Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


wato goga balmus, koda ya ganshi sai jikinsa ya kama bari
shikuwa goga balmus saiya tuntsure da dariya yace
kaga idan kana son ka tsira da rayuwArka kawai
ka bani makullin miftahul dinar ka juya da baya
ka sani cewa yau shekarata dubu hudu ina labe
abayan taskar dukiyar saubatul azwas ina jiran ranar da za'ayi mantuwa abar kubar ajikin kofar kogon
amma ba'a taba yin mantuwabarba, sai gashi yau akaron banza
ta dauki kubar da hannunta ta baka, duk abinda ya faru tsakanin ka da Ita na gani amadubin tsafina
ina horonka daka gaggauta bani kubar nan kafin saubatul azwas tazo nan ta riskemu
kodajin wannan batu saì kalmus yayi ajiyar numfashi yace
tabdijan ainima shekarata dubu shida ina sauraron dazan
sami wannan damar ya za'ayi akaron banza kazo akaron banza ka kwace
tabbas idan kaga ka mallaki wannan kuba bana numfashi
kafin ya gama rufe baki tuni goga balmus ya zare takobinsa
ya kai masa wawan sara, nanfa suka kaure da matsiyacin fada asaman teku
sukayi wa junansu jina jina
sannan goga balmus ya sami nasarar rike kubar miftahul dinar
nanfa suka ci gaba da kokarin fizge kubar kowa yana ja in ja
kuma suka cigaba da saran juna
adaidai wannan lokacin ne na riskesu
saboda tsananin razana da ganina sai suka saki kubar
miftahul dinar kowannensu ya cika wandonssa da iska
itakuwa kubar miftahul dinar saita nutse acikin teku
nan fa na shiga cikin tekun nayita lalube iyakar kokarina amma ban gantaba
hakika nayi matukar mamakin batan kubar miftahul dinar acikin tekun
kuma nayi iyakar binciikena amadubin tsafi
amma bangano inda takeba
daga nan ne na dawo wajenki yake kawata tazubul luhucul
yanzu zan tafi dake izuwa dakin tsafina don mu zauna mucigaba da jiran
lokacinda ajalin sarakunan guda shida nan zaizo
don mu ci gaba da hada tsafin mu na gano inda sihirin tsafin yake
tazubul luhucul tayi murnushi tace
hakan yayi daidai kawata
nan take tazubul luhucul da saubatul azwas da izlis suka bace bat
tamkar basu taba wanzuwa ba
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN TAZUBUL LLUHUCUL DA KAWARTA SAUBATUL AZWAS 'YAR SARKIN ALJANU NA SIN
al'amarin su yarima sammaru kuwa yayinda aljanun nan shida wato hadiman boka hulumul bakahur
sukayì sama dasu suna tafiya ,suna tafiya acikin
gajimare sai da suka shafe sa'a bakwai cur suna tafiya sannan suka iso dajin farko
wanda ake kira baharul mahaful
da shigar su cikin dajin sai wata irin iska ta taso ta hana
aljanun shida motsi gaba daya bisa dole sukayo kasa
da niyyar su sauka bisa turba
koda sukayo kasa kasa sai sukayì arba da dubunnan dodannin
nan masu cin naman bil'adama har aljanun nan shida sun yunkura
da nufin su sakeyin sama sai suka ji an rurruke fuka fukansu
ashe dodannin ne da wannan aiki kafin aljanun su ankara dodannin sun fara yage fuka fukansu
tamkar ana yagar fallen littafi,
nanfa hankalin aljanun danasu yarima sammaru ya dugunzuma
cikin zafin nama gimbiya ashwarya ta zare ta takobinta ta kutsa kai cikin dodannin ta hausu da sara da suka
koda ganin haka sai su yarima sammaru sukayì yadda tayi
nanfa wuri ya hargitse dodannin suka rinka ruri mai ban tsoro
suna kokarin cafke jaruman biyar da kuma boka karluz
ko kadan basu damu dasu aljani guluz ba
domin sun ciccire musu fuka fukai dai dai sun kasa tashi, bare su tafuka komai
nanfa aka cigaba da dauki ba dadi
shima boka karluz a wannan rana ya nuna cewa shi namijine
domin ya manta da batun tsafi sai gididdiba dodannin ya dinga yi da kaifin takobinsa
duk inda yasa kai saidai kaga suna zubewa kasa matattu
babban abinda yafi tayarwa da su yarima sammaru hankali shine
kashe dodannin sukeyi amma kamar dadosu akeyi
tabbas idan aka ci gaba da wannan yaki zuwa wani lokaci karfin su
sammaru zai kare dodannin su cinyesu
aikuwa ana cikin hakane daya daga cikin dodannin ya sami nasarar kama hannun yarima lubaika yasa acikin bakinsa
nan take ya gutsure masa hannunsa iya gaba
lubaika y kurma ihu, lokacinda sammaru yaji ihun lubaiku ya hanga yaga abindaya faru
saiyayi tsalle sama ya dinga taka kan dodannin yana gudu
harya iso wajen lubaiku ,cikin hanzari ya zaro kuttun maganin nan da boka hulumul bakahur
ya bashi ya kwarara akan raunin dungulmin hannun
nantake jini ya tsaya, shima lubaiku yaci gaba da saran dodannin da hannu daya cikin fushi
duk wannan gumurzu da akeyi gimbiya ashwarya nata fafatawane tana neman hanyar da zasu kubuta
daga can sai dabara ta fado mata ta ruga da gudu
tana gudun tana hadawa da saran dodannin
koda ganin haka sai su yarima sammaru sukayi kiyi da ita
sai gashi kuwa sun same waraka domin wadannan dodannin basa iyayin gudu sosai
nan da nan jaruman suka tserewa dodannin suka barsu abaya nesa
bisa dole suka diana binsu
a sannan ne suka tsaya su shidan sukayì cirko cirko suna haki da kallon junansu
kawai ba tareda dayansu yace uffan baa
can sai yarima lauhana yace
yanzu menene abinyi shin zaku koma da bayane
mu karbo ababan hawanmu su guluz ko kuwa muci gaba gaba da tafiya da kafafunmu?
kodajin wannan tambaya sai gimbiya ashwarya tace
haba wace irin magana kake haka shin ka mantane
akwai wasu dodannin acikin dajin nan
domin sun kasance kabila kabila
kuma dolene fa mayo kwana uku acikin jejin nan kafin mu fita daga cikinsa
haka boka hulumul bakahur ya gaya mana
ai babu abindaya fi mana kamar mu cigaba da tafiya
adaidai wannan lokaci ne yarima lubaiku ya dubi dungulmin hannun sa
sai takaici ya turnukenshi take idanunsa suka ciko da kwalla
ya fara zubar da hawaye
al'amarin daya jefa gaba dayansu cikin tausayinsa kenan
ashwarya ta mike tsaye daga inda inda take zaune
ta dawo inda lubaiku yake ta durkusa daf dashi
sannan ta dafa kafadarsa tace yakai abokina
ka kasance mai rungumar kaddara bisa wannan al'amari daya faru
domin rai ba abakin komai yakeba indai akwai biyan bukata
ka sani cewa muma nan duk bamu tsiraba daga abin daya sameka ba
babu mamakima wasun mu su rasa Rayuwarsu gaba daya,
abinda nakeso dakai shine ka jajurce kasa aranka cewa lallai sai ka sami nasarar debo wannan magani a taskar tsafi
haka dai gimbiya ashwarya ta cigaba da baiwa lubaiku kwarin gwuiwa her yaji
baya shakkar komai a ransa
kuma yaji ya kagu da aci gaba da tafiya
nantake suka mike gaba dayansu
da nufin nausawa cikin daji
kawai sai suka hango wasu tsuntsaye abayansu
sun taho ta sama
yayinda tsuntsayen ke kara kusanto su suna kara girma
koda sukazo kusa sai sukaga ashe su aljani guluz ne kowannensu na kada
fukafuki daya babu daya
cikin farin ciki su yarima sammaru suka ruga wajen su guluz suka taryesu,
bayan sun sauka sai yarima sammaru ya dubi guluz yyac
yaya akayi kuka tsira daga hannun mugayen dodannin nan?
sa'adda guluz yaji wannan tambaya sai yayi yake yace
kasan ance mai rabon yaga badi sai ya gani
ai lokacinda kuka fita da gudu kuka tserewa dodannin suma biyoku sukayì dayansu bai sauraba awajenmu
koda naga sun tafi sun barmu kuma dukkan mu ajigace muke sakamakon yagewar fukafukan mu da zubar jinin da muke tabbas babu wanda zai iya kyakkyawan motsi acikin mu
a wannan lokaci
cikin karfin hali na fiddo irin ruwan maganin nan da shugabana hulumul bakahur ya baka
na dinga jan jiki ina zubawa 'yan uwana ajikin raunikansu
saida n tabbatar da cewa kowannenmu ya warke
sannan na zubawa kaina, nan take muka tashi sama muka kewaye ta bayan hanyarda dodannin sukabi mukazo nan muka riskeku
sa'adda guluz yazo nan azancensa sai yarima sammaru yayi murmushi yace
amma dai ka iya ganganci
yanzu inda ruwan maganin ya kare baka samuba ya zakayi? da shikenan sai yan uwanka su tafi su barka ka mutu abanza tunda duk ka fisu hikima da kokari.
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
Mu hadu a part H don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART H ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
GORON JUMA'A ❤️🙏
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.....
Guluz yayi dariya yace
aikoda maganin ya kare nasan 'yan uwana
bazasu tafi su barni ba
kasan muna da matukar hadin kai
da dai su tafi su barni gwara su tsaya duk
abinda
zai sameni ya samesu gaba daya
kodajin haka sai gimbiya ashwarya ta tsoma
baki acikin zancen tace
au kana nufin ku aljanu bakwa tsoron mutuwa
nikam ina ganin idan sukaga wani bala'ìn zasu
iya guduwa su barka
guluz ya sake bushewa da dariya yace
aimu aljanu muna da son junanmu
fiye da mutane
kuma munsan mahimmancin alkawari bama
karya shi
ku kuwa mutane akan dukiya ma kuna iya karya
alkawari ko kuci amana
wannan batu ba karamin haushi ya baiwa
gimbiya ashwarya ba
ta bude baki zata mai d raddi sai yarima
sammaru
ya tari numfashinta da cewa
hirar nan ta isa haka kuzo muci gaba da tafiya
cikin hanzari ya haye bayan aljani guluz ya zauna
koda ganin haka sai dukkansu suka hau kan
sauran aljanun
alokaci guda aljanun shida suka tashi sama
tafiyar rabin sa'a sukayì kacal suka iso nahiyar
wadansu manyan dodanni wadanda suka
kasance dogaye zankala zankala
saboda tsawon su duk sun kere bishiyoyin dajin
da tsaunika
koda wadannan dodannin suka hango su
yarima sammaru
asama 'yan kanana kamaI'm tsuntsaye zasu
gifta
ta samansu sai suka daga kawunansu sama
suka wangame bakunansu suka hura musu
wata iska mai tsananin karfi wacce inda acikin
garice zata iya rushe gidaje.
kuma zata iya daukar mutane ta rinka yawo
dasu asama
nan da nan gagarumar iskar ta birkita hankalin
su yarima sammaru da
aljanun shida ya zamana sun kasa gaba sun
kasa baya
kuma sai gware suke da juna, tabbas idan aka
kara 'yan dakiku ahaka
zasu iya hallaka, cikin karaji yarima sammaru ya
baiwa su guluz umarnin saukowa kasa
nantake kuwa suka bi umarnin
kafin su iso kan turba tuni jaruman shida sun
zare takubbansu
suna dira kasa wuri ya hautsine da rurin mazaje
dana dodannin
wannan karon sai su yarima sammaru suka
gane ruwa ba sa'an kwando bane
domin saran dodannin suke amma
kamar a banza domin dodannin sun kasance
masu tsananin juriya
karfi da taurin kai
nanfa dodannin suka kuntata musu yazamana
su
yarima sammaru basa iya komai sai kokarin kare
kai
ana cikin hakane wani dodo ya kama kafar
yarima yauhana ya
karyata da karfin tsiya
yauhana ya kwarara uban ihu cikin dimaucewa
kafin yauhana yayi wani yunkuri tuni dodon
ya saka kafar gaba daya abakinsa ya gutsireta
da bakinsa
ya kama ci kamar mutum yana asuwaki da
cinyar kaza
nantake yauhana ya sulale kasa sumamme
koda ganin abindaya faru sai yarima sammaru
ya
fusata ya daka tsalle sama tun a saman yarima
sammaru ya
zare wata rantsatstsiyar wuka kawai saiya duro
akan dodonnan dake cin kafar yauhan
take ya luma masa rantsatstsiyar wukar a
tsakiyar kansa
kuma ya zareta da karfin tsiya take jini ya kama
tsartuwa asama kamar an fasa goran ruwa
nanfa dodon ya kama make make da ruri ya fadi
nan
ya tashi can har rai yayi halinsa
wannan ce damar da jaruman shida suka samu
suka gano makasar dodannin
don haka suka ci gaba da saransu da sukarsu
aka
kawai sai gani akayi dodannin suna zubewa
kasa matattu
a wannan lokacin ne yarima sammaru ya samu
dama y kwararawa yarima lauhana
wannan ruwan maganin
a karshen cinyar guntulalliya
take wajen ya bushe kamar anfi shekara da
gutsure kafar
adaidai wannan lokacin ne wasu dodanni suka
kawowa yauhana sura don su karasa cinyeshi
cikin zafin nama sammaru ya daukeshi ya
azashi abayansa
sannan ya kaiwa dodannin sara aka alokaci
guda
cikin sa'a kuwa ya raba musu kawuna Kamar an
datsa kabewa
gida biyu take suka zube kasa matattu
nanfa aka cigaba da ragargazar dodannin nan
saida aka shafe sa'a uku
ana gumurzu sannan aka karar da dodannin
awannan yaki babu wanda bai samu rauni ajikin
sa ba
sama da guda uku
yarima sammaru ne kadai ya sami rauni biyu
daya akafarsa wani dodo ya yankeshi da farcen
hannu
daya kuwa a cinyarsa aka caka masa kahon ka
wanda saidaya durkusa kasa yana mai ihu
amma cikin tsananin juriya ya sake mikewa
tsaye
yaci gaba da sara da suka her aka gama yakin
yarima lauhana
yana sabe akafadar yarima sammaru kuma
asume
gimbiya ashwarya ce kadai tayi jarumtaka
kwatankwacin irin wacce
yarima sammaru yayi, amma itama ta sami rauni
abayan kafarta
saikuma larbuz wanda ya taka mahimmiyar rawa
awannan yaki
gaba dayan su dai babu wanda baisha wahala
da samun raunika da yawaba, don har jirine ya
rinka dibarsu saida
sammaru ya kai masa daukin magani
da gaggawa sannan ya dawo hayyacinsa
bayan an gama yakinne kowa ya sharbe akasa
harda suma aljanun shida
sai yarima sammaru ya bisu daya bayan daya ya
saka
musu magani aci wukansu
saidaya gama da kowa sannan yaje kan gimbiya
ashwarya wacce
take zaune agefe guda akan wani karamin dutse
koda yazo gareta ya kalleta sama da kasa baiga
wani rauniba
saiya juya da nufin tafiya
ya zaka tafi baka samini magani ba?
ta tambaya tana murmushi
cikin mamaki yarima sammaru ya waigo ya
dubeta yace
ai banga rauni ko daya ba ajikinki
ashwarya tace baka duba sosai bane
zagayo bayana ka kwaye rigata ka ga ʀɑuɳi
batareda d gardama ba yarima sammaru ya sa
hannunsa zai kwaye rigarta sai hannunsa
ya kama kakkarwa, bakomai ne ya haddasa
hakanba
face ganin kyakkyawan surar jikinta da kuma
fatarta
mai tsananin haske da laushi, duk da cewar
raunin dake bayan nata na da dan girma
amma bai razana sammaru ba kamar yadda
kyakkyawan jikinta
ya razanashi, kamar tasan halin daya shiga sai
tace
me kake jirane ko kuwa kaima zuciyar ragwaye
gareka ciwon y firgita ka
sammaru yayi murmushi yace
ai abin tsoro baya firgita mazajen kwarai
saidai abin mamaki
hakadai ya daure ya zuba mata maganin
hannunsa na karkarwa
bayan ya gama da ita saiya juya don ta koma
inda yake
ba zato ba tsammani saiyaji ankira sunansa
cikin mamaki ya waigo suka dubi juna tana mai
murmushi agareshi
zauna nan abinda tace dashi kenan kawai
sammaru ya zauna
yana mai mamakin hakan kawai saita karbi
kuttun maganin
dake hannunsa ta fara zubawa akan rauninsa
dake cinya
gaba daya. jaruman nan kuwa da aljanun nan
shida sai suka zuba musu ido
tuni awannan lokaci kishi ya turnuke yarima
lubaiku da larbuz
idan na barka kasa maganin da kanka
banyi maka adalciba
domin kai kadai kasawa kowa maganin nan
kamata yayi kaima ayi maka kara
koda jin wannan batu sai sammaru ya yi
murmushi yace
nagode ammafa inason zama da mutumin dake
da kara
kuma inason zama da mace mai zuciyar maza
ashwarya ta bushe da dariya sannan tace
daina kodani haka karkasa
kaina y fashe in banda abinka ina abin yake
ai gadai mAce can mai zuciyar maza tana
kafsawa dasu
cikin mamaki sammaru yace
wakenan kike nufi?
gimbiya fauwaz mana
duk lokacinda na tunoda lokacinda boka
hulumul bakahur
ya nuna mana ita amadubin tsafinsa sa'adda
take ragargazar maza
sai naji kishi ya kamani tabbas fauwaza ta fini
jarumtaka
da kyau nesa ba kusaba
ace nice ita da dolene na shahara ko ina acikin
duniya
awannan zamani, sammaru yayi murmushi yace
ai yanzu ma zaki shahara aduniya idan her kika
sami nasarar
shiga cciki kogon muddarul ikisina kika debo
ruwan
tsumin tsafin bokanya tazubul luhucul acan
taskar tsafinta
kodajin haka sai ashwarya tayi ajiyar zuciya tace
tana zaton dayanmu zai iya cika wannan buri
ka sani cewa naji daga bakin manyan bokayen
duniya cewa
fiye da shekaru dubu baya
babu wani mahaluki daya taba shiga cikinsa ya
fito araye
don haka ba shigar bace wahalaba fitowarce
wahala
sammaru ya jinjina kai yace
hakika zancenki dutsene, to amma ai ance
faduwar gaba asarar namijine
dadai mu zauna mu zuba ido muna gani
iyayenmu su hallaka
gwara muma mu hallaka kan kokarin cetonsu
kafin ashwarya tace wani abu saiga boka karluz
ya taho garesu
da zuwa ya durkusa agabansu sannan ya fiddo
madubinsa na tsafi ya ajiye agabansu
yace, yakai sammaru jagoran tafiya kayi sani
cewa
zan iya nuna maka sauran hadarin dake
gabanmu acikin dajin nan yanzu anan wurin
cikin murna sammaru yace
maza ka nuna mini don musan matakin da zamu
dauka
nantake karluz ya shafi madubin tsafinsa
saiga hoton wadansu dodannin acan gaba
wadanda sunfi n baya girma daban tsoro
madubin ya sake nuna wasu acan gaba suma
sunfi na baya harsaida madubin ya nuna
kabilar dodanni kala biyar wato idan aka hada
dana baya
sunzama kabila bakwai cif cif koda gama ganin
su
sai hankalin sammaru dana ashwarya ya
dugunzuma
nan take sammaru yakira su lubaiku suma suka
gani
awannan lokaci ne yarima yauhana ya farka
daga dogon suman
da yayi
koda yaga kafarsa ta hagu a guntule saiya rusa
ihu
ya fashe da kuka, da kyar sammaru ya
rarrasheshi
ya daina kukan bayan nan sai sammaru ya dubi
jaruman duka
daya bayan daya yace.
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
MU HADU A PART i DOMIN JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART I ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA....
Yɑku abokan tafiyata ina mai sanar daku cewa gwagwarmayar da muka sha abaya tamkar sharar fage ce akan wacce zamu tunkara agabanmu
ina mai rokonmu damu kara damu kara zage dantse
mucire tsoro da fargabar komai domin matsoraci baya zama gwani
ko wanene ko dan wa
musa aranmu cewa ko mu mutu ko muyi rai
sai mun kai gaci, ku tuna cewa akwai sauran
aiki agabanmu don haka zamanmu anan tamkar hutun jaki da kaya aka ne
ina mai umartarmu damu tashi mu kara gaba
ba zamu tsaya ako'ina ba harsai mun karar da dukkannin dodannin dake cikin wannan daji
koda sammaru ya zo nan azancensa saiya zare takobinsa ya dagata sama
yayi kururuwa
irin wacce ke firgita maza afilin daga
nantake kururuwar tasa
ta cika dajin harda amsa kuwwa izuwa nesa
al'amarin daya janyo hankalin sauran kabilun dodannin
kenan suka san cewa lallai yau sunada baki
don haka sai kwadayi ya kamasu, suka fara tande baki
suna dalalar da yawu akasa,
lokacinda yarima sammaru suka gama rurinsu
don karawa kansu kaimi da kuzari sai suka dane bayansu guluz
sukaci gaba da tafiya a sama cikin tsananin gudu
aikuwa cikin kankanin lokaci suka riski kabilar dodanni ta uku
ana haduwa yaki ya barke akayi dauki ba dadi
wohohoho
awannan rana rayuka sun salwanta, jini kuwa ya malala
don saida ya zamana koramai da fadamomin dajin
sun rine sun zama jini maimakon ruwa
awannan gumurzun da akayi ne da kabilar dodannin ta uku yarima lubaiku ya rasa rayuwarsa
domin saida dodannin sukayì walima da sassan jikinsa
ba'a samu komai ba daga barin jikinsa hatta gashin kansa
saida suka cinye tabbas awannan lokaci su yarima sammaru
sunga tashin hankali irin wanda basu taba ganiba
alokcinne aka cirewa boka karluz kunnuwansa aka cinye
shikuwa yarima larbuz saida ya rasa 'yan yatsun hannunsa na hugu
babu wanda ya bada mamaki kamar yarima lauhana domin
duk da kasancewar kafarsa daya zamewa dodannin alakakai
yayi musu muguwar barna domin saidaya kashe sama da guda dubu uku shi kadai
kuma har aka gama yakin saidaya sami rauni ajikinsa
inbanda sammaru da ashwarya babu wanda bai samu mugun rauni ba a wannan yakin
bayan an gama yakin ne su duka suka zauna suka fashe da kuka
bisa tunawa da irin mutuwar da yarima lubaiku yayi
gaba dayansu sai jikinsu yayi sanyi hankalinsu ya dugunzuma
kowa zuciyar sa ta fitar da rai ga rayuwa
kuma sukayì nadamar baro kasashensu da sukayì
don cika wannan buri nasu mai matukar hadari
anan ne dare ya riskesu kuma yunwa d kishirwa
ta addabesu bisa dole aka kunna wuta aka zagayeta anajin dumi
saboda hunturun sanyin dake kadawa sannan aka fara
tunanin yadda za'a samu abinci da ruwan sha
tunda shi kansa ruwan dake dajin ya zama jini
anacikin yin shawarane boka karluz ya dubi aljani guluz yace
kune aljanu ina dabara? ko zakuje kudan zagaya
ku samo mana abinci da abinsha?
guluz yace haba bakaji kunyaba ka fadi haka
ka tuna cewa kai bokane zaka iyayin tsafi abinci da abinsha su bayyana nantake
karluz ya daka masa harara yace
baka da hankali, ai kasanma idan na mayi tsafin wani aljaninne zai kawo
kasan kuwa babu wani aljani dazai iya shigowa
cikin jejin nan don ya tabbatar da cewa halaka zaiyi
ai kawai ku cire tsoron komai kuje ku samo mana abinci
abinci dai idan kukayi hakuri mun kusa rabuwa daku
tunda saura jeji biyu kacal mu iso takiyar duniyar nan
cciki damuwa da tsoro boka guluz yace
shikenan
munyarda zamuje mu nemo muku abinci amma ka duba
mana cikin madubin tsafinka inda zamuje mu nemo muku abinci
batareda munsha wahalaba ko mu afka cikin bala'i
boka karluz ya bushe da dariya yace
oh! waiyau aljani ne da tsoro kamar farar kura
nandanan ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiye a kasa
ya shafeshi
saiga hoton wata katuwar barewa kwance acikin wani rami
acan gaba kadan daga inda suke zaune yanzu
kuma abayan ramin wata korama ruwa na gudu
acikinta mai kyau da haske wanda jini bai gurbatashiba
agaba daya harabar wajen babu alamar dodanni
koda ganin haka sai aljani guluz ya dubi aljani amzil
da hurus yace maza kuje ku dauko barewarnan
kuma ku debo ruwan koramar nan isasshe
ku kawo musu, kafin ya gama rufe bakinsa
tuni su amzil sun bace, saida dakika dari uku da sittin ta wuce
amma basu dawoba, al'amarin daya tayarda hankalin kowa kenan
gimbiya ashwarya tace
kai jama'a ruwafa baya tsami banza
lallai akwai abindaya faru ga su amzil donya kamata ace sun dawo
tun dazu, kodajin haka sai boka karluz yace
kwarai kuwa hakane kinyi gaskiya
amma bara mu duba muga halinda akeciki
cikin sauri ya sake fiddo madubin tsafinsa ya ajiye akasa ya shafe shi
saiga hoton aljani amzil shikadai
asama daukeda barewa da kumA ruwa
acikin babbar batta
duk jikinsa jina jina yana tafe yana kayi asaman kamar zai fado kasa
koda ganin haka sai Hankalin su ta sake dugunzuma
ba'a jimaba saiga aljani amzil ya fado agabansu
yana kakarin mutuwa nanfa kowa ya manta da batun yunwa da kishirwa
akazo kan amzil aka tsaya
aljani guluz ya tallafo kan amzil ya dora akan cinyarsa
yana mai kallon fuskarsa yace
yakai dan uwana mai ya faru gareku kaida hurus na ganka cikin wannan hali
cciki matukar karfin hali amzil yace
yakai guluz kayi sani cewa alokacinda
muka shiga cikin kogon nan
don kama barewarnan bamu fuskanci matsalar komai ba
har muka fyadeta ta mutu sai bayan mun fito daga cikin kogon
sai kawai mukaga wasu irin dodanni sunyi mana kawanya
kafin mu yunkura sunfara kai mana cafka
mukuwa saimuka fara kokarin ceton kanmu
inaji ina gani suka kama hurus suka dinga yaga jikinsa
sunaci saida suka cinyeshi tas, nikuwa dama iyakar karfina nake yakarsu
dayake su biyarne kacal saina zame musu alakakai
kasancewar nafisu karfi saida suka kusan hallakani
dakyar ma samu na tsere musu, koda yake tsiran banza nayi don na tabbatar mutuwa zanyi
yakai guluz ina mai rokonka daka kula da matata
idan har kana da sauran kwana aduniya kuma ka sami damar komawa gida
kasani cewa matata tana da tsohon ciki
haihuwa yau ko gobe
idan ta haihu lafiya kuma ta sami da namiji kasa masa sunana
idan kuwa macece asamata suna muddarul ikisina
don ta zamo abin tunawa da iyakar rayuwata
koda amzil yazo nan azancensa sai idanunsa
suka kafe, komai na jikinsa ya daina motsi
guluz ya rungume gawar amzil ya fashe da kuka
al'amarin daya karya zuciyar sauran aljanun kenan
wato karmash, karfil, da azgar suma suka kama kuka
saida aka dan jima ana alhilin wannan mutuwa ta aljani amzil
sannan aka gasa naman barewar nan kowa yaci ya koshi
akasha ruwa, daga nan sai yarima sammaru ya tashi
ya koma gefe daya ya zauna yana mai tunanin gida
koda ya tuno da mahaifinsa sarki alyasil buhus
ya tuno halin daya baroshi na kamuwa da cutar mutuwar rabin jiki
saiya fashe da kuka, sammaru ya sake tuno lokacinda mahaifiyarsa
ta rungumeshi tana kuka
sa'adda da suke bankwanan rabuwa
kawai saiya rushe da kuka
al'amarin daya jefa gimbiya ashwarya cikin tausayi kenan
ta taho ga sammaru da zuwa ta zauna dafdashi
ba tareda ta kalli fuskarsa ba tace
yakai abokina kayi sani cewa
aduniya babu abindaya fi dadi sama da zama da masoyi
tabbas nasan kana tunanin iyayenka ne
'yan uwanka, danginka da kasarsu
shine sanadin wannan kuka naka
kayi sani cewa nima na kasance acikin irin wannan tunani naka
kuma duk da kasancewata 'ya mace ban bari
kukana ya fito filiba
amma nayi na zuci harnagaji, inason mu kasance masu hakuri
domin ya zama wajibi agaremu
koda ashwarya tazo nan azancenta sai yarima sammaru ya dago kai
ya dubeta inda yaga kwallah cike a idanunta
nan take yaji tausayi da kaunarta sun dabaibaye zuciyarsa
baisan sa'adda ya saki murmushiba agareta
jim kadan sukayi shiru su biyu dayansu bai ce uffan ba
daga can sai sammaru ya katse shirun
da cewa
yake kawata hakika tun lokacinda na baro gida naji ina cikin kadaici
fargaba da rashin kwanciyar hankali
amma kuma sanda na farajin kalamanki sai naji duk wadannan abubuwa sunyi kaura daga gareni
aduk sa'adda na kalleki ko naji muryarki
sainaji kamar ina cikin gidanmu ne
tareda iyayena da 'yan uwana
tabbas duk wanda ya sami mace kamarki mai dadadan kalamai
masu tausasa zuciya ya gama morewa don ko abakin
kura yake bazaiyi fargaba da bakin ciki ba
koda yarima sammaru yazonan azancensa sai ashwarya taji wani irin farinciki ya baibayeta
take itama taji ta kamu da tsananin kaunarsa
batasan sa'adda ta kura masa ido ba
harsuka shagala da kallon juna
duk wannan abu dake faruwa larbuz, yauhana, da karluz nadaga can gefe suna kallo.
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
MU HADU A PART J DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️
Najibullahi Muhammad
#LEGENDs.
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART J ❤️🥰
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
CIGABAN LITTAFIN....
Kuma dukkaninsu sun fahimci cewa lallai soyayya
tashiga tsakanin matasan biyu kai hatta su aljani guluz sun
fahimci hakan, suma kuma matasan biyun sunsan suna son juna
amma nauyin baki ya hana kowannensu yayi ɓɑyɑɳi
hakadai sukaci gaba da hira har dare ya raba sosai
inda yarima sammaru ya umarci su aljani guluz
dasuyi musu gadi su kuma suka kwanta sukayì barci
basu farkaba saida gari ya waye her gAri yayi haske rana ta fito
sakamakon tsananin gajiyar dake tare dasu
bayan sun farka ne kowa ya wanke fuskarsa
sannan aka ci ragowar naman barewar jiya akasha ruwa
bayan an kimtsa sai yarima sammaru ya dubesu
daya bayan daya yace
yaku 'yan uwana abokan tafiya inamaiyi muku tuni da cewa adafa mu goma shabiyune
muke wannan tafiya amma yanzu mun zamo saura tara
don haka ya zama wajibi agaremu mm zage damtse
muyi iya yinmu, yanzu sai kowannenmu ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On MATSATSUBI BOOK 3
avatar
abasu-kala

9 months ago

Reply

Good really enjoy the book waiting for Miftahul Zarbil

Please Login or Register in order to submit comment