Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gunki tamkar almajiri agaban malaminsa
shamharu na cikin bincikensa saiyaji motsi
acikin aljihun rigarsa
al'amarin daya bashi mamaki kenan
domin asaninsa bai ajiye komaiba acikin aljihun
nasa
kawai saiyha zura hannunsa a cikin aljihun mai
zurfin rijiya gaba dubu
ya kwaso abinda ke aljihun nasa ya watsa bisa
bisa tebur din dake gabansa
bisa mamaki saiyaga
ashe boka jinsan,boka sulbaini,markahus sabus
,aljni durfus,da bokanya samaratune
sai asannan shamharu
ya tuno da cewa shida kansa ya watsasu acikin
aljihun nasa.
shamharu ya dubesu daya bayan daya dukda
sun kasance
mitsi mitsi agabansa sannan ya bushe da
dariya.yace
yanzu ku nan atunaninku zaku iya ja dani?
shiyasa kuke tunanin yadda saku aiko aljani
balbus yazo har nan ya sato muku addar tsafi
hakika kun tafka babban kuskure wanda zai
zamo muku abin nadama
lu'umanu ya karewa markahus sabus kallo
sannan ya dubi sarki shamharu yace
ya shugaba na
ai wannan markahus sabus ne wanda y nemi
matata fatisa
nasa aka sashi acikin akwatin karfe
aka kulle acan kurkuna dake karkashin kasa
shamharu yace kwarai kuwa shine
abinda baka saniba ai su jafar je suka fito dashi
suka turashi yaje ya samo musu kubar miftahul
zarbil
har suka sami narar bude kundun tsatsuba
kai makahus sabus k cika tsinanne,matsiyaci
domin .duk bala'in nan dana shiga kaine sanadi
inda bakaje ka dauko kubar mitahul zarbil ba
da yanzu hankali na akwance yake lallai kaine k
bankada sirrina ga duniya
idan kuwa kanason ka tsira da rayuwarka
dolene ka sake rufe wannan sirrin
kodajin haka sai markahus sabus ya rissina
agaban shamharu
yace
ya shugaba na idan kwai yadda zanyi na rufe
wannan sirri nka zanyi ko menene
koda kuwa zan rasa rayuwata
shamharu ya tuntsure da dariya sannan yace
hakika akwai yadda zaka rufe wannan sirri nawa
zan turaku ku tafi izuw aiwatar da wani aiki ku
hudu banda mahaifiyarka samaratu
damin zan tsareta anan
harsai kun sami nasara kun dawo gareni
sannan n sake ku gaba daya
ku koma duniyarku
idan kuwa bakuyi nasara ba zan kashe
mahifiyarka
sannan kuma na hallakku gabA daya
kodajin haka saihankalin markahs sabus
ya tashi
ya rasa abin dake masa dadi aduniya
lu'umanu ya dubshi yace
haba jarumi uban jarumai ka tunaa cewa kaine
ka kara da dodo kiryanu
harka debo tsumin tsafinsa
kaine aljanin da baisam tsoro ba
kuma kaine sarkin sa'a da nasara wanda bai san
bacin ranaba
markashu sabus yayi yake yace
haba lu'umanu
ai indai jaruntaka nake takama da ita da
tsagwaron karfi ban kaika ba
meyasa kai baka tafi aiwatar da wannan aiki ba
wanda za'atura mu yi?
lu'umanu yayi shiru ɓaice komaiba don baisan
amsaar da zai bayarba
shikuwa shamharu saiya busheda dariya
yace
wannan matsalar kuce ku biyu
kai darfus nasan cewa kafi jinshan,sulbaini da
markahussabus karfin sihiri ayanzu
don haka dolene ka zamo jagoran wannan
tafiya.da za'ayi don samo abubuwa guda uku
wadanda dasune zan kera kubar muftahul zarbil
wacce bude fadar saukatul askur ta sarki azmul
gallar
don na dauko kundun tsatsubansa
kaikuma markahus sabus nasan kafisu
hikima,rashin tsoro da juriya
domin gado kayi wajen mahaifinka
larkatul bin sabus
lallai kaine jarumin wannan tafiya da za'ayi
kafin n gaya muku abubuwan da zaku samo
mini
kuma na sallameku inda akwai mai tambaya
yayi tambayar sa naji
gaba dayansu sukayi shiru sai markahus sabus
yace
ya shugabana tambaya ta guda biyu ce kacal
inaso kayi mana bayani akan wanene azmul
gallar
tambaya ta biyu itace dama akwai wani kundun
tsatsuban daban banda naka
wanda su jafar suka bude?
kodajin wadannan tambayoyi sai shamharu yayi
murmushi yace
gaisheka dan masu hikima hakika kayi
tambayoyi masu amfani
saidai basu da mahimmanci acikin wannan
tafiya da zakuyi
ku sni cewa
sarki azmul gallar wani basarake ne dake mulkin
wata babbar duniya
daga cikin duniyoyin sama
shikuwa kundun tsatsuba guda uku ne
akwai kundi nafarko
wato nawa wanda su jafar suke karantawa
sannan akwai kundi na biyu wanda ahalin yanzu
su ruziyal suke karanta wa
shikuwa kundi na uku
yana nan an kammala kuma an ajiyeshi
acikin fadar azmul gallar
acan duniyar sama.wannan kundin ne wanda
nakeso naje na dauko
amma dole saina mallaki kubar miftahul zarbil
wacce da taimakon kune zan kerata
abu na farko da zaku tafi nema shine
narkakken dutsen da yafi kowanne dutse girma
aduniya
shidai wannan yanzu haka yana can wani tsubiri
da ake kira narul mahut
acan kusa da karshen duniya bangon kudu
kuyi sani cewa babu komai awannan tsauni face
duwatsu kala kala wadanda akarkashinsu
wutace takeci
fiye da shekara dubu arɓa'in
duk shekara sai daya daga cikin duwatsun yayi
bindiga ya tarwatse saidai kaga tafasasshen
dutse
ya cika dajin gaba daya ya zama kamar teku
idan kukayi rashin sa'a kukaje wannan tsubiri
alokacin da daya daga cikin duwatsun ua fashe
kuma narkewa zakuyi saboda tsananin zafin
dajin
dolene kuje inda wannan babban dutse yake
wanda yafi sauran girma kuyi haka akansa zira'i
dubu arba'in
sannan ku debo narkakken dutsen da kuka tarar
ku kawo mini
abu na biyu da zaku kawo mini shine dutsen
wutar
dake duniyar ku zuwa wannan duniya tafiyace
ta shekara dubu arba'in amma zan sanyaku
acikin sundukin tsafi
wanda zai kaiku acikin kwanaki hudu
a inda zaku debo wannan dutsen wuta akwai
wasu
halittu masu kama d birrai
hikimar kuce kawai zata kwace ku ahannunsu
har ku iya debo dutsen wutar ku baro duniyar su
abu na uku da zaku debo shine rabin ruwan
tekun duniya
nasan zakuyi mamaki kuce tayaya zaku iya debo
wannan ruwa
to ku sani cewa zan baku wani siririn bututun
tsafi
wanda dashine zaku tafi tsakiyar bahar zulmus
ku sani cewa ita bahar zulmus itace cibiyar
dukkanin tekunan duniya
anan ne zaku tsoma bututun tsafin dazan baku
kuna tsomashi zakuga ruwa yayi tsiri
yana tafiya sama
,asaman ne ruwan yana rikida yana zama hayaki
sai ruwan yayi kwana arba'in yana tsiri asaman
shikuwa wannan hayakin gaba dayansa zai
koma
cikin bututun dana baku ya rufekansa
kuma shine rabin ruwan tekun duniya
indai kuka sami
naaarar kawo mini shi sai anyi wahalar ruwan
sha aduniyarku
domin tekuna da koguna da koramai zasu kafe
d yawansu
koda shamharu yazo nan azancensa saiya
dauko abubuwa guda uku ya ajiye agabansu
markahus sabus,abu na farko shine gatari
wanda aka kerashi
da lu'u lu'u
abu na biyu sundukin tsafine abu na uku kuwa
shine bututun tsafi
shamharu yace
ga kayan aikin nan na baku yanzu zan hadaku
da
bokin tafiya wanda dashi zakuje wadannan
gurare gaba da ya
kafin wani daga Cikin su markahus sabus yace
wani abu
tuni shamharu ya kira wani aljani waishi
darmazulu
take aljani darmazulu ya bayyana.
MATSATSUBI B PART 7
Author:-ABDL'AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:-HABIBULLAH KBR
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Durmazulu yakasance gabjejen gaske domin ya
ninka shikansa shamharu
agirma sau goma
yana da fuka fukai guda miliyan daya
guda dubu dari biyar akwibinsa na hagu
dari biyar akwibinsa na dama
durmazulu n iya zuwa duniyar kasa daga fadar
boka shamharu ta baharzus
adakika arb'in
duk duniya babu wani aljani mai karfin gudunsa
awannan lokaci
shamharu ya dubi durmazulu yace
na umarceka daka dauki su markahus sabus da
kayan aikinsu
ku tafi izuwa wuraren nan uku
don samo mini mahadin kera kubar miftahul
zarbil
kodajin haka sai durmazulu yace
angama ya shugabana
kaine MATSATSUBI uban KUNDUN TSATSUBA
ita kanta TSATSUBAR IDAN TA GANKA
FIRGICEWA TAKE
shamharu yayi dariya saboda jin dadin wannan
kirari da aljanin yayi masa
sannan yace
kaidai bari kawai ai har yanzu da saurana domin
sai kun kawo min wadannan abubuwa uku
sannan zan zan cika MATSATSUBI
uban TSATSUBA
kafin shamharu ya gama rufe bakinsa tuni aljani
durmazulu
ya suri su markahus sabus ya dora abayansa
harma ya hada da samaratu
saida shamharu ya fisgota
ya ajiyeta kasa yana mai cewa banda wannan
durmazulu y sake debo kayan aikinsu markahus
sabus
guda uku ya azasu abayansa sannan ya bude
fukafukansa
gaba daya guda miliyan daya ya tashi sama
ya ratsa ta cikin saman ginin fadar baharzus
kamar haske sannan ya cilla da gudu ya iso
duniya su jafar inda za'a samo wadannan
abubuwa
guda uku
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU TSAKANIN
SU MARKAHUS SABUS DA BOKA SHAMHARU
SHAHARARRE ACAN FADARSA TA BAHAR ZUS
WACCE KE SARARIN SAMANIYA
Al'amarin su sarki hudes kuwa bayan sun dauke
jarumi hubairu
daga birnin tehran sa'adda aka fafata kazamin
yaki tsakanin sarki lu'umanu mai rai dubu
sai suka tafi dasu izuwa birnin sarki hudes
har aka sauka agidan sarautar gimbiya sima
bata farfadoba
saukarsu keda wuya saiga abtarul hudes tsaye
abakin kofar fada kamar dama yasan da
zuwansu
koda jarumi hubairu ya hango abtarul hudes
sai ya rugo gareshi suka rungume juna cikin
farin ciki
nandai aka dunguma gaba daya aka shiga cikin
fadar
aka zazzauna abtarul hudes ya kawowa hubairu
da
kuddaru abinci da abin sha irin nasu na
bil'adama
suka kimtsa cikinsu awannan rana dai babu
wanda yafi waziri kuddaru farin ciki
saboda ganin ya kubuta
daga hannun sarki lu'umanu saidai har yanzu
hankalinsa
nakan gimbiya sima wacce aka shimfide ta
bisa wata kujera akwance cikin halin barci
koda aljani abtarul hudes ya ga cewa waziri
kuddaru
na cikin damuwa bisa halin da sima ke ciki
sai ya dubeshi yayi murmushi yace
yakai kuddaru ka kwantar da hankalinka
ka sani cewa babu
abinda zai taba lafiyar sarauniyarka gimbiya
sima
lallai tana bukatar addu'a sosai domin sarki
lu'umanu
ya juyar mata da kwakwalwa koda jin wannan
batu sai jarumi hubairu ya
yi ajiyar numfashi yace
haba nifa mamakin yadda sima taso ta hallakani
da hannunta
alhalin ta kasance mai matukar kaunata jini da
tsoka
hakika sarki lu'umanu ya kasance hatsabibin
gaske
hubairu na gama fadin haka kenan sukaga
sarki hudes tareda manyan malaman garin
sunyiwa sima
kawanya suna karanta addu'o'i suna tofa mata
bayan kamar dakika arba'in da kammala
addu'o'in
sai 'yan yatsun hannun gimbiya sima suka fara
motsi
daga can kuma sai tayi attishawa sau uku
ta mike zumbur tana mai fadin
innalillahi wa inna ilaihirra ji'un
gaba daya musulman aljanun suka dauka da
alhamdulillah
cikin farin ciki abtarul hudes ya rungume
hubairu yana. cewa
barkanmu masoyiyarka ta sami lafiya
koda gimbiya sima ta kyallara ido taga kuddaru
da jarumi hubairu
saita cika da tsananin mamaki
cikin murmushi ta dubi kuddaru tace
yakai kuddaru
yaushene zamu koma gidane?
kuma nan inane?
waziri kuddaru ya rugo gareta ya rissina yana
mai kwasar gaisuwa yace
ya shugabata kiyi sani cewa abubuwa da dama
sun faru
abaya tsawon kwanaki masu yawa
bakisan da faruwarsuba
don bakya cikin hayyacinki labarine mai tsawo
wanda ya isa a rubuta littafi babba akansa
yanzu dai saimu godewa allah tunda mun samu
kanmu
sai kuma batun komawa birnin luharim kici
gaba da mulkinki sima ta sauko saga kan
kujerar. da take zaune ta ruga ga jarumi hubairu
suka rungume juna cikin farin ciki
her suna zubarda hawaye asannan ne sarki
hudes ya taho garesu
koda ganinsa sai hubairu ya rissina yayi godiya
bisa taimakon gaggawan da ya basu ya ceci
rayuwarsu
daga hannun sarki lu'umanu
sarki hudes yayi murmushi yace
yakai wannan jarumi kayi sani cewa
bani zakayiwa godiyaba allah zaka godewa
ka sani cewa ya zama wajibi agareni na yaki
mushrikai adoron kasa, kuma bazan gusheba
ina wannan aiki
harsai ajalina. ya riskeni, yanzu babu abinda
zakuyi
face ku tafi izuwa birnin laharim don a daura
aurenku acan
amma wannan tafiya bazata yiwuba face na
baku
kyakykyawan tsaro kuma dolene ku rike
wadansu addu'o'i wadanda zakuyita yinsu harku
isa can birnin luharim
akwai wadansu 'yan kyaututtuka da nake son na
baku na wadansu
littattafan addini dana tarihi da kuma wadansu
sitturu da kayan ado amatsayin tawa
gudunmawar
ta aurenku wadannan kayayyaki na can ajiye
agidan ajiye kayan tarihin kasarnan
don haka saiku saurara na aika aje a debo muku
kayan nanda rabin sa'a
domin wajen nada dan nisa wani garine da ake
kira madinatul auzal
kodajin wannan batu sai gimbiya sima ta cika d
farinciki tace
yakai wannan sarki kayi sani cewa
nakasance mai matukar sha'awar tafiya bisa
doron kasa
don na morewa idanuna kallon abubuwan
al'ajabi dana tarihi
don haka zanso ace ka shirya mana wannan
tafiyar bisa dawakai muje birnin madinatul auzal
naga wannan gida na kayan tarihin ku da
idanuna
sarki hudes yayi murmushi yace
ai wannan mai saukine saidai kawai maimakon
aje madinatul auzal acikin rabin sa'a
sai anyi sa'a uku
sarki hudes ya dubi dansa abtarul hudes yace
yakai dana ka sani cewa kai zan baiwa jagoran
wannan tafiya
kuma zan hadaka da dakaru dubu goma don ku
tsare lafiyarsu gimbiy sima
don haka tabbas nasan sai makiya sun biyo
bayanku
nantake sarki hudes ya kira sarkin kira
aljani ikmal yace
yaje ya kera sabon keken doki mai karko sosai
da zallan karfe
wanda ingarman dawakai shida zasu ja
ikmal ya rissina yace
angamayq shugabana, kamar walkiya ikmal ya
bace shikuma sarki hudes saiya shiga cikin
turakarsa
ya dauko rantsatstsiyar takobinsa ta yaki
ya baiwa abtarul hudes
yace
ga wannan ka tafi da ita zatayi maka amfani
matuka
abtarul hudes ya karbi takobin cikin murna
ya ratayata akafadarsa dama ya dade yanason
abashi aron takobin amma anki
itadai wannan takobi ta sarki hudes na dauke da
rubutun wasu addu'o'i guda dari ba daya
addu'o'in gaba daya na neman tsarine
bisa shaidanu
da kuma samun nasara akansu
tun sa'adda sarki hudes ya mallaki wannan
takobi bai taba
jagorantar yaki anyi galaba akansa ba
saidai a gudu abarshi
bayan kamar dakika dari hudu da sittin
da tafiyar sarkin kira aljani ikmal
sai gashi ya dawo dauke da sabon keken doki
na karfe zalla
mai kyan gaske harda kosassun dawakai guda
shida daure
ajiki bisa tafin hannunsa
ikmal ya ajiye hannunsa akas ahankali dawakan
nan suka ja keken dokin suka sauka
daga kan tafin hannunsa suka tsaya kyam awaje
guda
koda gimbiya sima da jarumi hubairu sukaga
keken dokin saiya yi matukar basu sha'awa
suka hau dudduba keken dokin
ba tareda bata lokaciba sarki hudes yayi
bankwana
dasu hubairu kuma yayi musu addu'ar tsari
domin daga can birnin madinatul auzal zasu
wucene birnin luharim inda za'a daura aurensu
hubairu da gimbiya sima suka shiga cikin keken
dokin
shikuwa kuddaru saiya hau kan daya daga cikin
dawakan
keken dokin ya zauna take aka ware dakarun
musulunci
guda dubu goma wadanda zasuyi musu rakiya
har izuwa can birnin luharim
sarki hudes ya raba dakarun kaso uku
kashi na farko suka tsaya a sama gaban keken
dokin su hubairu
kaso na biyu agefe da gefen keken dokin
kaso na uku kuma bayan keken dokin
ba tareda bata lokaciba aka kama hanya
akayita tafiya sauri sauri gudu gudu
don a isa birnin madinatul aulaz inda kayan
tarihi suke da wuri
saida akayi rabin tafiya cikin kwanciyar hankali
ya zamana jarumi hubairu da gimbiya sima sun
shagala suna ta yin hirarsu ta ma'abota soyayya
a wannan lokaci aljani abtarul hudes na saman
keken dokin
yana kada fuka fukansa hannunsa na dama na
dafe da rantsatstsiyar takobinsa
kuma yana kalle kalle da waige waige don
tabbatar da tsaro
koda akazo tsakiyar wata gada wacce kasanta
ramine mai zurfi
sai dawakan nan guda shida sukayi turjiya
suka daga kafafuwansu sama cikin alamun
razana
suna masu son juyawa da baya, al'amarin daya
baiwa su abtarul hudes mamaki kenan
don basu san dalili ba hubairu da gimbiya sima
kuwa wadanda suka shagala da hirar soyayya
sai sukaji keken dokin yayi girgiza kuma an
tsaya cak
cikin fargaba suka leko waje ta cikin tagar keken
dokin don suga abinda ke faruwa
ashe gungun dakarun bakaken aljanu ne suka
tsorata
dawakan wadanda suka baiyana agabansu
kamar walkiya.
A DAI-DAI NAN LITTAFI NA UKU YA KARE, DON HAKA SAI KU SAURAREMU RANAR LARABA DOMIN JIN CIGABA☝️☝️✍️✍️✍️🙏🙏
FATAN ALHERI.
DOCUMENT COMPILED BY SHURAIHU USMAN
TYPING HABIBULLAH MUHAMMAD KABARA
POSTED BY NAJIBULLAH MUHAMMAD
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On MATSATSUBI BOOK 3
avatar
abasu-kala

9 months ago

Reply

Good really enjoy the book waiting for Miftahul Zarbil

Please Login or Register in order to submit comment