Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi hatsarin bansan inda kai na ya ke ba,amman kiyi hak'uri da abinda na yi miki.....


"Don Allah kayi hak'uri wallahi ban san ma anyi rasuwa ba,amman ka yi hak'uri".



Daga nan Masoyan suka cigaba da hirarsu cikin so da k'aunar junansu.




***
Hutun Jameela a kano ya yi mata matuk'ar dad'i sosai,don tana samun kulawa so da k'auna awajen masoyinta harma da y'an uwanta,kulawar da bata samu a da ba yanzu ne ta ke samu,ga wata shak'uwa mai k'arfin gaske da ta shiga tsakaninsu.

Sai dai abinda bata sani ba shine mahaifinta har ya fad'awa Inna tasan komai,sai dai fa Inna ta buga tsalle tace babu wanda ya isa ya yi wa y'arta Auren dole,wannan munafukin Auren ma du kuncesa domin kuwa babu yadda za'ayi su yadda da wannan had'in,babu yadda mahaifin Jameela ya iya, don haka yaja bakinsa ya yi shiru bai ce komai ba.


Abinda bai sai ni shine?Matarsa tasan komai a game da abinda ya faru don duk wayar da ya ke yi tana lab'ewa ta ji me yake cewa,don haka ta shirya yadda zasu b'ullowa lamarin ita da k'aninta Sooraj.




" kin san Allah babu wanda ya isa ya hanani Auren Jameela matuk'ar kuwa aka hanani to komai ma zai faru,don ko kece kika hanani Auren Jameela to ki kuka da kanki"!ya juyo yana nuna yayar tashi da hannunsa.


Tana matuk'ar mamakin yadda aka yi Sooraj ya ke mugun son Jameela don ta yi imani Sooraj zai iya ki sa akan hanashi Auren Jameela.



"Ni shawarata kawai idan ta dawo ku gudu da Jameela don hakan shine zai kawo k'arshen komai,don na fuskanci Uban nata mata lallab'ata kawai ya ke yi bason Auren ya ke yi ba."


"Babu inda zan gudu da ita?ko su so?ko kada su so?bai dameni ba ya zama dole Jameela ta zama mallakina,haba shekara nawa ina dakon yawo da soyayyarta acikin zuciyata kuma na iya hak'ura da Aurena da ke kanta,to yanzu ya zama dole Jameela ta zama mallakina na gaya miki.


Sai da ya kusa buge Yayar tashi don tsabar b'acin ran da Sooraj ya ke ciki,don a rayuwarsa babu abinda ya keso Irin Jameela,ko uwar da ta haifeshi bai damu da ita ba kamar Jameela,donshi a ganinsa Jameela ita ce rayuwarsa,don ko yanzu Jameela ta mutu to shima ya zama gawa.


🤔Ni kuwa Ummu Maher na ce,Son ma so wani k'oshin wahala.







***
Yaya Sadiq zan cen da nake gaya maka ba k'arya bane Mahaifina ya yi min Auren dole,a tunaninsa ban sani ba don na dad'e da sanin wannan labarin kawai sai bana nuna wa ne,kuma nasan kud'in mahaifina ne ya rud'esu,Amman mahaifina ya dad'e da Aurar dani........



" What Jameela kin san me ki ke cewa kuwa?"






Please kuyi hak'uri nayi tyiping kad'an rasuwa aka yimin ne.🙏🏻




Ummu Maher ce🤞🏻💚✍️
*_🍀JÁMÈÈLÈR🍀_*



By

_Ummu Maher(Miss green)🍀_

_Wattpad@Rabiatu222_




_24/25_

Destiny
_______

Hankalin Sadiq ya tashi sosai akan maganar da na gaya masa,sai da mukayi sati 1 ni da Sadiq muna wasan b'uya don tunda mukayi wannan maganar dashi hankalinsa ya yi mummunan tashi don arayuwarsa bayan Allah da manzon da kuma iyayensa babu wata halitta da ya keso kamar Jamila akullum burinsa bai wuce yaga ya mallaki Jamila a matsayin matarsa ba.





....sai yamma ya sauka a garin Bauchi da kwatancen da Inna ta bashi har yazo katafaren gidanmu kai tsaye ya shiga gidan ba tare da wanu tunani ba,me gadin Gidan ne ya taso da sauri yana cewa"Tsaya Mlm ina zakaje?wajen wa za ka je aciki ayi maka iso?had'e rai Sadiq ya yi sannan ya ce megidan na ke nema,ko baya nanne?"A'ah yana nan bari in tambayo jira ni ina zuwa.



"Alhaji ka yi bak'o a waje yace ayi mishi iso".
" kace waye"?
"To Alhaji"

Ba,afi minti na ba ya dawo ya ce" wai Sadiq ne daga kano d'an uwansu Jamila"

Alhaji ya ce ya shigo dashi amman yana mamakin wannan waye haka da daga kano?kodai wani abu ne ya samu Jamilar sa?..


"Assalamu Alaikum"
Da sauri Alhaji ya d'ago kansa yana kallon Sadiq yana hango wata fuska a fuskar Sadiq tabbas yasan me irin wannan fuskar.


Bayan sun gaisa ne Sadiq ya yi mai cikakken bayaninsa nan Alhaji ya ke cewa tabbas yasan fuskar Sadiq don tun yana k'arami rabonshi dashi ya gane d'ana ga yayan Mahaifiyar Jamila.


Sadiq bai b'ata lokaci ba ya fara gabatar da maganar da ta kawo sa don gani ya keyi Jamila ta yi hakanne don ba ta sonshi.



Lokaci 1 idon Abba na ya dawo kan Sadiq ya shaida masa ya riga da ya yiwa Jamila miji don haka ya yi hak'uri,hankalin Sadiq ya tashi sosai da ya yi niyyar kwana A Bauchi Amman babu abinda zaisa ya cigaba da zama a garin Bauchi don jin garin ya ke yi kamar an zuba wuta mai zafi.


Bayan sunyi Sallama da Abbana Sadiq ya bud'e murfin


Duk maganar da Mahaifina sukayi da Sadiq Sooraj ya ji shida Yayar sa,don haka ayanzu sun shirya abinda za suyi wa Sadiq,don gani suke yi sunyi sakaci da har sukabar wani ya ce yana son Jamila har ya iya shigowa gidansu da sunan maganar Neman Aure.

A kullum hankalinsu yana kan dukiyar da Mahaifina ya ke da ita don burinsu ace su kad'ai ne mallakinta.

Don haka tun kafin Sadiq ya fito suka sace tayar motar yadda koda hatsari ya kama za,ayi mummunan hatsari.

Ni kuwa Ummu Maher na CE Allah ka tsaremu da wannan mummunan zuciyar ka bamu Rayuwa mai kyau har k'arshen rayuwarmu.




Innalillahi wa inna Ilaihi Raji'un lallai dukkan mai rai mamaci ne da sauri na yarda wayata a hannuna Inna tana ta magana Amman ban San me ta ke cewa ba sai tashi na yi a gadon asibiti na suma.



Ina tashi na fara kiran sunan Allah,kwalla na fitowa a hankali daga cikin idanuwa,yanzu shikkenan ta tabbata Sadiq ya mutu ya bar wannan duniyar?.


Inna ma kuka ta ke yi tana gogemun hawayen fuskata,Gefena kuma da k'annen Sadiq suma kukan su ke yi,alokacin ne na tabbatar da mutuwar Sadiq kuka na ke yi kamar raina zai fita.da k'er likitoci suka yimin allurar bacci.




Sai da safe na tashi ina nayi wani mummunan mafarki wai ina gudu zan fad'a wani rami ina juyawa sai na hango Abbana ya fad'a gaba d'aya ina ihu ina kiran sunan Abbana dai dai nan na farka ina haki.


Da Sauri Inna ta taso tana tambayata na kasa bata amsa,waya ta ce ta fara ringing Inna ta mik'omin na amsa da k'er na kai wayar tawa kunne.



"Please ke ce Jamila"?.


Da k'er na CE" eh ni CE"?



"To daman Mahaifinki Allah ne Allah ya yiwa rasuwa jiya y'an fashi suka shigo Gidan.........




Wani ihu na saka Inna na zubamin ruwan shayi a Kofi.




😢😭The destiny.

Lallai wannan ita ce k'addara Allah yasa muci dukkanin kaddarorinmu n rayuwa Amin.








*Ummu Maher CE*


Vote
Share
And
Comments👏🏼
*_📲📲Tyiping_*
_ဎကကဎ ကခիer_


*_🏮JÂMÊÊLÊR_🏮*




Ña
_Ummu Maher(Miss green)💚☘️_



_Fans d'in Jamila kuyi hakuri abubuwane sukayi min yawa shiyyasa bana samun damar kawo muku shi amman yanzu zan cigaba_




_26//627_

"Jamila na yi kukan rashin mahaifina sosai don sai da na yi kusan wata 2 bana magana sai Hm sai A'a,amman saboda rashin imani irin na Mama Asiya ta saka aka b'atar dani b'at a duniya sai tsintar kaina na yi a wannan duniyar".


" Lallai Namesake kin had'u da jarrabawa kala²sai dai ince Allah ya sa muci dukkanin k'addarorinmu baki 1,don labarinki ya k'ara koyar dani sanin waye d'an adam don rayuwar nan ba matabbata ba bace.


.......
*Cigaban Labari*
Masu karatu idan kuka ji na ce Jamcy ina nufin wacce ta fara bada labarinta,idan kuma kuka ji na ce Jamey to ina nufin ta k'arshen.

To mu fantama don muga wata wainar ake toyawa gidan Mlm wanda ya taimaki Jamcy da Jamey.



°•°•° • °•°•°
Mama Amarya ita ce Amaryar Mlm mace me hankali da sanin yakamata,Inna kuma itace Uwargidan Mlm mata me son abin duniya da rashin mutunta mutane,Inna Mara kuma ita ce y'ar tsakiya kinfi Amarya kenan🙄🥴,macece me iya takunta da shegen wayo ammanfa idan ta samu waje za'a cuceka da ita don bata da imani ko kad'an.



"Wallahi Mlm yarannan da ka kwaso zasu iya haifar mana da matsaloli don haka ka mayar dasu inda suka fito tun wuri,don kasan Allah duk yadda a kayi duk cikin shege suka yi suka shigo duniya".....



" Kar ki kuskura ki k'ara kiran wad'annan yaran da wannan kalmar koma me sukayi zan rik'esu tsakani na da Allah don bazan bati rayuwarsu ta lalace ba,yadda zan rik'e y'ay'a ns haka zan rik'e wad'annan yaran"...


Yana kaiwa nan ya yi tafiyarsa yana Allah wadai da halin Uwargidan nasa wato Inna,don Inna irin mutanen nanne masu son zuciya da kuma wulak'anta d'an adam.


Kai tsaye ya wuce sashen Hajiya Rabi wato Amaryarsa don yasan anan ne kawai zai iya samun farin ciki,don itama Inna Marak'isiyya ya gama gano ta yanzu don kanwa ce uwar had'e wato fuska 2.



Yana shiga wani k'amshi me dad'i ya daki hancinsa har ya shiga babbsn farlonta yana jin wannan k'amshi me dad'i,Jamcy ya hango tana turare farlon da turaren wuta wanda aka kunna na Bunner,Sannu da zuwa Ta yi mishi ya amsa cikin fara'a sannan ya tambayeta y'ar uwarta.


"Baba Jamey tana Sallah Hajiya kuma tana ciki". Ta fad'i hakan cikin jin kunya.

Har ransa yaji son yaran don suna da Biyayya kwarai,yana fatan ya samu lokaci yaji labarin yaran don ya samu ya mayar dasu ga iyayensu.


Sosai yaji dad'in ganawa da Hajiya Rabi ta ce" Malam wannan yaran da ka ke ganinsu Ajiyar Allah ce, kuma amana ce a hannunmu don haka don Allah Mlm inason muci gaba da yi musu addu'a kafin komai ya dai dai ta".




*Bayan wasu watanni*

Sosai Mlm ya tausayawa su Jamila da labarinsu da suka bashi kuma insha Allah zaiyi iya bakin k'ok'arinshi ganin ya dai daita komai cikin hikima.


......
Muna zaune muna shan hira da Hajiya Rabi wacce ayanzu muke ce mata Mami kawai sai mukaji Sallamar Inna Ladi wato y'ar tsakiya muka gaisheta cikin fara'a itama ta amsa cikin fara'a har tana tsokanarmu wai Y'ay'an Mami ta samu y'ay'a daga sama to tunda haka ne itama d'aya ta dawo wajenta,cikin hikima muka fara gano halin Inna ladi don mutunce me k'ananan magana don haka muma muka biye mata muna ta washe baki.


Can kuma sai cewa ta yi"Hmm Wallahi Rabi na rasa hali irin na Inna wai ace tunda yarannan suka zo babu wata magana me dad'i da ta ke shiga tsakaninsu,jiya fa ina ji ita wannan y'ar lukutar ta nuna Jamcy jiya ana rabon abincin almajirai wasu basu samu ba Ta ce bari a k'ara dafa musu wani kawai sai cewa ta yi,wai tunda bana ubansu bane kada ta k'ara dafa wani ke zagi dai har da ce mats wai wa yasa ni ma ko karuwai ne su".....


Da sauri Hajiya Rabi ta ce"Kai Haba Hajiya Ladi wannnan fa ba magana bace koda ma ta ce hakan bai kamata ki fad'i haka ba don Allàh akiyaye".


Sosai Hajiya Ladi ta ji haushi don a fuskarta ta nuna fushi sosai,amman bata ce komai ba ta yi shiru,sai cewa ta yi"Hava Hajiya Rabi be kyautu ki ce haka ba,saboda shi icce tun yana d'anye ake tankwarashi gwara ayiwa Hajiya Babba magana don ta daina"......


"Haba Hajiya Ladi kinfi kowa sanin wacece Hajiya Babba tunda itace babbarmu amman bai dace muyi mata magana ba,Allah dai ya kyauta".



Tana fad'in haka ta tashi ta shiga d'akinta, kawai sai mukaji ta ce K'asa²" Hmm tana wani tafiya tana juya mazaunai d'uwawu kamar an hura balo🤨shiyyasa miji ya na ne mata".tana kaiwa nan itama ta tashi Fuu ta yi sashenta.




Muka kalli juna muka saki dariya duk da ada hankalinmu a tashe ya ke don munji babu dad'i kirawo mu da karuwai da a kayi,amman sai gamu muna dariya daman Manya ma suna kishi😄😄.



Ni kuwa Ummu Maher na ce ai kishi Halak ne amman fa na ilimi bana jahilci ba.




*Ummu Maher ce*



*Vote*
*Share*
And
*Comments*
*_📲Tyiping📲_*


ပကကပ ကခիér

*_🏮🌹JÂMÊÊLÊR🌹🏮_*


Ña
_Ummu Maher(Miss green)_☘️






_28to30_



......"Jamcy!Jamcy!!kitashi muna cen muna ta aiki,Hajiya tana nemanki muk'arasa aikin."


Da sauri na tashi ina mik'a harda Hamma,yau na yi mafarkin y'an gidanmu kuma wai suna wani hali na nema na suna bina suna kuka wai in dawo gida......"Haba Jamcy ina tashinki kinyi min shiru please ki tashi mana".Jamey ta fad'i hakan kamar zata yi kuka.



Aiki muke sosai Ashe yau Twins d'in Mami zasu dawo don ta dad'e tana bamu labarinsu sunyi Aure su dukkansu suna Tunisia Bashir Wanda shine (Hussain) sai Ahmad (Hassan)shekararsu 2yanzu da Aure suna cen da matansu suna wani course ne da ya ke su dukkansu acan suka samu aiki Amman yanzu zasu dinga yi a Nigeria d'aya Likita ne d'aya kuma Sojane me zaman kansa, haka suka taso kowa da burinsa tun suna k'ananu shiyyasa Mlm wato mahaifinsu ya basu kwarin guiwar cika wad'annan burikan nasu.


Har da decoration ranar sai da akayi ya k'atar sosai,Su Safiya da Anty Rabi'atu duk sunzo suma y'ay'an Mami ne daman y'ay'anta Hud'u 4, 2 maza mata 2.


Haka Allah ya tsara mata Haihuwarta ita ba me yawan Haihuwa bace,yanzu Shekararta 48 da Aure sanda akayi mata Aure Shekararta 11 da yake su Fulani da Wuri suke Aure sai da tayi Shekara 5 sannan ta haihu Twins duk maza alokacin tana da shekara 21,Sai da ta yi shekara 5 again sannan ta haihu ta haifi Mace Safiya sannan tsakanin Safiya da Rabi shekara 4 tun daga nan bata k'ara Haihuwa ba.



Ayanzu Bashir da Ahmad suna da shekara 33 zuwa da 4,Safiyya kuma 28 tana Aure a Sudan y'ay'anta 3,sai Rabi 24 tana da d'a 1 ita kuma gidanta babu nisa da gidansu.



Hajiya Ladi ce kawai bata da d'a don bata tab'a Haihuwa ba,Inna Uwargida Y'ay'anta 6 uku maza uku mata duk sunyi Aure da y'ay'ansu har an Aurar da wasu.





Less orange and Red Mami ta d'inka mana Wanda yasha adon stone work da ya ke Buba akayi mana sai mukayi kamar Twins har Lalle ja ranar sai da akayi mana harda Kitso.




Mlm ne ya shiga kwala mana kira har ya k'arasa shigowa farlon yana cewa"Y'an biyuna kuna inane kufito zaku rakani Airport taro Mazaje".daman haka ya ke kiran Y'an biyun nashi.



Da sauri muka d'auko hijabanmu Red me kyau irin Hijabin yayi da ake yi yanzu,sunsha guga Wow zokaga yadda sukayi kyau,Jamcy da kuma Jamey abin burgewa suka mak'ala glass d'insu irin me y'ar zaren nan abin ba'acewa komai.



Wani Red d'in High Hill Wanda yasha adon Black and Red kasancewarsu duk masu matsakaicin tsayi ne,don haka sai suka fito gwanin sha'awa.





Around 5:pm
_______



Muka sauka a airport d'in me kyau da tsari iska me tare da wata ni'ima a hankali muka fito daga cikin motar cikin happy don muna tafiya muna shan hira a motar Malam.



Kusan sandarewa mukayi a wajen tsabar kyau da haiba na Mazajen Mlm kowannensu hannunsa sak'ale da matarsa sai dai tun daga nesa zaka hango banbancin kamanni a tsakanin Bashir da Ahmad,Bashir yana da tsayi kuma yana da jiki,Ahmad kuwa ba shida jiki sannan d'aya yafi d'aya haske Amman duk da haka suna kama.






Please kuyi hakuri ina tyiping kad'an jiki da jini😊👏👏👏.



*Ummu Maher ce*


*Vote*
Share
And
Comments👏

Hope🤗🤗ina gaida maaoyana a ko ina👏.
*_🍁☘️JAMILA☘️🍁_*



_True life story📗📙_




Na
_Ummu Maher(Miss green)☘️_



~Dedicated to Aisha Fulani Girl,and Hajara L Sadiq💋💋
Inayin ku over²~




🅿️34🟨35



"Wallahi matannan suna matuk'ar bamu haushi yadda kika San dabbobi haka suke kwata² basu San hakk'in d'an Adam ba,ni fa tunda Na ke basu tab'a yimin ko da kallon arzik'i ba."


Kallon Aunty Hamida mukeyi da mamaki wai matan yayyinsu basu tab'a koda yi musu kallon arzik'i ba abin yayi matuk'ar d'aure mana kai,gaskiya abinda wasu matan suke basa kyautatawa Na raba y'an uwa musamman uwa 1.





**** **** ****

"Malam lfy naga kayi tagumi haka?"
"Lfy klau Amman ba lauba ba?"

Shiru Mami ta yi don tasan ba komai ne ya ke d'agawa Mlm rai ba matuk'ar kuwa kaga ya shiga irin wannan halin to abin yayi yawa ne,"Rabi inason had'a Auren Bashir da Jamey Ahmad da Jamcy".


Da sauri Hjy ta tashi tsaye tare da dafe k'irjinta,tabbas tasan za'a Rina don yadda Twins d'in nata suka kafawa Y'ay'an nata idanu"Amman Mlm sune da bakinsu suka ce suna sonsu ko me?".


"Kwarai kuwa jiya da magrib suka sameni da wannan batun yanzu inason ki kirawomin su inji ta bakinsu idan suna sonsu shikkenan"ba don ran Mami yaso ba ta k'arasa zuwa farlonta,da Jamcy t fara cin karo tana yiwa Anty Hamida kitso suna ta hirarsu kamar daman sun San juna.




"Jamcy tashi daga kitsonnan ki kirawo y'ar uwarki Mlm yana kiranku"?.

Gabana ne ya fad'i Amman sai Na tashi Na kirawo Jamey da ta duk'ufa tana tunani,hawaye na tarar yana fitowa daga idanunta tausayi sosai ta bani na dafa ta sannan na CE" Haba Jamey ki daina sakawa kanki damuwa kowa da kika gani akwai k'addararsa a duniyarnan don haka kiyi hak'uri ki taso Mlm yana nemanmu".


"Jamcy a kullum ina tunowa ne da Mahaifina yana cen a kabarinsa ya kasa kwanciya saboda duk mutumin da yarasu abubuwa irin wad'annan suna faruwa zaki ga ya kasa kwanciya,ga shi momi wato matar Mahaifina ita da k'aninta sun gaje komai? Ga Sadiq d'ina sun kashe min shi " Sai na k'ara rushewa da kuka me cin rai.


"Kiyi hak'uri Jamcy ni da kaina da kika ganni kullm sai na yi tunanin yaya y'an uwana suke?Mahaifina?mahaifiyata?aminiyata Fatima? A wani hali suke ciki?don nasan yaya Saif da Aunty safiya suna cen sun bud'e sabuwar rayuwa don daman basa son ganina a duniyarsu."


Da k'er muka bawa kanmu hak'uri muka fita idanunmu jawur alamar munyi kuka harmun k'oshi,su Aunty Hamida suna farlo suka bimu da kallon tausayi har muka fita daga farlon.


Aunty Hamida ta ce "Wallahi Rabiatu yarannan suna bani tausayi tunda suka bani labarinsu,gaskiya duniyarnan akwai Abubuwa sosai a cikin ta".



Sai da Mlm ya fara mana da wa'azi sannan ya fad'a mana abinda yasa y kirawo mu,sannan ya k'ara da cewa kuma bazan d'aura muku Aure ba har sai kowaccenku ta had'a da iyayenta.


Kanmu har lokacin a dunkufe ya ke a k'asa,hawaye yana silalo mana,muna tunanin had'uwarmu da familynmu may be zasu zargemu da munje Neman maza ne yanzu duniya ta juya mana baya mun dawo.






Kuyi hak'uri bana jin dadi ne shiyyasa nake small² page.




*Vote*
Share
And comments




Ummu Maher (Miss green)
*_🍁☘️JAMILA☘️🍁_*


_True life tsory_📗📙





Na
_Ummu Maher(Miss green)☘️_



*_please don Allah kuyi hak'uri rashin kawo muku JAMILA kwana biyu bana tyiping abubuwa ne sukayimin yawa,kuma zakuga spell din sunan Ya koma JAMILA,maimakon Jameeler complen d'in mutane ne mussaman fans d'in kuyi hak'uri insha Allah yanzu zamu cigaba_*.



_31&32_

``````•kallon² muka shiga yi don da sauri suka tsugunna suna gaishe da Mlm,bakinshi ya k'i rufuwa sai murna ya ke da ganin y'ay'an nashi,Ahamd ne ya fara kallonmu mussaman Jamcy da ya kasa d'auke idonsa a kanta,ita ma Jamey Bashir ne ya kafe ta da ido kamar wani maye,da sauri Amira matar Ahmad ta CE"Mlm wad'annan kuma su waye?".


Da sauri Maryam ma ta CE"Wallahi nima tambayar da Na keso inyi kenan y'ar uwa kika Riga ni"?.


Murmushi Mlm ya yi don sun bashi mamaki sosai baba wacce ta gaishesa a cikin su Amman daga ganin yara sun fata tambayar su waye?


Juyowa yayi ya kalli Amira wacce kishinta ya fi fitowa a fili sannan ya CE"kada Ku damu da wad'annan suma y'ay'ana ne,y'ay'an d'an uwanane su da ya ke Cameron suka kawo min ziyara.


Masha Allah Twins d'in Mlm suka had'a baki wajen fad'a,ran matansu kuwa ya yi matuk'ar b'aci daga dawowarsu sai kuma a tare su da bak'in ciki,wad'annan y'ammata kamar flower tsabar kyau.


Ko da a kazo wajen shiga mota sai da a kayi d'an daru,don Mlm ne ya shiga gaba shi da Ahmad Sai Jamcy, ita kuwa Jamey da Bashir da kuma Amira da Maryam,dukkaninsu idan ka kallesu kamar an aiko musu da mutuwarsu tsabar bak'in ciki,don tun kafin mazajen nasu su d'aukesu zuwa Tunisia suka tsani Mlm mahaifin mazajensu don shi mutunne mai kamata gaskiya.




Rungume Mahaifiyarsu suka yi sosai su duka biyun suna me godewa Allah da suka samu mahaifiyarsu cikin k'oshin lfy,don a duniya suna matuk'ar son Mahaifiyarsu don Mami uwace tagari,tun tasowarsu basu tab'a jin CeCe kuce a tsakanin iyayen nasu ba,shiyyasa ma suke matuk'ar son mahaifiyarsu don akwai ta da ladabi da biyayya.



A wani yangance suka gaishe da surukar tasu suna wani k'arewa Gidan kallo,don babu k'arya Gidan ya yi kyau sosai,don tun Twins suna Tunisia suka aiko da kud'i aka k'ara gyare Gidan tsaf gwanin sha'awa.


Itama Mami ta kula da kallon k'urillar da yaran suke mata Amman ta watsar da su don tasan tun kafin suyi tafiya haka suke mata suyi ta kallon k'asan zaninta tun bata kawo komai har yanzu ta fara ganewa.




Wajen Inna Uwargida suka tafi suna gulmar surukar tasu don harga Allah har cikin ransu sun tsani surukar tasu,don babu abinda Mazajensu ba sa yiwa Mahaifiyarsu,wannan ne ya ke k'ara musu haushinta don sunyi su raba su Amman sun kasa,sai su kirawo inna Uwargida sau biyar ko Hajiya Ladi awaya ba su kirawo surukarsu sau 1 ba,don ma wani lokacin idan sunyi waya da mahaifiyarsu idan ta tambayi matan nasu su kirawo su su ba su wayar Shima ciki² suke amsawa don idan akwai wacce suka tsana to bai wuce Surukar tasu ba wato Mami, don haka sai suka k'ulla abota da su Inna Uwar gida,don daman duk wata gulma daga gurinsu ta ke fitowa shiyyasa suke zuwa wajensu.



Sosai Twins suka zage dantse suka ci Dinner da aka baje musu,ita kuwa Mami sai kallonsu ta ke cikin so da k'aunar y'ay'an Na ta.


Suna yi suna kallon y'an biyun Mlm Jamey da Jamcy Wanda har yanzu ba su saki jikinsu ba kasan cewar irin kallon da suke musu,don har yanzu les d'in nan lemon green d'inkin Riga da siket gashi ya d'an kama su,mussaman ma Jamcy ita CE me jiki.



Suna cikin cin abincin Hamida ta CE"Wai Ammi inasu Anty Amira suka shiga ne gashi ana cin abinci babu su."?


Rabiatu CE ta CE "Suna wajen Inna Uwargida kin San ita CE surukar ta su."

Ammi CE ta katsesu da cewa"wai ina ruwanku da inda suka shiga ne?kun bi kunsa ka yara a gaba da mitarku cen inda suka je ai za suci don da cen da nan duk 1 ne."

Tsit! sukayi ba su k'ara magana ba haushin matan yayyen nasu Na k'ona musu rai,don suna sane da yadda suke wulak'anta Mahaifiyarsu.



To su ma dai Twins d'in Na Ammi sunji haushi matuk'a ta yadda suke wulak'anta Mahaifiyarsu suna sane kawai ido suka saka musu don masu iya magana sunce shiru ma magana CE.




Muna gama cin abincin su Anty Maryam suka shigo suna jifanmu da mugun kallo,babu Wanda ya kulasu suka kalli Mazajen nasu sannan suka CE "Am: daman zamuje gidane muma mugana iyayenmu"?.


Banza suka yi musu sai da Mami ta CE" Ku yi tafiyarku ai dama dole kuma kuje gida".

Sun d'an ji dad'i kad'an don sun San indai ta mazajensu ne ko zasu kwana suna yi musu magana ba zasu amsa ba,Amman duk da haka Surukar tasu bata fita ba, suna fita suka fara gulmarta wai yanzu mazajensu sun zama remote control sai abinda uwarsu ta CE suyi shi su keyi.



Ko kafin dare mun share ko ina mun gyara tsaf har falo mun gyara harda b'angaren Twins d'in Mami tare mukayi aikin da su Anty Hamida yaransu tuni sunyi bacci.



"Jamcy kin kula da yadda wad'annan fitinannun Twins d'in suke bin mu da kallo Allah kamar Na yi fitsari a wando".



Dariya Jamcy ta yi sannan ta CE Ayya Jamey ni wallahi Na fiki tsorata dasu gasu da kyau kamar aljan......


Dariya sosai Anty Hamida ta ke sannan ta yi bud'a ta CE" ai insha Allah sai sun Aureku,Ku sharewa Mahaifiyarmu hawaye.



Kunya da nadamar maganar da mukayi suka hanamu d'ago idanu mu kalli Anty Hamidar da ke ta Smilling.






*Ummu Maher CE*
*_🍁☘️JAMILA☘️🍁_*




_True life story📗📙_



Na
_Rabi'atu B Abdullahi_
*Ummu Maher(Miss green)☘️*



Not edited......

🅿️36🟨37


Kallonmu kawai Mlm ya ke don yasan tunanin da muke yi bai wuce na had'uwa da danginmu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment