Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*Surayya Dahiru Gwaram*
*(Mrs M.I. Nashe)*
*Marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza*.


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*Rok'on addu'arku*!
*A irin wannan ranar ta 09 ga wata 09 shekarar 2000. Ubangiji ya karbi ran mahaifiyata. Dan haka ina baran addu'arku dan nema mata raham da gafarar Allah daga bakunanku masu albarka dan Allah*.

*Haka nan ina mika sak'on ta'aziya ta ga dukkan musulmai bisa babban rashin da muka yi na bijimin malaminmu kuma uba*.
*Sheikh Abubakar Giro Argugun*
*Allah ya jikan magabatanmu gabad'aya kwata.*

*JAN KUNNE*
*KADA A TA'BA MINI LABARIN NAN, KO KARANTA SHI A KOWACCE IRIN KAFA TA SADARWA BA TARE DA IZININA A RUBUCE BA*.
*IDAN KUMA AKA YI KARAMBANIN TABAWA, ZA'A FUSKANCI TUHUMA DAGA LAUYANA BAR MUSTAPHA ISA GWARAM*.


*GARGADI*.
*WANNAN LABARIN KIRKIRARREN LABARI NE*
*BA SHI DA ALAKA DA KO WANNE MAHALUKI*.
*IDAN KIN CI KARO DA RAYUWAR DA TA YI KAMANCECENIYA DA TA KI, KO WANINKI, TO ARASHI NE*.
*DOMIN MANUFAR MARUBUCI ISAR DA SAKO DA HANNUNKA MAI SANDA A CIKIN ZAMANTAKEWARMU*.
*LITTAFAN SURAYYA BASA NUFIN HABAICI KO SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA.*
*NA GODE*.

*GODIYA GA*
*SADIK ABUBAKAR*
*NA GODE MADALLAH*.

*GAISUWAR GIRMA GA IYAYENA KUMA MARUBUTA*
*HAJ SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIA*.
*HAJ HAFSAT C SODANGI*.
*HAJ MARYAM KABIR MASHI*.
*HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM*.


*YABO GA*
*K'AWATA JAMILA JANAFTY*
*IDAN DA WANDA NA GAMSU DA TULIN SOYAYYARTA GA RUBUTUNA DA CIGABANSA TO KE CE*
*DUK WATA KALMA TA YI KA'DAN TA FAYYACE GIRMAN SHA'ANINKI A WAJENA*
*INA FATAN UBANGIJI YA SHIGA AL'AMARIN KI, YA BAKI MIJI NA GARI*.

*GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA MARUBUTA*
*Sumayayyah Takori*
*Binta Umar Abbale*
*Fadilah lamido*.
*Hassana D'anlarbawa*
*Zainab MAZAWAJE*
*Lubna Sufyan*
*Nazifa Nashe*
*Ayusha Muhd*
*Nana Diso*.
*Kulsum Baffah*.
*Safiyya Um Abdul*
*Umm Asghar*.
*Aisha Dansabo*
*Aisha jos*
*Zee Kumurya*
*Da dukkan y'an kungiyarmu ta lafazi*.

*FATAN ALHERI GA IYAYEN D'AKINA*.
*HAJ HALIMA D'ALHA SHEHU*
*HAJ RABI SANI*
*HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA*
*HAJIYA HADIZA FARI*.
*HAJIYA ZAINAB ABDULWAHAB*
*ALLAH YA HA'DA Y'AY'ENKU DA MUTANAN DA ZASU MUSU KARAMCI FIYE DA YADDA KUKE MINI, INA MATU'KAR GODE MUKU*.

*TUKUICIN LABARIN SUKUTUM GA*
*AISHA MUHD LAME*
*ALLAH KA SO AISHA, KA FARANTA MATA, KA BIYA MATA BU'KATUN TA NA DUNIYA, KA BATA BABBAN RABO A LAHIRA*.
*IDAN AKWAI WANDA JINI BAI HA'DAMU BA, NA KE DAKACEN INA MA JINI YA RATSA TSAKANINMU TO AISHA LAME CE MAI KAYAN Y'AN GAYU TA ORIFLAME*
*SURAYYA DEE TA GODE, TA YABA MIKI, UBANGIJI YA TAYA NI GODE MIKI*.


*Doka mi lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*.

*1&2*.

*SHIMFI'DA*.
Sunana Asiya Sani Toro.
Amma mafi yawa da Yabi ake kira na a dalilin mahaifiyata ta yi aikin Hajj da ni a cikinta.
Mama ce kawai bata kira na da hakan sai Asiya saboda tana adawa da Yabi tunda ana nufin nima Hajiya ce.
Gidanmu babban gida ne a garin na Toro domin ko yaro k'arami ka tambayi gidan Marina zai nuna maka. A dalilin asalin kakanmu da ya zo daga Kano ya fara kafa wannan sana'ar a garin. Fiye da shekaru saba'in kenan, amma har yau ba'a juya wa sana'ar baya ba, duk da dai an zamanantar da ita, ba kuma cikin gidan ake yin ta ba saboda warinta.
Gidanmu babban gida ne k'warai da gaske.
Idan na ce babban gida ina nufin mai d'auke da ahali daban daban masu yawa.
Ko a k'ofar mahaifinmu Alh Sani (Baban Marina) da shi ne babba mata uku ne.
Hajiya Habiba ita ce uwargidan mahaifinmu, mace mai k'ifadi da kutunguila. Duk wani rikicin da yake k'ofarmu, dama cikin gidan tana da sa hannu, ta tsani ta ga ko wanne irin cigaban d'an wata sai nata yaran kawai.
Sannan komai cikin dabara da girma ta ke yinsa, ba kowa ne ya fahimci irin makircin da take k'ullawa ba. Sai mu da mu ke rayuwa da ita kullu yaumin.
Ta kanka ne komai, ta yadda komai ta shimfi'da akan haka za'a tafi, sai dai ranar da ta samu bacin rana Baba ya bijire mata.
Ya'yanta biyar.
Yaya Musa, Yaya Hadiza, Yaya Salamatu, Yaya Indo sai autarta da ta haifa bayan ta shafe shekaru masu yawa Nazira, wacce ita ce sa'a ta ta girme ni da wata uku.
Sai Mahaifiyata Hajiya Àsma'u wacce muke kira da Goggo. Ba dan tana mahaifiyata ba, amma mace ce mai sanyin hali da matsanancin ha'kuri. Idan na ce ha'kuri, ina nufin ha'kuri gangariya, irin ha'kurin nan da mai yinsa kan saka a alummar da suke kewaye da shi su halaka saboda hakkinsa da za suyi ta d'auka.
Yaranta takwas cif.
Yaya Salisu, Yaya Rabi'u, Yaya Ummi, Yaya Adnan, Yaya Ali, sai ni Yabi, duk dai bani nake bin Yaya Ali ba, akwai wani ya rasu ne, sai Anas da kuma autarmu Ikilima.
Wannan yawan yara da mahaifiyata ta tara a d'akinta, kuma maza, ya sanya Mama ta tisa ta a gaba da masifa da tuggu, kusan kowa a gidan ya tsani mahaifiyarmu, ba kowa ne yake mua'amala da ita ba.
Duk gidan bakinsu daya ne a kanta. Duk kuma Mama ce ta b'ata ta, take adawa da duk wanda zata ga ya mu'amalan ce ta
Shi yasa hatta mu yaranta bamu da wani kwarjini har a wajen Dada kakarmu da ita ma tana cikin gidan bangarenta daban.
Sai Hajiya Sahura muna k'iranta da Innah. Yaranta biyar Na farkon ma mun dan girme masa ka'dan Ubaid, Ubaida sai Abida, Hajara, Ismail da autarmu gaba'daya Saliha.
Duk yadda Mama ta so wajen raba zumunta a tsakaninmu bai yi tasiri a tsanina da Nazira ba.
Duk yadda bata kula ni, bata sakar mini fuska hakan bai hana ni yin dabdala a dakinta ba a dalilin Nazira.
Bare ita kuma da dakin Goggonmu take kwana..
Sau dubu gara Inna akan Mama. Domin dai ba yadda za'a yi Inna ta ha'da wa Goggo sharri, ko ta tsokane ta da gangan, amma bata wani girmama ta a dalilin Mama ta dabarbarce ta, ta hana ta yin mu'amala da Goggo ta hanyar fa'da mata Goggo ce da gida, duk yaranta maza ne, idan Alhaji ya mutu duk su din y'an kallo ne.
Da na fara mallakar hankalina sai nake tambayar kaina wai mene ne mahaifinmu ya mallaka da har ake fatan ya mutu?
A da kam ya yi arziki k'warai da gaske, domin duk girman Gidanmu shi ya zaga ye ya gine shi, sannan mafi yawa na cikin zuri'arsu shine ya biya musu suka sauke farali.
Amma tun shekarar da aka haife ni ya ha'du da y'an damfara suka yi masa sanadin karayar arziki, har yanzu da muke da shekaru goma sha biyar bai farfad'o ba.
Yan'uwansa kuma kowa ya zuba masa ido ya zama abin tausayi.
Amma a hakan Mama take fa'din Goggonmu ce zata ja komai.
Wannan kenan.
Sai k'ofar Alh Badamasi(Baban Tsakiya).
Matansa biyu da yara sha biyu.
Na uwargidan Hajiya guda bakwai . Babban d'anta Yaya Jabir, Zakiya, Jamila, Hauwa, Firdausi, Aisha sai k'aramarsu , Basira. Nan Firdausi ce warinmu.
Sai amaryar Momi tana da yara biyar, Nasiru, Naziru, Sararu, Rumanatu da Kubrah.
Anan ma Saratu ce sa'armu.
Sai kofar k'arshe ta Alh Iliya (Baban kasuwa).
Matarsa daya da yaransu shida.
Amina, Aminu, Maijidda, Kaltume Abba andda Aliya.
Maijidda ce sa'armu
Sai wajen kakarmu Hajiya Binta! wadda Yaya Umminmu sunanta ta ci. Kowa Dada yake ce mata, wata irin tsohuwa mai wahalar sha'anin gaske.
Tana daga zaune rikicin da take yi ba dan ka'dan bane, haka nan bata damu da ha'din kai a tsakanin ahalin gidan ba.
Domin bayan su Babanmu akwai yan'uwansu mata biyu.
Bangaren Dada ma hawa biyu ne, domin akwai wata k'ofar a can ciki bayan ka wuce k'ofarta ta farko, sannan ana iya fita waje ma ta wannan wajen Sai dai kofar a rufe take. Amma ba kowa ciki sai kayan ajiye ajiye da dangin kayan noma da tarkace.
Babar Bulkachuwa(Hauwa) ita ta biyo Baban Tsakiya, tana aure a Bulkachuwa, mijinta Alh Yusufu babban d'an kasuwa ne a kasuwar kayan miya ta Muda lawal a Bauchi.
Ita ce amarya amma sai a kanta ya samu haihuwa ta tsaya masa, uwargidan wabi take yi, ma'ana idan ta haihu sai su koma.
Tijjani ne babba sai Aliyu, sai Nasir. Sai bayan haihuwar Nasir ne uwargidan ta haifi Maryam da kuma Hafsa.
Daga nan sai Babah ta sake haifar Ihisan. Kenan yaranta hudu na uwargidan kuma biyu.
Tijjani ya taso cikin wani irin gata a wajen mahaifinsa a dalilin tsawon lokacin da ya shafe babu haihuwa.
Sai dai kash gatan ya zame masa d'an zani domin gaba'daya sai ya kangare, tun yana karaminsa ya ko yi fitina iri iri, shine kame kaji da awakin jama'a yana siyar wa, gaba'daya ya ki kar'bar tarbiyar da ake ba shi a sanadin duk abokansa lalattu ne.
Duk yadda Baba ta Bulkachuwa da mahaifinsa suke son fige masa wannan dabi'ar abin ya ci tura.
Akan dole suka raba shi da garin, suka dawo da shi wajen Mahaifinmu da Baban Tsakiya, tunda su din zafi ne da su ainun.
A lokacin bai fi shekaru sha biyar ba.
Sa'an Yaya Salisu ne, amma shiriritarsa ta mayar da shi cikin kannensa su Anwar, duk dai su din ma sun raina shi, sun ware shi ba wanda yake son a ganshi da Bulkachuwa saboda munanan TA'ADODIN sa.
Yayin da mu muke k'ananu sosai
Sai Baba Maryo ita ce autar Dada.
A nan Toro take aure, yaranta biyar amma biyun farko na wajen Dada da ta haifa da mijinta na farko.
Anwar da Nasiba.
Yaya Jabir, Yaya Rabi'u, Yaya Abba da Yaya Anwar duk sa'annin juna ne tare suka taso, fikon junansu mafi girma watanni biyar ne.
Kazalika muma y'anmatan tare muka taso. Duk da babu ha'din kai ko ka'dan a tsakanin iyayenmu mata, hakanan ni da Nazira an fi mayar da mu banza da wofi a dalilin mahaifinmu ba shi da shi, ga shi dai shine babba amma ya zama fanko, ya zama wofi dai dai da shawara ba a yi da shi.
Duk yadda ba wani shakuwa a tsakaninmu irin na zumunci, in dai fita ne, to tare ake tafiya zuwa makarantar boko ko Islamiya.
Haka za'a ganmu zaratan y'anmatan reras da mu.
Kusan ba'a ta'ba yin y'anmata da muke sa'anni da yawa a gidanmu irin akan mu ba.
Domin mun doshi bakwai
Ni Yabi, Nazira, Basira, Firdausi, Maijidda, saratu, Nasiba.
Dukkanmu kowa turbarakallah babu makusa, tunda asalin Kakarmu Dada Bafulatanar Lame ce asalin fulanin Mali.
To kusan dukkanmu mun samu tsayi da gashinta.
Duk da ni din bani da tsayi, yar shafal ce, matsakaicin kyau ne da ni amma fara ce sol, sannan kuguna a dan bude yake ka'dan, sai dai kirjina kam ko na kai shekarun budurci sosai baza su yi wani girma ba.
Kowanne irin sutura na saka sai ta yi mini kyau.
Duk da kayan nawa mafi yawansu masu sau'kin farashi ne a dalilin mahaifinmu baya samun sukunin yi mana sutura.
Abinci ma da wahalar gaske muke cinsa, duk da ga yan'uwansa nan suna cin duk abin da suke so.
Amma ba'a yi mana kara ni da Nazira idan zasu yiwa y'ay'ensu sutura su ha'da da mu.
Ko da yake Nazira ta fini sutura a dalilin Mama tana sanya yayyenmu na d'aki suna yi mata.
Yaya Salamatu tana d'an yin kara tana bada kuncen har da ni, da yake babu laifi mijinta yana da rufin asiri, amma Mama bata bari a bani, sai dai da Yayar ta fahimci hakan sai take bani a b'oye tana fa'din ba sai na fa'da ba.
Ni kuma bana iya yin shiru sai na nuna wa mahaifiyarrmu, ita kuma sai tasan yadda ta yi ta yi mata godiya tana kuma jan hankalina na kula da ita.
Sosai nake ganin kirkin Yaya Salamatu duk da dai sai ta zab'e mafi kyau ta bawa Nazira ni kuma ta bani saffa saffa, amma dai ta k'ok'arta a yadda mutanan yau suka dauki y'an uban ci.
Yayata da muke d'aki d'aya ita ma tana cikin matsanancin babu, domin duk talaucin gidanmu a hakan Goggo take tara mata k'anzo dan ta ci ita da yaranta.
Wani irin bahagon miji take aure, bai san hakkin komai ba sai hakkin auratayya tunda kusan duk shekara biyu suke haihuwa ita da uwargidanta tamkar masu gasa. Dan ma yanzu uwargidan ta daina yi.
Hatsin da za'a yi tuwon dare kawai zai bayar, dai-dai da cefanen miya mace ce zata yi, da safe a yi dumame a ci yadda ya samu, ba dan an koshi ko dan da'di ba.
Da rana kuwa ko wacce ita zata ciyar da kanta da y'ay'anta.
Ba maganar sabulun wanki bare a je ga na wanka.
Yaya Ummi kyakkawar mace amma wahalar da miji ya sakar mata da muguntar kishiya ta saka duk ta fita a hayyacinta.
Domin ita ce mai k'ananun yara, ita d'ayar al'amura sun fara saisaita mata, tunda manyan ya'yanta sun kawo k'arfi, amma komai zasu kawo a boye ne, ita kawai zata amfana.
Duk cikin yaran gidanmu tafi kowa shan wahala a gidan aure.
Shi yasa take a ware, sai idan Yaya Rabi'u ya d'an figi wani abu ya kai mata a dalilin suma suna fama da rik'ewa Babanmu gidanmu.
Rayuwar ta yi mana tsananin gaske, mahaifiyarmu ha'kuri take yi kan ha'kuri.
Kuma wani abin mamaki da Mijin Yaya Ummi mai tarin dukiya ne amma fa baya iya ci, sai dai ya yi ta lissafin kadarorin da ya tara.
Manyan yaransa sai fatan ya kauce su ci abin da bai bari sun ci ba suke.
Gaba'daya tausayin Yaya Ummi nake ji, abubuwa sun yi mata yawa, ga tashin hankalin gidanta, ga azabar yan'ubancin da su Yaya Indo suke yi mata.
Sun wareta, Yaya Salamatu ce mai sassauci kawai.
Duk sadda ka je gidanta haka zaka ganta tamkar mahaukaciya.
Wankau take yi, kamar me? yini take tana wanki.
A hakan take samu ta wanke kayanta da na yaranta, ta kuma samu ku'din da zasu ci abinci da rana.
Duk da dai bashi yafi yawa, sai ta yi wanki sau nawa ba a biya ba.
Na kan yi mamakin yadda mutanen yau suka shagala da fa'din Annabi (S.A.W.) na cewa "Mafi adalcin mutum shine Wanda yake biyan hakkin Wanda ya yi masa aikin wahala kafin guminsa ya bushe.
Amma a wannan zamanin sai mutum mai wadata ya bawa miskini aikin wahala amma biyansa hakkin wai sai ya zama bashi, abin kaicon ma idan an yi masa aikar a bayar da ku'din nan, sai ya zama laifi.
Mace ma'aikaciya sai ta bari ku'din mai wanki, ko markade, ko kuma mai dakan hannu ya taru a kanta.
Ba tare da yarjejeniyar sai k'arshen wata zata biya ba.
Anya kuwa muna son ganin dai-dai jama'a?
Wannan wahalar data taru ta yi mana k'awanya ya sanya na mayar kitsona na ku'di.
Domin tun daga alhamis idan na fara k'itso har lahadi, amma ba wanda zai cire ko da sisi ya bani a cikin matan gidanmu da duk kusan sati nake yi musu kitson su da y'ay'ansu.
Kuma na sani hakan baya hana su karbin ku'din kitson a wajen mazajensu, ko iyayensu.
Bisa shawarar Nazira na daina yiwa kowa kitso sai ta biya.
Iya y'an k'ofarmu kawai nake yiwa kitso kyauta.
Mama kuwa bata yarda ta ba ni kanta dama.
Amma ina yiwa Inna da Gwaggonmu.
Da kuma yan'uwana na k'ofarmu.
Ai wannan bijirewar da na yi akan sai an bani ku'din kitso ya sake jefa tsana a tsakaninmu, domin duk inda Mama ta zauna sai ta ce "Uwarta ce ta kitsa mata, me za'a yi da irin wannan haihuwar a ce ba zaka bari aci arzikinka ba?"
Iyayenmu maza da suka san suna biya basu dauki al'amarin a wani abu ba. Domin suna k'yashin a ce mu d'in muna da mamorar da zamu yi musu alfarma.
Domin fa'di suke yi "Idan ku'di ne ku bata kudinta daidai da yadda na waje zasu biya ta, ko kuma daidai da wanda idan kun je wajen bare zaku bayar. Ita ce bata gaji arziki ba".
Yayin da muka k'udire a ranmu ni da Nazira ba wanda zai sa na yiwa yaransa ko matarsa kitso akan dole domin suma basu taimake mu ba, dai-dai da ku'din islamiya da bai taka kara ya karya ba, basu ta'ba ha'da mu da y'ay'ansu sun biya ba.
An sha koro mu da sauran k'annenmu, akan ku'din islamiya.
Yayin da sauran yaransu basu da wannan matsalar.
Idan zamu yi wata a zaune, Mahaifinmu ko iyayenmu mata basu samu sukunin biya ba, ba wanda zai dube mu.
Dada kuma ba zata ce wane biya wa yaran nan ba.
Ita kanta ta manta irin da'din da Babanmu ya jiyar da ita.
A yanzu kam ta mayar da shi da dukkan ahalinsa tamkar wasu barori a cikin ahalinta.
Tarin Baban kasuwa ya fi maganar Babanmu sau dubu.
Tunda shine yafi kowa rufin asiri, sai Baban tsakiya.
A batun soyayya kuwa kowa shaida ne Dada bata ha'da lamarin Yaya Anwar, da Tijjani da kuma Nasiba da kowa.
Sun fi kowa lasisi a gidan, gasu dai ba y'an gidan ba ne tunda iyayensu mata ta haifa.
Amma sun fimu gata da gadara a gidan.
Yanzun nan Dada zata hau ihu matu'kar aka ta'ba guda a cikinsu.
Sai yaran Baban kasuwa, sai na Baban tsakiya.
Hakan dai hawa hawa abin yake.
Canjin da nake samu a kitso ba k'aramin taimakona yake yi ba.
Haka Gwaggo tana yin kokon safe, muna samu mu sha a ciki, har watarana a aikawa Yaya Ummi.
Asusu na siya nake tura dan wani abu, domin ina matu'kar jin haushin yadda mu da gwaggonmu muke koma baya a gidan.
Yaranta maza an d'ora musu nauyi mai yawa.
Yaya Salisu ne kawai ya yi aure, shima ba wai wadatar ne da shi ba, aikin gini yake yi duk da ya yi karatu amma aiki ya yi wuyar samuwa tunda babu hanya.
Su Yaya Rabi'u kuwa koami na gidan sune, Mama fa'di take ai sune maza, sune zasu taimaki ubansu, ga karatunsu su suke daukar nauyin kansu.
Dan haka Gwaggonmu bata samun komai, amma idan an nutsu za'a fahimci kowa a kofarmu yana cin arzikin yaranta.
Duk yan dakinmu ni ce mai tsiwa, ban dauko sanyin halin uwarmu ba.
A tsaye nake kan kafafuna cak, haka zuciyata bata daukar raini. Sai dai kuma bani da kullaci, ina da saurin afuwa.
A duk sadda na kalli Gwaggonmu da Yaya Ummi sai na tsinci kaina da yiwa kaina da Iklima addu'a samun miji na gari mai wadata, ko muma ma shiga sahun masu mutunci.
Tun kafin hakan kuma sai Ubangiji ya hore mini iya yarfa kitso.
Duk wata matashiya yar kwalisa a yankin nan ni ce mai yi mata kitso.
A hankali sai na fara gwada lalle.
Nan da nan sai Ubangiji ya sake haska mini.
Layi ake yi mini na kunshi da kitso duk satin duniya.
Muka fara dan warware wa, domin muna samun yan kuda'den yin bu'katar yau da kullum.
Hatta Yaya Ummi ta d'an samu sau'kin matsatsacin da take ciki.
Domin duk sati sai na cire mata wani abu.
Da ku'din asusuna ya yi auki na fasa na siya mana kayan kwalliya masu sau'kin ku'di ni da Ikilima da Nazira, har ma da Ubaidan Innah. Sai kuma na sake siyan wani na k'udire niyyar dinki zan yi mana idan kudi ya taru.
Tsawon dauki lokaci ina zubi, kafin na samu na yi mana y'an suturu ni da Iki.
Ai Mama tana ankara da y'ar nutsuwar da muka fara samun kanmu a ciki, sai ta tayar da ballin sai na bar kitso, domin gashi yana yawa a gidan, ba dama ta zubo abinci, zata yi ta ganin gashi.
Ko ina gashi ne, ta gaji da wannan k'azantar.
A wannan karon Babanmu ya yi jarumtar cewar ba zai hana ni yin sana'a ba, tunda shi da kansa ya sani ba k'aramin rufa masa asiri sana'ar take yi ba.
Kusan kullum sai na ba shi naira dari hud'u.
Maganar maganina kuwa idan ba ni da lafiya, na dauke wa kowa.
Dan haka sai muka fara saje wa da su Maijida.
Tunda muma yanzu muna samun yan suturu babu laifi, duk da bai kai nasu daraja ba.
Idan akwai abin da ya yiwa Mama tarnaki rashin kintsuwar Yaya Musa ne.
Gashi dai shi ne babba, amma gaba'daya ya lalace, ya zama d'an iska, hakan kuma yak'i ya zame mata izna, a kullum cikin aibata yaran da ba nata ba take.
Ta kuma gasgata hannu aka sawa d'anta, da kuma bakin mahassada.
Ta kasa fahimtar rayuwa har yanzu.
Tsabar kyashinta ta hana ya'yanta mata su tallafawa Babanmu da d'an abin da zasu iya .
Kullum fa'di take ai hidima ta y'ay'a maza ce. Dan haka komai yaranta mata zasu kawo gidan to nata ne, sai ko idan dafaffe ne sai ta samma wadanda take so, wadanda bata so kuwa ko ta yi babu.
Sai nake mamakin idan tana habaicin ku'din kitson da nake kar'ba, wai Gwaggo ta kasa bari a mori haihuwarta, ko ita wa ta bari ya mori tata haihuwar?
Ko Babanmu da ya yi mata hidimar yaran ba dai tasa su kawo masa wani abu na tallafin gida ba tunda yana da k'ananun yara. Idan ma sun yi hankalin kawo wa to fa ita ce a hakku a kan kayan, ta dinga gadara kenan duk ba wasu kaya masu yawa ba ne, tunda dai ba wai ku'din ne da su ba, rufin asiri ne kawai.
Sai nake mamakin wai mene ne manufarta ne?
Da na kasa gane wa sai na ha'kura, amma hakan ya ja hankalina har nake sha'awar yin bincike da nazari akan gidan yawa mai dauke da mabanbanta iyalai.
*GIDANMU ne kawai kwamacala ta dabaibaye shi?*
*A GIDANMU ne kawai ake yin kasafi irin na kashin dankali ma'ana na sama ya danne na kasa?*
*A GIDANMU ne kawai ake mayar da babba k'arami saboda ba shi da wadata ko kuwa?*
*A GIDANMU ne kawai ake ta'ba yan ubanci ko kuwa?*
*Ba k'aramin caji kwakwalwata take yi ba dan neman sahihohin amsoshi wadannan tambayoyin*.

*Ayi bitar da nutsuwa domin wannan karon gidan yawa zamu kutsa sosai*


VIP 1K.
REGULAR 500.
2384876855
SURAYYA IBRAHIM
ZENITH BANK.


*ASSALAMU ALAIKUM*
*Masoyan rubutun Surayya Dee na gaishe ku, na kuma yaba muku*
*Dafatan zaku yi hakuri, ku bi labarin sannu a hankali, har ku fahimci sakon da nake nufin isar wa.*
*Ba zan ce muku komai ba. Abu d'aya nake da tabbaci ba zaku yi nadamar bibiyarsa ba.*
*Kawai fatana

1 Comments On BAKAR TA'ADA
avatar
aisha-aminy

7 days ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment