Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin da tazarar
su da kogin ba ta wuce kamu ashirin ba.
Ko alamar Kadan ba su gani ba kuma babu wani
bakon sauti a cikin kogin face na gudun ruwa.
A dai-dai wannan lokaci ne jarumi Imran
Muraisu ya ce, "Yanzu ta ya ya kuke ganin zamu iya
ya dubi su
tsokano wannan Kada ya fito?"
Koda jin haka sai kowa ya yi shiru aka kama kallon
juna aka rasa wanda zai bashi amsar tambayar.
Koda ganin haka sai Imran ya yi murmushi ya ce,
"Kada fa ku manta baya na gaya muku cewar ba wai
tsagwaron karfin lan senmu banc zai bamu sa'a dole sai
mun yi amfani da basirarmu da hikimarmu sai kuma
taimakon Ubangijin grskiya."
Koda jin wannar batu sai jarumi Muraisu ya numfasa
va ce, "Ni ina ganin cwa dabarar da zamu iya yi mu sa
Kadan nan ya fito tbu daya ne, dole ne mu samo fatsa mu
jefata a cikin wannan kogi mu fara su. Tun da dai Kadan ya
san an daina zuwa yin su a wannan kogi, to wata kila
kamun Kifin ne baya so don haka da zarar mun fara zai fito
don ya hallakamu".
Koda jin wa
wanr an batu sai jarumi Imran ya yi
murmushi ya ce, "Tabbas ka amsa tambayata dai-dai. Na
yaba da tunaninka da lasirarka".
Nan take jarumi imran ya bude wata jaka da ke rataye
a kafadarsa ya fiddo fitsa guda daya tal ya ce, "A cikinmu
waye zai jarraba shiga wannan kogi ya yi su?"
Nan fa kowa ya kama muzurai aka rasa wanda zai ce
zai iya. Kawai sai iarv mi Imran ya yi murmushi ya ce, "Ni
Zan shiga cikin kogin na jarraba. Amma gaba dayanku ku
zauna cikin shiri".
Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya durfafi
cikin kogin yana inai karanta wata addu'a a cikin ransa,
kuma yana rike da vvannan fatsar da hannu daya, daya
hannun nasa kuwa ya dafe kufen takobinsa.
Imran ya shiga cikin kogin sai ya jefa fatsarsa a ciki
ya fara yin su.
Ai kuwa sai gashi nan da nan ya fara kamo wadansu
manyan kifaye.
Haka dai ya ci gaba su yana waige-waige da kalle-
kalle a cikin ruwan domin ya ga ta inda Kadan za ta bullo
masa, amma shiru kamar Malam ya ci Shirwa.
Su jaruma Suzaila da ke tsaitsaye a can bayansa a
gabar tekun kamar ka ce kyat su fita da gudu sai kyarma
jikinsu yake duk da kasancewar su manyan sadaukai masu
dakawa maza gumba a hannu.
Ashe duk wannan abu da ke faruwa tun dazu Kadan
ya ga sa'adda jarumi Imran ya shigo cikin kogin sa'adda ya
yi lambo a can karkashin kogin, amma da zarar ya durfafi
inda jarumi Imran din yake wannan su sai yaji kamar
gagarumar wuta ya durtafa wacce ke barazanar narkar da
dukkan jikinsa.
Wanann ta faru ne albarkacin addu'ar da jarumi Imran
ke karantawa a cikin ransa.
Lokacin da jarumi Imran ya sami dan lokaci mai
tsawo yana karanta wannan addu'a kuma yana ta yin su
abinsa ya zamana cewa komarsa ta fara nauyi saboda ta
cika da Kifi, sai ya tsaida yin su din domin ya fito daga
cikin kogin.
A sannan ne ya sha'afa ga barin ci gaba da karanta
addu'ar da ke bakinsa.
Ai kuwa sai wannan mugun Kada ya sami damar da
ya durfafi inda jarumi Imran ya ke.
Sai da ya rage bai fi saura kamu uku ba Imran ya iso
bakin gabar kogin sai kawai ya yi arba da wannan Kada daf
da shi ya taso sama yana mai wangame bakinsa da nufin ya
hadiyeshi.
Cikin tsananin zafin nania Imran. ya goce Kuma ya
Zare takobinsa ya afkawa Kadan suka kacame da
azababben yaki.
Duk sa'adda takobin Imran ta hadu da jikin Kadan sai
dai ka ga tartsatsin wuta na tashi tamkar karfe da karfe ne
suka hadu.
Babban abinda ya dagulewa Imran lissafi shi ne,
Takobin tasa ba ta iya yiwa Kadan lahanin komai kuma
dakushewa take dada yi.
Abu na biyu kuma shi ne tun da Imran yake gumurzu
da mutane , aljanu da dabbobi bai taba haduwa da halitta
tmai zafin nama ba kamar wannan Kada.
Saí da aka shafe kusan rabin sa'a ana artabu tsakanin
jarumi Imran da Kadar ya zamana cewa Kadan ya kasa
hallakashi, shima kuma ya kasa cutar da Kadan.
Duk wannan abu da ke faruwa su jarumi Muraisu na
tsaye a bakin gabar kogin suna kallo kawai an rasa wanda
Tai kaiwa Imran đauki.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face firgicewar da
jaruman suka yi sakamakon ganin girman wannan Kada
yami da kwarjininsa.
Ya yin da Imran ya fara gajiya shi kuwa Kadan yaci
caba da kai basa mugaycn hare-harc yana neman
hallakashi, ai hankalin Lushaira ya dugunzuma ainun, ba
ta san sa'adda ta fashe da kuka ba.
Ita kuwa jaruma Suzaila sai ta fusata ainun, bata san
sa'adda ta zare takobinta ba ta falfala da gudun tsiya izuwa
Cikin kogin tana mai rusa ihu ta kaiwa jarurni Imran dauki.
Koda ganin haka sai Muraisu da sauran jaruman ma
Suka sani kwarin guiwa suka uga izuwa cikin
kogin suka kaiwa jarumi Imran dauki gaba dayansu.
Koda Kadan ya ga an yi masa rubdugu sai ya fusata
ainun ya rinka kai mugayen hare-hare ta ko ina da bakinsa
da jelarsa.
Duk sa'adda ya daga katuwar jelar tasa ya kai duka da
ita, idan jaruman suka goce jclar ta fado cikin kogin sai ka
ji gaba dayan Kauyen ya yi girgiza saboda nauyin jelar
Kadar da karfin dukan ruwan da tayi.
Wani irin mugun ruri kuwa da Kadan ke yi sai da ya
firgita duk wani abu mai rai wanda ke bisa doron kasa da
karkashinta a wannan Nahiya.
Babu shiri mutane suka rinka toshe kunnuwansu,
dabbobi kuwa suka rinka shigewa cikin ramuka suna buya.
Ai kuwa ba a dade da fara wannan wumurzu ba
Kadan ya fara yiwa jarunan mummunar barna ya rinka yi
musu munanan raunika da jelarsa tamkar takobi aka sa ana
saransu, sai dai ka ga jikinsu na darewa jini na fallatsi suna
ihu suna zubcwa kasa Sumammu.
Kafin cikar wani lokaci gaba dayan dakarun da
Gimbiya Suzaila ta z0 da su sun zama gawa har da
wadannan tagwayen sadaukai.
Koda jaruma Suzaila ta ga mummunar barnar da
Kadan ya yi sai ta fusata ainun ta kurma uban ihu tana mai
Fashewa da kuka. Ba ta san sa'adda ta daka uban tsalle ba
sama ta dira akan gadon bayan Kadan ta daga takobinta
sama da hannu biyu da nufin ta soke Kadan.
Maimakon takobin ta nutse a cikin gadon bayan
Kadan sai ta 6alle ta rabu gida biyu.
Kafin Suzaila ta yi wani yunkuri tuni Kadan ya sa
jelarsa ya dokoto ta baya. Saboda karfin
AA Misau ke Magana
dukan sai da ta yi sama ta fado wajen kogin ta baje a kasa
sumammiya.
Al'amarin da ya firgita jarumi Muraisu da Husnaila ke
nan, zuciyoyinsu suka karaya, jarumi Imran ne kadai bai
karaya ba ya ci gaba da yakar Kadan ba tare da ya gaji ba
ko ya ja da baya.
A wannan lokaci Lushaira, Hasnalu na can gefe daya
a bakin gabar kogin suna kallon ikon Allah.
Lushaira tana ta karanta addu'ar da jarumi Imran ya
bata, shi kuwa Hasnalu jikinsa na ta karkarwa saboda
tsananin tsoro.
Gashi dai yana hango jaruma Suzaila a kwance can
gefe daya a sume, amma ya kasa kai ma ta dauki.
Ana cikin haka ne Kadan ya sake mangare Muraisu
da Husoaila, su ma suka sulale kasa sumammu, kuma suka
nutse izuwa karkashin kogin.
Koda jarumi Imran ya ga sauran shi kadai jal! a
gaban Kadan suna fafatawa sai ya kwalla kabbara da karfi
yana mai neman taimakon Allah. Ai kuwa sai ji ya yi ya
sami wani irin gagarumin karfi irin wanda bai taba ji ba a
jikinsa.
Take ya daka tsalle sama tamkar an cillashi daga
cikin baka ya soke idanun Kadan duka biyu da tsin in
takobinsa a lokaci guda.
Ai kuwa sai ga jinı yaa feshi la cikin idanun Kadar
tamkar idaniyar ruwa ta 6alle.
Nan fa Kadan ya kama mata-gun-gun yana birgima
akan kogin yana ruri
Nan da nan jinin Kadan ya yawaita akan kogin.
Sai da Kadan ya shafe kusan rabin sa'a yana
wannan mata-gun-gun sannan ya sandare ya zama gawa.
A sannan ne jarumi Imran ya yi nuts0 izuwa kasan
kogin ya dauko Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila ya fito
da su daga cikin kogin ya zubesu a bakin gaba ya shiga
danna cikinsu da bayansu ruwa na ta fitowa ta cikin
bakinsu.
A wannan lokaci ne su Lushaira na suka ruga wajen
jaruma Suzaila da ke kwance a sume suka kai ma ta dauki
suka fara tsayar da jinin da ke zuba a jikinta sannan suka
kama yi ma ta fifita.
Cikin ikon Allah kuwa ba a jima ba Suzaila da su
Muraisu suka farfado daga dogon suman da suka yi. Koda
ganin haka sai jarumi Imran ya mike tsaye cikin murna ya
daga kansa sama ya yiwa Allah godiya bisa wannan nasara
da ya samu.
A dai-dai wannan lokaci ne gawar wannan Kada ta
taso saman ruwa, kuma igiyar ruwa ta kadota izuwa bakin
gabar kogin.
Kawai sai jarumi Imran ya mike tsaye ya dauko wani
kaho da ke cikin aljihun igarsa ya busashi. Take sautin
karar kahon ya cika Kauyen gaba daya yana amsa kuwwa
izuwa cikin dazuzzuka.
Koda mutanen Kauyen suka jiyo sautin wannan kaho
sai suka zabura, maza da mata, nanya da yara suka rinka
falfalowa da gudu izuwa bakin kogin.
Duk wanda ya ZO ya ga gawar Wannan Kada sai ya
cika da tsananin al'ajabi ya kama yin kabbara yana godiya
ga Allah kuma yana yiwa jarumi Imran jinjina.
Sannan shima AA Misau aka shiga yi masa jinjina Saboda shine ya Fara saran wannan kada da har aka samu galaba akanta hhhh
Zamu dakata anan saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu rai da lafiya
Admin
AA Misau
Ke Magana
Ku bibiyemu a wannan shafukan
Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau
DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAU
BUSA A MUTU💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part D💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing by AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐
DUK WANDA YA ZO YA GA GAWAR WANNAN KADA SAI YA
CIKA DA TSANANIN AL'AJABI YA KAMA YIN KABBARA YANA GODIYA
GA ALLAH KUMA YANA YIWA JARUMI IMRAN JINJINA.
Al'amarin Muraisu, Suzaila da husnaila kuwa.
lokacin da suka farfado daga dogon suman da suka yi, suka
ga jarumi Imran a gaban gawar wannan Kada kuma suka ga
takobinsa ta yi faca-faca da jini sai suka cika da tsananin
mamaki suka sallama masa.
Duk su ukun sai jikinsu va yi sanyi kuma zuciyoyinsu
suka kama wasiwasin anya kuwa addinin Imran ba shí ne
addinin gaskiya ba?
Lokaci guda duk su ukun suka mike tsaye suka z0
gabansa suka yi masa jinjina.
Suzaila ta dubi gawarwakin jama'arta sai ta fashe da
kuka cikin tsananin takaici.
Ganin halin da ta shiga ne ya sa kowa ya kamu da
tausayinta har jarumi Imran ya zo daf da ita ya shiga
rarrashinta yana bata baki.
Wannan abu da jarumí Imran ya yi ma ta ba karamin
dadi da farin ciki ta ji ba, don haka sai ta daina kukan ta
dubeshi cikin murmushi mai taushi ta c, "Godiya a gareka
ya Sarkin jaruman duniya."
Cikin matukar mamakí Imran ya dubeta ya ce, "Haba
ya ke wannan 'yar Sarki saboda me za ki bani wannan
matsayi wanda ban cancanta da shi ba?
Ki sani cewa ita fa duniya fadi gareta, haka ma abin
cikinta yawa yareshi.
Ina mai tabbatar miki da cewa akwai jarumai da yawa
a cikin duniyar nan wadanda suka fini karfi da jarumtaka
nesa ba kusa ba,
Suzaila ta sake yin murmushi mai taushi a karo
biyu ta e, "Ai ruwan da ya doki mutum shi nc ruwa. Ban
ga jarumtakar sauran jaruman da kake fadi ba, ammna na ga
ta ka jarumtakar.
Na rantse da darajar iyayena ban taba ganin irin taka
jarumtakar ba.
Lokacin da aka fara gumurzu da wannan katon Kada
na ga ka shafe sama da rabin sa'a kana artabu da ita ba tare
da ta sami nasarar koda lakutar jikinka ba sai na tsorata da
al'amarinka kuma na sallama maka".
Koda jin wannan batu sai jarumi Imran ya yi dan
guntun murmushi ya ce, "Ai duk wannan jarumtaka da kika
ga na yi ba kokarina banc, taimako ne kawai daga
Ubangijina.
Shin yanzu wannan gagarumar nasara da Ubangijına
ya bani na sami nasarar hallaka wanann Kada ba ta isa ta sa
ku yi imani ba ku karbi addinina?"
Sa'adda Suzaila taji wannan tambaya sai ta yi shiru
tana mai sunkui da kanta kas ta ce, "Hakika wannan hujja
ta isa ta sa na yi imani da Ubangijinka, amma dai sai mun
gama jarraba gaskiyarka da adalcinka kamar yadda
Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila suka kuduri niyya.
Adalcinka na farko da nake son na gani shì ne, yadda
za ka karôi soyayyata kamar yadda ka karbi ta Gimbiya
Lushaira. Shin za ka sota nc fiye da ni?
Yadda duk kake tunanin cewa Lushaira ta kamu da
Sonka, to ni nawa son ya ninka na ta, kuma nima a shirye
nake da na kar6i wannan addini naka muddin za ka yi
alkawarin aurena.
Ka sani cewa kaine irin namijin da na dade in
farauta wanda nake mafarkin ya zamo abokin rayuwata.
Kai ne kadai wanda na ga ya dace da ni,
kuma ina ganin ccwa idan na rasaka hakura da aure ke
nan har abada"
Koda gama fadin hakan sai jaruma Suzaila ta tafi ta
bar jarumi Imran cikin tsananin damnuwa da fargaba bisa
kalmomin da ta gaya masa.
Muraisu da mahaifiyarsa kuwa, lokacin da suka koma
gefe daya, sai Muraisu ya dubeta ya ce, "Ya ke Ummina
yanzu dai kin ga irin gagarumar jarumtakar da Imran ya yi
da idanunki, kuma kowa ya tabbatar da cewa wannan
jarumtaka tasa ta fi karfin ta karfin dantse zallah dole sai
dai aga taimako daga wani Ubangiji.
Shin me kika yanke hukunci a cikin zuciyarki? Shin
Zamu karbi addinin jarumi Imran nc ko kuwa ba zamu
karba ba?"
Sa'adda IHusnaila taji wannan tambaya sai tayi ajiyar
Zuciya ta ce, "Ai ko zamu karbi addinin Imran sai bayan
mun cika burinmu mun kashe Sarki Imras da Sarki Huraisu
kuma ka hau karagar mulki ta Birnin Lairuf.
A sannan ne zamu sami nutsuwa da kwanciyar
hankali"
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya gyada kai ya ce,
"Ya ke Ummina da furko kin ce na sami soyayyar Lushaira
domin na ji inda mahaifinta ya boye wannan kwalba kum
yanzu gashi mun sanıt wanda zai je ya sato mana kwalbar,
me ya kamata na yi akan wannan al'amari?"
Koda jin wannan tambaya sai Husnaila tayi murmushi
ta ce,
"Ka
janye batun neman soyayyar Lushaira tunda mun
sami mafita.
AA Misau ke Magana
Yanzu kawai abinda muke jira shi ne dawowar manzo
Ashtar a gobe ko jibi domin mu ga amsar wasikar da na
aikawa Sarkin 6arayi Zaltar ibini Mazwar."
Koda Husnaila ta zo nan a zanccnta sai suka ga
maigari ya sa an datse kan wannan Kada an ciccibeshi an
tafi da shi izuwa cikin gari.
Nan take masunta suka yi ta shiga cikin kogin suka
kama sana'arsu ta yin su cikin tsananin farin ciki da mnurna.
Lokacin da jarumi Imran tare da maigari da sauran
jama'a suka iso ko far gidan maigari, sai Maigari ya sa aka
kafe kan wannan Kada domin ya zamana cewa ko daga can
nesa mutum ya durfafo Kauyen babú abinda zai fara atba
da shi face wannan kan Kada saboda ya zamo abin tarihi
abin tunawa.
A sannan ne jarumi Imran ya yi jawabi mai ratsa
zukata ga mutane bisa wannan nasara da Allah Ya bayar
aka kawar da mugun kadan, sannan kuma ya tabbatarwa da
mutanc cewar gobe kuma za a yı shiri a shiga dajin farauta
domin a kawar da wadannan mugayen abubuwa guda uku.
Ya ce za a fara ne da yakar wannan muguwar
Dodanniya mai hannaye guda goma sha biyu."
Nan dai aka sallami kowa, jama'a suka watse, suma
Su jarumi Imran sai suka tafi masaukinsu.
Har jaruma Suzaila ta Juya za ta tafi izuwa na ta
masaukin sai Gimbiya Lushaira ta dubeta cikin alamuin
matukar tausayi ta ce, "Ya ke kawata bai kamata ki tafi
masaukinki ba ki zauna ke kadai saboda kadaici-da tunani
Zai yi miki yawa tunda gaba dayan jama'arki sun hallaka
Saura ke kadai.
Zai fi kyau ki bimu namu masaukin ni da dan uwana
domin mu dcbe miki kewa"
busa a
Koda jin wannan batu sai hasnalu ya kamu da
matukar farin ciki.
Ita kuwa Suzaila sai ta dubi jarumi Imran cikin
damuwa, amma sai ya yi ma ta nuni da ta amince.
Imran ya dubi Lushaira ya ce, "Ya kamata fa ki bi
Ka'idojin addini.
Kin sani cewa Suzaila ba maharramar Hasnalu ba ce,
don haka kada ki bari su rinka kebanta ba tare da ke ba
kuma kema kanki bai kamata kí rinka kwana a daki daya
ba tare da hasnalu duk da ya kasance dan uwanki.
Abinda za a yi yanzu, ke da Suzaila ku rinka shiga
cikin daki kuna kwana tarc, shi kuma ya kwana a falo",
Gama fadin hakan ke da wuya sai jarumi Imran ya
juya ya nufi nasa masaukin.
Da isar Imran cikin dakinsa sai ya iske an kawo masa
abinci da abin sha. Imran ya zauna ya sa abincin a gaba,
amma sai ya kasa ci duk da cewar yana jin yunwa.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tunanin
kalmomin da jaruma Suzaila ta gaya masa.
Nan fa ya fara zancen zuci yana mai cewa;
nan"
"To ni yanzu ya Va zun yi da soyavyar mata biyu ke
Baya ga wannan kuma sai tunanin gumurzun da zai yi
gobe ya fado masa a rai, ya tuno da irin masifar dabbobi
ukun da aka yi masa bayani a cikin dajin farautar, sai
ZACiyarsa ta karaya sabodą ya tabbatar da cewa karfinsa da
dabararsa basu isa su sa ya sami nasarar kawar da mugayen
abubuwan uku ba sai dai taimakon Allah.
Lokacin da dare ya raba Kauyen yai tsit! ba a jin
sautin komai face na gyare da sauran tsuntsaye, sai ga
wadansu Dakaru su biyu kacal sun bayyana a cikin garin
sun yi shigar bakaken kaya kuma sun rufo fuskokinsu,
idanunsu ne kadai a bude.
Da yake dare ne mai duhu, ko kadan babu hasken
farin wata, sai wadannan dakaru suka saje da duhun gari, in
dai ba haskesu aka yi ba babu yadda mutum zai iya ganinsu
a lokacin da suke sanda suna durfafar gidan da aka sauki
Muraisu da mahaifiyarsa.
Wadannan dakaru biyu dai ba wani bane ya turoSu,
kuma ya nuna musu gidan da su Muraisu suke ba face
Attajiri Almas ibni Balmaru, wanda ya Zo Kauyen a
matsayn dan kasuwa ya kama cinikin fatu da yawa har
jama'a suka aminta da shi a cikin kwana daya da yini daya.
A haka ne ya sami damar gano gidan da aka sauke su
Muraisu. A wannan yammaci ya yi amfani da karfin sihirin
tsafi ya aikawa su Sarki Muraisu bayanin komai, su kuma
suka aiko da wadannan kwararrun dakaru wadanbda suka
kware a iya kisa.
Lokacin da Dakarun biyu nasu bakaken kaya suka
iso kofar gidan da su Muraisu ke ciki sai suka daka Tsalle
sama tamkar tsuntsaye suka dira akan saman rufin gidan
sannan suka diro kasa a farfajiyar gidan, suka kama sanda
da dube-dube.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda
dakarun suka sami damar shiga har cikin harabar gidan ba
farc da. masu gadin gidan Sun gansų ba
alhalin masu gadin sun kewaye giden ne kuma adadinsu ya
kai goma.
Koda dakarun biyu suka isa kofar dakin da su
Muraisu ke ciki sai suka cika da mamaki domin sun iske
kofar ne a bude ba a kulle ta ba.
Kawai sai suka kunna kai ciki. Suna shiga suka iske
shimfidu guda biyu alamar mutane ne a kwance sun lullube
jikinsu da mayafai.
Nan take dakarun biyu suka daga takubbansu biyu
suka caka a cikin shimfidun.
Bisa mamaki sai su ka ji sun caki tudun matasan kai.
A fusace suka waigo, sai suka yi arba da jarumi Imran
tsaye a gabansu rike da fitilar ice da kuma takobi a
hannunsa, sannan suka hango Muraisu da mahaifiyarsa a
can gefe daya suna ta shara barci abinsu basu ma san
abinda yake wakana ba.
Cikin zafin nama suka sake yunkurawa za su kaiwa
su Muraisu hari, amma sai Imran ya taresu aka ruguntsume
da azababben yaki.
Karar haduwar takubbansu ne ya sa Muraisu da
Husnaila suka farka daga barcin a firgicc.
Koda suka ga jarumi Imran yana yaki da wasu bakin
dakaru da suka 6oye fuskokinsu sai su ma suka mike tsaye
zumbur! Suka dauko takubbansu da nufin su taimaka masa,
amma sai ya yi musu nuni da su bari
Nan fa su Muraisu suka zuba ido suka zama 'yan
kallo.
Shi kansa jarumi Imran bai taba haduwa da
kwararrun mayaka irin wadannan masana sarrafa takobi
ba, domin wani irin rubdugun har suke kai
masa cikin bakin zafin nama ta sama da kasa, gefe da gefe.
In ba don shima yana da matukar zafin nama ba da tuni sun
sassarashi.
Tun ana yin wannan artabu a cikin daki sai da aka fito
waje cikin harabar gidan aka ci gaba da masifaffen yaki ya
zamana cewa dakarun biyu sun kasa koda lakutar jikin
Imran, shima ya kasa lakutar jikin dayansu, sannan kuma
ya hanasu zuwa kusa da su Muraisu bare su sami damar
hallakasu.
Muraisu da Husnaila suka fito daga cikin dakin suka
ci gaba da kallon wannan gumurzu suna al'ajabin irin
jarumtakar wadannan dakaru biyu.
Koda aka dan jima ana wannan dauki ba dadi ba tare
da fuskantar wata nasara ba sai dakarun biyu suka fusata
suka sauya salon fadan ya zamana cewa suna hadawa da
kai naushi da bugu hannu da kafa bayan kai sara.
Ai kuwa nan take daya daga cikinsu ya sami nasarar
naushin jarumi imran a fuska.
Yai baya taga-taga kamar zai fadi amma sai ya tirje
ya tsaya daram da kafafunsa.
Kawai sai Imran ya ji danshi akan lebensa. Yana
shafe leben da hannunsa sai ya ga jini. Al'amarin da yai
matukar fusatashi ke nan, shima sai ya sauya salon yakin
ya koma yin irin nasa salon.
Faruwar hakan ke da wuya sai fadan ya dada
rikicewa ya zamana cewa kowa yana jin jiki. Suna bugunsa
shima yana bugunsu.
A haka ne dakarun biyu suka sami nasarar yankar
Imran a lokaci guda. Yankan farko akan damtsen hannunsa
na hagu, yanka na biyu a kafadarsa.
Amma saboda juriya da jarumtaka irin ta Imran ko
yi
gezau bai ba, kawai sai ya dan ja da baya ya gyara
tsavuwa a lokacin da jini ke diga a jikinsa.
Su kuwa dakarun a jikin takubbansu ne jinin Imran ke điga.
Koda dakarun biyù suka ga sun sami wannan nasara
sai suka yi murmushi, a tunaninsu sun samo lagon jarumi
imran, don haka za su iya hallakashi yanzu farat daya.
Kawai sai dakarun biyu suka yi kukan Kura suka sake
afkawa Imran aka ruguntsume da sabon azabbaben yaki.
Wannan karon sai suka ga zafin naman Imran ya
ninka nasu, don haka da kyar suke iya kare harin da yake
kawo musu.
Nan da nan Imran ya rudasu kuma ya shammacesu ya
daka tsalle sama ya shallake tsawonsu. Kafin su waigo
baya su fuskanceshi tuni ya dankarawa kowannensu sara a
gadon bayansa.
A tare dakarun suka tsandara ihu suka fadi kasa
lokacin da jini ke zuba a bayan nasu.
Ba zato ba tsammani sai suka mkie tsaye zumbur!
Suka daka tsalle sama suka doki kirjin jarumi Imran yai
tsalle sama ya fadi can gefe daya.
Kafin ya mike tsaye sai suka cika wandunansu da
iska suka falfala da azababbcn gudu domin su tsere.
Ai kuwa sai Muraisu da Husnaila suka bi bayansu a
guje, aka kasa tscre.
A lokacin da dakarun da ke tsaron su Muraisu suka
farga da abinda ke faruwa suma sai suka bi bakin a guje.
Koda dakarun suka ga sun kasa cimma bakin dakarun
sai suka fara sakar musu harbi da kibiyoyi.
AA misau ke Magana
Cikin sa'a kuwa aka sami daya daga cikinsu a kafa ya
kurma ihu ya fadi kasa.
Har dayan ya tsaya da nufin ya janye wanda aka
harba din, sai ya ga shima za a kamashi sai ya take da gudu
don ya kai labari.
Lokacin da Badakaren wanda aka harba da kibiya ya
ga ba zai iya mikewa ba ya gudu kuma ya ga sauran kiris
su Muraisu su iso kansa sai ya zare wata wuka a jikinsa ya
kirba a cikinsa ya kashe kansa.
A dai-dai wannan lokaci ne su Muraisu suka iso
kansa tare da dakaru aka kewaye gawar Badakaren aka
tabbatar da cewa ya mutu.
A sannan ne ma jarumi Imran ya karaso wajen a guje.
Koda ya iske gawar wannan Badakare mai bakaken
tufafi sai ya kamu da tsananin bakin ciki da takaici.
Kawai sai ya hawaye fuskar Badakaren ya ga bai ma
taba ganin mai irin kamanninsa ba.
Imran ya caje jikin gawar da aljihunan rigarsa da
wandonsa, amma bai sami komai ba.
Kawai sai ya mike tsaye ya dubi Muraisu da Husnaila
ya ce, "Hakika kuna da sauran kwana a duniya da tuni
wadannan Dakaru sun hallakaku in ba don Allah Ya sa na
shigo gidan ba a wannan lokaci.
Wai shin waye ku ke zaton ya aiko wadannan
kwararrun masu kisa domin su hallakaku?"
Koda jin wannan tambaya sai Husnaila ta yi shiru
tana tunani.
Daga can sai ta dubi jarumi Imran ta ce, "Babu wanda
ya tanadi irin wadannan kwararrun mayaka a Nahiyar nan
kaf face Sarki Huraisu, saboda ya dade yana tanadi akan
cikar burinsa."
Imran yai ajiyar zuciya ya ce, "Na godewa Allah da
wadannan dakaru basu sami nasarar hallakaku ban
Da jin haka sai Muraisu da Husnaila suka durkusa a
gaban jarumi Imran bisa guiwoyinsu suka kama yi masa
godiya bisa ceton ransu da yi.
Imran ya yi murmushi ya ce, "Ai mutuwarku a yanzu
ba karamar asara ba ce a gareni, kuma rayuwarku za ta
kaini ga cimma babban burina".
Koda jin haka sai Muraisu da Husnaila suka cika da
mamaki, domin basu gano abinda yake nufi da wannan
jawabi nasa na karshe ba.
Nan dai dakaru suka dauke gawar wannan bakon
Badakare suka tafi da ita.
Jarumii Imran ya dubi su Muraisu ya ce, "Dole ne mu
kara karfin tsaro a Kauyen nan domin makiya ba za su
daina yunkurin kawo hari ba."
Nan dai kowa ya kama gabansa aka watse.
Kashe gari da safe bayan kowa ya kimtsa an yi shirin
tafiya Dajin Farauta sai aka taru a kofar gidan maigari
kamar yadda aka saba.
A sannan ne mai gari ya dubi jarumi Imran, Muraisu,
Husnaila da Suzaila ya ce, "Ya ku wadannan manyan
Jarumai ku yí sani cewa har abada ba zamu taba mancewa
da. ku ba bisa gudunmawar da ku ka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

1 Comments On BUSA A MUTU Book 7
avatar
walid

8 months ago

Reply

Is so sweet

Please Login or Register in order to submit comment