinjayi son zuciyarsa.

450.

Idan wani ya ce maka wane ya zage ka, ka tambaye shi, ya aka yi ya ji daxin zagi

na a gabanka?

32

451.

A cikin hadisi Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya hana mutane zagin Zakara

saboda yana ta da mutane Sallah. To, me ina kuma ga mai zagin malamai masu wa'azi da
karantar da mutane yadda ake Sallah?

452.

Yana da daxi ka samu wanda kake so. Yana da daxi ka samu wanda ke son ka.

Abin da ya fi wannan daxi shi ne ka samu wanda zai sa ka san Allah, ka so Allah, ka bi
Allah.

453.

Ka yi hulxa da mutane a matsayinsu na mutane. Kada ka auna mutane da kuxi ko

matsayi ko wani abin duniya. Abin duniya mai wucewa ne ya bar xan Adam a kan
matsayin sa.

454.

Gano Abin da mutane suke so ba shi ke da muhimmanci ba. Abin da yake da

muhimmanci shi ne ya za ka zama wanda mutane suke so? Wanda ya fi shi muhimmanci
shi ne sanin ya za ka zama wanda Allah yake so?

455.

Karanta littafi ba shi yake da muhimmanci ba kamar sanin me ka qaru da shi a

cikin sa?

456.

Rayuwa tana ba ka wata dama a kullum sunan ta "Gobe". Abin da ya gagare ka a

yau sai ka hari gobe da shi. Gobe ma rana ce.

33

457.

Kowane mutum yana da wani rubutu a goshinsa wanda ido bai ganin sa amma

masu hankali suna karanta shi. Abin da aka rubuta shi ne: "Ka kula da ni. Ka ba ni
muhimmanci".

458.

Ka je duk inda kake so. Ka vuya duk inda kake so. Amma kada ka manta komai

daxewa sai ka tafi wajen Allah. A yau ake aiki, gobe ranar sakamako ce.

459.

Wasu mutane ba ka iya tuna farkon haxuwar ka da su, amma sukan zama jigo a

rayuwarka. Sanin Maza jari ne.

460.

Ka zama kai kaxai ya fi kana tare da wanda bai dace ba. Nemi abokin qwarai.

Zama da maxaukin kanwa shi ke sa farin kai.

461.

Babu Abin da yake tabbas a duniya sai Canji. Komai ka gani a yau watarana zai

canja daga yadda ka san shi. Komai yana canjawa ban da sarautar Allah.

462.

Ruwan gulbi da na teku duk ba su iya kashe wutar lahira. Amma hawayenka za su

iya. Hawayen tsoron Allah ko na tausayin bayinsa su ke kashe wutar azabar Allah.

463.

Maganin ciwo haquri. Maganin wauta kawaici. Maganin gajiya bacci. Maganin

matsala addu'a.

34

464.

Qwaqwalwar mutum kamar lema ce. Ba ta aiki sai an buxe ta.

465.

Ka riqe gaskiya, kada yawan mabiya ya ruxe ka. Shaixan ya fi kowa yawan

mabiya, amma ba za su hana shi shiga wuta ba.

466.

Duniya rana biyu ce. Ta farko taka ce, ta biyu ta xan uwanka. A ranarka kada ka

yi rowa. A ranar xan uwanka kada ka yi raki.

467.

Yarda da kai ba girman kai ba ne. Kuskure xaya ba ya nuna mai mugunta. Girma

ba a babbar riga yake ba. Mai girma shi ne wanda ake so, kuma ake samun alheri a wurin
sa.

468.

Kada ka raina kanka don wani ya fi ka iyawa. Koma wani fanni ka nemi taka

qwarewa. Kowa da irin hikimar da Allah ya ba shi.

469.

Sarki abin girmamawa ne a garin sa. Malami abin girmamawa ne a garin kowa.

470.

Babbar bishiya ta fi ba da inwa fiye da yadda take ba da 'ya' ya.

471.

Ka aurar da xanka duk sadda kake so. Ka aurar da 'yarka duk sadda ta samu miji.

Idan Macce ta samu mijin tsara ba daidai ne ayi masa jinkiri ba.

35

472.

Idan Alqur’aninka ya yi qura ka zargi kanka. Duk wanda ya kwana uku bai

karanta Alqur’ani ba lallai ne zuciyarsa za ta bushe.

473.

Idan ka mutu ma'aikatarka za ta xauki wani ma'aikaci, matarka za ta auri wani

namiji, dukiyarka za ta samu wani mamallaki ba kai ba. Ba Abin da za ka je lahira da shi
sai aikinka. Gyara lahirarka, kada qyalqyalin duniya ya ruxe ka.

474.

Ababe uku suna da wuya amma suna da amfani. Kyauta a cikin talauci, da kamun

kai a lokacin kaxaici, da faxin gaskiya a gaban wanda kake tsoro.

475.

A lokacin da kake qarami kana ganin laifin manya idan suka yi maka gyara,

amma da ka girma sai ka gane su ne daidai. A lokacin kana makaranta kana ganin laifin
malamai idan suka matsa ka bi doka, da ka zama Malam sai ka gano ashe su ne daidai.
Ka riqa ba da uzuri ga wanda ba matsayin ku xaya da shi ba, wataqila watarana za ka
gano shi ne daidai.

476.

Gaskiya zuma ce. Akwai harbi amma tana da zaqi. Wanda aka buge shi da bulalar

gaskiya bai faxi ba, ka sa masa ido, idan ya qarasa gaba zai faxi.

477.

Ana ba da baya wani lokaci ba don tsoro ko jin girman kai ba. Sai don kauce ma

karo da wanda bai dace ba.

36

478.

Mai hankali idan ya yi magana sai ya kawo hujja. Wawa idan ya yi magana sai ya

yi ta rantsuwa. Mai gaskiya ba ya buqatar rantse rantse. Gaskiya ba ta neman ado.

479.

Ana samun Rayuwa mai daxi ta hanyar barin wasu abubuwa fiye da yadda ake

samun ta ta hanyar samun wasu.

480.

Wanda yake ba da turare ba za a rasa qamshi a hannunsa ba. Mai yin alheri ba zai

rasa samun alheri ba.

481.

Mai mugun hali kamar mataccen shantali ne. Ba a iya amfani da shi, kuma ba a

iya mayar da shi ya koma laka.

482.

A duniya mutane iri huxu ne: Wani yana bin Allah kuma yana cikin jin daxi.

Somin tavi ne aka ba shi. Wani kuma yana bin Allah amma yana cikin wahala. Wannan
yana cikin jarabawa. Na uku ba ya bin Allah kuma yana cikin wahala, wa'azi ake yi masa.
Na huxu yana cikin savon Allah dumu dumu amma yana walwala da jin daxi. Wannan an
yi masa kamun talala, idan mutuwa ta riske shi ba mafita. Allah ya kiyaye mu.

483.

'Ya'ya ba su cika sanin irin son da iyaye ke yi masu ba har sai sun girma sun haifi

nasu 'ya'ya su ga yadda suke son su.

37

484.

Komai yana da musaya a duniya. Macce za ka auri wata, 'ya'ya za ka haifi wasu,

abokai ma za ka samu wasu. Iyaye ne kaxai ba su da musaya. Mu san matsayin
iyayenmu.

485.

Wayewa ba ita ce sanin duniya ba. Wayewa ita ce sanin manufar da ta kawo ka

cikin ta, da neman gamawa lafiya da ita.

486.

Mutum xaya, a kwana xaya, zai iya rusa abin da mutum xari suka yi a kwana xari.

Gwani shi ne mai gini ba mai rusau ba.

487.

Allah ya yi mutane don a so su, ya yi kuxi don a kashe su. A yau muna cikin

matsala ne don muna son kuxi, muna kashe mutane.

488.

A lokacin da kake cikin damuwa ka tuna wani na can yana fatar kasancewa a

cikin yanayinka. Wani yana gudun hijira, wani yana kurkuku, wani yana asibiti, wani ma
yana cikin kabari. Gode ma Allah, ka ci gaba da rayuwa. Ba kullum take salla ba.

489.

Aljanna da Wuta duk na masu zunubi ne. Wuta ta masu zunubi ce su kangare.

Aljanna kuma ta masu zunubi ce suna tuba.

490.

Idan ka yi zunubi sannan kuma ka ji cewa Allah ba zai yafe maka ba to Shaixan

ya yi maka bugu biyu kenan.

38

491.

Wanda ba ya fahimtar shirunka ba lallai ne ya fahimci maganarka ba.

492.

Idan zuciyarki ta nuna maki sha'awar ki bayyana sashen jikinki don mutane su

gani, ba damuwa. Ki bayyana iya wurin da kike son wutar jahannama ta qone shi.

493.

Kafin ka yi alfahari da iyayenka, yi qoqari ka zama abin alfahari ga 'ya'yanka.

494.

Mabuxan talauci guda uku ne: Bacci da Rowa da Tsoro.

495.

Jin daxin duniya shi ne ka tuna babu abin da zai same ka sai wanda Allah ne ya

qaddara maka.

496.

A duniya mutane goma ke akwai. Xaya yake aiki, biyu suke yabawa, uku na

gunaguni, huxu suna zagin sa. Manta da mutane, ka yi aikin gabanka. Ka tuna: Nasara ba
ta da qafafu da za ta cim ma ka, kai ne kake da su. Yi hanzari ka same ta.

497.

Ka nisanci mugun zato domin kai yake cutar wa. Ka yi hattara da qeta domin mai

yin ta ne take cinyewa. Ka kiyayi hassada domin mai yin ta zuciyarsa ke bushewa. Kada
ka zargi iyali domin aure yake kashewa. Tsaftace zuciyarka a wajen hulxa da kowa.
Wannan shi zai ba ka ni'imar duniya ta haqiqa.

39

498.

Imani shi ne ka nemi yardar Allah ko da mutane za su yi fushi da kai. Kada ka

gode ma kowa a kan arzikin da Allah ne ya ba ka shi. Kada ka zargi kowa a kan abin da
Allah ne bai ba ka shi ba. Arziki nufin Allah ne, kuma rabo ne da yake bayar wa ba tare
da ya yi shawara da kowa ba.

499.

Bayarwa ba shi kaxai ne kyauta ba. Hanawa ma wani lokaci kyauta ce. Voye aibin

xan uwanka, ko voye masa cutarka, ko kame masa harshenka, duk wannan kyauta ce abar
godewa.

500.

Idan kana son gane duniya kake so ko lahira? Ka duba, wane ka fi farin ciki da shi

wanda zai ba ka, ko wanda za ka ba?

Mu haxu a kashi na uku cikin yardar Allah

40


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment