Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bbu wasa,kuma iyayenta suna kiranta sosae awaya.


Wata ranar juma'a suntaso daga lecture,suka biya office din yaya Rafeeq ranar Iman na hostel sbd lecture din chemistry suka taso.


Zuhra na sanye da hijabinta tare da liqab,Islam kuma doguwar riga ce tayi rolling dama ita tafison irin wannan shigar.

Kamar kullum yauma saida yabasu umarni sannan suka shiga office din.

Zaune yake gaban table yana duba wani littafi,amma da mamaki suna ciga yadago fuskarshi bbu walwala sosae.

Bayan sun gaishe da shi cikin harshe turanci kamar kullum.

Yadan saki fuska,yabasu umarni da suzaina.

Bayan sun zauna,Islam tace"yayana me ke damunka naga fuskarka cikin damuwa?"

Yaya Rafeeq yyi murmushi karo na daya wanda yaqarama fuskarshi kyau yace"Islam bbu komae"

Zuhra tayi mamakin sakin fuskar da yyi ma Islam wanda tinda suke zuwa baitaba yiba,tou kodae da gaske yafison Islam ne.


Yaya Rafeeq yasauya maganar yace"Mami kullum sae tayimin tambayar wae yaushe zakuje weekend ne?"

Islam tasan halin yaya Rafeeq sosae,tasan akwai abinda ke damunsa amma bayason asani shiyasa ya canxa maganar.

Islam tace"ai Aunty hanan tace mutafi kaduna tare da ita muyi weekend din acan"

Yaya Rafeeq yace"kinfa san banason yawo ko?"

Islam tace"nima bazan tafi ba,sbd idan natafi zamubar zuhra ita daya,saedai Iman tayafi"

Yaya Rafeeq yace"wa cece zuhra kuma?"

Islam tace"yayana yanzu duk zuwa gaishe da kai da mukeyi da ita baka santa ba,kuma fa itace highest score a course dinka,kuma fa yaya ko Mami tasan zuhra"


Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"ya isa haka,parrot din Mami"

Islam tagwabe fuska tace"kai yayana kafasan banaso amma shikenan,idan kuna magana da Mami akan Aunty hanan bazan sake saka bakina ba"

Yaya Rafeeq yyi dariya karo na daya, da yyi dariya kamar haka agaban wani ko wata.

Yace"haba Islam kada kiyimin haka mana"

Islam taqara shagwabe fuska tace"tou bakai bane yaya Rafeeq"


Yyi murmushi yace"double sorry"


Aunty hanan ce tashigo tare da sallama bata ko tsaya yabata izinin shigowa ba tashigo,sanye take cikin wani tsadadden material dinkin riga da siket sun zauna ajikinta ,tayi kyau sosae,dan qaramin mayafi ne tayafa sai kamshi ke tashi.

Yaya Rafeeq yadaure fuska,zuhra ce tafara gaishe da ita,amma tana yamutsa fuska ta'ansa,amma da Islam tagaishe da ita lfy qlau ta'ansa mata.

Islam batajin dadin abinda Aunty hanan takeyima zuhra sbd ita bataga abinda tayi mata ba.


Aunty hanan tace"Islam narabu da ganin ki,sae Iman nake gani"

Islam tace"Aunty hanan lectures sunyi mana yawa,ga Assigment yashaga gabammu"

Aunty hanan tace"amma ae kinsamu time din da zakizo mugaisa ko,Mummy nata cigiyar ki"

Ganin baida niyyar yimata magana tace"Dr. ya aiki?"

Bai kalli inda takeba yace"lfy"


Aunty hanan tasanyaya fuska tace"haba Dr.lfy naga ranka abace?"

Yaya Rafeeq yace"Hanan,idan har bazaki gyara halinki ba tou bazamu daidaita da ke ba"

Aunty hanan tabata fuska,cikin bacin rai tace"Dr.wae mi yasa bakason zama lfy ne?"

Yaya Rafeeq yanuna hanya ranshi abace yace"fitarmin daga office"

Aunty hanan tace"bazan fita ba,inason magana da kai yau"


Islam da Zuhra najin haka,Islam tace"yaya Rafeeq zamu tafi" sukayi masu sallama suka fita.

Hanan tabi zuhra da harara,tafin tayi tsoki.

Hanan tace"Dr. mi yasa kake wulaqanta ni agaban wannan jakar yarinyar ne?"

Yaya Rafeeq ranshi bace yace"wa ce jakar?"

Hanan tamaida mashi cikin nuna isa tace"wannan yar iskar yarinyar da take makalema Islam,kodae sonta kke yi ne?"


Ranshi yakai qololuwa wurin 6aci tini idanuwanshi suka canza laune yace"wlhy idan baki fitaba zan iya aikata komae akanki Hanan"


Ita kanta taji tsoron ganin yadda Rafeeq yasauya cikin mintina kadan,fita tayi tabar office,idanuwanta cike taf da hawaye.

Zuhra da Islam suna fita suka nemi nafef suka hau.

Islam tace"Zuhra dan Allah kiyi haquri akan abinda Aunty hanan take yimaki"

Zuhra tayi murmushi tace"Islam kenan,ni bbu abinda tayi mani,may be ni nayi mata wani laifi"

Islam tace"bbu abinda kikayi mata Zuhra,wannan kadan ne daga cikin halin Aunty hanan shiyasa basu shiri da yaya Rafeeq"


Haka suka isa bakin hostel,aka saukesu sannan suka shiga..


Suna shiga room dinsu suka tarar da Iman tagama shiri zata fita lecture din maths.

Iman tace"sannu da dawowa"

Zuhra tace"yawwa sis"


Islam tace"wlhy nagaji sosae"

Iman tace"wlhy yawon zuwa lecture akwai wahala,dan Allah Islam kiyima yaya Rafeeq magan yasa baki,daddy yabamu mota"

Islam tahau gado takwanta tace"kema idan kika fadi mashi ae bawani abu bane"

Zuhra tashiga toilet,Iman tace"na tafi sae nadawo zamuyi magana,may be nakwana quarters wajen Aunty hanan tinda mummy batanan"

Islam tace"uhm,Allah ya kiyaye hanya"


Haka zamansu yakasance har suka fara exams karatu wurin zuhra da Islam da Iman ba'a magana suna maida hankali sosae.


Tsakanin yaya Rafeeq da Hanan bbu wata gituwa,kuma kusan kullum sae taje office dinshi sbd taganshi,amma shi tin hayaniyar da sukayi haryanxu yaqi sakar mata fuska abin duniya ya isheta,gani take yaya Rafeeq son Zuhra yake(ni miss j ne yaya Rafeeq din da baisan fuskar zuhra ba🤔).

Ahaka su Zuhra suka kammala first semester exams dinsu,exams sunzo masu da sauki sosae,sunyi karatu bbu kama hannun yaro.

Ranar da Zuhra da Islam suka gama exams,Islam tayima yaya Rafeeq magana akan dan Allah yatafi da Zuhra gida,tinda shi yau zai tafi,Iman sae gobe take gamawa kuma Aunty hanan zata taho da su goben.............





*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:20] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*




*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*



_DEDICATED TO_ *zahra Galadima (Noor)...*


*40-45*



Dr. Rafeeq yadaure fuska yace"islam yaushe kika fara rainani ne?"


Islam tazaro ido tace"wlhy yaya rafeeq ba raini bane"

Dr. Rafeeq yace"tou bazan yiba"


Islam batace da shi komae ba,sbd tasan halin kayansu ba'ayi mashi musu.

Islam tace"tou yayana ni zantafi,Allah yatsare hanya"

Abinda yyima Islam baiji dadi ba,bae taba tinanin akwai abinda Islam zata nema awurinshi tarasa ba,sbd Islam tadaban ce agurinshi,bazata tabayin abinda zata batama wani raiba shiyasa yake sonta kuma tana bashi girmanshi fiye da Iman.


Islam hartakai bakin kofar office dinshi,yakira sunanta murya asanyaye.

Yace"Islam,xonan"

Islam tajuyo sannan ta'ansa,fuskarta bbu alamar damuwa sbd ita dawuya kagane fushinta.

Takoma cikin office tace "gani yayana"

Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"Islam ina alfahari dake amatsayin ki na qanwata"


Islam tayi murmushi tace"nagode yaya Rafeeq"

Yaya Rafeeq yace"zantafi da ita,abinda kikeso kenan?"


Islam tace"eh yayana sbd Zuhra tanada kirki sosae"

Yaya Rafeeq yace"har tafiki ne?"

Islam tace"sosae ma yayana"


Yaya Rafeeq yace"tou tashirya yanxu danaje gida zanzo mutafi"


Islam tayi mamakin yaya Rafeeq,sbd shi idan yace bazaiyi ba tou bazaiyin ba,amma kuma gashi yau sa'a daya yacanxa.

Islam tayi murmushi cikin zuciyarta tace yaya Rafeeq Allah yabaka mace mai haquri,amma da alama Aunty hanan batada haquri,afili tace"yayana nagode sosae"

Yadan daure fuska sannan yace"tashirya yanzu tajirani bakin gate,kinsan banason abatamin lokaci"

Islam tanufi hanyar fita tana cewa insha Allah bazamu bata lokaci ba.


Islam nafita tasamu nafef takaita bakin hostel.Bayan tashiga cikin hostel tanufi room dinsu,tana shiga tatarar da Zuhra tashirya ita daya take jira suyi sallama.

Iman tace"dama ke muke jira wlhy"

Zuhra tace"bari intafi, Islam kada nayi dare ahanya"

Islam taja trolly din tace"mutafi bakin gate kada yaya Rafeeq yajira mu"

Iman tace"Islam yaya Rafeeq zaizo ne?"

Islam tace"eh zaitafi da Zuhra ne"

Zuhra ji tayi gabanta yafadi sbd ita tsoronshi takeji yadda taga yanayima Aunty hanan da su Iman.

Zuhra tace"Islam da yabarshi wlhy danaje tasha zansamu mota"


Islam taja hannunta harsuka isa bakin gate,sannan tace"Zuhra motar haya tanada matsala amma idan yaya yatafi da ke,muma hankalimmu zai kwanta"

Iman tace"gsky Zuhra kinada sa'a da yaya Rafeeq zae rage maki hanya wlhy da Aunty hanan ce bazai tafi da ita ba"

Ganin lambar motar da sukayi shiyasa suka gane shine ciki,sabuwar motace maroom colour qirar RANGEROVER,glass din motar mai duhu(tint)baka ganin abinda ke cikin motar.


Can gefe dasu yyi parking,students sae faman kallon motar suke wasu suntsaya suka wanda zaifito daga cikin motar.

Suka qarasa inda yyi parking,glass din motar yasauke sannan yabude masu boot din motar batare da yafito,bayan sun saka trolly din cikin boot sannan suka koma saitin driver yake zama suka gaishe da shi.

Ba yabo ba fallasa ya'ansa,sannan ya umarceta da tashigo.

Saida sukaga yatada motar sannan suka koma hostel,suka fara hada kayansu sbd yau quarters zasu kwana gidansu Aunty hanan.


Tinda suka shigo motar bbu wanda yyi magana sae waqar ice prince dake tashi ahankali tare da mayataccen qanshin turarenshi mae tada hankali.


Ahankali tadaga kanta talleshi,ji tayi gabanta yafadi,sbd tsananin kyau da yyi,farar shirt ce jikinshi mae kwala tare da maroom din wando,gashin kanshi yasha gyara yaqara baki sae shining yake,kyawun fuskarshi yaqara fitowa,tare da sayenshi wanka yaqa tona asirin kyawunsa,cikin sanyayyar muryarshi mai kashe jiki yace"ko kina buqatar wani abu ne?"


Batasan lokacin da tadawo duniyar tinanin data lulaba sbd tsabar tsorata tace"a'ah bana buqatar komae"

Zuhra tayi ajiyar zuciya,cikin zuciyarta tace"Allah yayi maka komae mai kyau kuma yabaka komae narayuwa.

Nokia dinta tashiga ringing dasauki tadauka dan kada yace tadame shi.

Cikin zazzaqar muryarta tayi sallama,daga can bangaren Baba ya'ansa,bayan tagaishe da shi,yake tambayarta tataho ne?,Zuhra tace"eh Baba muna hanya yanzu"

Baba yace"ke da suwaye ne?"

Zuhra tace"Baba yaya Rafeeq ne muka taho tare?"

Baba yace"waye haka?"

Zuhra tace"Baba,yayan Islam ne"

Baba yace"tou Allah yakawo ku lfy"

Sukayi sallama.

Yadda yaji ta'ambaci sunanshi baisan lokacin da yajuyo yakalleta ba,sbd bai tabajin irin wannan dadin da sunanshi yyiba abakinta..............







*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:20] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITING JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*


```Wannan page din sadaukarwa gareki,kuma ke tadan ce,muna alfahari da ke kuma kinsan mi kikeyi,bakida hassada ni shaida ce,``` *Aunty fauzah🤝🤝....*


*45-50*



Saida suka dauki hanya sosae,sannan wayarshi ta fara ringing har sau ukku amma da mamaki bae daukaba da alama Aunty hanan ce saidae yyi tsoki.

Aka qara kira da sauri yadauka,cikin harshen turanci tare da girmamawa ya gaishe da ita,sannan yafadi mata yana hanya yanxu.

Daga can bangaren Mami tace"Hanan tacemin idan takira ka baka dauka,ko inada ikon sanin meye dalili?"

Yaya Rafeeq yace"Mami,diyarki nada matsala sosae,tana neman rainani ne"

Mami tace"Rafeeq kafasan wulaqanci baida dadi ko?"

Yace"wlhy Mami bbu maganar wulaqanci,Hanan batajin magana ahaka zan aureta"

Mami tace"komi kenan sae ka'iso,munyi magana,sbd abinda kakeyi yyi yawa"

Yace"Mami kinfison farin cikinta akan na danki?"

Mami tace"ba haka bane Rafeeq,ina bayan gsky ne,Allah yakawo ka lfy"

Ya'ansa da ameen sannan sukayi sallama.

Tini idanuwanshi sun canza launi sakamokon bacin rae,ji yyi yatsani Hanan sbd nema takeyi tatarwatsa mashi tinaninshi,amma zatasani ne.

Suna isa cikin garin kano,yajuyo yakalleta karo na biyu yace"wace unguwa ne?"

Zuhra tafadi mashi,ta kwance har suka isa kofar gidansu Zuhra.

Yaya Rafeeq yatausaya masu sakamokon irin gidan da suke rayuwa,qaramar katangace taqasa dukta zaizaye,idan kakai mata wani naushi tana iya rushewa,idan kamiqe tsaye zaka iya hango filin tsakar gidansu,wanda bbu ko siminti aciki,bazaka taba tinanin Zuhra a irin wannan enveronment din take rayuwa ba,sbd tsabar kyau da Allah yyi mata.

Tana qoqarin fiddo trolly dinta a boot sakamokon bude mata da yyi taci,sae ga malam Umar yadawo daga masallaci hannunshi dauke da carbi.

Da sauri Zuhra tadurkusa tana gaishe da ita,cikin fara'a tare da murnar ganinta ya'ansa.

Ji tayi andurqusa a kusa da ita,mursarshi da taji yana kwasar gaisuwa wurin Baba shiya tagane yaya Rafeeq ne,amma taba taba tinanin yaya Rafeeq zai iya durkusawa yagaishe da wani ba banda iyayenshi sae yanzu.

Cikin ladabi da biyayya yagaishe da Baba,ya'ansa yana mai jin dadi.

Baba yace"shine yayan Islam din ne?"

Zuhra dasauri tace"eh Baba shine"

Baba yace"ae baikamata katsaya awaje ba kashigo kasha ruwa mana"


Baiyi gardama ba yabi bayan Baba,Zuhra tabisu dauke da trolly dinta.

Mama tashifida mashi tabarma yazauna,sannan yagaishe da ita cikin ladabi,Mama ta'ansa cikin jin dadi tare da godia.

Baba yace"zo Zuhra anshi naira ishirin anso mashi ruwa mai sanyi,tinda bbu mai sanyi anan"

Yaya Rafeeq yace"a'ah Baba bbu komae,nagode"


Mama ce tagabatar mashi da fura wacce taji nono,agabanshi.

Yaya Rafeeq yabata mamaki sose ganin yasha furar bbu laifi sannan yatashi,tare da ajiye ma mama dame guda na yan dari biyar,sannan yyi masu sallama yafita.

Sunyi mashi godia tare da addu'a mai kyau,mama tace inbishi inqayi mashi godia.

Abin haushi sadda nafita yashiga cikin mota amma yaran unguwarsu duk sunbi sunzagaye motar tare da me ita da kallo,har wasu na fadin ga balarabe da karfi nasan yajisu.

Zuhra taqarasa kusada motar tace"yaya Rafeeq mungode,Allah yatsare hanya"

Yadago manyan idanuwanshi wanda yanzu sunkoma farare tas,sabanin dazu da ranshi yabaci suka canxa launi.

Yace"ameen Zuhra,bbu komae"sannan yatada motarshi yatafi.

Haryabace Zuhra na tsaye akofar gida tana tinanin wai dama yasan sunanta ko kuma yanzu dasu Mama suka fadi agabanshi.

Zuhra tagaji da tinaninta amma bata samo ansa ba dole tahaqura takoma gida.

Mama da Baba suka shiga murnar dawowar Zuhra,itama taji dadi tasamu iyayenta lfy.

Baba yace"ana karatu sosae dae ko Zuhra?"

Zuhra tace"eh Baba"

Mama tace"kuma anadae ganewa ko?"

Zuhra tace"ina ganewa sosae"

Mama da Baba sukace"Alhmdllh,Allah yabada sa'a,Allah kuma yatsare ku daga sharrin masu sharri"

Zuhra tace"ameen ya rabbi"

Bayan taci abinci tatashi tayi wanka sannan tahabar da sallah,Islam da Iman suka kirata suka gaisa suayi firarsu sannan sukayi sallama.


Yaya Rafeeq ya'isa gida,bayan yyi parking din motarshi agurin da aka tanada dan ajiye motoci,sannan yashiga porlour.

Porlour wanda yaji kayan alatu dana more rayuwa,kamar ba'asan zafin kudi ba,komae na porlour purple da white yyi kyau sosae,sae hoton yaya Rafeeq window size manne a bango,cikin wasu qananan kaya da alama acan England yyishi,sae kuma nasu Islam da Iman,wurin yyi kyau sosae.

Mami ce zaune aporlour tana karatun newspaper sanye da medical glass dinta.

Bayan sungaisa,Mami tashafa gashin kanshi tace"my son kaje kayi wanka sannan kaci abinci zamuyi magana zuwa anjima"

Rafeeq yashagwabe fuska kamar wani qaramin yaro yace"Mami badai akan Hanan bane ko?"

Mami tace"Rafeeq kakoyi tinanin yakamata ayi aurenku kaida Hanan sbd jiran ya isa haka"

Yace"Mami,tinda harkuka zabamin Hanan amatsayin mata,bazance maku a'ah ba,amma inason sai taqara hankali"

Mami tabata fuska sbd taga cin zarafin yyi yawa tace"kana nufin Hanan batada hankali ne,wae kodan kaga tanason ka ne shiyasa kake yimata haka,Hanan batada makusa,zaune da kyau tsaye da kyau"

Yaya Rafeeq tini idanuwanshi suncika da hawaye,daura kanshi bisa cinyar Mami,yashiga zubar da hawaye kamar mace"

Mami taji tausayin shi sosae sbd duk abinda Rafeeq yyima kuka awannan lokacin babbane,rabon da taga yazibar da hawaye hartamanta.

Mami tafara shafar gashin kanshi da hanninta na dama,sannan tashiga lallabarshi.

Mami tace"Rafeeq kayi haquri,amma yau daddyn ku yyimin maganar sa ranarka kai da Hanan"

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga idanuwanshi,yace"Mami kunfi damuwa da farin cikin Hanan fiye da nawa,sbd Hanan dan tana sona zata aureni nikuma bana sonta Mami"

Mami taci ajiyar zuciya sannan tasanyaya murya sbd yanada gaskiya shi anbata matashi ana neman gyarama wata.


Mami tace"ba haka bane,amma ka'iya tini yarinyar nan tintana yarinya take sonka,kuma sbd kae bata kulawa kowa,kayi haquri ka aureta zaka sota kamar yadda take sonka"


Taci gaba da cewa"nima inaso inga yaran da suka fito daga gareka Rafeeq,Hanan tana qaunarka zaku zauna lfy"

Bbu yadda ya'iya dole yyi shiru,yatafi part dinshi yashirya.

A school tinda Aunty hanan taji Rafeeq yatafi tare da Zuhra ranta yabaci hankalinta yatashi sosae,dan ita,kallo ma batason wata kalli Rafeeq bare kuma ace sunyi musayar lumfashi da wata ba ita ba,ji take bbu macen da kaita sonshi da kishinshi,akanshi bbu abinda bazata iya yiba sbd shi natane ita daya........





*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:21] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*


```A gsky nayi mamaki,wlhy ban ta6a tinanin wannan littafina yasamu kar6uwa kamar haka ba,masu kirana da masu yimin text,dama masu yimin magana a chat,nagode sosae da nuna kulawarku garen,i luv u all😘😘😘.....```



*50-55*



Yaya Rafeeq nashiga room dinshi,wanda yaji kayan more rayuwa sae kamshi dake tashi,komae neat bisa lafiyayen bed dinsa yazube zuciyar shi cike da tinani kala daban daban,wani 6angare na zuciyarshi yana tausayin rayuwar Zuhra ga kuma takaicin Hanan ya fara ruda mashi tinanin shi.

A kwance yake yyi lamo kamar me bacci,amma kuma ba baccin yake yiba,wayarshi dake kusa dashi tashiga ringing,yana dubawa yana sunan Hanan,yyi tsoki ya'ajiye wayar.

Saeda tasake kira karo na biyu sannan yyi tinanin yadauka yaji kiran mi takeyi mashi,saeda takusa yankewa sannan yadauka ba tare da yyi magana ba.


Daga dayan bangaren cikin fada take magana tace"wa yace kadauki wannan yar iskar yarinyar kayafi da ita?"

Ranshi yaqara baci fiye da da,sbd baisan dalilin dayasa duklokacin da Hanan tajefi Zuhra da wannan kalmar yake qara jin takaicinta ba.

Cikin zafin rai yake magana yace"ke wace irin marar tarbiyace?,aka koya maki sallama ba bare kuma gaishe da nagaba da ke ne?"

Cikin tsiwa tace"sae natambayo,kuma wlhy kana gab da jama yarinyar mutane bala'i"

Yaya Rafeeq yace"wlhy idan kika sake kika yima Zuhra wani abu,sai kinsani"

Hanan tace"saedai insani,wlhy indai akanka ne RAFEEQ"

Yace"magana ta dake taqarshe,duk ranar da kika sake kiran Zuhra da yar iska,zakiyi ladamar sanina,kuma kada nasake gani qazamin kiranki awayana"yyi tsoki yace jobless sannan yakashe wayar shi.

Ba qaramin takaici Hanan tashiga ba,wani bangare na zuciyarta tace kodae son yarinyar nan yake,afili tayi saurin cewa wlhy billahi RAFEEQ baka iyasa ba,kayi kadan kuma zakayi ladama.

Saekuma wani bangaren yace ya za'ayi kamar Dr. Rafeeq yaso wannan yarinyar?,saekuma tayi tinanin kawae da yarage mata hanya ne dan yana ganinta tare da qannanshi,amma shida ko qannanshi baya sakarma fuska mizai da wannan wawiyar,haka yita sake sakenta,amma bata yarda yanason Zuhra ba.


Tashi yyi yashiga bathroom yyi wanka sbd wani zafi daya taso masu dukda room din akwae a/c tana aiki.

Washe gari bayan Zuhra tayi wanka tashirya cikin wani material dinkin riga da siket mai zanen flower green tayi kyau sosae,Mama tace"tashirya taje tagaishe da Haj. Hadiza matar chairman,kafin lokacin tafiz yyi,Zuhra tafiddo hijabin milk tasaka tayima Mama sallama.

Baya Iman tagama exam dinta,Aunty Hanan tadauke saeda suka biya kaduna tadauko wasu takardunta sannan suka wuce Kano,bbu inda tayi parking sae gidansu,zuwa anjima sae ida kaisu gida.

Dama kuma ranar Mummy tadawo daga Cairo,Mummy taba zama school sosae saedai deputy provost shi yake gudanar da aiyikan cikin school din.


Bayan tayi parking aharabar gida suka fito,ma'aikata sae faman gaishe da ita suke amma ko kallon mutunci bbu atsakninsu,dama ita mutum ce wadda batason talaka,shiyasa lokuta da dama idan Mummy tagani tanayi maya fada,da anyi maya fada kuma sae kuka har tacema ba'a sonta tinda ba'ason abinda takeyi,dole Mummy talallabe ta tinda ita daya suka mallaka kamar rai.

Aporlour suka tarar da ita tana duba wasu takardu,Mummy taji dadin ganinsu sosae,bayan sungaishe da ita kamar yadda suka saba.

Mummy tace"amma Hanan kin kyauta min da kika kawomin su gida,ni da yarana amma sae nadade bangansu ba,ba kamar ke Islam"

Islam tayi murmushi tace"Mummy karatune yaboye ni ae"

Mummy tayi murmushi tace"ina fatan kunyi kokari a exams dinku,sbd wannan shekarar akwai provost award da zamu bayar"

Hanan tace"Mummy sunyi karatu sosae ae"

Mummy tace"wel,Allah yabada sa'a"

Suka ansa da ameen ya rabbi.

Hanan tatashi takoma kujerar da Mummy take tafara shagwaba wae yunwa takeji,Mummy tayi murmushi tace"wae wadda ake shirin yima aure itace batabar yimani shagwaba ba"

Su Islam da Iman sukayi dariya.

Hanan taqara shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace"Mummy ko nakira wayarshi baya dauka kuma bayason kulani"

Mummy tace"laifi kikayi mashi ko?"

Hanan tace"mummy bbu abinda fa nayi mashi"

Mummy tace"tou shikenan,zanyi bincike kuma zangano gsky"

Daddy ne yakira wayar mummy,bayan sungaisa yake tambyarta Hanan tadawo ko,mummy tace"ina tare da ita hadasu Islam da Iman"

Mummy taba Hanan wayar,bayan sungaisa Hanan tace"daddyna nayi fushi,shine kakira mummy baka kirani ba"

Daddy yace"am sorry nima inanan nakusa dawuwa"

Haka sukasha firarsu har saeda suka gaisa dasu Islam sannan sukayi sallama,suka yi wanka sannan sukaci abinci,da marece Hanan takaisu gida,Allah yasa har tagama zamanta Rafeeq baidawo ba.

Bayan sati biyu da dawowarsu gida,kullum basu da labari saena Zuhra dukda suna waya da ita,yanzu ko Mami tasan Zuhra sosae dukda bata taba ganinta ba amma tana ganinta ahoto cikin waya,taji yarinyar takwanta mata arae yadda taji yaranta suna labarinta tasan suna zaman mutunci sosae kuma sunshaqu da juna.

Islam tacema Mami gobe zasuje gidansu Zuhra,haka Mami tabasu kudi suje suyi shopping hadda Zuhra,komae guda ukku saka saya kuma iri daya saedae kala tabanbanta dayake kowa nada best colour dinshi,kuma sunsan kalar da takeso.

Washe gari suka shirya ado sukayi bana wasa ba,driver yakaisu,dama tafadi masu sunan unguwarsu,da suka isa suka kirata sae gata tafito,sunji dadin ganin junansu,sannan takaisu gida............





*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:21] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*



*I luv u all😘😘😘...*


*55- 60*



Islam da Iman sunyi mamakin muhallin da Zuhra take rayuwa sosae,sbd bazaka taba tinanin yarinya kyakykyawa irin Zuhra tana rayuwa anan ba,kuma sannan takama kanta a school karatunta tasa gaba.

Lokacin da sukazo Mama batanan tana gidan chairman,sae ita daya.

Dan qaramin gidane ginin kasa,bbu ko yabe,tare da qananan katangu,gidan daki biyu ne tal,shima ginin kasasae dan filin tsakar gida wanda bbu ko sitinti,a tsakar gida murhummu yake tasancewar bamu abinyin kitchen ko yar rumfar da zamu riqa sanwa kodan damina,sae ma kewayimmu wanda akiyi da langalanga bbu ko murfi,dakin mama sae na Babana,dakin mama nasaukesu,wanda bbu komae sae dan qaramin gado da karfe,da wata yar qaramar katifa,kujeru guda biyu wanda sun tsufa,sae wani tsohon carpet wanda mama tasamo gidan chairman.


Dama tinda sukace suna hanya,tasawo masu So6o da kunun aya a makwabtansu,dambun masara ne da mai da yaji mukayi,shi nazuba masu kuma sunci sosae sae santi sukeyi.

Suka bata kayan da Mami tace abata,Zuhra taji dadi sosae sbd acikin irin kayan su Iman suka sanyo nasu.

Suka shiga firarsu ta school,sbd baifi sati biyu sukoma school ba.

Suna cikin firarsu Mama tadawo gida,cikin girmamawa suka gaishe da ita,mama taji dadin ganin irin yaran da Zuhra take rayuwa da su,sbd tinda tagansu tasan natsatstsune,kuma sannan suna da tarbiya,dukda yanayin muhallin da suka iskesu baisa sunji qamarsu ba,shiyasa mama taji tana son yaran sosae.

Sae wajen qarfe 6pm sannan suka miqe zasu tafi,suna cikin sallama da mama,Baba yadawo dauke da huluna ahanninshi,Zuhra ta'ansa tare da yimashi sannu da zuwa.

Islam da Iman suka gaishe da shi cikin girmamawa,Mama tafada mashi cewa su Islam ne,Baba yayita sak masu albarka sannan suka fita.

Mama ce tarasa wane abu zata basu,sae tatina da wata kuka da bushashshiyar lu6ewar da aka kawo mata daga qauye,takira Zuhra tace gashi tabasu,sunyi godia sosae.

Zuhra tarakasu har kofar gida inda driver yyi parking,ji suke kamar karsu tafi sbd wani sonta da tausayinta,daqer sukayi sallama da juna suka shiga mota suka tafi.

Haka suka dawo gida cike da mamaki,koda sukaba Mami labarin rayuwar su Zuhra,Mami tatausaya masu sosae.


Yaya Rafeeq atsaye gaban mirror cikin shigar dogayen kaya,wata dakakkiyar shadda ce,tsadaddiya,ruwan toka sae shining take,yasaka huka da takalma bakake,yyi kyau sosae sae ni'imtatcen kanshinsa ke tashi.


Haka yafito porlour fuskarshi bbu walwala,Mami ce tasashi yaje yagaishe da Mummy yyima kuma daddy sannu da zuwa,yadawo daga Umara.

Mami nalura da yanayinshi sati biyu yadan rame,da alama yana cikin damuwa sosae,amma tasan bazai wuce akan saranar auren shi,kuma ita bbu yadda zatayi.


Yarar da Mami a kitchen tana hada coffee mate,tana ganinshi tayi murmushi tace"har kashirya kenan"tashafa fuskarshi tace my son kayi kyau.

Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"nagode Mami"

Mami tace"cikin kwanakin nan me ke damunka ne?,naga kadan rame"tana kallon cikin idanuwanshi yasan ansa takeson ji yanzu.

Yace"bbu komae Mami"

Mami tatausasa murya tace"kayi haquri,nasan maganar Hanan ce,nasan katakura kanka akan yi mana biyayya Rafeeq,muna matuqar farin ciki da Allah yabamu yaro mae biyayya kamar ka"

Yaya Rafeeq yyi murmushin karfin hali yace"bbu komae,Mami nayarda zan aureta amma ina buqatar dan wani lokaci"

Mami tace"naji,amma kana tinanin Alh.da iyayen Hanan zasu qara maka wani lokaci"

Yace"insha Allah bbu damuwa Mami,sae nadawo"

Mami tace"Allah yadawo dakai lfy,kagaishe min da Haj.fatima"

Bakar motace yashiga qirar corolla sabuwa fil,cikin isa da izza yake driving har ya'isa unguwarsu,unguwace ta masu kudin gaske.

Mai gadi yabude mashi katafaren gate yashiga,yyi parking din motarshi,yafito masu aiki suka shiga kawo gaisuwa shikuma yana ansa tare da basu yan nakashewa.

Kofar da zata sada shi da porlour yashiga,tare da sallama,bbu kowa porlour sae plasma dake manne a bango tanata faman aiki tare da karar a/c.

Bayan kamar minti ukku Mummy tafito daga bedroom dinta,tana ganinshi tayi murmushi tace"yau Rafeeq ne agidammu"

Yaya Rafeeq yyi murmushi,bayan sun zauna yagaishe da ita,cikin jin dadi ta'ansa.

Suka shiga hirarsu akan school tare irin award da za'aba students da irin decoration din da yakeso ayima dakin tarbar bakin.


Mummy tace"wae kwana biyu mi yahadaka da qanwar taka?nasan dae laifi ta'aikata"

Yaya Rafeeq yadan sosa kae sannan yace"bbu komae Mummy"

Mummy tayi murmushi irin nasu na manya tace"adai riqa haquri,Allah yadaidaita tsakanin ku"

Tatace tace bari infadima Alh.zuwanka,sannan tafita.

Bayan kamar minti goma saeta tare da Daddy,bayan sungaisa da daddy,mummy tatashi tafita.

Sukadan yi hirarsu sannan daddy yyi murmushi yace"ya zance sa biki kuma?"

Rafeeq yadan sosae qeya yyi shiru tare da sunkuyar da kai kasa.

Daddy yyi murmushi karo na biyu yace"my son ko akwai wata magana ne,ko miye kafadi mani,yadda nadauki Hanan haka nadauke ka har cikin zuciyata wlhy"

Tabbas yanada magana kuma yanajin kunya kamar yadda daddy yadauke bai dace ace yakawo mani uzuri ba amma dole ne yafadi kuma yanemi alfarma.

Yaya Rafeeq yace"dama daddy ina neman alfarma adan qaramin lokaci sbd wata hidima data taso mani"

Daddy yyi murmushi yace"dama akan wannan ne,ae bbu komae,kuma aduk lokacin da kke buqatar wani abu,kasanar da ni plz"

Yaya Rafeeq yyi godia sosae.

Hanan ce tashigo sanye da wanibmatsatstsen jeans da yar body hug takamata sosae,gashinta bbu ko hula tadaure shi da ribom a guri daya tamaida jelar baya,hannunta dauke da qaramin tray da lemon kwali da ruwan roba asama sae glass cups.

Cikin sallama tashigo tadaura tray din abisa centre table,sannan tazauna bisa kujerar da daddy yake zaune tayi mashi sannu da hutawa.

Daddy ya'ansa cikin sakin fuska sannan yace"Hanan bakiga yayanki yazo ba?"

Hanan tayi murmushi tasa tafin hannunta tarufe fuskarta tace"yaya Rafeeq sannu da zuwa"

Daddy yace"ae kema kinsan baki kyauta,ni bari naje inyi wanka tafin kugaisa"

Yatashi yafita.

Yana fita Hanan tadawo kujerar da ke kusa da Rafeeq tazauna,tana kollonshi amma

Please Login or Register in order to submit comment