Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amman kamar wani yaro ka kasa gaya mata kuma ka kasa zuwa gidansu ka gaya mata?gaskiya ka canza tsari ka fi kowa sanin yadda banason ɓacin ranka ko kaɗan,don Allah ka gaya mata ko kuma ni inje har gidan na su in tona komai don bazanso ɓacin ranka ba?".

"Insha Allah zan gaya mata Hajiya ta".dariya ta yi sannan ta ce"gaskiya Babana baka da kirki".nan dai suka saka dariya dukansu abin sha'awa wanda haka ya kamata kowacce uwa ta kasance da ƴaƴanta,ko da yaushe ka gansu cikin annushuwa ba wai kaje gida ka gansu kamar gidan makoki ba,kowa yana danna wayarsa kamar gidan karuwai.


****

Babu yadda Abeed ya iya yana ji yana gani ya fara zuwa ɓangaren Bilkisu gani ya ke kamar zai cuci yaranne don shidai babu yadda za'ayi ya ƙwana da mace ba tare da wani abu ya faru ba,kuma shi ga irin lalurarsa yana ganin ba kowacce macece za ta iya auransa ba,idan ba irinsa ba wacce ta kasance mai irin matsalarsa.

Bayinta suna kusa da ita suna mata fifita ya shigo,tsaɓar sarauta ko da ya yi sallamar ma sai da taga damar amsawa sannan ta kori bayin na ta,shima abinda ta yi masa shi ya yi mata ya shige ɗakin ƙwanansa ya barta anan.

Cixon yatsanta ta yi tabi inda yabi da idanu tana harararsa,ranta yana mata suya shifa namiji haka ya ke idan yaga ana sonsa babu abinda ba zaiyi ba don ya ƙuntata maka.

Tuno wani abu da ta yi yasa tabi bayansa badon ranta ya so ba,sai don wannan abin da ta tuno,yana cire kayansa ta samesa sai ta wayance sannan ta amshi kayan ta fara taya sa cirewa,wani abu yaji tun daga kansa har zuwa ƴan yatsunsa,amman sai ya daure ya cije ya shiga wankan.

Yana fitowa daga wanka ta nufo inda ya ke ta rungumesa ta baya,yaji wani yar ajikinsa yana nema ya saki layi jin abinda ta ke masa.ya yi saurin janye hannayensa sannan ya ce"ke baki iya gaisuwa ba ko?".ɗan turo bakinta ta yi sannan ta ce"ina wuni".?

"lafiya".

Kawai ya ce mata ya cigaba da saka kayan baccinsa sannan ya umarceta da ta yi alwala suyi sallah,babu yadda ta iya don ita wataran ma sai ta ga dama take sallah don haka ta turo baki sannan ta wuce banɗakin,yana hangota ta cikin madubi shi kuma lokacin yana shafa body spray ya ce a zuciyarsa yanzu wannan har ita ce mace ta gari?kana saka ta bautawa Allah tana turo baki lallai aƙwai aiki a gabansa.

Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwalar tana wani kallonsa kamar mayya,yadda ya yi mata wani mugun ƙyau daya saka wata jallabiyya mai sulɓi ruwan fari mai ƙyau da haiba.gashin kansa duk ya ƙwanta don kan Yarima Abeed ba ƙaramin gyara ya ke sha ba.
Gashin jikinsa ma duk a ƙwance gashinan da yawa kamar ka kitsesa,wani haɗiyar yawu ta yi aranta tana cebwa gaskiya na yi sa'ar miji,tuna ba ita kaɗai ba ce matarsa yasa ta wani turo baki,amman tuna wani abu yasa ta yi murmushin mugunta ta bi sa suka yi isha'i sannan sukayi nafila raka'a biyu.

Suna idarwa ya ɗaga hannayensa sama yana addu'ah yana kukan Allah ya yaye masa irin lalurar da ya ke ɗauke da ita.

Kallon ƙasa ƙasa Gimbiya Bilkisu ta ke wa mijinta Abeed daman ya iya wannan addu'ar haka?bata gama mamakin ba ya kama goshinta ya fara yi mata addu'ar da manzon Allah(S.A.W)ya koyar damu idan mutum ya yi sabon aure.
Mamaki sosai Bilkisu ta yi to wannan kuma wacce irin addu'ah ce oho?ni kuwa Ummu maher na ce ikon Allah ita kuwa Bilkisu tana ƴar musulmi amman bata iya komai na musulunci ba?to Allah ya ƙƴauta Allah ya shiryar damu Amin.

Yana gamawa ya janyo naman ɗawisun daya shigo dashi ya ajje mata sannan ya yi addu'ah ya hau gado ya fara bacci,wani baƙin ciki ne ya ɗarsu a azuciyar Bilkisu ta hararesa tsabar rashin son da ya ke mata shine ya hau gado ya barta anan?wato ita ce za ta shayar da kanta a matsiyanta na amarya.

Tashi ta yi tabar abin anan sanan ta saka wata tsaleliyar rigar bacci wacce da kanta ta siyo ta a ƙasar germany.

Sosai rigar ta yi mata ƙyau kasancewarta fara sol,kuma kalar rigar baƙace ta taje gashin kanta ta shafa turaren da Mahaifiyarta ta bata na janyo hankalin Abeed.

Ƙamshin turaren yaji kamar daga sama nan da nan ya gigice ya janyo Bilkisu ya rungume yana addu'ah,sosai ta basa kanta musamman ma da taga Yariman kamar ɗan hannune don ba dai sarrafa mace ba.

Sai dai da tafiya tayi tafiya tun talitainin dare ya ke abu ba har safiya kuma bashi da niyyae haƙura,ta yi kuka ta yi magiyar ammanfa abu yaƙi ci yaƙi cinyewa,har suma sai da Bilkisu ta yi babu yadda ta iya dole ta ƙyalesa,amman shiru bai kawo ba,ɗan sauran ƙarfin daya rage mata ta ture sa gefe ta miƙe da k'er za ta shiga banɗaki ya yi saurin wafto ta amman ta zame ta shige banɗaki ta saka sakata.

Awajen ya tsaya yana riƙe da mararsa wacce ke murɗa masa kamar zai mutu,anan ya fara murƙuƙusu yana magiyar ta buɗe masa ƙofar amman shiru bata buɗe ba.
Anan ya lallaɓa ya hau kan gado duk da sanyin A c amman wani zazzafan zazzaɓine ya yi gaba dashi ya hau rawar sanyi.












*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green🍀: *🔖BASMA🔖*




NA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN🍏)


Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kiji👂🏻*

yawan istigfari yana kankare mana zunubinmu,yawan istigfari yana ƙara kusanta mu ga ubangiji.
--------------------------


21⚪22


. . . . .ina ɗakko kaya acikin sif ɗina na hango wannan ɗan ƙaramin kit ɗin da Aliyu ya bani na ɗakko ina murmushi na buɗe ,waro idanuwa na yi ganin sarƙar gold ɗin da ke cikin ɗan ƙaramin kit ɗin,duk da ban san gold ba amman ko da ba'a gaya min ba sheƙi da walƙiyar da ya ke zai shaida maka hakan.

Hafsat da ke saka kayanta ta waro idanu sannan ta ce"Basma waye ya baki wannan sarƙar haka?".ka sa magana na yi sannan ta amsa tana dubawa ta ce"Basma kinyi shiru fa baki gaya min ba?" A hankali na fara ƙwatanta mata wanene ya bani da maganar kurame,na rungume hannuwana a ƙirji sannan na yi mata alamar zanen heart da hannu na.

Waro idanu ta yi ta ɗala min duka sannan ta ce"lah!lah!! Mutuniyar a ina ya ke kuwa wannan wanda Ya yi dacen Mata Basma".

dariya na yi ina ɓoye fuskata waini kunya ta ce"hmm yanzu zamuje gidan anty shamsiya idan yaso sai ki gaya mata tunda na ga kamar kunfi kusa da ita".

ƴar dariya na yi sannan na ƙarasa saka rigata sannan muka haɗa kayanmu cikin troly guda ɗaya mukasha hijabanmu har ƙasa sannan muka fito.

Idris ne kawai a farlon ƙanin Hafsat sai Mama dake kitchen,ƙarasawa kitchen ɗin na yi sannan na yi mata magana da hannu alamun zamu tafi kenan,mama ta tsame hannunta daga cikin yankan naman da take ta ce"to shikkenan idan kunje kuce ina gaisheta da yaran na ta da maigidan".da to muka amsa sannan muka fito muna ɗan hirar mu Maryam da Salimat ne suka taho ganinmu da troly sai suka kallemu suka ce"Hafsat ina zuwa kuma?".

"inda kuka aikemu"?.sosai abin ya basu haushi musamman maryam da ta yi maganar Salimat ta ce"ai kinga Yaya maryam kin janyo ta gaya mana magana ni fa a harkata bana son raini kin san kuma wannan siririyar yarinyar raini gareta,balle yanzu tana ji da kanta waidon an kawo kuɗinta,ai dole ta dinga ganinmu wasu ɗai ɗai,in dai aure ne ayi mugani".

tana faɗar hakan taja hannun Yayarta Maryam suka wuce,sosai abin ya damu Hafsat duk da na ba ta baki sosai,saboda haka ma shiyasa bana kulasu sam.

Muna hanya ina tunanin Aliyu,yanzu dana taho ta ina zai ganni har mu gaisa kamar yadda muka sabayi,tabbas yanzu na yadda ina son Aliyu abinda ban taɓayi a rayuwata ba,wai ince inason wani ɗa namiji.


Sai dare sannan muka isa garin Abuja gari me daɗi da ni'ima har tasha Anty shamsiyya ta aiko aka ɗaukemu har unguwarsu,kallon gidajen unguwar ta su na ke masu ƙyau da kuma tsari,har muka iso na su katafaren gida mai ƙyau dashi,azuciyata na ce lallai anty shamsiyya ashe gidan da suka canza ɗin haka ya ke".?
da ya ke adacen ba anan suke ba,kuma rabonmu da zuwa Abuja mun daɗe sosai,gwarama Hafsa tazo alokacin tana da ciki har ta haihu shekara biyu kenan,Anty shamsiya ita ce ƴar mama ta biyu Anty Atika ita ce ta farko,Atika itace babba sai Shamsiya sai Iklima sai Hafsat sai idris,Atika tana aure a Bauchi,Iklima kuma tana aure a lagos bata daɗe da aure ba shekara ɗaya kenan,sai hafsat sai idris ƴaƴanta biyar kenan.


Har cikin gidan aka shigo damu gidan gwanin sha'awa gidan sashe biyu ne sashen kishiyarta da kuma na ta.

Ina ganin anty shamsiya na rungumeta ina dariya,ita ma dariyar ta ke tana ce wa"oyoyo ƴan matan Mama sannunku da zuwa".
Hafsat ta ce"ikon Allah na ga alama an manta da wata halitta Hafsat don haka wallahi yanzu sai in koma abina tunda ba a son zamana."

"autar mama ban manta da ke,lale marhabin amarya".ɓoye fuska Hafsat ta yi sannan ta wuce da sauri tana ce wa"lah anty banga twins ba"?.
"twins suna skull anjima zasu dawo amman ilham da kausar suna ciki yanzu suka gama drama".

dariya dukanmu mukayi Hafsat tana cewa"lallai yarannan har yanzu basu daina faɗan nan ba?ah lallai ki ce yau zan gyara musu zama".ta faɗi hakan tana dariya ta shiga gidan.
Ai kuwa muna shiga suka taho a guje suka rungumemu ni kuwa mamaki ya kamani yadda na ga dukansu sun zama ƴan mata,ilham tana da shekara 14 kausar 10,dukkansu suna sona sosai don idan muna hira dasu sai kice da mai jin magana suke don har dariya munayi dasu don su basufi shekara ɗaya da zuwa kano ba,don haka mun saba dasu sosai.




****

"Ahmad wato dana ce maka kaje kaga yarinyar nan shine ka yi min kunnen uwar shegu ko?ni nan isa in zaɓa maka abinda ya ke mafi alkhairi a rayuwarka ba ko?".

"Hajiya wallahi yarinyar nan bata dace dani ba sam bata da kunya balle tarbiyya shiyasa ni banso kika haɗa aurenmu ba tunda halina da na ta ba ɗaya bane?".

"ikon Allah lallai Ahmad na yarda wannan yarinyar ba iya asirin sonta ta yi maka ba,har da haɗani da kai ta yi don adacen baya ba ka yimin musun duk abinda na sakaka."

"Hajiya ki yi haƙuri insha Allah zan aure ta in dai hakan zai sakaki farin ciki,amnan ki daina zagin Basma baiwar Allah wacce bat damu da duniya bama ballanta na. . . ."

"kai shasha rufemun baki dalla,tunda baiwar Allah ce ai mu ba yinka ne?ai insha Allah sain karya wannan mugun asirin da ta yi maka da ina faɗa kana faɗa".

ganin abin ba na ƙare bane yasa Ahmad ya tashi ya yi wa Hajiyarsa sai da safe sannan ya tashi ya tafi,harar bayansa ta yi sannan ta ce"zanyi maganinka ne ƙwanan nan don na ga alama kuruwarka ma ta cinye shegiya ƴar matsiyata".nan dai Hajiya ta yi ta zagin Basma wacce bata ji ba bata gani ba.
*****
Sai da Gimbiya Bilkisu ta yi bikin jikinta sosai don ba ƙaramar wuya tasha ba,kana ganin tafiyarta kasan me ya faru,shi kuwa Yarima Abeed yana samun sauƙi ya fara shirin tafiya,ai kuwa wannan tafiyar anyi tashin hankali sosai don ita Gimbiya Abeeda ce wa ta yi ai Yarima abeed yana sane don ya ga ƙwananta yazo shiyasa ya shirya tafiya,don wannan maganar ai har bakin Sarauniya jidda ya je,ta kira Admiral B.tana tambayarsa abinda ya faru,wayo ya yi mata sannan ya ce mata an kirawosa ne agun aiki shima don babu yadda zaiyi ne.

Fatan alkhairi ta yi masa sannan ta kira Abida ta shaida mata abinda ke faruwa,amman duk da haka gani take ai cin fuska ne me yasa a ƙwanan Bilkisu ba a kirawosa ba sai akanta tunda ita aka fi tsana.

Shi kuwa Admiral B.tausayinta kawai ya ke ji don yadda ya yi wa Bilkisu abin har tsoro ya basa shiyasa ya koma don aƙwai likitansa da ya ke gani a yanzu haka kuma akan matsalarsa.

Bilkisu kuwa murna sosai ta yi da tafiyar mijin na ta don abin ya ba ta mamaki sosai,don ko a tarihi bata taɓa ganin namiji haka ba.






*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green🍀: *🔖BASMA🔖*




NA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN🍏)


Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kiji👂🏻*

Mu dinga ƙyautatawa iyayenmu kula da iyaye yana saka kyakkyawan ƙarshe.
----------------


23🟣24


. . . .ina duba kayana na ɗakko wannan kit ɗin da Aliyu ya bani,na kalli Hafsat ita ma ni take kallo ta ce"au daman dashi ki ka taho?wallahi na ɗauka a gida ki ka barsa?muna cikin wannan maganar ne Anty Shamsiya ta shigo tana tsokanarmu da ƴan matan Mama.ƴar dariya mukayi ni da Hafsat sarƙar da ɗan kunnen suna hannuna ina juya su.

"Basma a ina ki ka samu ɗan kunne da yarin sarƙar gold haka me tsada?".da mamakinta ta faɗi hakan tana duba sarƙar da yarin.

Nima kallon sarƙar na ke yadda take ta walwali Hafsat ta ce"Anty itama Basma wani saurayinta ne ya ba ta wai sunansa Aliyu suna haɗuwa hanyar makaranta,amman dai nima Allah baisa na taɓa ganinsa ba."

"idan kun koma Basma ki ce ya turo kinji"?.ta yi min alamar hakan da hannu na ɗaga mata kai da to.

rannan da yamma muka fita wani super market na ci ƙwalliyata cikin doguwar riga abaya baƙa tasha stone mai ƙyau na yafa mayafinta a kaina ban wani yi ƙwalliya ba amman na shafa hoda da kuma lipstick na yi ƙyau sosai Hafsat na ji kawai tana ɗaukana a hoto da camera ƙaras ƙaras,ta ce"wow Babyn mama gaskiya kinyi ƙyau kin ganki kamar wata half case.

Ƴar dariya na yi na wuce gaba tana dariya itama,mai motar gidan yana tsaye yana jiranmu alokacin ya dawo daga kai Anty Shamsiya aiki da kai yara skull.
Kallona sosai Hamza ya ke yana ayyanawa aransa,ina ma dai ace ya auri wannan yarinyar da ya caɓa wallahi yarinya sai ka ce wata matar shuguban ƙasa babu abinda ta rasa na mace a cike take ɓam,shi babu ruwasa da wai kurma ce shi a haka ya ke sonta,amman fa yasan wannan tafi ƙarfin ajinsa matar manya ce.

Ko a mota ina lura dashi kallon tsaf ya ke min,sai in juya in kalli windows ɗin motar,idanuwanta kawai Hamza ya ke kalla yadda suke a lumshe kamar mai jin bacci,leɓenta kamar ta shafa jan baki.

Hafsat ta ce"don Allah Hamza ka yi tuƙinka ka daina kallon wani wajen?sai ka saka munyi hatsari"?.
"af Hajiya don Allah ki yi haƙuri insha Allah bazan ƙara ba".dariya Hafsat ta yi ta ce"ah to gaskiya dai ya kamata adaina don kada ayar damu.

Muna zuwa katafaren wajen muka shiga hankali fa gaba kiɗ ɗaya ya koma kanmu yadda kasan sun samu abin kallo,Hafsat ta ce kau gaskiya ni fa mutanen garin nan sun fiya kallo kamar zasu cinye mutane wallahi".


Kallonta na yi bance komai ba na yi dariya don ni tun shigowarmu na ga irin kallon da ake mana amman duk ban kula dasu ba sa yi har su gaji indai kallo ne,don ni dai duk inda na yi yadda kasan talabijin haka suke kallona.
Ko da muka shiga ma masifa Hafsat taks mutane suna ta kallonmu,ita fa dai da tasan haka ne da baza tazo ba,haƙuri na dinga ba ta amman fir Hafsat ta ce sai dai fa mu canja wani wajen nan an fiya kallon mutane.


Muna fitowa shima Hamza ya kafeni da idanuwa Hafsat na lura da hakan,daman Hamza yana jikin motar ya tsaya ya yi face ɗin ƙofar wajen ta kalleshi ta kalleni ta ce"na shiga uku na wai su mutanen garin nan wasu irin mutane ne kamae mayu suyi ta bin mutum da kallo kamar sun samu talabijin?".

har muka shiga mota Hafsar tana ta mitarta babu wanda ya ce mata ƙala,shi daman Hamza ba shida bakin magana don kunya ma ya ke ji da Hafsat ɗin ta kamasa yana kallon Basma.


To wajen da muka je yanzu daɗan dama dama don wajen ba wajan kowa da kowa bane sai wanda ya amsa kansa sannan zai je wannan shahararren waje.

Shuke shuke ne suka cika wajen gwanin sha'awa ga kuma tables na cin abincin mai ƙyau da tsari,na kalli wajen ina murmushi Hafsat ta ce"Basma wajen ya yi ko?".ɗaga kaina na yi alamar eh.

Hafsat ta ce"yauwa ko dai na ji wannsn wajen babu wannan saka idon nan kowa yana harkarsa ne,idan ma da saka idanuwan to fa babu yawa kamar na can".ni dai duk ina jinta bance komai ba ina ta kallon wajen gwanin sha'awa.


Na hango swimiming pool mai ƙyau Hafsat na danne danne a wayarta ba ta kula dani ba na tashi ina zagayen wajen har na iso wajen wannan ruwan,a hankali na janye fararwn ƙafafuna na saka ƙafata duka biyu acikin ruwan na zauna a bakin wajen ina wasa da ruwan ina jin wani daɗi a cikin raina.

Na kalli wani yaro ya yo wajen ruwan mamansa da babansa na binsa da gudu zasu kama sa suna dariya kamar abin wasa,sosai suka bani sha'awa wasu hawaye suka zubomin na gogesu ina ce wa a zuciyata Allah sarki uwa tana da daɗi duk da ban taɓa ganin mahaifiyata ba,amman ina matuƙar sonta da ƙyaunarta na sha ɗaukar hotonta inyi ta dubawa ina mata kiss,mace ƙyaƙƙyawa da ita kamar itace ta yi kanta tsabar ƙyau.sam bana tuna mahaifina a rayuwata sam bai damu dani ba bai san ciwona ba ko kaɗan rabonda inga babana yau shekara 7 kenan alokacin ina da shekara10 mukaje ni da Mama da Hafsat amman har muka je muka dawo sau ɗaya na gansa baya zama a gidan sam,kullum yana cikin yawo abin ya zauna min sosai a zuciyata,rannan na buɗe fridge ɗin ɗakinsa kawai giya ce ƙwalabensu manya manya duk da ban iya karatu ba na ɗauka na nunawa mama.

Sosai ta yi mamaki don bata taɓa zata abin na sa ya kai har haka ba,ai kuwa washe gari yana dawowa mama ta ce tafiya zamuyi,to shima daman bai damu ba ta wani ɓangaren ma gwara mu tafi ɗin don nun takurawa rayuwarsa,don ya saba ɗauko mata har suyi ƙwanaki a gidansa kamar matansa yanzu kuwa tun zuwanmu komai ya tsaya masa cak.
Kuɗi ya bamu sosai don yana samun kuɗin banza wajen Hajiya,don haka muka taho tun daga nan bamu ƙara zuwa maiduguri ba har yau.

Ina son in zauna tare da mahaifina ko don ganin idona wata ƙila zaisa ya ɗan rage wani abin,ina ji masa mutuwa wacce ako da yaushe take zuwar wa ɗan adam ko ka shirya ko baka shirya ba.


Wasu hawaye suka zubomin na gogesu yanzi mahaifina kenan ɗan wuta ne?kai gaskiya inason in zauna tare da mahaifina don gani na ke tunda na rasa mahaifiyata bai kamata in rasa mahaifiba tunda yanzu a halin da ake ciki tunda ta rasu bai yi aure ba.


A hankali na tashi na hango Hafsat tana zaune kan tebir ɗin tana yimin dariya tare da ɗago min hannu,nima dariyar na yi cikin ikon Allah silɓin wajen ya ƙwasheni luuu na faɗa ruwan ji ka ke tsundum.

Da gudu Hafsat ta taso tana kirana tare da nemab taimko,amman kowa ya yi shiru a wajen saboda suma duk basu iya ruwan ba.


Jiniyar wasu motoci ne ta fara karaɗe wajen kamar motocin ƴan sanda sai dai ba na ƴan sanda bane na sojoji ne.
Hafsat sai kuka ta ke harda majina,duk ta tayar da hankalinta ni kuwa sai facal facal na ke a cikin ruwan.



Dukkansu ƙamewa sukayi awajen suna sarawa ogansu ya fito a hankali cikin motar wow,sai da na yadda birona tsabar kallo.

Swiming ɗin da ya ke zuwa ne duk ranar da babu aiki don yana matuƙar son yin wanka a swiming amman fa kowa sai ya bar wajen sannan.

Rigarsa ya cire daga shu sai boxer amman yana da ɗan tsayi.


"Ranka ya daɗe wai wata yarinya ce ta faɗa cikin ruwan"?.da sauri ya kalli cikin ruwan ya tsaya kamar wani ba'adare yana kallonta,tunda ya ke aduniya bai taɓa ganib surar da ta yi masa ƙyau kamar ƴaƴan lu'u lu'u irin wannan yarinyar ba,yana cen yana tunani shima silɓin ya ƙwashesa ya faɗa.



*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green🍀: *🍏BASMA🍏*

BOOK 2📃


BY
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)


Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



---------
SIRRINKI👂🏻

ƳAR UWA KI KASANCE MAI RUFE SUTURARKI AKO DA YAUSHE,RUFE JIKINKI YANA TAIMAKA MIKI WAJEN YIN RIGAKAFI GA MUTANE DA KUMA SHAIƊANU.
----------------------------------


*25🟢26*

. . . . .numfashin Basma har ya fara ɗaukewa saboda da ɗewar da ta fara yi acikin ruwa,da sauri ya ruƙota ya rungumeta sosai kamar wani zai ƙwace masa ita,abin gwanin sha'awa kamar a india,mutane aka fara tafi awajen da sauri Hafsat ta taho ta rungume Basma tana kuka bayan ya ajje ta a gefen wajen,da kansa ya saka hannuwansa guda biyu a ƙirjinta,sai da yaji wani shork har cikin ƙwaƙwalwarsa ya daure ya fara danna ƙirjinta ruwan yana fitowa har dai ya gama fitowa,ya tsira mata idanuwa yana kallon fuskarta,ya shagala sosai da kallonta,ita kuma a lokacin ta buɗe idanuwanta da sauri ta tashi tana kallon wajen kamar bata san tazo ba.


Da sauri ya tashi bayan ya dawo daga hayyacinsa ya amshi rigarsa daya cire ya saka yana kallon Basma kamar zai cinyeta,Hafsat ta ruƙo hannuwana muka fara tafiya.

Wani abu yaji mai kamada kishi saboda yadda mutanen wajen suke kalle masa matarsa,don shi har ya yi mata don tunda ya ke zai iya cewa bai taɓa ganin macen da ta ƙwanta masa arai irin Basma ba.

Motar su ta sojoji ya shiga ya kafa glass ɗinsa a fuska wato no respect suma sauran sojojin ganin ogansu ya shiga mota da sauri suka shiga suna sara masa.

Muna fitowa waje Hamza ya taho da sauri yana ce wa"iyayen ɗakina lafiya me ya faru?naga Basma duk jikinta ya jiƙe tana rawar sanyi haka?.shiru hafsat ta yi masa ganin ya dage da tambayar sai ta ce"Hamza don Allah kaja mu mu tafi Basma ce ta faɗa ruwa yanzu".

da sauri ya juyo yana ce wa"subhanalillahi sannu Basma,amman babu abinda ya sameta ko?shiyasa banji daɗi ba da muka baro wancen wajen tunda na ga cen ɗin babu irin abubuwa nasu hatsari".


har ya gama maganarsa babu wanda ya ce masa ƙala har ya gaji ya yi shiru,muna zuwa gida Anty shamsiyya ta dinga yi mana faɗa akan mudinga kula da kanmu,daga cewa zamu super market shine muka tafi wani waje harda swiming pool,ganin ranta ya ɓaci ne muka bata haƙuri tare da yi mata alƙawarin ba zamu ƙara fita ba har mu koma kano.


Sosai suke gudu a motar don su gano inda motarsu Basma take,amman sun duba ko'ina babu su babu labarinsu,dukan sitiyarin motar ya yi ya kifa kansa yana addu'ar da ma yana ɗago idanuwansa ya ganta,tabbas babu abinda zaisa yabar Abuja idan har bai ga Basma ba.


****

Yau ake ɗaura auren Ahmad da amaryarsa,amman fa kana ganin fuskarsa kasan ƙwata ƙwata baya cikin hayyacinsa don tunda ya rasa Basma gani ya ke tamkar ya rasa komai na rayuwarsa,tunda aka dawo daga ɗaura auran na sa yaji baki ɗaya kansa yana wani irin sara masa ya cire kayansa ya shiga wanka bayan ya fito yasha magani ya ƙwanta.

Yana ƙwanciya babu da ɗewa Hajiyarsa ta shigo ɗakin nasa,ganinsa ya rufu da blanket sai taji gabanta ya yi mugun faɗuwa sosai,a hankali ta isa inda ya ke ta zauna a bakin gadon a hankali ta yaye blanket ɗin ta shafa fuskarsa,wani zazzafan zazzaɓi taji a jikinsa yana tashi harda huci.

Cikin tashin hankali ta kira sunansa tana haɗa baki wajen ce wa"Ah.Ah..Ahmad tashi mu tafi asibiti ba kada lafiya jikinka ya yi zafi sosai.


"Mama ki barshi na fara jin sauƙi yanzu".ya faɗi hakan yana dafe kansa"gaskiya Ahmad bakaji sauƙi ba,ga kanka nan har yanzu zafi zau kamar wuta."

babu yadda ta iya dolenta ta haƙura ganin ɗan na ta ya dage,tana addu'ar Allah ya bawa ɗanta abin sonta lafiya,tunda ta takura masa akan wannan auren shikkenan ya shiga ciwo yau lafiya gobe babu lafiya,ita kanta amaryar ta kasa gane kansa sam,don irin wannan zancen da ake zuwa

Please Login or Register in order to submit comment