Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita yake musamman ma da ya sama mata 'yan Duniya Hansatu Tantiriyar mace da banda bin bokaye da malaman tsubbu domin mallakar miji babu abin da ta iya. Haka ma Maryamu sai dai ita ba boka balle Malam sai shegen kissa da kisisina Wurin ta shi ya sa gaba ɗaya suka susuta Adamu ko kallon Salamatu ma ba ya yi dama kuma can halinsa ne wulaƙanta mata suma su Hansatu ɗin ba tsira suka yi ba domin duk Ranar da abin nasa ya motso ko su ba ya bari..


Tohm haka dai Rayuwar ta ci gaba da tafiya Salamatu tana kula da ɗan ta mafi soyuwa a gare ta sama da komai na Duniyar ta wato Aryaan tana son sa sosai domin ita ce uwansa kuma ubansa bai san kowa da komai ba a Duniyar sa sai ita ɗaya....



Aryaan ya taso yaro ne shi mai matuƙar kaifin basira sosai wannan dalili ya sa ya kasance zagwagwurin jajirtaccen ɗalibi mafi hazaƙa cikin Makarantar su sam Aryaan ba shi da wani sake wa sosai da mutane domin ba mutum ne mai son yawan surutu ko hayaniya ba yana da sanyin hali da kyakyawar zuciya kyakyawa ne shi sosai domin komai sak mahaifinsa ya yo sai dogon hancin ne Kawai irin na Mahaifiyar sa. So da yawa idan ya tambaya Salamatu akan ainihin iyayensa sakamakon yawan gori da Adamu da matansa Hansatu da Maryamu suke ma sa akan shi ɗin agola ne cikin gidan ba kowa ba. Idan ya yi ma ta tambayar sai dai ta sha re hawaye Masu zafi ta faɗa masa kyawawan halaye irin na mahaifiyarsa Maragayya Aisha. Zuwa lokacin ya san cewa Mahaifiyarsa ta rasu sai dai bai san komai Dangane da Mahaifin sa ba duk da sanin da ya yi yana raye.

A lokacin ne kuma wani babban abu ya kasance musu na alhini sakamakon hatsarin motar da Abdulyasar ya samu shi da matar da aka Aura masa juwud suka rasu sai dai 'yar su ɗaya tilo ta rayu mahaifiyar Abdulyasar ta ci gaba da kula da ita.
Sosai Salamatu tayi kuka lokacin da ta sama labarin rasuwar Abdulyasar sai da ta ba uku lada ta bisa da addu'a shikenan kuma Aryaan ya zama cikakken Maraya. Sai dai ta ƙudirta a ranta ko wuya ko daɗi zata zame masa majingini na Rayuwa indai tana Raye bazai taɓa kukan rashin iyaye ba in sha Allah kuwa haka ta ƙudirta.


Har zuwa lokacin kuma haihuwa Shiru daga Salamatu tun abin yana damunta tana kuka da damuwa har ta haƙura ta fawwalawa Allah komai domin yana sane da ita tabbas Allah maji roƙon bayin sa ne......✍️🌹


*KIN CUCE NI*



Oum yasmeen


And

Nainarh KD


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



EP 9



_Previous_


Har zuwa lokacin kuma haihuwa Shiru daga Salamatu tun abin yana damunta tana kuka da damuwa har ta haƙura ta fawwalawa Allah komai domin yana sane da ita tabbas Allah maji roƙon bayin sa ne......✍️🌹



_Continue_





Yayin da adamu ya kara tsanan ta mata yanzu ya zare hannunsa akanta ficikarsa baya bata yau kam tana zaune tun safe take wankau ɗin da aka kawo mata wasu ma tayi a hanata kuɗin sallamar Aryan taji cikin sakin fuska farin ciki ya mamaye ta farin cikin ta ya dawo tace


"Ɗan albarka andawo,


Be fiye fara'a ba da sai murmushi da yasakar mata yace


"Eh inna,


Taƙarda ya miƙo mata goge hannun ta tayi sannan ta amsa yace


"Taro ne na makaranta ance kowa abbansa yazo,


Wani tashin hankali ta shiga gumi ya dinga yanko mata ƙoƙarin saita kanta tayi tace



"Aryan Allah ya kai mu ai mace tana iya wakiltar namiji ni zanje,

Be nuna da muwarshi ba sanin halinsa na zurfin ciki inna tace


"Aryan,


Ɗago kyawawan idanuwansa yayi ya dube ta yace



"Na'am,




Kuɗi ta ciro agefen zaninta ta miƙo mai tace


"Inka cire kayan ka kasiyo karin kwaki ka sha kaji yau ban da kuɗin yin girki sannan ruwan da muke amfani da shi ya ƙare,


Amsa yayi yace


"TO,


Malam Adamu ne ya shigo hannunsa riƙe da yaro amma aryan ya girme sa yana kuka wuf aryan yayi saurin shiga ɗaki baya kaunar ganin wannan mijin inna azalimine jama'a yana cire kaya yaji wani ashar da ya lailayo ya ɗannawa inna da sauri ya toshe kunne sa malam adamu yace



"Wato dan rashin mutum ci shine kika yiwa musa faɗa to ke dan kutu mar uban ki kin haifa ne ko kinsan ciwon ƴa'ƴa da har zaki wa wani faɗa ke gaki yar gidan malam ko uwar iya?,


Ajiye wankin da take ta ɗurƙusa ƙasa muryar ta na rawa tace



"Malam kai haƙuri insha Allah bazan ƙara ba malam ganin su nayi shi da iliyasu almajinrin da ke yiwa hansatu tallah suna wasa da gaban su shine na ce mai babu kyau,


Aguje hansatu ta fito daga banɗaki tace



"To annamimiya ina gidan ban fita ba wato Ni za aiwa iya shege malam sai ta sa kuka ta shiga ɗaki ganin ran yar gold ya ɓaci ya tsinko igiyar da tayi shanya ya shiga labta mata yana ta sababi aguje aryan ya fito ya rungume inna yana kare mata


Aikuwa haka ya haɗa su ya zane zuciyar inna ta ƙeƙashe dan haka ba kukan da tayi sai na zuciya gajiya yayi yana hura hanci ya bar gidan


(Hattara iyaye yau duk wanda zai wa ya'yan ku faɗa to wallahi me ƙaunar ko ne musamman wannan yazu zamani yar da ake lalata ya'yan mu ba mazan ba ba matanba musamman masu ɗauko almajire ku ɗinga kula da irin wasannin da sukewa ya'yan ku yana gama ku bashi abin da zaku bashi ya tafi ƙar ku yarda wata alaƙa ta shiga tsakanin ku da ya'yan ku ya kama garuruwan da suke turo almajerai suji tsoron Allah baka san a ina ɗan ka ya ke kwana ba bakasan wake wa ya'yan ku tarbiyya ba wallahi ina jin ciwo in fito inga almajirai yara ƙanana a kawo su uwa duniya da sunan karatu abin mamakin shine har suna da kwanciyar hankali yaya su suna watan gaririya a gari

Wallahi wani ma sai yayi sati malamin nasa be son baya nan ba me yasa Ubangiji yake jarabamu iri iri ai daman ya fadi in har aka kauracewa faɗar sa to zai jarrabemu su ya'ya amana ce a gare mu akwai ranar da Allah zai tambaye mu kiwon da ya bamu )

Haka rayuwa ta ci gaba da kasan a gidan dangin uban Aryan ba wanda yake zuwa ganin sa duk da cewa kamar su ɗaya da mahaifinsa ko hakan ya ja hankalinsu su soshi amma ba wannan shekarar Aryan goma sha huɗu yana gab da fita junior school Allah ya bawa salamatu ciki tun daga fitowar cikin nan abubuwa suka cakuɗe mata malam adamu motar sa ta ɗinga lalacewa nan fa ya dorawa cikin ta shi ya jamai domin shi har ya manta yau she rabun da wata ma'amallah ta aure ta haɗa su nan fa yace aljanune sukai mata ciki billahir lazi sai dai ta nemi uban ta acan duniyar aljanu haka ta ɗinga jurewa saboda matsaloli sun mata yawa gana matar ubanta ga nata ta daina zuwa gidan jikin ta yayi nauyi ana haka Aryan kungiyar tallafawa marayu da mara ƙarfi ta America ta ɗauki nauyin su a lokacin ya shiga senior yana aji biyu ganin kwazon sa yasa suka zaɓe sa duk da secondary ɗinsa a college of Qur'an yayi makarantar kusa da S.A.S ranar da yaci jarabawa ranar Allah ya sauki salamatu


Ba tare da dugowar na ƙuda ba ranar kuma motar adamu ta kone ƙurmus shima sai zaro shi akai ga kuɗin mutane da kayan su yana dawowa aka shimfida mai tabarma ya zauna su maryamu da hansatu sai fifita akai mai ni kuwa ina ban ɗaki ina wanka fitowa nayi naga kafar shi duk akone sannu nayi mai da ƙƴar ya amsa shiga ɗaki nayi na ɗauko yarinyar da na haifa nace malam yau Allah ya sauke ni sa hannu yayi ya buɗe ta ihu ya saki ganin idanuwanta da kuma irin kyawun ta yace



"Haba ashe yar aljanu aka haifar min shi yasa na gamu da wannan ifti'ila'in to ke da ita kutattara ku barmin gidan nan,


Cikin kiss maryamu tace



"Haba malam ai yanzu ka koreta sai su ƙona mu muna kwai ka ƙƴaleta ta amshi gashi,


Dariya yayi yace


"Kuma hakane fa ,


Girgiza kai salamtu tayi ta tashi Aryan da yake me jikin girma ne ya zama saurayi ya shigo bakin sa da sallama fuskarsa ta ƙasa ɓoye murnar da yake ciki tace


"Inna na ci jarabawa ta nan da sati me zuwa zamu tafi kasar waje sun ɗauki nauyin karatuna........✍️

إِنَّ اللّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ

Tabbas Ubangiji yayi gaskiya me haƙuri yana tare da Allah

Muslims will face all kinds of adversity, we will face all kinds of trials and bear all kinds of deprivation. This is why Allah in Surah Baqarah ayat 153 Allah says, surely he will be with the patient



Allah is with those that are patient”. It emphasizes the Islamic concept of sabr meaning endurance, perseverance and persistence. For a Muslim, Sabr represents one of the two parts of faith


💔💔💔
*KIN CUCENI 10*
💔💔💔

BY
OUM YASMEEN
&
Nainarh KD



https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



_____
****

Duk da cewa sosai Salamatu tayi farin ciki da samun tallafawar gwamnati da Aryaan ya yi zai tafi zuwa ƙasar waje domin karatu amma bataso ta rabu da shi ko da kuwa na sakan guda ne sai dai babu yadda ta iya haka Allah ya nufa cikin wannan tazaran ne aka fara shirya shirye na tafiyar Aryaan zuwa ƙasar waje karatu ta hanyar tallafawar gwamnati.

Yayin da gefe guda kuwa Salamatu take kula da Jaririyar ta Yarinya kyakyawar gaske fara tas ga hanci dogo ma daidaici komai nata daidai sai kwayar idanunta da suka kasance shuɗaye masu kyalli da kyau sannan suka janyo ma ta gagarumar tsana a wurin uban ta Adamu Jaririyar taci suna Aisha yayin da ake kiranta da Ilham.





Ilham ta taso Yarinya ce Shiru Shiru bata fiye surutu ba Kuma tana da saurin kuka sosai sanadiyar tun tasowar ta bata da wani aiki sai kuka sakamakon yawan cizguna ma ta da Mutanen gidansu da unguwa suke yi suna kiranta da Aljana mai idanun mayu haka ma mahaifinta abin bai sauya zani ba daga garesa domin kuwa ba ƙaramar wahala da baƙar Azaba Ilham take kwasa a wurinsa ba, a cewar sa ita ɗin mai ƙashin tsiya ce kuma mai farar ƙafa domin tun da aka haifeta ya fara ganin Bala'i kala kala cikin Rayuwarsa da fari motarsa ce ta ƙone ƙurmus daga nan kuma sana'a ma gagarar sa take yi sai da kyar ake samun na cefane shi ne ya ɗauki karar tsana ya ɗaura ma Baiwar Allah Ilham a cewarsa ita ba jininsa ba ce saboda ita ɗin mai farar ƙafa ce ga kuma waɗan nan shuɗayen idanun nata na mayu. Tsaban tsanar da ya yi ma Ilham ya sa ko abincin gidan sa baya taɓa yarda a bata kuma ya ce duk wacce ta bata to a bakin Aurenta....



Waɗan nan duk suna daga cikin dalilan da suka saka Ilham ta taso a Rayuwarta bata da kowa sai mahaifiyarta dama tuntuni Aryaan yana ƙasar waje karatu bai dawo ba tsawon shekaru sai dai idan ya kira waya ta hannun wani sunusi ɗan unguwan ne suke samu su gaisa da Inna Salamatu...


Hatta a makaranta bata sauya zani ba babu sunan da aka sakama Ilham kuma aka kiransa da shi fa ce Aljana mai idon Mayu wannan dalilin ya sa ko ƙawa Ilham bata da ita. Sai Naseeba da ta kasance ɗiyar Ɗan Juma ne Babban Yayansu Inna Salamatu ita kaɗai ce takeson Ilham har zuciyarta kuma take tausaya ma ta duk da cewa mahaifinta yana da rufin Asiri daidai gwargwado amma domin kuwa da daɗewa ma sun tashi daga unguwar talakawa sun koma unguwar masu da shi. Amma ko kaɗan baya tausayawa 'yan uwansa musamman ma Salamatu da take cikin halin buƙatar tallafi amma saboda rashin imani ko kallo ma bata ishesa ba, kuma ya hana matarsa ko 'ya'yansa tun karar inda Salamatu take balle su tallafa ma ta tsaban baƙar zuciya da rashin imani amma duk da hakan a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba Naseeba take yawan kaiwa Gwaggon nata ziyara kuma tana tallafa ma ta da duk abin da bai fi ƙarfin ta ba..


****
_*Bayan wasu Shekara...*_



A yammacin wata Ranar Juma'a ce kuma Ranar da ta kasance ɗaya daga cikin ranakun da Salamatu ba zata taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta. Ita ce Ranar da Ɗan Lelen ta Aryaan ya yi ma ta dawowar bazata domin bai sanar da kowa Dawowar tasa ba sai kawai ganinsa suka yi. A lokacin kamar kullum ita da ɗiyar ta Ilham da ta fara girma dan kuwa takai shekaru goma sha uku a Duniya suna daga can gefen tsakar gida Inna Salamatu tana fama da Sukola na aikatau da take yi yayin da Ilham take tayata duk da cewa ba wani iyawa tayi ba Kawai sai sallamar wata sassanyar Muryarsa mai cike da daɗin sauraro sukaji ya yi lokacin da ya shigo gidan Aikuwa gaba ɗayan su har da su Hansatu da Maryamu da suma suke nasu aikace aikace na gida da ma Adamu da yake daga kishingiɗe saman tabarma yana sauraren Radio gaba ɗaya suka juya suna kallon wani kyakkyawan matashin Saurayi dogo kuma fari mai faffaɗan ƙirji ma'aboci cikar zati da kamala sanye cikin wasu shegun Korean suit masu masifar tsada da kyau fuskarsa maƙale da wayfarer sun glasses da ganinsa kaga cikakken Bature ziryan bawai wanda ya yi haye ba domin daga ganin shigar nasa na Turawan zaka danganta shi da su....


Tsakanin ta da Allah da fari Inna Salamatu bata gane ko wane ne ba sai daga bayan ya cire Glasses dake rufe da manyan kyawawan idanunsa farare tar tar da su sannan cikin kamilalliyar Muryarsa ya ce.


"Inna.! Inna ta Inna ni ne fa Ɗan Lelen ki Aryaan....!"


Mutuwar zaune Inna Salamatu tayi baki wangame tsaban mamaki da kaɗuwa na jin kalaman sa da kuma tabbatar da cewa shi ɗin ne da gaske ba mafarki ba kamar yadda ta saba. Tsaban Farin ciki kawai sai ta saka masa kuka amma fa na farin cikin ganinsa da sauri cikin sassarfa ya saki Suitcase da yake janye da ita ya ƙari sa da sauri ya rungumo ta cike da farin ciki shima yana hawayen sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba tare da kowannen su ya iya sakin ɗan uwansa ba yayin da mutanen gidan suke binsu da kallo cike da mamaki...



Farin ciki da murna na dawowar Ɗan Lelen ta ya mantar da ita duka wata wahalar da suka sha a baya ta miƙa dukkanin godiyan ta ga Allah lokacin da Aryaan yake bata labarin da daɗewa ya kammala karatun sa kuma ya sama aiki ne a can shi ya sa ya ɗiba waɗan nan shekaru ba tare da ya dawo ba a halin uma shi ɗin Pilot ne ma'ana dai Matukin jirgi..



Sosai tayi farin ciki da hakan sai dai ta nuna masa rashin jin daɗin ta na kwashe tsawon shekarun da ya yi ba tare da ya neme su ba nan dai ya bata da hakuri da kare kansa da faɗin can ɗin ne suka riƙe sa yanzu haka ma wata ɗaya kacal zai yi ya koma kuma ya tabbatar ma ta da zuwan sa gaba da zai yi in sha Allah tare zasu koma gaba ɗaya gefe guda kuwa mamakin girman Ilham yake yi Yarinyar da ya tafi ya barta ko wata ɗaya batayi ba a Duniya....


****


Kwanaki kaɗan da Dawowar Aryaan Inna Salamatu ta tilasta masa akan ya shirya ya zaga danginta ya sanar da su dawowarsa a so samunta ma har Dangin Mahaifin sa ya je amma tasan yadda Aryaan ya tsani dangin mahaifinsa ko giyar wake ya sha ba zai je ba. Sakawa ya tafi danginta domin kai musu ziyara shi ne wani babban kuskure da Salamatu ta tafka ba tare da ta san hakan ba domin kuwa Fateesat Jikar Gwaggo Marka matar Malam Mai Allo ta Biyu ita da Mahaifiyarta tun daga kallon farko da kuma samun labarin komai da suka yi akan Aryaan shikenan suka raya Fateesat ta sama miji ita kuma Mahaifiyar ta ta sama suruki domin a ganinsu banza ta faɗi Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba suka fara Aiwatar da mummunar ƙudurinsa akan Bawan Allah Aryaan da bai san suna yi ba. Watannin sa Uku da su Inna Salamatu zuwa lokacin ta murmure ta fara kumari ƙibanta ya fara dawowa haka ma Ilham. A lokacin ne ya yi musu sallama zai koma sannan kuma ya bawa Inna Salamatu lambar waya da zata dinga Kiransa sannan ya siya ma ta wayar ya tafi suna cike da kewarsa haka ma ita sai dai wayar nan da ya siya ma ta a Ranar da ya tafi ta nema ta rasa cikin gidan sama ko ƙasa. Daga wannan komawar da Aryan ya yi ne komai ya sauya komai ya lalace domin kuwa shekarar sa ɗaya da komawa sai da Mahaifiyar Fateesat ta tasan yadda tayi da Asiri ta aurawa Aryan ɗiyarta Fateesat suka bisa can ƙasar da yake kuma suka rufe bakin kowa babu wanda ya isa ya yi maganar. Sosai Inna Salamatu ta shiga matsanancin tashin hankali da damuwa lokacin da ta sama wannan Labarin sanadiyar hakan har ciwo sai da ta kwanta amma bai canza komai ba na daga mummanar ƙaddara dake tunkarar Rayuwar su shekarar Fateesat ɗaya da auren Aryaan ta hanyar mallake sa da Asiri suna zaune ƙasar da yake can zauna kwatsam ta kwazzaba masa akan zata dawo Nigeria ta zauna domin kuwa ba zata iya zaman can ba dama ta addabesa amma baya iya yi ma ta Komai haka ya nema ma ta tamfatsetsan gida katafaren gaske anan Nasarawa G.R.A Kano ta dawo ta ci gaba da sheƙe ayar ta tsawon shekara ɗaya ke nan. Yayin da ya kasance tsawon shekaru uku ke nan rabon sa Inna Salamatu ta kuma saka Aryaan a ido tun Dawowar da ya yi kuma tana nan maƙale da takardar da ya bata na lambar waya bata taɓa kiransa ba. A wannan taƙin ne kuma ciwon Ilham da take fama da shi ya tsananta har ya kai su ga kwanciya a asibiti likitoci suka tabbatar da aiki za'ayi ma ta sannan kuma kuɗaɗe ne masu yawa wannnan dalilin ne yasa hankali a tashe Inna Salamatu ta tafi gidan matar Aryan Fateesat a tunaninta yana ƙasar amma Fateesat tayi ma ta rashin mutunci marar daɗin faɗe a taƙaice dai wannan shi ne labarin Rayuwar Baiwar Allah Salamatu da ɗiyarta Innocent Ilham da take kwance a halin yanzu rai a hannun Allah......


_*Present*_
_Ci gaban Labari...._


*KIN CU CE NI*



Story and writing

By


Oum yasmeen

And


Nainarh kd


___________________________________________________________________________________________________________________________


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k



*EPISODE 11*





Ajiyar zuciya me karfi ta saki kwallah na taruwa a idonta da sauri nasiba tace


"Inna lafiya ?,


Karfin halin ta aro tace


"Nasiba lafiya qalau dare yayi ki tashi ki tafi kar aimiki fada ,


Zama nasiba tayi tace


"A'a inna yaya bashi da niyar bugowa kinga mu tashi muje gida ko a cikin su musa Allah zai dube mu mu samu jini,


Shiru tayi tana nazari bata so ranta ya ɓaci amma fa tilon yar ta tana gaɓar mutuwa ko rai ya kamata tayi wani abu duban nasiba tayi tace


"Nasiba zauna ni zanje in nemo me jinin,


Hannun Ilham ta kama inda taji sanyi qalau gashi ta ƙara yin fari tace



"To inna Allah ya temaka mu samu,


Amin tace ta fita tafiya take a hankali domin jikinta yayi mata nauyi ga ciwon kafar da take fama da shi jan kafar ta take har ta isa gidan su sallama tayi ba wanda ya amsa duk kuwa suna tsakar gidan ɗurkusawa tayi tace


"Malam barka da yamma ,


Lomar shinkafa da miya ya kai bakin sa ta ji kifi zuƙu xuƙu ya haɗiye jikake yabada wani sauti kutt alamar ya abincin ya waɗa mai yace


"Yauwa uwar gantali anya salamtu kina so ki shiga aljanna ?,


Da sauri ta ɗago ta kalle sa tace


"jikin ilham ya tashi yanzu ma jini ake buƙata me 0+ jininta ya ƙone za ai mata juyan jini to shine na dawo ko za'a dace a sami me irin jinin a gidan nan,


Jin ta ambaci jini ya saki baki ya dakata da cin abincin furzar da na bakin sa yayi saboda duk daɗin abincin ji yayi yayi mai ɗaci yace



"Maryamu hansatu jaƙar uban can kunga abin da nake so ku gane tun haihuwar yarinyar nan amma kukaƙi ganewa ko da kun barni na kore su amma ai gashi anxo kan gaɓa wallahi gidan sarkin ruwa yau zani na bashi ita ya aura dan shine dai dai da su ya nake jin wata masifa jini jini wato ta rasa na wanda zata sha shi ta bullo da wannan hanya ta shaye jinin ta tab yau akwai tashin balagar tsintsaye yasin ni za akawo wa rainin hankali ta zuke jini ance jini ya ƙone ai wannan tafi ƙaska,



Hawaye ta share tace


"Wallahi malam cuta ce ilham ba aljana bace mutum ce,


Ƙwano ya ɗauka yayi jifa da shi aka ce sa'a be dira a ko ina ba sai a ƙasa ta kauce ya e

"Kan uban can zanci bura'uban mutum ce ke salamatu ki nemo mahaifin yarinyar nan aljani ya amshi yarsa wallahi tashin hankalin nan har ina wallahi dole in nemo ma fita tab wani ta shanye jini tarasa yarda zatayi ban da jinin mu da take sha hakan be mata ba sai tayi me gabaki daya tashi yayi ya ɗaga malin malin ɗin sa yace



"Hansatu daga be ni duk nabi na rame ashe shan jinin mu ake da bargon mu kai wallahi ba zata saɓu ba dole in nemo mafita satin da ya huce yar akuyar da na gada ta kasa sai mahauci nakira ya siya a she game ci a kusa kai wannan jarabar har ina gidan sarkin ruwa zani shine dai dai da su yasin ko ta nemo ubanta aljani ga yarda aka kawo yarinyar nan maryamu duk sai tabi ta fige yawa kazar matsiyata tun da aka haifi yarinyar nan dole indau mataki tun kafin ta sheƙani barzahu da sauran kwanana a gaba,


Dadi hansatu taji tace


"A'a me gida kawai ka aura mata sarkin ruwa shine dai dai amma yaushe zaka ce a nemo ubanta sai sun ƙara ƙona ka kamanta shekarun baya abin da sukai maka yanzu kuma kaga mekan uwa da wabi za suyi sarkin ruwan shine dai dai da su tunda har fito na fito yake yi da aljanu shi zai iya zama da ita


Hula yaci re yace


"Eh kuma hakane da zafi zafi ake bugar ƙarfe ya gyara babbar rigarsa wani yaro ne ya yace


"Wai malam adamu yana nan inji idi tsohun direba,


Washe baki yayi yace


"Faɗuwa ta zo dai dai da zama muje ya rakani domin bilya hillazi yau sai na kawo karshen annobar nan,

Tusa kan yaron yayi suka fita leƙawa hansatu tayi ganin yayi nisa tace


"A hayye rass chass muna da shan biki rawa take tana juya ɗuwawu yawa lotsassiyar tasa,

Tashi inna salamatu tayi bata nuna mata taji abin da ta ce ba ko ta gani

sai da ta zo soro ta saki kuka ta rufe fuskar ta da mayafin ta yawa an kwato shi daga bakin kura tunani ta shiga yi

wannan ne irin ubane yanzu yarinyar da shekarar ta goma sha shidda ita za aiwa aure da dan shekara 70 har ya'yan jikoki ya aurar tashi tayi ta bar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment