Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci sannan sukabar part dinta,part din yaya Rafeeq suka tafi.

Yaya Rafeeq yakamo hannun Zuhra tare da zaunarda ita bisa gado,kanshi yadaura bisa cinyarta kafin yadago fuskarshi yana kallon cikin idanuwanta,fuskar yashafa yana murmushi.

Yace"kema insha Allah nan bada jimawaba zaki samu"...............







*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*



_DEDICATED TO_ *SARAH ADIYYA,*```Allah yabar zumunci🤝🤝🤝....```



*160-165*



Zuhra tasa tafin hannunta tarufe fuskarta alamar taji kunya.

Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"oh haryanzu anajin kunyana kenan"

Zuhra dae batace mashi komae ba.

Labarin cikin Aunty hanan yazagaye family dinsu gaba daya,murna ba'a magana wurin Mami da Mummy.

Bayan sati biyu yaya Rafeeq yyima kowace cikinsu kyautar motar qirar ANACONDER,driver kekai Zuhra school kafin ta'iya,kuma duk ranar weekend yaya Rafeeq ne yake koya mata driven.

Hanan bata cika fitaba yaya Rafeeq yahanata yahanata fita sbd rainon ciki.

Duk yadda yaya Rafeeq yakeqin akawo mashi masu aiki agida,saedai Mami taturo masu Asabe mai aiki,sbd Zuhra tana zuwa school yaya Rafeeq kuma yana zuwa wajen aikinsa,dole akawo wadda zatayi masu aikace2.

Zuhra datariga tasan halinshi narashin son abincin masu aiki saedae tana dawowa daga school tadaura mashi abinci kafin yadawo.


Hanan tanata rainon cikinta har cikin yatsufa,Mami tana zuwa dubata sosae.


Gsky Zuhra tayi dacen iyayen miji da dangin miji basu nuna mata banbanci tsakaninta da Hanan ko kadan kodan sunsan halin Dr. Rafeeq oho,hadama bai bada fuskaba.


Tin lokacin da Aunty Hanan tasamu ciki yaya Rafeeq yana kula da ita sosae,Zuhra najin dadin hakan sbd itama matarshi ce.

Akullum addu'arshi Allah yabashi zuri'a tagari,Allah yaba Zuhra itama.

Haka itama Zuhra duk kulawar da tadace yanabata sosae,fiye da canbaya dan yakwantar mata da hankali.


Ana cikin haka su Zuhra suka fara exams karatu take sosae kuma yaya Rafeeq yana qara yimata explain din inda bata ganeba.


Wata ranar monday lokacin Zuhra tatafi school yaya Rafeeq kuma yaje zaria,Hanan ce zaune porlour bisa kujera tana kallon cikinta ya'isa haihuwa.

Ringing din wayarta tajiyo cikin bedroom dinta,takwada ma Asabe kira,da sauri ta'iso tana Aunty gani tare da durkusawa agabanta.

Hanan takalleta sama da qasa cikin masifa tace"sae yanzu kikaga damar zuwa kenan"

Asabe tasanyaya murya tare da kwantar da kai tace"kiyi haquri Aunty wlhy banjiba ne"

Hanan da daka mata tsawa tace"shut ur mouth up,wawiya phone dina zaki daukomin bisa side drower dina"

Asabe tatashi jikina rawa tare da bata haquri tatafi takawo mata wayar sannan takoma kitchen.

Hanan tana dubu missed calls taga sunan Mummy,fara'a tabayyana afuskarta tareda dialing call dinta.


Bugu ukku Mummy tadauka,Hanan tashagwabe fuskar kamar tana ganinta tafara yimata shagwaba.

Mummy tace"ya kikejin jikin naki?"

Hanan tace"Mummy lfy qlau,saedai wani lokacin inajin motsi aciki,amma yaya Rafeeq yacemin bbu komae"

Mummy tace"eh bbu matsala,Allah yaraba lfy,dama jiya ni da Alh.muke magana nace mashi zaki dawo gida kihaihu yace sae kinyarda da hakan"


Hanan tace"ni dae Mummy nafiso nazauna tare da mijina gsky"

Mummy tace"tou ae shikenan,ya Rafeeq din da Zuhra?"


Hanan tashagwabe tace"nifa Mummy banason kina tambayana wannan yarinya,nafison idan kika tambayeni mijina shikenan"

Mummy tace"Hanan ni kike fadima haka?,lalle kinkyauta sae anjima"


Mummy takashe wayarta.

Hanan ko kuka tashiga yi kamar qaramar yarinya har yaya Rafeeq yadawo.

Saeda yashiga part Zuhra yagama abinda yake sannan yatafi part din Hanan domin duba lafiyarta.

Haka yatar da ita cikin kuka,hankalinshi yatashi da sauri yaqaraso inda take zaune.


Hannunshi yadaura bisa cikinta yafara shafawa yace"lfy Hanan ko baby nane yake wahalar da ke?"


Hanan takada kai alamar a'ah.

Yace"kinga Hanan banason irin wannan kuka,kinji abinda Mami tafada maki data dubaki,ba'aso kuna shiga cikin damuwa"


Hanan tace"Mummy ce tayi fushi da ni yaya Rafeeq"

Yace"aikuwa baki kyautaba,tinda kikaga Mummy tayi fushi wani babban laifi kika aikata mata..................







*Miss j🙋🏻😘*
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*


```Wannan page din sadaukarwa ne gareku all members in``` *🌈KANUWA WRITERS ASSOCIATION🤝,*```Allah qara baseera tare da zaqin hannu...```

_Allah yabar zuminci ameen thumma ameen🙏🏻🙏🏻🙏🏻....._



*165-170*



Hanan tashare hawayenta tace"yayana kakirata da layinka plz saeka bata haquri"

Yaya Rafeeq yace"mai laifi daban mai bada haquri daban,kedai ki kiarata da kanki mana"

Hanan tashagwabe fuska tace"haba yayana kada kayimin haka mana"

Yaya Rafeeq yace"kinga wasa nake maki,let me try to call her"


Yafara qoqarin neman layin Mummy,bugu ukku tadauka tare da sallama.

Yaya Rafeeq ne yagaisheta cikin girmamawa,Mummy ta'ansa cikin jin dadi.

Yaya Rafeeq yace"Mummy dama Hanan ce keson yin magana dake"


Mummy tace"hmm,Hanan manyan gari kenan"


Yaya Rafeeq yace"Mummy kiyi haquri plz,tagane kuskurenta ae"

Mammy tace"a'ah bbu komae Rafeeq yariga da yawuce insha Allah"

Yaya Rafeeq yace"muna godia Mummy,Allah yaqara yawan rae,ga Hanan din"tare da miqama Hanan wayar.

Hanan ta'anshi wayar tagaishe da Mummy sannan taqara bata haquri,Mummy tasaki rae sosae sukayi fira da Mummy,sannan Mummy ke fada mata nextweek zatayi tafiya zuwa Germany,one week zasuyi sudawo,tare da yimata fatan sauka lfy.

Sukasha firarsu har sukayi sallama takashe wayar.

Fuskarta dauke da jin dadi take kallon kyakykyawar fuskarsa tace"yayana nagode sosae"

Yaya Rafeeq yace"idan kika sake aikatama Mummyna laifi,bazan sake shiga cikiba"

Hanan tayi murmushi tare da rungumeshi tace"i'll not repeat it again"

Wata ranar sunday lokacin Zuhra sungama exams da kwana biyu,cikin dare Hanan tatashi da ciwon nakuda bbu wanda yasani acikinsu,sbd yaya Rafeeq apart dinta yakwana.

Ita daya adaki taita faman ihunta bbu wanda yasani acikinsu.

Saeda ciwon marar yadan lafa sannan tasamu tanemi layin yaya Rafeeq acikin rashin sa'a wayar akashe take gashi kuma batada number din Zuhra.

Tana cikin wannan tinanin ciwon yadawo sabo,Hanan batasan lokacin da tayi wurgi da wayar hannunta ba,taci gaba da ihu.

Hana cikin wannan yanayin har asuba tayi lokacin Hanan tagalabaita sosae.


Yaya Rafeeq ne bayan sunyi sallah yazo part dinta da niyyar yatasheta daga bacci,hankalin yatashi sosae tare da ruduwa ganin halin da Hanan take ciki tariga data galabaita.

Da sauri yadauketa yafita da ita harabar gidan wurin da aka tanada domin ajiye motoci,sae yanzu yatina da bbu key ahannunshi.

Hankalinshi atashe yasamu ya'iya part din Zuhra,tana ganinshi dauke da Hanan,tasan bbu lfy itama hankalin nata yatashi.


Yyi qarfin hali yace"dauko mani key din mota"sannan yanufi hanyar fita,Zuhra tasaka hibinta na sallah tare da daukar key din mota dinta tabishi abaya.

Yashigar da ita back sit Zuhra matashiga sannan yashiga yatada motar suka fita da guje.

Suna zuwa asibiti,emergency aka ansheta,har gari yafara wayewa bbu haihuwa.

Cikinsu bbu wanda hankalinshi yakwanta gashi basuzo da wayarsu ba bare akira su Mami.

Saeda Nurse tafito tace su'ajiye kayan baby akusa dasu sannan suka tina d basuzo da komae ba.

Yaya Rafeeq yace"Zuhra natafi nadauko kayan kuma zankira su Mami nasarda dasu"

Zuhra tace"tou yaya Allah yatsare hanya"

Yace"ameen,akwai abinda zantaho maki da shi ne?"

Cikin muryar tausayawa Zuhra tace"bbu komae yaya,amma kadawo da sauri,ina fatan tahaihu kafin kadawo"

Yace"Allah yasa my dear"tare da yimata murmushi sannan yatafi.

Bayan 15mins saega Mami da Islam da Iman tare da Aunty jamila sunzo,Zuhra tagaishe dasu cikin kulawa kamar yadda tasaba,suka ansa cikin jin dadi,tare da tambayar mai jiki,Zuhra ta'ansa da da sauki Mami.


Bayan 10mins da zuwansu Mami,yaya Rafeeq yadawo hannunshi dauke da tani qaramin jaka,kayan baby ne aciki sae kuma kayan Hanan kala biyu.

Yana cikin gaishe da Mami tareda Aunty jamila,Nurse tafito tace akawo kayan baby tare da gaisheda Mami.

Mami tace"Nurse me muka samu?"

Nurse tace"ranki yadade baby boy ne"

Kowa bakinshi bude dan murna hada Zuhra baiwar Allah.

Bayan anshirya baby Nurse takawo masushi,Mami ce tafara daukarshi tace"masha Allah lalle nayi miji"


Mami tamiqama Rafeeq baby,yanaganinshi wani dadi da son yaron baby yashigar mashi rae.

Yana gama mashi addu'a yamiqama Zuhra baby.

Zuhra fuskarta dauke da jin dadi,baby yana kama sosae da mahaifinsa wato yaya Rafeeq,Zuhra tayi murmushi tace"masha Allah,Allah yaraya mana shi"

Suka ansa da Ameen.

Bayan angama shirya mai jego,sannan suka shiga cikin room din.

Kowa yyi mata ya jiki,Hanan ta'ansa tana kallon fuskar yaya Rafeeq tana murmushi.

Basu wani dade a asibitinba aka sallamesu kasan cewar Hanan tahaihu lfy.

Mami ce tasanar da Mummy haihuwar Hanan da abinda aka samu,taji ddi sosae ji take kamar tayi tsuntsuwa tajita agida Nigeria.

Mami taba Hanan wayar suka gaisa tare da yimata sannu,sannan tasanar da ita ranar wednesday zasu dawo.

Su Hanan sunkoma gida lfy,tin amita baby yake hannun Zuhra harsuka iso gida.

Ahaka dare yyi Zuhra ji take dama abarmata baby takwana da shi.

Mami da Iman suka tafi gida akabar Islam takwana a part din Hanan.

Bayan 11pm Zuhra hartakwanta yaya Rafeeq yashigo hannunshi dauke da baby,Zuhra tana ganinshi da sauri tatashi ta'isa inda yake.

Yaya Rafeeq yamiqa matashi yace"dama zuwa yyi yaimaki saed safe"

Zuhra tayi murmushi tace"amma nagode maka"

Takoma bakin gado tazauna fuskarta na kallon baby tana murmushi.

Yaya Rafeeq ne yazauna kusa da ita,kissing din kumstunta yyi sannan yyi kissing din goshin baby.

Yace"Zuhra ina sonki kamar yadda nakeson raina,zaki zauna dani har abada?"

Zuhra tadago dara daren idanuwanta tana kallonshi tace"wannan wane irin magana ne,bana fatar abinda zairabani da kai har abada mijina,kuma ina godia da soyayyarka gareni"

Yyi murmushi yace"i'm so glad my wife"baby ya'ansa yadaura bisa bed dinta,fuskarta yatallabo yafara tsotsar lips dinta.

Kukan baby ne yadawo da ita cikin duniyar da suka lula,da sauri Zuhra tadaukeshi tana lallabashi.

Amma baby yaqi yyi shiru,Zuhra tace"yayana ina tinanin yunwa yakeji fa"

Yaya Rafeeq yace"taso mutafi mukaishi sae muyi masu sallama mudawo mukwanta"tare da kashe mata ido daya...........








*Miss j🙋🏻😘*
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*



```Ina mai bada haquri akan jina shiru da kukayi kwana biyu,amma insha Allah nesa tazo kusa,nagode da nuna kulawarku gareni🙏🏻...```



*170-175*



Zuhra tayi murmushi tare da tashi tsaye,hijabi ce tasaka ajiinta sbd rigar dake jikinta,ziciyarta cike da tinani tare da fargabar zuwa muhallin Aunty hanan sbd talura tin cikin mota take harararta.

Tin lokacin da Dr. Rafeeq yafita da baby,Hanan taketa faman zazzaga ruwan bala'i dan tasan part din Zuhra zaikai mata baby,Islam tanajinta saedae batace mata komae ba.

Haka yaya Rafeeq da Zuhra suka tarar da Hanan tanata faman bambami kamar wadda tasha wani abu.


Tanajin sallamarsu tayi shiru taqara daure fuska kamar wadda taga wani abu.

Ko sallamarsu bata ansaba saedae Islam dake zaune gefen gado ta'ansa.


Yaya Rafeeq ya'isa inda Hanan take yace"yunwa yakeji muka maidoshi"

Islam da Zuhra suna ganin ikon Allah,shi uwar gayyarma bai lura da halin da Hanan take ciki ba.

Hanan tasa hannu ta'anshi baby tana qunquni,baiji abinda tafadiba.


Yaya Rafeeq yakalleta adaqile yace"lfy kikeyin wani surutai kamar marar hankali?"

Hanan taqara fusata tace"nace banason aqara kaimin baby wancan baqin part din nata"

Yaya Rafeeq yadaure fuska yace"kee,wa kike fadima wannan maganar cike da raini?"

Hanan tace"yaya Rafeeq gsky kana shiga haqina,nidai banaso ana kaimin yaro can"

Yaya Rafeeq yagyara tsayuwa yace"shut up nonsense,ke kin'isa kusamin doka Hanan,ko kinmanta koni waye agurinki?"

Hanan tace"Dr. Rafeeq abinda kikeyimin yyi yawa,kuma nace banaso ana kaimin babyna part din Zuhra,idan taji haishi gobe inga nata mana"

Yaya Rafeeq yadaka mata tsawa saeda baby yafashe da sabon kuka,Islam ko jikinta yafara rawa kamar mazari,hatta Zuhra saida tarazana,ita kanta Hanan saeda tashiga taitayinta.


Cikin bacin rai yake magana yace"kifadamin baby nan idan yanada wani uba bayan ni Hanan"

Hanan bakinta na rawa tace"kaine mahaifinsa"sbd taga tana niyyar 6allo august,kuma tasan halinshi sarai.

Yaci gaba da cewa kuma da kike maganar idan taji haushi itama gobe kiga nata,ae kema ba dan Allah yafi sonki bane yabaki,kuma itama insha Allah zata samu,kuma baby tin lokacin da aka haifeshi nayi mashi huduba da Umar Farouq(sunan mahaifin Zuhra)kuma duk lokacin da Zuhra tazo daukar shi kika hanata abakin aurenki"

Jin kalaman yaya Rafeeq ba Hanan ba hatta Zuhra da Islam saeda hankalinsu yatashi.

Islam cikin zuciyarta tace ai shine daidai ke.

Hanan ko fashewa tayi da kuka tana fadin yaya Rafeeq katsaneni kafison Zuhra akaina.


Afusace yafice yabar bedroom din ranshi a jagule idanuwanshi sunyi jajir.

Zuhra tamara mashi baya zuciyarta ciki da tashin hankali sbd wannan bala'i ita yaya Rafeeq yajawo mawa.


Baby wanda yanzu yaci sunan Umar Farouq sae kuka yake qwalawa amma Hanan batabi takanshiba sae Islam ce tadaukeshi tafara lallashinshi yyi shiru sannan takoma wurin Aunty hanan tafara bata haquri,daqer tasamu Hanan ta'anshi Farouq.

Hanan tadade batayi bacci ba sbd tsabar takaici,sannan tasamu bacci yadauketa.


Suna shigowa parlour yaya Rafeeq yazauna bisa daya daga cikin kujerun parlour ranshi bbu dadi.

Zuhra tafita kitchen tadauko coconut juice wanda yaji madarar peak data hada bayan magrib yyi sanyi takawo mashi.

Da hannunta tabashi abaki yadan sha bbu laifi sannan ta'ajiye glass cup din.

Zuhra tazauna abisan carpet kusa da kafafunshi fuskarta cike da damuwa.

Yaya Rafeeq yasauko bisa carpet din shima yazauna,yahada hannayenta da nashi yana kallon cikin idanuwanta.

Yaya Rafeeq yasanyaya murya yace"Zuhra kiyi haquri akan maganar Hanan,bbu abinda yake damunta sae mugun kishi,insha Allah kema Allah zai baki".

Zuhra tayi sanyayyar ajiyar zuciya tace"yaya Rafeeq,maganar Aunty hanan bata 6atamin rai ba,amma kamar hukuncin daka yanke akanta yyi girma"

Yaya Rafeeq yace"Zuhra idan ba wannan hukuncin nayanke mataba,bazata bar yimiki wulaqanci akan babyn ba"

Zuhra tace"yaya Rafeeq ina sonka fiye da yadda nakeson kaina,banason ganina cikin farin ciki"

Yaya Rafeeq yace"Zuhra kinada hankali kuma kinsan abinda yakamata,ina sonki fiye da komae"

Zuhra tayi murmushi tace"yayana ina roqonka wani alfarma"

Yyi murmushi yace"ina sauraronki my only"

Zuhra tace"yayana dan Allah inaso kuzauna lfy tsakaninka da Aunty hanan,amma idan na6ata maka kayafemin"


Yaya Rafeeq yace"Zuhra,Hanan batason zaman lfy,amma zanyi qoqarin yin hakan insha Allah"

Zuhra tace"nagode sosae yayana"


Yace"bbu komae"yakama hannunta yace taso muje bacci nakeji sosae,tare da kashe mata ido guda.


Washe gari tinda safe Hanan,tashiga hada kayanta wai ita gida zata tafi.

Bayan tagama hada kayan tashiga kiran layin Mummy,cikin sa'a bugu ukku tadauka.

Hanan tafashe da sabon kuka tace"Mummy kiyima driver waya yazo yadaukeni"

Mummy tasaka salati tace"lfy dae Hanan?,mike faruwa?,me zakiyi agida?"

Hanan tace"Mummy,yaya Rafeeq ne yatsane ni nida baby na,wai kuma zai sakeni sbd matarshi Zuhra"

Mummy tace"subhanallahi,Hana banda rashin mutuncin da kike aikatamashi yanzu kuma had sharri"


Hanan tafashe da sabon kuka tace"wlhy Mummy da gaske nake ba sharri bane"

Mummy tace"insha Allah yau zamu dawo,zamuzo gidan amma kada kisa damuwa aranki kinga yanzu bakida lfy sosae"


Dahaka Mummy tayita lallashinta har tasamu tahaqura da zuwa gidan,Islam batasan abinda akeyiba bare kuma Zuhra da yaya Rafeeq.............






*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*



*175-180*



Bayan Hanan tagama waya da Mummy saitaji ana knocking,da kamar kada taje tabude dan tayi tinanin yaya Rafeeq ne.


Badan ranta yasoba tanufi porlour,tana bude kofar taga wata mata wadda bazata wuce 28yrs ba kuma kamar tasan fuskar matar.

Hanan tabude mata suka zauna porlour,suka gaisa tare da tambayar Hanan ya qarfin jiki?.

Hanan tadan yamutsa fuska tace"jiki da sauki"

Matar tayi murmushi tace"ni sunana Aysha Muhd,tare da ni ne aka anshi haihuwarki a Twins International Hospital,(asibitin Mami)Haj.(Mami) ce ta'umarce ni da nariqa zuwa inayima baby wanka safe da yamma"

Sae yanzu Hanan tatina da inda tasan fuskar matar.

Hanan tace"ok nagane"

Suna cikin magana da 6ter Aysha,Islam tafito daga room din da take kwana,jikinta sanye cikin riga da wando na bacci,da alama yanzu tatashi daga bacci.

Islam tana ganin 6ter Aysha taganeta,cikin fara'a tagaishe da su.

Islam tace"Aunty Aysha ya aiki?"

6ter Aysha tayi murmushi tace"lfy Alhmdllh"

Hanan tadan yamutsa fuska tace"Islam kaita bedroom dina zatayima baby wanka"

Islam tace"tou,Aunty Aysha taso mutafi"

Islam takaita har inda baby yake,sannan tafiddo duk abinda yake buqata wajen wankan baby,sannan tatsaya suna labari har aka fara yin wankan,ana farawa baby yafara tsala kuka,dama Hanan kamar jira take taji kukanshi cikin hanzari tashigo cikin bedroom din.

Islam da 6ter Aysha basusan Hanan tashigo ba,saedai sukaji tace"kinga malama kada kisamishi soap acikin ido mata"

Islam tayi murmushi tamayarda abin wasa tace"Aunty hanan,itada aikinta ne"

6ter Aysha tace"hmm,baza'a samu matsalaba insha Allah"

Hanan dae batace dasu komae ba banda tsoki da tayi sannan tafita.

Islam takalli 6ter,tace"dan Allah Aunty kiyi haquri da abinda yafaru"

Aunty Aysha tayi murmushi tace"bbu komae Islam,bbu abinda Haj.maryam zata nema agurina tarasa,tayimin komae tinda tadaukeni aiki a asibitinta,tanemi alfarmar da nariqa zuwa inayima baby wanka har kwana bakwai dukda ba aikina bane,amma sbd mutuncin da take dashi agaremu bama ni daya ba,shiyasa nazo,kuma wannan baby ai nima nawane"

Islam tayi murmushin jindadin kalamanta tace"so muna godia"

Saida tashirya ma baby sannan tayi masu sallama tatafi.

Hanan tana zaune porlour ko breakfast da mai aiki tayimata magana akan yana bisa dinning table,haryanzu bata ciba kawae tana jiran zuwan Mummy.

Bayan Islam tayi wanka tashirya yaya Rafeeq yakira awaya yace takawo mashi baby yana part dinshi.

Islam ta'ansa mashi da tana zuwa.

Islam tashiga bedroom din Aunty hanan tare da sallama.

Aunty hanan ta'ansa dauke take da baby tana kallon kyakykyawar fuskarshi tare da shafa gashin kanshi mai taushi.

Hanan tana ganin Islam tayi murmushi tace"har kinshirya"

Islam taqaraso inda take zaune tare da zama gefen gadon tace"eh nashirya Aunty hanan sannu da hutawa"

Hanan tace"ywwa Islam,ya kke"

Islam tayi murmushi zuciyarta cike da tinanin ya zasu kwashe da Aunty hanan idan tace yayane ya'aikota?.

Islam tace"lfy qlau,ya baby?"

Aunty hanan tamiqa mata baby tare da cewa "lfy qlau"

Islam tace"zuwa anjima Iman zata shigo tare da su Aunty jamila"

Aunty hanan tayi murmushi tace"Allah yakaimu lfy Islam"

Islam tace"Aunty,dama yaya Rafeeq ne yace nakai mashi baby"

Tini Hanan tatsuke fuska kamar ba ita bace take murmushi yanzu,bacin rae yabayyana afuskarta,hawaye suka fara zubowa daga cikin idanuwanta.

Islam hankalinta yatashi tafaraba Aunty hanan haquri.

Hanan tashare hawayen fuskarta tare da masu qoqarin zuwa tace"haba Islam,wulaqancin da yaya Rafeeq yake yimin yyi yawa,yanzu har bai'iya zuwa yaga yanakwana ni da wannan baby saidai yace akai mashi shi,nimafa iyayena suna sona"

Islam tace"kiyi haquri kinsan yanayin yaya Rafeeq"

Aunty hanan tace"6acin ranshi kawae yasani,kuma shine zai sakamin sunan mahaifin wata yar iska,tou ni sunan mahaifina nasakama baby"


Wayar Islam dake hannunta tashiga ruri,da sauri tadauka bakinta na rawa tace"hlo yaya Rafee...."


Tin kafin ta'ida fadin abinda take fadi yakatseta yace"uban me kike jira ne?"

Yadda taji yana maganar tasan ranshi a6ace yake,batasan lokacin data tashi tsaye ba,kafin tayi magana har yakashe wayarshi.

Islam tasa hannu zata anshi baby,amma Hanan tadaukeshi,tace"baza'a kaimin baby part din wancan munafukarba fa"


Islam tazaro ido tace"dan Allah Aunty hanan kirufamin asiri wlhy part dinshi yace nakai masa shi"


Hanan bata yardaba saeda takai Islam har bakin qofar part dinshi taga Islam tashiga sannan tadawo cikin part dinta tazauna parlour zuciyarta cike da takaici.............






*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*

.
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSICIATION🤝*


```Gaisuwa ta musamman tare da fatan alkairi,``` *Badiya Sada Mashi*```Allah ya'ida nufi tare da angon naki💃...```


*180-185*



Babban burin shine Mummy tazo gidan domin asan yadda za'ayi,dan itadae bazata yadda ba amanna ma baby dinta sunan uban wata shegiya.

Jikinta har 6ari yake sabon tsabar tsoro tashiga parlour dinshi tare da sallama amma da alama bbu kowa aciki.

Tayi sallama har sau ukku bbu wanda ya'ansa,cikin zuciyarta tace yauni nashiga tara ni Islam kardae ace yaya Rafeeq har yafusata akan dan jimawar da nayi bankawo baby ba.

Jikinta bbu qwari tajuya tafito,kamar almara taga Aunty Hanan abakin qofa kamar wata mai gadi.

Tin kafin tayi magana Hanan tace"yawwa haryama ganin baby ko?"

Islam fuskarta cike da damuwa sbd tasan akwai rigima wurin Hanan idan tafada mata yaya Rafeeq baya cikin part dinshi.

Hanan takawo hannu zata anshi Farouq,Islam tadan ja dabaya tace"Aunty hanan dan Allah kiyi haquri wlhy baya cikin part dinshi".

Hanan tayamutsa fuska tace"kamar ya baya part dinshi,ni miye hadina da shine?"

Islam tace"nasan yana nufin nakai mashi baby a part din Zuhra"

Hanan cikin qanqanan lokaci ta6ata fuska tace"wlhy Dr. Rafeeq bai isaba,sbd wannan baby nawane kuma bazaki kai manishi baqin part din can ba"

Ae take Islam tafara zubar da hawaye sbd batasan irin bala'in da Aunty hanan zata jawo mataba wurin yaya Rafeeq.

Aunty hanan tace"Islam lfy?,me akayi maki?"

Islam bata'iya yimata magana ba saedae tashiga cikin bedroom din da aka ware mata.

Hanan tabi bayanta zuciyarta cike da tinani tare da son sanin dalilin dayasa Islam kuka cikin qaramin lokaci.

Bisa lafiyayyen bed dinta tafada taci gaba da kuka.

Hanan bayan takwantar da baby agefe tamatso kusada Islam tafara lalla6arta tare da tambayar abinda takeyima kuka.

Cikin muryar kuka Islam tace"Aunty hanan,kinfi kowa sanin halin yaya Rafeeq yanzu yana zuwa zaifara zagina akan rashin kai mashi baby da nayi,ni gsky gida zan koma bazan iya zama agidannan ba Aunty"

Hanan tace"haba Islam,yanzu wannan kikeyima kuka,aidae nasan bazai dakekiba"

Islam juyawa tayi taci gaba da kuka,tare da qudirin itadae yau da Mami tazo zata bita sutafi saedae idan Iman tazauna,amma idan tana gidannan jininta zai iya hawa sbd ganin tashin hankali.

Yaya Rafeeq yanacan yaqule sbd takaicin Islam wae tayi jin kirin kawo mashi baby dinsa.

Banda Zuhra da taketa faman lallabarshi da tini yabiyo har part din Hanan ya'isketa.

Ita Zuhra tafahimci cewar Auny hanan ita tahana Islam kawo baby part dinta amma batason yaya Rafeeq yagane hakan sbd akwai matsala sosae.

Zuhra tace"yayana kayi haquri yanzu zakaga tazo indae Islam ce"

Rafeeq yace"banda raini mezai hanata zuwa tindazu da nakirata awaya,kuma gashi nakira wayar bata daukaba"

Cikin kissa Zuhra takauda zancen tare da cewa"yawwa yayana,Mama zatazo barka yau"

Yaya Rafeeq yyi murmushi tare da kallon kyakykyawar fuskarta yace"amma naji dadi sosae,Allah yakawota lfy"


Zuhra tayi murmushi tace"ameen ya rabbi"

Bayan kamar minti goma yaya Rafeeq yatashi tsaye zaifita daga cikin room din.

Da sauri Zuhra tasha gabanshi tace"yaya Rafeeq lfy?,ina kuma zaka tafi yanzu?"

Yaya Rafeeq yace"zantafi part din waccen yarinyar zanji idan itace tahana Islam kawomin yarona a'inda nake,idan kuma Islam dince bataga damaba zangani"

Zuhra kwantar da murya tace"yaya Rafeeq bai kamata kayi tinanin haba,may be anayima baby wanka ne,naga wadda takeyi mashi wanka tazo"

Yaya Rafeeq yasaukar da ajiyar zuciya yace"har kinsa nacanza tinanina sbd kalamanki masu sanyi da dadi"

Zuhra tayi murmushi tace"godia nake ranka shi dade"

Yaya Rafeeq yace"kin wuce hakan my wife,well bari inje nayi wanka kafin Mama tazo,lokacin da zangama shiryawa anshiryama baby,wae wane suna ne za'a riqa kiranshi da shi ne my wife?"

Zuhra tayi murmushi tace"yayana ae Aunty hanan ne zata fada mana"

Yace"ae kema naki ne my beloved wife,tinda bazaki fadana ba,saimu riqa kiranshi da SULTAN"


Zuhra taji ddi sosae,saeda tayu baquwa sannan yatafi part dinshi yarabu da ita.


Zuhra tayi ajiyar zuciya bayan fitar shi tare da godema Allah,sbd da batace anayima Sultan wanka ba da yau Hanan tabani itada Islam.

Wata course mate dinta ce a B.U.K tazo barka da yake unguwarsu daya da ita,Zuhra taji dadi amma tana tinanin yadda zata kai Khairat part din Hanan tayi barka............






*Miss j*🙋😘
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*


*185-190*



*B*ayan sungama gaisawa da Khairat,suka dan ta6a labarin skul,suna cikin labarin ne,saiga Mummy tashigo part din Zuhra tare da sallama,fuskarta dauke da fara'a,cikin jin dadi Zuhra suka ansa tare da yimata sannu da zuwa.

Mummy kenan mahaifiyar Hanan albasa batayi halin ruwa ba,mutuniyar kirki da son mutane.

Cikin girmamawa Zuhra tagaishe da Mummy,Mummy ta'ansa tare da tambayar mai jego da baby,Zuhra tace"suna lfy Mummy"

Mummy tace"nima ban jima da dawowa qasar ba,nashigo ganin ku"

Haka sukadan ta6a fira kafin sutafi part din Hanan.

Hanan tana ganin Mummy tafara murna tare da shagwa6a,amma koda talura da Zuhra sae tadaure fuska kamar bata ta6a dariya ba,haka Khairat tayi mata barka daqer ta'iya ansawa sannan suka fita tare da Zuhra.

Fitarsu keda wuya Mummy tahau yima Hanan fada akan irin yadda takeyima Zuhra da baquwa.

Hanan tafara kuka wae ita ba'a qaunarta kowa Zuhra yakeso ba'a qaunarta,Islam na ganin haka tatashi tafita tatafi part din Zuhra dama tanason zuwa suyi labarin yaushe gamo.


Mummy tace"yawwa yanzu inaso kifadamin dalilin ki nayin yaji"

Hanan tana kuka takwashe labarin abinda yahadata da yaya Rafeeq tafada ma Mummy hada sunan mahaifin Zuhra dayasama baby dinta

Hanan tana gama fadima Mummy,Mummy tayi tsoki tace"ashe ke haryanxu bakida hankali Hanan?,anfadi maki anayima mutum gorin haihuwa,kuma idan yasama baby sunan da yaga dama ae nashine,dan haka ni banason yawo rigima kingani nan banason tashin hankali,yanzu ina Rafeeq din yake?"

Hanan cikin muryar kuka tace"bansan inda yakeba Mummy,duk yau baizo yaga yamuka kwana ba fa"

Mummy tace"ya za'ai yazo,tinda kina 6ata masa rae,kuma kina niyyar mayar da shi sae yadda kikeso,kinsan Rafeeq tin yana yaro man of policy ne yanada tsatstsauran ra'ayi"

Hanan taci gaba da kukan takaici tana ladamar sanar da Mummy halin da take ciki dama Daddy ne tafadimawa.

Sultan take hannun Mummy tafara kuka,Mummy tace"kinga bashi yasha,yafara jin yunwa"

Hanan cikin muryar kuka tace"ni fa wlhy Mummy baby dinnan yacika yawan jin yunwa wlhy madara zan riqa bashi yanasha"

Afusace Mummy take magana tace"ahir dinki kada nasake jin wannan maganar mar hankali yaron da kika haifa shine zaki qi shayarwa kiriqa bashi madara"

Hanan da taji Mummy bbu sauki batasan lokacin dana anshi Sultan tafara bashi nono yanasha ba amma cikin zuciyarta badan ranta yaso ba,sbd Khubra ta ta6a fadamata cewa breast feeding shikesa mace tana saurin tsufa ko kuma mijinta yafara neman aura ita kuma yarainata tare da wulaqanta ta.

Mummy taci gaba da yimata fada saida Sultan yasha yaqoshi yyi bacci sannan Mummy ta'ansheshi tare da umartar ta da taje takirawo mata Rafeeq.

Badan ranta yaso ba tanufi part dinshi fuskarta dagani kasan tasha kuka tayi jajir abu ga farar fata.

Bbu ko sallama tashiga part dinshi har cikin bedroom tatarar da shi lokacin yyi wanka yana saka kaya,yyi kyau sosae yau kadai da bata ganshi ba.

Yana kallonta tacikin dressing mirror shiyasa bai juyo yakalleta ba,ita kuma yar ikon batayi mashi magana sbd haushinshi takeji.

Bayan yagama saka kaya yafeshe jikinshi da tsadaddun turaruka masu

Please Login or Register in order to submit comment