Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fashe wa da matsanancin kuka.
Saboda fishin Baban kasuwa ya sanya Baban Tsakiya tsayawa ya mini irin wannan tozarcin da zai yi wahalar gaske na sake ganin girmansa.
Na samu kaina da tambayar anya kuwa Babanmu ba dan uba ba ne a tsakaninsu?
Sai nake ayyana ai ko y'ay'an Baffanni suke (cousins) bai kamata su dinga yi masa irin wannan kaskancin ba, dan kawai sun fishi wadatar abin duniya. Balle kuma girman nasaba irin ta uba guda, sai dai kuma babu haufi cikinsu daya ma'ana Dada ce ta yi nakudarsa tun gabbannin a yi tasu.
Babban farin cikina d'aya, bai rasa wadatar zuciya ba, tunda duk tsananin wahala ba zai bu'de baki ya ce su taimake shi ba.
Idan sun yi niyya akan kansu sun yi masa kyauta to zai kar'ba, amma idan zamu kwana mu yini bamu ci ba, ba dai ya ce wane ga halin da nake ciki ba, sai dai idan ya'yan cikinsa ne.
Har ya k'wammace ya fa'da wa aminisa Alhaji Tanimu tsananin da yake ciki, ya tsananta.
Matu'kar kuma zai fa'da masa to kuwa zai sauke masa buhun masara, dawa, dana gero.
Sau tari kallon wadatar da ake yiwa su Baban Kasuwa yake hana masu k'arfi tallafa wa Babanmu.
Sannan mutanan yau suna da dabi'ar k'in taimaka wa matu'kar ba ro'konsu ka yi ba, yayin da mafi yawa aka fi taimako da azumi, shima fake wa ake yi da sunan neman lada alhali a ku'din zakkar da Allah ya wajaba a fitar ne suke siyan kayan abinci suna rarraba wa.
Oh mutanan yau mun rungumi *Bakaken Ta'adodi* daban daban.
Allah ya shirye mu kawai.
Muryar Inna na ji cikin sigar umarni ta ce "Ki cire Jabiru a ranki, nasan zai yi matu'kar wahalar gaske wannan al'amarin bai zama sanadin yin shamaki a tsakaninki da shi ba.
Ina son ki ninka jarumtar ki, tun kafin su miki 'kwalele da shi."
Kafin na bu'de baki sai ganin Baban Marina muka yi ya shigo a fusace yana fa'din "Ina Asiya?"
Da rawar murya na ce "Ga ni Babanmu".
Ya ce "zo ki fice ki bar mini gida tunda har zaki iya tsaya wa gar da gar ki zagi Badamasi da Iliya akan idonsu.
Ai bansan zaki iya irin wannan dib'ar albarkar ba. Na dauka abin naki akwai lissafi a ciki amma tunda kina ganin idan kin yi karo tsakanin kwai da dutse zai miki daidai sai ki je ki yi a wani gidan, amma ba a nan ba.
Ban haifi d'an da zai zagi dan-uwana akan idonsa na bar shi ba.
Na sha fa'da miki babu ruwan ki da shiga tsakanina da y'anuwana.
Amma sam kin k'i ji"
Cikin kuka na ce "Ka yi ha'kuri Babanmu!
Ba yadda aka fa'da maka al'amarin ya kasance ba. Ban zage su ba, har abada kuma ba zan zage su ba, kada ka kore ni a gidanka, zai iya zama sanadin tabarbare war al'amura masu yawa, ka mini dukkan hukuncin da zaka gamsu. Ka taimaki kanka, ka kuma tserar da ni fa'da wa halaka akan wad'anda basa nufin ka da alheri".
Ya jijjiga kai ya ce "Yabi ki yawaita hamdala da baki zo a cikin mutanan farko ba, lah shakka da irinku ne masu kafiya akan ra'ayinku ko da ya ci karo da gaskiya.
Na ji ba zan kore ki ba, amma dole ki yi nisa da gidan nan tun ban fusata na miki baki ba, tunda ba'kin cikin da kika cusa mini a sanadin musayar yawun da kika yi da iyayenki ba mai sau'ki ba ne, akan kannena mahaifiyata take mini mugun baki. Yabi kibi a sannu fa."
Na sake tsorata na ce "Àllah ya huci zuciyarka Baba, Allah ya shiga cikin al'muranka, ya iya maka da iyawarsa".
Nan da nan ya sauka ya hau fa'din "ameen".
Gobe ki shirya ki tafi gidan Salisu har sai na nemi ki, saura can din ma ki nemi gigita masa zaman lafiya a gidansa, dan nasan zaki gano masa laifukan da iyalinsa take yi wanda shi yake yin uzziri a cikinsu".
Na yi kasa da kaina na kasa cewa komai.
Washagari kuwa Gwaggo da kanta ta shirya mini kayana a ledar biba tana ta jaddada mini idan na kuskura na yi rikici da matarsa to ba tantama da ita na yi.
A sanyaye na ce "Komai zan ga ni zan runtse idona babu ruwana, ko da kuwa zata tsokane ni."
Wani irin salama ya shiga Gwaggo ta dinga fa'din "Yauwa Yabina Allah ya sassauta miki".
Anas ne ya fara yi mini gaba da kayana.
Yayin da zamu tafi da Nazira da Iki idan anjima.
Nazira sai kuka take akan tafiyar da zan yi na barta.
Na yi shirin zuwa gaida Dada wanda rashin zuwa wannan gaisuwar ba k'aramin abu take mayar da shi ba.
Babu kuzari na ce "Nazira mu je mu gaida Dada".
Ta girgiza kai tare da cewa "je ki kawai, bana jin dadi anjima na leka".
Na ce "Tom na tafi, ina jin da'di tare da k'arfafa wa kaina guiwar ko na rasa soyayyar kowa a fuskar zumunci ina da yakinin ba zan rasa soyayyar Nazira ba.
Tana sona fiye da zatona, haka nima nake sonta tamkar yadda nake son shakikiyata Yaya Ummi.
Tun daga bayan katangar Dada nake jin tashin muryoyinta da na Ya'yanta
Na karasa har cikin soron sosai na dinga jin kumfar bakin da Baba Maryo uwar Nasiba take yi akan ba zata ta'ba yarda a dauki Nasiba a bawa Tijjani ba.
Kuka take yi wiwi. Tana cewa "sai dai a ga laifina a banza, amma wannan ha'din ba mai yiwu wa ba ne."
Yayin da Babah ta Bulkachuwa take fa'din "Ai ban ga laifinki ba, gaskiyar magana kika fa'da.
Kuma dama mutum shi yake mutunta kansa, da ya nutsu ya zama mutumin kirki ina ce a ko ina zai nemi aure a ba shi?.
Yanzu kuwa da ya zama abin da ya zama a cikin danginsa ma gudunsa za'a yi bare a waje".
Dada ta ce "Ya isa haka, ba cece-kuce zaku yi mini ba.
Na rufe wannan maganar, na yi zaton auren nasa da ita zai kawo masa dai-daito tunda tana sonsa, idan aka yi sa'a sai ya shiryu, ruwan wankan aure ka'dai maganin wanda ko wacce suka fand'are ne. Amma tunda abin zai zama tashin hankali a bar maganar haka nan
Nasiba ba matarsa ba ce."
Kafin na yi wani motsi sai jin muryar Baban Tsakiya ya yi yana fa'din "Kazalika wannan yar iskar yarinyar ba matar Jabir ba ce, ko bayan raina idan aka bari ya aure ta Wallahi Allah ya isa, na fa'da a gabanku, kuma yanzu ma idan na tashi zan je na sami Yaya Sani na tabbatar masa babu maganar aure, mun gama magana da Iliya, Maijidda zai aura.
Domin ba zan yadda ya dauko mini majuniniyar yarinyar nan ta zo ta tarwatsa mini zuri'a ba".
Daidai lokacin na yi sallama na gaida Dada sannan na gaishe su a jamma'u.
Babar Bulkachuwa ce ta amsa cikin karfin hali tana danne bacin ran da ya ke kutso mata.
Nima na yi jarumtar cewa "Ashe kin zo Babah?"
Ta ce " Na zo dazun nan kin san sammakon zuwa nake yi saboda motar Jos muke shigowa.
Na yi yake na ce "Sannu da zuwa".
Na mike da nufin tafiya sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Dawo ki zauna.
Na zauna ina kallonsa k'ir domin ya riga ya wanke mini a zuciyata.
Ya kausasa murya ya ce "ki hanzarta turo wanda kuka shirya domin kuwa watan jibi da saba'a zaku bar gidan nan".
Cikin son nuna masa iyaka na ce "To ai Jabir naka muka daidaita da shi, wannan satin zai iso garin, wajenka zan turo shi, ko wajen Baban Kasuwa?"
Ya zabura ya mini dakuwa ya ce "Marar kunya, marar mutunci ki zagi dan-uwana, ki mini tsaki a gabana ki yi zaton kuma zaki zama surukuta, ko dai bayan sharholiyar da kike yi har shayeshaye kike had'a wa da shi?
To saurara ki ji! Jabir ba zai auri wanda zata zagi ubansa ba."
Babu fargaba na ce "Na karbi wannan hukuncin da hannu biyu Baba, ban kuma saka ka cikin masu son rai ba, domin na yi laifin da na cancancin hakan.
Alfarma d'aya nake ro'ko a wajenku tunda ni ce bani da tarbiya, to ku musanya wa Yaya Jabir ni da Nazira domin dukkanku nan ba wanda zai zargeta da rashin tarbiya ko sharholiyar da ni nake yi".
Nan da nan Baban kasuwa ya ce "Anki a bashi ita din dan uwarki, makira, algunguma, Maijidda ce matarsa har a kiyama kuwa".
Ga mamakina sai na mike na tsinci kaina da cewa "Gaskiya Baban Marina ne ba a so, shi kuma har yana kora ta saboda ku.
Ba komai Ubangiji ya sanya alheri".
Har na fice ba wanda ya iya bu'de baki ya ce mini kala tsabar kad'uwar da suka yi da furucina.
Baban Tsakiya ne cikin fishi ya ce "Ba shakka dangin uwar yarinyar nan akwai majununai".
Na so na tsaya na ce "ko wanne d'a yafi gadon dangin ubansa, dan ya gane sune majununai ba mutanan Kangire ba. Sai dai kuma duk iyashegena ai wata fuskar tafi gaban mari, kannen ubana ne, ta ko wacce fuska idan na yi musayar yawu da su ni ce bani da gaskiya. Sai kawai na had'iye.
Ina fitowa na yi kicibus da Bulkachuwa yana tsaye da buta a hannunsa, tabbacin daga bayi ya fito.
Na tabbatar kuma ya ji komai har maganganun da aka yi a kansa da Nasiba.
Domin gaba'daya manyan idanuwansa sun kad'a, sun yi jajur.
Na wuce shi ban sake kallonsa ba, kallonsa ka'dai ya sanya na ji tamkar na yi amai tsabar yadda na washe shi.
Wannan abin da na yi ya sake ki'dima wadannan bayin Allah domin dukkansu ba wanda maganar bata shige shi ba.
A ranar na koma gidan Yaya Salisu ban san wainar da ake toyawa a gidan Marina ba.
Zama nake yi irin na taka tsantsan a gidan, ba dan komai ba sai togaciyar da aka yi ta yi mini a gida.
Da safe zan yi wanke wanke da shara, na yiwa dansu wanka shi kenan sai na shige daki.
Idan ta gama abinci zata mini zubin auki.
Yadda nake gudun bata mata, hakan ita ma take kaffa kaffa dan kada na ga beken ta, ko idan na koma gida na bada ba'kin labari a kanta.
Ranar da na yi kwanaki hudu sai ga Nazira da Iklima.
Muka yi hira, sun kusa tafiya Nazira ta ce da Iklima ta fita ta jira ta a waje.
Ba musu Iki ta fita.
Ta sassauta murya tabbacin bata son a ji maganar ta ce "Kinsan me yake faruwa kuwa a gida?"
Na girgiza kai ina fa'din a ina zan sani Adda Nazi?"
Ta sake yin kasa da murya ta ce "wata yarinya ce ta yi cikin shege har ta kusa haihuwa fa, to ana ta shari'a, da ta lissafo wadanda suke mua'amalantar ta har da Yaya Bulkachuwa yanzu haka kullum sai sun je kotu".
Zuciyata ta harba da tsananin gaske, na ce "Tijjani gaskiya baya kyauta mana, gaba'daya sai ya gama ruguza darajar gidanmu alhalin shi ba dan gidan ba ne".
Nazira ta ce "Hmm abin sai ha'kuri ba ki ga yadda ya zama ba, ya kuma kafe akan ciki ba nasa ba ne ba zai kar'ba ba. Babah ta Bulkachuwa ita ma ta zama abin tausayi sosai tsabar ba'kin ciki."
Hawaye ya balle mini wata irin damuwa ta shige ni, kishin zumunta ya murde ni, ko yaya ba zaka so ganin jininka a cikin tozarci ba.
Mun jima a hakan kowa da k'wallarsa ta ce "Jiya Malam Yunus Econs ya aiko a bashi izinin neman aurena kinsan tunda matarsa ta rasu a wajen haihuwa har yanzu bai sake wani auren ba, ga yaron nan tuni ya shekara biyu."
Na ru'ko ta ina fa'din "Kai na yi murna sosai Allah ya tabbatar da alheri mutumin kirki ne, na amince Adda Nazi ta so shi ta bashi dama, Allah sanya albarka a tafiyar".
Muka fito ina musu rakiya tana ce wa "Abdul sau uku yana zuwa amma Baba bai bari an fa'da masa inda kike ba."
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

Na ce zai bari ne, domin ko Yaya Jabir ne autan maza na bar shi Nazira".
Ta ru'ko hannuna ta ce "Madallah da zuciyar Yabin Marina! Ni nasan zuciyarta ba zata cigaba da son wanda zata yi kuka a hannun ahalinsa ba, ba zata so wanda ubansa yake k'yamarmu ba, in sha Allah sai kin auri wanda ya fishi komai, aurensa da Maijidda kuma bama adawa. Sai kuma kuka ya goce mata, nima hawaye ya sake zubo mini, domin idan na ce bana sonsa ko abin bai dame ni ba na yi k'arya.
Amma zan nuna wa su Baban Tsakiya ni din yar halak ce ina kishin ubana, ina kuma kishin kaina.
Babban rufin asirin da Allah ya yi mini shine dama ina da Abdulrashid. Su biyun duk ina sonsu amma nafi son Yaya J.
Yafi daukar hankalina matu'ka da gaske sai dai zan iya rayuwa da Abdul ba tare da na takura ba.
Sai da muka yi kukanmu son ranmu sannan muka je gidan Yaya Salamatu, muka bata labarin halin da ake ciki.
A sanyaye ta ce "Babanmu ne basa so fa, gara miki ma hakan, Allah ya kawo miki mafi alheri me za'a yi ma da auren dangi irin namu ne?"
Mun jima sosai sannan muka tafi, bayan na bata labarin Malam Yunus da yake son Nazira.
Ta yi murna, ta yi farin-ciki, ta bamu dari biyar mu hau mashin. Bayan ta bawa Nazira kaya a leda ta kaiwa Mamansu.
Na koma gidan Yaya Salisu, su kuma suka wuce gida.
Kwanana shida da barin gida sai ga Yaya J a gidan Yaya Salisu.
A matu'kar birkice na ganshi.
Ya kasa mini magana, tsawon lokaci kafin ya ce "Me yasa haka Yabi?"
Ba walwala na ce "me yasa, me ke nan?"
Ya ce "na dauka ko baki ha'da komai da su Baban Tsakiya ba zasu ci darajata bare kuma iyayenki ne da zasu daura miki aure".
Na bata rai na ce "Bana ma bukatar su mini walittaka Jabir, domin komin kashin Babanmu da ake ga ni, Ubangiji ya azurta shi da yara mazan da zasu maye mana gurbin kowa.
Kai ko ba ni da yan'uwa maza a cikin gidan Wallahi Ammar da Bulkachuwa zasu iya daura mini aure duk da kasancewarsu ya'yan mata ne, amma idan har ya kasance sai ku to lah shakka zan iya saka hula na wakilci kaina ko kuma na samu alkali ko liman".
Jikinsa ya yi matu'kar yin laushi.
A sanyaye ya ce "Ni yanzu mene ne laifina a nan Yabi?'
Yana rufe baki na ce "Rashin biyayyar ka. Na tabbatar an fa'da maka ka kiyaye ni, domin ban cancanci ka aure ni ba, saboda mahaifina ba shi da daudar duniya".
Ya yi kasa da kansa ya ce "Ni da ke muke magana ki daina sako mini manyanmu domin wannan ba dabi'a ce mai kyau ba.
Na gallah masa harara na ce "Madallah"
Na tsuke bakina na yi gum.
Ya marairaice ya ce "Yabi kada ki bari a bada kofar da za'a yi mana farraku, ina son ki, ina kaunar kasance wa da ke, jikina na bani kamar ma na kusa barin duniyar nan, ki taushi zuciyarki kada ki zalunci wanda yake tsananin sonki Yabi. Ban miki komai ba, kada ki hukunta ni da laifin da bani na yi miki shi ba".
Jikina ya yi sanyi. Na kasa magana domin gaba'daya ya d'aure ni da jijiyoyin jikina. Zufar da take karyo masa ta sanya na sake jin sonsa na taso mini.
Kafin na yi magana sai kawai na tuno maganganun mahaifinsa a kaina, wai ni da nake matsayin y'arsa, yar dan-uwansa amma ya jefe ni da mafi munin kalma wai ina bin maza, ke nan karuwa ce?
Bayan ga hakan kuma ya ci mutuncin mahaifina wanda wansa ne.
Take na ji karshen jakanci ne na cigaba da mua'amalantar jininsa da sunan soyayya.
Mussaman da ya ce yana tausayin zuri'ar da d'ansu zai kwaso musu ni.
Na dago cikin karfin zuciya na ce "Jabir mu yi datse wannan soyayyar ka ji, na rantse maka tun jiya na shak'e ta, na kwashe mata karama.
Babanka ya tabbatar mini Maijidda ya za'ba maka, domin ita ce arzikin ubanta yayi daidai da shi, ban yi ba'kin ciki ba, domin kullum zabin Allah muke nema.
Alhamdulillah! Na karbi wannan kaddarar da hannu bibbyu, domin Ubangiji na bar wa al'amarin, ya yi mana za'bi da kansa.
Amma zan roke ka Yaya Jabir ka yi iya kokarinka wajen taka burki a ta'ba mutuncin Baban Marina da ahalinsa.
Ina jin tsoron kada wannan matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba.
Ina jin tsoron kada a wayi gari a ga gidan Marina ya zama sansanin yaki a tsakanin jini guda".
A matu'kar birkice ya ce "Allah kada ya kaddara mini ganin hakan Yabi! Ina fatan mutuwa ta riske ni kafin wannan lokacin"
Na girgiza kai na ce Shi kenan".
Ya marairaice ya ce "Na tsugunna miki Yabi Asiya?
Ki taimake ni, ki fahimce ni, idan kin kwantar da hankalinki ai za'a a samu sulhu ta sanadin aurenmu.
Sai mu kawo dai-daito, an yi abin da yafi haka muni, kuma an dawo an shirya, kada ki tsananta, ki yanke mini hukuncin da babu laifina. Allah da kansa baya kama mu da laifin iyayenmu ko na y'ay'anmu. Daure ki ji tausayina, na rantse idan kin bani ha'din kai ba abin da zai sa na bar ki komai za'a yi kuwa" .
Na girgiza kai na ce "Idan na yi hakan ba sonka nake da gaske ba.
A gaban iyayenmu Baban Tsakiya ya ce "Idan aka baka aurena Àllah ya isa.
Baya ga hakan kuma ya tsane ni, tsanar da ya danganta ni da karuwa ce ni, kuma ya ce na zage su, hakan ya janyo ubana ya kore ni saboda shi kullum yana sonsu, yana musu kyakkawan zato".
Daga haka kuma sai kuka ya subuce mini.
Bai hana ni yi ba, shima kuma idonsa ya ciko jijiyar kansa ta yi rud'u rud'u tabbacin yana cikin rud'u mai girma.
Da murya kuka na ce "Maijidda ta fini kyau, ta fini gata tunda Babanta mai ku'di ne, ta fini komai, ka karbi zabin iyayenka na tabbatar Ubangijin adalci zai juya maka al'amarint fiye da al'amarina, tunda ka yi biyayya.
Zan fa'da maka gaskiya ko zan yaudari kowa bazan yaudare ka ba. Kana da muhimmanci a rayuwata, da gaske ina ganin mutuncin ka.
Na roki arzikin ka rabu da ni, na riga na ha'kura da kai Wallahi, maganar soyayya kam ta kau".
Ya numfasa ya ce "Oh! Haka kaddara ta za'ba mini? Na so ace kin saurare ni, na so ace kin bani dama mun ha'da hannu da k'arfe mun yaki wannan *BAK'AR TA'ADAR* da take neman zame wa alummarmu tamkar wutar jeji.
Ina cikin zullumin yadda zumuncin yau ya koma tsakanin masu kumbar susa.
Ina cikin takaicin yadda aka jahilci d'an-uba.
Ina matu'kar so a ce kin zama matata ta yadda zamu kawo cigaba ta fuskar zumunci a cikin zuri'armu ta hanyar mua'amalantar kowa da girmama wa.
Amma babu komai, mu ci gaba da addu'a Allah baya juyar da addu'ar masu kyakkawar manufa".
Ya saka hannu ya zaro hankicif ya fara goge zufar tashin hankali da take yanko masa, kalaman sa ba k'aramin sukurkuta ni suka yi ba.
Amma na yi jarumtar waske wa domin har cikin zuciyata nake jin ban cancanci na zama cikin ahalin Baban Tsakiya ba.

Ya kasa cewa tsawon lokaci sannan ya yi karfin halin cewa "Fatan alheri mai yawa gare ki Yabin J".
Sai ya dawo da sauri cikin rawar murya ya ce "Yanzu kin mini adalci idan kika jingina sunan ki da wani na?
Yanzu kin manta komai, bani da wata alfarma a wajen ki?"
Na yi kasa da kaina na ce "Alfarmomi masu yawa kuwa .
"Kai na fara so, kai kawai nake yiwa uzziri da sassauci bayan iyayena, sannan idan akwai wanda na yarda da son da yake mini to kuwa kai ne.
Sai dai ko kusa bazan yaudari kaina ba.
Iyaye girmansu yawa ne da su, Annabi (S.A.W) ya yi ta jan hakankalinmu akan mubi su.
Idan kuwa hakane zan gwada maka cikakkiyar soyayya ta hanyar dora ka akan turba sahihiya, iyayenka duka biyu basa son almarinka da ni.
Dan haka ka bar son zuciyarka, ka musu biyayya, na yi imani Ubangiji ba zai barka haka ba".
Daga haka na fashe da azababben kuka.
Jikinsa ya dinga kyarma ya ce "Na sani kina sona. Na roki arzikin, ki mini uzziri, kar ki ce mu rabu, mu bar wa Allah ya yi mana za'bi, mu yi addu'a mu ga ni. Jikina bai bani akwai namijin da zai aure mini ke alhalin ina numfashi a wannan duniyar ba".


*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.

*BAKAR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*ALBISHIRINKU*
*MASOYAN LITTAFAN MARUBUCIYA HAFSAT C SODANGI*!
*DUBA DA YADDA KUKE KEWAR RUBUTUNTA YA SANYA TA YI SHIRIN SAKE DAWOWA DAN TA SAKE MUKU WANI RUBUTUN SABO DAL*
*AMMA KAFIN HAKAN TA DAWO MUKU DA TSOFAFFIN LITTAFAN TA ZUWA KAN WAYA, DAN KU SAKE BITA TARE DA NAZARIN KYAWAWAN SAKON DA TAKE NUFIN ISARWA GAREMU*.

*A YANZU HAKA LITTAFAI HUDU NE RIGIS*

*WAYYO DUNIYA 1-3*
*KYAUTATA 1-3*
*DAGA K'IN GASKIYA 1-3*
*MATA MASU DUNIYA 1-3*
*KO WANNE 1K NE AMMA AKWAI DISCOUNT IDAN ZA'A SIYA SAMA DA GUDA DAYA*

*MISALI GUDA BIYU-1500*
*GUDA UKU 2500*
*GUDA HUDU 3500*

*ZA'A TURA KUDIN TA ASUSUN MARUBUCIYAR KAMAR HAKA*
*0082739293, ACCESS BANK HAFSAT YUNUS ABDULLAHI*

*SAI A TURO MINI SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*SAI NA BADA LITTAFIN DA AKE SO*

*MADALLAH DA KARFAFA GUIWARKU*
*MADALLAH DA SOYAYYARKU GA RUBUTUNMU*

*AKWAI LITTAFANTA SAMA DA GUDA GOMA DA A YANZU SUKE SOFT COPIES, KAWAI KI TAMBAYI DUK WANDA KIKE NEMA A WAJENA CIKIN LITTAFANTA NA BAYA*.



*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*

13&14.
Da azama na shige cikin gidan na bar shi domin na samu sau'kin halin da nake ciki.
Kuka na dinga yi tamkar zuciyata zata fa'do k'asa, bansan son Yaya J ya tumbatsa a zuciyata irin hakan ba sai yau, domin sai na tsinci kaina da addu'ar na zama gawa kafin igiyar aure ta d'auresu da Maijidda.
A wannan daren barci rabi rabi na yi shi.
Washagari da hantsi sai ga shi ya dawo, kallo d'aya na yi masa na gane yana cikin zullumi mai yawa domin gaba'daya ya zube ya sake fige wa.
Yaya Salisu da ba shi da matsala da kansa ya masa iso har cikin falon gidan da yake dakuna uku ne a jere falle falle.
Na fito a sanyaye sanye da hijabi idanuwana a kumbure a dalilin kuka da rashin barci.
Na zauna a kujerar da ta yi nesa da wacce yake zaune.
Tsawon lokaci muna zaune jigum jigum, tamkar masu makoki, daga karshe dai ya k'osa cikin murya marar amo ya ce " Yabi babu gaisuwa ne?"
Kaina a kasa na ce akwai gaisuwar da tafi nema maka amincin da na yi?
Shin ka raina sallamar ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Hakkun Yabi. Kin fini kusa da daidai, kin yi barci kuwa?".
Kaina a k'asa na ce "Me zai hana Yabin Marina barci a wannan duniyar? Sai mutuwa, ko ciwo".
A matu'kar sanyaye ya ce "Idan kuwa hakane ki shirya kwanan zaune domin kullu nafsin za'ikatul maut. A kowanne lokaci muna iya rasa mutane mafiya daraja a rayuwarmu, ko kuma a jarrabemu da ciwo mai hana runtsawa. Fata dai Allah ya bamu ikon cinye dukkan jarabawowin da suke dunfaromu.
Ban da dai dan-adam an jarrabe shi da tsoron mutuwa, mene ne abu mai da'di a cikin wannan duniyar da a kullum tsanani da bacin rai suke sake yiwa mumini k'awanya?"
Ban tanka masa ba, domin kuwa gaba'daya zuciyata babu sukuni, kuma cike take da ba'kin ciki mai nauyi.
Cikin alhini ya ce "Yabi ban yi zaton munin dambarwar da take faruwa ta kai lalacewar da ta yi ba!
Na gamsu, na ha'kura da aurenki a yanzu, dan na tsaremu daga fa'dawa halaka.
Amma na rantse miki

1 Comments On BAKAR TA'ADA
avatar
aisha-aminy

7 days ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment