Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DUNIYA MAKARANTA

2
(Hikimomi 251-500)

Rubutawar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

1

Bugawa da Yadawa:
Bugu na farko 1437H/2016
Haqqin Mallaka @ Mawallafi

mansursokoto@yahoo.co.uk
isbn 9960-49-972-3

2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Gabatarwa
Yabo da godiya da’iman wa abadan su qara tabbata ga Allah. Tsira da sallama da
gaisuwa zuwa ga Annabinmu fiyayyen halitta, shugaban Annabawa, jagoran
Manzanni; Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki xaya.
Wannan shi ne littafi na biyu a jerin darussan Duniya Makaranta da muka fara
bugawa, wanda tasharmu mai farin jini ta Wisalhausatv take yaxawa a duk
marece da safiya.
Babu shakka na samu qwarin guiwa matuqa daga karvuwar da littafi na farko ya
samu, musamman ganin yadda aka riqa buga shi a garuruwa daban daban ana
rarrabawa kyauta ga jama’a a lokutan bukukuwan aure da makamantansu.
A dalilin wannan maraba da aka yi da littafin na duqufa ga inganta shi ta hanyar
rubuta wani sabon littafi mai suna “Abokin Fira” wanda yake kawo labarun kunne
ya girmi kaka masu tabbatar da sahihancin waxannan darussa na Duniya
Makaranta. Littafin yana gaf da kammala kuma da yardar Allah kashinsa na farko
zai fito ba da daxewa ba.
Mai karatu zai lura mun sanya ma waxannan darussa lambobi, ci gaba a kan na
farko don sawwaqe komawa gare su.
Allah nike roqo ya karvi wannan aiki, ya amfanar da ni da waxanda suka karanta
shi.
Baban Ramla
Jum’ah 8 ga Rajab 1437H
(15 ga Afrilu 2016)
A Sakkwato Babban Birni

3

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
251.

Idan za ka faxi magana ko za ka bayyana wani ra'ayi kada ka xauka maganarka ta

fi ta kowa ko ra'ayinka ya fi na kowa. Duk wanda ka gani yana da ra'ayi, yana da fahimta.
Fahimta fuska ce, ra'ayi riga ne; kowa da irin tasa.

252.

Ba dole ne a kowace magana ya kasance kana da wani ra'ayi ba. Idan kana da shi

ba dole ne sai ka faxa ba. Idan ka faxi ba dole ne kowa ya goyi bayanka ba. Wanda bai
goyi bayan ra'ayinka ba ba dole ne ya zama maqiyinka ne ba. Mu koyi zaman duniya.

253.

Idan kana savani da wani ba dole ne sai ka qaurace masa ba. Idan har ka buqaci

qaurace masa ba dole ne kowa ya qaurace masa ba. Sa'ar da kake qin wani sannan wani
yake son sa. Kowa da kiwon da ya kama shi.

254.

Idan ka ji kana son mutum ka bayyana masa kana son sa, sai danqon zumunci ya

yi qarfi a tsakanin ku. Idan ka ji kana qin mutum ka voye masa. Wataqila nan gaba zai
amfane ka, ko ya taimake ka, ko ka ga wani alheri tare da shi, sai sabuwar soyayya ta
qullu a tsakanin ku.

255.

Tsuntsu a kan reshe ba ya damuwa da kariyewar sa. Ba ga reshe ya dogara ba, ga

fukafukansa. Saki reshe, kama tushe. Saki kowa, kama Allah.

256.

Ka koyi kawaici kamar yadda kake koyon magana. A lokacin da magana ta kasa

amfanin ka kawaici zai iya kare ka .
4

257.

Idan kana tunanin za ka iya canja duniya, to ka hanzarta ka yi tun ba ka yi aure ba.

Idan ka yi aure ko canja tashar talabijin a gidanka sai ya gagare ka.

258.

A lokacin da kake saurayi burinka shi ne aure. Idan ka yi aure sai ka riqa addu'a

kana son 'ya'ya. Idan sun girma sai ka riqa fatar ka rabu da su, su ma su yi aure. Daga
baya za ka gaji da aiki ka buqaci ritaya. Sai ka sake komawa kai kaxai, kewa ta dawo
maka. A da, hawa kake yi, a yanzu gangara kake yi. Kana son hardace Alqur’ani amma
qwaqwalwarka ba ta xauka. Kana sha'awar koyon larabci amma ba za ka iya ba. Sallar
dare da yawan azumi duk suna ba ka shawa amma lokacinsu ya wuce. Wannan shi ne
labarinka a duniya. Ka nemi lahira tun da wuri kafin lokaci ya qure maka.

259.

Idan ka ji alamar girman kai zai shige ka, ka duba qarqashin qafarka ka kalli qasa

wadda ita ce asalinka, ka faxa ma zuciyarka "Daga can muka fito, kuma a can za mu
koma".

260.

Abu biyu kada ka yi sakaci da su: Abokin qwarai da Aikin qwarai. Abu biyu

kuma ka ci moriyar su tun ba su wuce ba: Dama da lokaci. Abu biyu kada ka gajiya da
neman su: Lafiya da zaman lafiya.

261.

Abu uku suna hanzarta tsufa: Fushi da Hassada da Yawan damuwa. Babban

maganin su shi ne Yafiya da sanin Allah da bar ma Allah.

262.

Duniya fuska huxu gare ta: Murna da Damuwa da Ciwo da Lafiya.
5

263.

Tsadar kaya da araharsu duk ba su hana xan Adam cin arzikin da aka rubuta masa.

Nemi halaliya. Saurin nema ba ya kawo samu.

264.

Tufafi su ne suturarka ta zahiri. Tsoron Allah shi ne suturarka ta baxini. Yi qoqari

ka gyara ciki da wajenka.

265.

Idan kana cikin damuwa ka yi shiru. Idan an vata ranka ka yi Haquri. Idan kana da

kuxi ka yi kyauta.

266.

Ba yarda da kuskurenka ne yake da muhimmanci ba, xaukar matakin gyarawa.

267.

Kauce ma maqiyi guda xaya ya fi yin aboki xari.

268.

Wasu mutane kamar Sukari suke a cikin rayuwarka. Ko ka daina ganin su amma

xanxanonsu yana nan.

269.

Idan ka tuna yadda magabata suke duqufa ga karatun Alqur’ani sai ka duba yadda

muke duqufa wajen latsa wayar hannu. Kowa da kiwon da ya karve shi.

270.

Idan za ka roqi Allah ba sai ka sa kati a waya ba. Ba sai ka yi booking

appointment ba. Babu jakada, babu shamaki. Idan ka fara roqon Allah ba buqatar sai ka
xaga murya, don ya san abin da ka faxi da wanda ba ka faxi ba.

271.

Sassafta muryarka, amma ka gyara zancenka. Da Ruwan Sama ne ake samun

shuka ba da tsawa ba.

272.

Idan mutane suka riqa gwamatso da kai a sha’anin duniya, bar ma su ita kawai.

Amma idan suka gwamatse ka ga sha’anin addini da samun lada yi sauri ka wuce su.
Allah yana ba da duniya ne ga kowa da kowa, amma lahira kam sai masoyansa.

6

273.

Hudahuda ya yi dalilin musuluntar mutanen qasar Yaman. Tururuwa ta canja ma

Annabi Sulaimana hanyar tafiya. Giwa ta qi karbar umurni a lokacin da Abrahata yake
nufin rusa Ka'aba. Ko cikin dabbobi akwai masu basira.

274.

Wanda yake cikin ginin gilashi ba daidai ne ya yi wasar jefa dutse ba. Lura da

ayubbanka da zunubanka, ka manta da na mutane.

275.

Banbancin Ilimi da kyan fuska: Allah ya bai wa Annabi Yusuf (Alaihis Salam)

ilimi da kyawo. Kyawonsa ya kai shi kurkuku, iliminsa ya fis she shi.

276.

Sallah ita ce abu na farko da za a tambaye ka gobe qiyama. Kada ka mayar da ita

qarshen abin da ya dame ka.

277.

Duniya kowa tafiya yake yi. Hanyarmu xaya ce, amma masauki kowa da nasa.

Wasu za su sauke kayansu a aljanna, wasu ko qarshensu makamashin wuta. Ya Allah ka
yi mana garkuwa daga shiga wuta.

278.

Ababe uku ne suke maganin wahala: Addu'a, da Godiyar Allah, da Taimakon

mabuqata.

279.

Wasu mutane kamar madubin likita suke. Laifi qarami girmama shi suke yi.
7

280.

Hawayenka littafinka ne. Babu mai karanta shi daidai sai masoyanka.

281.

Idan za ka yi hukunci kada ka saurari vangare xaya. Sau da yawa mayaudari yake

kuka, ga mai gaskiya a gefe yana kallo.

282.

Kada ka zama kamar alawa a shanye ka. Kuma kada ka zama kamar maxacci a

furzar da kai. Ma fi alherin al'amurra shi ne na tsakiya.

283.

Nasiha: Kada ka ci abinci bayan ka qoshi. Kada ka yi magana in da babu buqata.

Kada ka zauna da wanda ba ya qimanta ka.

284.

Da abinci a hannunka kake bin tsuntsu yana tserewa saboda ya fi son 'yanci da

abinci. Wasu' yan Adam a nan tsuntsu ma ya fi su.

285.

Annabi Musa Alaihis Salam ya ratsa tekun Maliya a cikin akwati shi kaxai ya fita

lafiya qalau. Fir’auna ya ratsa tekun a cikin dubun dubatar jama’arsa amma ya nutse a
ciki. Idan kana tare da Allah lamarinka duk mai kyau ne.

286.

Idan kana kula da lokacinka, kana jin sauqin ibada, ba ka jin wahalar yin sadaka,

kana kwaxayin bin Sunnah, kana kusantar mutanen kirki, to kai ne kake cikin Rayuwa
Mai Daxi.

8

287.

Ba da kuxi kawai ake sadaka ba. Zikiri da addu'a, da Murmushi da Fara'a duka su

ma sadaka ne .

288.

Tsakanin Miji da Mata: Idan ya yi kuskure za ta nuna damuwa sai ya ba ta haquri.

Idan ta yi kuskure zai nuna damuwa, sai ta yi kuka, sai ya ba ta haquri! Mata ‘yan gata. In
ba ku ba gida.

289.

A wuri biyu ne ake gane kirkinka: Yin Haquri idan ka rasa, da bayarwa idan ka

samu.

290.

Sau dubu ashirin da huxu ne xan Adam yake shexawa tsakanin wuni da safiya.

Ni'imar Allah dubu ashirin da huxu kenan. Me kake yi ma Allah don godiya?

291.

Ka yi abota da duk wanda kake so, amma ka sani abu xaya ne zai abokance ka a

cikin qabarinka; shi ne aikinka da ka aikata.

292.

An tambayi wani malami mai hikima, ko ka san wanda ake karvar addu'arsa? Sai

ya ce, a'a. Na dai san wanda yake karvar addu'a. Wannan shi ya san Allah. Wani kuma
mahaifiyarsa ta fashe da kuka yana cikin halin mutuwa, sai ya tambaye ta, idan ke za ki
yi min hisabi za ki sanya ni wuta? Ta ce, a’a. Wallahi ba zan iya sanya ka cikin wuta ba.
Ya ce, to, Allah yana so na fiye da ke, kuma yana tausayi na fiye da ke. Wannan shi ya
kyautata zato ga Allah.

9

293.

Da ace bankuna suna cire mana kuxi idan muka ci naman wani su jefa ga akawun

xin sa, da mun kama kanmu. Amma da yake ladarmu ce ake cirewa ba mu ji sam, ko a
jikinmu.
294.

Mai bacci ba ya sanin mafarki yake yi har sai ya farka. Haka duniya take; ba ka

sanin kana cikin ruxi sai mutuwa ta riske ka.

295.

Idan kana iya yin awa xaya a kan keke don ka rage kitsen jikinka, don me ba za

ka iya tsayawa minti goma sha biyar a gaban Allah kana neman rage zunubanka ba?

296.

Iya dambe da kokawa ba shi ne qarfi ba. Cikakken qarfi shi ne iya kama kai da

haxiye fushi.

297.

Ana haifuwar xan Adam a jimqe da hannayensa saboda kwaxayin duniya da Abin

da yake sa ran ya samu a cikin ta. A ranar mutuwa yakan buxe su don ya tabbatar bai
samu komai ba a cikin ta.

298.

Idan mugu ya haxu da na qwarai nan take asirinsa yake tonuwa. In da wahala take

shi ne idan mugu da mugu suka haxu, wanne ne ya fi Mugunta! Idan na qwarai guda biyu
suka haxu wanne ne ya fi alheri?

299.

Mutum komai matsayinsa akan samu givi a cikin tunaninsa, ko kuskure a cikin

aikinsa, matuqar shi ba Annabin Allah ne ba. Amma a cikin mutane akwai waxanda bai
dace ana faxin kurakuransu ko ayubbansu ba.

10

300.

Duk lokacin da Shaixan ya haxu da iyalansa babu abin da suke farin ciki da shi

kamar abu uku: Musulmin da ya kashe xan uwansa, da mijin da saki matarsa, da xan
Adam mai rowa don tsoron talauci.

301.

Babbar musiba ce mai gaskiya ya yi shiru, maqaryaci ya saki bakinsa. Babbar

fitina ce malami ya yi kawaici, jahili ya xaga muryarsa. Abin da ya fi wannan hatsari shi
ne, mai gaskiya ya yi qarya ko malami ya yi aikin jahilci.

302.

Sau da yawa kana buqatar qarfi ne idan za ka aikata mugunta.

303.

Ba za ka ji daxin ibada ba sai ka bar abu uku: Ka daina neman yardar mutane ka

nemi yardar Allah. Ka daina cin haram ka nemi halaliya. Ka bar abota da Fasiqai ka yi da
mutanen kirki.

304.

Idan ka bari wani ya gano dalilin kukanka, a gobe shi zai sa ka kuka. Rufa wa

kanka asiri don ka tsira da mutuncinka.

305.

Dariyarka da kukanka duk ba su tsayar da rayuwa. Komai zai ci gaba idan ka yi

murna ko ka yi baqin ciki. Sassafta ma rayuwarka kada ka kashe kanka a banza.

306.

Ana son Macce ta mutunta gavovi uku daga jikin mijinta: Hancinsa, da idanunsa,

da kunnuwansa. Ma’ana, kada ta bari ya shaqi wari, ko ya ga qazanta, ko ya ji hayaniyar
da ba ya so a cikin gidansa.

11

307.

Aboki kamar matakalar bene ne. Ko dai ya yi sama da kai, ko kuma ya yo qasa da

kai. Zavi abokan da kullum sama suke yi da kai; masu amfanin ka.

308.

Soyayya tana dushewa. Mutum yana mutuwa. Idan kana da gata ban da Allah

watarana za ka tashi ba ka da gata. Allah abin dogara.

309.

A hannunka, yatsan da ya fi kowane nisa da ‘yan uwansa shi ne babban yatsa.

Duk da haka sauran ba su iya komai sai tare da shi. Ba kusancin xan uwa ne muhimmi
ba, amfaninsa.

310.

Mai yawan kuka ba ya rabuwa da baqin ciki. Mai yawan godiyar Allah ba ya

shiga damuwa. Idan kuma ya shiga take za ta koma murna.

311.

Ba a san coffee zai yi daxi ba sai da aka haxa shi da Sukari da Madara. Haka ne a

rayuwa, amfanin wani ba ya tabbata sai da wani.

312.

Tuna mutuwa yana sa abu uku: Saurin tuba, da wadatar zuci, da himmar ibada.

Manta mutuwa kuwa yana sa abu uku: Jinkirin tuba, da haxama, da kasala wajen bautar
Allah.

313.

Idan muka rasa kuxi mukan ji ciwo, mu samu damuwa. Amma a kullum muna

rasa kwanukanmu na duniya ba mu ji a jikinmu. Kuxi abokan tafiya.
12

314.

Sau da yawa nasihar da ba ka son ji ita ce wacce kake buqata.

315.

Abin da ya fi komai takaici a alqiyama shi ne, ga ladarka ba ka iya ba iyayenka da

'ya'yanka da masoyanka amma kana kallo za a xauka a ba maqiyinka don ka ci naman sa
ko ka zalunce shi.

316.

Ba kowa ne zai ga sakamakon aikinsa ba. Amma kuma babu wanda zai samu

sakamako sai da aiki.

317.

Idan ka yi ma wani alheri ka yi shiru. Amma idan wani ya yi maka alheri ka

yayata.

318.

Idan ka kalli baya akwai abin da zai sa ka damuwa. Idan ka kalli gaba akwai Abin

da zai ba ka tsoro. Kalli sama. Can ne ubangijin da ke tausayin ka yake.

319.

Magana mai kyau akan faxe ta da lafazi mummuna. Mummunar magana akan

faxe ta da lafazi kyakkyawa. Kafin ka yi tunanin maganar da za ka faxi, yi tunanin yadda
za ka faxe ta.

320.

Khalid bn Walid ya kasance yakan xauki Alqur’ani ya yi kuka yana cewa, Jihadi

ya hana mu karatun ka. Ikon Allah! Mu kuma a yau me yake hana mu karatun sa?
13

321.

Duniya kamar maciji ce; ga kyau, ga laushi. Amma fa dafin cikin ta ya fi guba

zafi.

322.

Idan ka kai qafarka inda bai dace ba, kada ka ga laifin wanda ya zage ka. Idan ka

tsoma bakinka a cikin abin da bai shafe ka ba, abin da ya same ka kai ne ka janyo shi.

323.

Wanda duk ya xunka tufan kunya ya yi maganin a ga wallensa.

324.

A lokacin da wani zai yi tafiyar awa xaya don ya nemo abinci wani kuma zai yi

gudun awa xaya ne don ya wargaza abincin da ya runtuma ma cikinsa. Duniya zaman
‘yan Marina.

325.

Idan mutum ya mutu abu uku ne suke raka shi. Biyu za su dawo, su bar shi da

xaya. Masu raka shi su ne iyalansa da dukiyarsa da aikinsa. Iyalansa da dukiyarsa sukan
dawo su bar shi da aikinsa. Tanadin abokin zama ya fi tanadin abokin rakiya.

326.

A duniya akwai wanda kake so, akwai wanda yake son ka. Wanda yake son ka a

kullum yana shirin ba ka ne. Wanda kake so kuma a kullum shirin karva yake yi daga
wurin ka.

14

327.

Ba ka samun hutu sai ka daina shiga cikin lamurran mutane waxanda ba su shafe

ka ba. Ba ka zama mai ladabi sai ka san maganar da kake furtawa. Ba ka zama gwani sai
ka iya kama bakinka.

328.

Bishiya ba ta faxi idan ta ji qishiruwa. Ko dai ka ba ta, ko ta mutu salun alun.

Haka wani mai rai yake. Ba a sanin darajarsa sai ya mutu.

329.

Kada ka wulaqanta wanda ya girme ka, watarana kai ne matsayinsa.

330.

Taimaki xan uwanka, tausaya ma qanenka, kyautata ma maqwaucinka. Duniya

inwar hantsi ce.

331.

Talaka ba shi ne wanda bai da kuxi ba. Talaka shi ne marar ladabi da tarbiyya. Ita

kuma Tarbiyya ba a sayen ta, ba a saida ta, koyon ta ake yi.

332.

Mutane kamar madubi suke a gare ka. Idan ba ka ganin komai sai sharri a cikin su

to kai ne masharrancin.

333.

Nasiha: Kafin ka yanke ma mutum hukunci yana da kyau ka saurare shi. Allah

yana son adalci.

15

334.

Masunci yana kama kifi ne ta bakinsa. Idan kifi ya rufe bakinsa masunci ba zai

iya kama shi ba. Rufe bakinka. Akwai masunta da yawa a cikin mutane masu farautar
kurakuranka.

335.

Idan ka bi ta kan manyan gidaje rayuwarka ta gwada maka cewa Allah ya raba bai

ba ka ba, wuce asibiti ka duba. A nan ma Allah ya raba ciwo ba da kai ka.

336.

Kishi kyakkyawan ciwo ne da ba shi da magani sai tsoron Allah.

337.

Hankali da harshe suna hannun riga ne. Idan hankali ya yi faxi harshe zai taqaita.

Idan kuma hankali ya taqaita harshe sai ya qara tsawo. Wanda ka ga maganarsa ta yi
yawa ka tuhumci hankalinsa.

338.

Masu hikima sun ce: Bango ya ce da qusa me ya sa kike damu na? Sai ta ce ma

sa, tambayi mai duka na! Ka riqa yin uzuri ga mutane. Wani lokaci ba za ka iya sanin
hanzarinsu ba.

339.

Masoya sirri suke yi suna nesa da juna. Mafaxata hargowa suke yi alhalin suna

kusa da juna. Kusancin zukata shi ne kusanci ba na gangar jiki ba.

340.

Duk mutumin da kake yawan faxa da shi ba za ka iya rabuwa da shi ba.

16

341.

Idan Allah ya xaukaka ka masoyanka za su san matsayinka. Idan ka shiga

jarrabawa za ka san masoyanka.

342.

An tambayi wata mai hikima, wa kika fi so a cikin 'ya'yanki? Sai ta ce, qarami har

sai ya girma. Da marar lafiya har sai ya warke. Da wanda ba ya nan har sai ya dawo.

343.

Duk mutum bawa ne. Ko ka zama bawan Allah ko ka zama bawan Shaixan ko na

son zuciya. Wanda bai yi sharan masallaci ba ya shari kasuwa.

344.

Makaho bai tava kallon zunubi ba. Kurma bai tava sauraren qarya ba. Bebe bai

tava gulma da bakinsa ba. Marar hannu ba ya sata. Da ni’imar Allah muke savon sa. Mu
ji tsoron Allah.

345.

Idan kana son sauqin mutuwa yawaita sadaka. Idan kana son hasken qabari

yawaita karatun Qurani. Idan kana son sauqin tsallaka Siraxi yawaita Zikiri. Idan kana
son maganin qishirwa a gobe qiyama yawaita azumi.

346.

Sau da yawa damuwarka za ta sa wasu dariya. Yi qoqari kada dariyarka ta zama

damuwa ga kowa.

347.

Ka yi kuskure ba shi ne matsala ba. Ka yarda ka yi kuskure shi ke da

muhimmanci. Abin da ya fi shi muhimmanci shi ne, ka koyi darasi daga kuskurenka.

17

348.

Wanda ya fi mutane hankali shi ne wanda ya fi su kawaici. Wanda ya fi kowa sani

shi ne wanda ya fi kasa kunne ya yi saurare.

349.

Duk motsin da babu lada a cikin sa zama kurum ya fi shi.

350.

Zuciya kamar tukunya ce. Abin da ka dafa a cikin ta shi kake furtawa. Duk wanda

ya buxa bakin sa za a san abin da ya dafa a cikin ransa.

351.

Wayar Salula da intanet suna kusanto maka wanda yake nesa. Amma idan ba ka

yi hankali ba sai su nesanta ka da wanda ya fi kowa kusa da kai, shi ne Allah
mahaliccinka.

352.

An tambayi wani mai hikima, me ya sa muke ganin sama fara tas? Sai ya ce, don

ba mu rayuwa a cikin ta. Ido na raina wanda yake gani kullum.

353.

Abu biyu ne suke sa ka ci riba a rayuwarka: Sanin girman kai da barin girmankai.

354.

Mutane da yawa da ka san abin da suke faxi a bayan idonka, da ka yanke hulxa da

su. Wani rashin sani ma yana da amfani.

18

355.

Duk abin da ka yi masoyanka ne kawai kake burgewa. Masu hassada sai dai su yi

murmushi don su vatar da hankalinka. Amma fa hasada ga mai rabo taki ce.

356.

Ba duk abin da kake so ne kake samu ba. Ba duk abin da ya same ka ne kake fata

ba. Qaddara ta Riga Fata.

357.

Yin fushi idan ba ka da gaskiya taurin kai ne. Yin fushi idan kana da gaskiya

rashin sanin girman-kai ne. Haquri da iyali qauna ce. Haquri da maqwauta dattaku ne.
Haquri da jama'a mutunci ne. Haquri da bin dokokin Allah shi ne imani.

358.

Daina tunanin baya, ka riqa tunanin gaba. Sanya murmushi ya zama alamarka. Ba

ko wane abu ne kyakkyawa yake alheri ba. Amma duk alheri kyakkyawa ne.

359.

Masu hikima sun ce: Allah ya raba ‘yan yatsunmu don mu kama hannayen

junanmu mu cike su.

360.

Idan ka sha ruwan rijiya kada ka jefa dutse a cikin ta. Idan wani ya tava yi maka

alheri kada ka yi ma sa butulci.

361.

Tsuntsu a tukunyar gidanka ya fi rago a gidan wani. Mugun gatarinka ya fi sari ka

ba ni.

19

362.

Abu biyu kada ka faxe su: Cutar da mutane suka yi maka, da alherin da kake yi

masu.

363.

Idan wani ya yi kuri da iya magana ka yi masa kuri da iya kawaici.

364.

Babu mugun abu kamar bashi. Yakan tozarta mutum da Rana. Da dare kuma ya

hana ma sa bacci. Allah ka tsare mu da sharrin bashi.

365.

Abokan zama biyu ne: Wanda za ka qaru da shi, da wanda zai qaru da kai. Na

ukunsu banza ne. Ka guje shi.

366.

Abu biyu ba su dorewa: Qarfi da Quruciya. Abu biyu ba su vacewa: Alheri da

Zumunta .

367.

Gara qarewar lokaci da vata lokaci. Idan lokacinka ya qare za ka mutu. Mutuwa

tana yanke ka ne daga duniya da abin da ke cikin ta. Vata lokaci kuwa yana yanke ne
daga Allah, da jin daxin bautar sa.

368.

Duk abu mai daraja yana da mayafi. Alqur’ani yana da makari. Alqalami yana da

marufi. Takobi yana da kube. Alawa tana cikin takarda. Lemu da Ayaba, Abarba da
Gwadda. Kai, duk abin qwarai ana yi masa sutura. Lulluvi adon matan kirki.

20

369.

Idan kana son duniya ka yi karatu. Idan kana son lahira ka yi karatu. Idan kana

son duniya da lahira ka yi karatu, sannan ka yi aiki da karatu.

370.

Alqur’ani shi ne daminar zukata. Idan ka ga ana karanta Alqur’ani ba ka jin wani

tasiri a zuciyarka to ka yi kabbara huxu ga zuciyarka. Ta riga ta mutu.

371.

Idan kana son ka ji daxi nan take ka rama abin da aka yi maka. Idan kana son ka

daxe kana jin daxi ka yafe abin da aka yi maka.

372.

Komai gaskiyar namiji akwai gaskiyar da ba zai iya faxa ma macce ba a lokacin

da yake neman ta da aure. Ita ce, niyyarsa ta qarin aure a nan gaba.

373.

Shiru ya fi maganar banza. Da zama tare da mugu gara zama kai kaxai. Fitar da ba

ta da lada zaman gida ya fi ta.

374.

Kada ka yawaita faxin abin da Allah ya ba ka. Bakin mahassada ya fi takobi kaifi.

375.

Sadaka maganin matsala ce. Addu'a maganin wahala ce. Azumi maganin cuta ne

kuma garkuwa ne daga shiga wuta.

376.

Dariya babban magani ce. Amma idan kana yin ta babu dalili to kana buqatar

magani.
21

377.

A kowace mota

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment