Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

time idan kuna bukatar taimako ku sanar Dani.....kunji

Mubarak ne yayi wannan batu yayin da yake mika mana card Nasa..

*HAKA MUKA ZAMANTO ABOKAI CIKIN KANKANIN LOKACI*
sannan muka shaku sosai,haka ya shigo cikin tawagar tamu....
Amma ko sunfi shakuwa da *qudsy* domin koda yaushe saita yi masa magana ta WhatsApp....
Sannan tayi hanyar da aka sakashi cikin department group namu....

Kullum tare muke da juna,wajen shan coffee,labary....resting place dadai sauran wajajen....

Dukkan abubuwan dake faruwa babu wanda ke da sanin cewa wannan shakuwar tamu na bakantawa *may ah* rai

Tuni muka manta da ita.......haka Mubarak ma yayi mata rata....
Sannan wasu lokutan idan tana naimansa sai ta naimesa ta wayan mu domin mu hadasu.....


Bayan kwanaki kalilan y'an ajinsu *Mubarak* suka soma hada shagulgula sannan kuma kowace shagalin sai sun gayyace mu...domin mune close friend na Mubarak....


Haka muka hallauci shagulgula iri daban daban tare kuma da Mubarak din.....
Haka ma yau muna tare wajen shagali inda na soma jin barci tun 9:00 saina wuce na kyale su qudsy a wajen......



Karasawa nayi gida 9:30 inda ban tsaya ko inaba sai kan katifa ta...
Nan na fadin kan shunfudar na soma mishari.......



*TWO DAYS LATER*


farkawa nayi daga barci,6:59 inda nayi saurin mikewa na nufi bayi.....sannan na Watsa ruwa
nan nafito...cikin kankanin lokaci na shirya sannan na taka izuwa falo..
Inda na tadda abba na zaune yana karanta *news paper*

Gaidashi nayi sai yace dani......

"Imraan,yana ganka cikin rushing?

"Chem 101 muke da shi yaushiyasa nake saurin.....
Haka na basa ansa shiko yace dani

"Kennan bazamu karya kummallo tare ba....?

"Eh dad,ina da poket money zanyi using......na karya a school din..

"Ok wish you the best......


Nanfa na taka izuwa bakin titi inda na tsaya....inda na tsaya din kuma takasance wurine da mutane ke tsayawa domin hawa daidaita.....

Tsayen nake sai ga wasu samari biyu sun zo wajen da muke tsayen.....
Tsayawa gefen namu sukayi,bayan wasu yan dakiku sainaga sun zaro waya daga aljuhunsu sannan suka soma duba wani abu ciki wayan....
Suna duba cikin wayan hade da nuna ni da yatsa suna cewa

"shine....wallahi shine fa ku duba kugani.......
Nan kaina ta dagule na kasa sanin meke faruwa...


Haka duk gurin dana ratsa saina ga wasu na nunani suna "shine,gashinan.....

Hakama cikin school din sukai ta nuna ni
Niko bansan meye silar faruwar haka ba.....

Duk inda na jeni saina ga kowa ya tashi ya wuce......






*GAJERAN LABARI,YAKAMATA KUSAN DA HAKA*
*DAGANI ABDUL ALHAJI MUSA*
*MASU BADA SHAWARA,KO KUMA GYARA KOFA A BUDE TAKE*
.

*KU TUNTUNBE WANNAN LAYIN*.

.

*🌹🌸SOYAYYAH CE🌸🌹*
*MINI SERIES*







*SOYAYYAH CE*©®2020
*MINI SERIES*
*✍STRONG PEN WRITERS ASSO.🖋🖊*
_aiki da nazari domin farin cikin makaranta(readers)_




*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIN*

MEENAH SERIES
RAEES AND NAJMAH
AWANNI CESA'IN
WAYE SILA

*AND NOW*

*🌹🌸SOYAYYAH CE🌸🌹*


*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Wattpad*
@Abdul10k
*WhatsApp no:*
@09077974042
*Facebook acc*
Abdul Alhaji musa
*YouTube chennal*
Rahama TV



https://www.facebook.com/groups/282175586024233/



*DEDICATED TO MY FANZ ONLY,LOVE YOU ALL*






🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*FINAL EPISODE 3*




Zaune nake a rest-benci Ina jiran coffee....wacce na cinye akalla mintuna talatin ina jira but babu labari zuwan coffee din....
Nan saina yi niyar tafiya,kwatsam saiga *Hussein* yazo shi cikin rushing........

Zuwan sa keda wuya yace dani.....
"I'm sorry nayi keeping naka waiting ko,dan Allah kayi hakuri....."

Muna kan wannan maganar saiga *qudsy* ta taho itama ta zauna kusa dani.....jikin ta duk amace...
Juyawa nayi na dube ta sannan na tambaye ta "lahiya kuwa....yana ga jikin ki duk babu kwari.?"

Dajin wannan tambayan saita juya ta kalli cikin idanun *Hussein.....*
Inda nako gano cewar da kwai wani abun da suke boyewa....

Sake tambayar ta nayi karo na biyu.....nan saita ce dani.

"Lafiya *imraan* babu matsala...... komi normal......

Nan saita anshi waya ta, ta duba sannan bayan ta duba saita dago kai ta kalli *Hussein* sannan tace dani.......

"Au ashe ma ka kwan biyu baka hau online ba...."

"Eh wallahi na kwan biyu,aiko kinsan karatu bazai had'a hanya da chatting ba.......
Amma mai yasaka kikai wannan tambayan...."

Ansar dana bata kenan had'e kuma da tambaya.....


*BANGAREN GIDAN MU KO*

Bayan tafiya ta da mintuna talatin abbana shima ya shirya ya wuce gurin aiki.......
Yaudai ba kamar kullum ba....abban nawa ya kasance sai 4:00 yake dawowa daga gun aiki a kullum but yau saiya dawo kafin wannan lokacin.....


Inda wannan zuwan nasa ta matukar razana *ummah* ta domin bata tsammaci zuwan saba.....

Shigo gidan yayi jikin sa amace....yana taku a hankali....
Ganin sa a wannan halin da tayi sai ta ruga izuwa wajen sai.....sannan tad'an dafeshi.

Janshi tayi a hankali ta Zaunar dashi inda ta soma tambayan sa cewar.......


"Mai gida lafiya kuwa,?....yanaga ka dawo yau da wuri....?
Haka ummah ta tambaye sa cikin muryar tsoro...

Mika mata wani farar takarda yayi wanda ya shigo gidan dashi a hannu.....
Karba tayi daga hannun nasa inda ta duba.........babu abin da idanuwan ta suka soma gani illa..wasu rubutun dake nuna *Kora* ga mijin nata....


Nan fa idanuwan ta suka cike da kwalla....
Ta kasa cewa komi....

'Dago kai mijin nata yayi sannan yace da ita

"Sun wulakantani,sun cimin mutunci....hatta d'an uwan ki *mamood* yana daga cikin...."

Dajin wannan batun sai tayi saurin sake tambayar sa cewar...

"Bangane inda ka dusa ba..mai gida,mai ke faruwa....suwa suka wulakantaka sannan kuma akan meye wai....?"

Dajin wannan zabgazabgan tambayoyin.........saiya zaro wayar sa...dake cikin aljihu.
Ya bude sannan ya mika mata .......ansa tayi daga hannu nasa.
Saita zuba ido domin ganin meye yake shirin nuna mata.....ta cikin wannan wayar.


Wani abun ta gani wacce yasaka idanuwan ta suka cike da kwalla..ta kuma kasa cewa komi...
Nan jikin ta ya soma rawa kaman zata fadi kasa.


*BANGAREN GIDAN SU MUBARAK*


Kwance yake da ruwan cikin sa a falo,yana ta dannadannen laptop....abinsa sai ga kanwarsa ta tako izuwa wajen sa...
Zama tayi gefen sa sannan tayi masa magana hade da Nuna masa abinda ta gani a *Facebook* Cewa tayi...

"Yahya amma kuwa kana hawa *Facebook* , kaga ire iren abubuwan da mutane ke posting a shafin ka kuwa?."

Tambayar datai masa kennan shiko ya bata ansar cewa...

"Uhmm maizai hana...aiko kowa da abinda yayi masa a duniya...wani yafison ya yad'a abunda bashi da sani akai..........so don't worry,kinji."

Hakan ya bata ansa itako ta sake cewa dashi...

"Toh yahya idan kai bai dameka ba wannan din kuma fa.....ya kake tunanin zaiji sannan wani irin hali zai kasance ciki a yanzun....

Dajin haka sai ya yunkura daga kwanciyar da yake ya kalli photo data ke nuna masa....

Furucin *kut* yayi nanfa ya mike tsaye ya kuma taka ya fice daga gidan.....



*CIKIN UNIVERSITY*

fitowa mukayi daga labary inda nake rataye da jaka ta a wuya......
Taku muke a hankali muna mai fira cikin raha..... nanfa saiga wasu yan Mata biyu sun karaso gun mu...
Suka kuma shige gabana suka tsaya..sai daya daga cikin su tace....

"Uhmmm abin mamaki *imraan* shin daya bai isheka bane da kake kokarin kara na biyu...."

Dajin wannan batu sai kaina ya daure domin bansan inda take nufi ba......
Nan na tambaye ta cewar.......

"Lafiya baiwar Allah make faruwa..."

Nanfa dayannan ta bani ansar cewa

"Toh ai kafimu sanin ko meya faru....kasanfaa dubun kane ya cika kuma allah yayi walkiya mungan idanun ka.....sannan ka sani wallahi saika wulakan ta a duniya...."

Ji kawai nayi an wanka mata mari sannan na jiyo muryar meshi na cewa....

"Kinyi kad'an....ballagazar yarinya.....toh bari kiji ke zaki wula kanta bawai *imraan* ..
*qudsy* ce tayi wannan batu.......sannan itace wanda wanka mata marin nan.

Nan da nan ko sai naga tarun student sun kewaye mu suna kallon fad'ar.....wasu hadda dauka a waya.......
Cacan baki sukai tayi inda takai ta kawo har *Hussein* ya shige fadan...

Niko tsaye nake bayan su na kasa cewa komi domin bamma san meye suke fad'an akai ba.....


*40 MINUTES LATER*


zaune muke cikin motan *Hussein* inda nake sake tambayan su cewar...

"Wai shin meke faruwa ne........abokai,nafa kasa gane ko meye kye shirin faruwa dani...da 'faari a *boss stop* naga wasu na nuna ni sannan suna maganganu a kaina.....secondly wajen *classmate* namu naje sun tashi sun kiyaleni ni kadai........
Thirdly gashi kuma yanzu an tareni da maganganun banza.....what is happen".

Shiru *Hussein* da *qudsy* sukayi sannan suka dubi juna...

Nan na sake da cewa......

"Nasan kunsan meke faruwa,dan haka karkuyi kokarin boyemin komi".....

Dajin haka ko sai *Hussein* yayi ajiyar zuci sannan ya daugo laptop nasa dake ajiye gefena.....ya kuma kunna ta...

Shiru mukayi dukkan mu uku nadan wasu lokuta ta sanadiyar muna jiran ta gama loading...

Nan ya bude sannan ya shige *social media* kai tsaye ya shiga *department* group namu yayi kasa da hirar mutane ya kaini wajen wani *photos*

Nan na anshi laptop din daga hannun sa,ba tare da na tambaye shi komi ba na soma dubawa...
Firar mutane iri iri nake ta gani...niko banyi kasa a gwiwa ba na tsaya karan tawa....

Nan sai nayi arba da wani photo wacce yasa duk gashin dake jikina suka mike tsaye...
Idanuwa na suka cike da kwalla sannan zuciya ta, ta soma bugawa da sauri.....

Ba komai bane na gani illa hotona ni da *Mubarak* zaune waje daya wacce wannan hoton an dauke shine ba tare da sanin mu......
Abinda wannan wanda yayi posting din ya fad'a akan hoton shine...

"Shin kunsa ko waye wannan,..........nace dai kunsan *imraan* sabon d'alibi a wannan makaratar......
Uhmmm,abin kunya ya tafka babba........gaskiya banyi zaton haka zai kasance ba....
Bari na faiyace muku zancen *imraan* da *Mubarak* allah ya toni asirin su....
Sun kasance sunyi *auren jensi* watanin baya da suka wuce....suna kuma cin gashin kansu,amma cikin wannan kwanakin sai allah ya toni asirin su, ta hanyar Baiyana wata hoto......nasu.


Da ganin haka sai naji kamar an soka min mashi a kirjina.....
Banko tsaya a nan ba,duk da cewar ina zubar da kwalla.........saina sake duba wani posting din wacce naga still hoton mune lokacin da mukaje *night party* na graduate nasu....

Meshi yace......

"Naga hakan da idanuna.....wallahi na gansu tare a rungume da juna........"

Nanfa nasan.........da akwai masu karya iri iri a doron kasa.....tunda nake ban taba sanin haka zata faruba....... amma sai gashi yau ta faru akan kaina....

Nan na soma ganin comment d'in mutane.....iri daban daban

Wasu na Allah tsine....wasu kuma na cen daman halinsa kenan.....
Wasu ko harda d'ura asher.

Nan nake inata karanta comments din......
Saina soma ganin comment na abokan *Mubarak* wacce suke daura laifin a kaina......cewar su wai nayi hakanne domin na bata masa suna....

Nan nake inata duba group by group.....bayan na kammala sai idanuna suka sake cikowa da kwalla.......

Mika masa nayi sannan na dauki jakata na rataya a wuya.......banko cedasu komi ba na sauka daga motar inda bai wuce dakiku talatin da tafiya taba saiga *Mubarak* yazo shima ya shige motor.......


Shigar sa ya tambaya cewar

"Ina *imraan* .......sannan ina fatan yana cikin koshin lahiya......

"Eh yana lafiya,amma matsaloli taimai yawa......kasan hayin *yanar gizo* takan zaga ko ina a fadin duniya......nidai fatana shine yan gidan nasu su gane gaskiya yake fadi musu.....idan ya kaiga sun gano zancen.....
Domin bazan iya jurar ganin sa cikin wannan hali ba....
*qudsy* ce tayi wannan batu inda *Hussein* yace ita

"Gaskiya ya kamata muyi wani abu akan wannan zancen.......wannan fa *kagene* sannan kuma kwata kwata baya effecting na *Mubarak* .......illa shi kadai abin ya Dama...."

Dajin haka sai *Mubarak* yayi sukum ya kasa cewa komi domin baisan tayi ba.....


*BAYAN NA FICE DAGA CIKIN MAKARANTAR*

Na tsaya a wajen da muke hawa.....adaidaita
Nan nake tsaye......naci kusan minti talatin ina ta tsayar da *keke napep* but idan sun tsaya suka kalli fuskata sai suyi tsaki su wuce....

Haka yasa na yanke shawarar takawa da kafa izuwa gidan namu wacce ya kasance *drop uku* daga wannan makarantar.

Haka nake ta tafiya ina kuma tunano maganganun mutanen nan har na karasa gida....
Inda na jeni gidan daf da sallar *magariba* tarar da ummah tawa da abba zaune sunyi sukum suna jirar zuwa na.....

Da ganin yanayin da suka zauna a tsakar gidan ko nasan labarin ya riske su.......

Nan na tsaya guri daya kem bayan mun hada ido hudu da umma.....


*AL'AMARIN MUBARAK KUWA*



komawa gidan nasu yayi jikin sa a sanyaye yana mai taku a hankali......
Ummar sa hango sa tayi saita tashi taje gurin sa....
Cewa tayi dashi....

"Mubarak make faruwa.....yanaga jikin ka babu kwari.......
Kaida kace wancen zancen bata dame kaba......yanaga kuma kamar anyi maka wani abun....
Haka ummar tasa ta furta yayin da take rike da kafadar sa.


*Uhmmmm Rayuwa kenan.....gaskiya ganin ire-iren wannan abubuwan a *whatsApp* ko *Facebook* a yad'a bata yiba....domin ta sanadiyar yad'a wannan hoton rayuwata ta shige tsaka mai wuya.....bangaren Mubarak ko sabida alzikin da suke dashi babu mai tunkarar su da wannan zancen sannan yan family sa sun goyi bayan sa....sun kuma tsaya tsayin daka akan zancen*



"Mubarak bawa umman tasa labarin komi yayi......akan yadda abin take cimin tuho a kwarya sannan ya sake cewa

"ummah hanya dayace zamubi mu sharewa *imraan* hawaye.....

Dajin haka tace dashi...

"Uhmmm wacce hanyace wannan sannan taya zamu zartar Dashi....


"Inaso nayi aure cikin sati mai zuwa....domin hakan zata tabbatar wa duniya cewar babu alaka tsakanina da *imraan* .....babu alakar komi tsakanin mu"





😥😢
*imraan* haka umma ta kira sunana cikin muryar kuka inda dayin wannan furucin sai naga *Eysha* ta fito daga cikin daki........
Nanfa wata zazzafar kwalla ta zubomin nan na soma zubar kwallar babu fashi.....

Zuwa da sauri sukayi su biyun suka rungume ni....inda mahaifina ko yake zaune ko motsawa bai yiba.....

Nan ummah ta soma cewa

"Meya faru da kaine haka d'an nan........
Tayi wannan furucin ne yayin da take zabga kuka...

*Eysha* cewa tayi dani.

"Imraan da fatan komin ka na tafiya daidai.......
Amma ya kayi haka *imraan* meyasa kayi wannan abu.

Juyawa na kalli cikin idanun *Eysha* sannan nace da ita....

"Nayi zaton kece zakifi fahintar halin da nake ciki.....
Domin kullum atare muke...... *Eysha*
Nayi zaton zaki iya tantance abubuwan da zan iya aiwatarwa da wacce bazan iya ba *Eysha* .........
Wannan tambayar taki ta tambatar mini da cewar kema kina daga cikin wayan da suke zargina da wannan halin Eysha.

Dajin haka sai kwalla ta tsinkewa ummah tare da *Eysha* sukai ta kuka......niko banyi shiru ba na cigaba da cewa.

"Allah shiyasan Mai gaskiya cikin duniyar nan.....sannan shiyasan abin boye dana sarari.........Allah yasan gaskiya nake fada muku........babu alaka tsakanina da wancen mutumin.....wacce ta wuce na abota.


"Fad'ar haka saukine da ita *imraan* ........... amma kwakwalan mutane Bazasu iyya daukan hakan ba,idan har suka kalli wannan hoton da idanun hikima......"
*Eysha* ce tayi wannan zance yayin da take nunamin wani sabon photo.....wacce bansan yadda akayi ta samu ba....

Hoton ya kasance marne nake jikin *Mubarak* sannan kuma a kwance......babu ko kaya jikin mu illa barkon dake zube kugun mu.....barci muke dukkannin mu biyu......kuma muna rike da juna domin har filo nayi da kirjin shi........

Da ganin wannan hotan ko bansan lokacin da jiri ya dibe ni na fadi kasa somemme ba.......
Farkawa nayi karfe 8:00shap inda na tadda umma zaune a gefena......

Tashi danayi sai muka sake rungume juna na soma cewa.....

"Wallahi umma ban aikata komi ba......bansan lokacin da aka dauki wannan hoton ba....wallahi sharrine wannan,wasune suka shirya......umma ki yadda dani"

Ina kan furta haka sai na jiyo muryar *Eysha* na cewa....

"Don't worry my dear....musan baka aikata komi ba....
Sannan bazaka iyya aika ta hakan ba,domin munsan kada tsoron *allahu subuhanawu wata'ala* so karka dami kankan komi zai dawo daidai....
Komai zai gushe kamar ba'a yiba"

Da ganin umma da Eysha sun goyi bayana sai naji dan dama dama cikin raina sannan na amince musu na daina zubar kwallar.....amma ko na manta ban tambaye su abbana ba har suka wuce...




Ajemin abinci sukai gefe na sannan suka wuce....niko na kasa cin abinci ta sanadiyar natuno cewar banyi magana da abba na ba.......

Haka washe gari na tashi.....inda na wuce dakin abban nawa kai tsaye.....

Tadda shi nayi zaune inda na tabbatar dacewa kwana yayi a zaunen...
Tsunkuyawa nayi gefen sa na gaishe shi baki na uku amma bai ansa ba...

Nan na mike na ce dashi....

"Abba nasan ka d'auke ni a matsayin mai laifi......wajen ubangiji subuhanahu wata'ala,
Abba ko ka kimin magana ta shekaru dari bazan taba daina kiran ka da abba na ba domin kai ka kawoni duniya....
Abba akan turbar gaskiya nake sannan zan cigaba da zama akai........ko da zan kasance ni kadai...babu mai goyamin baya..


Nanfa na juya na fice daga dakin......na nufi kofa.


*FITA NAYI DAGA GIDAN*

Banko hada ido da umma ba.....fitar tawa keda wuya sai ummah ta shige dakina inda ta tadda abincin dare a jibge banko saka hannu naba...
Diba tayi sannan tayi waje dasu........



Niko Takawa nake da kafa domin nasan ko na tsaya *boss stop* babu adaidaitar dazata dauke ni...
Haka nake ta takawa sai nayi karo da wasu yan samari biyu...

Sun kasance y'an anguwan mune su....shiyasa sukai tamin din lokacin da zan fito domin su tare ni.....

Wabce jakar dake hannu na sukayi sannan suka zazzagar da littattafai na cikin ruwan kwata....hade kuma da zabgamin tafi dan nayi yunkurin tsaida su.......

Muna kan hakan ko sai wata bakar mota tayi fakin a gefen mu...inda wasu samarin biyu suka fito ta ciki da zabga zabgan Bel......

suka hau kan wayencen da duka suka ko fikarfin su...... Shiyasa suka ruga a guje...suka bar wujen...

Bayan sun gudun sai naga wata farar mace mai suffar matan manya ta fito ta cikin motar...
Tace taho mu ajeka *school* din....

Amimce mata nayi domin bani da zabin daya wuce na shige motar.....
Bayan munyi nisa ga tafiyar sai tace dani

"sunana *hajiya rayya* nasan baka san niba but ni nasan ka....
Ta dalilin wani posting da akayi a group namu a WhatsApp.....

Nan tayimin nuni da hannun ta kan mai jan motar tace Dani.....

"Wannan mijina ne.......dayan kuma kanina...
Nima na taba shigewa irin wannan halin da kake ciki....
Amma saidai tawar bata kai naka kunci ba....domin hada hotona aikai dana jarirai aka ce ina satar yara......
Haka mutane sukai ta karyayyaki akan labarin harta kai ta kawo na sunduma y'an sanda ciki.....zancen....
Sannan nayi nasarar kamo wanda yayi wannan aika aikar...
Amma kai *imraan* mai ya hanaka sanarwa yan sanda?"

"Just bansan yadda zan yiba.....abbana da kansa shima bai bani goyan baya ba......
Shine kawai na bar komi a hakar sannan kuma a hannun Allah...."
Haka na bata ansa itako ta sake cewa....

"Amma dai banyi laifi badai kam,idan nasa kanina yaayi bincike akai......domin banajin dadin ganin abinda ya furu dani ya faru da wani........



Amince mata nayi sannan na naimi da su sauke ni domin mun karasa school din.....


*HAKA RAYUWATA TA KASANCE KULLUM SAI AN TAUZARTA MINI SANNAN BANI DA FARIN CIKI IDAN NA KOMA GIDA ......DOMIN ABBANA NA FUSHI DANI....AKAN LAIFIN DA BAN AIKATA BA*


Duk kwanakin nan hudu da aka dibe ban hada ido da *Mubarak* sannan ban sake jin labarin sa ba.....
Kullum tare muke da *Eysha* da kuma *Hussein*
Sannan sune kadai suka goyi bayana suka kuma tsaya bangare na.....

Ban taba zatan da akwai wani abu da zata raba muba....domin ganin yadda suka damu dani ko kansu bazasuyi wa haka ba.....

Nanfa na gane rael diffenation of friendship.........
Tsayawa tare dakai a duk lokacin da kake da bukatar wani kusa dakai....
Sannan su goya maka baya inda kana da bukatar haka....


Duk da cewar afkuwar wannan zancen takai sati daya....but har yanxu idan ka leka WhatsApp ko Facebook zaka zaci yau aka jiyo labarin.......sabida yadda mutane ke maimaita maganan....

Zuwa mukai gidan su *qudsy* domin ta naimi muje mata ziyara.....
Asheko birthday nata take ita kadai shiyasa ta naimi mukai mata ziyara.....domin mu tayata murna..

Mun gane hakan ne bayan munshige gidan........inda muka tadda ita da umanta zaune.....
Nanfa muka zauna hira bayan mun tayata yanka *cake* ....inda muke kan wannan hirar sai ga mahaifin *qudsy* ya shigo gidan

Nan ya naimi dana bar gidan sannan kada kuma na sake shiga rayuwar y'ar sa.....
Cikin bacin rai yake wannan batu sannan kuma yayi furucin cewar duk wanda ya tunkare ni.....saina tarwasa masa rayuwa...


Gaskiya *qudsy* bata ji dadin faruwar haka ba shiyasa ta kasa rikewa tafadawa abban nata cewa


"Abban kafa bar hanya ......wannan ba hujja bane dan kaga wani abu a social media kayi aiki dashi.....

Zabga mata mari yayi sannan yace da ita....

"Qudsy idan nina haihe ki.... Toh ki fita hanyar wannan la'anennen.....

Dajin wannan batun da abban qudsy yayi saina fice daga gidan cikin sauri banko saurari Hussein ba.......


Haka na fice daga rayuwar su......wato Hussein da kuma qudsy......domin ko sun kirani a waya bana d'agawa sannan bana musu reply idan sun turamin sako ta WhatsApp....

Haka na koma rayuwa ta irin ta da......tare da *Eysha* kadai....
Itace ta rage gare ni sannan me debemin kewa.....


A kullum saina shige dakin abbana na gaishe shi but hallau baya ansawa....niko abin na tabamin zuciya.........
Cuz about sati guda da d'oriya baice dani kala ba....



*BANGAREN MUBARAK*

Shirya komi yayi na auren nasa ba tare da ya sanar da *mayah* ba
Duk da cewar ita zai aura......
Yayi hakan ne saboda yayi mata bazata....

Indako ya shirya bazatar suka wuce gidan su *mayah* tare da ummar sa da kuma kanwarsa........

Shigewa gidan sukayi domin suyi mata bazata sai suka tadda *mayah* na waya da kawarta inda take cewa.....

"Gaskiya *zee* kin iyya bada shawara........ kinga yadda *imraan* ya zamanto tamkar mujiya cikin al'umma......
Hmmm aiko bakisan meye ya faru ba........lokacin da kika bani maganin barcin nan a *night party*
Dana saka musu ko karo daya suka zunduma barcin mutuwa.....
Najasu na nakuma kasa saida na biya wasu gayu suka taimakamin.....

........Oh wow iko kinsan inda na saka baki cikin maganar da tuni *Mubarak* ya gano shiri nane....
But yanzun dana cire kaina saina zamanto babu mai zargina......

bushewa tayi da dariya hade kuma da waiwayawa baya.....
Nan ta juya inda tayi ido hudu da *Mubarak* da sauran familin sa a tsaye bayan ta.....

Daganin suko Wayar dake hannun ta ya fadi......sannan ta kasa cewa komi.........




*Komawa gida nayi* inda na wuce dakina kai tsaye ba tare da na tsaya ko ina ba........
Da shigana dakin na soma kuka kamar idona zata zube....ina nai furucin cewa...

" Allah mai nayi.....Allah wacce laifi nayi....allah nasan kana saurarona ,yah rabbi ka cireni kicin wannan hali...........da karfin izzar ka....



*MUBARAK*
TSAYEN YAKE yana kallon cikin idanun *mayah*
Nanfa saita soma cewa
"Dan Allah Mubarak ka gafurce ni....banyi haka dan na tauzar taka ba......
nayi hakanne domin na sami gurbin zama cikin zuciyar ka.....
Umma ki fada mishi........sister sanar dashi yayi hakuri...

Birgijewa tayi tana ta furucin haka kamar wata mahaukaciya........babu kuma mai yimata magana...

Cigaba tayi da cewa....

"wallahi *soyayyace* soyayyar kace tasaka Mubarak.......
Umman kice mishi *soyayyace* silar faruwar haka....

Furta hakan take yayin da take zubar kwalla kuma tana kokarin taba jikin *Mubarak*
Inda ya tureta ta fadi kasa tare kuma da kayakin dake hannun *Mubarak* ta zube.....

Kwancen take a kasa inda tayi ido hudu da katin gaiyatar auren su.......

*MAYAH* _wed_ *MUBARAK* haka ko ta gani jikin katin sannan ta duba date.....sai taga jumma'a mai zuwa ne ai....... but gashi komai ya ta'bar'bare......


*KWANCE NAKE A DAKINA*
inda na zaro waya ta na soma duba comment a Facebook............
Still bakaken maganganu nake ta gani.....nan sai idanuwa na suka sake cikewa da kwalla.....
Sake tuno maganganun da abban *qudsy* yayi min sai naji kwalla ta zobomin.....

Ina kan wannan kukan sai na yanke shawaran goge Facebook da kuma WhatsApp daga wayata ko tad'an sa naji dama dama cikin raina.......

Bayan na goge nakuma jefar da wayar gefe guda sai ga ummata ta shigo da shayyi kofi daya a hannun.....

Dafani tayi bayan taga kwalla cike cikin idanuwa na sai tace dani......
"Zama cikin kad'aici bazata magance maka komi ba.....
Nasan bakajin dadin abinda ke faruwa tsakanin ka da mahaifin ka.......
Insha Allah zan magance komi kaji.....
Yanzu tashi kaje wajen gidan su *Eysha* ko kwad'an yi firar acen kaga yanzufa 7:00pm ne amma ka wani kwanta.......


Daji haka saina yunkura na wuce izuwa gidan nasu... inda da shigana gidan na jiyosu suna tattaunawa ita da umman ta kancewar......

..........Ni take so... Gaskiya ni ya cencenta ta aura,itadai nakwanta mata a rai"

Hakan ta furta inda nayi gajeriyar murmushi......sannan nayi niyar shiga dakin but sainajiyo muryar abban ta na mata fadar cewa......

"Amma ko ba'ki da tunani.....mutumin da mutane ke tsanan sa, shine zaki kaunace shi......
Nima idabadan za'ace banda mutunci ba da tuni na tsiyaye kaina daga gidan nasu......
Toh bari kiji wallahi zumunci mu ta abota ta ishemu.....sannan kuma bazamu kuma wani ba.

Nan nake nakasa motsawa ina mai kallon su daga nesa....
saina sake ji ya soma sako mahaifina cikin zance yana kuma alakanta shi da zargin da ake mini......
Cewar sa shine.........

"Aiko tun wuri nasan da walakin gwaro a miya domin da aikin.....mahaifin nasa bai taka kara ya karya ba... Amma suke sheka ayar su babu mai ganin asirinsu.....ashe da d'an nasa yake fakewa su ci kudin manyan gari......

Dajin haka nayi furucin......

"No........
Cikin ihu...na furta hakan yayin da nake zubar kwalla....ina mai ja da haha....

Dukkan ninsu uku suka juya idonsu zuwa kaina.....
Inda na soma cewa.....

"Wannan bah halin mahaifina bane......khawu
Kawu abbana ba haka halinsa yake ba.....

Nan na juya na fice a guje inda na tarar da motar *Mubarak* a fake kofar gidan namu....

Umman sa da kuma kanwarsa sune suka naimi da ya kawo su gidan mu domin su tattauna da iyaye na akan zancen.....

kin amincewa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment