Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bamu a wannan
Kauyen musamman jarumi Imran wanda ya fitar da mu
daga duhu zuwa haske.
Yanzu kuma gashi kun dawo mana da harkar
kasuwancinmu na su daga jiya zuwa yau har baki sun fara
cin kasuwarmu.
Ni a tawa shawarar iya wannan kokarin da ku ka yi
mana ya isa me zai hana ku hakura da shiga cikin wannan
daji na farauta saboda mugun hadarin da ke cikinsa?"
Koda jin haka sai jarumi Imran ya yi murmushi ya ce,
"Ai tunda har muka yi alkawarin shiga babu abinda zaí sa
mu janye.
Abinda muke bukata kawai a wajenku shi ne ku
tayamu da addu'a".
Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya juya ya
nufi hanyar da za ta kaishi cikin dajin Farauta.
Ba tare da fargabar komai ba kuwa su jaruma Suzaila
suka bi bayansa, Hasnalu da Lushaira ne daga baya.
A Can
Birnin Hutaira kuwa,
Sarki Imras da Sarki
Huraisu na zaune a fada
cikin kaguwa bisa jiran dawowar wadannan dakaru masu
bakaken tufafi wadanda suka je kashe Muraisu da
mahaifiyarsa Husnaila, amma shiru basu dawo ba a lokacin
da ake sa ran dawowar tasu.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sarakan ke nan
suka kasa zaune ko tsaye.
Kwatsam! Sai ga daya daga cikin dakarun biyu ya
shigo cikin fadar yana layi kamar zai fadi, jini na zuba daga
gadon bayansa.
Cikin dimauta Sarki Imras ya tari Badakaren ya
allafeshi da hannayensa biyu a lokacin da Badakaren ke
Kokarin mutuwa ya daka masa tsawa ya ce, "Ina daya
abokin aikin na ka?
Shin kun sami nasarar kashe Muraisu da mahaifiyarsa
kuwa?"
Badakaren ya budi baki da kyar ya ce, "Ranka ya
dadei wannan bakon jarumi ne ya ceci rayuwarsu
lokacin da muka shiga har cikin masaukinsu,
An kashe abokin aikina a can, nima da kyar na karaso
nan".
Garma fadin hakan ke da wuya sai idanun Badakaren
suka kafe, jikinsa gaba daya ya sandare ya zama gawa.
Koda ganin haka sai Sarki Imras ya kwarara uban ihu
cikin tsananin bakin ciki da fusata ya mike tsaye zumbur!
ya dubi Sarki Huraisu ya ce, "Dole ne mu yi shirin karshe
yanzu tmu tafi izuwa wancan Kauye domin mu yaki su
Muraisu da shi kansa wannan bakon jarumi wanda ya ke
karesu daga sharrinmu".
Da jin haka sai Sarki Huraisu ya dubi Sarki Imras
cikin alamun matukar danuwa ya ce, "Ta ya ya ka ke
ganin zamu iya samun nasara akansu alhalin yanzu sun san
cewa muna harin rayuwarsu tunda gashi mun tura a kashe
su bamu sami nasara ba sun tsallake Rijiya da baya?"
Sarki Imras ya yi guntun murmushin mugunta ya ce,
"Ai yakin sumname zamu kai musu cikin MAMAYAR
BAZATO.
Tun daga nesa zamu sa ayi ta harbawa Kauyen
kibiyoyin wuta yadda koda kibiya ba ta soki mutum ba bai
isa ya tsallake masifar wuta ba,
Topa Nima AA Misau jin wannan tuggu da su sarki huraisu ke shiryawa yasa zan tsaya nan
Saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu
Admin
AA Misau
Ke Magana
Ku bibiyemu a shafukan nan
Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau
DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAU
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q
BUSA A MUTU 💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part E💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing by AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐
(WANNAN SHINE KARSHEN POSTING DIN MU AKAN LITTAFIN BUSA A MUTU)
TUN DAGA NESA ZAMU SA AYI TA HARBAWA KAUYEN
KIBIYOYIN WUTA YADDA KODA KIBIYA BA TA SOKI MUTUM BA BAI
ISA YA TSALLAKE MASIFAR WUTA BA, KA GA KE NAN
komai da kowa da ke cikin Kauyen sai ya kone.
Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya bushe da
dariyar farin ciki saboda ya tabbatar da cewa wannan
dabara da Sarki Imras ya zo da ita dole ne ma a sami
nasara.
Nan take Sarki Huraisu ya bada umarni aka fara
shirye-shiryen yaki.
Sai da aka tara mayaka sama da dubu dari biyar.
Dubu dari uku daga cikinsu duk masu kwari da baka ne.
Nan da nan aka gama kimtsa komai Sarki Imras da
Sarki Huraisu suka yiwa wadannan dakarun yaki jagora
suka fice daga cikin Birmin Hutaira.
Duk wanda ya dubi yawan wannan runduna yaji cewa
za su je su yaki dan karamin Kauye ne wanda gaba đayan
mutanen cikinsa ma basu wuce mutum dubu ashirin ba dole
ne ransa ya baci saboda kawai zalunci ne.
_Kash! Rashin sani ya fi dare duhu,_ inda su Sarki
Hutaira sun san abinda zai biyo baya da ba su yị wannan
kuskure ba na bin bayan su Muraisu.
Nan da nan su Sarki Huraisu suka ci gaba da durfafar
wannan Kauye cikin tsananin sauri ta hanyar amfani da
karfin sihirn tsafi don gajarce nisan tafiyar.
Ai kuwa sai gashi sun iso Kauyen da safe, kuma tazararsu
da su jarumi Imran bisa tafiyar da suka yi izuwa dajin
farauta ba ta wuce ta rabin sa'a ba.
Lokacin da tazarar da ke tsakanin rundunar su Sarki
Imras da Kauyen ba ta wuce taku dari ba sai Sarki Huraisu
ya baiwa masu kwari da baka umnarni su fara kunna wuta a
jikin kibiyoyinsu. Lokaci guda aka sake basu umarnin
harbi.
Kaico! Mutuwa ba ta da lokaci. Nan fa aka fara yiwa
Mutanen Kauyen ruwan kibiyoyın wuta. Sai dai ka ga
kibiya ta soki mutum kuma wuta ta kama jikinsa. Take
mutane suka rinka kalmar shahada suna mutuwa. Kauyen
gaba daya ya yarmutse.
Mutane maza da mata, yara da manya suka rinka
guje-guje da iface-iface domin su tsira da rayuwarsu, amma
babu wajen gudu, mutuwa ce kadai matserarsu.
Allahu Akbar! Komai rashin imanin mutum idan ya
ga yadda wuta ta kama Kauyen gaba daya tana ci ganga-
ganga kuma ya ga yadda kananan yara, mata da tsofaffi
suke mutuwa dole ne tausayi ya kamashi ya zubar da
hawaye.
Haka dai aka ci gaba da yiwa Kauyen ruwan kibiyoyi
har sai da aka daina jin ihu da koke-koken jama'a, kuma sai
da Kauyen gaba daya ya kone kurmus sannan aka daina
harba kibiyoyin.
A sannan ne rundunar ta su Sarki Imras ta karasa daf
da Kauyen.
Koda su Sarki Imras suka ga gaba dayan mutanen
garin sun zama gawa kuma sun babbake sai suka kama
dariyar mugunta da farin ciki.
Sai da suka yi dariyar suka gaji a lokacin da komai ya
gama konewa sai toka da hayaki da konannun gawarwaki
sannan Sarki Imras ya bada umarnin a shiga cikin Kauyen a
nemo masa gawar Muraisu, Husnaila da ta jarumi Imran
domin su shaida da idanunsu su tabbatar da cewa sun mutu.
al'amarin
su jarumi Imran kuwa,
lokacin da suka nausa
cikin daji farauta suka
durfafi inda wannan Dodanniya take.
Sai da suka yi tafiyar rabin sa'a sannan suka hango
tsaunin da aka tabbatar da cewa akansa Dodanniyar take
rayuwa.
Nan take jarumi Imran ya juyo domin ya dubi sauran
abokan tafiyar, kawai sai ya hango alamun tururin bayakin
vuta a can bangaren da Kauyen yake.
Cikin tsananin kidimewa da đimauta ya nunawa su
Muraisu hayakin da hannunsa. Suma a rude suka waiga
baya suka yi arba da hayakin.
Take jarumi Imras ya ce, "Tabbas babu lafiya an
kawowa Kauyen can hari bayan tahowarmu."
Cikin razani Suzaila ta duti Inran ta ce "To yanzu
meye abin yi?
Zamu karasa wajen wannan tsauni ne mu yaki
Dodanniyar ko kuwa zamu koma can Kauyen ne mu kai
musu agaji?"
Imran ya ce, "Ai bashi da Wani amfani mu je mu yaki
su Dodanniya a yanzu tunda wadanda za mu yi yakin
dominsu suna cikin masifa. Kawa: ku zo mu ruga da baya",
Imran na gama fadin hakats ai ya juya da baya ya
falfala da azababben gudu.
Nan take su jarumi Muraisu ma suka rufa masa baya.
Birnin Hutaira kuwa, a dai-dai
lokacin da su Sarki Imras suka
kwashi dakarun yakin su ne suka
fice daga cikin Birnin Sarkin Barayi Zaltar ibini Mazwar ya
baiyana tsulum! A kofar gidan sarautar.
a can
Gashi dai gidan a kewaye yake da Dakaru masu tsaro
amma ta gabansu ya wuce kuma ya shige har can cikin
gidan ba tare da wani ya ganshi ba saboda karfin sihirinsa
na bata.
Sai da Zaltasr ya shiga har cikin turakar Sarki Huraisu
asirinsa bai tonu ba, kuma duk inda ya iske kofa a rufe sai
dai ka ga ya ratsa ta cikin bango ya wuce tamkar ratsawar
danshi daga cikin karkashin kasa.
Lokacin da ya tsinci kansa a cikin turakar Sarki
Huraisu sai ya shiga laluben wannan kwalbar sibiri, amma
sai da ya caje turakar gaba daya, ko ina da ina ko alamunta
bai gani ba.
Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalinsa ke
nan ya fara tunanin cewa shi ke nan ya yi asarar makudan
kudaden da ya dade yana mafarkin mallakarsu
rayuwarsa.
Har ya juya zai fice daga cikin turakar sai yai arba da
wani dan karamin gunki da aka sokeshi a cikin wani dan
rami da ke jikin bango.
Kai tsaye ya je gaban gunkin yasa hannunsa don ya
đauko gunkin.
Yana janyo gunkin sai ya' ga wata kofa ta bude a
JIkin bangon wacce ko alamunta babu da farko.
Yana lekawa cikin kofar dakin sai ya hango tarkacen
kayan tsafi iri-iri.
Cikin tsananin farin ciki ya kunna kai cikin dakin ya
ci gaba da neman wannan kwalba wacce aka sa gashin
sihiri a cikinta.
AA Misau ke Magana
Ai kuwa bai dade ba yana dube-dube ya ga wata 'yar
karamar kwalba a cikin wata bakar akwatin karfe. Babu
alamar wata kofa a jikin kwalbar, amma kuma ga wani dan
siririn gashi a cikinta.
Cikin alamun tsananin tsoro Zaltar ya kai hannu zai
dauki kwalbar amma sai ya kasa.
Kawai sai ya karanta wadansu dalasiman tsafi guda
uku sannan ya dauki kwalbar.
Bisa mamaki sai ya ga ya dauki kwalbar lafiya ba tare
da wani abu ya same shi ba.
Nan take ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya yi
girgiza ya bace bat daga cikin dakin tamkar bai taba
wanzuwa ba
A wajen.
Kauyen Zirmal kuwa, lokacin da
su Sarki Imras suka sa a shiga
cikin Kauyen a nemo musu gawar
su Muraisu, sai da aka caje ko ina amma ba a ga gawar ta
Su ba.
Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalinsu ke
nan ainun, Sarki Imras ya kurma uban ihu ya ce, "Tabbas
mun yi babban kuskure da muka baro Birnina mu duka.
Jikina ya bani cewa can Birnina su Muraisu suka tafi.
Idan kuwa can din suka tafi lallai za su yi kokarin dauko
wannan gashin sihiri ne.
Da zarar sun daukoshi kuwa shi ke nan har abada ba
zamu iya kawar da su ba sai sun sami nasara akanmu.
Babu wani abu da zamu iya yi a yanzu face mu ruga
izuwa Bimina domin mu hana faruwar hakan".
Yana gama fadin hakan ya bayar da umarnin a bar
Kauyen a koma izuwa Birnin Hutaira.
Nan take gaba dayan tawagar ta juya da gudu ana
zaburar dawakai aka đauki hanya.
Tafiyar su Sarki Imras da kamar kusan rabin sa'a ke
nan sai ga su jarumi Imran sun karaso Kauycn a guje
Koda suka ga yadda aka kone Kauyen gaba daya
kuma aka kashe gaba dayan jama'ar Kauyen maza a mata,
sai dukkaninsu suka kamu da tsananin bakin ciki da tausayi
suka fashe da kuka.
Haka dai suka ci gaba da duba gawarwakin suna kuka
saboda tsananin bakin ciki ma jarumi Imran bai san sa'adda
ya kwarara uban ihu ba ya durkushe kasa.
Daga can sai ya mike tsaye zumbur! a fusace ya zare
takobinsa ya yunkura zai ruga da gudu ya bi bayan sawun
dawakan su Sarki Imras, saui Suzaila ta yi wuf! Ta sha
gabansa ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani cewa
idan muka bi bayan abokan gaba a yanzu ba zanu sami
nasara ba saboda bisa ganin sawun dawakansu suna da
tsananin yawa kuina ka san cewa Sarkin yawa ya fi Sarkin
karfi."
Da jin haka sai jarumi Imran ya dubi Sużaila a fusace
ya ce, "Kawai kice ba kya so naje na yaki mahaifinki
saboda na tabbatar da cewa shi da Sarki Imras ne suka zo
suka yi wannan mummunar barna saboda sun turo a kashe
su Muraisu basu sami nasara ba".
Da jin haka sai hawaye ya zubowa Suzaila ta ce, "Ban
taba goyon bayan mahaifina ba bisa duk irin zaluncin da ya
yi a baya kawo i yanzu.
Na hanaka zuwa ka tunkareshi ne a yanzu saboda na
damu da rayuwarka da lafiyarka kuma a shirye nake na
taimakeku ku yaki mahaifina da Sarki Imras domin a
kawar da su.
Abinda ba ran iya ba kawai shi ne ba zan iya kashe
mahaifna ba da hannuna."
Har jarumi Imran ya budi baki zai ce wani abu sai
Husnaila ta tari numfashinsa ta ce,"Abinda wannan
yarinyar ta fada maka gaskiya ne
Idan har ka ce za ka bi bayan su Sarki Huraisu a
yanzu ka yake su ba za ka tab:a samun nasara ba kumna babu
wanda zai iya tserar da rayuwarka face Ubangijinka."
Koda įin wannan batu sai jikin jarumi Imran yai
sanyi, kuma ya dubi lusnaila cikin tsananin mamaki ya ce,
"Yanzu kina nufin ki ce da ni kin yi imani cewar babu wani
karfi wanda ya fi na Ubangijina?"
Husnaila ta yi dan guntun murmushi ta ce, "Duk mai
hankali, kuma mai son gaskiya idan ya yi la'akari da irin
nasarar da ka sanu a bakin kogi ka kashe wannan katon
Kada ya tabbatar da Kartin Ubangijin Musulunci.
Na yi maka alkawari ni da dana Muraisu za mu karbi
wannan addiní naka mai daraja da adalci, amma ba yanZu
ba sai bayan komai ya lafa".
Gama fadin hakan ke da wuya sai suka hango wanı
AA Misau ke Magana
mahayi bisa kan doki a sukwane ya durfafosu.
Gaba dayansu sai suka zare takubbansu suka juyo
suna kallon mahayin suna jiran karasowarsa.
Koda ya kara matsowa kusa sai Husnaila ta shaida
mahayin.
Ba kowa bane face Sarkin barayi Zaltar ibini Mazwar
wanda fuskarsa ke cike da annuri alamar cewa ya samu
nasarar aikin da aka turashi yi.
Cikin tsananin farin ciki Husnaila ta ruga izuwa
wajen Zaltar ta tarcshi.
Zaltar na isowa daf da ita ya ja linzamin dokinsa ya
tsaya cak, kuma ya sauko daga kan dokin.
Nan take Zatar ya dauko wannan kwalbar sihiri daga
cikin aljihunsa.
Koda HIusnaila ta yi arba da wannan kwalba sai ta kai
hannu da nufin ta karba, amnıa sai Zaltar ya janye nasa ya
dubeta ya ce, "Haba ranki ya dade ai da sauran magana.
Ya za ki karbi wannan kwalba ba tare da kin bani
cikon ladana ba?'
Koda jin haka sai husnaila ta yi murmushi, nan take
ta rafawa Zaltar wadansu kalmomin tsafi guda uku, sannan
ta ce, "Sai mun hadu a Birnin Lairuf a ranar da dana ya hau
karagar mulki."
Nan take Zaltar ya risina ya yi godiya ga Husnaila
sannan ya yi ma ta sallama ya ba ta wannan kwalba kuma
ya hau dokinsa ya juya da baya ya zaburi dokinsa da gudu
cikin tsananin farin ciki.
Muraisu ya rugo da gudu wajen Husnaila ya ce, "Ya
ke Ummina me ake ciki yanzu? Shin Sarkin 6arayi ya yi
nasara?"
Husnaila ta ce, "Kwara kuwa, bukatata ta biya.
Yanzu mnu je wajen su jarumi Iriran na yi magana da shi"
Nan take Muraisu ya takewa Husnaila baya suka
dawo wajan su jarumi Imran.
Da zuwansu sai Husnaila ta dubi Imran cikin nutsuwa
ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani cewa ni da dana
yanzu mun sami abin dogaron da muka tabbatar da cewa
sami
zamu iya yakar abokan gabarmu mu
hallakasu.
Na sani cewa kaima yanzu ka yankewa su Sarki
Huraisu hukuncin kisa tunda sun kashe yan uwanka
Musulmai, zancen yin sulhu ya kare. Ina mai rokonka da
ka bamu dama mu je mu kaddamar musu mu hutassheka
yaki da su".
Lokacin da Husnaila ta z0 nan a zancenta sai jarumi
Imran yai shiru yana nazarin al'amarin.
Daga can sai ya dago kai ya dubcta ya ce, "Dalili
daya ne zai sa na baku wannan dama.
Dalilin kuwa shi ne, kin yi min alkawarin za ki karbi
addinina ke da danki.
Na yi muku izini ku je ku yaki abokan gabar taku.
idan har kun fuskanci wata matsala ko kuma kuna bukatar
gudunmawa ku aiko mini.
Ni yanzu zamu tsaya mu binne gawarwakin jama'ata
da aka kashe a wannan Kauye, kuma mu yì musu addu'a
gami da zaman makoki na kwana uku saboda bakin cikin
abinda aka rasa.
Bayan kwana ukun zanu wuce izuwa Birnin Lairuf
domin na kai musu tallan addinina.
Da zarar kun sami nasarar kawar da su Sarki Imras
sai ku taho Birnin Lairuf mu hadu a can".
Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya dubi
jaruma Suzaila, Lushaira da Hasnalu ya ce, "ina tausaya
muku bisa kasancewar yanzu iyayenku sun zama manyan
abokan gabarmu.
Ina mai shawartarku da ku dauki hakuri da dangana
domin wannan al'amari mukaddari ne daga Allah.
Ya kai Hasnalu yanzu kai mene ne matsayinka? Ka
ga dai 'yar uwarka ta karbi addinina kai kuma fa?"
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
Hasnalu ya ce, "Ai yanzu na ga zahiri da idanuna don haka
bani da sauran kokwanto akan addinin musulunci, a shirye
nake na karbeshi yanzu.
Mahaifinmu kuwa Sarki Imras duk abinda ya sameshi
shi ne kaddararsa tunda Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa
ke duka".
Da jin haka sai farin ciki ya lullube jarumi lmran.
Nan take ya biyawa hasnalu KALMAR SHAHADA va
maimaita. Al'amarin da ya jefa Lushaira cikin tsananin
murna da farin ciki ke nan bisa musuluntar dan uwanta
Hasnalu
Husnaila da Muraisu kuwa sai suka zagaya izuwa
bayan wata bishiya suka tsaya.
Take anan Husnaila ta karanta wadansu dalasiman na
tsafi ta tofa akan wannan kwalba.
Kawai sai kwalbar nan ta fashe, wannan silin gashi da
ke cikinta ya tashi sama ya shige cikin bakin Muraisu.
Faruwar hakan ke da wuya sai Muraisu ya ji wani irin
azababben karfi ya shiga jikinsa.
Kahon BUSA A MUTU kuwa da ke rataye a bayansa
sai ya kama jijiga tamkar ruhi ne ya shige shi.
Kawai sai Muraisu ya kwarara wani uban ihu, sannan
ya ciro kahon daga bayansa ya kafa a baki ya busa.
Karar busa kahon ta cika nahiyar gaba daya, ta firgita kowa
da komai!
Nima Kuma AA Misau jin wannan karar Kaho yasa zan dakata anan Saboda tsaro
SHIN SU MURAISU ZA SU DAUKI FANSA
AKAN SU SARKI IMRAS?
TSAKANIN SUZAILA DA LUSIIAIRA WACE CE
ZA TA ZAMA MATAR JARUMI IMRAN?
WANE DAN SARKI NE ZAI MUTU YANZU
SAKAMAKON BUSA KAIION BUSA A MUTU DA
MURAISU YA YI YANZU?
Mu hadu a busa a mutu 8 (Kashi na takwas) don
jin karshen wannan kasaitaccen kayataccen labari.
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe
Sarkin marubuta liutattafan yaki
abdulaziz
sani madakin gini
SAIDAI KUMA KASH AN SAMU MATSALAR RASHIN SAMUN LITTAFI NA 8 DIN A WAJENA WANDA YASA DOLE MU DAKATA ANAN KODA BAMA SO
AMMA A CIKIN MAKARANTA IDAN AKWAI WANDA YAKE DA SHI SAI YAMUN MAGANAA PRIVETE
ADMIN
AA MISAU KE MAGANA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

1 Comments On BUSA A MUTU Book 7
avatar
walid

8 months ago

Reply

Is so sweet

Please Login or Register in order to submit comment