Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soron ko gaban ta bata gani sosai ta nufi gidan mahaifin ta a kofar gida ta ganta gaishe dashi tayi


Cikin kulawa ya amsa yana tambayar ta lafiya


Bakin mayafinta ta sa ta share hawaye muryar ta na rawa ta bashi labari


Shiru yayi yana tunani ya saki ajiyar zuciya yace


''insha Allah zan kawo karshen matsalar nan kije zan toro miki mudadssir ko jinin sa zeyi,


Godiya taimai ta tashi dan ko gidan ba zata iya shiga ba isa asibitin tayi ta shiga ɗakin su nurse din ce ta dawo tace


"An samo likitan da zaitai mata ta kusan zuwa tunda ta safe ta tafi baku samo ba,


Inna da ƙƴer ta buɗe baki tace


"Yanzu zai zo,

To tace mata ta juya ta fita da sauri a wata matashiya ta shigo ta miƙa wa inna wayar tace


"Gashi ankira,


Hannunta na rawa ta amsa sai dai me ta katsai bata lura ba ta kara tana hell hello jin shiru ta sauke wayar nasiba tace


"Ta katsai bara in ƙara kira,


Tashi tayi tace


"Nasiba bara inyi salla magariba ankira,


To tace mata domin ita bata yi fita tayi ta ɗauro alwala ta da sallah ƙara kira yayi da sauri nasiba ta ɗaga ta fashe da kuka tace


"Yaya katafi kabar inna da ilham ba lafiya tana nan rai a hannun Allah ga ciwon inna yaya me inna tayi maka ta can can ci rashin kulawa ƙarfin ta ya ƙare ko aikaton da take yi take samawa kanta abincin ci ta daina tallan da ilham keyi ba lafiya ta daina ba makaranta karatu ya tsaya yaya,


Shiru yayi yana sauraren ta ji yayi kansa na juya mai anya kuwa ya kyauta ga irin halatcin da inna tayi mai anya kuwa lafiyar sa qalau ina kuɗin da yabawa fateesat ta bawa inna anya kuwa ma taje har ta bata ransa a mutuƙar ɓace yace


"Fateesat ta baku kuɗi ?,


Kuka nasiba ta saki domin ta tuno cin mutuncin da tayi musu

Tsawa ya daka mata domin shi baya ɗaukar nonsense yace



"Magana nace kimin ba kuka ba ,


Sanin halinsa tace


"A'a munje sai zagin mu ma da tayi,


Tsai kiran yayi ransa ya ɓaci wato da takira shi sun zo basu da lafiya har ya turo mata dubu dari biyu ta basu bata basu ba me fateesat take son zama


Ita kuwa kallon wayar ta shiga yi kira tayi amma ba a ɗauka ba me yake nufi inna ce ta zo tace


"Me yace miki ina lazumi naji kina magana?,


Hawayen da tun ɗazu suke maƙale suka sami nasarar zubowa tace


"Inna ya tsai ba abin da yace,


Shiru inna tayi budurwar da ta saba su waya ce tazo ta amshi a barta


Ganin tunanin zai zautar da ita ta sami gu ta zauna akan takalman ta tana karatun kur'ani da yake mahaddaciya ce ko zata sami sauƙi a zuciyar ta


*********✍️💅******


12&15
Last Of Free Page's 🙌
✨💖
KIN CUCENI
💖✨


BY
OUM YASMEEN
AND
NAINARH KD


_____

Wannan littafin na kuɗi ne zaku iya biya ta wannan account ɗin har kati muna amsa MTN


8141785374

Zaku iya turo sheda ta nan

07067953066
Ko
09061890481

_____
Anan Asibitin suka kwana ita da Naseeba da sassafiya kuma Naseebar ta koma gida domin taho musu da abin karin kumallo yayin da Inna Salamatu ta tsaya tana ci gaba da kula da Ɗiyar tana, ko zuwa sha ɗaya na safe Naseeba ta dawo tare da abin da zasuyi karin kumallon sai dai daga gani ranta a ɓace yake.

"Wani abu ne ya faru acan Gidan naga kamar bakya cikin walwala?."

Inna Salamatu ta tambaya cikin kulawa....

Sai da Naseeba ta ja qwafa cike da takaici kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce.


"Babu komai Inna Salamatu kawai mamaki nakeyi wannan zamanin da mutanen cikinsa ace son Kai yayi yawa uwa ɗaya uba ɗaya ma bai ji tausayin ƙanwarsa ba ina ga mutanen gari kuma wannan abu yana bani mamaki da tsoro."


Inna Salamatu tayi Murmushi mai ciwo da jin abin da Naseeba ta faɗa ko bata ma ta bayani ba ma tasan kwanan zancen. Buɗe baki tayi da niyyar magana sai dai shigowar da wata Nurse tayi da sauri ne ya sa ta dakata gaba ɗaya suka mayar da kallon su gareta.

"Yallaɓai zaka iya shigowa nan ne ɗakin."


Nurse ta faɗa cike da girmamawa tana kallon ƙofar Room ɗin yayin da Inna Salamatu da Naseeba da suka mimmiƙe tsaye suka zuba ido domin ganin mai shigowar.
Cikin nutsuwarsa yake taku na burgewa ya ƙari sa shigowa Room ɗin gaba ɗaya ƙamshin sa ya cika ko'ina. Dogo ne kuma fari tas tas mai cikar kamala haiba ga kwarjini sanye cikin wata arniyar Korean suit maroon color ƙafafuwan sa sanye cikin wasu Oxford Shoes coffee Brown color hannunsa agogo ne na Rolex expensive kansa babu hula gashin kansa baƙi siɗiq wanda da gani ba ƙaramin kuɗi ake kashe masa ba a washe sai walwali yake gunin ban sha'awa gaba ɗayansa dai ya haɗu haɗuwa ba ƙarama ba. Sallama ɗauke a bakinsa ya ƙari sa shiga ciki yayin da Nurse ɗin tayi waje abin ta. Cikin Naseeba da Inna Salamatu har shi kansa uban gayyan rasa mai iya furta komai aka yi. Sai da kyar Naseeba ta samo kalamai ta haɗa a Bakinta ta ce. "Wa'alaika Salam kamar wannan dai kamar Yah Aryaan?..."


Daga yarda tayi maganar zaka fahimci zallar mamaki al'ajabi a tare da ita. Zura hannunsa yayi cikin pocket trouser nasa ba tare da yace komai ba ya yi ma ta nodding kai alamar haka ne. Inna Salamatu kuwa rasa mene ne abin da ya kamata ta yi a wannan taƙin tayi shin farin ciki ko aka sin hakan, a hankali dai idanunta suka fara lumshewa alamar zata suma yayin da tayi baya zata yi ƙasa. Cikin wani irin zafin nama duk da ɗan Interval dake tsakaninsu Aryaan ya isa gareta tare da tallafota kam yana faman kiran sunanta. Buɗe idanun nata tayi ta zuba masa yayin da Bakinta yake motsi kaɗan alamar magana kafin ta iya cewa. "Ɗa na kai ne kuwa kai ne a gabana Ɗa na Aryaan ashe da rabon zamu sake ganin juna ashe da rabon zamu sake haɗuwa da kai bayan shafe waɗan nan shekaru." Wannan shi ne first time da ta kira sunansa tun bayan girmansa hakan ya sa cikin sauri tare da nadama bayan ya taimaka ma ta ta zauna saman wata Plastic Chair na wurin ya tsuguna da duka gwiwowin sa a ƙasa gabanta tare da haɗe hannunsa ya fara magana kamar dai haka.

"Ni ne Inna ta ban san da wani ido ba, ban san da wasu kalamai zanyi amfani wurin neman afuwarki ba Tabbas nasan nayi butulci a gareki sai dai bayin kaina ba ne kamar a mafarki nake ganin komai Dan Allah Inna ta kiyi haƙuri ki yafemin da duka abubuwan da suka faru a baya..."

Gefe tayi da kanta tana sha re kwalla na tausayin kanta da shi kansa ta ce. "Aryaan ai bakayimin komai ba rayuwace sai dai Tabbas naji zafi da kayi aure ba tare dana sani ba kuma ka rasa wacca zaka aura sai Fateesat ko ka manta mene ne abin da yake Tsakanina da mahaifiyarta ce uhum Aryaan?."

Ta ƙarishe maganar tana kallon sa. Sunkuyar da kansa ya yi ya ce. "Ni dai ina mai bada haƙuri."
"Karka damu in sha Allah komai ya wuce."
"Na gode sosai Inna ta Allah yaji kan Iyaye gaskiya ke ta dabance."
Duk abin da yake gudana tsakaninsu Naseeba tana daga gefe bata saka musu baki ba. "Ilham ce ta zama haka kodai ba ita ce Ilham dana sani ba?." Ya tambaya mamaki ƙarara yana nuni da saman gadon da Ilham ɗin take kwance rai a hannun Allah da alama Bacci ma take yi, mamaki Biyu ne a tare da shi na farko dai ta girma ba kamar yadda ya barta ba ta fara zama budurwa na biyu kuma yadda ya lura ba ƙaramin ciwo take fama da ba.

Ko kafin ta basa amsa ya nufa hanyar fita yana faɗin. "Bari nazo Inna wurin Doctor zanje muyi magana akan rashin lafiyar nata." Da kallo ta bisa har ya fita. Da sauri Naseeba ta ƙari so tare da kama hannunta tana Murmushi ita ma Inna Salamatu ɗin Murmushi Kawai take yi Yaron ta ya dawo gare ta.


Ƙoƙari sosai Aryaan ya yi a ɗan wannan taƙin ya biya kuɗin komai da za'a buƙata nan da nan aka shirya komai aka fara kici kicin shiga theater Room da ilham domin Aryaan ya yi kokari an samo komai har maƙudan kuɗaɗe ya biya a taƙin aka samo jinin da ake buƙata kuma an tabbatar da ingancin jinin sannan aka shiga da ita ɗakin aiki sai fatan fitowa lafiya. Kuɗaɗe maƙudai ya bawa Inna Salamatu da duk take cikin fargaba da fatan waraka ga ɗiyar nata sannan ya yi ma ta sallama da faɗin dama saukarsa a ƙasar ke nan ya yo hospital ɗin direct yanzu tun da komai ya saisaita zai wuce gida ya shirya sannan suka taho da Matarsa. Badan Inna Salamatu taso ba ta bari ya tafi domin fargaba take yi sosai na abin da zai biyo baya..... Shi kuwa ta ɓangaren Malam Adamu Mahaifin Ilham a Ranar sai da yace ya sama mutumin da Maganar Aurar masa da 'yar sa Ilham kuma a sadaka cikin washe baki kuwa Mutumin mai shekaru 70 a duniya ya amince suka gama magana suka a je akan gobe za'a ɗaura Auren a masallacin juma'a bayan an idar da sallar juma'a daga wurin mutumin gida ya koma ya fara sanarda da jama'a ɗaurin Auren da zai yi gobe wasu na tayasa murna tare da mamaki wacece kuma zai aurar sanin da sukayi da bashi da wata Budurwar 'ya a halin yanzu duk an musu Aure da ya koma gida ya faɗa ma su Hansatu da Maryamu sun yi farin ciki sosai burin su zai cika Salamatu da ɗiyarta zasu wulakanta nan dai suka ƙara zigasa. Washe gari da ya kasance juma'a kuma ranar ɗaurin Auren Direct Malam Adamu gidansu Salamatu ya wuce ya sama Malam Mai Allo kamar kullum yana zaune ƙofar gidan an shimfiɗa tabarmu dai ai kuwa ko gaisawa bai bari sun yi ba ya faɗa masa abin da yake tafe da shi wai na Aurar da Ilham da zai yi a yau. a cewarsa ma saboda ya kasance uban matarsa Salamatu ne ma shi ya sa ya faɗa masa da sai dai suji a gari bai bari Malam Mai Allo da Mamaki ya cika sa ya ce komai ha ya karkaɗe Babbar riga ya yi gaba abin sa. Cikin wannan hali na tashin hankali da ruɗu tare da Mamaki da ɗunbin al'ajabi Aryaan ya ƙari so ya sama Malam Mai Allo domin bayan barinsa daga asibiti Direct gidansa dake Nasarawa G.r.a ya wuce ya yi wanka ya shirya kuma matar gidan bata nan sannan bai san ina ne take ba har ya shirya ya yi waya company aka kawo masa mota ya kuma fitowa bata ma san ya dawo ba shi kuwa Direct Gidan kakansa Malam Mai Allo yayo shi ne ya sama sa a wannan hali koda ya tambaye sa abin da yake faruwa nan dai Malam Mai Allo ya faɗa masa komai. Aryaan sam bai yi mamaki ba domin kuwa yasan Wanene uban Ilham wato Malam Adamu mara mutunci da yake a lokacin ana gab da shiga sallar juma'a dan haka shiryawa Kawai Malam Mai Allo ya yi Aryan ya ɗauke sa a mota suka wuce can Masallacin juma'a ɗin da za'a ɗaura Auren. Bayan an idar da sallar juma'a duk an tsayar da su da cewar za'a ɗaura Aure. Malam Adamu baki a washe a ganin sa zai yarda kwallon margwaro ne ya huta da ƙuda zai rabu da mayyar gidansa duka an nutsu ana jiran Ango sai dai mene ne zai faru shiru Shiru babu ango babu Labarin sa sai can ɗan aike yazo musu wai an ce a faɗa ma uban amarya an fasa Auren 'yar sa saboda mayya ce ba za su iya da Dangin Mayu ba. Turƙashi.......!!! Wannan abu da ya faru ba ƙaramin mamaki ya bawa Kowa ba shi kuwa Malam Adamu sai zarar ido yake yana muzurai bai taɓa ji ya tozartu ba kalan yau kuma bai ɗaura laifin akan kowa ba sai Salamatu da ɗiyarta. Ana shirin watse wa ne sukaji sanarwar za'a ɗaura auren da wani kowa ya tsaya da Mamakin wani mai ƙarar kwanan ne zai aura Yarinyar da ake kira da mayya. Shi kuwa Aryaan Ransa a matuƙar ɓace yake da wannan lamarin dama koda Angon bai fasa ba bazai taɓa bari a gabansa a tozarta Ilham jinin Innarsa Salamatu ba saboda haka koda Angon ya sanar ya fasa abin ya yi masa daɗi nan take ya fitar da kuɗaɗe da bai san adadin su ba, ya yi ma Malam Mai Allo magana akan a ɗaura Auren da shi ai kuwa cike da farin ciki Malam Mai Allo ya amince ya sa ka aka yi sanarwar. Nan dai Malam Adamu yanaji yana gani aka ɗaura Auren A'ishatu Adamu da Aryaan Abdulyasar, Malam Mai Allo shi ne ya yi ma Aryaan wakilci yayin da Malam Liman aminin malam Mai allo ya yi ma Ilham domin kuwa Malam Adamu ƙin saka baki ya yi a zancen an ɗaura Aure tare da shaidawar dubban jama'a Ilham ta zama matar Aryaan.....


______
*_Turƙashi...!!! Akwai ƙura fa. Wai shin Mene ne kuke tunanin zai faru ne. Aryaan dai ya aura Ilham Ɗiyar Innarsa Salamatu Yarinyar da take cikin halin rai ko Rayuwa sannan kuna tunanin Malam Adamu da matansa zasu amince su bar Ilham ta zauna a tare da Aryaan koda ta sama lafiya. Wai shin Ilham zata warke kuwa. Ina labarin Fateesat wani irin mataki zata ɗauka idan ta sama labarin auren da Mijinta Aryaan ya yi. Wai shin ina labarin Dangin Mahaifin Aryaan ne._*
*To dai ba zaku sama amsoshin waɗan nan tambayoyi ba sai kun kasance cikin wannan tafiyar a labarin _KIN CUCENI_ Wacece zayi cutar????.....*
*In sha Allah an kammala free page's zamu ci da posting on Paid Grp ga waɗan da suka yi payment don't Miss It Dearest Sister's 🙌💖*



____
Wannan littafin na kuɗi ne zaku iya biya ta wannan account ɗin har kati muna amsa MTN


8141785374

Zaku iya turo sheda ta nan

07067953066
Ko
09061890481

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment